Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wace irin magana kikeyi,
tace ni nasan duk ranar da ka mutu to nima zan mutu,
yace to ke waye yace miki zan mutu, tace ba kowa ina dai
fada maka ne,
yayi dariya sosai yace to naji,
ta marairaice tace dan Allah yaya jabeer karka mutu kabarni
kai kadai nake dashi a duk duniyar nan,
kai kadai kake understanding dina, kuma kai kadai kake
tolerating dina, kai kake sani dariya kuma ka hanani kuka,
dan Allah ka dinga yi mana adduar in mutuwa tazo ta
daukemu lokaci ďaya kaji,
yayi murmushi ya share kwallar da ta zubo daga idonta a
zuciyarshi yace yaro yaro ne, ya kalleta yace naji amma ki
daina kawo mana maganar mutuwa ke da zaki zama
amaryata ranar Saturday,
kar in kara ganin hawayen nan kinji, tace too,
yace yauwa babynah, kin san meye, ta girgiza kai tace a'a,
yace banaso in faďa miki sai kin min alkawari,
tace alkawarin me, yace alkawarin bazaki yi kuka ba, kuma
bazaki damu ba, kuma zaki min addu'a,
tace umm nayi alkawari Allah ya bani ikon cikawa,
yace ameen baby,
ina zanje daura gobe amma fa gobe zan dawo in shaa
Allah,
Afeeyah ta karkatar da kanta gefe tace ni um umm wayau
kamin wallahi na kwance alkawarin,
yayi dariya sosai yace ba'a kwance alkawari yarinya, dan
Allah kimin hakuri gobe kawai akwai abinda zanyi mai
muhimmaci, kuka ta fara yi tana bubbuga kafa tace wallhy
ni bazan yadda ba saidai mu tafi tare, ya rike baki yace ina
zamu tafi tare, tace daura mana,
yace haba Afee nah yanzu kinaso in ďaukeki mu tafi gurin
su kaka liman tare, ay sai suce amaryar ma bata da kunya,
ta turo baki tace naji ay sau ďaya zasu ce, ya daura
hancinshi kan nata yana gogawa a hankali yace haka zasu
dinga faďa kullum,
jikin Afeeya ya mutu sosai saboda yadda yakeyi da
hancinshi kan fuskarta, ta kalli idonshi dake lumshe ta fara
kokarin kauda fuskarta,
hanata yayi ta hanyar daura bakinshi kan nata a hankali
yace I love uu to d moon nd bck baby,
ta sunkuyar da kanta kasa tace I love u too yayana,
yace to tunda u love me ki barni inje I promise you komin
dare in na shigo gari zanzo in ganki kinji,
ta kalli cikin idonshi tace ko biyu na dare ne fa zan jira ka,
yace na yarda baby kiyi fatan Allah ya kaini lafiya,
tace to Allah ya kaimun kai lafiya ya dawo min da kai lafiya,
yace ameen Afee nah,
sun daďe tare a ranar suna hira kamar kar su rabu,
Da kyar suka rabu gurin 11 ya tabbatar mata zai shigo ya
ganta kafin ya tafi,.
rakiyar kura suka dingayi har saida ya gaji ya kaita har cikin
daki ya tabbatar ta kwanta sannan ya tafi gida cike da
nishadi, ya yi matukar kosawa Afeeya ta zama mallakinshi,
shi yasan auren Afeeyah shine lst dream dinshi, yasan yana
aurenta ya gama samun komai a rayuwarshi,
da wadannan tunaninkan masu dadi bacci yayi gaba da
jabeer da gidan Bara'u...

.: ◆◆ RABO AJALI 29◆◆ By

Sulaiman Bomboy
Tun 5 saura na asuba jabeer ya farka jikinshi duk da ya jike
da zufa, duk sanyin a.c dana damuna basu hanashi yawan
jin zafi a yan kwanakin nan,
bayi ya shiga yayi wanka da ruwan sanyi ya ďauro alwala
ya fito yayi nafila ya zauna jiran a kira sallah..
