Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daina motsi, Affan yace ehh, tace to shima ya tafi bazai
kara dawowa ba saboda halin shi bashi da kyau, mugu ne
so yakeyi ya kasheka shiyasa yake yawan zuwa yace kuje
kuyi sallah,
Affan yayi narai narai da ido yace mummy ba mugu bane,
yana kawo min cwts, baya dukana kuma baya min ihu
kamar yadda su anty salma suke min,
oyizah tace muguntar kenan ay saboda yanaso ya kasheka
wata rana shiyasa yake maka haka, amma kaga saboda
am wit u gashi yanzu ya mutu har an kaishi rami, ka manta
dashi kaji Affan din daddy,
Affan ya gyaďa kanshi hawaye suka sauka a kuncinshi
wanda shi kanshi baisan yanda akayi suka fito ba,
maganganu ta cigaba da yi mishi tana kara tsoratar dashi
har saida ta tabbatar ya tsorata sannan ta kaishi ďaki ya
kwanta tababbiyar zuciyarshi na karyata maganganunta
akan jabeer,,
Daki ta koma tana sauke ajiyar zuciya dan ba karamin yaki
tayi gurin sanyawa Affan tsoro a ranshi ba, a zuciyarta tace
tabbas sai tayi da gaske dan mutuwar jabeer na neman
karya duk wasu alkadarinta..... ◆◆ RABO AJALI ◆◆
3⃣6⃣
.
By Suleiman Bomboy
.
Da sassafe alhj basheer ya shigo dakin ya tarar da Affan
zaune a lallausan gadonshi yayi tagumi, a hankali ya cire
hannun da yayi tagumin dashi yace me ya sameka dan
daddy,
Affan ya kwanta kan cinyar daddy yace daddy Afeeyah tana
can a gida tana kuka, ya ďago kanshi da ya ciko da kwalla
yace daddy abokina ya zo yace in je in rarrasheta,
alhj basheer yayi murmurshi dan ya dauki maganarshi
shirme yace in ji wa yace maka tana kuka,
Affan yace jabeer ne ya faďa min,
alhj basheer yace a ina kaga jabeer din,
Affan yace ana ruwan sama na ganshi a window na,
alhj basheer ya shafa kanshi cikin mamakin yadda akayi
kwakwalwar Affan ta fara rike mafarki yace tashi kaje kayi
wanka zan je in rarrasheta anjima,
Affan yace to daddy yaushe zata dawo nan gidan sai in
dinga rarrashinta,
Alhj basheer yayi hanyar waje yace kayi wankan kazo ka
karya tukunna,
Affan ya mike yayi hanyar bayi yana kallon window inda
yaga jabeer cikin baccinshi amma shi ya kasa gane mafarki
yayi dan ya hakikance a zahiri yaga jabeer,
bayi ya shiga yayi wanka ya jika ko ina kamar yadda ya
saba har ya bude pampo zaiyi alwala kamar yadda kaka
liman ya nuna mishi sai kuma ya fasa saboda tuno kalaman
oyizah,
da sauri ya fito daga bayin ya shirya cikin matsatsun
kaya...
Alamarin Affan ya fara bawa alhj basheer tsoro saboda
kullum sai yayi mishi magana akan ya dawo mishi da
Afeeyah gidansu, abinda yake fin bashi tsoro bai wuce
yadda yake haddace mafarkan da yakeyi akan jabeer ba,
yawan mafarkin da yakeyi ne ma yake hanashi tambayar
inda abokinshi yake saboda yana ganin kamar a zahiri yake
ganinshi,,, duk wannan mafarkin da Affan yakeyi bai taba
faďa ma oyizah ba dan ko yazo zai faďa mata sai ya fasa
ya kama harkar, daga shi sai mahaifinshi kadai suka sani...
A ranar da za'ayi sadakar bakwan jabeer kuka sosai Affan
ya tsare mahaifinshi dashi akan shi gobe in ba'a kawo
mishi Afeeyah gidan nan ba bazai kara cin abinci ba,
hankalin alhj basheer ya tashi matuka saboda yadda Affan
ke kuka harda majina,
dakyar ya lallabashi yace gobe in shaa Allahu zan dawo
maka da ita gidannan kaji, Affan ya share hawayenshi ya
rungumeshi cikin jin dadi yace bari inje in faďa ma mummy
sai tayi mata abinci mai dadi ko,
alhj basheer ya gyaďa kanshi,
Affan ya tashi ya fita yana ihun murna, binshi alhj basheer
yayi da kallo a zuciyarshi yana tunanin yadda zai tinkari alhj
bara'u da mahaifin Afeeyah da maganar auran mahaukacin
danshi dan in ba aure ba babu abinda zai kawo Afeeyah
gidanshi ta zauna,
dakinshi ya wuce yana jiyo ihun Affan a waje yana yi yana
tsallen murna....
