Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin bala'i take,
Afeeyah ta girgiza kanta tace da hannuna nakeson
in kasheta kuma yau dinnan,
Affan yace hmm nima naso hakan tun ranar da na
dawo
cikin hayyacina,
nan ya bata labarin komai harda dawowar umma da
bacewar oyizah,,,,, cikin mamaki Afeeyah tace zatayi abinda yafi haka
muguwa
azzaluma, Allah ya isa tsakanina da ita,
in shaa Allahu sai tayi mutuwar kask---Affan ya
katseta da
sauri yace wannan adduar bata kamace ki ba, Allah yasan
yadda zai tafiyar da irinsu ki zuba ido ki jira lokaci,
Afeeyah tayi shuru tana kallonshi kamar ba shi bane
tababben bawan da baya taba maganar da zaka iya
fahimta
a da, Allah mai iko......

***** RABO AJALI*****
****64 TO 66*****
.
BY SULAIMAN BOMBOY.
.
Daren ranar suna zaune gurin meeting bayan sun
dawo
daga gurin dodon tsafinsu,
gaba dayansu suna sanye da jajayen kayansu da
suke
amfani dashi, bayan sun gama tsaface tsafacensu sai chummy ta
mike
taje ta shigo da ďan tsoho,
a tsakiya suka sashi kamar yadda suka saba,
kewayeshi ta farayi tana yan sirkullenta a kanshi
sannan ta zauna,
ďaya bayan ďaya tsohon yake bin mutanen gurin
da kallo,
yana zuwa kan oyizah ya tsayar da idonshi kyarr a
kanta
baya ko kiftawa, kureshi itama tayi da ido cikin rashin tsoro ta daka
mishi
tsawa tace daina kallona, idon wannan tsohon ko
rawa baya
yi ya fara motsa bakinshi da babu hakori ko ďaya a
ciki, oyizah ta kalli chummy tace my lord plss mu gama
da
tsohon nan mu cigaba da abinda ke gaban mu,
chummy bata kalli oyizah ba ta cigaba da haďe
haďenta na
tsafi cikin wani katon koko, mikewa tayi ta iso gaban tsohon ta ja hannunshi da
karfi
har yana bigewa ta jona mishi wani abu mai tsini
kamar
kibiya a jijiyar hannunshi tana kallon cikin kokon,
a firgice ta juyo tana kallonshi ta kuma maida idonta cikin
kokon dan gasgata abin da ta gani a ciki,
da sauri ta saki karfen taja baya saboda yadda ya
dauki
zafi kamar tana rike da garwashi,
wata irin dariya tsohon nan ya saki yace jinin nawa ya
isheki haka, in kina bukatar kari kizo ki diba san
ranki dan
ko zaki dibi cikin tanki bazai kare ba,
su oyizah duk suka marmatso suka leka cikin
kokon, a gigice suka ja baya saboda ganin wani bakin
ruwa mai
kaurin gaske a ciki,
oyizah murya na rawa tace my lord kiyi wani abu
plss
wannan kamar ba mutum bane, cikin su esther da alhj sambo ya ďuri ruwa suka ce
kwarai
wannan ba mutum bane,
cikin dakewa chummy tace ko ma waye shi tunda
yazo nan
bazai taba fita ba, ta dauko wata sanda mai mugun kyalli ta nufi
wannan
tsohon dashi,
tana karasowa gaban shi ta ďaga wannan sandar
ta saita
cikin idonshi ta turata ciki, ga mamakinta sai ganin sandar
tayi ta rabe gida biyu, daya a cikin idonshi ďaya a
hannunta,
sa hannunshi yayi ya zaro sandar yana dariya ya
mika mata
yace haďata guri ďaya, a harzuke ta yar da sandar hannunta ta koma ta
shirya
kanta sosai tace yau ko waye tsohon nan sai na
gama
dashi,
ta bayanshi ta bullo ta sa farcen hannunta ta shako wuyanshi ta baya, da azama ya juyo ya sanya nashi
faratan
a makogoranta,
wani irin kakari ta farayi tasa kafarta ta haureshi
yayi baya,
nan suka fara b'ace b'ace suna faďa sosai, ba karamin wahala chummy take sha ba amma
saboda
tsabar ta dahu da tsafi kuma bata so mabiyanta
suga
gazawarta haka ta jajirce suka cigaba,