Yana idar da sallah ya zauna kan kujera ya lumshe idonshi
kanshi na kallon sama,
Allah kaďai yasan tunanin da yakeyi a wannan lokacin,
sai 8 ya mike jikinshi a sanyaye ya gama shiri cikin farar
shadda, yayi matukar kyan da bai taba yin irinshi ba shi
kanshi saida ya faďi da ya kalli madubi,,,
saida ya gama shiryawa tsaff har zai fita daga ďakin sai
kuma ya dawo ya dinga kallon ko ina ko akwai abin da ya
manta bai dauka ba, drawer ya buďe ya dauko driving
licences dinshi har zai rufe drawer sai yaga wasu takardu,
daukosu yayi ya dubasu yayi murmushi ya mayar dasu
mazauninsu ya rufe drawer yasa kai ya fita daga ďakin,
A parlor ya tadda babanshi zaune yana karyawa ya tsuguna
ya gaisheshi, ya amsa da fara'a yace sammako zakayi
kenan,
jabeer yace eh baba ina son in dawo da wuri ne shiyasa,
Abida ta fito rike da cup din kunun gyaďa da plate din alale
ta zauna kusa da mijinta, jabeer yace ina kwana ummi,
tace lafy lau jabeer yau dai kaka liman yayi kira irin wannan
sammako hka,
jabeer yayi dariya yace na kosa inje in ga uwargidana
sarautar gida shiyasa,
ta gutsiri alalen ta kai bakinta tace kace ka kosa kaje kuyi
faďa har ku gaji,
yayi dariya yace kamar kin sani,
dai2 lokacin Amirah ta shigo parlorn cikin uniform itama
rike da break dinta a hannu ta gaisheshi ya amsa yace miko
min naki kije ki zubo wani, Amirah ta turo baki tace yaya fa
nayi latti dan Allah kasa Dayyaba ta zubo maka,
alhj bara'u yayi mata dakuwa yace gidanku, zubo abincin ne
zai hana ayi miki dukan latti, ajiye mishi kije ki zubo wani,
Amirah ta ajiye tana kunkuni ta wuce kitchen ta zauna ta
zuba wani kunun tana sha tana mita,
shima jabeer kaďan yasha kunun ko alalen ma bai taba ba
ya mike yayi sallama da iyayenshi sukayi mishi fatan Allah
ya tsare hanya,
har ya shiga mota yaji kamar ana kwala mishi kirah,
fitowa yayi ya nufi parlon yace gani baba, alhj bara'u yace
ban kira ka ba jabeer saidai ko umminka,
Abida tayi dariya tace muna tare a zaune zan kirashi baka ji
ba,
ta kalli jabeer dake tsaye yana kallonsu yana murmushi
tace ni wai me ma zakayi a daura ne ka kirkiri tafiyar
gaggawa,
alhj bara'u yayi dariya yace zuciyarki ce ta kirashi kenan
dan tayi mishi wannan tambayar,
jabeer yayi dariya kamar zai faďa musu sai kuma ya fasa
yace ziyara kawai zanje yi ummi,
tace to Allah ya bamu ladan tare, duk sukayi dariya haďe da
cewa ameen,
kallon babanshi yayi yace baba akwai maganar da zamuyi
dakai akan wasu takardu suna nan a ďaki na in na dawo in
shaa Allahu zamu tattauna, alhj bara'u yace Allahumma
yashaa ka gaida Baba da Goggo,
yace zasu ji sosai ya fita Amirah ta biyoshi da gudu tana
mishi bye bye,
hararta yayi yace Allah yasa a fasa miki jiki da dukan latti,
tayi mishi gwalo ta shige mota tana dariya tana daga mishi
hannu,
shima motarshi ya shiga ya tada ya fita yana gaisawa da
baba ado da sauran masu aikin gidan..
