Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskan nan duk sun baci da hawaye.zuwa yayi ya durkusa a gabanta,yana especting ciwoyu kan nata da gani tana jin jiki sosai.

Da dabara ya dauke ta zuwa part dinta, akan gadonta ya shimfide ta sannan ya fice a gidan. bayan kaman 30 mins ya dawo tare da abokansa uku,umar da hafiz sai bakura wanda yake doctor ne.a parlour ya bar su ya hau sama zuwa dakinta.

A zaune ya same ta duk ido sun yi ja da alamu wani kukan take.a gefen side drower ya ajiye leda da ya shigo da su.bai mata magana ba ya wuce sip dinta ya dauko mata dogon riga da hijab saboda ba kayan kirki bane a jikin ta yace"karbi kisa rigan nan, na kira doctor a duba miki kafan".

Karba tayi tasa ba tare da tayi magana ba.rigan yana zuwa cinya ta rasa yanda zatayi ta jawoshi yazo kasa dan duk yanda ta motsa jikinta ciwo suke mata sakamokan mulmulowa da tayi kan stairs.yana ganin ta tana ta fama da rigan amma girman kai ya hana tace ya taimaka mata.daga ta yayi yaja mata rigan sannan yayi hanyan fita yana cewa ta saka hijab kamin su shigo.

Shida da bakura kawai suka hau sama yayin da su umar suke jiransu a parlourn kasa.suna shiga parlourn ta bakura ya zauna shi kuma ya karasa cikin bedroom din ya same ta,ta zura hijab din da yace tasa. yana daga tsaye yace mata"zamu shigo yanzu da doc ya duba ki saura ki cika mutane da rakin naki da kika saba ki dama nadan ke raguwa ce"hararan sa kawai tayi ta dauke kai,dariya yayi yana girgiza kai ya fita dan shigowa da bakuran.

Doctor b yana taba kafan ta zabura tana kokarin rike hannunsa,ganin haka yasa farhan hauwa godan ya rike ta. da na daman ya fara tayi kokarin dauriya ba tayi kuka ba.sosai ya duba sannan ya dawo na hagun wanda shine ya bugu sosai.

Kankame sh tayi sosai tana hawayen azaba dan ta kasa dauryan,bayanta yake shafawa a hankali alamun rarrashi, sun dauki lokaci a haka sannan doc bakura ya gama aikin shi.alhmdllh! duka kashin kafafun lafiya sai buguwan kawai, ya rubuta musu magani na sha da dana shafawa kuma yace ta samu bedrest sosai kar tayi saurin motsa kafan kuma ana gasa mata da ruwan zafi.


Dawowa dakin yayi ya samu ta kwanta sai maida numfashi n wahala take ya tausaya mata sosai amma ya dake ya wuce inda ya ajiye leda dazu.budewa yayi ya fito da take away da yazo mata da shi .plate da fork ya dauko ya juye a ciki.chips ne wit egg souce da plantain.maimakon ya bata dan shi sai da yaci abinci a gidansu umar kamin yazo.amma dan neman magana sa fork yayi ya fara ci. sai da yayi loma kusan uku sannan ya juyo yana kallon inda take,sarai kuma yasan yunwa take ji dan ko break fast batayi ba.

Cike da tsokana yace"bismillah ga abinci hajjiya ta"sai a lojacin ta juyo tana masa kallan wulakanci tace"wlh kayi kadan inci sauran abincika,baka kai wannan matsayin ba".

"Meye yayi zafi hajjiyata?daga tayi sai ys zama magana.taimaka miki fa nayi ganin yanzu kin zama gurguwa but tunda ba kya so na daina"hanyan fita yayi da abincinsa a hannu yaji tace"miko min wayata kan mirrow"fasa fitan yayi ya dawo ciki yana smilling ya dauko wayoyin kaman zai bata kuma sai ya tsaya kaman mai tunani yace"yanzu fa kikace ba kya son taimakona,wannan ma ai taimakon ne in kina si taso ki bini ki karba".