wani lungu ta shiga a cikin ďakin ta fito rike da wani magani
ta bace tana kokarin watsa ma wannan tsohon,
sam bata san yana kallonta ba ta ďaga wannan
maganin
zata zirara mishi yayi saurin juyar da hannunta ya
zuba wannan ruwan a tsakiyar kanta,
wani irin ihu ta saki ta faďi kasa tana ta shure shure
nan
take kanta ya fara zagwanyewa, tun tana ihu mai
karfi har
ta koma yi a hankali gaba ďaya mummunar halittarta ta
canza kama,,
a gigice su oyizah suka fara ja baya hankalinsu a
tashe
babu wanda a cikinsu yayi kokarin zuwa gurin
wacce suke kira mai taimakonsu, itama yau gashi ta kasa
taimakon
kanta,
mikewa wannan tsohon yayi yana kallon su
oyizah,
mai da hankalinshi yayi gurin alhj sambo yace alhj sambo
Bana, minister mai fuska biyu,
a fili fuskar kamala a zuci ta zalunci,
ina son kayi ma kanka hisabi ka zabi hukunci cikin
jerin
abinda zan lissafo, na farko ko in kasheka anan in kaika gida da
kayan jikinka,
ko kuma in barka ka koma gida ka fito media ka
faďi ko me
kakeyi sannan ka fadi adadin mutanen da ka bayar
akasha jininsu,
alhj sambo cikin rudewa yace kayi min rai dan
Allah,
dan tsoho yace Allah shi ke da rai bani ba,
alhj sambo yace ka rufamin asiri wallhy na tuba,
har abada bazan kara aikata irin wannan aikin ba, dan tsoho yayi dariya yace zunubin da kayi baya
kuma fa,
kayi kisan kai, shirka, da sauransu duk dan ka
samu mulki,
haka nake so kaje gidan talabijin ka sanar musu da
halinka, alhj sambo ya girgiza kanshi yace mutunci na zai
zube,
dan tsoho yace ai gara ya zube a duniya, alhj
sambo yace
dan Allah ka kasheni anan kawai gara suga
gawata, dan tsoho ya girgiza kanshi yace a'a bazan yi kisa
ba gara
a hukunta ka kafin kaje ka tarar da na ubangiji,
kuka sosai alhj sambo yakeyi yana mishi magiya
akan ya
kasheshi ya huta amma tsoho yayi kememe yaki, alhj sambo da yaga babu sarki sai Allah sai ya
amince da
abinda tsoho yace mishi ya kimtsa ya bace yayi
gida
hankalinshi a tashe,
kallon sauran yan gurin tsoho yayi ya dinga neman wacce
tayi silar zuwanshi gurin bai ganta ba, girgiza
kanshi yayi
yace in kere na yawo,,,
sannan ya kalli su esther da suka tsure yace kuje
Allah yasan yadda zaiyi daku itama waccan ogar taku
banyi
niyyar yi mata komai ba saida tazo cutar dani,
yana kaiwa nan ya bace,,
da sauri su esther sukayo kan chummy da ake iya
hangen komai na tsakiyar kanta,
dagota sukayi suka ga komai na kanta na zuba a
kasa,
a firgice suka saketa suka fara tattara kayansu,
wata a cikinsu mai suna HADASIYYA ta kalli kujerar
tsafin chummy, muguwar zuciyarta ta sak'a mata ya
kamata ta
gaji kujerar itama ta zama 1 daga cikin matsafan da
ake ji
dasu ta samu mabiya tayi mulkinta san ranta,
murmushi tayi ta ajiye kayan hannunta tayi gurin kujerar,
tun kafin ta karasa karnikan gurin da eagles suka
dinga
kuka irin nasu na dabbobi,
tana taka step din gurin esther tasa ihu tace
Hadiscos karki zauna,
nan hankalin sauran yakai kanta suka haďa baki
suka dinga
rokonta akan kar ta zauna taxo su gudu,
inaa wanda yayi nisa baya jin kira domin dai
hadasiyya gani take bakin ciki suke mata dan karta fisu matsayi,
tana daura mazauninta akayi sama da ita,
wani irin girgiza ďakin ya farayi yana cilli da duk
wanda
yake cikinshi,
saida ya gama cillar dasu sannan ginin ya ruso gaba
dayanshi kan ragowar chummy, "hmmm duniyar
chummy
ta kare"
saura oyizah ko ina ta shiga....
