Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi dan bazata iya juran irin kallon da yake mata ba.

Cak ya d'agata ya nufi bed d'insu da ita,cikin kunnesa ta rad'a masa " wankan fa?"

Kallonta yayi da idonshi da ya canza launi har wani lumshewa yake saboda zallan fitana irin nashi "na fasa".ya amsa mata a takaice.
Asuba ta gari Farhan Farhat.

Tundaga wannan rana su Farhan suka shan amarcinsu kaman wa'yanda suka zo honey moon,kullum sai sun fita shopping tare da kaita wajan shakatawa kala -kala.

Sumayya ma yanzu Alhamdullilah sauki ya samu ta bar wheel chair tana takawa da kafafunta.

Farhat in ta zaune ita kad'ai wataran tayi tayiwa kanta dariyan yanda da tayi haukan son zuwa london Abbanta yaki yau gashi aure ya kawo ta.

Zuwa su london kaman da sati uku Farhan yayi mata maganan makaranta,kan cewa ya kamata tacigaba.cikin tsananin murna tace tana so.

A oxford university ya nema mata gurbin karatu,zata karanta m.b.b.s.amma sai nan da sati 2 zata fara fita.

Ranan wata safiyar asabar da misalin karfe tara da rabi na safe sun yi wanka sun shirya cikin shiga mai k'yau amma basu sauk'o k'asa ba suna zaune a parlourn su suna hira.

K'wank'wasa kofan parlourn nasu suka ji anayi,cike da mamaki Farhat ke kallon Farhan dan tunda suka zo ba wanda ya tab'a buga musu k'ofa koda zasu kai azahar basu fito ba.

Zata tashi Farhan ya hanata yace bari shi ya duba.

Yana bud'e k'ofan wata classic beautiful baby fara sol da ita,a haife bazata wuce ta ba ta bayyana a cikin parlourn cikin fara'a.

Suna had'a ido da Farhan tasa ihun murna shima dariyan jin dad'in ganin ta yayi.tafawa sukayi sannan suka juya suka kara tafawa ta baya.

Cikin jin dadin ganin juna Farhan yace" Ummina saukan yaushe?"

"Last night,aida tun jiyan naso zuwa in ganka momy ta hana ni wai dare yayi.kaga saboda zumud'in ganinka ko breakf
ast ban momy tayi ba na taso ta muka zo".


"Gaskiya nima nayi missing d'inki tunda nazo akace kin raka Aunty malaysia naji garin ma ba taste coz ba Ummina a kusa".yace yana dariya.

Farhat tana zaune a inda ya barta zuciyar ta na bugawa fat-fat tunda ta d'ora idonta akan wannan lafiyayyar budurwan.more especially ganin yanda Farhan d'inta yake ta washe mata hak'ora.duk da ta fahimci wacece ita a gare shi amma sam hankalinta yaki kwanciya.

Muryan Maryam d'in taji tana " my so ina amaryar taka take mu ganta dan lokacin bikinka ina final exam shiyasa ban samu hallarta ba".

Ki shiga tana ciki bari inje mu gaisa da Aunty fadila ku same ni a k'asa" yace tare da sa kai ya fice abinsa.

Wani irin kallo take bin Farhat dake zaune kanta k'asa dashi,cikin takunta na k'asaita ta karaso har gaban Farhat.

Sai a time d'in ta d'an d'ago suka had'a ido taga tana mata wani irin kallon tsana da wulakanci.ganin haka yasa Farhat saukar dakai k'asa ba tare da tace mata komai ba.

Dan dariya Maryam ta saki sannan tace " dama nasan wannan tshohon kanurin mai nacin tsiya ba zai bar mu haka ba,duk maula dake a karkashin my son bai ishe shi ba sai da ya jona masa wannan abar" tace tana nuna Farhat da hannau.sannan tacigaba.

"Ina son kisawa ranki cewa Farhan nawa ne na ni k'ad'ai tun ina yarinya na tashi cikin kaunar shi ina jiran right time d'in da zan fad'a mishi Uncle Tahir ya tura shi can kauyenku.nasan tsiddabarunku na yan kauye kuka mishi if not ke d'in baki kai Farhan ya kalle ki coz ga classy gals anan ma basu ishe shi kallo ba.bare villaget irinki.