Ji tayi kaman ta kurma ihu dan takaici" wani irin wulakanci ne wannan ka dawo min da waya ta ko kuma kayi nadama" .winking ya mata kawai ya fice ya barta da haushi ya zatayi ta rayu ba kafa kuma ba mataimaki,dama niyan ta, ta kira ammi ta turo mata da ladi amma dan wulakancin na ya tafi mata da waya.


Alheri pharmacy nan yaje ya sayi drugs din sannan ya wuce gidan abba.da sallama ya shigo cikin palourn ya samu ammi da baki,tana ganin sa ta mike cikin farin ciki ta tarbe shi ya zauna.bedroom dinta ta wuce da bakin sannan ta dawo suka kara gaisawa take tambayan farhat.nan yake fada mata tsautsayi da ya same ta,da kuma baran a basu aron ladi saboda aikin gida.

"Zan baku ita ne sabida kace ance ta samu bed rest,in ba haka ba zan yarda in baku ita ba.dan nafi son ta dage ta iya abubuwan da da bata iya su ba.dama abban ku shiyake daure mata gindi take abinda taga dama,yanzu lokaci yayi da kamata tayi hankali".ammi tace.

Godiya yayiwa ammi.nan ta kwalawa ladi kira tare da bata umarnin zata bi farhan can gidan su ta kula da farhat saboda bata da lafiya.amsawa tayi da toh,ta wuce ciki ta hado yan kayan ta kadan ta fito duk jikin ta yayi sanyi.cos duk gidan suna murnan sun rabu da kaya,dan yanzu da bata gidan kowa hankalin shi a kwance yake suna rayuwar su cikin yanci.sai gashi ance ta koma gidan ta.bata san wani irin wulakanci zata tarar ba tunda ba idon ammi.

Farhan ya lura da halin da ta shiga kuma yasan irin tunanin da take,nan yace mata "kwantar da hankalin ki dan farhat ba za ma san kina gidan ba,na dauko kine saboda aiyukan gida ni kuma zan kula da ita".jin haka yasa ladi ta saki ran ta.

Dakin kusa da kitchen ya nuna mata a nan kasa,yace ta shiga ta ajiye kayan ta sannan tazo ta daura musu girki.


Bacci ya tarar tana yi lokacin da ya shigo dakin,dan haka bai tashe ta ba ya ajiye ledan drugs din ya fita.office ya dan leka akan zai dawo sharp sharp amma ya tarar da wani importan meeting wanda dole ya tsaya.sai bayan la asar ya dawo.a gurguje ya shigo gidan yasan by now farhat ta gama galabaita.abinci ya karba mata a wajan ladi wacce itama da gayya ta tuka tuwon semo da miyan kuks sanin farha bata ci da pepe soup din kifi danye,ya hada mata da juice da bottle water masu sanyi sannan ya nufi dakin ta.

A zaune yasame ta duk ta fige a cikin yini daya.ga azumin dole da ta yini da shi,ga kuma tana ji tana gani salloli har 2 suka wuce ta. ga fitsari ma tun dazu tana ji ba halin motsawa.

Ko kala baice mata ba ya zauna a gefen gadon yasa abincin a gaba ya fara ci.farhat sai hadiyan yawu take tana jira ya mata tayi irin na dazu amma ya bama iska ajiyanta.ganin da gaske ba zai mata tayi ba yasa ta juyo ta kwace plate din ta fara tura abincin cikinta ba tare da ta lura miyan kuka bane.loma ta rinka turawa hannu baka hannu kwarya.cike da tausayi yake kallon ta danta mugun bashi tausayi amma ya dake dan saita irin su farhat sai da haka.

