Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asali nasan kawayen ki zasu gane am frm village, hakan zai sa su raina ki ni kuma bana son bada ke .wannan tare mukayi karatu a london".

Tabe baki ta kara yi tace"an dai ji kunya".

Ruky ita ta bada tarihin amarya,daga nan aka bukaci su fito su yanka cake.

Kin tashi farhat tayi,dai dai kunnen ta ya rada mata cewa"kinsan allah in baki tashi ba,wlh chak zan daga ki in kai ki kuma kin san sab zan iya".ba bata lokaci ta mike sanin zai aika ta abinda ya fada,dariya yayi shima ya mike tare da riko hannun ta suka zo inda aka tanadar da hadaddiyar cake din su da yasha decorating irin dressing din jikin su.

A tare suka rike dan karamin wukan suka yanka cake din aka tafa musu.

"Kar ka taba sa ran wai ni zan baka cake a baki a bainar jama a"tace dashi kasa2 tana murmushi kaman abin dadi take fada masa.

"Nima bana bukata miss ego"yace mata shima yana murmushin.dauke kanta tayi gefe.

Gutsuro cake din yayi ya rike a hannun sa,dayan hannun kuma yana rike da hannun ta.matse hannun yayi da karfin sa,ai ko taji zafi.juyowa tayi da niyan masifa tana bude bakin ya tura mata cake din kamin ta ankara ya sunkyoda kan sa ya kawo bakin shi kan nata ya gutsiri cake din tare da tura mata sauran da bakin shi.

Gaba daya hall din ya kace da tafi da sowa saboda abinda farhan yayi ya bada kala sosai,ya burge yan matan wajan.wasu sai addu an allah ya basu romatic miji irin farhan suke.yayin da farhat haushi kaman ya kashe ta kan abinda ya mata cikin bainar jama a.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAN

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by ummee yusuf(maman yusuf)


Ina godiya gare ku masoya na,masu comments da kuma masu bina private ina jin dadin kaunar ku gare ni.bansan yanda zan misalta muku yanda nake jin ku a raina ba.ina so ku sani nima ina kaunar ku sosai.

Page 29~30

An cashe sannan kuma anci an sha,sai wajan 10:30pm sannan aka tashi a wajan dinnern

A al adan kanurai akwai masu yiwa amarya zaman 7,ana zaban mutum 1-1 ko 2-2cikin yan uwan maman ta da baban ta sai kuma kawa dan debe mata kewa.dan haka farhan tare da abokan sa ya wuce sabida yasan muddin yazo toh lalle za a wanko masa a kawo masa a daren nan.

Da washe gari akayi yini a gidan amarya,inda dangin amarya da ango zasu haduwa a yini tare.da yamma kuma akayi kalawa.

Wannan ma al adan yan maiduguri ne da yake bawa kowa dsman mika kyauta ga amarya da ango. A compound gidan akayi taron,katon carpet na alfarma aka shimfida da tim tim anan amarya da angon suka zauna tare da daga hannyen su kaman masu addu a.ana jika abu mai yauki kaman karkashi ko kubewa bushasshe,duk wanda yazo ya ajiye kyautar sa toh sai ya lakato wannan ruwa mai yaukin ya shafawa hannun amaryan ko ango.

Hakan ta kasance dan kyauta kam sun shata more especialy farhat,set din gwalagwalai car keys.tsaban kudi kam ba magana.kanta a kasa yake dan ta tsani abu mai yauki,kyankyami yake bata shiyasa bata son dago kanta balle ta gani.dan haka bata san su waye suka bata gifts ba but tasan yawanci daga yan uwan ammi ne cos yan uwan abba ba wasu masu kudi can bane.

Sai magarib aka watse daga taron.yauma farhan yaki kwana a gidan,yace yana can abokan sa da suke shirin komawa.cikin kwana 2 abokan sa suka wuce kuma a ranan aka sallami matan da suka zauna mata da sha tara na arziki.