Sauki sosai ya samu a gurin Afeeyah har an sallameta ta
dawo gida,
tana matukar samun kula gurin zeenatu da Affan
duk da ba
wani sabo sosai tayi dashi ba,
gyara sosai alhj basheer yasa ayi a gidan da saukar alqurani saboda shi har a lokacin a tsorace yake
dan yasan
indai safiya na raye to bazata taba barinsu ba,
farida ma ta nutsu sosai dan islamiyya ta koma ta
zama
saliha gwanin ban sha'awa, tsakaninta da zeenatu ba raini
sai matukar girmamawa,
haka suna girmama junansu ita da Afeeyah....
3mnts later
Alhj Bara'u ne tsaye a ďakin jabeer yana duba
wasu takardun Asiyah da jabeer din ya amso mata ana
sauran
sati biyu ya rasu,
cikin drawer ya bude ya gama bincikosu ya gansu
can
kasan kayanshi, har zai rufe drawer sai yaga wasu takaddu a
tsaftace cikin
file dinsu,
dariya yayi yace jabeer kenan sarkin ajiyar takardu,
daukosu yayi ya rufe drawer ya budesu yana binsu
da kallo, cikin mamaki yace wannan ai takardun kadororin
alhj
basheer ne,
fitowa yayi daga dakin ya rufo kofar ya kaima
Abida
takardun Asiyah sannan ya wuce gidan Alhj basheer....
A parlor suka zauna sai da suka gama gaisawa
sannan Alhj
bara'u yace wasu takardu na gani a dakin marigayi
kuma
da sunanka a jiki,
alhj basheer yace takardu kuma, alhj bara'u ya mika mishi yace kwarai kuwa,
alhj basheer ya amsa ya duba su cikin mamaki yace
ikon
Allah,
wadannan takardun sune silar shigan iyalina cikin
tashin hankalin nan alhj bara'u,
nan ya bashi labarin kyautar da yayi ma Affan, ya
daura da
cewa ashe jabeer ya bawa ajiyarsu,
tabbas nasan safiya tayi neman takardunnan bata
gansu ba,
kai gaskiya nagode alhj ubangiji Allah ya jikan
jabeer ya kai
rahama kabarinshi,
alhj bara'u yace Ameen,
nan suka cigaba da hirarsu hankali kwance,,,,, Fitowa tayi daga inda take makale kullum a cikin
gidan
bayan ta gama jin hirar alhj basheer da alhj bara'u,,
tunda
ta gudu daga gurin tsafin su kullum a gidan take
yini a makale bacci ne kadai ke mayar da ita wani
kurgugun daji
inda take hada kulle kullenta,
dariya tayi sannan ta shiga parlourn ta dauki
takardun tayi
kissing dinsu tace me ya rage min tunda na samu wannan,
bari kawai in tafi inje in fantama hankali kwance,
a hankali ta fito daga parlorn ta make jikin window
tana
jiran alhj ya shigo ta fita,
tana tsaye a gurin ta hango Afeeyah da cikinta dan wata
hudu da kwanaki har ya fito sosai kamar dan wata
bakwai,
Affan na tsaye kusa da ita ya daura hannunshi kan
cikin
yana mata magana kasa2 suna dariya, wani bakin ciki ne ya turnuke oyizah saboda tuno
cewar
Afeeyah ce silar fitarta daga gidannan,
itace silar rushewar komai na farin cikinta,
kwafa tayi cikin bacin rai tace wallhy bazan bar
yarinyar nan ta dawwama cikin farin ciki ba,
dole in dawo da shirina gobe in tarwatsa rayuwarta
kafin in
bar kasar nan gaba daya....
