Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kwance ana masa karin ruwa.nan ba madu yacewa abba wasu samari 2 ne a waje suke son ganin shi wai sun zo da labarin farhat.

Kamin abba yayi magana sai ganin farhan sukayi ya fizge karin ruwan da ake masa ya fita a guje har yana mangaje ba madu.

Na gode da addu'oin ku,ina muku fatan alkhairi masoya na allah ya bar kauna.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


Page 51~52


Farhan bai tsaya a ko ina ba sai bakin get,yana zuwa ya cukumo wuyan ozo tare da jijjiga shi yana cewa"a ina kuka ga farhat,a ina kuka ganta?

Ozo sai firfito da ido yake ba bakin magana saboda ba karamar shaka farhan yayi masa ba,ganin haka deen ya sulale ya bar gurin ba tare da farhan din ya gan sa ba.a haka su abba suka iso wajan.

Da kyar da sudin goshi ahmad dan yayar abba da abdul kareem dan kanin ammi sukayi nasaran banbare hannun shi daga wuyan ozo da har ya fara fita hayyacin sa.

Abba ne cikin lallami yake tambayan ozo wani labari ya kawo game da farhat?cike da nadama da dana sanin dauko farhat din yake nuna musu motan da hannu ba tare da ya budi baki ba.

Farhan ne farkon isa wajan motan,baya yayi zai fadi sakamakon mummunan gani da yayi.ahmad ne yayi saurin tarosa jikin sa,abba shima cikin mutuwan jiki ya karaso motan dan yaga me ya firgita farhan haka.

Innalillahi wa innailahi!!! rajiun abba yake maimaitawa.

A zuciye farhan ya ture ahmad da ya rikosa yayi kan ozo,ya hau kai masa naushi ko ta ina.nan ma da kyar abba ya tsawatar mishi da cewa ya bar wannan haukan nan yazo su kai ta asibiti.

Abba da farhan su suka wuce da ita royal private hospital.a hanya abba ya kira ammi ya gaya mata abinda ke faruwa,nan tace gata nan zuwa amma abba ya ce tayi hakuri ta zauna shi zai dawo ya kaita hospital din.


ahmad da abdul kareem su suka tsaya akan ozo dan jiran police da suka kira a waya.

Suna zuwa ba doctorn yace ba zasuyi mata aiki ba sai da da sa hannaun police saboda sunga alaman duka ne aka mata,nan abba yace sun kira police suna kan hanya dan kama wanda ya kawo ta.su kasa hakurin jiran police din ne saboda condition din da take ciki.

Jin haka yasa suka karbe ta akayi emergency da ita.

Sai bayan kusan 2hrs sannan doctors din suka a lokacin har su ahmad suma sun iso hospital din bayan sun damka ozo a hannun su.

An maida ta personal room dan haka aka ce zasu iya shiga su ganta amma banda hayaniya dan sunyi mata alluran bacci.

Kuka wiwi farhan yake ganin yanda farhat din shi uwar tsokana da tsiwa take kwance kaman matatciya in ba dan numafashin ta dake yake fita a.hankali ba.ga shatin belt rudu rudu a jikin ta,fuskan ta ma kaman ba nata.ba saboda kumburin da yayi.

A gida kuwa ammi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take jin wai anga farhat kuma anyi hospital da ita,tana ji a jikin ta duk yanda akayi yarta tana cikin mummunan yanayi shiyasa hankalin ta yaki kwanciya sai kuka take yan uwa suna ta bata baki.

Abba yace dasu farhan su dawo gida sai a taho da ammi ta kwana da ita.ba kunya farhan yace su su tafi shi zai kwana a wajan ta inya so gobe ammi ta zo da safe.

Murmushi abba yayi ya fita abin shi,su ahmad kuma sai da sukayi ta masa tsiya kamin suma suka bi bayan abba.

Kujeran sa ya kawo gaban gadon da take ya zauna tare da rike hannun ta da yake makale da drip ya zubawa fuskan ta ido ya tuno irin rayuwar da sukayi tun haduwar su har zuwa yau.