Tana zaune ita kadai tana yaba yanda aka tsara mata daki,komai yayi mata.tashi tayi ta fito parlon ta shima ya birge ta.sai ta samu daman karewa part din nata kallo,dan lokacin da matan sunan ko parlourn ta bata fitowa tana cikin bathroom komai su suke mata kaman wata sarauniya.

Haka tayi ta zaga gidan tana yaba tsaruwan shi tare da jinjinawa abban ta.ta tabbata ita yar gata ce duba ga gidan da ya basu da irin funitures da aka zuba,ba karya yafi gidan su komai da tsaruwa.dayan kofa da tagani a sama kusa da part dain ta,koda ta murda taji shi a kulle.tabe baki tayi tana cewa"da alama nan ne bathroom din shi, harda wan kullewa kome za a dauka a dakin oho"

Zama tayi a parlourn sama ta kunns kallo,sai dai ba kallon take ba chartn take dasu ruky.suna bata shawaran yanda zata gara farhan,murmushi kawai take tana jin su cos tana ganin nasu wasa ne akan tanadi da ta mishi.

Wanka tayi bayan tayi sallahn isha i,tayi shirin kwanciya,sleeping dress tasa riga da wondo.but wondon gajere ne kuma rigan shima iya guiwa ne.wani farin humra da akayi mata hadi na musamman da turaren lailatul sahara,ta shafe jikin ta dashi ammi da kanta ta hada mata shi

Parlourn ta tafito tayi kwanciyar ta kan 3 seater tana kallon film da ake a mbc bollywood.farhan ne yayi sallama ya shigo hannun sa dauke da ledoji,ciki ciki ta amsa sallaman tare da mayar da hankalin ta kan kallon da take.

Zama yayi kan kujera dake opp da nata,bai damu da halin ko in kula da tayi masa ba.kallon ta yake cikin wannan sleeping dress da ta saka ga wannan kamshin humran duk ya cika masa hanci,ganin in ya cigaba da zama a dakin shi zai cutu yasa ya mike ba shiri.tana ankare da yanayin sa,da gangan tayi wani mika tare da hamma wai ita bacci take ji.ba shiri ya ajiye mata ledodi 2 ya fice da dayan.dariya tayi tace"dani kake zancen yaro".

A parlour ya ajiye ledan hannun sa sannan ya shiga kitchen ya dauko plate, cup nd knife ya fito dasu bayan ya dauraye.zama yayi kan rug tare da fito da kaza gashasshiya da ya siyo a d ultimate suya.cika glass cup din yayi da fress milk.yana ci yana korawa da fresh milk din,sai da yaji yayi dam sannan yayi hamdala cos ya manta yaushe rabon da ya zauna yaci abinci haka.tattara kayan da ya bata ya kai kitchen sannan sauran yasaka a fridge.

Part dinsa ya shiga bai tsaya a parlon ba ya wuce bedroom, direct bathroom ya fada bayan kayan jikin sa.wanka yayi ya fito,singlet da boxer kawai ya saka ko mai bai tsaya shafawa ba dan rabon sa da samun bacci ishashe ya kusa sati.dan haka ba bata lokaci ya bi lafiyan gado.

Farhan ma kadan taci saboda a koshe take,brush tayi ta kwanta ita ma.

Washe gari ana kiran assalatu ya tashi,ya kama nafila har aka kira sallah.da zai tafi massalaci sai da ya kwankwasa mata kofa sannan ya wuce.bai dawo gida ba sai da rana ta fito koda ya shigo ya leka dakinta yaga ta koma bacci shima baccin ya kara komawa sai 11 ya farka.

Wanka yayi ya shirya cikin riga mara hannu fari da wando 3quater,fesa turaru kansa yayi sannan ya fito.wani kamshin abinci mai dadi jaji yana masa maraba.bude hanci yayi yana shakan kamshi wanda ya tayar masa da tsohuwar yunwan sa.hanyan kitchen din yayi.