Washe gari tun takwas na safe ta gama shirinta na
zuwa gidan alhj basheer ta gama da Afeeyah ta huta,
takardun da
ta ajiye can kasan katifarta ta daga cikin izza zata
dauka
taga wayam,
hankali tashe ta bankade katifar tanata dubawa ko idonta
ne amma sam bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta karaďe arear da take zaune
ko zata
ganshi nan ma babu labari,
a gigice ta sa takalminta ta nufi cikin gari rike da kwalbar
acid da ta tsaya ta siya jiya da daddare kafin ta
dawo
makwancinta,
bacewa tayi kamar yadda ta saba ta shiga gidan,
dakin alhj basheer ta shiga yana kwance yana bacci hankali
kwance
gidan sai kamshin girki yakeyi,
tana kallon side drawer dinshi ta hango takardun
da ta
tabbatar ta kwana dasu a dakinta, a rude ta daukesu tace ya akayi suka dawo nan,
rungumesu tayi tace koma wani tsinannan ne ya
dawo dasu
to sun dawo hannuna kuma bazasu kuma fita ba,
saurin bacewa tayi saboda jin motsin kofa tayi
dakin su Afeeyah,
Kwance ta sameta tana bacci cikin bargo shi kuma
Affan
yana zaune a gefenta yana duba wasu takaddu,
murmushi
tayi ta makale jikin bango ta buďe kwalbar hannunta ta
ďaga zata zirara a kyakykyawar fuskar Afeeyah,
juyi Afeeyah tayi hade da mika tana faďin
"la'ila ha illallahu muhammad rasoolullah sallalahu
alaihi
wasallam" Alhamdu lillaahil-lathee 'ahyaanaa ba'da maa
'amaatanaa
wa'ilayhin-nushoor.,,
nan kwalbar hannun oyizah ta fara girgiďi nan take
tayi taka
juye a fuska da jikinta, a gigice ta saki takardun hannunta tasa
razanannan ihun da
saida ya girgiza gidan saboda kararshi,
a firgice Affan yaja Afeeyah yana kallon oyizah da
ta sauya
kamanni, mikewa yayi da sauri yana fadin "Allaahumma
'innaa
naj'aluka fee nuhoorihim wa na'oothu bika min
shuroorihim."