Tunda ta fara magana Farhat zuciyarta ke suya barin ma yanda wannan 'yar karamar yarinya take ciwa Abbanta mutunci.a harzuke ta tashi ta d'aga hannu da niyan marinta amma caraf Maryam ta rike mata hannu tace "dont u ever try dis mistake in ur life".

Jin karan bud'e k'oga yada suka kalli k'ofan dukansu.Farhan ne ya shigo da fara'ansa yana cewa "hiran me kuke ne Ummina baku sauko ba?"

Kamin Farhat ta bud'i baki maryam ta rigata tace" ya Farhan kayi sa'an mata ga k'yau ga kirki kaganta nan tundazu nake son fita amma ta rik'e ni da hira".

Baki da hanci Farhat ta sake tana kallon yanda Maryam da har yanzu tanarike hannunta.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha Allah 🤝)

Salam ina godiya da kaunar da kuke nuna min masoyana.masu neman in sasu a watsapp group,kuyi hakuri wallahi abin ne a hankali.kuyiwa admins magana.nagode sosai ina yinku sosai irin over din nan my fans.😍😍


Page 67~68


Ficewa Farhan ya karayi ba tare da ya lura da yanayin da suke ciki ba.

Wurgi Maryam tayi da hannun Farhat da ta rike tana mata kallon warning,sannan itama tasa kai ta fice.

Dabas Farhat ta zauna akan kujeran dake bayanta,zuciyanta har yanzu kaman ya fito take ji.

Wani hawaye mai d'umi suka fara ambaliya akan fuskanta,da zuciyarta ta hasko mata hotonta lokacin da takewa mutane irin wannan cin mutuncin.

"Dama haka suke ji a cikin zuciyarsu, mutane nawa nasa suka zubar da hawaye a dalilina?nasan alhakin sune yake bibiyata".tace tana hawaye sosai.

Hannayenta duka 2 ta d'aga sama ta fara addu'a Allah yafe mata.

Ta dad'e tana addu'oi sannan ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskanta tare murza d'an powder da wet lips dan kar a gane tayi kuka.

Fita tayi itama zuwa k'asa,tasan suna can suna jiranta breakfast.a zuciyarta kuma tana godewa Allah da ba gida d'aya suke da Maryam ba.dan tasan in gida d'aya suke toh ba zata barta ta zauna lafiya ba.

Suna kan dining duk kansu kaman yanda tayi tsamani.

Tunda ta fito mahaifiyar Maryam wato hajjiya Fadila take kallonta tana murmushi.

Har k'asa ta durkusa ta gaishe da Mamy,sannan ta juyo wajan Hajiya Fadila ta gaishe ta itama.

Cikin sakin fuska ta amsa har tana zolayan Farhan ya iya zab'e.

Tab'e baki Maryam tayi tana hararan Farhat,dan ita bata ga abin k'yau ko birgewa a b'akar mace ba.

Hira suke tayi a parlour bayan sun kammala breakfast.

Maryam tana gefen Farhan kaman ta shige jikin shi wai tana bashi labarin malaysia.shima ya biye ta suna ta surutu.

Farhat tana zaune kusa da Sumayya tana bata labari amma hakalinta k'wata-k'wata baya kanta.yana kan Maryam da ta manne mata a jikin miji.lokaci-lokaci in sun had'a ido sai ta b'alla mata harara.

Murmushi Farhat tayi a ranta da ta tuna cewa duk wani abinda zatayi na wuni d'ayane ta koma inda ta fito.

Kaman tasan tunanin da take taji tana cewa" momy ni ba zan koma gida yau ba zan zauna da sis Sumayya na kwana 2".

Ras-ras taji zuciyarta buga.bata san lokacin da ta d'aga ido ta kalle ta ba,itama d'in ita take kallo da murmushin mugunta a fuskarta.

Mik'ewa kawai tayi tare da yin hanyan part d'in su.Mamy ce take tambayanta me yasa ta tashi ana hira?

"Zanyi waya ne" ta amsa mata atakaice.

Farhan ya fahimci kaman akwai abinda ke damunta dan haka yayi niyan binta,amma Maryam ta rik'e shi ta hanyan nuna masa pics a wayanta.