Yana zuwa ya ganta a tsaye ta juya baya tana cikin aikin ta.


Mukut ya hadiye wani yawu da ya tsaya masa a wuya sakamakon irin shigan da tayi,dan karamin wando ne a jikin ta wani riga wanda bashi da maraba half vest.kananan kitson da aka mata ya kwanta har gadon bayan ta.

Kamshin turaren shi da taji ya cika mata hanci yasa ta waigo,ganin shi tayi
rugume da hannayen sa a kirji ya jingina da kofan kitchen ya zuba mata ido .

Maida hankalin ta tayi kan aikin ta,kaman ba zatayi magana ba yaji tace"ya wannan kallon,ko ka kyasa ne?"sarai yasan magana da ya fada mata ranan dinnern su ta rama.

Dariya yayi yace"ko 1 nazo inga me kike jagwalgwala mana ne".

A zuciye ta juyo tana wani irin kallon kayi kadan sannan tace"bansan ranan da kanka zai fara lissafi ba,saboda rashin lisssfi irin naka ka dube ni kace wai ni zan maka girki?ko mijin da na aura ina so bai isa in masa girki ba balle kai poor bagger.tunda ka shirya zama dani dole ka koyi duk wani hidima na gida,abincin ma daga yau bazan kara girki ba nd dole kai zaka min tunda alfarman abba na kake ci".

Kashe gas din tayi bayan ta sauke abincin ta,kuma da gasken ta kanta kadai tayiwa.dauko plate tayi ta kwashe irish da ta soya,ta hada da chicken na jiya tare da vegis.baice mata komai ba yanan nan tsaye yana kallon ta,plate din ta dauko zata wuce ya tare hanya still idon shi akan ta.

"Matsa min a hanya "tace ba alamun wasa a fuskan ta.kwace plate din yayi yana shirin juyawa.a fusace tace"meye haka ne?zaka wani karbe min abinci,in kana so ne sai kayi abinda ka saba mana in baka.ba wai ka karbe min ba".

Sai a sanna ya juyo yace mata "me na saba?"

Ba tsoro bare shakka tace"maula mana,dats wst u re a bagger"tace cikin karaji.

Nan da nan fuskan shi ta sauya,ya fara shigowa ciki ganin yanayin fuskan shi yasa ta fara ja da baya yana binta.

Akan kitchen cabinet ya ajiye plate din abincin,zata gudu ya fizgo ta.cikin murtuke fuska yace"nine mai maula?"

Cikin dakiya tace"eh an fada karya nayi?kayi abinda zakayi mana in ba......."

Cike da mugunta ya kamo leben ta na kasa yana mata wani irin tsotsa cike da mugunta.radadi take ji har tsakiyan kant,dukan kirjin shi take da hannu 2 amma ko gezau.sun fi minti 10 a haka,sai da yaga tsayuwa na gagaran su sannan ya sake ta yana maida numfashi da kyar ga idon shi da ya canza kala.

"Next time watch ur tongue"yace batare da ya kalle ta ba ya dauki plate din abincin yayi gaba.ya barta da bakin ta sai zogi yake ,abinka da yar hutu tana tabawa taga jini jini.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by Ummee yusuf (maman yusuf)

I dedicated this page to my luvly sis adama muhammad goni.

Page 31~32


Jingina tayi da fridge din da yake bayan ta,kuka take son yi amma ta hana hawayen fitowa.haushi 2 ya hada mata,kaman ita wai ta bata lokaci tayi girki wannan poor bagger ya kwace,ga kuma muguntan da yayi mata ya fasa mata baki.

"Wlh bazan yarda ba sai na rama"tace,fitowa tayi a kitchen din ta wuce part din ta.a palour ta tarar dashi ya hada tea da abincin da tasha wahala ta girka yana ci.

Ko kallon inda yake batayi ba ta wuce shi fuuu tare da banko kofa,shima ko a jikin sa zagewa yayi ya cigaba da cin abincin sa.