Hanyar daura ya ďauka ba tare da ya tsaya yaga Afeeyah
ba saboda yana gudun bata mishi lokaci da zatayi dan
yasan in har ya shiga to bazai taba tafiya da wuri ba,,
Karfe 10 da mintina ya isa gidan kaka liman, bayan ya huta
yaci abinci da furah suka dinga hira dasu Goggo, basu fara
aiwatar da komai ba sai da sukayi sallar azahar sannan
suka fita shi da kaka liman,
suna tafe yana mishi bayanin irin mugayen tsafin da akayi
ma Affan wadanda aka binnesu a cikin gidan, kaka limann
yace saboda rashin imani irin na matar nan har kafin fita
gida tayi mishi dan kar ma ya fita wani ya ganshi yayi mishi
addu'a ko ya taimaka mishi, sannan ta katangeshi daga
dukkan adduar mutane ta mantar da mutane ciwonshi in ba
waďanda suke kusa dashi ba,
jabeer ya jinjina kai yace ay ni ban ďauka zaluncinta har ya
kai haka ba walhy kaka, amma in shaa Allahu karshenta
yazo,
wani kauye suka je a cikin kasar Nigar mai suna
"Tsatsunburum (s Burum)"
kauyen bashi da nisa da zangon daura, gaba da gidan sarki
sukaje kaka liman yace ya tsaya anan,
jabeer ya kalli gurin,
a katange yake da wata katuwar bishiya a ciki, kaka liman
ya fito ya shiga gurin jabeer na binshi a baya, ashe wata
katuwar rijiyace a cikin gurin mai cike da tarihi,
kaka liman ya kwance ledar da ya zo da ita ya fito da wasu
layu da magunguna ya fara haka rami ya binnesu sannan
ya ďauko wata gora a cikin jakarshi da magunguna a ciki
yasa hannu a cikakkiyar rijiyar ya debo ruwan cikinta
sannan suka fito daga gurin,
jabeer dai kallon gurin yakeyi ga rubutu a jikinshi amma
rubutun ya fara gogewa,
ya kalli kaka yace kaka amma wannan rijiyar tana kunshe
da tarihi ko,
kaka liman yace kwarai kuwa,
abin al'ajabi ya taba faruwa a gurin nan,
ya nuna mishi wata bishi dake dan nesa kaďan da gurin
yace kaga waccan bishiyar, jabeer yace eh kaka, yace to
daidai saitinta da gurin kiwon shanu ne, shanaye da yawa
ake kiwo a gurin, "akwai wata saniya guda ďaya kullum aka
bata abinci sai taki ci haka ruwa, saidai a ganta kullum da
yamma tazo nan gurin da muka shiga kafin a katange shi ta
daďe a gurin har sai dare take komawa cikin yan uwanta,
kullum haka takeyi sam bata cin abincin da ake basu, ana
cikin haka rannan sai mai shanun ya dinga binta a baya dan
ganin abinda takeyi a gurin, yana zuwa gurin yaga ta kafa
kanta a wani ďan tsukukun rami tana shan ruwa, tana
gamawa yaga ta kwanta karkashin bishiyar nan lokacin
tana karama sosai a gurin take bacci har dare sannan ta
koma cikin yan uwanta, in takaice maka dai wannan saniyar
tunda ake kiwonta bata taba cin abinci ba wannan ruwan
shine ya zamo ruwa da kuma abincinta sannan wannan
bishiyar ta zamo gurin hutu a gareta har ta mutu a gurin,
bayan ta mutu ne mutane suka haka wannan ramin ya
zamo rijiyar da bata taba kafewa ba duk wahalar ruwan da
akeyi a garin tofa wannan rijiyar na nan da ruwanta sannan
wannan bishiyar tana nan bata taba fadi ba shekaru fin 100
dan nima labari aka bani,
jabeer yace ikon Allah shine aka katange ta, kaka liman
yace kwarai kuwa kuma cikin ikon Allah ruwan cikinta yana
zama waraka ga duk wanda ya yarda da Allah kamar yadda
ta kusugu take,
jabeer yace Allah ya kara ma Annabi daraja, kaka yace
ameen jabeer shiga muje dan zan ga Aminina "Maina dogon
yaro" shima akwai abin da zai bani daga nan mu wuce cikin
daura mu karasa,
jabeer yace to kaka, suka shiga mota suka wuce jabeer na
kallon girman bishiyar yana tasbihi ga Allah...
