Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin abincin mu?ni dai gaskiya ka kira min ita ta same ni a kitchen yanzu".tace tana mikewa.

Dafe goshinsa yayi ya furzar da iska a bakin shi yace " huh my baby rigima ,ba kiyi break fast ba shine zaki shiga kitchen?"

"Eh ni na koshi ka kira min ita ".tace cikin shagwab'a harda gutun hawaye da ta kirkiro na dole.

Tashi yayi yaja hannunta ya suka fito parlourn direct kan dinning ya nufa da ita ya had'a mata tea yace ta shanye sannan ta shiga kitchen d'in.

Sai sakalci take masa shi kuma yakw biye mata yana ta lallab'ata yana bata tea a baki,har tasha mai d'an yawa sannan ta ture tace ya isheta a kira mata Maryam.

Kitchen d'in dake part d'insu ta shiga.

Shi kuma down stairs ya sauka ya kira wata maid mai suna Rossy yace taje ta kira mishi Maryam ta same shi a part nasu.


Maryam tana kwance taci kukanta ta gaji tana tsinewa Farhat tare da kudirin sai ta hana ta sukuni a gidan sai tasa ta zubar da hawayen da yafi wanda tasa ta zubar.

Rossy cetayi knocking a bakin k'ofa.saida ta gyara fuskanta sannan ta bataizinin shigowa.

Nan ta fada mata sak'on Farhan sannan ta juya ta fita.


Murmushi mai had'e da dariya ta fara tana cewa" i know!! Farhan loves me sai dai wannan devil d'in ce ta rufe masa ido da shaid'ancin ta.gashi ya kasa daurewa yana nemana ya bani hak'uri.zan koya mata hankali soon".

Tashi tayi a gurguje ta k'ara gyara fuskanta da tayi kuka sanna ta fice da sauri.

A parlour ta iske Farhan a zaune yana aiki a system d'inshi.

"My son gani" tace tana wani mak'e murya wai dam taja hankalin shi.

"Ki shiga kitchen ki taya my baby aiki"yace ba tare da ya d'ago ya kalleta ba.

Kasa motsi tayi daga inda take saima kafe shi tayi da idanunta,saboda tana kwankwanto koba dai-dai kunnuwanta suka ji mata abinda ya fad'a ba.

D'ago kanshi yayi ya kalleta jin bata motsa daga inda take ba yace " what are you waiting for,ko baki ji abinda na ce miki bane?"


Tafiya ta fara zuwa kitchen d'in ba tare da ta ce masa kala ba.zuciyarta na mata wani irin k'una.


Lalle Farhan ya gama da ita kuma ya nuna mata Farhat ta fita,ita da ta d'auka dan ya bat hak'uri ya kirata ashe wai saboda taya wannan bakar yarinyan aiki ya kirata kuma bayan yasan tunda take ko hanyan kitchen bata sani ba bare wani girki, duk masu aikin gidan nan ya rasa wa zaisa ya taimaka mata sai ita."i will show her" tace tana karasawa.


Tab'e bakin shi yayi ganin yanda take jan kafa kaman mai koyon tafiya.aikin gaban shi ya cigaba dayi ba tare da yabi takanta ba.

A bakin k'ofan kitchen d'in tayi tsaye tana kallon Farhat da ta juya baya tana ta aikinta.

"Ba kallona yace kizo ki tsaya kina yi ba,cewa yayi kizo kiyi min aiki".taji muryan Farhat tana mata magana ba tare da ta juyo ba.


Dogon tsaki Maryam taja tana hararan bayan farhat d'in tace ". Ke inba darajan Ya Farhan ba har kin isa ki taka inda nake bare har kiyi tunanin zaki sani aiki,nasan makircin kine wannan tunda Ya Farhan yasan bana shiga kitchen".

"Dad'ina dake akwai saurin fahimta,kaman kinsan nice nasa ya kirawo ki dan in taimaka miki kar aje gidan miji ana masa d'anyen tuwo.gashi kuma wacce bata da matsayin tasaki tako kitchen d'in ba".tace tare da juyowa tana mata murmushi.

Takaici ya hana Maryam maida mata martani.

"Shigo ki shafa min spices dana had'a da mai a jikin wannan naman".tace tana nuna mata kayan da yatsanta.