Bai hana ta ba,har ta cinye tas ta daura da ruwa shima sai da ta ahanye sannan ta dawo hayyacin ta

Ido yake son su hada amma taki dago da kai,itama da kanta kunyan kanta take."hajjiya ta ya haka ba tayi zaki cinye min abinci,beside kince ban isa in ci abu in rage ki ci ba.abincin ma na yan kauye irin mu,ko kin manta in tuna miki?"

Kunya kaman ta nutse amma ta daure tace"kana da wani abinci ne a gidan?kaima in ka manta in tuna maka da kudin wa ka sayo?"

A zuciyan shi yace ba zata taba canzawa ba amma zanyi maganin ki .yana lura da yanda take mammatse kafa alamun fitsari ya matse ta.dan haka bai kula ta ba ya mike ya nufi kofan fita,yaji tace"zanyi sallah".

Ko kula ta baiyi ba ya kama kofa zai fita,ganin zai fita da gaske yasa tace"farhan zanyi sallah".cak ya tsaya daga inda yake ya juyo yana kallon ta dan tunda ya santa bata taba kiran sunan shi inda ba iyayen ta ba.sai dai poor bagger ko villager yace hmm kowa ya tuba dan wuya ba lada.

"Ina ruwa na ko ni kikewa sallahn?"yace yana murmushi."alwala zaka taimaka inyi"tace kan ta a kasa tana wasa da yatsun hannun ta.

"Yau kuma taimako na kike so?"shuru tayi batayi magana ba.yace bari in taimaka in kawo miki ruwan badan komai sai dan kince sallah zakiyi"ganin yayi hanyan bathroom zai kawo mata ruwa ya sa ta katse shi.


"A bathroom nake son yin alwalan"tace still kanta a kasa,sarai ya gane nufin ta amma ya basar yace mata"no ai zaki wahala zuwa bathroom din bari in kawo miki buta da bowl sai kiyi anan yafi sauki"gaba daya ta rasa ya zatayi ta fada masa a matse ta take,bata son fada ya raina ta kuma a yanda take ji tana gani in tayi good 5 mins tana iya sake shi akan gadon.

Wai farhat tana neman shawara jama a meye abin yi?,
[12/8, 7:24 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by Ummee yusuf(maman yusuf)


Page 37~38


Dago idon ta da ya ciko da hawaye tayi tabi shi da kallo,ganin da gaske zai kawo mata ruwan yasa tayi magana can kasan makoshi tace"i want to use d bathroom"ya jita sarai amma yayi kaman baiji ba,ya kama kofan zai bude.daga muryan ta da yake shaking tayi tace"i want to use d bathroom".

Da sauri ya dawo wajan ta da murmushin tsokana a kan fuskan shi yace"u want to use d bathroom,4 wat,?"yace yana kallon ta can yayi kaman mai tunanni yace"kai kai kai dama masu kudi ma suna yin kashi?ai na dauka ku masu kudi bakwa yi.sai mu talakawa ko kuma ina ganin miyan kukan nan da kika ci shi ya ruda miki ciki kinsan abincin mu ne na talakawa.let me hurry up dan zawo ba a iya rike ta.

Kunya hade da takaici suka hadu suka mata yawa har suka hana ta magana.dama abinda take gudu kenan,amma ya zatayi?dole ta lallaba ta kwantar da kai tunda tana cikin larura,inya so tana warkewa itama sai ta rama.


Zuwa yayi ya daga ta zuwa bathroom din a hankali yanda ba zai fama mata ciwon ba.rufe ido tayi bata son su hada ido dashi,har suka shigo idon ta a rufe suke.


murmushin mugunta yayi ganin yanda ta wani lafe a jikin shi,koda yazo ajiye ta da gangan ya dangwarar da ita har tana bugewa da jazuzzi

Dan kara ta saki tana rike gefen kan ta inda ta buge."wayyo hajjiya ta subucewa kika yi dan kinyi nauyi gashi kuma wani hamami ya cika min hanci ina ganin yau baki wanka ba.amma bari in hada miki ruwan wanka kina gama gudawan sai kiyi wanka kuma ki gasa kafafun ki"yace yana hada mata ruwan wanka.