Ajiyan zuciya yayi da ya tuna wai guduwa tayi a gida dan ta koma gidan shi.murmushi ne ya kwace masa ba tare da yayi niyya ba,a zuciyan shi yace"dats means yanzu itama tana sona ko?"

Dora kan sa yayi kan gadon da take ya cigaba da tunanin sa har bacci yayi nasaran dauke shi ba tare da ya sani ba.yana nan yana baccin har nurse ta zo ta cire drip din da aka sata mata bai sani ba.

Ita ta fara farkawa,dakin ta bi da kallo taga ba dakin da azzaluman nan suka kaita bane.wannan yafi kama da asibiti,juyuwan da zatayi kaman a mafarki taga farhan ya dora kansa a gadon yana bacci,dan cire tantama yasa ta kai hannun ta a hankali ta shafa gashin kansa.

Cikin bacci farhan yaji ana taba masa gashi,bude ido yayi ya sauke su akan farhat da ta kura masa ido.cike da farinciki ya tashi zaune yana tambayan ta ina ke mata ciwo bari yakira doc.

Har ya juya yaji ta rike masa hannu,dawowa yayi a hankaki zuwa gaban gadon ya zauna ba tare da sun daina kallon juna ba.wani irin kallo mai cike da shauki da wuyar fassara suke aikama juna.

Yana zama ta fafa jikin sa ta kankame shi tana kuka kaman ta shide.shima rike ta tsam yayi a jikin shi yana sauke numfashi dan yayi missing dinta sosai.

Shafa bayan ta yake alaman rarrashi da kyar ya samu ta tsagaita kukan da take.

"Ya farhan i'm sorry dan allah ka yafe min.kayi min duk hukuncin da kaga dama amma dan allah kar ka guje ni,i can't live without u"tace tana kara rushewa da sabon kuka.

Cikin rarrashi yace"shhhh ya isa haka komai ya wuce .we will be together forever insha allah".

Lafewa tayi a kirjin shi tana shakan kamahin mai sanyi da tayi missing.nan ta shiga bashi labarin irin wahala da ta shiga na rashin sa a kusa da ita.shiru yayi yana sauraro tare da mamaki wai yau farhat ce take zuba masa kalaman soyayya haka harda neman gafaran shi.lalle abba yayi gaskiya da yace hukuncin da ya dauka shi zaiwa dadi,gashi ko ya gani.

Hamdala yayiwa allah tare da jinjinawa abba,da sauran iyayen zasuyi koyi da hali irin na abba da ansamu zaman lafiya atsakanin ma aurata.

Har aka kira sallahn asuba suna nan manne da juna ta hana shi fita bare ya kira doc.lallaba ta yayi ta kwanta sannan ya shiga bathroom dake cikin dakin ya dauro alwala sannan ya fice zuwa masallaci dake nan cikin asibitin.

Tare da doc suka shigo dakin,bayan ya dudduba ta yace a hada mata ruwa mai dan zafi a gasa mata jikin ta.

Heater ya kunna a bathroom din sannan yazo ya taimaka mata ya kaita ciki.

Cikuikuye shi tayi ta cusa fuskan ta a kirjin shi tana darya kasa kasa wai ta kunya take,shi kuma gaba daya tsayuwan na neman gagaran sa jin yanda take manne masa a jiki kuma.ba kaya a.jikin ta.

Basu fito a bathroom din ba sai kusan 6 dan da kyar aka gasa jikn saboda gaba daya shagala sukayi a bathroom din dan sun manta ma a asibiti suke.

Zama tayi a bakin gado bayan sun fito ta rasa ya zatayi tayi sallah saboda ba kayan da zata saka,wayan da ta cire kuwa ko kyan gani babu duk jini ya bata.