Sai bayan magriba suka gama komai suka dawo gida a
gajiye,
dakyar jabeer ya iya taba abincin da Goggo ta kawo mishi
sauri2 dan yana son ya dauki hanyar gida komin dare,
babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwana yace samm
bazai kwana ba dan gobe da wuri yake so fara aiwatar da
aikin cikin gidansu Affan wanda shine mataki na karshe na
aikin,,
sai da yayi isha' sannan kaka liman ya fito yayi mishi rakiya
yana kara nuna mishi yadda zaiyi amfanin da maganin
yana kuma mishi faďa akan yayi taka tsantsan da oyizah,
jabeer ya shiga mota yace in shaa Allahu kaka zanyi duk
yadda kace, mun gode sosai, kaka liman yace to Allah ya
tsare kayi tuki a hankali ďan boko, jabeer ya tada motar
yace baka da matsala tsoho, yaja motar suna ďaga ma
juna hannu, saida yaga kulewar motarshi sannan ya juya
gida,
haka kawai ya tsinci gabanshi da tsananin faďuwa,
a waje ya zauna yana bin sawun motar jabeer da kallo yana
mishi adduar Allah ya kiyaye hanya...
Kuka sosai ta ke mishi a waya yana rarrashinta, sam taki
barinshi yayi magana sai masifa takeyi sai dai yace yi
hakuri kawai,
saida ta gaji dan kanta ta kashe wayar tana cigaba da wani
kukan, kiran wayarta ya dinga yi taki dagawa sai hajja dake
kwance ta mike ta dauka tace masifaffe dai baiji dadi ba
wannan shegiyar zuciyar taki wata rana sai ta saki dana
sani, kara wayar tayi a kunnenta tace jabeer ya hanya,
yace lafiya lau hajja dan Allah ki bata hakuri ta karbi wayar
inyi mata bayani,
hajja tace ni fa bazan bata hakuri ba tunda ba wani laifin
akayi mata ba, haka kawai kai kuma bazaka yi sabgar
gabanka ba saidai kullum tafi son kana makale da ita
kamar kaska,
dan taga kana biye mata ne shiyasa, yau ko abinci bata ci
ba saboda jik'a wai saita jiraka ka dawo saboda haka ni
kaga komawata dan bacci sosai nakeji,
ya salam ya faďi hade da cewa haba hajja yanzu kina
kallonta taki cin abinci kuma har kike faďa,
tace kar in faďa, ni dadi ma abin ya min saboda nasamu
rarar na dumame da na sadaka,
jabeer yace kiyi wa Allah ki bata wayar hajja,
hajja ta ajiye wayar kan cinyarta tace in kinga dama ki
ďauka ta juya ta koma bacci,
Afeeya ta dauki wayar ta fita waje tana sheshshekar kuka,
tsayar da motarshi yayi yana mata magana tayi banza
dashi tana cigaba da kukanta,
kukan da takeyi yana taba zuciyarshi sosai saboda ya tsani
jin kukanta ko da kuwa na farin ciki ne,
a hankali murya a dashe yace Afee tunda baza kiyi shuru
ba na fasa dawowa yau, gara in kwana a daura gobe sai in
dawo lokacin kin huce,
wani irin kuka ta kara fashewa dashi tace ka kai sati dari
ma ba ruwana,
ya kwantar da kanshi jikin kujerar motar yace ki saurareni
plss baby kinsan yadda kukan nan ke taba ni kuma
kikeyinshi saboda ki bata min rai,
murya na rawa tace nima kasan abin da kamin zai sani
kuka shiyasa kayi min,
yace plss am sorry kinsan haka nan jabeer dinki bazai ki
kiranki ko yazo ya ganki ba, inada dalilai masu karfi,
ta kara shagwabe murya cikin kuka tace dalilan nan sun