Hawaye kawai farhat ke yi saboda irin cin mutuncin da farhan ke mata,amma ba tada bakin ramawa.yana gama hada matan yace in ta gama tayi mishi magana yazo ya taimaka mata wajan wanka.ko dago kanta batayi balle ta kula shi.


Tana wanka tana kuka kuma tana jawa farhan allah ya isa,dan shine silan jin ciwon ta kuma yake amfani da hakan yake ci mata mutunci.allah ya bata lpy sai tayi maganin wannan villagern.

Yana zaune a bakin gadon ta yaji alamun za a bude kofan bathroom din,da sauri ya mike ya nufi kofan ya ganta ta shimfida towel bayan tayi wankan ta zauna akai tayi jan gindi har zuwa bakin kofan.

"Meye haka farhat baza ki kirani ba?kin san ance kar ki motsa kafan amma har kike kokarin yin abu da kan ki"yace yana kokari daga ta zuwa cikin dakin.ita dai bata ce masa kala ba har ya dire ta akan gadon dan ta gwammace tayi kokarin yin komai da kanta,dan tsira daga wulakancin sa

Kayan shafawan ta ya kwaso mata akan mirro sannan ya dauko mata wani mini gown maroon colour da hijab din sallah.kayan ta saka ganin hankalin sa baya kan ta sannan ta tada sallah daga zaunen.ledan drugs din ya ajiye a kusa da ita yace tasha na sha kuma ta shafa na shafawan.

Fita yayi shima ya wuce part din shi. wanka yayi tare da dauro alwala ganin magrib ta gabato.jallabiya ash colour ya zura ya fesa turaruka ya fito sai da ya leka ta ya tambayi ko tasha maganin?da kai ta amsa mishi sannan ya wuce masallaci.

Sai da yayi sallahn isha i sanna ya dawo gida,direct dakin ta ya shigo ya tarar da ita tana kuka tana rike da guiwan ta da ya kara kumburi.

"Kukan me kike ne ko rakin zaki fara mana"yace yana jawo ledan maganin,yana budewa yaga ko taba drugs din batayi ba.bai tsaya jiran amsan ta ba ya tashi ya fice daga dakin ya sauko kasa wajan ladi dan karba mata abinci dan mantawa yayi bata son drugs.ya tarar still dan mugunta ladi tuwon ta karayi da miyan kubewa.

Tambayan ta yayi ba wani abincin ne sai wannan tace masa akwai peppe soup din kayan ciki.nan yace ta zubo shi din kuma daga yau kar ta dafa tuwo tunda farhat bata so.toh kawai tace ta zubo musu a wani warmer mai dan girma ta daura a tray.plates da spoons ta saka masa sannan ta miko mai,fridge ya nufa ya daukojuice da ruwa ya kara akai sannan ya nufi dakin ta da kayan.

Tana zaune a inda ya barta sai dai ta daina kukan,ajiyr trayn yayi agaban ta sannan ya zuba mata a plate ya tura mata gaban ta.ba musu ta karba ta fara ci a hankali,ta ci dayawa cos dama yuwan take ji.

Ruwan zafi da towel ya dauko a bathroom yazo dan gasa mata kafan dan da gani bata gasa ba dazun.towel din ya tsoma a ruwan zafin tare da matse dan ruwan sannan ya fara gasa mata.kuka ta fara tana rike masa hannu,ganin zata bata mishi lokaci yasa ya cire jallabiyan jikin shi a ajiye sannan matse ta a kirjin shi da hannu daya sannan ya samu daman gasa mata sosai.


Sake ta yayi ya dauko maganin shafawa,shima saida ya matse ta sannan ya shafa mata.