Kwnciya tayi a bedroom d'insu tana tunanin yanda zaman su da Maryam zai kaya.

Farhan bai shigo ba sai bayan sallahn azahar.

Zaune ya same ta a bakin gado tana game a wayarta,tayi wanka ta canza shiga zuwa wani fitted gown na atampa.bata d'ora d'an kwalin ba saima zubo da gashinta da tayi wanda yasha gyara.

Da sassarfa Farhan ya k'araso ya rungume ta dan shigan nata ya tafi da imanin shi sosai.

"Shine kika gudo nan kika barni a can ,harda sake sabon wanka ba ko gayyata" yace yana shinshinata kaman wani sabon maye.

D'ago shi tayi a jikinta tana kallonshi da murmushi a fuskanta tace "naga kuna hira da 'yan uwanka,bai kamata in katse muku ba".

"Bazan ma kara sauk'a ba bare su rik'e mutum da hira",yace yana laluban bakinta.

Suna cikin haka suka tsinkayi muryan Maryam a parlour tana kwalawa Farhan kira.

Cikin wani yanayi na an katse masa abinda yake,ya mike ya fito parlour ya sameta dauke da wani babban tray mai d'auke da warmers masu d'an karan k'yau.

Tana ganin yanayin da ya fito saida taji kaman taje ta shake Farhat har lahira saboda kishi,amma ta daure ta gyara fuskanta tace masa abinci ta kawo musu nan.a zuciyarta ko tayi alkawarin hana su sakewa muddin tana gidan.

Dole Farhan ya d'an gyara fuskan shi yace " haba Ummina,aida baki wahalar da kanki ba zamu sauk'o k'asa in time d'in lunch yayi".

Ajiye trayn tayi akan dinning table dake nan parlourn nasu sannan ta juyo tana kallon shi tana girgiza kai tace " ban yarda ba da wannan tsarin my son,bazan yarda kaida in-law na kuna wahalaba.since ina cikin gidan nan is my right to take care of u 2,come nd join me".tace tana jan kujera dan ta zauna.

Komawa ciki yayi ya samu Farhat kaman yanda ya barta tana kwance ta lumshe idanunta.

Duk yanda Farhan yayi akan ta tashi suje suci abinci,k'i tayi tace ita bacci take ji sai anjima zata ci.ba yanda ya iya haka ya fito wajan Maryam da ta tula abinci agaba tana jiransu.

Serving d'in shi tayi tana tambayan me yasa Farhat bata fito ba,amsa mata yayi da tana bacci.

Zagewa tayi tana masa surutu tana cin abincinta hankali kwance,shi kuma cakalan abincin kawai yake badan yaso ba,baya son ya gwaleta ne ganin ta nuna kulawrta garesu.

Koda suka kammala ma k'in tafiya tayi ta cigaba da zuba surutu har lokacin sallah la'asar sannan yace mata zai fita masallaci ya fice ya barta.

Tsam ta mik'e ta nufi bedroom d'insu.

Farhat tana tsaye a gaban mirrow tana gyara fuskanta.dan fitowanta kenan daga alwala.sai jin dariya tayi a bayanta harda tafi.

Ko bata juyo ba tasan wacece.

"Oh god matsalata da matsiyaci kenan ba'a iya samun waje ba sai an nuna zak'ewa.in ba haka ba menene abin kallo a wannan black face d'in nan.oh na manta ashe an shigo london anyi clean".tace tana kara kwashewa da dariya.

Farhat ko motsi batayi ba bare tayi yunkurin ramawa,hawayen da ya zubo mata ta share tana kara neman gafaran mahaliccinta tasan alhakine ki bibiyenta.

Da daddare ma haka ta hana Farhan tashi bayan sunyi dinner saida Mamy tasa baki sannan ya samu ya sulale zuwa part d'insu.

Sumayya an sata makaranta wanda yake dai-dai da secondry school dan haka bata zama a gida sosai.Farhan shima ya fara fita office,Mamy ma bata kasar ta taho nigeria wajan yaranta da suka zo wajan dangin bababsu hutu suka rik'e su.gida ya zama daga Maryam sai Farhat kad'ai suke wuni a gida.