Snacks da aka kawo mata tun na aure,shi ta debo a plate ta tea mai kauri.tana sha,tana hawaye dan tean in ya taba inda ya fashe sai taji kaman ta kurma ihu dan azaba.tana gamawa tayi kwanciyar ta,tana kisissima yanda zata rama dan wlh yayi kadan yaci bulus.

Farhan shima yana gamawa bai bi ta kan ta ba yayi ficewar sa.

Sai kusan azahar ta farka,wanka tayi bayan tayi sallah.ta shrya cikin wani tsadadden material milk colour dinkin doguwar riga ya mata kyau sosai.

Saukowa kasa tayi sannan ta fito compound din gaba daya tana karewa gidan kallo,can ta
hango wani dan matashin saurayi yana bawa flowers ruwa.

"Kai mallam"tace da dan karfi,dago kansa yayi ya kalle ta.ya fito shi tayi da hannu,ajiya tiwon hannun sa yayi ya taho a guje tare da rusunawa yana kwasan gaisuwa.bata amsa gaisuwan ba wani karamin paper da kudi 1k ta miko masa tace"kaje chemist ka siyo min wannan yanzu".

Karba yayi ya nufi gate da sauri.komawa tayi palourn kasa ta zauna jiran sa,bai dauki wani lokaci ba ya dawo.sallama yayi a bakin kofa sai da ta bashi izini sannan ya shigo ya mika mata maganin da change dinta maganin kawai ta karba ta wuce sama ta barshi nan durkushe yana ta faman godiya.murmushi kwance a fuskanta ta wuce kitchen ta fara gikinta.

Garnished macoroni tayi sai baked patatos wit coconut nd pineapple juice. wasu warmers masu dan karan kyau ta dauko abincin,juice din ma a jug 2 ta zuzzuba.maganin da ta sayo naga ta zuba a dayan jug din,spoon tasa ta juya da kyau sai da ta tabbatar ya narke sannan ta fito ta jera komai akan dinnig.ta tsara yanda zai ja hankalin mutum sannan ta koma kitchen ta dauki tray da ta shirya abincin ta akai tayi part din ta.dashi kana ganin fusakan ta u will know shes up to somrthing.

Zama tayi taci abincin ta hankali kwance sannan ta kwashe kayan ta koma kitchen din,bata fito ba sai da ta wanke kayan da bata tare da gyara kitchen din sab sannan ta fito ta dan gyara palourn,ta kunna coal tasa turaren wuta ko ina ya kama kamshi.

Motsi taji a main palo shiyasa ta fitowa farhan ta gani a dinning area alamun ya kwaso yunwa sosai. kallonsa tayi fuskanta dauke da murmushi can kuma ta murtuke face dinta ta nufo shi,a lokacin shi har yafara cin abinci.

Wani kallo ta fara mai ta iso dinnign tace "mallam ya haka?wai ta za'ayi inyi girki kazo kana cinye min,nagaya maka banaso dan baka isa inyi maka girki ba".

Ko kallanta baiyi ba yacigaba da kwasan gara cos abincin yayi mai dadi.ganin ba zai kulata ba yasa tace"poor bagger ta wuce da sauri har tana waiwaye.kwafa yayi a ransa yana cewa bari ingama cinye miki abincin sannan inzo inyi maganinki.

Sai da yaji dam sannan ya ture plate din,glass cup ya dauka ya cikata da juice din, yana dorawa a baki ya kasa saukewa saboda dadi da ya mai ba hakura ba sai da yasha cup 1 da rabi kafin ya hakura.

Farhat tana can bakin kofa tana lekenshi. kwashe wayoyinsa da car keys dinsa yayi dan ya karasa palo wani irin murda yaji cikinsa yayi har sai da ya durkusa daurewa yayi ya mike yana ciccize lebe yana tafiya dakyar,fitowa farhat tayi tana kwasan dariya har da rike ciki kallonta ya tsayayi dan baisan abinda take ma dariya ba.da kyar ta tsagaita tace"na gaya maka kabar cinye min girki kaki jiba.toh ga maganin mai kwadayi gobema in kaga abincina ka dauka kaji?" tace tana kara kwashewa da dariya.