Da wuri aka idar addu'ar bakwai akayi sadaka sosai mutane
suka watse,
alhj basheer zaune a parlon alhj bara'u suna yar hirah jefi2,
alhj Bara'u ya kalli alhj Basheer yace alhj tun a gurin addu'a
na lura da yanayinka kamar wani abu na damunka, alhj
basheer yayi ajiyar zuciya yace wallhy alamarin yaron nan
ne ke matukar bani tsoro, alhj Bara'u cikin damuwa yace
alhj Basheer kenan ay cuta kaffara ce,
ka dinga godewa Allah da lalurar da ya ďaura mishi dan shi
kadai yasan sirrin dake cikinta, gara kai ma zaka kalleshi a
haka kaji dadi,
yayi murmushi mai ciwo yace Allah ya kai rahama kabarin
jabeer, alhj basheer yace "ameen" amma ni ba ciwon Affan
bane ya dameni,
wani abu yake so inyi wanda a ganina son zuciya ne in har
na yarda na biye mishi,
alhj bara'u yace menene shi alhj,
nan alhj basheer ya faďa mishi duk abinda Affan ke faďa
mishi game da mafarkinshi, alhj bara'u yayi ajiyar zuciya
zaiyi magana kaka liman ya shigo da sallama,
da sauri suka mike suna mishi sannu da zuwa dan ya koma
Daura tun ranar uku, zama yayi a gajiye yana amsa musu,
bayan sun gaisa Amirah ta kawo mishi abin kari ya zauna
kamar ba gidan ďanshi ba dan baida wannan kauyancin
akanshi yaci abincinshi son ranshi yana ci suna hirah,
alhj basheer ya kalli alhj bara'u yace bari in tafi anjima ma
karasa maganar,
kaka liman yayi maza cikin wasa yace zauna tare za"a
karasa maganar dani in dai ba ta gulma bace,
suka kwashe da dariya suka ce bata gulma bace kaka, yace
to a cigaba mana, daga ganina sai ku bari,
alhj bara'u yace to Baba bari mu cigaba kaima sai ka bada
shawararka,
yayi murmushi yace to inaji,
alhj bara'u ya fada mishi komai kamar yadda alhj basheer
ya fada mishi,
kaka liman yayi murmurshin jin daďi a zuciyarshi yace ikon
Allah kenan jiyan nan nake tunanin yadda zanyi a karasa
burin jabeer sai gashi cikin sauki wacce yakeso ita zata
karasa aikin da ya dauko na amininshi, tabbas akwai wani
boyeyyen alamari a cikin wannan auren in har ya ďauru,
ya kalli alhj basheer yace to meye abin son zuciya anan,
aure fa kace bawai wani abu ba, kuma ay Affan a wannan
lokacin yana bukatar mata saboda haukarshi ba wata
hauka bace kawai dai yana abubuwan kananan yara ne,
yanzu in har Allah ya tabbatar da auren nan kai da kanka
zaka sha mamaki saboda yanzu ne zai samu wacce zai
zauna da ita dare da rana kuma nutsuwa sosai zata
shigeshi har ta iya kaishi ga samun sauki in Allah ya so, dan
komai sai ya so ko ba haka ba,? suka ce haka ne kaka, yace
to ku barmin komai yanzu zanje in samu malam atikun in
faďa mishi in so samune ma ayi auren yau tunda me zamu
jira, nayi imanin hankalin jabeer zai kwanta a cikin
kabarinshi in har wannan auren ya yiwu saboda
masoyanshi ne kuma hakan zaisa ako da yaushe su dinga
tunawa dashi, amma in mukayi sakacin barinsu suka auri
bare to fa zasu manta dashi cikin adduoinsu ko ba jima ko
ba daďe,
alhj basheer yace haka ne kaka, to ubangiji Allah ya
tabbatar mana da alkhairin dake cikin auren, Ameen sukace
gaba dayansu sannan suka kama wata hirar...