Dariya ne ya kwace masa yana yi yana nuna fuskan ta da yatsa da yayi daga daga da hawaye da majina.sai da yayi mai isar sa sannan ya tsagaita.ita kuwa har yanzu bata daina kukan ba tanayi tana hararan sa.drugs na sha ya miko mata,girgiza kai tayi maimakon ta karba."zaki karba ki sha ko kuma yanzu in danne ki kuma in kara matse kafan"jin haka yasa ta karba ta sha tana yamutsa fuska.

Dariya ya kara yi yana kallon ta,zuciya ne yazo mata wuya bayan matse ta da yayi ya mata mugunta kuma ya sata agaba yana mata dariya kaman yaga mahaukaciya?


"Wani kalan salon wulakanci ne zaka wani sani a gaba kana min dariya?"tace tana hararan shi.bai amsa mata ba ya mike ya dauko mata karamin madubi ya kawo dai dai fuskan ta.bata san lokacin da dariyan itama ya kwace mata ba ganin yanda majina da hawaye suka bata mata fuska.

Yana taya ta dariyan ya dauko tisue ya miko mata,karba tayi tana goge fuskan ta har yanzu murmushi bai bar fuskan ta ba.

Kallon ta yake cikin wani yanayi dan bai taba ganin ta tana dariya haka ba sai yau,dan haka ba karamin kyau tayi mishi ba.

Sukuyar da kan ta kasa tayi ganin irin kallon da yake mata kuma yana zaune ne daga shi sai vest da short neaker.ba zata iya misalta yanayin da take ciki ba amma she feel so comfortable being wit him.

Wall clock dake manne a bagon dakin ya kalla yaga har 10:20pm,dawo da kan sa kasa yayi yana ayyana ina ma su dawwama haka.


"Ermmm kinga time ya tafi bari in taimaka miki kiyi brush ki kwanta ko?"yace yana kallon ta.kan ta akasa tace"to"a hankali.

Tashi yayi ya dauke ta in a bride style ya fara tafiya a hankali kaman baya so.idon ta a rufe ruf tana shakan kamshin jikin sa da take matukar so.wara ido tayi da sauri jin sun shigo bathroom din dan bata manta yanda dazu ya dugurar da ita ba. dan dariya yayi yace mata"relax baby"cikin murya kaman mai rada. ajiye ta yayi hankali" kar kiyi abinda kikayi dazu kimin magana in kin gama"yace bayan ya miko mata duk abinda yasan zata bukata sannan ya fita tare da rufe mata kofa.

Jingina yayi da jikin bango yana jiran ta.can yaji tace"farhan na gama".murmushi yayi ya shiga ba tare da ya amsa ba.


Kwantar da ita yayi akan gado a hankali,kara mata karfin ac yayi tare da kashe wutan dakin ya bar mata side lamp sannan yaja mata bargo ya rufe mata rabin jiki.har ya juya zai fita ya dawo ya manna mata peck a goshi ya fit da sauri yaja mata kofa.

Idon ta a lumshe tana maida numafashi da sauri da sauri,hannun ta ta dora a goshi inda yayi pecking din ta,bargon taja ta rufe har fuskan ta,tana murmushi.
[12/9, 6:19 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

.FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee yusuf
(Maman yusuf).


Page 39~40

Jingina yayi da jikin kofan dakin ya lumshe ido,ya kasa koda daga kafa balle tafiya. inama zata yarda su kwana daki daya?.da kyar ya daure ya kai kansa part din sa,

Wanka ya karayi waiko zai samu sassaucin abinda yake ji.shirin kwanciya yayi cikin white pyjamer sannan yabi lafiyar gado.

Bacci ya kauracewa idon shi dan da zaran ya rufe ido yanayin su na dazu yake gani.ya dade yana ta juyi amma baccin yaki zuwa.shima mamakin kan sa yake dan tunda akayi auren su bai taba jin son kasancewa da ita ba irin yau.