"Wannan ne kuma ko wannan nataccen ubanki ba isa ba".tajuya ta fice rai a matukar b'ace.

Farhat taji zafin zakin Abbanta da tayi amma ta shanye,saboda tasan koba komai itama ta d'ura mata takaici.

A tsanake Farhat ta kammala girkinta tsab harda juices da ta had'a masu dad'i.

Da ta fito Farha baya parlourn dan haka bathroom ta fada tayi wanka ta shirya cikin wani material d'inta fari kal da flowers blue a jiki,dan kunne da tsarka duk blue tasa na wani fashion desiner tayi matukar k'yau.down stairs ta nufa bayan ta fesa perfumes kusan kala biyar.

Tun kamin ta k'araso sauk'owa taji muryan muryan su Junaid suna ta hayaniya.

Zama tayi kusa da Farhan sannan suka gaisa da samarin.

Hira aka dasa da ita ba laifi yau ta saki jiki ba kaman kwanaki da suka zo ba.

Ana cikin hira ne Junaid yacewa Farhan " bro banga mutumiyarka bafa,kota koma ne?*

"Wace mutumiyata kuma ,do u mean Ummina?"

"Yes ita mana please bro ka shigar dani wajanta mana wallahi na dad'e cikin kaunarta ban fad'a mata bane saboda ina jiran right time but yanzu ganin ka da mata ya rusa min agender na na farko.please help me ".

Naseer da Farhan suka shek'e da dariya har suna tafawa Farhan yace "kaji min yaro ko kunya zaka ce dan ka ganni da mata,toh ni sa'anka ne".

"Dalla mallam yi min shuru dan kaga ina lallab'aka har kake wani ce min yaro,wata 6 kawai fa ka bani".

"Ashema ya bakan".Naseer yace yana dariya.

Salim dai yana gefe yana jinsu bai tsoma musu baki ba.

Rage murya Junaid yayi wit a pity face yace " joke apart am serious bro,na biyo ta hannunka ne dan naga tana jin maganan ka".


"Zan duba in gani ".Farhan yace yana shan kamshi.

Dariya suka sa dukan su ganin yanda Farhan ya bashi amsa.

Tashi Farhat tayi ta nemi taimakon wasu maids 2 suka taimaka mata wajan kwashe girkin da tayi zuwa down stair suka jajjera sannan tace su tashi su zo suci abinci.

Kowa ya hallara amma banda Maryam Junaid duk ya damu da rashin ganinta har ya kasa hak'uri yayi magana.

Dakinta Sumayya ta nuna mishi ya tashi yaje dan kiranta.

Tana zaune da waya a hannunta yayi sallama ya shiga.

Cikin fara'a ta mike take tambayar shi yaushe ya zo?

"Ina zaki sani tunda kin maida kanku kullen d'aki jarfi da yaji"

Bata ce komai ba sai murmushi da taya tana kallon kasa.

Hannunta ya kama yana cewa suje suci abinci.

Haka ya jata har kan dinning d'in ind ake zaman jiransu.

A fakaice ta saci kallon inda Farhan yake zaune,sai ganin Farhat tayi kaman zata shige cimin jikin shi.

Tsaki taja a ranta tana wannan lalle ta tabbata mara kunya a gaban mutanen ma bazata barshi yasha iska ba

Junaid shi yaja mata kujera yace ta zauna,ba musu ta zauna aka fara cin abincin da ita.

Sauran samarin sai zuba santi suke suna cewa Farhat ta had'a su da k'anwarta su aura suma su kwashi gara.

Farhan ne yace bata da k'anwa ita kad'aice a gidansu,nan suka ce ko k'awayenta ne ta taimaka ta had'asu.

Haka suka gama cin abincin cikin raha da annashuwa amma vanda Maryam da duk haushinsu ya cikata na yanda suke wani k'oda wannan jagwalgwalon Farhat d'in.

Sai bayan karfe 8 suka bar gidan,Junaid yana k'ara tunawa Farhan sak'on shi.

Bayan tafiyan su Junaid ne Maryam zata tashi Farhan ya tsaidata dan lokacin kowa ya tashi sai su 2,yace ta zauna akwai magana mai muhimmanci da zasuyi.

Zama tayi tana sauraronsa a zuciyarta kuwa tana addu'an Allah yasa maganan aurensu zai mata.