Ammi ce ta turo kofa ta shigo tare da sallama bayan ta kuma su yaa dija kanwar abba da hjy halima kanwar ammi sai ladi da take dauke da.basket din abinci da katon ledan kayan sawan farhat

Rungume juna sukayi da ammi suna ta kuka da kyar suka tsagaita nan farhan ya gaishe su.ammi tace masa"kaje gida abban ku yana jiran ka zaku je police station wajan mutumin da ya kawo ta.


Farhan ya isa gida on time a gurguje ya shirya suka nufi police station din kusan su 6.ciki harda aminin abba alh nura.

Koda suka iso direct office din d.s.p suka wuce.yana ganin abba yasa ya mike cikin rawan jiki yana musu barka da zuwa nan yasa aka fito da ozo da ya daku yayi laushi.d.s.p shi ya koro musu bayanin abunda ya faru dan tuni ozo ya tona.

Yace"yanzu haka na tura yara su dubo gidan ko za a samu sauran su acan kuma shima dayan da ya gudu an fara bincike a kan sa".


Alex sai 7:00am ya farka daga nauyayyen bacci da yayi.tashi yayi yana neman keys din dakin da ya kulle farhat a ciki dan duba lafiyar ta kamin oga yaaz ya karaso.amma abin mamaki ya nema sama da kasa ya yarasa,mikewa yayi ya nufi dakin wai ko ya manta a jikin kofan.

Daskarewa yayi tare da firfito da ido waje yana kallon dakin da ya ganshi wangale ba alamun mutum a ciki.rasa inda zai ransa yaji dadi yayi,shawara ya yanke na ya gudu kawai in ba haka ba oga yaaz zai iya yin ferfesun shi a yau.

Cikin hanzari ya dauki wayan sa ya fita a guje ya nufi get,sai cikin rashin sa a yayi dai dai da isowan oga yaaz.

Dole ya bude mass get ya shigo cikin fara a yaaz yace"yauwa alex aikin ka na kyau ina so muyi tafiyan safe saboda da mota zamu tafi dan bincike yayi yawa naga ko ina a media ana tallan wanda ya kawo ta za bashi kyautan 10 millions".dariya ya kwashe da shi kana yacigaba da cewa"ta jirgin ruwa za mu bar kasan nan a yau cikin dare nayi maka alkawari zaka ji dadi sosai tunda ka zama kaine silan samun farin cikina".

In banda karkarwa da hada gumi ba abinda alex yake jin abinda yaaz yake cewa shi kuma kwata kwata saboda yana cikin farin ciki bai lura da halin da yake ciki ba.

Hannun shi yaaz yaja zuwa cikin gidan yana cewa"zo muje mu tsara yanda tafiyan zai kasance dan bamu da ishasshen lokaci".

A yanzu kam hawaye alex ya fara kuma sai a lokacin yaaz ya kura dashi.cikin kallon tuhuma yace "ya na ganka haka me yake faruwa".

Baki na rawa alex ya fara masa bayani da rantse rantse baisan ya akayi ta bar gidan ba.

Wani irin kallo mai wuyar fassara yaaz yake masa,can ya fito da pistol a cikin aljihun coat din shi ya dora akan goshin alex kana yace"zaka gaya min ina ka kaita ko in fasa maka kwakwalwa yanzu. Na yarda da kai na kori sauran yara na ashe yaudara ta kayi?"

Wani irin ihu yayi mai cike da kunci saboda yasha buri kan farhat cox da gaske yake son ta amma wannan ya bata masa budgent.

Bai tsaya wani dogon tunani ba ya dauke kan alex da piston din yana huci,kuma a dai dai lokacin moton police ya tsaya a kofan get din gida.
[12/24, 8:31 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha allah🤝)


Page 53~54

Zagaye gidan police din sukayi,suna neman yaaz ya mika kanshi amma ina saima harbi da ya fara da pistol din shi yana neman hanyan guduwa.

Basuyi niyan harbin shi ba,ganin ya harbi wani police a kafada yasa suma suka bude mishi wuta,nan ya fadi ko shurawa baiyi ba.