Alwala ya dauro ya fara nafila dan samun sauki.bai hakura ba sai da yaji idon shi suna rufswa saboda bacci sannan ya bi lafiyar gado.mikewa daga kwqncen kaman an mitsine shi yayi hanyan part din farhat dan ya kara duba ta kamin yayi bacci.

Farhat kuwa tunda tasa kanta cikin bargo ta kasa fitarwa sai murmushi take.can ta daure ta fito da kan ta ta lumshe ido da niyan bacci,sai ganin farhan tayi zai kara pecking din ta.bude ido tayi taga bakowa dakin sai ita kadai.tsaki taja tana jin haushin kan ta,cos tun ranan da ta dora ido a kan farhan bata taba kwanciya bacci ba tare da tayi tunanin shi ba.a lokacin dai tasan tunanin yanda zata kuntata mai ne ko kuma tanda zata kore shi a gidan su.amma yau ta rasa wani tunani take yi a kan shi yau.

Kallon agogo tayi taga biyu saura,cike da jin haushin kan ta tayi wani irin juyi wanda sam ta manta da rashin lafiyan kafafun ta.gum taji ta buge kafan da bango,wani irin radadi ciwon ya fara kuka ta saki tana jan allah ya isa ma farhan gashi ko tunanin shi tayi itace a wahala.

Tun daga parlourn ta yake jin kukan ta,da sassarfa ya karaso cikin dakin sannan ya kunna wuta haske ya gauraye dakin.

Hango ta yayi can karshen gado tana ta kuka,karasowa yayi yana tambayan ta ko kafan ne ya hana ta bacci,ko kala bata ce masa saima dauke kanta da tayi.

A mamakin ce ya tsaya kallon ta,yarinya sai kace mai aljanu kama ba dazu dazun nan suka rabu lafiya ba?.yaye bargon yayi dan yaga kafan amma abinda ya gani yasa yayi sauri rufe ta.gani yayi rigan jikin ta ya tattare yayi sama wajan juye juyen ta cinyoyin ta gaba daya a waje suke.nadaman zuwa dakin ya fara dan da kyar dazu yayi jinyan kansa ya samu sauki sai gashi yanzu yazo ya kalli abinda ya dagula mishi lissafi.

Cikin drugs din ta ya nemo mata pain releaver ya hada da ruwa sannan ya hauro kan gadon yace mata"tashi ki sha magani zaki ji sauka yanzu"

"Ni ka rabu dani bana sha duk kabi ka takura ni".

Fizogo ta yayi da karfi ya zaunar da yana zaro mata ido yace"kin san allah in baki sha maganin nan ba wallahi zan baki mamaki".ganin yanda ya harzuko yasa jiki na bari ta karba ta shanye.

Shima ganin yanda ta tsorata da yanda ya mata,yasa yayi murmushin nasara cos yaga hanyan rage zafi cikin ruwan sanyi.cikin hade rai yace" kwanta kuma in kara ji kina ma mutane kuka akan abu kalilan ki gani kar kiga ina kyale ki".

Kwanciya shima yayi a bayan ta,a razane ta tashi daga kwancen jin mutum a bayan ta,kara murtuke face yayi yace"me haka koma ki kwanta dan ba abinda kike tsamani ne ya kawo ni nan ba cos banida wannan time din,just behave urself".haka ta kwanta a daddare.tana ji ya jawo ta jikin shi ya rungume tare da sauke ajiyan zuciya mai karfi na samun relief.

Ko motsi batayi ba,illa shiru da tayi tana jin dumin jikin shi da kamshin turaren shi da ya saukar mata da wani irin natsuwa.farhan shima ta wajan shi haka sai ajiyan zuciya yake.

Zuwa can yaji tana fidda numfashi a hankali alamun tayi bacci,a hankali ya fara shafa mata jiki tare da dan mammatse mata kaman mai mata tausa.gyara kwanciya tayi a jikin shi sbd jin dadin abinda take ji cikin bacci.a haka har ya dan samu saukkn abinda ke damun shi.