Da gudu su alhj basheer suka shigo dakin suna
fadin lafiya, ganin oyizah sukayi a kwance tana birgima ta yage
duka
kayan jikinta tana ciccisge gashin gabanta dan
tsananin
azaba,
da kafarta alhj basheer ya ganeta yace safiya!!! Innalillahi
wa inna ilaihir rajiun,
ya waiga ya kalli zeenatu yace kin gani ko na fada
miki
safiya bazata kyalemu ba,
"Tabbas bata kyaleku ba dan tana bibbiyarku kullum a cikin
gidannan, tare kuke yini da ita,"
sukaji wata murya ta ratso kunnensu mutumin ya
bayyana
a gabansu,
gaba dayansu suka ja baya a tsorace, da sauri tsohon yace kar kuji tsorona, ni ba mugu
bane,
asalima na zama kariya a gareku tun lokacin da
take
bibiyarku,
a jiya ne ta samu damarta da take ganin ta gama samun
komai saboda kwashe wadancan takardun da tayi,
a daren na maido da takardun shine yau ta dawo ta
kwashesu kuma tazo da niyyar kashe Afeeyah ta
hanyar
zuba mata ruwan batir, cikin ikon Allah sai ta farka da addu'a nan take mai
kowa
mai komai ya tsareta ya mayar mata da kaidinta,
mamaki suka dinga yi suna Allah wadai da oyizah
dake ta
faman ihu tana fisge fisgen gashin gabanta, godiya suka dinga yi ma tsohon har ya bace ma
ganinsu
sannan suka dawo akayi waje da oyizah dake
zabura babu
komai a jikinta,
gudu ta dingayi tana ihu kamar mahaukaciya ta fada gidan
Malam Atiku,
suwaiba na zaune tana cin kosai tana hararar hajja
taji an
fado kanta ana ihu,
da sauri suwaiba ta mike tana ihu ta fada daki ta datso tana
leke tana haki,
cikin kuka oyizah tace suwaiba nice, nice safiya,
suwaiba
tace safiya, safiyar alhj basheer,
oyizah tace eh ita, ki bude min kofa, suwaiba tace Allah ya kyauta in bude ma matsafiya
kofa,
safiya ta kara sa ihu tace suwaiba na daina, wallhy
na
daina, nayi dana sani, ki yafe min, ni na kashe
abulbait, ni na bashi sweet yasha ya mutu muka sha jininshi,
suwaiba ta saki salati tayi saurin bude kofar tace ke
kika
kashe abulbait,
oyizah tace nice ki yafe m--- ay bata karasa ba taji
saukar tabarya a bakinta,
wani ihun ta saki ga azabar konewar fuska gata
jibgar
tabarya,
bugunta suwaiba takeyi baji ba gani tana kuka
tana fadin kin cuceni,
dakyar hajja ta hankada oyizah waje ta dawo bawa
suwaiba hakuri,
cikin kuka tace hajja ki yafemin na cuci kaina, dan
ALLAH ki
yafemin, hajja tace babu komai ai dama duk wanda ya hau
motar
kwadayi to babu a inda zata saukeshi sai tashar
wulakanci,
wannan ya zama darasi ga masu hali irin naki,
daki suwaiba ta shige cikin nadama tana kukan mutuwar
danta....
Kwanan oyizah huďu tana yawo akan titi babu
wanda yake
kulata bare yayi yunkurin taimaka mata,
gaba daya ta gama cisge gashin gabanta da hannunta,
ga ciwon jikinta da fuskarta yana mata radadi
kamar zai
tarwatsa kwakwalwarta,
gurin wata kwata take zama ta dinga ďiban ruwan
gefe tana watsawa a jikinta ko zata samu sassaucin azaba,
a ranar kwana na biyar din ne tana zaune tana ihu
tana
fadin irin mugayen abubuwan da tayi taji an
tsuguna a
gefenta, da ido ďaya ta kalli gurin taga Afeeyah ce ta daga
kanta
taga fareeda tsaye tana kuka,
mikewa tayi tana kokarin rungume farida tayi
saurin ja baya
tace karki tabani mummy, zuwa kawai nayi in ganki saboda an fada min
hakkinki a
kaina,
Afeeyah tace a'a fareeda uwa uwa ce, kome tayi
mahaifiyarki ce,
oyizah tayi tsaki cikin azaba tace kece ma kike fada mata
abinda zata min,
ta kalli farida tace wannan ce take saki a hanya,
zata kara magana ciwon jikinta ya mintsileta ta
zaburah ta
fara tsalle tana kokarin sosa jikinta, Afeeyah ta kalli farida
tace kije ki kamota farida mu suturc--- bata karasa
magana
ba sukaji karar bugun abu,
da sauri suka kalli gurin wata katuwar trailr ce tayi
ciki da oyizah ta murje kanta,
da gudu suka isa gurin mutane har sun taru ana
kallon
oyizah amma babu wanda yayi yunkurin taba ta,
wasu daga
sun kalleta suke barin gurin, sunfi karfin awa daya a gurin babu wanda ya
taimakesu
dakyar drivernsu ya dauketa aka nadeta cikin boot
suka tafi
da ita gida,
saida zeenatu tasa baki sannan alhj basheer ya kira akayi
mata wanka aka suturce ta,
daga alhj bara'u sai alhj basheer sai malam atiku da
masu
aikin gidan kadai suka tafi kai oyizah gidan ta na
gaskiya, gidan da kafa bata fitowa,
gidan da ibadarka sune abokan hirarka,
gidan da kudi ko mulki bazasu hanaka kwanciya
kan kasa
ba,
gidan da babu fanka bare a.c babu iskar shaka sai in kayi
aikin alkhairi,
Allah kasa mu cika da kyau da imani......