A police staion su abba suna shirin komawa gida da zuman in anyi nasaran kamo sauran zasu dawo a maka su a kotu.

Wayan d.p.o ne yayi ringing,inspector da operation din kama su yaaz yake hannun sa shi ya kira ya fada mishi abinda ya faru.shima d.p.o bai tsaya bata lokaci ba ya fada musu mutuwan yaaz ta enconter.

"Yanzu saura wanda ya gudu shi zan sa acigaba da binciko sa.shi wanda ya mutun ma za'ayi cikekken bincike akan sa.duk yanda ake ciki zan sanar da kai alhajji.."

"Toh ba komai d.p.o nagode sosai,
sai na jika ".

Nan suka mike tare da yin musabaha sannan suka fice. direct asibiti suka
nufa.


A asibiti kuwa yan uwa sai tururuwa zuwa dubiya suke tare da yin barka da arziki. both dangin abba da na ammi da abokan arziki.

Lokacin da su farhan suka shigo dakin cike yake dayan dubiya.dan haka basu jima sosai ba dakin suka fita.

Har yamma farhan yana nan yaki komawa gida zaman sa yayi a haraban asibitin,lokaci-lokaci yana dan lekawa yana duba jikin ta kuma alhmdllh bata Kwanta ba ana ta hira da ita.

Da daddare lokacin yan dubiya sun ragu sosai,sai su yan gida.abba ma yana nan,anan yake mai dawa ammi abinda ya faru yace...."ba kidnappers bane suka dauke ta kaman yanda kike tsammani,yaron minister man fetur ne na nan naija dazu d.p.o ya kira ni yake min bayani.wai a baya mama na ta wulakanta shi harda mari a wajan shopping dan ya biya mata kudin kayan da ta saya.shine ya sawa yaran sa kudi ga duk wanda yayi nasaran dauko ta saboda ya dauki fansa."....

Hmmmm numfashi ya sauke ya juya yana kallon farhat da take hawaye,a zuciyar ta tana lalle wulakanci dodo ne.abinda faru da dadewa,ashe yana nan yana binta,da auren ta da komai.sai dai ta godewa allah daya kare mata mutuncin auren ta.dole yace mata uban tane bagger ashe dan minister ne......

Abba ne ya katse mata zancen zuci da take yace ko ta gane shin?

Labarin yanda suka hadu da yaaz da abinda tayi mishi sannan da yanda su alex suka dauke ta har zuwa yanda yaci mata mutunci duk saida ta fada musu tana hawaye.

Farhan sai huci yake idon sa sunyi jawur saboda baccin rai.in ba dan police sunyi nasaran kashe shi ba,da kuwa shi zai kashe shi da hannun shi.ba dan minister yake ba allah yasa dan karuna ne shi.

Cikin kukan nadama farhat ta kara rokon su gafara.farhan ji yake kaman yaje ya rungume a barsa ya lallashe ta yake ji.

Kowa a dakin jikin sa yayi sanyi.can abba yayi gyaran murya yace"a yanda d.p.o yace duk rundunar yan sanda ta kasa suna farin cikin encounter da ya rutsa da yaaz, in ba haka ba sau nawa yake aikata manyan laifuka amma ana kama shi lawyer zai zo yayi belin din shi kuma ba yanda suka iya dole su bayar tunda uban sa babban mutum ne.sosai suke
murna an rage bakin iri".

Haka dai ayi ta jajan tawa sannan abba yace su tashi su Koma gida,nan kowa ya mike banda farhan da ya sunkuyar da kai kasa yaki motsawa.

Ammi ce tace"ya dai son tashi mana dare fa yana yi".

Baice komai ba kuma bashida niyan tashin.

Abba ne ya cewa ammi ta dauko hijab ta raka shi wajan mota.ammi bata kawo komai a kan ta tasa hijab din ta tabi bayan abba.

Suna zuwa bakin mota yace"shiga mu tafi gida".

