Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

boye muku kamar yadda Affan ya boye
ma su
daddy sai naji wayar "Badiyya Aliyu" tana gargadina akan in
rubuta muku komai har coma, da fullstop. kamar
yadda
"bingel" takeyi,
Da sauri na dauki wayata na shiga typo muku abin
da na gani mai ban mamaki,
cikin bacci naga Affan ya rike kanshi yana juyi anan
inda
yake kwance a kasa,
a hankali bakinshi ke motsi yana faďin umma,
Jabeer, daddy,
can kuma naga ya matse kanshi da karfi yana faďin
wayyo
ummana,
sun kasheta,
sun kasheta, sun kashetaaaaaaaa....
ya faďi da karfi hade da mikewa zaune zufa duk ta
jika
mishi jikin shi,
waige2 ya fara yi a rude yana fadin ina ne nan,
waya kawoni nan,, ya maza ya mike ya buďe kofar dakin
a firgice
ya farayin hanyar dakin zeenatu,
ihu ya jiyo a side dinshi yayi saurin daukar hanyar
gurin,
yana zuwa kofar dakin yaji oyizah na faďin "kamar yadda
na kawar da zeenatu da jabeer" kema haka zan
kawar dake,
lekawa yayi dan ganin ko dawa take,
a gigice ya ja baya saboda ganin Afeeyah da yayi
bakinta duk jini,
a ruďe yace yaushe jabeer ya mutu, me Afeeyah
takeyi a
nan gidan, yanzu ummanshi ta mutu kenan,
tambayoyin da ya dinga ma kanshi kenan idonshi
na ambaliyar hawaye,
da sauri yaja baya ya boye ya shiga dawo da
abubuwan da
suka faru dashi shekaru uku da suka wuce,
babu abinda idonshi ke hangowa sai lokacin da ya
tarar da kartin maza su biyu sun bankare mahaifiyarshi
suna shirin
shaketa da farin kyalle gabansu cike da
kayayyakin tsafi
mummy kuma tazo da wuka tana kokarin dab'a
mata a wuya,, ,
shi dai yasan tun daga lokacin bai kara sanin inda
hankalinshi yake ba sai yau da ya farka ya kuma
tarar da
wani tashin hankalin,
me jabeer yayi mata ta kasheshi, wani irin kuka ya kufce mishi mai ban tausayi ya
mike da
niyyar komawa dakinshi ya ceci Afeeyah daga
kaidin oyizah,
har yakai kofar ďakin ya hango oyizah da wata a
bakin kofar,
da sauri ya juya yayi hanyar dakin da ya farka ya
ganshi a
ciki ko zai samu makamin da zai iya yakar ta dashi,
yana shiga dakin yaji karar waya, da kamar bazai
dauka ba, sai kuma yayi saurin dauka,
ba"a bari yayi magana ba daga daya bangaren,
murya yaji
ta tsofaffi cikin rudewa tana cewa ina fatan kina
nan lafiya
Afeeyah, nayi wani mummunan mafarki akanki,
ki tabbatar kin mike kinyi sallah dan komai na iya
faruwa
cikin daren nan,
a hankali Affan yace waye ke magana, daga daya
bangaren kaka liman yace kai din waye,
Affan yace nine Affan, kai fa,
cikin mamaki kaka liman yace Affan nine, kaka
liman ne na
daura,
Affan ya fashe da kuka yace kaka kana ina aka kashe min
jabeer, me jabeer yayi kuka bari aka kasheshi,
kaka liman yayi kabbara da karfi yace Affan ka
dawo cikin
hayyacinka,
Allah mai iko, ka daina kuka wannan maganar ba ta waya bace
yanzu ina
matarka,
a gigice Affan yace wacece matata kaka,
kaka liman yace Afeeyah itace matarka wacce take
dauke da cikinka,!
wacce ta yarda ta aureka cikin larura domin ta
kubutar
dakai daga cikin masifar da kake ciki,!
wacce ta fara zame ma matsalarka ciwon ido,!
nan ya takaita mishi duk yadda akayi ya auri Afeeyah da
kuma irin taimkon da tayi mishi,
zaman dirshan Affan yayi yana kuka sosai yace
kaka babu
mamaki itama bazata rayu ba don gata can sun
ritsata a daki zasu kasheta,
innalilliahi W.I.I.R kadai kaka liman ke iya fada yana
sauraren kukan da Affan keyi,
a hankali yace ka kwantar hankalinki Allah zai
kareta ko don
Rabon dake jikinta, karar da tayi ne yasa shi saurin kashe wayar ya
mike zai
fito yaji mahaifinshi ma ya fito, jingina yayi da
bango yana
zubar da hawaye har suka fita da ita suka sata cikin
mota, kara kira kaka liman yayi Affan ya dauka yace ta
kasheta
kaka, gashi can sun tafi kaita asibiti da daddy,
da sauri kaka liman yace bata mutu ba,
na fada maka bazata mutu ba sai wannan rabon ya
taka duniya, kayi saurin bin su karka sake ka barta ita
da
wannan matar dan zata iya yi mata illah, kuma
karka nuna
ma kowa kaji sauki domin yin hakan kamar ka
bata goma ne daya bata gyaru ba,
da sauri Affan ya fita, musababbin binsu asibitin
kenan,
ajiyar zuciya nayi dana gama tariyowa sai kuma
nayi gaba
har zuwa inda na tsaya muku wato inda Affan ke kuka yana
fadin sai ya dau fansa....
Allah ya baka ikon karasa yakin nan Affan domin
wannan
kawar Bilki Nabayin Hatsabibiyace....

*******RABO AJALI********
*******60 to 63********
.
By Sulaiman Bomboy.
.
Tafe take cikin motarta tana neman tsohon almajirin
da
zata bashi sadaka ta saceshi ta kaima chummy suyi
bandaro da jininshi domin ta samu sa'ar kashe
Afeeyah,,
tana karya kwanar Gyaďi2 ta ga wani tsohon almajiri tukuf
da kwaryar bara a hannunshi,
parking tayi ta sakko ta dunkule dubu biyu hade da
farin
kyalle ta bashi,
godiya ya dinga mata sannan ya juya mata baya, nan take
ya bace ma ganinta,
cikin murna ta shige mota dan duk tunaninta
hakanta ne ya
cimma ruwa,
da murnarta ta koma gida ta wuce dakinta ta rage kayan
jikinta, muryar Alhj basheer taji yana kwala mata
kirah da
karfi,
da sauri ta fito dan jin abinda ya faru, kauda kanshi
yayi dan a yan kwanakin nan sam baya kaunar ganin
fuskarta wani
lokaci ma tambayar kanshi yakeyi daliilin da yasa ya
aureta,
mutunta ta kawai yakeyi saboda darajar aure da
kuma yarshi, badan haka ba da tuni yayi ma kanshi
katanga da
ita,
kallonshi tayi tace alhj ka kirani kuma kayi shuru,
yace eh baki zanyi daga cameroon zuwa anjima,
ina son ayi musu girki, ta bata rai dan ta tsani wani dan
uwan alhj basheer ya rabeshi tace to naji sannan ta
wuce
daki tace wallhy taliya zan kwaba ma tsinannun..
Har bayan magriba baki ba su zo ba sai da akayi
isha'i sannan motarsu tayi parking a kofar gidan Alhaji
Basheer
Balarabe (BB), su hudu ne suka fara shigowa, mata
biyu
maza biyu,
a parlon suka zauna alhj basheer ya tsuguna ya gaisar da
baffa da dayan bakon cikin girmamawa, sannan ya
kalli
matan suka gaisa ya kure daya daga cikinsu da ido
yace
kamar nasanki, tayi dariya zatayi magana oyizah ta fito tana ya tsina,
dakyar ta gaida baffa shima dakyar ya amsa dan kar
ace
bai amsa ba,
sannan tabi matan da kallon raini tace sann---
muryarta ta sarke saboda ganin Gaje da tayi,
cikin mamaki tace gaje,
gaje ta dago tace na'am,
oyizah tace long time ina kika shiga haka tsawon
shekaru
uku babu ko zuwa duba mu, Gaje tace walhy kuwa aure nayi shiyasa, oyizah ta
tabe baki
tace na miki murna,
bari a kawo muku abinci,
Baffa ya kalli alhj basheer yace labarin zeenatu har
yanzu shuru ko?
Alhj basheer yace wallhy kuwa baffa, amma mun
baza
addu'a ana nan anayi kuma muna sa ran in shaa
Allahu
zata bayyana, oyizah tayi murmushi a zuciyarta sannan a fili tace
alhj in ta
mutu fa,
shekara uku mutum ya bace har yanzu babu labari
ay ni ina
ganin ta mutu, Baffa ya galla mata harara yace bashiru ina ganin
Allah ya
amsa addu'armu dan kuwa na samu labarin inda
zeenatu
take,
saboda firgici oyizah saida ta kusa karya kujerar da take
kai, zaro ido tayi tace kana da labarinta,
Baffa ya kalli cikin idonta yace kwarai kuwa inada
labarinta
mai karfi ko kuma ince ina tare da ita ma,
alhj basheer ya dafa kafar Baffa cikin rawar murya yace
tana ina Baffa,
kafin baffa yayi magana an murďa kofar palourn an
shigo,
da sauri alhj basheer da oyizah suka daga idonsu ya
sauka kan zeenatu da tayi wata irin muguwar rama,
da sauri ya mike yana fadin z-e-e-natu, Abida da
yadikko
dake rike da ita suka nemi guri suka zauna, gabanta
ya
karaso ya kamo hannunta saboda ya gasgata ita din ce,
murmushi Abida tayi tace ita ce alhj zeenatun ka ce
matarka kuma uwar danka,
Allah yayi zaku kuma ganawa,
alhj basheer ya tsuguna a gabanta idonshi ya ciko
da kwalla yace ina kika shiga zeenatu,
idonta ya ciko da kwalla ta kalli gurin da oyizah ta
sankare
a tsaye tace na shiga cikin ukubar da bawa baya iya
fitar
da danuwansa bawa saidai Allah ya fitar dashi, an so kasheni amma da yake shan ruwana bai kare
ba sai
gashi Allah ya dawo dani bayan mutuwar danayi ta
dan
lokaci,
mikewa tayi a hankali kamar zata fadi saboda rama, ta
karasa kusa da oyizah tace ribar me kikaci a wannan
izayar
da kikayi mana,
me kika samu mai amfani bayan tafiyarmu,
meyasa zuciyarki ta zabi ta dinga kisan kai akan abun
duniya da zaki tafi ki barshi a duniyar,
meye ribarki dan na mutu ni da ďana ke kuma kina
rayuwa
keda yayanki,
ki sani safiya Allah na kare wanda yaso a lokacin da yaso,
kin---- oyizah tayi saurin katseta cikin tsawa tace
duk
wadannan maganganun na menene,
ina ruwana dake da zan kasheki, me kikayi min,
ta fara kukan munafurci ta matso kusa da alhj basheer tace
sharri zatayi min dan kawai ta shiga duniya ta kwaso
cutar
kanjamau shine zata ce ni nayi niyyar kasheta,
alhj inda zan kasheta da Affan shekararshi nawa ina
kula dashi ban kasheshi ba,
ba'ayi min godiyar kula dashi ba sai dai a bini da
sakayyar
sharri,
kan alhj basheer ya ďaure sosai yace wai meke
faruwa ne, zeenatu zata fara magana
"Affan ya fito yace ni zan faďa maka duk abinda ke
faruwa
daddy"
cikin mamaki suka mai da kallonsu kan Affan,
karasowa yayi ya rungume zeenatu yana faďin baki mutu
ba umma,
ta dago fuskarshi tana shafawa tace kaima baka
mutu ba,
ashe kana nan da ranka Affan,
kuka sosai suka dinga yi na tsawon mintuna, alhj basheer ya janyo Affan cikin mamaki yana shafa
kanshi yace kaji sauki ne Affan,
Affan ya gyaďa kanshi yace na dawo cikin hayyacina
daddy,
Allah ya kwatoni daga hannun wannan azzalumar
da take kiran kanta matarka,
farida da shigowarta parlon kenan ta karaso da
sauri ta
buge hannun Affan tace karka kara zagar min
mahaifiya,
Affan yayi mata wani irin kallo yace kice kar in kara zagar
miki matsafiyya ba mahaifiyya ba,
oyizah ta sa kuka tace alhj kanajin sharrin da danka
yake
min, ko da yake bazan ga laifinshi ba dan nasan
mahaukaci ne shi baya cikin hayyacinshi,
alhj basheer dai kanshi ya ďaure yace dan Allah
karku
rikirkitani, ku fada min abinda ke faruwa,
Baffa ya kalli Affan yace zauna Affan bari mu fara jin
komai daga bakin mahaifiyarka
sai muji naka.