A wannan zaman da suke ba k'amin hak'uri da juriya Farhat keyi ba dan wulakanci kala-kala take mata,amma in a gaba mutane ne sai ta nuna tafi kowa sonta.wani lokacin in iskancin ta ya motsa har aiki take sakata kuma a gaban Farhan wai ita surkuwarta ce.

Gashi gaba d'aya ta hana su sakewa a gidan kullum tana mak'ale da su.

A yanzu shi Farhan d'in ma ya fara gajiya da lamarinta just dai baisan yanda zai yakice ta daga jikinsa bane.

Farhat tun tana hak'uri tana shanyewa saboda tana ganin alhaki ne ke binta amma yanzu tana ganin lokaci yayi daya kamata tayi maganinta coz ba abinda zata nuna mata na irin wannan maikircin just dai ta k'yale tane.

Yau tunda safe ta tashi da niyyan maganin Maryam,dan haka wanka tayi cikin k'anan kaya.rigace mini gown red colour wanda ko guiwarta ba kai ba sai make up da tasha ga wani sexy red lip stick da ta shafa.tayi bala'in k'yau.

Maryam kaman yanda ta saba ta shigo musu da breakfast tana k'wala sallama a palour.

" my son fito ur breakfast is readyyyyyyy"

Tsaki farhan yaja yana kallon Farhat da ta gama k'wallitarta,yaso ace shi zai bata amma wannan yar damuwan tazo da sassafen nan.

"Bazan ci abincin nan yananzu ba tunda yau asabar,bari inje ince taci rabonta kawai" yace yana shirin mik'ewa.

Hannunsa Farhat ta rike tana mada wani killer smile" muje muci my Baby yau yunwa nake ji".

Cike da mamaki da jin dad'i yake kallonta coz yaushe rabon ta zauna suci abinci tare saboda fitinan Maryam.

Hannunta ya kamo yana murmushin jin dad'i yace" muje muci tunda kika ce zaki ci naji nima yunwar ta taso min".

Dariya kawai tayi ta tashi tare da manne masa a jiki sannan suka fito.

Ganinsu a haka ba k'aramin razana Maryam yayi ba a zuciyarta tana mamakin yaushe Farhat ta zama haka.

Muryan Farhan da taji yana mata magana shi yayi sanadin dawowarta daga tunanin da ta tafi.

Mamakinta ne ya k'aru da taga Farhat zaune akan cinyan Farhan tana zuna mishi shagwab'an ya bata abinci a baki yana biye mata.

Takaici kaman ta mutu amma ta daure zuciyanta, bari ta nuna mata nata salon.

Shayi da ta kurb'a ta feso jikin Farhat wai k'onewa tayi.

Nan Farhan ya hau mata sannu har yana neman tashi bai kula da yanda ta fesowa Farhat ruwan tea d'in ba dan shi har ga Allah ya d'auka da gaske k'onewan tayi.


Wani kara Farhat tasa tana wayyo idona shi yayi sanadiyan fasa tashi da yayi niyya ya kama ta yana "what happend my shinning star?"

"Yaji wash hura min baby,wash idona".

Bakin shi ya kai kan idonta yana hurawa a hankali yana "is ok my baby shhhh is ok"

Satan kallon Maryam tayi da ta cika tayi fam saura tayi bindiga,murmushi ta sake mata sannan ta fara " wayyo bakina baby bakina harshena zafi shhhh"

Barin idon yayi yana" mugani me yasamu harshen kuma?"

Dan zaro harshen tayi tana yarfe hannu,shi kuma ganin harshenta a waje yashi manta akwai wata Maryam a wajan kai baki yayi zai kamo harshen nata.

A zuciye Maryam ta tashi fuuuu ta fice dan inta cigaba da zama tana iya shek'ewa dan bakin ciki.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha Allah🤝)


Page 69~70


Sun d'auki lokaci mai tsawo a haka coz Farhan yama manta aina suke.ita Farhat kuma tana sane ta cigaba da d'auke masa hankali dan kar ya ankara bata wajan.

Dakyar ta k'waci kanta a hannun Farhan da yake kokarin zarcewa.

Abincin ta nuna masa da hannu tana mishi.dariya.

Dafe goshinsa yayi da hannunsa na dama yana yana kallon inda Maryam ta tashi.