Ameen
Tunatarwa--
Ya yan uwana mata masu son mallakar namiji ta kowane
hanya,
shin in mun mallakeshi muna tunanin in mun mutu
wannan
mallakar bazata hana namiji ya manta damu yaje ya
nemi wata ya aura ba,
mallakar namiji itace biyayyarki in kikayi ma namiji
biyayya
tsakani da Allah wallahy kin gama mallakeshi
duniya da
lahira dan bazai taba mantawa dake ba, akwai matan da suke wanke najasar gabansu su
sawa
namiji a abin ci ko sha,
wallhy,
wallhy,
duk macen da take wannan aikin in tazo mutuwa sai ta
cisge gashin gabanta gaba daya da hannunta, shan
najasa
haramun ne,
cutarwa ne ga dan uwa musulmi,
in mallaka muke so to muyi koyi da matan manzon Allah
s.a.w, akwai ayoyin saka soyayya a zuciya ko ita
muka rike
mun gama mallakar mazajenmu ba cuta ba
cutarwa,
saboda saida soyayya mallaka ke tafiya, Allah ya ganar da dukkan yan uwa musulmi baki
daya, su
kuma mazajenmu masu sa mu kauce hanya ta
hanyar
wulakanta mu Allah ka ganar dasu ka basu ikon
kulawa da hakkokinmu Ameen thumma Ameen...
Rayuwa mai cike da so, kauna, nishaďi, farin ciki,
da
annashuwa shi akeyi a gidan alhj basheer, rayuwar
mai cike
da koyarwar addinin islama,
Ni'imtacciyar rayuwa sukeyi wacce duk a da suka cire rai
da samunta,
Alhj basheer yana matukar kula da kowa a cikin
gidan, duk
wasu hidimdimu nasu yana kokari wajen daukeshi
ba tare da sun kai ga bukata ba,,
haka zeenatu kulawa sosai takeyi ma kowa har
masu
aikinta, bata bari kowa ya koka saboda matukar
sanin
darajar biladama, Fareedah ma rayuwa takeyi me dadi wacce take
ganin ashe
da can baya ba rayuwa takeyi ba saboda tana
zaune cikin
duhun kai ga rashin samun nutsuwar zuci saboda
rashin ibada da batayi, yanzu kuwa wani nishaďi take ciki
musamman in ta idar da sallah sai ta dinga jin
kamar iskar
wannan lokacin daban take saboda yadda take
ratsa ko ina
na jikinta... ( tabbas iskar wannan lokacin kam daban take ga
wanda ya
hankalta,
duk wani musulmi da zaran ya idar da sallah to
nasan a
wannan lokacin zaiji kamar an sauke mishi wani nauyi
akanshi kuma zai dinga jin yalwatacciyar iska mai
dadin
gaske,
kaii musulnci yayi, Allah ka sa duk ibadun mu
karbabbu ne, Alhamdulillah ala ni'imatul islam)....