Zaune take a gefen gado kanta na kallon sama hawaye na
gangarowa daga gefen idonta,
cikin muryar damuwa Hajja dake zaune a gefenta tace
yanzu dan Allah bazaki yi tawakkali ba Afeeyah, ace yau
kwana bakwai babu ci babu sha sai aikin kuka, duk kin
rame kin lalace, wannan kukan da kikeyi bashi zai dawo da
jabeer ba, Allah ya fiki sonshi shiyasa ya ďaukeshi daga
wannan rikitaciyyar duniyar, kamata yayi hakuri ki dangana
lamarinki ga Allah ki dage wajen yi mishi addu'a wannan
shine kadai zai nuna lallai son da kike mishi babu algus a
ciki, kinsan yadda jabeer ya tsani yaga zubar hawayenki
gashi saboda shi kin kwana bakwai kinayi ba bacci bare cin
abinci, gaskiya in har kikace haka zaki cigaba dayi
hankalinshi bazai taba kwanciya ba gara ki dawo da
walwalarki kamar yadda kika saba duk da nasan da kamar
wuya amma hakan zaki daure tunda kinsan ba'a taba
mutuwa an dawo ba,,
Afeeyah tunda har manzon Allah S.A.W yabar duniya to ki
tabbatar da babu mai shigowa cikinta ya zauna,
muma yau ko gobe zamu bi jabeer inda yaje,,,
Cikin kuka Afeeyah tace Allah yasa yau ďin ne, Hajja kin
kasa ganewa ne, nayi duk iya kokarin da zanyi in hana
kaina kuka na kasa,
dan Allah ki fada min yadda zanyi in daina kukan mutuwar
yaya jabeer, tun ina karama bansan kaina ba fa nasanshi,
ya bani kulawar da babu wanda ya bani ita, ya soni ya
kaunace ni, kuma yayi yaki da duk wani abun da zai sani
damuwa,
ta kara fashewa da kuka murya na rawa tace ya Allah ka
sassauta min wannan jarabawar tayi min zafi da yawa,,,,
sallamar malam Atiku ce ta hana hajja yin magana, zama
yayi yana kallon Afeeyah yace hajja yarinyar nan na rasa
wani irin rubutu ne zai saukar da salama a cikin zuciyarta,
hajja tace sai dai addu'a kawai nasan in shaa Allahu bazata
dawwama haka ba,
malam atiku yace haka ne, ya kalli Afeeyah cikin taushin
murya yace tashi kije dakina kakan jabeer zaiyi magana
dake, Afeeyah ta mike dakyar kanta na sara mata tasa hijab
ta fita,
a kofar dakin inna suwaiba kausar ce da kawayenta zaune
suna gulmarsu akan Afeeyah basu san ta fito ba,
kausar tace kunsan irin wannan shakuwar fa bata Allah
bace kukan da take yawan yi tana tunanin wanda zai aureta
ne saboda jabeer ya gama bata mata rayuwa,
inna tace ya maida ita baiwar gadonshi kullum sai ya
kwasheta kamar abinci,
Hidaya tace kai kausar,?
kausar tace wallhy da gaske nakeyi inna tace ta taba kama
su turmi da tabarya a dakin hajja lokacin babu kowa a
gida,,,,
Karima tace haba shiyasa kullum take kara kyau kamar
sabuwar amarya ashe ashe "Mammannur yoghurt" ke gyara
ta, Sahura tace Allah sarki ay dole tayi kuka tunda yanzu ta
zama saura wanene zai kwashi saura,
suka watse da dariya suna tafawa da Karima suna
tambayarta meye mammannur yoghurt, karima tace au
baku sani ba,
a hankali ta raďa musu suka sake watsewa da dariyar
shakiyanci, ,,, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kaďai Afeeyah
ke iya faďi saboda tashin hankalin mugun kazafin da
kausar da inna suwaiba suke musu,,,
kuka ne ya kufce mata saboda kalamansu sunyi mata tsauri
da yawa tayi saurin fadawa dakin mahaifinta gurin kaka
liman.......

◆◆ RABO
AJALI ◆◆ 3⃣7⃣to3⃣9⃣
.
By Sulaiman Bomboy
.
Zama tayi a gefenshi cikin muryar kuka ta
gaisheshi,
sai da ya ďan jima sannan ya kalleta batare da ya
amsa ba
yace bazan hanaki hawayen nan ba dan bansan
dalilin
zubar su ba,
ki zubar da su san ranki in kin gama sai ki
saurareni,,
Afeeyah ta haďiye kukan hade da goge hawayenta
tace
nagama kaka,
kaka liman ya kalleta yace kin tabbata,,
ta gyaďa mishi kai tana ajiyar zuciya, yace to Allah
ya kara
miki hakuri ya kuma kara miki dangana, tace
Ameen,
kaka liman yace magana nakeso muyi dake, inaso
ki
saurareni kuma kiyi wa maganar kyakyawan duba
a
mizanin hankali, kina jina,?
tace eh inajinka,
yace madallah,
yau jumma'a dai2 kwana bakwai da mutuwar
jabeer ko ba
haka ba,
tace haka ne kaka,
yace gobe sati, satin da yaso zama ranar tarihi
mafi girma
a rayuwarku ke da jabeer,
sai kuma Allah mai kowa mai komai bai yarda ba
saboda
dama ya rubuto ke ba matarshi bace kuma shima
Allah ya
rubuto bazai taba yin aure a rayuwarshi ba zai
koma
gareshi,
Shin Allah baya sonku ne yayi muku haka,
ta girgiza kanta da sauri,
yace Allah shi kadai ya barwa kanshi sanin
boyayyen
alamarin dake tattare da rayuwarki shiyasa ya
ďauke jabeer
a lokacin da kike bukatarshi domin ki fuskanci
wata
rayuwar,
ki sani Afeeyah in har a rubuce a allon Allah gobe
ne ranar
da zakiyi aure to babu makawa sai an ďaurashi,
Allah sarki
jabeer, bayan iyayenshi da yanuwanshi baiso kowa
ba
kamar yadda yaso ku ke da Affan, shin a soyayyar
da
jabeer ya nuna miki zaki iya cika burinshi da ya
fara bai
karasa ba,
da sauri tace koda kuwa wahalarshi zaiyi
sanadiyyar raina
kaka,,
alhmdullh kaka yace a zuciyarshi sannan yace
bana fatan
yayi sanadiyyar ranki jikata, nasan zakiyi duk
abinda nace,
jabeer ya dauko aiki mai matukar hatsari kuma
Allah bai
bashi ikon karasawa ba, yanzu ni da ke zamu
karasa shi
amma banason ya zama hatsari a gareki,
Afeeyah dole ki fitar da kanki a sahun yara domin
ke ba
yarinya bace, dole ki zama mai jajircewa a cikin
wannan
kasadar da zamu sa kanmu,
da siyasa nakeso muci yakin nan domin yakin yafi
karfin
yinmu amma baifi karfin Allah ba,
Allah yasa zaki daure zuciyarki in kikaji jahadin da
zakiyi
domin masoyinki,
Afeeyah tace koma menene zanyi kaka in shaa
Allahu,, kaka
liman yayi murmushi cikin jin dadi yace Afeeyah
gobe in
Allah ya kaimu zaki bar gidanku ki koma gidan Alhj
basheer
da zama a matsayin matar ďansa,
mikewa Afeeyah tayi da sauri tana girgiza kanta
idonta ya
fara kawo ruwa tace kaka" Affan??, innalillahi wa
inna ilaihir
rajiun,
kaka liman yace nutsu Afeeyah ki nutsu ki zauna
muyi
magana domin babu abinda zai hana wannan
auren sai
Allah, kafin ki shigo dakin nan nayi istahara akan
lamarin
nan na gano abubuwa da yawa saboda haka ki
zauna mu
cika ma marigayi burinshi,
Afeeyah ta zauna tana kuka tace kaka har abada
bazan
taba iya auren wani ba, bazan iya ba,
na daukarwa kaina alkawarin bazan yi aure ba har
in koma
ga mahaliccina, nasa a raina ni zan zama uwar
gidan yaya
jabeer a aljanna,
kaka liman yayi dariya yace kuruci dangin hauka,
alkawarin
ki kenan, kika san alkawarin Allah akanki, bakisan
mijinki
ba, yawan ya'yanki da kuma adadin rayuwar zakiyi
kafin ki
koma gareshi,
dan haka ki kauda wannan maganar ki fuskanci
rayuwar
gaba, jabeer ya riga ya tafi bazai dawo ba dan
haka mu ida
aikin alkhairin da ya fara domin samar ma ruhinshi
salama,
nidai bazan faďa miki komai yanzu ba,
zanso ki zauna a gidan ki fara ganin komai dake
faruwa da
kanki hankalinki zai baki ki gane abinda nake nufi,
zan
dinga waiwayoki akai akai dan akwai yan
tambayoyi da zan
dinga miki domin mu dinga sanin matakin dauka ta
kasa2,
duk abinda kika gani karki nuna kin gani saboda
tsaro kin
gane ko,
Afeeyah da kuka yaci karfinta ta kasa magana sai
kallonshi
kawai takeyi yana mata jawabi kamar tace mishi
ta yarda
da maganar auren,
Kaka liman ya dade yana sako ma Afeeyah
magana cikin
magana dan bayaso ta fahimce shi ya jefa
rayuwarta cikin
hatsari,
yasan tana shiga babu dadewa tausayin Affan
zaisa tayi ko
me ya sata dan kubutarshi,,,
Da daddare bayan ta idar da isha'i ta hade kai da
gwiuwa
tana kuka sosai tana hango rayuwar da zatayi a
gidan su
Affan tare da su mummy masu kirar samudawa,
yaya zatayi ta iya zama da Affan a wannan halin
da take
ciki, bata tunanin zata iya taimakonshi domin
itama neman
wanda zai taimaketa ya tausheta takeyi,
babu irin rarrashin da hajja batayi mata ba akan ta
dauki
auren a matsayin kaddara, ita kanta hajja tsoro
abin yake
bata domin tasan jikarta zata shiga wata irin
rayuwa mai
cike da jarabawa,,
saida tayi kukan ta gaji dan kanta ta bingire da
baccin
wahala a takure gurin,,,
Karfe uku da kwata na dare hajja ta jiyo muryarta
cikin
bacci tana sambatu hawaye da zufa sun jika
fuskarta da
wuyanta,
a hankali ta matso kusa da ita ta kama hannunta
zata fara
mata magana taji ta matse hannun sosai tana
faďin
"bazan iya ba yaya jabeer, bazan iya ba,,, dan
Allah ka dawo
gareni, kasan a irin wahalar da kabar zuciyata, dan
Allah
karka kara tafiya ka barni, hajja ta fara cire
hannunta cikin
nata ta kara matsesu da karfi tana faďin "bazan
kara
barinka ka tafi ka barni ba,""
hajja ta share hawaye ta janyota jikinta tana
karanto addu'a
tana tofa mata a hankali, cikin ikon Allah tayi lamo
jikin
hajja tana ajiyar zuciya,,
hajja bata koma bacci ba saida ta tabbatar
Afeeyah ta
daidaita sannan ta kwantar da ita itama ta kwanta
tana
kallonta.... Washe gari karfe 10am aka ďaura auren "Afeeyah
da Affan"
banda Hajja, Abida da Asiyah babu wanda yasan
da
maganar auren, alhj basheer ba karamin farin ciki
yayi ba
dan ji yayi kamar ya goya malam Atiku dan murna,
godiya kuwa yayita har yana neman tsugunawa
saboda
acewarshi wanda zai dauki ya' kamar Afeeyah ya
bawa
mahaukaci ay ba karamin jihadi yayi ba,
kaka liman kuwa zan iya cewa yafi su murna dan a
ganinshi
ya jefi tsuntsu biyu da dutse ďaya, yasan in Affan
ya samu
sauki Afeeyah zatayi alfahari da kasancewarshi
mijinta dan
yasan babu yadda za'ayi Affan ya wulakanta
Afeeyah tunda
yasan muhimmacinta a rayuwar Jabeer,
Bayan an gama daura auren da adduoi suka danyi
ciye
ciyen da alhj basheer yayo ordr sai kowa ya wuce
gida cikin
farin ciki,,
A kofar gida alhj basheer ya hadu da masu
furnitures din
daya kira dan gyara side din Affan da rabonshi da
shiga
tunda ya fara ciwo,, , karasawa ciki sukayi ya nuna
musu
inda zasu gyara nan da nan suka fara aune aune
da gwaje2,
karan mashin din aikinsu oyizah ta jiyo ta fito da
sauri tana
fadin karan meye wannan,
tsayawa tayi tana kallonsu tace kaiiii daga ina
kuke?
Ganin alhj basheer tayi ya fito daga bayi da mai
gyaran bayi
suna magana tace alhj gyaran me akeyi haka,? ko
Affan zai
dawo nan da zama ne,
alhj basheer ya bawa mai gyaran bayin kudi
sannan ya
kalleta yace eh nan zai dawo, oyizah ta haďe rai
tace
saboda me, kasan fa bazai iya kwana shi kadai ba
shiyasa
na bashi daki daya a cikin nawa,
alhj basheer yayi murmushi yace nan din ma bashi
kaďai
zai dinga kwana ba, oyizah tace kamar yaya,?
Alhj basheer yace surprise nakeso in baki, naso sai
an
kawota sannan zaki ganta amma tunda kin dan
fara
dagowa bari in fada miki,
yanzu aka daura ma Affan aure,
oyizah cikinta ya ďuri ruwa tace aure alhj? Yace
kwarai
aure, zanso kiga farin cikin dake raina game da
wannan
auren safiya,
oyizah ta share gumin fuskarta tace da wa aka
daura mishi
auren, wayarshi ta fara ringing yayi saurin ce mata
da
Afeeyah yar gidan malam Atiku, ina zuwa bari muje
mu
dawo zanyi miki bayani ya fita da sauri saboda
wayar ta
sake kara alhj Bara'u ke jiranshi zasuje yi mata
siyayya tare
da Asiyah, ,,
tsaye yabar oyizah baki sake tana kallon masu
aikin gurin,
dakyar ta iya ďaga kafarta ta wuce parlor,
wani irin zama tayi akan kujera har saida kujerar
ta amsa,
da sauri farida ta mike a kujerar tace haba mummy
wannan
ay sai kisa muyi kasa, oyizah da idonta yayi jawur
tace
mukai kasan mana,
farida ta dawo kusa da ita tace mummy lafiya,
oyizah tace
hmmm aure aka ďaura a cikin gidannan,
farida cikin kidima tace daddy ne yayi aure,
oyizah tace gara min shi yayi aure dan nasan duk
wacce
zatazo baza tayi karko ba,
farida tace to waye yayi aure, dai2 lokacin Affan ya
wurgo
kwallo yana bugawa cikin farin ciki ta kalleshi tace
wancan
saunan aka daura ma aure,
fareeda ta kwashe da dariya tace ita kuwa wannan
wace
dakikiyar ce ta yarda ta aureshi,
mummy tayi tsaki tace mune dai dakikan da
tuntuni banyi
tunanin nemo mace sakarya na haďashi da ita ba,,
Farida tace ban gane ba mummy,
oyizah tace ay kwakwalwarki bazata gane ba
amma nasan
in na faďa miki amaryar zata gane, Ay
kwakwalwarki tasan
Afeeyah yar kishiyar suwaiba ko?, farida ta dafe
kirji tace
farin sani mummy ita ya aura,
tace aka daura mishi dai, ta kalli Affan taga ya
kara mata
nuri sajenshi ya kwanta luff" yayi matukar kyau
kamar
yasan yau zai angwance,
da karfi ta kira sunanshi ya taho da gudu ya zauna
kusa da
ita,
ta kalleshi tace u luk very happy my son,
ya kara gyara zamanshi cikin murna yace am
happy
mummy yau za'a kawomin Afeeyah,
ta kalleshi sosai tace waye ya faďa maka, yace ni
nace
daddy ya kawomin ita mu dinga wasa ba jiya nazo
zan fada
miki ki mata girki mai dadi ba kika koreni,
oyizah tayi saurin dafe kanta da ya sara mata tace
tashi ka
tafi,
ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya juyo
ya
tsuguno saitin kanta yace mummy zakiyi mata
girkin,
a hassale ta dago ta daka mishi tsawa tace
ubanka zan
girka mata, wuce ka bani guri,
Affan ya wuce cikin tsoro yana waigenta kamar
zaiyi kuka..
Farida ta dafata a hankali tace mummy meyasa
kike
damuwa naga Affan is under ur control dole itama
in ta
shigo ta zama a karkashinki, ni mummy kin bani
mamaki
wannan small girl din kike damuwa akanta, duka fa
bata
wuce 17 to 18,
oyizah tacee uhmm kawai ta mike tayi sama tana
tunanin
yadda zata fara bullo ma wannan alamarin...
A can gidan Malam Atiku kuwa tunda suwaiba ta
samu
labari take bala'i tana zaginshi, wai akan me za'a
boye mata
maganar auren saida aka daura za'a fada mata
dan anga
ba ita ta haifeta ba,
malam Atiku cikin fushi yace sannu uwata, wani
abun zaki
tsinana min in na fada miki, ko nairah dari bazaki
kawo kice
a siya mata cokali ba to niko saboda me zan faďa
miki,
aure ne an daura shi babu wanda ya isa ya
warwareshi, nan
fa suwaiba ta cigaba da bala'i tana aibata auren
harda kuka
saboda bakin ciki,
acewarta ita bata bakin ciki da auren musaki
amma can
cikin zuciyarta takaici ne dankare saboda tasan ko
Affan zai
dawwama cikin ciwon hauka Afeeyah ta gama
warkewa,
hangowa ta dinga yi da kausar ce da tuni yanzu
alhj
basheer ya fara jikata da kuďi,
daki ta koma bayan ta gama sababinta tana kukan
rashin
sa'arsu ita da diyarta,
malam Atiku ya fita ya barta, hajja kuwa ko
dekowa batayi
ba tana ďaki tana aikin rarrashi... Bayan isha'i Alhj basheer da kanshi yazo daukar
Afeeyah,
suna zaune da hajja da Asiyah suna rarrashinta
suna kuma
bata shawara akan ta kula da mijinta duk
haukarshi mijinta
ne kuma aljannarta na karkashin kafarshi,
Asiyah tace yanzu kin zama kamar uwa a gareshi
da
taimakonki komai nashi zai fara daidaita,
dole ki jajirce ki manta da ke yarinyace ki rike
darajarki da
ta mijinki kuma karki yarda wani ya raina shi a
gabanki,
Nasiha sosai sukayi mata har malam atiku ya
shigo shima
ya daura ya kuma yi mata tuni da riko da adduoi,
sannan ya
umurceta ta tashi suje ga alhj basheer can yana
jiranta,
mikewa tayi tana kuka Amirah ta miko mata sabon
hijab
dinta tasa Asiyah ta fesheta da turare ta riko
akwatinta suka
fito rakata,
dakin suwaiba ta shiga yi mata sallama ko
kallonta batayi
ba ta cigaba da cin tuwon gabanta tana yan wake
wakenta,
tashi sukayi suka fita basu ko kulata ba,
motar alhj basheer suka nufah suka sakata a baya
ta rike
hannun hajja sosai tana kuka tace saidai hajja ta
shigo su
tafi, dakyar malam atiku ya lallabata ta saki hajja
sannan
alhj basheer yayi sallama dasu suka wuce hajja na
kuka
tana ďaga musu hannu sai kace wacce zata bar
unguwar,,
Runtse idonta tayi da suka shigo harabar gidan
tana
karanto adduoi akan Allah ya taimaketa yayi mata
jagora a
cikin wannan sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a
ciki,
alhj basheer ya fito ya buďe mata kofa yace mun
iso diyata,
Allah yasanya alkhairi a farkon shigowarki
gidannan, ya
kuma dawwamar da farin ciki a cikin zaman
aurenku har
karshen rayuwarku,
a zuciyarta ta amsa sannan ta sako kafarta kasa
da
bismillah,
Zubur Affan ya mike daga kan kujera ya karaso
kofa yana
faďin daddy na ya dawo, yana buďe kofar ya
hangosu da
Afeeyah suna tahowa ya rugo da gudu yana cewa
oyoyo
barbie, chakk" ya ďagata cikin murna yana
jujjuyata ya
karaso cikin parlon da ita yana fadin mummy kizo
ga barbie
nah daddy ya kawo min,
wani irin kuka Afeeyah ta fashe da shi yayi saurin
sauketa
yana nunama daddy hannunshi yana faďin ba
ruwana
daddy wallhy bani na sata kuka ba,
alhj basheer yayi dariya yace kai ka sata kuka
nima babu
ruwana bari ma in tafi kar ace har dani,
Affan ya zaro idonshi zaiyi ma oyizah magana tayi
saurin
jifanshi da mugun kallon da yasa shi ďauke kanshi
ya ďago
fuskar Afeeyah kamar zaiyi kuka yace ay bani na
saki kuka
ba ko,?