Sai alokacin ya fahimci inda ta dosa wato wani abin tasa masa a abinci? a zuciye yayi kanta amma kamin ya karasa yaji cikin ya wani hausinewa aiba shiri yayi hanyan part dinshi dan bashi da wani burin da ya wuce ya ganshi a toilet.a dari ya isa dakinsa ba wata wata ya fada toilet ya kece da matsaneciyar zawo sai zufa yake hadawa.

Bin sa farhat tayi tana cigaba da dariya tana shiga palonsa, wani katuwar ashar ta lailayo ganin yanda palon ya mugu haduwa da tsaruwa.ko makaho ya shafa yasan yafi nata komai,kaman tunzurata ake ta fada bedroom din shima the samething. tab wallahi ba zai taba yiyuwa ba tayaya abbanta zai gina gida ya basu nd a dauki most precious part a bawa wannan villagern,tab da sake tace tana ta faman cika da batsewa dan Jira take ya fito daga toilet din,farhan sai da yayi wanka sannan ya fito yana tsara yanda zai taka yarinyan nan da wallahi yau ta kaishi makura sam baisan tana nan ba ya fito daga shi sai dan wani karamin towel yana ta faman hakki kaman wanda yayi gudu,dan shi ya san irin azaba da yasha yau.

Lokacinda ya fito tana ganinshi sai da taji wani sabon yanayi ya ziyarce ta, zuba masa ido tayi taga yanda jikinsa yake a murde har da wani packs ga farin fatan sa har wani powder2 yake.jin alamum mutum yayi a dakin nan ya Juyowa ya ganta zaune akan bed dinshi.

Wani mugun kallo ya bita dashi yace"me kike min a daki?".

sai a lokacin ta dauke idonta akanshi tare da tabe baki, tace "kana da dakine a wannan gidan? gidan abba nane so duk inda naga dama nan zan zauna so daga yau zan dawo dakin nan kai kuma ka koma wancan."


Kamshin sabulun da tajine yasata saurin juyowa,ganin shi tayi a gaban ta fuskanan nashi kaman bai taba dariya ba yace, "miss ego u will never change. wannan dakin da kika gani shine nawa before the count of 3 ki koma inda kika fito if not.."

If not wat? do wat ever u ting".


"Haka kika ce?.yace yana kallon ta.

"Yes "tace tana hararan sa. towel din jikin sa ya fara kuncewa,da sauri ta rufe idon ta da hannayenvta tana shirin guduwa a dakin tace"a nan kafi kauri ai".


Cafkota yayi yace "me kika samin a abinci?".

Ba tsoro tace"aika gani da idon ka no need to ask but tunda kai dump head ne toh maganin ruda ciki na saka maka dan next time ka kiyaye abincina."

kankace ido yayi yana kallonta ya rasa ma me zai mata yaji dadi,koya shirya mata mugunta,son da yake mata yake sawa yaji tausyinta.


Hankada ta kan bed din yayi da karfi ta fada sai da ta danyi kara cos taji zafi tana yunkurin tashi yabita ya mata rumfa ya danne mata hannu da hannuwan sa yace"zanyi maganinki yarinya."

Bakinsu ya hade waje daya ya rinka musu wani irin tsosa wanda yafi na dazu da ya mata da safe,gashi dama har ya dan kumbura kuka take son yi amma ta danne ga azaba, yafi 15 mins a haka sannan ya sake mata baki ya fara kokarin neman zip din riganta.


Cikin dishashiryar muryan ta yaji tana cewa"allah ya isa mugu kawai,ba abinda ka iya sai iskanci".

"Iskaci?toh ai baki ga iskanci ba yarinya.let me show u now" yace ya dago ta da karfi tare da zuge zip din ta.

Tumurmusa ta yake son ransa cike da a mugun ta tun tana daurewa har ta fara magiya tana hawaye amma kaman kara tunzura shi take.ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta tattara dan karfin ta,ta ture shi.

Da gudu a fita a dakin tana kuka,ko kadan baiyi yunkurin binta ba saima lumshe ido yayi yana maida numafashi.

Kan gadon ta ta fada tana kuka sosai amma bata daina cewa "allah ya isa mugu wlh sai na rama".
[12/5, 7:34 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by ummee yusuf(maman yusuf).


Page 33~34


Koda ta fito ta shirya,kulle kofan part dinta tayi dan bata son su kara haduwa ba tare da ta samu mafita ba.

Shima farhan bai damu da kulle kofan da tayi ba dan dazu shima da kyar yayi jinyar kansa ya dawo dai dai. fito yayi ya bar gidan.

Sai bayan sallan isha' ya dawo gidan still kofanta a rufe yake,kuma da
alamu bata fito ba tunda ya fito.ganin haka yasa ya fita yaje ya musu take away ya dawo.

Spare key ya dauko ya bude part din nata ya shiga ,kwance ya sameta cikin dogon riga na roba pink colour, yabi jikinta ya lafe da alamu bacci take.tsayawa yayi akanta yana kallon yanda take bacci bakinta ya tsurawa ido yaga inda ya mata mugunta har ya dan kumbura yayi ja.har ya sunkuya zai shafa
gefen fuskanta sai ya fasa,ya daga hannu ya fallawa boom boom dinta mari.

A razane ta farka tana neman guduwa ganin shine yasa ta hada rai tana masa kallon up and down murmushi yayi yace"kimma yi sallah kuwa?kin wani hangame baki kina bacci".

A wulakance ta kallesa tace"ina ruwanka da sallata ko kai nake ma sallahn?"

Abincin ya ajiye mata ya wuce ba tare da ya kara kulata ba.yasan inya biye ta zuciya zai iya dibansa ya mata illa.

Da washe gari da safe ta kira ammi ita gaskiya a kawo mata ladi dan ba zata iya da aikan gida ba.

"Ki koya da kanki ba wata ladi da zan turo miki, dama auren kenan. bare gida daya ke sai mijinki shine za'a turo miki yar aiki?"kaman zatayi kuka tace"ammi allah gidan ya min girma ban san ta ina zan fara ba,pls ammina".

Toh naji amma sai nan da zuwa sati mai zuwa zata zo".

Cikin jin dadi tayiwa amminta godiya suka dan taba hira irin na uwa da ya sannan suka katse.

Sun kwashe kusan sati ba ruwan wani da wani,ita farhat tana can tana tunanin hanyan da zata bita rama muguntan da ya mata, yayin da shi kuma yake fama da kanshi dan tun ranan da incident ya faru tsakaninsu yake matukar son kasancewa da ita, ga kuma wani sabon salo da ta samu kullum cikin sexy wears take.shiyasa ya daina shigaharkanta, yakw baya baya da ita, yafi son sai ta fara son shi da gaskiya kamin suyi rayuwar aure kaman sauran mutane.

Yau tun safe da tashi take neman takako maaifa dan bata da wani buri da ya wuce ta kuntata mishi wanda zaisa yayi nadaman auranta.

Wani bad dressing tayi cikin mini gown red colour mai spagetti hand. ta nufi part din farhan.

Farhan yana kwance yana baccin safe ta shigo har cikin bedroom ta tsaya a kan sa tana tunanin me zata mishi ya farka.

Parlourn ta koma ta dauko bottle water mai sanyi ta dawo. farhan yana cikin bacci,kaman a mafarki yaji saukan ruwan sanyi ajikin sa,a girgice ya farka yana neman wanda ya masa wannan aika aikan.farhat ya gani tsaye akan sa tana masa kallon wulakanci,"dallah mallam ka tashi kazo ka ninke min kaya'an samu sanyin a.c an baje ana baccin asara".

Bai taba jin baccin rai irn na yau ba,kullum samfurin wulakanci kala kala yarinyan nan take tsiro dashi.ido ya zuba mata yana aiyana yanda zai ci uban ta yau yake.

Saida tayi nadama ganin yanda fuskan shi da idon sa suka koma ja saboda bacin dan tunda take bata taba ganin bacin rai a tare da shi haka ba.

Tashi yayi a zuciye yana shirin kamo ta.ai da gudu ta fita ,shima bai wata wata ba ya rufa mata baya.a guje suka fito daga part din sa,tana zuwa bakin kofan parlourn ta,taga baifi taku hudu zuwa biyar ya kamo taba.hanyan stairs tayi dan sauka kasa.

Matakala uku kawai ta taka,takalmin kafan ta ya goce dama gata ma abociyar sa high hill.

Dan ihu ta saka jin yanda idon sawun ta na kafan ta na dama ya gurde.wani ihun ta kara wanda yafi na farkon sanadiyan faduwa da tayi guiwan ta na kafan ta na hagu ya daki karfen benen.mulmulowa ta fara tana cigaba da ihu har ta fado wanwas gaba daya daga matakalan benen.

Yana tsaye yana kallon ta gaba daya ta galabaita sai nishin wahala take,idanun ta duk sunyi ja ko hawaye ta kasa sabida azaba.

A nutse yake saukowa daga stairs fuskan shi ba yabo ba fallasa ,dab da ita yazo yana kallon yanda kafafun ta da taji ciwo duk sun kumbura sai dai guiwan yafi kumburi da akamu tafi jin ciwo anan.

Dago da jajayen idon ta tayi tana kallon shi'ganin yanda yake kallon kafafun yasa tayi tunanin yazo taimaka mata ne dan haka tace"meye ka tsaya kallo na?take me to my room i cant stand".

Dariya yayi yana girgiza kai yace"nayi miki kama da dan aiken ki ne?"

Dan aike ne mana ko ka manta a inwan da kake in tuna maka?toh a inuwan abba na kake".

Gyada kai yayi yana murmushi yace"kuma fa haka ne.kin ga ko dole in miki aiki.amma bari in fara duba miki kafan cos sosai na iya gyara.jawo kafan ta na dama yayi da karfi dai dai inda ta gurde.ihu ta saka tana rike masa hannu.yace"ke ni bana son raki,dama ammi ta fada.in ba raki ba meye abin kasa tashi anan?bari in duba dayan inga ko matsalan daga shine".

Guiwan ya matse mata da karfi cikin mugunta.ihu take cikin azaba tana"mugu kawai ka sake min kafa bana so.nace ka sake min kafa ko kuma wlh in na tashi sai kayi nadama.

Tashi yayi ya zura hannayen shi a aljihu yana kallon ta yace"oh me yayi zafi na bari i was only trying to help karki zama gurguwa.amma tunda kince in kin tashi zanyi nadama na bari"yace yana shurin hawa sama,da gangan yasa kafa ya buge mata guiwan yace" toh miss ego,oh sorry ashe fa kin samu karin matsayi.frm miss ego to gurguwa. a tashi lafiya"nan ya wuce sama abin shi ya barta tana ta kumfan baki.



Wayyo yau farhat yar gatan abban ta ake cewa gurguwa.pls kuyi hkr yau ba yawa.
[12/6, 7:47 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by Ummee yusuf(maman yusuf)


Page 35~36


Wanka yayi hankalinsa kwance ya shirya cikin kananan kaya,yayi kyau sai kamshi yake abin sa. koda ya fito zuwa ya nufa dan ya gano mutuniyar tasa.

Murmushi da baiyi niyya bane ta kwace mai ganin farhat mai aji jefe a kasan tiles tana bacci wahala

Please Login or Register in order to submit comment