A hankali zeenatu ta fara jawabinta kamar haka...
Ranar asabar bayan sallar isha'i ina zaune a daki sai
naji
kamar ana ihu acan sama gurin shan iska,
da sauri na mike na isa gurin dan duk tunanina
Affan ne a gurin shi da jabeer dan mun rabu dashi zaije gurin
jabeer,
ina isa gurin naga wasu kartin maza zaune kan wani
jan
kyalle da wani jan kaya a jikinsu,
juyawa nayi da sauri zan koma daki saboda sun matukar
bani tsoro,
ina juyowa naga safiya cikin jajayen kayan itama
tana
dariya,
da sauri naja baya ina ambaton sunanta sai naji saukar
sanda a tsakiyar kaina,
dishi2 na fara gani ina salati ina neman dauki gurin
Allah,
cikin karaji naji muryar safiya tana fadin kunji ko
addu'a takeyi na faďa muku wannan sai kunyi da gaske
saboda
nasha yin aiki akanta yana lalacewa,
jin haka yasani sake bude wani shafin na addu'a, sai
naji
sun ďaga ni, daya ya bankareni yana faďin zo ka shake
mata wuya muga ta inda addu'ar zata fito,
da sauri ya matso ya matsemin wuya inata kakari na
hango
wata katuwar wuka a hannun safiya tana faďin
wannan gara kawai mu kasheta sai mu kaita asha jininta,
tana
kokarin daura wukar a wuyana muka ji ihun Affan,
da sauri ta yar da wukar su kuma suka sakeni na
faďa kan
wani farin kyalle, daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba saida
na ganni
gaban wata mata wacce halittarta kaďai ta isa ta
tsoratar
da mai rai,
ajiyeni tayi a wani daki tana faďin yau dake zamuyi dinner,
tana fita naga wasu yara su biyu sun shigo dasauri
suka
tanbayeni wa ya kawo ni nan,
cikin rawar murya na ce musu kishiyata ce,
daya daga cikinsu tace nasan oyee ce dan bata da mutunci
tunda ta kawo uwarta kowa ma zata kawo,
dayar tace har wani karamin yaro ma ta kawo
lokacin da
take neman cikin ďa namiji,
cikin sauri suka ce in tashi zasu fitar dani, da sauri na mike
ina tambayarsu su bazasu tafi ba,
amsar da suka bani tasani zubar musu da hawaye
sukace
sunfi shekara ashirin a haka, yanzu gangar jikinsu
ya riga ya zama kasa,
wani hanya suka nuna min nayi saurin bi na dawo
jikina,
dakyar na iya mikewa ina kallon sanda suka dauki
Affan
zasu jefoshi daga sama su karasa shi dan kar ya tona musu
asiri,
da sauri na fito dan kar su ganni na sakko kasa ina
bin
bango ina neman wanda zaizo ya taimaki ďana dan
karsu kasheshi,
a kofar kitchen na hadu da Gaje ta dawo daukar
sakon da
safiya ta aiketa dashi,
da sauri ta rikeni tana tambayata,
dakyar na iya takaita mata, na kuma ce dan Allah ta dauko
min Aff--- ban karasa faďi ba naji karar saukar
mutum kasa
da karfi, tun daga lokacin ban kara sanin inda kaina
yake
ba sai kwana biyar da suka wuce,, ta karasa tana kuka mai tsuma zuciya,,
Ajiyar zuciya Gaje tayi tace kwarai abun da ya faru
kenan
dan tana faďuwa nayi saurin janta store saboda jin
muryar
madam da nayi ta sakko nemanta, munfi minti talatin a store sannan na daukota na fito
da ita
da sauri dan kar wani ya ganni,
ina fitowa naga wani me keke napep a kofar gidan
alhj
bara'u, dasauri na karasa nasata nace ya kaini dorayi gidan
kawu na,
bai tsaya musun kudi ba saboda ganin halin da
muke ciki,
tafiya sosai mukayi har muka iso nace ya jirani,
ďakin matar kawuna na kaita nace dan Allah su kular min da
ita kafin gobe da safe,
ba musu tace ba komai saboda sunsan irin alherin
da hajiya
ke musu,
sai kusan goma na koma gidan, ranar a tsorace na kwana,, washe gari ina tashi na
tattara
kaya na nayi ma madam karya nace mata mahaifina
bashi
da lafiya acan nijar,
kudi ta bani tace Allah ya bashi lafiya tare da jaddada min in
dawo da zarar ya samu sauki,
amsata kawai nayi na fita daga gidan na wuce
ďorayi,
a ranar muka wuce nijar ni da hajiya dan nasan acan
ne zata fi samun kulawa saboda kawuna malamine,
babu irin addu'ar da ba'ayi ba amma sam babu sauki
dan
ko motsi batayi,
A can na barta na dawo jigawa ina wani aikin, har
Allah ya hadani da wani mukayi aure,
yau kwanana biyar da zuwa gida na tarar ta farfado,
shekaran jiya ne ta matsa ita akaita can gidansu a
cameroon,
bamu so mu kaita ba har saita kara samun sauki
amma malam yace lallai mu kaita saboda ta samu nutsuwa,
a can cameroon da muka je ta labarta ma mahaifinta
komai
shine yace a shirya a taho nan kano domin a fayyace
komai
dan kar aja lokaci a kuma kullo wani mugun abun da zai fi
na da..
Cikin tashin hankali oyizah tayi kukan kurah ta
shako
wuyan zeenatu tana fadin ni zakuyi ma sharri
wallahy yau sai na kasheki,
da sauri Affan ya taso ya banbare mahaifiyarshi a
jikin
oyizah ya shiga dukanta yana haki yana fadin duk
abubuwan da tayi mishi da kuma wanda tayi ma
Afeeyah da kuma kisan da tayi ma jabeer,
shaketa yayi idonshi yayi jawur cikin ďaga murya
yace me
jabeer yayi miki kika kasheshi,
kakarin wuya oyizah keyi idonta sun firfito waje tana
girgiza kanta,
babu wanda yayi yunkurin hana Affan har farida da
kuka
yaci karfinta saboda jin mugun alkaba'in da
mahaifiyarta
tayi, zeenatu ce ta taso da sauri ta fara banbareshi a
jikinta
saboda kar yayi kisan kai,
dakyar ya rabu da ita yana haki idonshi cike da
kwalla,
mikewa oyizah tayi ta ruga dakinta da gudu tana haki
kamar zata mutu,
tana shiga ta bankade katifarta da katakon, tana
dagawa
taga babu komai cikin ramin sai kasa,
da sauri tasa hannu tana tone kasar ciki kamar mahaukaciya tana fadin ina kuke, waye ya kwashe
ku,
wayyo Allah na shiga uku na lalace,
buga kofar ďakin taji anayi da karfi kamar za'a
ballata,
a hankali ta leka ta windon don ganin ko waye, yansanda ta gani tsaye su kusan shida da mace
daya,
dariya ta saki wacce da gani kasan ta takaici ce ta
jawo
jakar kayan tsafinta nan da nan ta bace daga
ďakin....Yan sandan sunfi minti goma a tsaye suna bugawa
ba'a
buďe ba,
cikin sanyin jiki alhj basheer ya taso ya dauko wani
key
yasa ya bude, wayam suka gani ba oyizah ba sawunta sai katon
ramin
karkashin gadonta ne yayi musu sallama a
idanuwansu,
alhj basheer idonshi ya kara ja yace jikina ya bani
zata gudu dan shaidancinta bazai kare anan gurin ba,
da kun bar Affan ya kasheta mun huta dan yanzu
wallahi
bazata kyalemu ba,
malam maina ya taso yace ka kwantar da hankalinka
in shaa Allahu babu abinda zai faru,
zamu toshe duk wata kafar da zata samu shigowa
rayuwarku da addu'a,
alhj basheer ya sharce gumin goshinshi yace to Allah
yasa,
Ameen duk mutanen gurin suka ce, Alhj basheer ya kalli Affan ya dawo kusa dashi yace
Affan
dama duk abinda kakeyi kana sane,
Affan ya girgiza kanshi yace ranar da mummy tayi
niyyar
kashe Afeeyah ranar na dawo hayyacina da taimakon Allah
da taimakon Afeeyah,
nan ya kwashe duk labarin da kaka liman ya bashi
na irin
kokarin da Afeeyah tayi akansu ya fada musu
sannan ya kuma faďa musu dalilin da yasa mummy ta kashe
jabeer,,
ya share hawayen fuskarshi yace daddy dalilin da
yasa
kaga naki tafiya in bar Afeeyah a asibiti kenan
saboda nasan muna barin gurin zata karasa ta,
doctr musah ma yasan na samu sauki saboda washe
gari
da mummy ta matsa sai mun tafi naje na sameshi na
fada
mishi komai nace ya taimakeni ya dauketa yace su zasu
dinga jinyarta,
da kyar ya yarda dan a tunaninshi ban samu sauki
ba
shirme nake mishi,
muna tafiya yace min yaje dakin dan ya gasgata maganata
sai ya tarar ta cire pillow tana kokarin kashe ta,
hankalinshi ya tashi a lokacin sai ya tabbatar naji
sauki
shine ya shirya plan din za'a kaita dakin hutu,
alhj basheer ya jinjina kanshi hawaye na fita a idonshi yana
faďin ku yafe min, duk ni na jawo muku da na shigo
da
safiyya cikin iyalina,
gashi bata tsaya kai na ba har saida ta taba ya'yan
makota na, dan Allah kuyi min afuwa ku dau duk wani
hukuncin da
ya dace a kaina,
zeenatu tace ka daina kuka alhj ba laifinka bane
RABO ne
ya shigo da ita rayuwarka, Rabon salma da Farida zai iya
AJALIN duk wanda ya hana wannan auren a
lokacin,
cikin kuka alhj basheer yace tabbas ya ko yi ajalin
mahaifiyarta dan taki amincewa da zancen,
ashe safiyar ce ma ta kasheta da hannunta, Affan yace har Anty salma itace silar mutuwarta dan
jiya da
mukayi waya da kaka duk ya faďa min hatsaririkan
da
Afeeyah ta tsallake a gidan nan,
mamakin alamarin kowa ya dinga yi haďe da ganin jarumta
da jajurcewar Afeeyah,
Abida dai banda kuka babu abinda takeyi dan
mutuwar
jabeer ta dawo mata sabuwa fill a yau,
tabbas da an barta ita da hannunta zata kasheta ta huce
takaicin rabata da nagartaccen ďanta mai cike da
Haiba da
tayi..,
Cikin kuka fareeda ta matso kusa da Affan tace dan
Allah Affan ka yafe min abin da nayi maka wallahy sharrin
shaidan ne da kuma ganin mummy nayi,
Affan ya janye kafarshi ya galla mata harara,
cikin tsawa alhj basheer yace tashi ki bamu guri yau
dinnan
zaki bi uwarki dan ban sani ba ko ke din ma ta tsafin ce,
fareeda ta rushe da kuka tana bashi hakuri, a
hankali
zeenatu tace alhj laifin wani baya shafar wani,
duk wanda yaga farida yaga jininka dan haka
hannunka bazai rube ba ka yanke ka yar ba,
alhj basheer yayi saurin cewa saidai kuwa in bai
isheni da
wari ba,
yanzu ke kina so in zauna da jinsin matsafa a gida,
Baffa yace bashiru hakuri zakayi ya' dai taka ce dan haka
dole ka riketa ku koya mata tarbiyar da addini ya
koyar
kuma ku aurar da ita,
nan suka cigaba tattauna maganar cikin tsananin
al'ajabi.... Cikin tashin hankali oyizah ta bayyana a gurin
tsafinsu,
kuka sosai takeyi a gaban chummy tana faďa mata
duk
yadda akayi har dawowar zeenatu da samun saukin
Affan, chummy ta kalli oyizah cikin mamaki tace ya akayi
haka ta
faru,
oyizah tace nima ban sani ba, komai na kayan aikina
an
kwasheshi a karkashin gado babu komai a gurin sai kasa,
sai kuma kwalbar nan da yan iskan yarannan suka
fasa
nasan shiyasa zeenatu ta farfaďo,
chummy tace na sakeyin wacce tafi tada karfi kin
ganta can,
oyizah cikin mamaki tace to ya akayi haka,
chummy tace ni nafi mamakin na dakinki da wanda
kika
birne a bakin damo,
oyizah tayi saurin ďago kanta tace nasan wanda zaiyi min
wannan aikin,
wannan yar iskar yarinyar ce zatayi min, wallahi I will
not
spare her,
yanzun nan zanje asibitin da take in kasheta, chummy tayi murmushi tace daďina dake garaje,
bakya tunani kafin kiyi abu,
waye ya faďa miki suma yanzu zasu zauna,
, ai sun riga sun san sirrinmu so sai munyi da gaske
ta
karkashin kasa musa ki koma gidanki sai ki aiwatar da
ayyukanki cikin kwanciyar hankali,
oyizah ta gyada kanta tace wallhi wannan karan mai
zafin
zanyi duk saina kashesu in mallake alhj da
dukiyarshi muyi zaman mu tare har karshen rayuwarmu,,,
chummy tace yauwa ashe kin gane,
yau da daddare zamu fara aikin, kinsan akwai ďan
tsoho da
kika kawo to dashi za'ayi miki aikin, yanzu tashi
muje gurin Dodo BELAH mu dawo kafin lokacin meeting yayi,
oyizah ta mike zuciyarta wasai dan a tunaninta
komai nata
zai koma normal tunda CHUMMY tayi assuring dinta,,,
oyizah sarkin sa'a........
Kwance take kan kirjinshi ta cukwikwiyeshi tana
kuka mai
ban tausayi tana faďin
"meyasa ka tafi ka barni na tsawon lokaci, meyasa
baka
daukeni mun tafi tare ba ka barni cikin wannan wahalalliyar
duniyar mai cike da azzalumai marasa tsoron Allah,
ta tsunguna a kasa kukanta ya tsananta tace dan
Allah yaya
jabeer karka sake tafiya ka barni,
ba karamin wahala nake sha ba saboda rashinka, I grew up in your arms plss led me die in it, plsssss,
ďagota yayi suna kallon cikin idon juna taga wani
haske mai
matukar kyau a cikin kwayar idonshi,
a hankali taji yana faďin tafiyata bazata taba zama
wahala agareki ba,
naso kasancewa tare dake amma Allahn da ya
hallicemu
bai halicceki dan ni ba shiyasa ya ďaukeni domin ki
kusanta
da wanda yake makusanci na hakika a gareki, dama ni ba mazauni bane zuwa nayi in nuna
kamannina in
koma ga ubangijin talikai,
tabbas nasan lokacin da nake da rai baki da wata
matsalar
rayuwa, yanzu kuwa nasan ko baki gama sanin meye
rayuwa ba kinsan kadan daga ciki,
mu'imuni ako da yaushe Allah na jarabtarshi ta
kowane
bangare, duk wanda ya kansance cikin farin ciki a
kullum to tabbas ya binciki kanshi domin duniya kurkukun
mu'imuni
ce sannan aljannar kafiri,
kafiri marar tsoron Allah, ko wanda ke sabawa Allah
shi
kaďai ne ke samun farin ciki marar yankewa a duniya,
akwai lokacin da zamu shiga farin ciki amma cikin
lokaci
kalilan sai bakin ciki ya maye gurbin wannan farin
cikin,
to ki sani duk musulmin dake yawan shiga cikin jarabawar
Allah lallai ba karamar soyayya bace tsakanin
wannan
bawan da Allahn shi, domin shiga kunci ga musulmi
kankarar zunubi ne,
wasu kuma zaki ga basu da wata damuwa komin zunuban
da sukeyi ba shi zai hana Allah ya barsu cikin farin
ciki ba,
sannan kome suka nema suna samunshi kamar su
suka
tsara rayuwarsu, to wadannan Allah ya barsu da kansu ne
har sai sun tuba,
kullum mu'imunin kwarai yana cikin jarabawar
ubangiji
masu tsananin rabo su ke cinye jarabawar dari bisa
ďari, ya share mata hawayen idonta yace zanso Afeeyata
ta
zama daga cikin masu cinye jarabawar ubangiji a
koda
yaushe,
zanso ki daina yawan zubar min da hawaye domin hawayen basu kara komai sai wahalarwa ga
kyakyawan
idanuwanki,
zanso ki manta batun soyayyata a matsayin wanda
zai
aureki ki sanya soyayyar yaya a zuciyarki domin samun
tsaftattaciyar addu'a daga gareki,
ki kular min da Affan kamar yadda zaki kula dani
domin ni
da shi bamu da wata maraba kuma nasan zai kula
dake kuma ya kaunace fiye da yadda ni nayi, ki yawaita
istigfari
domin istigfari yana kusanta bawa da ubangijinshi
kuma
mai yawan yinshi zai kasance kullum cikin nutsuwa
da walwala,
cikin sheshshekar kuka Afeeyah ta buďe baki zatayi
magana jabeer ya sa hannu ya rufe bakin yace karki
ce min
komai ga Affan can yana jiranki zaku tafi gida,
nagode sosai da ziyara,
cikin kuka ta cire hannunshi a bakinta tace dan Allah
yaya
jabeer ka tsaya kaji abinda zan faďa maka,
girgiza kanshi yayi yana mata murmushi hasken
hakoranshi suka rufe idonta ta durkushe a gurin tana kallonshi
cikin
hasken tana kuka sosai tana kiran sunanshi,
wata sassanyar iska ta shiga kaďawa a gurin har
hasken
jabeer ya bace ma ganinta, runtse idonta tayi tana kuka sosai tana faďin dan
Allah
karka tafi ka barni,
Hannu taji cikin nata ana murzawa a hankali sannan
taji
saukar ruwa a kan hannun, a hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi
sosai ta
saukesu kan Affan dake zaune kusa da ita kanshi a
kan
hannunta yana zubar da hawaye,
lumshe idonta tayi hawaye na zuba ta gefensu ta fara tuno
mafarkin da tayi akan jabeer,
meyasa ya tafi bai tsaya yaji abinda zance mishi ba,
meyasa be bari nasan abinda zan faďa mishi ba,
shikenan bazan kara ganinshi ba har in koma ga
Allah, to ni yaushe zan mutu, wayyo Ya Allah ka dauk----
Affan
yayi saurin toshe mata baki da hannunshi yasa
hannu yana
share mata hawayen dake gangarowa daga cikin
idonta, buďe idonta tayi ta kalleshi tasa hannu ta ďan ture
hannunshi cikin muryar kuka tace kukan me kakeyi,
da mamakinta sai taji ya kwanto jikinta yace kukan
abin da
kikeyi,
a hankali tace ai bakasan kukan da nakeyi ba, ya ďago jajayen idanuwanshi yace nasan har duniya
ta
naďe bazaki taba yin kukan komai ba in ba na
rashin jabeer
ba,
cikin mamaki ta kureshi da ido hawaye ya kara zirarowa a
cikinsu cikin rawar murya tace kasa--- ya fashe da
kuka
yace nasani Afeeyah, nasani,
nasan jabeer ya tafi ya barni,
nasan bazan sake ganin fuskarshi mai dauke da murmushi
a kullum ba,,
nasan bazamu sake haďuwa mu rungume juna mu
faďa
ma juna damuwarmu ba,
bansan me yasa mutuwa ta zabi jabeer ta barni, bansani ba
Afeeyah,
ya karasa fadi yana kuka kamar karamin yaro,,
kuka suka dinga yi babu mai rarrashin wani a
cikinsu,
saida sukayi mai isarsu sannan Affan ya ďago ya kalleta
murya a dashe yace nagode, nagode da abin da
kikayi min,
kau da kanta tayi tace ka gode ma Allah da kaka
liman,
ya juyo da fuskarta yana kallon rinannun idanuwanta yace
kullum cikin gode musu nake,
godiyarki ta daban ce Afeeyah, babu wanda zai
dauki
kasadar da kika ďauka a duniyar mu ta yanzu,
kinyi mana abin da ko dan uwa na jini bazai iya yi mana shi
ba, bamu da wata kalmar da zamuyi amfani da ita
gurin
gode miki, Afeeyah tace karka gode min na cika
kudirin
jabeer ne, wannan shine burinshi na karshe, saboda wannan kudirin aka kashe min shi,,,
Affan yace nasan komai Afeeyah kuma in shaa
Allahu
wacce ta kasheshi ba anan duniya ba ma har a
lahirah
bazata taba samun kwanciyar hankali ba, Afeeyah tace tun a duniya nakeson Allah ya
wulakanta min
ita, wallhi da nasan ita ce silar mutuwarshi na rantse
da
bazan kyaleta ba da nayi mata abun da zata
gwammaci mutuwa da rayuwa,
Affan ya share mata hawaye yace ki kwantar da
hankalinki
nasan yanzu duk inda take a

Please Login or Register in order to submit comment