cuceni da suka sa na yini gashi har dare zai raba banga
MURADIN RAINA ba,
yaya jabeer meyasa bakayi faďa da dalilan nan ba, meyasa
ka zabi sufi farin cikina karfi a gurinka, wallhy zuciyata zata
iya bugawa in har nakai goma ban ganka ba, zuciyata
namin zafi a can ciki babu wanda zai iya fahimtar zafinta
sai kai, dan Allah kazo in ganka,
jikin jabeer ya mutu sosai idonshi yayi ja ji yakeyi kamar
yaji ta ajikinshi yana mata rarrashin da zai mantar da ita
damuwarta,
a hankali yace rufe idonki babyna,
ta lumshe idonta iskar hadari da kamshin kasa na ratsa
hancinta har zuwa makoshinta, yace buďe ki faďa min
abinda kika gani, ta buďe a hankali tace ni babu abinda na
gani, yace baki ganni kusa dake ba,
tace wayyo Allah na dan Allah kazo in ganka yayana,
jabeer yace kisa a ranki ina tare da ke ako da yaushe
babyna, in Allah ya yarda ko 10 ta wuce to da rabi bazata
wuce ba jabeer dinki zaizo gareki ya faranta zuciyar da ta
yini cikin kunci,
tayi murmushi tace promise,
yace in shaa Allah babyna, amma fa sai kin ci abinci, in baki
ci abinci ba zan shiga Daura Motel inyi bacci na,
tayi kara mai karfi a kunnenshi tace ni tare zamuci dakai,
ya sauke ajiyar zuciya yace tnk God dodon kunnena na aiki
da in na dawo sai na kashe naki da ruwa,
tayi dariya sosai tace kayi tafiya a hankali fa amma ka
dawo 10 din, yace zanyi amma sai kinci abinci kuma kin
daina kukan banza, ta turo baki kamar yana gabanta tace ai
kai ka koya min,
yace nakusa hanashi nidai je kici abinci ki ragemin wanda
kika ci kinji,
tace to yayana sai ka dawo,
yace sai na dawo babyna mai rigima,, tayi dariya ta kashe
wayar haďe da rungumeta a kirjinta,
tsaki taji anyi mai karfi ta waiga gurin taga inna suwaiba
rike da buta a hannunta, Afeeya ta mike itama taja tsaki har
sau uku ta fada daki tabar inna suwaiba tsaye tana zaginta,
Cooler Afeeya ta bude ta diba abinci tace kanki akeji ni baki
isa kiyi spoiling mood dina ba,
nan ta dan ci abinci tasha ruwa ta kwanta a kasa tana
kallon hoton jabeer tana murmushi har bacci yayi gaba da
ita bata sani ba.....

.: ◆◆ RABO AJALI 30◆◆ By
Sulaiman Bomboy
Tun bayan magriba hadari mai tsananin duhu ya taso yana
kokarin haduwa a gabas,
iska ce mai dadi taketa kaďawa a wannan lokacin har zuwa
karfe 9:32pm, lokacin ne hadarin yamma ya kusa haďuwa
da na gabas, iska mai karfin gaske haďe da guguwa da
walkiya su keta tashi ta ko'ina kamar zasu tashi gidaje da
motocin biladama,
yaf yaf ruwan feshi ke busawa a cikin iskar,
A wannan lokacin gudu jabeer yakeyi cikin motarshi yana
Allah Allah ya isa kano kafin goma ko kuma goma daidai,
wuce motoci yakeyi yana tafiyarshi cikin kwanciyar hankali
yana wiping yayyafin dake sauka a kan glass din motarshi,
karfe 9:50 ya rage saura k.m baifi 15 ba ya shigo garin
kano, murna ya dinga yi dan yasan in shaa Allahu kafin
10:30 zaiga Afeenshi,
har ya dauko wayarshi zai kirata sai ya fasa so yakeyi
kawai ta ganshi kafin lokacin da ya daukar mata..
Wani haske ya gani ya gifta gabanshi hade da girgiza mai
karfi wacce tayi sanadiyyar fitar tayar motarshi ta gaba,
runtse idonshi yayi sosai yana kalmar shahada saboda
yadda yaji shi a sama motar na juyawa sosai, wasu masu
trailer sukayi parking gefen hanya suna salati cikin tsoro
saboda yadda motar ke wulwulawa a sama,
saida tayi minti uku a haka sannan ta daki wani katon dutse
ta tarwatse a kasa dai2 lokacin ruwa mai karfi ya tsuge
haďe tsawa, mutanen gurin kowa ya kunna full light dinshi
suka karasa kusa da motar jiki na rawa saboda basu taba
ganin accident irin wannan ba,
ba karamin dagargajewa motar tayi ba, nan da nan suka
fara kokarin ciro mutumin da suka gani a gaban motar, da
kyar suka iya ciro jabeer saboda wani karfe da ya shige
cikin hancinshi ya bullo ta kanshi,
kuka mutanen gurin sukeyi suna salati saboda sun tabbatar
da wanda suka ciro a cikin motar nan bashi da sauran rai,
da sauri suka soma bincika aljihunshi dan motar babu abin
dauka a cikinta, driving licences suka gani sai kudin da ya
baci da jini ko ta ina,
farar shaddar jikinshi ma babu wanda zaice fara ce dan duk
ta koma ja, basu samu adress dinshi jikin d.l din ba sai dai
sunanshi,
daukarshi sukayi cikin mota suka shigo cikin garin kano
suka zarce police station dashi,, (innalillahi wa inna ilahir
rajiun)
A kuma dai2 wannan lokacin Affan na zaune kusa da
daddynshi suna dan taba hira duk da rabin hirar tasu
shirme ce,
a hankali ya karkatar da kanshi yana kallon daddy idonshi
ya ciko da kwalla yace daddy yau ma kaga har dare yayi
abokina baizo ba, ya kalli inda ya tara wasu fararen
duwatsu guda 8 na kirga yace daddy kagani yau kwana 8
kenan,
alhj basheer ya shafa kanshi yace kayi hakuri Affan kasan
yanata shirye shiryen biki dole ka rage ganinshi,
Affan ya marairaice fuska yace to daddy ni yaushe zaka
min aure, alhj basheer yayi dariya yace duk ranar da ka
shirya Affan,
Affan yayi dariya shima yace daddy ay na shirya, daddy
yace to wacece matar,
Affan ya rufe idonshi yana girgiza kai fuskar Afeeyah nata
mishi yawo a cikin kwayar idonshi da kwakwalwarshi,
yayi saurin bude ido yace Barbie din jabeer, daddy ya kara
sautin dariyarshi yace wacece kuma barbie, Affan yace
AFEEYAH, daddy yayi dariya yace Afeeyar da jabeer zai
aura,
Affan ya gyada kanshi yana dariya yace eh daddy ay yace
zai bani ita ta dawo nan gidan da zama,
daddy yayi dariya yace to naji tashi kaje ka kwanta kaga
ruwa na neman tsugewa,
Affan ya mike yana murna yana fadin daddy zai aura min
barbie..
dariya alhj basheer yayi ya mike ya wuce dakinshi dan
oyizah tayi tafiya tun da safe..
Affan na shiga ďaki ya haye kan gado yanata wakar abu
ďaya, tsawar da akayi mai karfi tayi daidai da faďuwar
gabanshi, mikewa yayi daga kan gadon ya leka window
yana kallon ruwan da ya tsuge kamar da bakin kwarya,
Affan cikin tsoro ya rike kirjinshi dake tsananin bugu ya fita
da gudu yayi dakin daddy,
da kyar daddy ya lallabashi suka kwanta tare amma fa
bacci ya kaurace a idonshi dan daga ya runtse idonshi to
fuskar jabeer zai gani yana kuka mai tsanani..
Hakan ta kasance da Afeeyah, wannan tsawar da akayi ita
ta farkar da ita daga baccin da bata san tayi ba mai cike da
mafarkai,
agogon wayarta ta duba taga 9:56 ta zauna tana sauraron
zubar ruwan sama tana kara duba agogo kirjinta na
harbawa da sauri,
10:20 ta kira wayar jabeer taji ta akashe, a hankali ta koma
bayan hajja ta kwanta tana duba wayarta ko zata ji kiranshi
shuru taji har 11 ta gota,
a hankali ta fara rero kuka tana kiran sunanshi,
kamar a mafarki hajja taji kukan ta farka da sauri tace
yanzu ke Afeeya har yanzu baki bar kukan nan ba,
wani irin iskanci ne wannan,
Afeeyah tace hajja sha ďaya fa ta wuce kuma shi ya cemin
goma da wani abu zai dawo,
hajja cikin masifa tace shikenan kuma ana wannan ruwan
in ya dawo sai yaki zuwa ya huta yazo gurinki saboda gaki
yar gwal ko,
Afeeyah ta shige jikin hajja tana kuka sosai tace hajja fa ya
kashe wayar shi ne, kuma tun jiya fa ban ganshi ba, dan
Allah ki taimaka min wallhy bazan iya bacci ba in ban
ganshi ba,
hajja taji tausayinta sosai tace to yi shuru ya isa haka,
kinga yanzu dare yayi babu mamaki wayarshi ta mutu babu
charge kuma bayason yazo ya sameki kina bacci kinga
kuma ruwa akeyi kina son ya fito cikin ruwan nan ne,
Afeeyah ta girgiza kanta,
hajja tace to ki mishi uzuri gobe nasan tun kafin ki tashi
daga bacci zaizo kinji, Afeeyah ta gyada kanta tana share
hawaye haďe da ajiyar zuciya,
hajja ta kwantar da ita tace yi addu'a kiyi bacci,
Afeeyah ta fara karanto adduoi hawaye na zubo mata ta
gefen idonta a zuciyarta tana jin haushin jabeer na kin cika
alkawarin da yayi mata, yanzu haka zanyi bacci banganka
ba yaya jabeer, atlst ko waya ya kunna naji muryarshi zan
dan rage wani zafin abinda ta dinga fadi a zuciyarta kenan,
baccin ranar a gurin Afeeya rabi da rabi ne, saboda duk
farkawa saita duba wayarta taga ko ya kirata,
( Allah sarki Afee zanso ace kinsan gani da muryar jabeer
ma bazaki kara ji ba bare har kiga missd call dinshi,)
Abida ma juyi take tayi idonta na kan agogo, babu irin kiran
da batayi ma wayar jabeer ba amma taki shiga,
Alhj bara'u yace Abida ya kamata ki cire duk wasu tunani a
ranki kiyi addu'a ki kwanta kiyi bacci in shaa Allahu babu
abinda ya sameshi babu mamaki mota ce ta bashi matsala,
Abida tace matsalar mota sai tasa ya kashe wayarshi yasan
dole hankalin mu zai tashi alhj,
alhj bara'u da shi kanshi daurewa yakeyi yace kinsan
sharrin netwk mu zuba ido zuwa da safe mu gani, Abida dai
uhum kawai tace saboda yadda takejin nauyi a kirjinta,
rungumeta yayi ta baya yana faďa mata kalamai masu
kwantar da hankali dan in ya bari tasan shima hankalinshi a
tashe yake to fa zata kara daga hankalinta fiye dashi ma,
Kaka liman ma ya kira har sau uku yaji ko ya iso,
shima hankalinshi a tashe yake saboda jin har lokacin
jabeer bai isa gida ba...

RABO AJALI

3⃣1

By Suleiman Bomboy

Washe gari tunda alhj Bara'u ya idar da sallah yake zaune
kan dadduma,
hankali tashe ya kalli Abida da ta zuba tagumi tana jan
carbi yace Abida har yanzu wayar yaron nan bata shiga ba
ko,
Abida ta gyada kanta kawai tana kallonshi,
yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah dai yasa jabeer
lfy yake dan bai taba irin wannan abun ba, ko wayarshi
nada matsalar charge ay duk inda yake bazai rasa wayar da
zai kiramu ya sanar damu halin da yake ciki ba,
Abida tace uhummm zuciyata tana faďamin duk inda jabeer
yake ba lafiya yake ba,
alhj bara'u yace ki daina faďin haka, haka kawai zuciyarki
ta dinga kitsa miki mugayen tunani, ya mike tsaye yana
duba lokaci yaga 7 har ta wuce ya fita daga dakin yayi
hanyar waje,
Abida ta share kwallar data ďan fito daga idonta tace ya
Allah ka sassauta min zafin da nake ji a zuciyata ka bani
ikon jure duk wani abu da zanji game da jabeer,
Malam Atiku na kwance idonshi a lumshe da radio a
gefenshi yanajin labaran karfe 7 kamar yadda ya saba
kullum, bayan an gama labarai akan halin da kasarmu take
ciki da kuma na kasashen ketare, sai aka sako labaran
kwallon kafa, cikin kosawa ya mika hannu zai kashe radion
saboda sam labaran kwallon kafa basa gabanshi,
tsayar da hannunshi yayi sakamakon jin sanarwar hatsari
da akayi anan hanyar shigowa gari wanda akace an tsinci
gawar saurayi mai suna Jabeer Bara'u, wadanda suka cinci
gawar sunyi saurin mikashi ga hukumar yansanda, yanzu
haka yana can asibitin Aminu kano, ga duk wanda yaji
kuma yasan inda yan'uwan baw----- ay malam Atiku bai
karasa sauraro ba ya diro daga kan gado yana faďin
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ko takalmi baisa a kafarshi ba ya fita waje da sauri jikinshi
na rawa,
a kofar gida ya samu alhj bara'u zaune kan dakali, da sauri
alhj bara'u ya mike yace malam Atiku lafiya na ganka haka
ko takalmi babu,
Malam Atiku ya saki ajiyar zuciya yace tunda na ganka
zaune lfy lau ay alhamdullh, wallhy wata sanarwa naji
yanzu a radio akan wani hatsari da ya faru a daren jiya
kuma sai naji an kira sunan jabeer shiyasa hankalina ya
tashi,
Alhj Bara'u ya mike yana salati kamar zararre, malam atiku
yace alhj lafy,
Alhj bara'u baki na rawa yace jabeer dina ne,
jabeer dina ne wallhy, tun jiya muke neman layinshi bamu
samu ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
malam atiku yace lahaulu wala kuwwat illa billah, alhj
bara'u ya rike hannun malam atiku ya rasa ta inda zai fara
sai janshi yakeyi yana fadin muje asibitin da suka ce,
malam Atiku zaiyi magana parking din motar alhj basheer
ya dakatar dashi,
da sauri ya fito yace lafy alhj bara'u ,
alhj bara'u ido zuru2 yace jabeer ya tafi,
alhj basheer cikin rudewa yace ina ya tafi,
malam atiku yace karka yanke hukunci alhj muje asibitin
tukunna, in shaa Allahu ma bashi bane, alhj basheer yace
wani asibiti,
malam atiku ya fada mishi abinda yaji a radio, alhj basheer
da sauri yace kuzo mu tafi asibitin,
alhj bara'u da bakinshi bai daina salati ba ya shiga motar
jikinshi a sanyaye suka wuce Aminu kano T.H,
Tunda suka shiga gaban alhj bara'u ke faduwa har suka
karasa cikin mortuary, suna shiga aka nuna musu D.L din
jabeer sannan aka karasa dasu inda yake,
Juyawa alhj bara'u yayi da ya kalli gawar sau ďaya ya fara
addua cikin sambatu kamar tababbe,
D.L din kawai yake kallo yana jujjuyashi yanaso ya gasgata
shin

Please Login or Register in order to submit comment