Baki sake ammi take kallon shi can dai tace"dear ya zamu tafi mu bar ta ita kadai?"

"Ba ita kadai bace mijin ta na tare da ita".

Sai a nan ta gane inda zancen abba ya dosa dan haka bata kara cewa komai ba ta shiga mota sukayi gida

Minti 5 farhan ya basu,ganin ammi bata dawo ba,ya tashi cike da jin dadin abba ya fahimce shi, kulle dakin yayi ta ciki.

Kallon sa farhat ta tsayayi.kallon irin me kake nufin nan,bai ce mata kala ba saima hayewa gadon da yayi tare da jawo ta jikin shi ya rungume yana sauke numfashi.

"Meye haka farhan?...kasan fa zata dawo pls ka sauka".tace tana kokarin ture shi daga jikin ta.

"Ammi ta tafi gida ba zata dawo ba sai da safe.nagodewa allah da ya bani sirki mai ganewa"yace yana kara matse ta.

Dariya tayi tana masa tsiyan ya kore mata ammi.shima dariyan yake yana aika mata da sakonni.sosai suke romancing din junan su dan sunyi missing din juna.

Kuka tasa masa ganin yau farhan da gaske yake son angwancewa akan gadon asibiti.

Da kyar ya saita kan sa ya hakura ya kyale ta sanan ya shiga rarrashin ta.shiru tayi tayi tare da lafewa a jikin a haka bacci mai dadi yayi nasaran dauke su.

Shiya fara farkawa da asuba sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala ya fito ya nufi masallaci bayan ya tashe ta.

Yau ammi ba tayi sammako ba dan sai wajan 8 sannan ta iso asibitin.a lokacin har farhat tayi wanka tare da gashin jiki da farhan ya mata.wanda da kyar akayi shi cox sai love suke sha kayan su .

Da yamma doc ya sallame su,farhan murna kaman ta kashe shi daman shi zam asibitin a takure yake yafi son suje can gidan su,su sha amarcin su.

Murnan sa ne ya koma ciki ganin hanyan gidan abba akayi,ba yanda ya iya haka yayi shiru har suka isa gidan.

A nan sukayi dinner koda wasa bai ce zai tafi gida ba.sai bayan anci an sha abba yace su dawo parlour yana da magana dasu.


Duk suna zaune a parlourn suna jiran abinda abba zai ce.

Farhan da farhatkuwa duk sunyi jigum-jugum.suna fargaban kar abba ya hana farhat komawa dakin ta.


Gyran murya abba yayi sannan yace.....

"Mama na wannan zaman naki ne,hakika nayi nadaman tare da bakin ciki yand so da ganin ke kadai ce ya ta ya mantar dani sa ido akan tarbiyan ki.wanda hakan ya jawo ki kayi abubuwa da dama har ya jefa ki cikin halin da kika tsinci kan ki kwana 2 da suka wuce.
Idon ki ya rufe ke ga baban ki mai kudi kike taka mutane son ranki ciki kuwa harda mijin ki".

Duk abubuwa da ta aikata a baya ga masu neman taimako wajan sa har zuwa ranan da yayi recieving din kiran da tayiwa farhan sai da ya maimaita mata.

Zaro ido tayi waje tana hawye jin wai ashe abba yaji irin cin mutunci da tayiwa farhan a waya...?

Jin muryan sa tayi ya cigaba da cewa"a ranan nayi bakin ciki nayi nadaman barin ki a duhu da nayi.kin san wani duhu ne?"

Girgiza masa kai tayi cikin hawaye.

"Gaskiyan dan ministern ne da yace miki uban kine poor bagger,saboda mijin ki da kike ciwa mutunci akan kudi,toh kudin da kike gani a hannun mahaifin ki da taimakon da kika ga yana yi,da abinda kike ci kike sha suturan ki makarantan ki,duk bana kowa bane face dukiyan mijin ki FARHAN ne"......
[12/24, 8:31 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha allah🤝)


Page 55~56


Kwakkwaran motsi *farhat* ta kasa sai firfito da ido waje tayi tana kallon mahaifin ta tare da neman karin bayani.