"Ina ta tafi ne?"yace yana kallonta da sexy eyes d'inshi.

"Wa kenan?"Farhat ta jeho masa da tambaya itama.

"Ummina mana she was seating here" yace yana pointin kujeran kujeran da Maryam ta tashi.

Wara hannayenta duka 2 tayi tare da d'aga kafad'a,alaman oho itama bata sani ba.


Shafa gashin kansa yayi yace "oh god we watch everything".

"And so......?"tace tana dariya.


Dariya shima yayi ya mik'e da niyyan binta.tana gani haka tasa masa shagwab'a ita yunwa take ji ya zai tafi ya barta basu ci abinci ba.

Dole ya dawo suka zauna cin abinci tana zuba masa sakalci wanda tuni ya mance da wata Maryam can.

Maryam tana fita direct bedroom d'in da ta sauka ta wuce,kan gado ta fad'a tana kukan bakin ciki ga kishi da take ji kaman tayi hauka.

Tana rufe ido fuskan Farhan take hangowa yana kissin d'in Farhat.wani yanyi take shiga wanda bazata iya k'watanta shi ba,ji take kaman ta mutu ta huta


Har rana Maryam ta kasa fitowa a d'aki sai sak'a da warwara take na yanda zata karkato da hankalin Farhan kanta.

Farhan kuwa yana can makale da matarshi,yau duniya sabuwa.sosai ya samu sakewa da matar sh,i rabon da su samu wannan privacyn tun kamin yar damuwan nan ta zo.


Sabon sunan da yasa mata 🤣🤣.


Ko masjid yau bai lek'a ba,in lokacin sallah yayi shi yake jansu jam'i.

Suna kwance kan gado Farhat tayi pillow da faffad'an kirjin shi suna hira kuma tana kallon pics a wayan Farhan.

Videos ta kamo tana kallo har tazo kan wani video da yasata tashi zaune ba shiri

"Lafiya me kika gani ya firgita ki haka?"yace shima yana tashi zaune.

Bata iya bashi amsa ba sai wayan ta mik'o masa.

Dariya ce ta sub'uce masa ganin abinda ya firgita ta.

Videon da ya matane tun a gidan su,tana motsa jiki a basket ball filled d'inta.

Kallonsa take cikin neman kar'in bayani.

Jawota yayi suka koma suka kwanta,sannan ya rad'a mata a kunne.

"Dont be suprice my shinning star,u have become a part of me when i set my eyes on u for d first time.
Which made me ur shadow,but sai naga ko kad'an bana gabanki.all wat i can see in ur eyes 4me was hatered.shiyasa ban fito maki da abinda yake zuciyata ba sai na biki a yanda kike so".

D'agowa tayi daga kwancen da tayi ta zuba mishi ido tap da cike da k'walla.

"Noo Farhan karka ce haka,ni kaina i fall in love wit u d moment i set my eyes on u in d airpot.but sturboness dake kaina ya hana ni fahimtar haka on time".

Kara jawota yayi ya kwantar da ita yana sauke ajiyan heart at d same time yake bayyana mata yanda yasha wahalan dakon soyayyarta a zuciyan shi.

"Hmmm gwara kai kasan sona kake a lokacin,nifa da nake ta hauka akanka wanda ni a tunanina kiyayyarka ce,kullum da tunaninka nake kwana nake tashi,amma duk ban d'auka so bane".


Bata fuska tayi kaman zatayi kuka tace " shine kake min lab'e kana k'are min kallo ban sani ba".

"Abubuwana nake kallo,ko nayi laifi?"yace yana kashe mata ido daya.

Turo baki tayi tace" ni dai bansan wasu abubuwanka ba".

"Are sure baki san su ba?"yace yana dawo da ita k'asa shi kuma ya haye samanta ya mata rumfa.

"Let me show u ".yace yana cusa fuskanshi a kirjinta.

Nan kokawa ya kaure tsakaninsu duk abinda ya mata sau tace bata yarda ba sai ta rama.


Sun d'auki lokaci mai tsawo suna wasanin baka jin komai sai dariyan su, basu san lokaci ya tafi ba sai kiran sallah magrib suka ji.

Tashi Farhan yayi ya shiga bathroom yana cewa yanzu kam masjid zai je,yau ta hana shi fita.