Gyaran murya yayi sannan yace " Ummina ina son ki amince abinda zan fada miki dan bazan so abinda zai cuce ki ba kinsan yanda nake ji dake cikin 'yan uwa domin ke ta dabance".

Zuciyarta ta fara harbawa da sauri jin kalaman Farhan da tayi kuma farin ciki tab ya cikata ganin Allah ya karkato mata da hankalin Farhan cikin sauk'i.

Murnan tane ya koma ciki a razane ta d'ago da idonta da ya ciko da hawaye take kallon shi.

Shi kuma hankalinsa kwance yake fad'a mata sakon Junaid ba tare da ya lura da halin da take ciki ba.

Sai da safe ya mata harda rok'on kar ta watsa mishi k'asa a ido ko kuma kar tasa yaji kunya tunda ansan tana jin maganar shi shiyasa Junaid ya biyo ta hannun shi.

Tafi minti talatin zaune ita kad'ai a parlourn tana hawaye,saboda ta rasa wani irin tunani zatayi.

Yanzu ta tabbatar Farhan baya sonta ko kad'an tunda da kansa yake cewa taso waninshi wannan ya nuna totaly baya kishinta.

Tashi tayi ta koma d'aki tare da had'a kayanta dan dole ta bar musu gida tayi nesa dashi.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by umme yusuf
(Maman yusuf)

💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha Allah🤝)

Page 73~74

Da washe gari ba wanda ya lura Maryam ta bar gidan,saboda Farhat a ranan ta fara fita school.

Farhan shi ya ajiye ta a school,ya gama mata komai sannan ya wuce office.

Maryam ta isa gidansu cikin tashin hankali idanunta a kumbure ga fuskanta ma yayi jajir da shi sakamakon kuka da rashin bacci da tayi fama dashi a daren jiya.

Da gudu tazo ta rungume momynta da fitowanta kenan cikin shirin fita,tana kuka kaman ta shide.

Hajiya Fadila hankalinta in yayi dubu a tashe yake ganin halin da taga yarta a ciki.

Kamata tayi suka zauna akan kujera tana tambayanta meya faru ko wani ne ya mutu?.

Dakyar ta tsagaita kukan da take sannan ta warwarewa momynta halin da take ciki.

Wani kallon baki da hankali momy ke binta dashi sannan tace" wai me yasa Maryam baki da tunani ne,in banda rashin tunani shi Farhan d'in ya tab'a cewa yana sonki?"

Girgiza kai tayi" momy nasan yana sona bai furta min bane kawai " tace tana cigaba da kukanta.

Murmushin takaici momy tayi tace " in har yana sonki ba zai taba tsallake ki yaje can 9ija ya auro wannan yariyan ba,kuma kince da bakin shi yake miki tayin soyayyar Junaid.kinga ko ba ko d'igon soyayyarki a zuciyar shi sai ta 'yan uwantaka.

Volume d'in kukanta ne ya k'aru jin abinda momy take cewa,shikenan ta rasa Farhan kenan saboda momyce last hope d'inta amma gashi bata goyi bayanta ba.

"Meye laifin Junaid,yaron nan shima yana da hankali ki bashi dama kiga iya gudun ruwan shi.na tabbata zaki so shi shima tunda duk cikin 'yan uwa ba wanda yake kama da Farhan d'in kaman shi Junaid.

Momysai fad'a take mata da nuna mata shima Junaid ba abin k'i bane.

Shiru tayi tana sauraronta,ba zasu gane bane abinda take ji akan Farhan daban ne.bazata iya had'a shi da ko wani namij ba.

Har d'akinta momy ta rakata tace tayi wanka ta kwanta ta huta yanzu zata dawo bazata dad'e ba.

Sai dare su Farhan suka san Maryam bata gidan,Farhat tafi kowa farin ciki amma saboda kissa irin na Farhat sai kirkiro damuwa ta d'aura a fuskanta tasa dole wai Farhan ya kirata yaji ko sunyi mata laifi ne ta tafi babu sallama.

K'in d'aukan wayan Farhan tayi,tana gani ya mata 3 missed calls.Momy ya kira nan tace mishi ya k'yale ta kawai rashin hankaline yake damunta.

Ajiye wayan shi Farhan yayi ba tare da ya fahimci inda maganan Momy ya dasa ba dan shi a zaton shi kan maganan Junaid ta bar gidan.

Farhat yanzu rayuwa mai dad'i da ban sha'awa suka bud'e ita da Farhan d'inta ba mai takura su dan Mamy ma zamanta tayi a gombe tare da yaranta.

Sumayya ta murmure ta samu lafiya sosai kaman ba ita ce ta kwashi shekaru tana jinya ba.sosai take samun kulawa daga yayanta da Farhat.

Junaid ya dage sosai wajan neman soyayyar Maryam,tun tana share shi har ta fara kula shi sai gashi soyayya da shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu.

Sai yanzu ta lura ashe Farhan ba son shi take ba shakuwace kawai.

Bayan wata biyar,
Shawara Farhan yayi tare da Uncles d'insa kan cewa zai barwa Abba companies d'insu uku da gidajen mai da duk sauran kadarori suka mallaka na can maiduguri kyauta sakamakon rik'e musau amana da yayi na tsawon shekarun nan ba tare da ha'inci ba.kuma shi ba zai iya komawa maiduguri da sunan zama ba.

Dukkansu sunyi na'am da shawaran kuma sun bashi goyan baya 100% saboda a wannan zamanin ba kowa ne zai iya abinda Abba yayi ba kuma koba komai surkinsa ne ya kamata ya k'yautata mishi.

Farhat bata san wainar da ake toyawa ba sai kiran Amminta ta gani tana fad'a mata abin alkhairi da Farhan yayi musu.

Farhan yana shigowa taje da gudu ta rungume shi tana kuka,cikin tashin hankali yake tambayanta me ya faru?

Godiya ta rinka zabga mishi na irin hallacin da yayiwa Abbanta

"Abinda nayiwa Abba yayi kad'an idan kika duba irin hallaci da yayi mana".

Bata rai yayi yana kallonta yace " karki k'ara shiga tsakanina da Abbana duk abinda zanyi mishi ki zama 'yar kallo".

Dariya had'e da kuka take tana gyada kai.kwantar da ita yayi a kirjin shi yana shafa bayanta yace nifa ban gane miki ba kwana 2 nan sai cin tuwo miyan kuka da shine abincin da kika fi tsana kike.

K'ara gyara kwanciyarta tayi a jikinshi tace nima ban sani ba just yanzu nafi sha'awan tuwon ne".

D'agota yayi yana shafa shafaffen tomynta yace " i feel like there is little me here".

Wara ido tayi tana kallon shi sai kuma ta tuna tafi 2 months rabonta da taga period d'inta.

Gira d'aya ya d'aga yana kallonta yace " ehen think well baby guilty or not guilty?"

Cusa fuskanta yayi a kirjin shi tana dariya.

D'agata cak yayi zuwa bedroom yace " muje in bincika da kaina tunda baza kibani amsa ba.

Farhat tana zaune a palour ta tura katon cikinta gaba ta wani mimimk'e k'afafu masa aiki suna mamatse mata saboda gajiya zuwanta kenan daga school.

Wayarta ne ya soma ringing rossy ta tashi ta d'auko mata,sunan Ramlat ta gani yana yawo akan screen d'in cikin farinciki ta d'aga suka gaisa tare da tab'a barkwanci kad'an sannan Ramlat tace " dama Ruky ce tasa na kiraki dan in nema mata yafiyarki akan abubuwa da suka faru a baya dan yanzu taga isharan rayuwa babanta yayi retire daga ambassodorn da yake.bayan retiren nashi abubuwa suka cakud'e musu daga gobara sai 'yan damfara,maganan da nake miki yanzu rayuwa ta juya musu baya sun zama abin tausayi".

Wani gwaron numfashi Farhan taja ta sauk'e tana tuna a baya duk da itama tana da nata halin amma mafi yawncin wani abu da take Ruky ce mai zugata ko
bata shawara,zata tuna last da sukayi waya da ita tun kamin zuwansu london,lokacin da take gidansu ta zagan mata miji.tun daga ranan ta watsar da lamarinta.

"Bakomi Ramlat ni dama ban rik'eta a zuciya ba,na dai yanke alakar dake tsakanina da itane saboda halinmu da ya banbanta.but tunda itama ta gane gaskiya bakomai zan kirata da kaina".