6:40am farhat ta bude ido sanadiyan hasken rana da ya dan huda ta window.

Ganin tayi a makale jikin farhan da yake baccin sa hankali kwance,kurawa face din shi ido tayi tana kallo,for d first time take ganin wani kyau na musamman a tare da shi.fuskan nashi yana baccin ma kaman mai murmushi ga eye lashes dinsa kaman anyi masa kari nd dogon hancin sa kuwa kaman na salman khan ga lips din sa pink kaman ya shafa lip stick.sajen fuskan shi daya kwanta ta kai hannu zata taba kuma sai ta janye.lip din ta kai hannu a hankali ta dangwala a hankali wai a zaton ta lip stick ya shafa amma ga mamakin ta taga yatsan ta empty.murmushi tayi tana kare masa kallo,dan ba karya farhan ya hadu over.


A hankali ta tashi zaune kuma da ikon allah yau taji jikin nata da sauki sosai.

Bude ido farhan yayi ya tashi zaune yana salati ganin yanda suka makara sallahn asuba.

Bai kalli inda take ba ya nufi bathroom yayi alwala ya fito tare da shimfida abin sallah.tana nan zaune ya idar da sallah.zuwa yayi bakin gadon yasa hannu ya dauke ta ya nufi bathroom da ita.

Ajiye ta yayi sannan ya hada mata ruwan wanka mai dumon gaske.tana nan zaune tana jira ya gama hada mata ya fita amma sai gani tayi ya nufo ta gadan gadan fuska a hade wai zai cire mata kaya,rike rigan tayi gam idon ta taf da hawaye take kallon shi amma bai dago ba balle su hada ido nd tsoran yi masa magana take ganin yanda ya hada rai."kar ki bata min lokaci dan na gaya miki i dont have time a kan abinda yake zuciyan ki just tryin to help u".

Ba yanda ta iya tana ji tana gani ya cire mata riga ya sata a cikin bath tub,ssi kakkare kirjin ta da hannayen ta.bowl din ruwan zafi da towel ta dauko yazo gaban bath tub din.tsoma towel din yayi a cikin ruwan zafin ya matso da zai dora kan kafan ta,ai ko nan da nan ta rude ta rike hannun sa mai towel din tana hawaye dan bata manta wuyan da tasha ba jiya.

"Dan allah kayi hakuri ka bari wallahi da zafi" tace still tana hawaye.

Dariyan jin dadi farhan yayi a cikin ran sa ganin tarkon sa ya kama tsuntsu cikin sauki.amma a zahiri kuma murtuke fuska ya karayi yace"karma ki bata bakin ki cos dole in gasa miki dan haka ki bar ma roko na".

Pyjama jikin shi ya cire,ya zama daga shi sai boxer,shiga yayi cikin bathtub din tare da kamo ta ya matse a kirji sannan ya fara gasa mata da kyar cos yanda jikin sa yake manne da nata ga ba kaya a jikin su.wani irin kasala ce ta rufe sauko masa,cikin dabara ya rinka wasa da duk inda yasan zai samu natsuwa a jikin ta da sunan gashin kafa.bata lura da abinda yake ba sosai saboda zaban da ya ishe ta.

Bai bar ta ba saida ya musu wanka tare ,farhat ta rasa wani sabon iskanci farhan ya samu gata ba bakin magana sai nannokewa take tana kare kirjin ta.alwala ya sata tayi sannan suka fito.lotion ya dauko zai shafa mata,kallon shi tayi da idon ta duk hawaye tace"na roke ka ka bari zanyi da kaina".

Ganin yanda ta zama kalan tausayi yasa ya kyale ta ya wuce part din shi bayan ya miko mata kayan sawa da hijab din sallah yau harda inner wear ya dauko mata.ita dai yau kunya

Please Login or Register in order to submit comment