Alwala yayi ya wuce fita masjid.

Wanka Farhat tayi sannan ta d'auro alwala ta gabatar da sallah magrib,bata tashi a wajan ba saida ta jira lokacin isha'i yayi,shima tayi sannan ta tashi akan sallayan ta koma ka dreesing mirrow ta tsantsra make up kaman mai shirin tafiya dinner.batayi amfani da perfume ko body spray ba.farin humra ta shafe jikinta dashi saboda ganin yanda Farhat yake susucewa in tayi amfani dashi.

Sanin Mamy bata nan yasa ta saka wani hot sexy english gown pink colour,dogone har k'asa sai dai anyi masa wani tsagu daga gefen dama tundaga cinya har k'asa.kayan bashi da hannu sai igiya da ake d'aure shi a wuya.

A cuci tayi da dogo gashin kanta da ribon pink,high hill shoe tasa sannan ta sauk'o k'asa.nan ta tarar da Sumayya da wata maid suna hira.

Zama tayi aka cigaba da hiran da ita Sumayya tana tsokananta da duk wannan k'walliyan na yayanta ne.

Basu fi 20mins da zama ba Farhan ya shigo,maid d'in tana ganin shi ta mik'e cikin girmamawa ta gaishe shi sannan ta bar wajan.

Hira Sumayya take musu amma Farhan da sun had'a ido da Farhat sai yayi mata alama da su wuce part d'insu.

Tana ganin shi ta basar,sai cewa ma tayi Sumayya takira Maryam suyi dinner.


Sumayya tana tashi ya dawo gaban Farhat ya tsuguna tare da kamo hannayenta cikin wani yanani dan wannan humran da ta shafa. yace " mu bar cin abincin nan muje part d'inmu nayi miki tanadin wani abu mai dad'i da yafi wannan abincin".

Mak'ale kafad'a tayi tana turo baki tace"ni bana son komai sai abinci,haka d'azu ma ka hana mu lunch".

Sumayya tana fad'wa maryam sak'on su Farhan ta wuce d'akinta dan d'auko tex book d'inta,akwai abinda ya shige mata duhu take son nunawa Farhan dan ya fahimtar da ita.

Maryam duk farinciki ya cikata jin Farhan ne ke kiranta wajan cin abinci.cikin zumud'i ta tashj harda d'an gyara fuska sannan ta fito.

Daskarewa tayi a bakin k'ofan shigowa parlourn sakamakon yanayin da taga su Farhan a ciki.

Da gangan Farhat take tayiwa Farhan salo kala-kala saboda taga fitowan Maryam dan tana facing d'in k'ofan shigowa.

Farhan sai birin shi kawai yake sakamakon ya juyawa k'ofa baya.

Da matsacin gudun tsiya ta koma ciki tana kuka.sai a sannan Farhat ta janye jikinta daga gare shi tace" ya isa mana kabari kar Sumayya ta ahigo ta ganmu haka".

"Ta gani mana,in ba kya so ta gani tashi mu koma part d'inmu"yace yana k'ara lalubanta.

"Naji zan tashi amma ka barni pls "

Tashi yayi a gabanta yana mik'o mata hannu.

Sumayya ce ta fito da saurinta tana cewa " yauwa ya farhan in munci abincin ka duba min wannan tex book d'in".

"Toh "kawai yace yayi gaba zuwa dinning area Farhat tana mishi dariya harda gwalo.

Leben shi na k'asa ya ciza yana girgiza kai irin zamu had'une yarinya.

Da washe gari basu farka da wuri ba saida rana tayi.

Tare sukayi wanka suka shiry tsab cikin english wears sai kamshi suke.

Sanin mayb Maryam zata shigo yasa taki locking d'in k'ofan parlourn nasu ta barshi a bude.

Maryam kuwa kusan kwanan zaune tayi tana neman mafita tare da mamakin ya akayi farhat ta falle lokaci d'aya haka.

Murmushi mai kayatarwa tayi da samowa kanta mafita.sai kusan asuba sannan ta kwanta bacci.

Wanka tasha itama cikin english wears tayi bala'in.

Ba bata lokaci tahi hanyan part d'insu Farhan.