Nan suka d'an tab'a hira har take fad'a mata ansa date d'in aurenta da d'an sarkin sudan nan da 1momth.murna sosai Farhat tayi tare da mata alkawarin in har Farhan ya amince zata hallarci bikin sannan sukayi hanging.

Haka Farhat ta cigaba da rainon cikinta wanda ya had'u mata da karatu,sai dai tana samun kulawa sosai daga wajan Farhan da Mamy,da tayi kusan 1month a gidan dan Farhan da kanshi yaje ya d'aukota saboda yanayin da Farhat take ciki.

Cikin wani dare suna kwance suna bacci,cikin bacci Farhat taji kaman ana mintsininta s mara,tun tana sharewa ta farka jin abin na kara gaba.

Farhan take kira a hankali kan ya tashi amma ina yayi shame-shame yana ta sharan baccinsa hankali kwance.

Wani wawan duka ta kwada masa a gadon baya da taji wani irin murd'a da cikinta yayi.

A firgice ya tashi saboda dukan ya shige shi.ba kad'an ba.

Masifan da yayi niyyan yi mata ne ya had'iye ganinta da yayi tana ta juye-juye take ga gumi ta had'a sharkaf duk da sanyi irin na garin london ga kuma a.c dake d'akin.

A rud'e ya rik'eta yana tambayanta me ya faru,amma yaga hankalinta ma baya jikinta bare ta amsa mishi.

Tsungumanta yayi a gigice yayi hanyan fita da ita dan zuwa hospital.

Basu kai k'ofa ba ta fara wani irin nishi jikinta duk b'ari yake,wani damk'a da tayiwa wuyan Farhan sai gasu a k'asa.

Farhan hawaye kawai yake,ka'ara tallobota yayi da niyyan ya d'agata su fita amma sai yaji Farhat ta rik'e masa hannu tana nishin da yafi na d'azu.

Kasa k'watan kansa Farhan yayi yana kuka wiwi,dan ba zai iya cewa ga abinda yake damunta ba.a rayiwarshi ko sau d'aya bai tab'a jin labarin yanda ake haihuwa ba.

Cak ya tsaya da nashi kukan sakamakon kukan jariri yaji,ido kawai ya tsurawa sabon halitta da yake wutsil-wutsil da kafa yayi.

Sai a lokacin Farhat ta sake hannun shi ta kwanta lak'was kaman matacciya tana maida numfashi a hankali.

Wani irin yanayi na zallan farincikin da bai tab'ayi ba rayuwarsa ya tsinci kansa a ciki.

"Ba kallo zaka tsaya yi ba ka kira Mamy"yaji tace cikin sanyin murya kaman bana Farhat ba.

Da sassarfa kaman zai kife ya sauk'a down stair,knocking d'in k'ofan bedroom d'in yana k'wala mata kira.

Cikin bacci Mamy taji muryan Farhan a rud'e ta fito tana tambaya ko nakuda ce ya tasowa Farhat.

Sai washe baki yake yace mata ai ta riga ta haihu tana d'aki.

Dafe kirji Mamy tayi tace " na shiga uku bangane ta haihu tana d'aki ba,kana nufin a gida ta haihi?"

Amsa mata da eh yayi ssnnan ya k'washe labarin abinda ya faru ya fad'a mata.
Bata karasa jin labarin ba ta k'wasa aguje tayi part d'in nasu.

A zaune ta tarar da Farhat har mabiya ta fad'o,jaririn Mamy ta d'aga nan taga ashe baby gal ce.

Asibitin da take zuwa antinatal Farhan ya kira ya gaya musu,nan da nan sai ga nurses har 2 sun zo duba lafiyarta dana baby.

Cikin lokaci kank'ani aka shirya su tsab da babynta wacce ta d'ebo komai na Farhan,kallo d'aya zakata kaji ta shiga ranka.

Cikin daren Farhan ya rinka kiran 'yan uwa da abokanen arziki yana fad'a musu kyakkwan albishir.

Da washe gari tunda sanyin safe gidan su yake cike da yan barka ciki harda Maryam da ta dad'e da zubar da makaman yakinta sun d'inke da Farhat sun zama aminai.