Afeeyah tayi banza dashi ta cigaba da kukanta,
alhj basheer yace zo nan diyata ki zauna rabu da
shirmenshi,
Afeeyah taja kafarta a hankali ta zauna a kasa
kusa da alhj
basheer Affan ma ya biyota ya zauna kamar zaiyi
kuka,
alhj basheer yace share hawayenki ki bude idonki
ki gaisar
da mamanki da kuma yayyinki,
oyizah tayi saurin cewa ta mayar da idonta abinda
muna
tare kullum yanzu,
alhj basheer yayi murmurshi yace haka ne,
ya kalli Afeeyah yayi mata yar nasiha ya kuma
roketa da ta
kula da Affan ta rikeshi amana sannan yace suje
oyizah ta
nuna mata ďakinta,
oyizah ta mike tace ma Afeeyah ta tashi suje,
kafin Afeeyah ta mike Affan ya mike yace barbie
tashi muje
ďakinmu,
Afeeyah ta mike tabi bayan oyizah da ya"yanta
zuwa side
din Affan,
saida tayi addu'a sannan ta shiga ciki ba tare da
ta ďago
kanta ba,
oyizah ta kalli Affan da ke binta a baya tace to
bita zaizai
wuce ka tafi daki,
Affan ya bata fuska yace ay nan ne yanzu ďaki na,
Salma ta daka mishi gigitaciyar tsawar da tasa shi
fita da
gudu, dariya suka watse dashi suka dawo da
kallonsu kan
Afeeyah,
oyizah ta ďago kumburarriyar fuskarta tana mata
kallon
banza tace "so called Amarya,"
farida ta kwashe da dariya tace su amarya man
gyaďa,
salma ta hada rai tace kuna dariya ne, ay sai ta
samu
damar raina mu, mummy ki bata warning din da
zaki bata
mu wuce dan wallahi na mugun tsanar ganin
yarinyar nan,
oyizah tace me kike ci na baka na zuba,
ta kalli Afeeyah tace nasan dalilinki na auren Affan
bai wuce
saboda dukiya ba, to kin makaro yarinya saboda
ke da
Affan kunyi ma juna nisa kamar tsakanin gabas da
yamma
saboda Affan is under my control sai abin da nace
mishi,
Sannan kisa a ranki aikatau ne ya kawoki
gidannan ba
zaman aure ba,
salma tace gud mummy dama tunda "Gaje" mai
aikin
shegiyar mum din Affan ta tafi bamu kara samun
mai aiki
mai tsafta ba yanzu tunda mun samu wannan sai
muyi
manage,
oyizah kwarai kuwa, yanzu zan fara miki lissafin
daily
works din gidannan,
karfe 5 in kika tashi ba ruwana da sallarki in kinga
dama
kiyi in kinga dama ki barshi, fareeda tayi saurin
cewa
mummy wannan small gal din ma ay sallah bai
wajabta
akanta ba,
salma tace tell her ooo,
oyizah tace oho in taga zata wahalar da kanta tayi
to tayi
nidai amin aiki, girki shine first,
sai gyaran kitchen, gyaran ďakin yara, sai parlor,
tsakr gida da sauransu akwai maza masu yi,
Farida tace mummy wannan special secret flower
bed din
naki da nake bashi ruwa plss spare me ki kara
mata shi a
aikinta,
da sauri oyizah ta kai mata duka hade da yi mata
dakuwa,
farida ta toshe bakinta tace sorry mummy sannan
ta fita da
gudu,
oyizah ta gama lissafa wa Afeeyah duk aikin da
zatayi a
gidan hade da concrete warning na in ta saba aiki
ko daya
ne she will be in fr it,
Afeeyah dai gyada kanta kawai takeyi hawaye na
kwaranya
a idonta,
har sun sa kai zasu fita oyizah ta juyo tace lastly
babu
ruwanki da rayuwar Affan, ban yarda ku kebe tare
ba bare
har ki yaudareshi da wadannan shanyayun
idanuwan naki,
salma tace haba mummy wannan mahaukacin
meye zai
rude shi,
oyizah ta harareta tace shi dutse ne ba mutum ba,
mahaukata ma ay suna da feelings tunda akwai
zuciya a
kirjinsu, dan haka na horeki da kebewa dashi bare
har--- ta
yi saurin dafe kanta tace bana ma fata dan har
abada,,,
salma tace har abada me, oyizah ta jata suka fita
tace muje
ďaki in faďa miki..
Suna fita Afeeyah ta fashe da kuka tana kiran
sunan jabeer,
kuka sosai takeyi har saida jiri ya fara dibanta
sannan ta
zauna bakin gado, saida ta gama tunane
tunanenta sannan
ta mike a zuciyarta tace Allah yasa yawan aikin da
suka
bani ya kasheni in huta,
drawer dake dakin ta

Please Login or Register in order to submit comment