Farhat tana zaune a kan kujera tana facing d'in hanyan ahigowa yauma.shi kuma Farhan yana k'wance ya d'ora kansa a kan cinyan Farhat suna hira,amma ita Farhat rabin hankalinta yana kan hanyan shigowa.


Jin alaman takalmi yasa tayi saurin sauk'e kansa daga cinyarta, ta haye kansa tana masa wani salo da ita kanta bata san ta iya ba sai yau.

Maryam tana tsaya bakin k'ofa tana kallonsu zuciyarta kaman ya fito,amma ta daure ta karaso ciki dan nunawa Farhat iyakarta.


"My son!! Muna ta jiranka wajan breakfast shiru baka sauk'o ba"tace idonta taf da hawaye.

Farhan baima jita ba coz Farhat ta zautar dashi da salonta.

Murmushi ta sake ma Maryam da suka had'a ido sannan tayi saurin ture Farhan gafe ta tashi zaune tana gyra zaman riganta daya kusa zamewa.

Wani kallo yake binta dashi da idanunshi da suka canza kala ba komai a cikin su sai zallan fitina yace cikin muryarsa da ta koma kaman ta 'yan maye,yace" meye haka kuma baby"

Bata bashi amsa ba sai nuna masa Maryam dake tsaye tana ma Farhat wani kallo kaman ta shake ta.

Cikin wani irin bacin rai Farhan yake kallon Maryam.

Cikin had'e rai da tsawa yace " ke meye haka zaki wani shigowa mutane ba sallama kaman ba musulma ba.kuma da kika shigo yaci ki koma inda kika fito tunda kiga ganmu cikin wani hali".

Hawayen da take rikewa ne suka samu nasaran zubowa.

Farhat ce tayi caraf tace " haba my baby mayb abinci fa ta kawo maka".

"To hell wit d abinci haba na gaji wani irin takura ne wannan,ba wani abu da tasani sai cin abinci?am fed up".yace ya tashi a zuciye yayi bedroom d'insu.

Tashi Farhat tayi tana kareraya zuwa gaban Maryam da take hawayen cin mutuncin da Farhan ya mata.

"Noo ki adana hawayenki 'yan mataba yanzu ya kamata ki zubar dasu ba,there are many more coming dan wannan somin tab'ine muddun baki fita a rayuwarmu ba.kar kiga kwanaki na d'aga miki k'afa ki d'auka na kyale kine,just ina jiran right time ne soooo...." had'a yatsunta 2 tayi suka bada wani kara sannan ta juya tayi shigewarta wajan mijinta.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by umme yusuf
(Maman yusuf)


💫FAGEN-MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

(Gidan aminci,zaman lafiya da yarda da juna insha Allah🤝)


Page 71~72


Da d'an gutun hawaye Farhat ta shigo bedroom d'in ta samu Farhan yana zaune rai a bace har yanzu.

Zama tayi kusa da shi tare da d'an kwantawa a jikin shi tana goge hawayenta.

D'agota yayi da sauri yana kallonta yace " wat is it my shining star,me yasa kike zubar min da precious tears d'in nan?"

Cike da salon jan hankali da shagwab'a tace " ba kai bane".

Ni kuma,me nayi har kike hawaye?"

Baki ta turo tace" abinda kayiwa Maryam ne banji dad'in shi ba,ina son yi maka danderu da kaina da abincin gargajiya da kake so,shine jiya da taji ina zancen tace zata taimaka min dan tana son koya itama but yanzu ta ina zan fara neman taimakonta? nasan yanzu tayi fushi mai tsanani".


" haba baby kema kinsan abinda tayi bata k'yauta ba a matsayinta na 'yar musulma.bayan haka aini yayanta ne dole in nuna mata kurenta in tayi ba dai-dai ba.yau sunday Sumayya tana gida kice ta taya ki mana ko ga maids a gidan nan birjik suma sun ishe ki".yace mata cikin tsigan lallashi.


Mak'e kafad'a tayi tana kara narke masa a jiki tace "um-um ni dai ita nake so tunda da bakinta ta nema.kana zancen Sumayya taya zanyi ince ta shiga kitchen alhali lafiya bata ishe ta ba.kuma wa'yanan maids din me suka sani a

Please Login or Register in order to submit comment