Murmushi Abba yayi yace "yau zaki san waye FARHAN.

Tuna baya......

****************

Mallam GONI ALIBE mazaunin kauyen dikwa ne dake jahar borno.

Mallam alibe ya kasance malamin makarantan allo ne.

Matar sa wato ya aisa sai yaran sa uku mata 2 da namij daya.

Babbar itace ya dija sai mai bi mata ina gana,duk suna gidajen su dan anyi musu aure saboda ba wani karatun boko aka sa su ba.sai autan su wato bukar da yake shi namiji ne yasa kan sa a bokon yanzu haka yana ss2.

Mallam bashi da wata sana'a taka mai-mai sai dai in damun ta shigo yakan dan taba noma shiyasa suke cikin talauci ko yaushe ci da kyar sha da kyar.

Lokacin da bukar yana ss3 Allah ya jarrabi mallam da cutan ajali,bai dade yana jinya ba allah ya karbi ran shi.

Mutuwar ta matukar girgiza su,sunyi kuka sosai daga baya suka fawwala Allah komai.

Rayuwa ta juyawa bukar da mahaifiyar shi baya,saboda suna matukar shan wahala dan basu da mai taimako.yayyen sa duk talakawa suke aure,ga dangin su ma basu shi kowa ta kansa yake.

Ya kasance sai bukar ya fita yayi aikin karfi irin su faskare da sauran su,sannan suke samun suci abinci da mahaifiyar shi.

Cikin wannan yanayi allah ya taimake shi ya zana ssce cikin nasara.

Ganin zama cikin kauyen yaki dadi yasa yayi shawara da mahaifiyar shi kan zai rika shigowa cikin maiduguri ko zai samu abun yi.

Bata hana shi ba,saima addu'an fatan alkhairi da tabi shi da su.


Lokacin da ya shigo cikin maiduguri ya sha matukar wuya,saboda bai san kowa ba kuma bashi da wata guzuri a tare da shi.kudin motan da sodin goshi ya hada su.

Shine kwana a tasha,kwanan titi duk yayi su.

Rannan cikin dare yana kwance a gefen titi aka fara ruwan sama.nan ya fara neman mafaka.

Wani hadadden car wash ya gani mai wadataccen rumfan.ba bata lokaci ya fada rumfan yayi kwanciyar sa kan wata benci da ya gani aciki.

Daga ranan bukar ya maida car wash din wajan kwanan sa.

Wasa wasa har suka fara sabawa da managern har ya bashi aiki.shima yanzu yana wankin mota.

Alhmdllh tunda ya samu aikin nan rayuwa tayi masa sauki.yana yiwa mahaifiyar shi aike akai-akai,shima in kuma yana yawan zuwa duba ta.

Ranan wata safiyar laraba wani mutum ya kawo musu wata mota hadaddiyar jeep,ayi masa general wash.

Ganin babban mutum ne yasa managern ya kira bukar ya bashi wankin motan.

Badan komai ba sai dan shi kadai ne mai aiki da gaskiya.in dai shine ya wanke maka mota,toh duk inda kake sai ka dawo.

Shiyasa manager in yaga mutum mai kudi ne sosai kuma in yana son su.zama permanet customer,toh bukar yake bawa aikin.

Kaman yanda ya saba aikin sa ya cire duk abubuwan cikin motan kamin ya fara wankewa.a can kasan seat din baya ya tsinci wata madaidaiciyar bakar jaka.

Ajiyewa yayi a gefe ya cigaba da aikin sa.koda ya gama boye jakan yayi a cikin kayan sa ba tare da ya bari wani ya gani ba.

Karfe 8:30pm yayi yana jiran mai motan ya zo ya dauki abin shi amma shiru.

Managern ya bawa key din motan ya tafi dan yaci wani abu.