Ana saura kwana 2 suna su Ammi da 'yan uwanta suka dira a birnin london ciki harda Ramlat da Ruky,da wasu abokan Farhan na can maiduguri wanda Faruk shi yayi musu jagora Farhan shi ya d'auki nauyin duk masu.zuwa dan haka mata da suka zo ba zasu lissafu ba dan 'yan uwan Abbama sune a gaba.

Ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar Farhan wato Maryam amma za'a ke kiranta da Umaima.

Anyi shagali bana wasa ba,sosai Farhan ya saki bakin aljihu, anyi hidima masu yawa kqman ana bikin wata 'yar shugaban k'asa.

Mai jego da babynta gifts d'in da suka suka samu ba zai fad'u ba.

A cikin bikin sunan ne kuma Allah ya had'a soyayya tsakanin Ruky da Naseer,Sumayya da Faruk.

Maryam tafi kowa murna da d'auki wai ita akayiwa tak'wara.haka akayi shagali kowa yaji dadin zuwan shi,dan bayan sunan Farhan yasa aka kaisu shopping kowa ya kwashi kaya son ranshi.

An maida kowa gida da sha tara na arziki kowa sai son barka yake.

********************

2years later abubuwa dayawa sun faru ciki harda auren su Ruky da naseer,Ramlat da Yarima Shamsudden,Maryam da Junaid sai Sumayya da Faruk.

Farhan ne zaune a office d'inshi duk ya canza ya kara kwarjini da kamala,ya duk'ufa yana duba abu a system d'inshi.

Wayar shice tayi kara,jawo wayan yayi kawai ya d'aga ba tare da ya duba sunan ba.

Muryan Farhat yaji tana kuka tana cewa "wayyo Ya Farhan kaina jikina duk ciwo suke min ka taimaka min dan Allah zan mutu".

Agigice ya mike tare da ture system d'in gaban shi yana tambayanta meya faru?

Sai kara sautin kukanta take tana cewa yazo ya taimaka mata zata mutu.

Ba shiri ya fito ya fad'a mota ya fita a guje ka ta kan guards d'inshi bai bi ba.ganin ya fita ba a hayyacinsa ba yasa suma suka rufa mada baya.

Ko parking d'in kirki motan bai samu ba ya bud'e kofan ya fita a d'ari ya cikin gidan,da yake idonshi ya rufe baima lura da Mamy da Umaima da suke kallo a palourn ba.

Sai wucewar shi kawai suka gani

Part d'insu ya fad'a yana kwala mata kira.

Kwance ya ganta a kan gadonsu da wata figilar night wear wanda dashi da babu duk d'aya ga gashin kanta duk ya babbaje kan pillow wasu sun rufe mata fuska.

Gaban gadon da take kwance yaje ya tsuguna yana tambayarta me yake damunta mesa bata fad'awa Mamy ba.

Kamo hannun shi tayi tana shafawa a hankali tana murmushi " tace yau ma ka fad'a tarkona so easly, yau zan maka sharrin da bazaka taba fita ba,a yau ba sai gobe ba zaka bar.......".

Hade bakunsu da yayi waje guda shi ya hanata karasa maganan da tayi niyya.sai da ya tsotsa iya son ranshi sannan ya sake mata baki yace " bari inyi yar mai gaba d'aya sai kiji dad'in yi min sharrin yace yana cire coat d'in jikin shi tare da haurowa kan gadan suna ta kyalkyalar dariya.

*Alhamdllilah*

*toh anan na kawo karshen wannan d'an gajeran novel d'ina.da fatan ya ilimantar ya nishand'anr da ku.kuskuren da nayi aciki Allah ya yafe mana,alkhairin dake ciki kuma Allah ya bamu lada baki d'aya*

*jinjina da godiya a gare ku fans d'ina musamman na group d'inmu na facebook zamana na amana dana watsapp farhat fans hausa novel 1,2nd3,sai sauran groups masu bibiyan farhat kaman su hafsat hausa novel,just hausa novel,norul janner novels,lina novels.khalisat haidar novels nd lots more*

*sai kuma gaisuwa da ban girma na musamman ga d'an uwana umar dalha da 'yan group d'in mu wato fagen marubuta writters ass.Allah ya bar kauna*

*sai kunji ni a sabon novel d'ina UKUBAR KISHIYATA soon*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment