Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali mana ko kin manta irin takalmin da yake kafan kine?no! Ammi ai kema kisan na saba da hill shoe tun ina yarinya"tace tana wani shagwabe fuska"uhum toh naji wuce muje time is running.gaba tayi itama cikin shiganta na alfarma yayin da farhat ta mar mata baya.driver na ganin haj kaltuma ya taso cikin ladabi ya iso gabanta ,tace "bala yi sauri airpot zamu jentaran ALh kar mubb makara ko?toh hjy",yace ya juya cikin sauri ya dauko wata fitananniyar mota suka shiga suka kama hanyan airpot

Lokacin da suka iso airpot sun tarar har jirgi ya sauka
dan tsakanin new g r a da airpot akwai nisa.wuri suka samu suka zauna suna jiran fitowan su ,basu fi minti 10 da zama ba passingers suka fara fitowa.farhat sai baza ido take taga abban ta ,aiko can ta hango shi da gudunta ta isa wajan shi ta rungume shi,ahima cikim tsananin farin ciki yasa hannu ya rike ta yana dariya yace "mamana yaushe zaki girma ne uhum?"itama cikin daryan tace "ni kullum a wajan abba na baby ce"dariya abba ya kara yi kamin yace wani abu har ammi ta karaso wajansu,itama cikin farin ciki take ma mijin nata sannu da zuwa.wani kyakkyawan saurayi ta gani wanda a kalla bazaifi 25years ba fari kal dashi ga gashin kansa baki tsidik ya kwanta lub lub dashi.karasowa yayi tare sa cewa "ammi mun same Ku lafiya"fuskan ta dauke da mamki take kallon sa ,da yatsa ta nuna shi tace "FARHAN"?da alaman tambaya.murmushi yayi ya sunkuyar da kansa kasa,abba ne yayi dariya yace "ashe zaki gane shi"itama cikin dariyan tace "haba alh taya zan manta dashi?kawai ku zo mu karasa mota"a tare suka kama hanya yayin da farhat har ta tsufa a wajan mota ita da driver yana saka kaya a boot.shiga motan sukayi abba da ammi.ita kuma farhat tana kokarin bude seat din gaba taji abban ta na cewa"zo nan mamana ki barwa yayan ki can din.sai a sannan ta lura da wannan kyakkyawan guy din ,suna hada ido a sai da zuciyar su ta buga a tare.
[11/16, 8:37 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee Yusuf(Maman Yusuf)

Wannan shafin naki ne Hafsat SHEHU,INA gdy da kaunar ki gare in da yanda kika karfafam min guiwa.ina yin ki sosai Allah ya bar kauna.

Page 10

Kasa dauke idon ta a kansa tayi,shine ya janye nashi idon tare da karasowa inda take.tsaki taja a ranta tana mai jin haushin kanta ko menene nata na zuba mishi ido har yana wani dauke kai.wani tsiriri tsakin ta kuma ja ta bashi hanya,tana me cigaba da mita a ranta halin iyayen ta na jan talakawa a jiki.duk inda zai je ba zaka raba shi dasu ba,ba wayan da take jin haushi kaman wayan da suke zuwa abroad karatu da alama shima daga can yake.sai wani ji da kai yake kaman dau kudin uban sa yayi karatun.sauran talakawan in sun dawo har wani girma suke bata na musamman amma shi wannan har wani dauke kai yake.hararan keyar sa tayi ta madubi tare da yi kwafa wanda har ya fito fili "lafiya dai mama na"?abban ta ya bukata,ba komai abba"tace tana juya kai.

Ko parking bala bai gama ba,ta fiti da saurinta ta sgige ciki dan bata son kara kallon wannan mai kama da sadaka yallan.ammi ce tabi ta da ido tana cewa"bansan ranan da yarinyan nan zatayi hankali ba"abba ya hada rai yace "ah ah kar ki takura min uwa baki san uzurin ta ba"ammi gani yanda ya hada rai yasa tayi shiru,tasan tunda ya dawo kuma shagwaba sai abinda ya karu.farhan yana jin su baice komai ba sai murmushi da yake "muje ciki mana son"abba yace tare da riko hannnun sa,suka yi cikin palour suka zazzauna cikin manyan kujeru na alfarma.nan aka kara gaisawa"ku fara watsa ruwa ga abinci na jiran ku"ammi tace.mikewa suka yi abba yayi sama,ita kuma ammi ta kai farhan wani hadden daki anan cikin palourn.tana masa murmushi tace "ga dakin ka nan son,go nd freshen up muna jiran ka dinning ko?"godiya ya mata sannan ya shiga cikin dakin.kallon dakin ya tsaya yi komai neat kuma ya hadu komai na dakin brown nd milk colour.sosai dakin ya birge shi saiu kamshin turaren wuta ke tashi.murmushi yayi yana jinjina karamci irin na abba da ammi ba ruwan su kowa nasu ne tsabanin yar su da ya gani alamun kanta na hayaki.tabe bakin sa yayi tarebda cewa"ina ruwa na ma da ita.kayan jikin sa ya rage sannan ya shiga bathroom,nan ma komai neat.wanka yayicikin minti 10 ya fito daure da towel daya kuma yana goge gashin kansa mai matukar laushi da tsanti.trollyn kayan sa ya bude ya fito da kayan da zai sa,bayi amfani da kayan da ya gani a gaban mirrow ba.nashi yayi amfani dasu,shiryawa yayi cijin dark blue t-shirt da black jeans ya feshe jikin sa da perfumes sannan ya fito parlour.

Dukkan su uku ya tarar akan dining suna jiran sa,cikin sauri ya karaso yana basu hakuri.murmushu kwance akan fukan su ammi tace "haba son ba komai ai"farhat kuwa ta cika tayi fam saura kiris ta fashe,an hana ta cin abinci akan wani banza can ,ya shanya mutane shine har ake wani ce mai ba komai?dago kai tayi aiko karaf suka hada ido wata muguwar harara ta balla mai.shi kuwa dariya ma abin ya bashi dan haka sai da ya murmusa."me za a zuba maka son"?ammi ta bukata bayan ta zubawa kowa saura shine kadai bata zubama ba.plate din abba ya kalla ya gani shake da tuwon ndalayi da miyar danyen kubewa yasha man shanu ga naman danderu shima tururi.na ammi kuma kisire ne shima da miyan danyan kubewa"ammi a zubs min tuwon ndalyin dan nafi son abincin gargajiya"yace yana murmyshi "toh"tace ta fara zuba masa,kowa yana cin abincin sa hankali kwance banda fsrhat da take ta juya spoon tana zancen zuci,"dama dan qauye dai dan qauye ne in ba haka ba duk zaman da yayi a abroad ya dawo ya bige da cin tuwo?ita wlh haushi ma yake bata wai ammi ko wani jill nd jerk take kira da son.tsaki taja ammi tace"lfy kike ma mutane tsaki?baki na ne ba taste" tace dan tasan in ammin ta tasan abinda take ma tsaki toh in ranta in yayi dubu sai ta bata mata"ke dai kice abincin ne ba kya son ci dama"ammi tace tana hararan ta.abba ne ta katse ammi da cewa "kyale min uwa ta,me kike son ci mama na?"cike da shagwaba tace "abba ni ice cream zan sha amma kullum ammi sai ta hana ni kuma......yau abban ki ya dawo tashi kije ki sha na kawo miki favorite choculates dinki.

Ko Yaya zaman farhat da farhan zai kasance a gida daya
[11/17, 8:06 PM] Ummee Yusuf: 🔥💥🔥💥🌹🌹

FARHAT

🔥🔥💥💥🌹🌹


Written by ummee yusuf(maman yusuf)

Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki,Godiya da jinjina gare ki UMMi GARKUWA marubuciyar ummi allah ya kara basira.


Page 11


Mikewa tayi cike da happy har da Dan tsallen murna"u re d best dad in d word"tace tana karasawa wajan fridge Dan daukan ice cream,palour ta wuce cikin jin dadi ta zauna sha.

Parlour n suka dawo suma bayan sun kammala suka samu waje suka zazzauna,farhat kuwa had yanzu ice cream dinta take sha cikin kwanciyan hankali tana kallon wani film a MBC 2.gyaran murya Abba yayi alamun zaiyi mgn mai mahimmanci,duk suka maida hankali gare shi.kallon farhat yayi yace"mama na Ga Dan uwan ki nan Baku gaisa ba kuma zai zauna damu na kwana 2"taji haushi zama da aka ce zaiyi a gidan su,amma ta kudirta a ran ta da kafar Sa zai bar musu gida cos she promised herself to make his life miserable.

Zamewa tayi kadan daga kan kujera cike da ladabi tace"Yaya sannu da zuwa ya hanya"?kusan daskarewa farhan yayi a wajan cos karara yaga tsantsan kiyayar Sa a idon ta but Ga yanda take yi masa mgn harda ladabi?da kyar ya saita natsuwar shi ya amsa mata da "lafiya lau kanwata ya karatu"?dariya tayi cikin zuciyan ta na ganin mamaki karara a fuskan shi,a ran ta tace baka Ga komai ba in dai nice."lafiyau alhmdllh" ta amsa tana gyra zamanta a kan kujera.

Abba ne yacigaba yace "yanzu ka huta na kwana 2 sai muje kaga company ko"?"toh abba duk yanda kace haka za ayi,nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"Ameen"abba da Ammi suka amsa cikin jin dadi."zan shiga in Dan huta abba"yace yana mikewa "toh son a fito lafiya"Ammi ta amsa mishi.

Takaici kaman ya kashe farhat,tana bakin cikin abban ta ya tura shi abroad karatu kuma kasan da tafi so,yanzu kuma harda wani wai za a bashi aiki a company.tsaki taja"I hate poors,they all baggers"tace tana tashi a palour dama ita kadai ta rage.

Koda ya Shiga dakin kwanciya yayi akan bed Dan ya huta amma sai tune tune da kuma yanda zaman Sa zai kasance a gidan,har aka kira la asar.alwala yayi ya fito palour amma ba kowa,direct masallaci da ya gani a kofar gidan
ya fito sukayi sallah.tare suka shigo da abba cikin gida.

Farhat ce kadai a parlourn tana zaune akan 2 seaters ta daura kafafun ta akan handle din,tana chat dash ramlat tana lbrn abban ta ya kawo Sabon poor bagger mai jiji da kai.d worst part kuma wai a gidan zai zauna for 2days."just teach him a lesson"suka ce mata."sai kace ba starn Mu ba har akwai Wanda zai Iya Sa mini headache?"kuma kunsan hali na I don't tolarate nonsense, I know how to deal wit him"Sallama da sukayi ne ya katse mata charting da suke,amsawa tayi tare da dago kanta tana yiwa abban ta murmushi.zama suka dukan su,ganin harda farhan ya sata mikewa tare da yin hanyan sama"mama na ina zuwa ne, ba zaki zauna muyi hira ba?"abba yace mata .juyowa tayi ba tare da ta dawo ba tace"abba sallah zanje inyi"abba yace assha ba kiyi sallah ba,kika zauna latse latse a waya?yi maza ki je kiyi kar lokaci ya wuce".toh Abba" ta amsa ta karasa haurawa.a zahirin gaskiya tayi sallahn kawai zama da poor bagger ne bata son yi.


Har dare basu kara haduwa Dan ko cin abinci kin saukowa tayi,kwanciya tayi tana charting da frnds din ta har tayi bacci.

Koda washe gari,kwanciyar ta ta karayi bayan tayi sallahn asuba.

Sai kusan 7:30am ta tashi,tasa kayan sports din ta.Karamain Riga pink colour da wando 3quater fari kal da facing cap shima fari.tayi parkng din gashin kan ta a tsakiya in a pony style jelan gashin ya fito ta bulin hulan yana reto a bayan ta.wannan al adar tace every weekend sai tayi wasan basketball cos tana bala'in son game din ,dalilin haka abban ta yasa aka fitar mata da katon fili a gefen garden din gidan.

Fitowa tayi parlourn kasa,bakowa kaman yanda ta zata sai ladi kadai da ta tarar hannun ta rike da wani karamin tray ta daura lemon
juice da table water masu sanyi da cup din glass.sai wani karamin farin towel a gefe.

Wucewa tayi abin ta ba tare da tabi ta kan ladi da take Haida ta ba.

Filling basket ball din isa ,ba bata lokaci ta fara wasan ladi kuma tana gate tana kallo.

Farhan duk kadaici ya ishe shi,abba da Ammi suna kokarin su na Jan shi a jiki amma ya kasa sakin jiki dasu.

Fitowan shi daga wanka kenan,shafe jikin sa yayi da lotion masu kamshi sannan ya shirya cikin polo shirt brown da ratsin fari.jeans yasaka shima fari kal, gaban Mirror ya tsaya yana combing gashin kan sa bayan ya shafe su da mayukan gashi. Turare kusan kala 4 naga fesa bayan body spray da yayi amfani.wow gaskiya farhan ya yadu.

Wajan windo yazo ya yaye curtains din ya juya,waiwayowa yayi da sauri ganin yanda farhat take ta wasan basketball duk ta hada gumi.

Baisan minti nawa ya dauka nan tsaye ya kallon taba Dan ya shagala sosai.

Knocking kofan dakin Sa da akayi ne ya dawo dashi hayyacin Sa,murmushi yayi yana shafa gashin kan Sa yace"crazy gal"kofan yaje ya bude,mai aiki ya gani tsaye.

Tana ganin ya bude tayi saurn dukawa ta gaishe shi tare da sanar dashi Ammi na kiran shi."toh"yace kawai yabi bayan ta.

Yana tafiya hankalin shi na kan agogon sa da yake Daurawa a wrist din shi.farhat kuma shigowan ta kenan ,hannun ta rike da farin towel tana goge gumin fuskan ta.ji tayi,tayi karo da mutum,dagowa tayi cike da bacin rai taga wani mai tsautsayin ne da wannan gangancin Dan ta dauka cikin Yan aikin gidan su ne. Amma i don ta ya gane mata Wanda tafi tsana a duniya.
[11/18, 8:03 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹
FARHAT
💥💥🔥🔥🌹🌹

Writing by ummee yusuf(maman yusuf)

Wannan page din naku Ne yan group din ZAMA NA AMANA 2.tnx 4 ur surppot.


Pg 12


Murmushin sa mai kara masa kyau ya mata yace"sorry lil sis ban lura bane".kallon tsana take masa tare da nuna kanta da yatsa"nice lil sis dinka?"ta tambaya tana kallon cikin idoj sa.

Hannu ta dora a goshin ta,tace "gosh wai mesa duk wani talaka brain din shi a toshe ne huh?if not dan ka samu alfarma abba na ya dauki nauyin karatun ka shine har ka samu bakin hada kan ka da ni?never i'm not ur sister mallam go nd find ur sis else where.poor bagger.Mtw...taja tsaki tayi wucewar ta ciki ta bashi nan tsaye kaman an dasa shi.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yke mai mai tawa a ranshi.yau ne rana na farko da mace kuma karamar yarinya taci masa mutunci.meye laifin sa dan kawai yna zaune a gidan su?in ba dan yana sanyin hali ba kuma yana ganin mutuncin iyayen ta ba da wlh sai ta gane kuren ta.

Karasowa yayi cikin parlourn inda ya tarar ammi u suna zsune ko wanne yayi shigan alfarma.dukawa yayi har kasa ya gaishe su,amsawa sukayi cikin sakin fuska.abba yace masa ya zauna a kan kujera mana, nan ya hau ya zauna sannan abba ya tara masa bayanin company.

Sun kai kusa 20 mins suna tattauna.kwas kwas suka ji karan takalmin farhat tana saukowa.tayi wanka tasha kwalliyar tA cikin riga da skirt blue colour na english wears tayi matukar kyau .farin veil da ta nada a kan ta ya kara fito da kyan ta.

Kusa da abban ta ta samu waje ta zauna,cikin shagwabA ta gajshe ya amsa tare da tambayan lafiar ta.juyowa wajan ammin ta tayi tana gaishe ta,itama ta amsa.kaman daga sama ya tsinci muryan ta,tana cewa"ya farhan ina kwana ya bakunta kuma?mamaki ne tsantsa a fuskan shi duk da jiya ta gwada masa acting din ta amma na yau yafi bashi mamaki.harda ce masa yaya bayan ta gamaci masa mutunci dan yace mata sis.

Amsawa yayi kawai daga nan yaja bakin sa yayi gum."break fast is ready"tace tAna kallon abba."owk muje mana"yace yana mikewa,ammi tana gaba yana biye da ita sai farhan shima ya mike yabi bayan su.bai ankara ba yaji an mangaje shi, fuuu ta wuce shi da cewa kasa kasa"poor bagger ba zuciyan nema sai maula"

Yanzu kam ta kai shi bango but ya zaiyi?murmushi naga yayi tare da karasowa dinning din yaja kujera ya zauna,still Smile bai bar face din shi ba.farhaf ba haka taso ba.taso ya zuciya ya mata wani abun a gaban abban ta da zaisa ya Kore shi kaman yanda tayi nasara akan sauran.amma shi kwata kwata bashida zuciya.shiko farhan dariyan mugunta yayi a zuciyar Sa lokacin da yaga ta wurga masa harara.

Kaman daga sama taji yace"yauwa lil sis ya maganan mu na dazu kafin ki fita game,"dagowa tayi cike da mamaki tana kollon Sa.bata gama tsinkewa Bama sai da taji yace"da kika ce in rakaki shan ice cream naki,amma yanzu na yarda kinga daga nan nima sai inga gari".

Tari ta fara ba kakkautawa sakamakon kware da tayi da Pepe soup din naman kaza da taken sha.cikjn hanzari Ammi ta bata Ruwa tana bubbuga mata baya.gaba dayan su ,suna mata sannu da kyar ta Samu tarin ya tsaya,idon nan yayi jazir ga hawaye shabe shabe sakamakon yajin Pepe soup din.bayan komai ya lafa Ammi tace"ni dai bansan wani irin son zaki ne dake ba kuma kinsan kina da islamiya yau shine kika ciri fita Yawo?ga farhan din shima ko hutawa baiyi ba.toh ba inda zaki na gaya miki".Abba ne yace"as kar kice haka ki barsu su he mana tunda shi farhan din ma Ai zama waje daya ya ishe shi"gaskiya ne Abba zan so hakan nima"farhan yace."yauwa Ku gama sai Ku shirya Ku tafi "yace yana ajiye tea cup da yake hannun Sa tare da mikewa.Ammi ma mikewan tayi Dan yiwa mijin ta rakiya.

Dariya farhan yayi Wanda ya kara fito da kyan Sa a fili yana kallon farhat da ta daskare a wajan.kashe mata ido data yayi tare DA daga mata gira daya yace"ya kika gani" wasan zatayi kyau ko?murmushin takaici tayi tace"ayya poor begger har kana ganin kayi wining kenan?it is just the begging let's see who will win"tace tana mikewa."alright"yace shima ya mike fuuu ta wuce shi ta haura sama murmu shin yayi yana shafa gashin Kansas dan shi harga Allah yarinyan tana burgeshi but danyan kanta yayi yawa

Tana shiga bedroom dinta,Dan kara ta saka tare da Sa hannun ta duka 2 cikin gashin kan ta,tana hargisawa."who d hell is he?dole in San yanda zanyi ya bar gidan nan for sure".ringing phone dinta da yake ajiye a kan side drower ne ya katse ta.ganin rukky ce yasa ta dauka,tana magana da kyar saboda yanda take huci .

"What happened babe"?rukky ta tambaya cike da tashin hankali Dan ko kadan bass son abinda zai taba bestie su.sai da ta Dan ja numfashi sannan ta Koro mata yanda Yakaye da farhan da kuma abinda abban ta yace.

Tsaki rukky taja tare da cewa"haba mana star,ya kike Abu kaman ba starn da na sani ba?ki tuna fa haddaun guys ma suna shakkan ki balle wani villager zaki rinka bata ranki .kinsan yanda zamuyi?shi gashi sarkin masu kwadayi ba?and har yayi nasara Abba yace Ku fita tare ba.ki kawo shi sidis zamu jira Ku a can tare da ramlat sai mu koya masa lesson mai kyaua can,koya kika gani?"numfashi taja ta sauke tare da cewa"hakan zAnyi bana son tension Sam.he must leave dis house and go back to his village today tanx 4 d idea."

Wanka ta shiga wit full confidence tana ayyana yanda zata ci mutuncin poor begger. bayan rukky ta tabbatar mata zata kira ramlat ta fada mata.

Toh kome farhat da frnds dinta zasuyiwa farhan kuma ko zasu yi nasara?sai Ku biyo ni a next episode.
[11/19, 7:38 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹

Written by Ummee yusuf(Maman Yusuf)

Page 13. & 14

Shiryawa tayi cikin black leggings jeans wit purple top amma ya sauko mata kusa da guiwa black veil tayi rolling dashj,tare dasa wani hadadde black high hills.simple make up tayi tare da makala sun glasses akan veil din.black hand bag ta dauka bayan ta fesa perfumes masu kamshi.phone daya kawai ta dauka,har ta kai bakin kofa ta dawo ta jefa chewing gum a baki mai kamshin strawberry.

Farhan kuwa tunda ya zauna a parlour bai tashl ba suna ta hira da Ammi.kamshin perfumes dinta da karan takalmin ta su suka ankarar dash saukowan ta.
Ammi "tace toh sarkin yawo har kin shirya?"turo Dan karamin bakin tayi tace"Allah Ammi ya farhan ne fa yace muje wai muje da wuri.ko ya farhan?"tace tare da juyowa tana kallon farhan din.shima murmushi yayi yace"haka ne Ammi ni nace muje da wuri"toh ni dai ka tashi mana"tace masa cikin shagwaba.tashi yayj tare da yiwa Ammi sallama,ita kuma ta bisu da addu an a dawo lafiya.

Suna fita daga parlour ta kara saurin tafiyan ta wai Dan kar su jera tare.shi kuma a nutse yake tafiyan Sa har ya iso motan .ita kuma har ta tada mota shi take jira,ta cika tayi fam but a dole take controlling tempern ta.wai har kaman ita zata dauki wannan villager a motan ta baya Ga haka ita ce take jiran sa kaman wata drivern shi."I will show u"tace lokacin da yake rufe kofan side din shi,da yake a hankqli ta fada bai ji me tace ba amma yasan wani cin mutunci ko wulakanci ta shirya masa tunda har ta yarda su fita tare.ko kallon inda take baiyi ba balle ya mata mgn.same itama haka.Jan motan ta fara a hankali zuwa get ,ba madu mai gadi ya bude musu get suka fita yana gaida su.farhan kqdai ya amsa da murmushi dauke a fuskan shi har yana daga mishi hannu.ba madu shima cikin jin dadi yake daga masa bannu 2 Dan baiyi tsammanin amsawan farhan ba.cike da takaici taja dogon tsaki irin ya bada ita nan.a hankali taci gaba da tafjya a cikin anguwan nasu har ta fito nan n.u.j India take tsayawa ta canza kan ta.parking tayi ta sauke glass din da daura a kan veil dn ta,ta rufe idon ta tare dasa music ta kure volume ta figi motan da gudun tsiya ta nufi hanyan milk shop inda many an shaguman saida kayan alfarma suke.

A bakin sidis bakery tayi parking sannan ta fito shima fitowan yayi yana kallon tsaruwan wajan.wata BMW baka tayi parking a gefen su.Yan mata 2 ne a ciki suna masa kallon kuilla.farhat ce ta zagayo wajan motan wit a smile on her face tana musu mgn.cike da mamaki suke kallon farhat da ta gama ce musu Ga poor baggern nan su fito suyi maganin Sa.ramlat tace"star dama wannan hadedden guy din kike bamu lbr?"Ruky ma cewa tayi" oh my god yanxu dai Ku dakata do u mean kin dauko shine Dan mu ci masa mutunci ko me?"farhat cike da takaici take kallon frmds dinta tace"wai me kuke cewa ne,ke Ruky ba ke kika bani idean ba kuma kika tsaya min tambayan raining sence?me ya tsorata Ku ne wai he is no 1 but a poor bagger in our House. Come on lets get going joor".tace tana kokarin juyawa.

Cikin sauri ramlat ta rike hannunta tace" wait star,kin gane guyne ya hadu da yawa Ga kwarjini gaskiya i can't do dis" tace tana sunkuyar da kai kasa.afusace take kallonsu tana shirin juyawa ruky tayi saurin riko ta again ta juya tana kallon direction din farhan taga shi har ya tsallaka wani shop din Mtn ajiyar zuciya tayi tace "pls star we are sorry bazaki gane bane he is damm hot but i have another idea "katse ta farhat tayi cikin tsawa tace "to hell with ur idea if u can't just leave alone and see wat will happen i hate him.ni ina ruwana da wani haduwanshi infact ni banga wani haduwa anan ba sai wani face kanan sadaka yallah.all i know is a poor bagger."Ruky ta kara sassauta voice dinta tace "i know gal just listen to me in idea baiyi miki ba u can do wat ever u like kinsman we are always supporting u" . hakan da tace ne yasa farhat dan saukowa kada tace "ehem I'm listening".Ruky tace "why not kita zaga gari dashi a sunan yaga gari tunda kin ce he is from village i know baisan kan gari ba sai ki samu wani area da ba zai Iya ganewa ba ki barshi a wajan tare da yi mishi warning kar yasha wahalan neman gidanku ki bashi transport money ya wuce kauyen su or else zaki hada shi da solders a matsayin boko haram nasan villagers da tsoro.from there motan kauyensu zai nema kinga kin huta yabar muku gida. murmushi tayi cikin jin dadi tace yes i agree with u nasan yanda zan mishi". ramlat tayi rau rau da ido dan idea bai mata ba sam dan ita har ga Allah da zai amince da ita zatace tana son shi kuma tausayi yake bata tunda sukewa guys wulakanci bata taba jin ba dadi ba sai akan farhan.nan tace "amma star me zaki cewa abbanki in kin koma ke daya?don't worry nasan yanda zanyi "tace tana kallon farhan da ya dawo wajan Moran yana latse latse a phone dinshi.kusa dashi suka zo bayansu ruky sun fito a motansu,a hankali ya dago idonsa masu daukan hankali yan mata ya tsare su dashi cikin murmushi mugunta farhat tace "amm poor bagger ga frnds dina Ku gaisa".Ruky da ramlat da kyar suka tattaro nutsuwarsa suka gaisa suna mamakin

Please Login or Register in order to submit comment