A gaggauce yaci abincin ya dawo saboda jakan nan.amma yana zuwa mai motan kuma yana fita a car wash din.

Napep ya hau ya bisu amma sun bace masa.haka ya dawo ya cigaba da boye jakan a wajan shi.ko sau daya bai taba budewa ba bare yasan ko menene a ciki. ya san halin managern su bashi rikon amana sam.


Wata yammacin laraba yaga mai motan nan ya kawo wata mota a wanke masa tayoyin su da alama daga kyauye suka dawo.

Bukar yayi matukar farin ciki da ganin sa.ana gama wanke masa,ya matsa kusa da mutumin cikin ladabi ya gaishe shi tare da miko masa jakan da ya tsinta a motan shi a watan da ya gabata.

Mutumin nan" yace anya kuwa?amma bari in nunawa yallabai"

Nan ya karbi jakan ya juya gun mai gidan shi da hankalin sa yana kan news paper da yake karantawa na daily trust.

Matashi ne da ba zai wuce 40 years ba,yana zaune cikin wata tsadaddiyar shaddar sa fara kal da hular sa amina rawaram.ga wata farar glass da manna a fuskan shu wanda ta kara fallasa kyan sa da hutun sa da a sarari.

Shi dai bukar kallon shi yake dan sai yanzu ma ya lura da shi dan ya dauka mutumin farkon ne mai motan ashe drivern sane?

Mamaki da zallan farin ciki suka bayyana a kan kyakkyawan fuskan shi.hannu yasa ya bude zip din jakan .sai ga daloli da wasu files sun bayyana.

Zaro ido bukar yayi cikin figici ganin abinda jakan nan ya kunsa.

Dago fuskan shi yayi dake cike da haiba yace "mallam bala wallahi nama manta da wannan jakan kwata kwata".

Kallon bukar da mamaki ya daskarar da shi yayi,ace irin wannan uban dukiya ace an manta da su?

"Ya sunan ka?"ya tambaya

"Bukar alibe"ya amsa a takaice.

"Ok ga kati na nan,gobe ka same ni a gida".

Amsa yayi tare da godiya,su kuma suka ja mota suka wuce.

Gari yana wayewa,bukar ya shirya cikin kayan sa masu dan haske sannan ya kama hanya Alhaji mustapha jidda kaman yanda ya gani a card dake unguwar damboa road.

Katon gida ne gari guda ga securities nan burjik.

Da farko hana shi shiga sukayi.sai da ya nuna musu card din,sannan wani security yayi miahi jagora zuwa cikin gidn har zuwa parlourn baki.

Tunda bukar ya shigo gidan.sakin baki da hanci yayi yana kallon gidan dan shi kam tunda yazo dunya bai taba ganin irin wannan gidan ba.hasalima bai taba tsammanin akwai su a dunyan nan ba.

Kasa zama yayi cikin kujerun alfarma da ya gani a parlourn. Dirshen ya zauna a kasa yana faman kalle-kalle.

Kusan awa daya sannan aka masa iso zuwa wani parlourn inda ya tarar da Alhaji yana jiran sa cikin shigan kananan kaya da ya fito da kuruciyar sa.

Bukar zubewa yayi a kasa yana kwasan gaisuwa,tambayan shi yayi tarihin rayuwar shi.ba bata lokaci ya sanar dashi bai boye komai ba.

"Naji dadi da kace kayi karatu,amma tunda ba kayi nisa ba,zan tura ka zuwa ghana kayi koda degree ne.akwai wani dan karamin gida a nan sai ka dauko mahaifiyar ka ta zauna anan har ka dawo daga karatun".

Godiya Bukar ya fara harda hawayen farin ciki wai yau shine zai je har abroad karatu?

Cikin lokaci kankani shirin tafiyan shi ya kan-kama,a time din har ya dauko mahaifiyar shi daga kauye.suna zaune cikin jin dadi a sabuwar gidan su.

Haka ya tafi ghana

Please Login or Register in order to submit comment