Soyayya da shakuwa su suka shiga tsakanin
ma'auratan
biyu, soyayya sosai suke gwadawa junansu haďe
da
mutuntawa, basa taba yarda su bata ran juna, komai nasu suna yinshi cikin so da kulawa gwanin
ban
sha'awa,
Affan sam baya kaunar ganinta ita kaďai tana
damuwa dan
yasan damuwar akan jabeer ne, wani lokacin ma in ya sameta tana kuka in ya bata
hakuri
sam bata yin shuru har sai ya dangana da zeenatu
sannan
dakyar zasu hadu su rarrasheta tayi shuru,
shima kuma duk ranar jumma'a sai ya kai ziyara kabarin
amininshi bayan yasa an sauke qur'ani yayi sadaka
sannan
ya zauna a gurin ya dade yana mishi addu'a,
haka cikin dare in sun idar da sallah addu'a ta
musamman suke mishi da sauran yanuwa musulmai wadanda
suka
rigamu gidan gaskiya...
Cikin ikon Allah cikin Afeeyah ya isa haihuwa yayi
girma
sosai dan ko mikewa bata iya yi in kuwa ta mike to sai tafi
minti ďaya kafin ta iya daga kafarta,
rubutu da magunguna sosai take shansu dan kaka
liman
musamman yake mata jarkar rubutu tun cikinta na
wata, a wannan lokacin ne wani dare ta farka da nakuda
mai
zafin gaske,
cikin gaggawa suka kaita asibiti, likitoci sun fi
karfin awa
biyu akanta ana abu ďaya, Affan kuka ya fita waje yakeyi saboda jin irin
kukan azabar
da takeyi,
ganin har lokacin ba improvement doctor ya yanke
shawarar yi mata c.s saboda service dinta bai buďe
ba,, alhj basheer da kanshi yasa hannu saboda yadda
yaga ta
galabaita,
a gaggauce suka shiga da ita dakin theater suka
fara
aikinsu cikin kwarewa, cikin farin ciki doctr ya fito musu da jarirai mata
manya
manya guda biyu,
da sauri zeenatu ta mike ta karbi ďaya alhj basheer
ya karbi
daya sunata ma doctor godiya, Affan kuwa bai bi takansu ba dakin da aka kai
Afeeyah ya
shiga ya zauna gefenta yana shafa kanta yana mata
addu'a
yana jin sonta na kara ratsa ko ina jikinshi...
Kwananta hudu a asibiti aka sallameta suka koma gida aka
cigaba da kula da ita da yaran dan jikinta har
lokacin baiyi
kwari ba,,
Ranar suna yara suka Amsa sunan Asma'u
(Nuwairah) da Zeenatu (Nawwarah),
anyi shagalin suna cikin kwanciyar hankali dangi
kowa ya
halarci sunan harda su suwaiba da akayi nadamar
gaske... .
TAMMAT BIHAMDULILLAH.
DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH
UBANGIJIN TALIKAI MAI KOWA MAI KOMAI.
TSIRI, AMINCI, DARAJA, DAUKAKA SU KARA
TABBATA GA SHUGABAN HALITTU ANNABIN RAHAMA (S.AW), ALAYEN SHI DA KUMA SAHABBAN
SHI.
TAMMM! YAU ALLAH YASA MUKA ZO KARSHEN
WANNAN LITTAFI MAI SUNA #RABON_AJALI.
DA FATAN KUN NISHADANTU KUUMA DA FATAN YA
FADAKAR SOSAI. MUNA FATAN ALLAH YA KARE MU DAGA IRIN MASU
MUGAYEN HALAYEN DAKE CIKI YA KUMA SADA MU
DA MASU KYAWAWAN HALAYEN DAKE CIKIN SHI YA
BAMU IKON KWAIKWAYON SU AMEEN.
.
DAGA KARAMIN KANIN KU: #SULAIMAN_BOMBOY.

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment