Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki ba,ita dai tasan tun lokacin da abba yace zai raba auren su da farhan ta nemi natsuwar ta rasa.

Koda ta karaso daki rage kayan jikin ta tayi sannan ta kwanta lamo a kan gadon ta,bata san mesa ba bata son abba ya raba auren,toh ai basu gama game din su ba,in abba ya raba kuma ai ya katse musu game.

Juyi take a kan gadon ta kasa bacci sosai gani take gadon ya mata fadi ga wani sanyi sanyi da take ji.remote ta dauka ta rage a.c,still tana ji.jan bargo tayi ta lulluba dashi but har yanzu dai bata daina ji ba.nan ta fahimci dumin jikin farhan take missing.tsaki taja tana cewa"wai wannan dan rainin hankalin ina ya shigane tace cikin ranta tare da jawo waya

Tsaki take ta jerawa jin har yanzu layin sa a kashe.

Rufe kanta tayi da bargo tare da lumshe ido ko baccin zai zo.ganin fuskan farhan tayi lokacin da ya fara kissin din ta,murmushi tayi tare da gyara kwanciya.

"Miss ego who gave d permission din tunani na?"taji muryan farhan a kusa da ita.

Wara ido sosai tayi tana kallon yanda ya wani hada rai.

Murguda mishi baki tay tace"waye ma rashin aiki ya same shi da zai yi tunanin poor bagger".

Marairaice fuska yayi yana kallon ta yace"nine poor bagger ko?"

Saurin rufe bakin tayi da hannu tana girgiza kai alaman ba take ba.har yanzu bai yanzu bai saki fuskan sa ba ya langwabar kai yayi kalan tausayi yana kallon ta.

"Sorry bazan sake fadan sunan nan ba har abada"tace masa itama in a pity face.

Shagwabe fuska yayi yace"promise"cikin jin dadin ya sake fuska tace"yes dear promise"

"Then come here wife"yace yana dariya tare da wara hannayen sa.mirginowa tayi zuwa jikin sa tana dariya.timmm taji ta a kasa,ba karamin daurewa tayi ba da bata saki ihu ba dan ta bugu sosai.

Kallon kan ta shiga yi yanda tayi rashe rashe a kasa ta kasa tashi."oh god wats wrong wit me"

Can kuma ta kwashe da dariya kaman wata mahaukaciya tana cewa"vari ya dawo wallahi a kan sa zan rama faduwan da nayi"tashi tayi ta koma kan gado tana ta smiling.duk yanda taso yakice shi a ranta ta kasa sai tuna good moments din da sukayi take.da kyar bacci yayi nasaran daukan ta.koda asuba da ta farka shi ya fara fado mata a rai tana cewa ko ya tashi yanzu?.

Yau satin farhat 2 da wasu kwanaki cikin ukubar ammi duk wani aikin gida ita kadai ke yin su dan ammi ta sallami su ladi kan cewa zata neme su nan da sati uku kuma ba wai za a hana su albashin su bane akwai dalili.dan haka suma basu damu ba suka wuce garuruwan su.

Duk aikin da take yanzu ko kadan baya damunta abinda yafi tsaya mata a rai shine rashin dawowan farhan gare ta.kullm addu'an allah yasa yana lafiya take,gashi su abba ko tayi musu zancen shi basa daukawa da muhimmanci.tasha gwada layin shi sai dai ko yaushe amsar daya ce is currently switch off.akwai ranan da hakurin ta ya kare tace zata je gidan ta dubo shi in ma baya nan zata zauna acan har ya dawo daga inda ya tafi.amma budan bakin abba yace mata"wannan ai wahalar da kai ne,nan da can din ai duk gidan mu ne,so kiyi zaman ki anan ba sai kinje can ba".ire iren amsan da take samu daga iyayen nata kenan shiyasa ta daina zancen farhan a gidan ta barwa zuciyar ta.

Ta rame tayi baki duk ta fita daga kamannin ta saboda tunanin farhan da tasa a ranta ko abincin kirki bata iya ci.tayi sanyi sosai kaman ba farhat ba .

In tana cikin aiki ta tuna da irin wulakanci da take ma su ladi har kuka take ba tare da kowa ya ganta ba.dan yanzu sosai take nadaman abinda tayi musu a baya saboda yanzu tasan yanda suke ji in anyi musu wulakanci bayan sun sha wahalan aiki.dan yanzu sai tasha wahala tayi aiki ammi ta hau ta sa fadan ba tayi dai dai ba wani lokacin har bige ta take tana mata gorin ba abinda ta iya a rayuwa sai ci ta kawanta.

Tabbas tasha yiwa mutane irin wannan more especially ladi,duk wulakanci da zatayi musu dole suyi dan nan ne hanyar cin abincin su gashi har gidajen su suke barowa suzo suna neman halal din su,maimakom a tausaya musu sai dai ana musu kallon kaskalntu.

Itako tunda ta tashi cikin jin dadi take batasan wani wahala a rayuwa ba maimakon tayi wa allah godiya gurin kyautatawa na kasa da ita kaman yanda abban ta yake amma saima amfani tayi da hakan wajan muzgunawa na kasa dasu.ciki kuwa harda mijin ta wanda yake son ta tsakani da allah kuma cikin faranta mata yake amma ita kullum burin ta taga ta kuntata mishi.kar dai ace ya gaji da halin tane ya gudu ya barta.ko tana bacci in ta kawo hakan a ranta ta rinka kuka kenan.

Yau ammi ta kira yan aikin gidan kan dawo da bakin aikin su,saboda itama yanzu tana ganin canji sosai a tattare da yar ta amma tana son tabbatarwa kuma hakan ba zai yiwu ba har sai yan aikin sun dawo.

Zaune take a palour tana aikin da ta saba wato tunanin mijin ta farhan,,bata san da zuwan su ladi ba.

Ladi tazo wucewa da mug din kunun gyada a hannun ta zata wuce kitchen amsa kiran ammi,bata lura da farhat dake zaune ba hankalin ta yana kan t.v sai ji tayi tayi tuntube da mutum wanda ya haddasa faduwan mug din hannun ta zuwa kan kafan farhat,tarwatsewa mug din yayi sannan kuma kunun ya fantsama jikin ta.

A rude ladi take kallon ta jikin ta har bari yake ganin dan yatsan ta ya fara fitar da jini tasan in tashiga hannun farhat ta me kwatan ta sai allah.

Farhat kuwa a firgice ta dago suka hada ido da ladi ai bata tsaya wata wata ba tazo ta rungume ta tana kuka cewa ta yafe mata.kasa motsi ladi tayi cos bata gasganta idanu da kunwan ta ba.cigaba da kuka tayi tana cewa"kullum addu'an allah ya hada ni da ku in nemi gafaran ku saboda nasan na zalunce ku a zaman da mukayi dan allah ki yafe min ba dan hali na wallahi son zuciya da sharrin shaidan suka kaini ga aikata haka".

"Dan allah hajjiya kiyi hakuri aini ce nai miki laifi"

"A a kar kice haka ladi shekaru nawa nayi ina cutan ki ni dai dan allah ki yafe min"

A razane ladi ta fara kwalawa ammi kira ganin yanda kafanta yake fitar da jini.

Share hawayen ta ammi tayi da murmushi akan fuskan ta ta karaso wajan su dan tariga taji abinda ya kwakana tsakanin su saboda tun dazu suka fito daga kitchen ita da ya falta da suka ji karan fashewan glass din.

Kama ta sukayi zauwa dakin ta,ammi ta dauko first aid box tayi dressing din inda cup din ya yanke ta.mikewa tayi da niyan fita farhat ta kama kafan ta tare da fashewa da wani sabon kukan tana cewa"na tuba ammi dan allah ki yafe min,na fahimci abinda kike son ganar dani tun ina karama zan iya juran ko wani irin hukunci a gare ki amma dan allah ki daina fushi dani".

Dagota ammi tayi ta rungume tanana bubbuga bayan ta alaman rarrashi har ta samu ta tsagaita da kukan sannan ta kama ta suka zauna a bakin gado.tana murmushi tace"inyee my baby is a grown up now am very proud ban taba fushi da ke ba illa burina allah ya daura min tilon yata kan hanya mai kyau kuma alhmdllh allah ya amshi addu'ata.yanzu no more crying kwanta ki huta ko?"tace tana shafa kanta .

Ammi har ta kai bakin kofa taji tace"ammi dan allah in abba ya dawo ki taya ni rokon sa a nemo farhan shima in nemi gafaran shi"

Murmushi ammi tayi tace "a a ba ruwana keda abban ki kunfi kusa in ya dawo sai ki fito ki fada masa da kanki".dan yake kawai tayi ammi ta fita,duk yanda zata fada musu yanda take ji game da farhan abin ya girmi tunanin ta cos yanxu duk lokacin da zatayi tunani farhan sai taji zuciyar ta na mata wani irin nayyi.

Tana kwance hawaye na bi ta gefen idon ta hannun ta rike da wayan ta da kullum sai ta gwada no farhan sau ba adadi.

Karan wayan tane yasa ta tashi a firgice tare da addu'an allah yasa farhan ne,sunan ruky ta gani yana yana yawo akan screen din.ajiyan zuciya tayi ta goge hawayen ta sannan ta daga.

"Ruky ya kike kwana 2?"tace da dashasshiyar muryan ta.
"Lafiya gani a kofan gidan ki mai gadi yace min wai kunyi tafiya"cewar ruky.
"No ina gida tun kiran nan da abba ya min ban koma ba".tace hawaye na taruwa a idon

"Kaman ya baki koma ba,kodai kun yi fada ne da poor baggern naki kike boye mana".

Cikin karaji ta ka katse ta"hey will u shut dat dirty mouth of urs,mijin nawa kike kira da haka"?

Dariya ruky ta sheke da shi "farhan shi kike kira da mijin ki"?

A zuciye ta katse wayar tana huci ji take ina ma ace zata ga rukyn a gaban ta ta kakkaura mata mari jin suan da ta kira rayuwan ta dashi,sai yanzu ma take kara jin wani zafi a ranta da ta tuna ita ce silan shigan ta wannan hali cos duk abinda take mafi yawanci ita ke zuga ta.allah sarki ramlat kawa ta gari dan ko yaushe tana kokarin dora ta kan hanya mai kyau ita kuma a lokacin da yake idon ta ya rufe suke mata kallon bata waye ba shiyasa tafi shiri da ruky.

Wayar ta ta dauko tayi dialing no ramlat,kuka ta fashe mata dashi da ta daga kiran.

Cikin tashin hankali take tambayar ta ko lfy amma sai ma kara volume din kukan ta take.da kyar ta rarrashe ta sannan ta tsagaita nan ta kwashe lbrn abinda ya faru ta fada mata sannan tace"nasan ya gaji da abinda nake mada ne ya gudu ya barni a yanda nake ji i cant move on without him in my life".tace tana kara rushewa da sabon kukan.

"Look star yanzu ba lokacin kuka bane tun farko abinda nake jiye miki kenan kika biye ma ruky amma duk da haka lokaci bai kure ba nasan farha really loves u duk yanda zakiyi kisan yanda kika futa kije ki bashi hakuri nasan zai saurare ki".

Nan tayi ta rarrashin ta tare da karfafa mata guiwa kan ta tukare shi.daga karshe dai sallama sukayi akan yau zata koma gidan ta tare da bawa farhan hakuri suci gaba da zaman su.

8:30 ta.leka palour taga su ammi suna zaune da abba suna,sadaf sadaf ta wuce ta kofan baya ta tare da sun gan ta ba.direct get ta nufa ba madu mai gadi yana ganin ta ya dauke kai yasan ba karamin aikin ta bane ta mishi rashin kunya.

Tana fita daga gidan ta fara zuba sauri duk da zogin da kafan ta keyi bai dame taba burim ta kawai ta ganta a bakin babban kwalta.ga anguwan ko kare babu kowa na cikin gida.

Wata karamar mota ce a bayan ta da samari 2 aciki suna binta kuma suna musun akan itace ko ba itace ba.mai jan motan yace "kai alex baka gani da kyau itace mana."wanda aka kira da alex din yace "no way tunda oga ya bamu umarni muke nan ya bamu taba ganin fitowan ta sai yau,na gaya muku anyi mata aure"deen din yace "tsaya ka gani"kara speed yayi suka taro ta sannan yace"FARHAT"juyowa tayi a razane tana kallon su ganin bata ganin mai kama dasu ba yasa ta kara sauri ganin gaka alex ya fito da sauri ya sha gaban ta zata yi musu ihu ya hura mata wani hoda a fuska tayi baya luuuj zata fadi deen yayi sauri ya taro ta.suka ciccibeta suka sata a motan sannan suka fita a guje.😭😭😭😭😭

Wayyo farhat not again
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by ummee yusuf
(Maman yusuf)


Page 49~50


Yaaz bai bar maiduguri ba sai da ya tara yaran sa su takwas,babban cikin su ozo shi ya dankawa assigment din su nemo masa information akan farhat kuma duk yanda zasuyi su kwamasota kuma yasa musu kyauta mai tsoka ga wanda yayi nasara kuma zai bashi matsayin p.a din shi.

Jin Hakan yasa su duka daukan damara sannan suka rabu zuwa gruop 4,sai dai kash basu dade wajan bincuken ba suka gano har tayi aure nan suka kira yaaz suka fada mishi amma yace ina ruwan shi da auren ta,su tabbatar dai sun kamo ta.nan kuma ya kara yawan kudin da yace zai bawa wanda yayi nasaran kamotan.wannan kenan.


Su alex basu tsaya a ko ina ba sai wani secret farm house na yaaz dake can moramti bayan gari,suna yin parking a compound din gidan suka cicbeta suka shiga da ita cikin wani daki cikn dakuna hudu da suke flat din.alex ne yacewa deen "ka daure mata hannayen ta bari in kira oga yaaz in fada masa mune mukayi nasaran kwamasota".

Can balcony alex ya fito kamin ya kira oga yaaz.

Yan mata uku ne akan sa duk sanye suke cikin bikini, yana kwance shima saman resting chair a bakin swimming pool daga shi sai baxer suna massaging din shi idan a lumshe a lokacin da call din alex ya shigo,daya daga cikin yan matan ne ta dauka sannan ta kara masa a kunne.

Can bangaren kuma alex yana ji an daga wayan ya fara masa kirari sannan yace ai shine yayi nasaran kamo masa farhat.

A take ya tashi zaune har yana hankade yarinya daya,cikin muryan yan maye yace" re u really sure of wat u re saying"

"I'm very sure oga wallahi ita ce,yanzu haka tana farm house dinka na moramti".

Cikin jin dadi yace "good job alex u wll be rewarded for this".nan yayi hanging din call din sannan ya kira airpot kan neman ticket din maid gobe da safe,but aka ce ba na safe sai rana.haka ya hakura ba dan yaso ba.

Kiran alex yayi yace ya kula da ita da kyau yana nan zuwa gobe,suna gama wayan sannan ya koma ciki wajan deen.nan deen yake tambayan sa ya sukayi?

"Na gaya masa mu 2 mu kayi nasaran kamota kuma yace mu kula da ita da kyau yana nan zuwa gobe da rana".

Nan suka kwana da ita a gida sai dai har yanzu bata masan a wace duniyan take ba.

Da washe gari 1:30 a filin maiduguri internation airpot yayiwa yaaz,gaba daya yaran sa sun zo taran sa ciki kuwa harda su alex da deen.

Wata haddadiyar jeep suka bude masa ya shiga nan ozo ya zo da gudu zai shiga driver seat sabida ko yaushe shine mai jan sa amma sai yaaz ya dakatar da shi yace alex ya shiga su tafi cox tun yanzu ya kamata ya fara cika alkawari da ya dauka.abin ya daki ozo a zuciya amma ya danne ya shiga wata motan suka rufa musu baya.

Karfe 10:30 Farhat ta farka da matukar ciwon kai,dakin take bi da kallo ganin dai ba dakin ta bane,sai daga baya ta tuna abinda ya same ta jiya da daddare.

Yunkura tayi zata tashi cikin tashin hankali amma taji hannayen ta a daure,bata fasa ba haka ta mike cikin dabara ta nufi wajan kofa ta fara ihu tana neman agaji,muryan ta har ya fara dishewa amma bata ji alamun mutum ba.nan ta zube a jikin kofan a matukar galabaice sabida kishirwa take ji har na fitan hankali.tana na zaune tana ta hawaye tare da nadaman fitowan da tayi,da tayi hakuri ta zauna tayiwa iyayen ta biyyaya da hakan bai same ta ba.

Takamaimi bata san ina ne nan ba kuma bata san suwa sukayi mata hakan ba.yan boko haram ko yankan kai ko kuma kidnappers,no wayan nan sun santa tunda saida suka kira sunan ta suka tabbatar ita ce sannsn suka kamata.addu'a ta fara na neman taimakon rabbis samawati wal ardi,ta san yanzu haka iyayen ta suna cikin tashin hankali.

Murmushi ta fara da ta tuna da farhan ko yana ina yanzu ko yaji labarin batan ta?haka ta kwanta lamo tana ta addu'an da yazo bakin ta.

A compound din gidan sukayi parking sannan suka fiffito suna jiran yaaz ya fito,akex ne ya bude masa kofan motan sannan ya fito yana shan kamshi alex na gaba zai kai shi dakin da suka kwantar da farhat,ganin haka yasa deen shima ya fara kokarin bin su amma wani mugun kallo da yaaz ya watsa masa ya yaja ya tsaya nd a zuciyar sa kuma yana jin wani iri ,ya za ayi suyi aiki tare amma a rinka ware shi?.

A nesa da dakin alex ta tsaya ya nuna mai sannan ya juya ya koma cikin yan uwan sa.

Bude kofan yayi ya shigo dakin,da kallo ya fara bin dakin dan shi bai ganta akan gadon ba kaman yanda alex ya fada masa.can kuriyar dakin ya ganta a yashe tana baccin wahala ta cikuikuye cikin dogon hijab din jikin ta.

A hankali ya fara takowa yana kallon fuskan ta da murmushi akan fuskan shi,it was d same beauty face da ya tafi da imanin shi.a take ya hada rai da ya tuna marin da ta mai yana shafa gefen fuskan shi da ta mara a lokacin,yana karasowa gaban ta ya durkusa tare da falla mata wani wawan mari da yayi sanadin farkawan ta a gigice har tana buge kan ta.a bango.

Dariya irin ta bosawa yaaz ya kwashe da shi tare da mikewa ya zura hannayen sa duka 2 a aljihun wandon shi yana kallon ta.

Wani wahalallen yawu farhat ta hadiye cox tabbas bata manta face din shi ba,ashe shi yasa aka dauko ta yau ta shiga tara ba uku ba a lokacin tana ganin zata taka kowa ta kwana lafiya ashe babban kuskure tayi duk da yanzu tayi nadaman irin rayuwan da tayi a baya,sakayya ce na mutanen da ta ciwa mutunci a baya shi yake bibiyan ta.

Baki na rawa tace"dan girman allah bawan allah kayi hakuri kar ka cutar dani ni matar aure ce...."

Wata dariya da tafi na dazu ya kece dashi sannan kuma ya hada rai yana kallon ta da yace"yau kuma nine bawan allah?"

Shiru tayi bata tanka ba illa jikin ta da yake rawa.

Tsawa ya daka mata yace"nace yau nine bawan allah?ko kin manta sunan da kika kirani dashi a lokacin?POOR BAGGER huh".yace yana huci idon nan yayi jawur saboda bacin rai.

"Na tabbata da kinsan koni waye ko da kudi aka hada ki akace ki min abinda kika min ba zakiyi ba,nasan rashin sani yasa har kike kallon mutane kina kiran su da poor baggers while uban ki ne poor baggern".

Dago jajayen idon ta da yake ambaliyan hawaye tayi ta kalle shi.

"Yes bukar alibe is d biggest bagger i have i ever seen"yace yana zaro mata ido.

Cikin bacin rai ta mike da kyar tana masa kallon wukakancu tace"mind ur tongue kar kaga dan ka sa an kawo ni nan yasa kana ganin kan ka as hero,un ka cika namiji mesa baka dauki mataki ba lokacin da nayi maka,mesa baka dauko ni da kanka in ka isa?nd last warning duk abinda zakayi kayi but kar ka sake saka sunan iyayena a ciki if not......"

"If not wat?"yace yana shako ta tare da buga ta a jikin bango,sai da ta saki ihun azaba.

"Har ni zaki kalla kin gaya irin wannan maganan?yes bukar alibe is a bagger na fada bari inyi maganin wannan shegen bakin naki" yace yana zaro belt din shi.gani haka yasa ta fara bashi hakuri daga kwance da take cox ko motsawa ta kasayi sakamakon buguwa da tayi a bango.

Jibgan ta ta farayi da belt din kaman aiko sa akayi tun tana bashi hakuri tana ihu har bakin ya mutu,sai da ya gaji dan kansa sannan yayi jifa da belt din yana haki kaman wanda yayi gudu sannan yace"kin ce am not a hero tunda sawa nayi aka dauko ki toh let me show u gobe zan wuce dake los angel cos baki da miji sai ni".yace sannan ya sa kai ya fice a dakin.

A waje ya samu yaran sa suna jiran fitowan sa nan ya cewa alex ya shirya gobe zasu wuce los angel kuma ya fita ya samo mata abinda zata ci nd daga yanzu ya sallami dukan su baya bukatan kowanen su since they re good for nothing.deen ne ya bishi yana kokarin fada mishi tare fa sukayi aikin amma ko sauraren shi baiyi ba ya shiga mota ya fita a guje yayi hanyan gidan aunty shi.

Alex ne yazo yake cemasa kar ya damu in oga ya bashi kyautan zai bashi wani abu.deen takaici bai barshi ya kula shi,wato yayi masa dabara kenan ya fadawa oga yaaz shi kadai yayi aikin.

Yanan nan tsaye ya rasa me yake masa dadi duk an watse an barshi shi kadai,ji yayi an dafa kafadan shi ta baya juyowa yayi yaga ozo yana masa murmumushi hannun sa yaja suka shiga moton ozon suka bar wajan.

Wajan su abba kuwa duk inda hankalin su yake in yayi million toh a tashe yake barin ma fahan da har wata rama yayi na musamman,sune police station sune giwa barack sune wajan yan gora.ganin har yamma abin yaci tura yasa aka watsa a media duk wanda ya samo ta ko ya kawo labarin inda take kudi akasa zunzurutu har million 10.sun kasa tsaye sun kasa zaune.ammi idon ta duk ya kumbura saboda kuka.ga police duk sunyi tracing layukan gidan ko za a kira dan su duk a zaton su kidnappers ne cox ramlat tazohar gidan tana kuka sannan ta fada musu yanda sukayi kamin ta fita.

Farhan ji yayi kaman yayi hauka da yaji dalilin fitan farhat din shi har wannan kaddaran ta same ta.

A can moramti kuma farhat tan nan yashe kaman yanda yaaz ya fita ya bar ta har alex ya sayo mata abinci da ruwan sha,kunce ta tayi bayan ya ajiye mata abuncin sannan ya fita ya rufe ta ta baya tare da mamakin kome ya samu oga yaaz na dukan mace haka.


Da kyar ta yunkura ta tashi zaune saboda yanda jikin ta yayi tsami gashi duk ba inda bai kumbura ba a jikin ta.ruwan ta kafa kai sai da ta shanye tass sannan ta koma ta kwanta ko kallon abincin ma batayi ba.

8:30pm alex yan zaune a parlor ya kunna kayan kallon sai shaye shayen sa yake hankaki kwance.

Mutane 2 nagani sun hauro ta get din gidan fuskan su da mask,durowa a hankali ta yanda na ciki ba zai ji motsin su ba.cikin sanda suka iso bakin parlourn suna jin karan t.v.ta key hole dayan leka ya ga alex yayi dai dai akan three seater yana ta bacci bayan ya kora syrup kala kala.

Cikin jin dadi suka bude kofan suka shiga ganin allah ya kawo musu saukin aiki,basuyi wata wata ba suka dauki bounch din keys da suka gani a kan center table suka nufi daku nan suna bincikawa wanne a kulle,a na tsakiyan suka tsaya dan shine a kulle.nan suka fara gwada keys din har allah ya basu sa'a suka bude.

Can suka hango farhat ta gudundune cikin bargo sai rawan dari take saboda zazzafan zazzabi da ya rufe ta.zuwa sukayi suka daga ta suka yi waje da ita ko gardama bata musu ba saboda duk ta fita haiyacin ta.gate din suka bude sannan suka fita suka sata a mota sannan dayan ya dawo ya rufe gate din ta ciki san an ya haura ta saman gate ya dira ya shiga motan suka fita a guje sai a.lokacin suka cire mask din fuskan su suna dariyan samun nasara.

Basu tsaya a ko ina ba sai new g.r.a kofan gidan alh bukar,sai anan naga faces din su,ozo ne da deen.

Kwankwasa get din sukayi ba madu mai gadi ya leko dan ganin ko waye ne,yaga samari 2kuma bakin fuska nan suka gaishe shi tare da tambayan ko alh na ciki?.


Amsa musu yayi da yana ciki amma suyi hakuri ba zai iya sauraren su dan yana cikin matsala shi a zaton sa masu neman taimako ne.
Nan suka ce ya taimaka ya fada mishi sun zo mishi da labarin yar sa farhat.aiko cikin sauri ba madu yayi cikin gida.a kofan
Parlourn ya tsaya yayi sallama izinin shigowa aka bashi bayan sun amsa sallaman.

Shigowa yayi ya durkusa yana gaishe su duk sunyi jugum jjugum farhan kuma

Please Login or Register in order to submit comment