Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari in yi miki
cikakkun bayanai akan abubuwan da baki fahimta
ba
tukunna sai mu shiga wani,
mijinki ba lafiyar koshi kadai gareshi ba harda ta kwakwalwa,
tambayarki zanyi,? tsakaninki da Allah kinajin zaki
iya yin duk abinda ya dace domin ki kubutar da
mijinki
daga
wannan halin da yake ciki,? Afeeyah ta gyada kanta tace zanyi kaka,,, yace
yauwa yar
albarka, Ki sani mijinki ya samu saukin tabuwar da
kwakwarshi tayi
sai dai kuma azababben sihirin da ake mishi shi ke
kara dagula kwakwalwar ya rasa fahimtarshi ya dinga
yin
abu kamar yaro, wani magani ake bashi wanda
idan yayi
awa
shida bai sha ba zai iya dawowa mai lafiya amma ba sosai
ba saboda akwai wasu tsibace tsibbacen da aka
birne a cikin gidan wanda gano su sai ansha
matukar
wahala,
duk ranar da aka hako wadannan asiran to wannan
ruwan
maganin ya daina tasiri a jikinshi domin duk wata
tabuwar kwakwalwa zata barshi, karki ce sihirin
wasa akayi
mishi, wannan na gasken gaske ne wanda yake da
matukar
wahalar karyewa, kin fahimceni ko, Afeeyah ta
gyaďa kanta tace ay kaka duk abinda aka ce min
matar nan zatayi
bazan musa ba saboda ni ganau ce ba jiyau ba,,,
shigowa dakin sukaji anyi babu sallama,
da sauri suka waigo dan ganin ko waye......
Oyizah suka gani tsaye idonta kyarr kan Afeeyah,
gefenta
kuma salma ce rike da basket din abinci, gaban Afeeyah sai faduwa yakeyi a zuciyarta tana
adduar
Allah yasa bata ji tautanawarsu ba, gyaran murya
kaka liman yayi ya kalli oyizah yace an
wuni
lafiya, da sauri ta kauda kanta tace lafiya lau ta karaso
gaban
gadon Afeeyah jikinta a mace tace ya jikin, da sauki
Afeeyah ta fadi ba tare da ta kalleta ba,
salma kuwa ajiye basket din tayi ta koma gefe tana
cika tana batsewa,
mikewa kaka liman yayi ya kalli Afeeyah yace bari
in
koma, Kiyita "hasbunallahu wa ni'imal wakil"
saboda
maganin musibun duniya, Allah ya kara sauki ya kuma
inganta abin
dake cikin ki,
Afeeyah tace ameen kaka nagode yaushe zaka
dawo,
yace too zan dai gani amma ay bazan koma ban sake
dawowa ganin jikin naki ba, tace to sai ka dawo
kaka,
ya kalli oyizah da kanta ke kasa yace to hajiya sai
anjima
ko, tace to sai anjima, har ya fita ya kuma lekowa yana kallon kwandon
abincin
yace
"ki danne kwadayinki, in har ya taso miki to ki
tambayi goro
a baki domin kwantar dashi kin gane ko" Afeeyah ta kalli kwandon nan take ta gane
manufarshi tace
to kaka nagode,
Oyizah da ta tabbatar kaka ya tafi sai ta dago kanta
ta
zauna ta dafa Afeeyah tace sannu, amma jikin da sauki ko,
umm kawai Afeeyah tace,
oyizah tace kin ci abinci kuwa,
Afeeyah ta yatsina fuska tace bana iya cin abinci
amai yake
sani, oyizah tayi murmushin mugunta tace shiyasa na dafo
miki abincin da nasan masu ciki naso,
salma ďan zubo mata,
Afeeyah tayi saurin cewa a'a ta barshi doctor yace a
daina
bani abinci saboda aman na wahalar dani, oyizah tace
doctors din nan sun cika iyayi manta dasu kici babu
aman
da zakiyi, Afeeyah tace saidai ko zuwa anjima dan
yanzu bacci
nake ji, oyizah zata kara magana cikin bacin rai salma ta
katseta
tace haba mummy dole ne, ji yadda kike wani pettn
dinta tunda tace baza taci ba ba sai ki kyaleta ba,
cikinta,,,,
oyizah ta harari salma tace baki san me lalurar ciki sai
an
matsa mishi yake cin abinci ba,
ko so kikeyi in bari ta wahalar min da jika,
Afeeyah ta kwanta tace uhmm, oyizah tace rabu da
salma kinji bata san lalurar ciki ba
shiyasa, salma tayi tsaki ta tashi ta fita daga dakin
tana
mamakin yadda mummy ke lallaba wannan yar
iskar
yarinyar, babu yadda oyizah batayi ba akan Afeeyah taci
abincin da
ta kawo amma firr taki, har hajja ta shigo tasa baki
Afeeyah
tace ita sam yunwa ne bataji kuma tana ci zatayi
amai, oyizah ta boye bacin ranta tace to hajja anjima ki
tabbatar
taci saboda bai kamata mai karamin ciki ta dinga
zama da
yunwa ba,
hajja tace karki damu in shaa Allahu zata ci, oyizah ta dan
kara zama shuru kafin ta tashi tayi musu sallama
haďe da
jaddada ma hajja akan ta kula da Afeeyah ta dinga
cin
abinci akai2, cikin mamaki hajja ta kalli Afeeyah tace kin ga matar
nan
yadda ta canza kamar ba ita ba, gaskiya naji dadin
yadda
ta nuna kulawarta gareki ga dukkan alamu ta
saduda ta fara sonki, Afeeyah ta juyar da kanta gefe a zuciyarta tace
kwarai
kuwa tana matukar son kasheni hajja ai dole ta
kula
dani
kafin hakanta ya cimma ruwa, buďe kulolin abincin hajja tayi tana fadin masha
Allah irin
wadannan namomi haka,
Afeeyah tayi saurin mikewa tace hajja dan Allah a
ina
zan samu agwaluma ko cashew anan gurin, hajja tace
aiko akwai wani mai agwaluma da na gani
anan
waje bari in duba Allah yasa bai tafi ba,
Afeeyah tace ameen dan Allah hajja ya baki mai
tsami sosai, hajja tace to ta fita da sauri, tana fita Afeeyah
ta mike ta kwashi kulolin abincin
tayi waje
dasu ta zuba a bola tayi saurin komawa daki, ko
minti biyar
hajja batayi ba ta dawo da agwaluma cikin leda ta mika mata,
kwanciya Afeeyah tayi ta dauki agwaluma daya ta
fasa ta
fara sha,
salatin hajja ne yasata juyowa da sauri tace lafiya
hajja, hajja tace kulolin ne naga babu komai, Afeeyah tace
eh na
cinye baki ga dama na mutum daya ta yi ba, hajja
tace
daga fita ta har kin cinye, Afeeyah tace eh mana to
nawa abincin yake, hajja tace shine dan bakar mugunta ko naman baki
ragemin
ba,
Afeeyah tayi dariya tace ke kuma nama ne aranki
sai
kace wata kurah, hajja tace waya sani ko kurar ce gaskiya kin shiga
hakkina,
Afeeyah tace karki damu hajja nah anjima nasan
zamu
samu wasu naman, hajja tayi tsaki ta tashi ta fita
wanko coolers din... Bayan isha'i kaka liman ya dawo asibitin, sun dade
suna
hirah da hajja kafin ta basu guri shi da Afeeyah,
kaka liman kalli Afeeyah yace dazu muna magana
bamu gama ba na tafi,
yanzu sai muyi sauri dan naji gobe za'a sallameku ko,
Afeeyah tace eh,
kaka liman yace nima goben zan koma,
da fatan duk abubuwan da na fada miki dazu kin
fahimcesu
ko, Afeeyah ta gyada kanta,
yace yauwa to yanzu sai ki faďa min abinda kika
gani,
nan Afeeyah ta faďa mishi duk abinda ta gani jiya
da daddare,
kaka liman ya jinjina kanshi yace wannan shine abinda
nakeso Allah ya nuna miki dan nasan da na faďa
miki hakan
tun farko to tsoro bazai barki ki shiga gidan ba ma
bare har
tausayin affan ya shigeki ki yarda da taimakon da zakiyi ba,
wannan abun da kika gani shi jabeer ya gani amma
nashi
ya banbanta da naki saboda shi yaji suna tsafin ne
akan
Affan da mahaifiyarshi, shin tunda kika shiga gidan kinji ko sau ďaya alhj
yayi
maganar zeenatu,
Afeeyah ta gyada kanta, kaka liman yace to bashi
ba ma
har yan uwanta da makusantanta basa iya maganarta ko ke
kin taba tuna ta tun bacewarta,
cikin mamaki Afeeyah tace a'a kaka,
kaka liman yace mugun asiri akayi mata, karyewar
asirin na farko shine jin da jabeer yayi
mata har ya sanar da ni,
a aikin da nayi na gano laya ce aka turata cikin
bakin
DAMO
aka binne ta anan cikin gidan da kuke, Afeeyah ta
zaro idonta tace a cikin gidan? yace kwarai
kuwa,
sannan duk wasu asiran da tayi a cikin gidan ta
binnesu da
yawansu bansan takamaimai inda ta binne ba
amma suna cikin gidan,
in har Allah ya taimakemu muka san inda suke har
muka
ciresu to saukin abun yazo dan mun riga mun
gama
wasu ni da jabeer karashen ne wannan kuma sune masu
wahalar,
Afeeyah ta jinjina kanta tace to kaka ya za'ayi
musan
inda
tayi binne binnen, kaka liman yace shine yanzu abinda nake tunani,
hannu yasa a aljihu ya ciro wata bakar leda, bude
ledar yayi
ya fito da wasu layu guda biyu da wani ruwan
turare
sai garin magani,
layun ya fara mika mata yace rike wadannan layun,
dafatan
zaki jajirce akan duk abinda zaki gani,
Afeeyah tayi kulu kulu da ido tace kaka banyi
yarinya da daukar wannan kasadar ba kuwa,
kaka liman yayi dariya yace Afeeyah kenan sai kiga
abinda
zakiyi ni bazan iya yinshi ba saboda wani lokacin
kwakwalwar yaro tafi ta babba kaifin rike abu,
Afeeyah ta gyada kanta tace to Allah ya bani juriyar iyawa
yace ameen abinda ya kamata ki fadi kenan,
wadannan layun a karkashin pillown ki zaki sasu,
in zaki kwanta kiyi alwala kiyi sallah kiyi addu'a
sosai akan
Allah ya bayyana miki guraren da akayi wadannan binne
binne, sannan ki shafa wannan turaren a jikinki ki
kwanta
kina mai kyautata niyya, in shaa Allah cikin kwana
bakwai
Allah zai nuna gurin da suke, duk wani abun tsoron da zaki gani na rokeki ki
daure kar wannan tsoron ya sare gwiwarki,
ke kadaice garkuwar bayin Allahn nan, in har kika
sare to ki
sani babu wani wanda zai iya daurewa yayi
wannan aikin,
Afeeyah ta gyaďa kanta tace in shaa Allahu kaka
zan daure,
nasan ina tare da Allah da kuma kai,
yace masha Allah, sannan wannan maganin ki
dinga ba
Affan yana sha, kafin kwana bakwan nan zai dinga
yin wasu abubuwa wadanda zasu dinga dawo
dashi
cikin
hayyacinshi ya dinga tunanin abubuwan mamakin da suka
faru dashi a shuďaďdun lokuta, kin gane bayanin
ko, Afeeyah ta gyada kanta tace eh na gane, to
amma
kaka
yaya zanyi in na gansu, kaka liman ya mike yace wannan kuma shawararki
ce,
in kiga zaki iya ciresu ki taimaki uba da kakar abin
dake
cikinki to in kuma zaki barsu su dawwama a haka
nidai na gama nawa yanzu naki kadai ya rage sai mu barma
Allah
sauran, Afeeyah tace to kaka nagode sosai, ya
miko mata
wayarshi
yace samin numberki kiyi flashing in wani abu ya shige miki
duhu kya nemeni,
Afeeyah ta amsa tasa mishi numbrta sukayi sallama
ta
bishi da kallo har ya bace ma ganinta
, ganinshi kadai yana kwantar da hankalinta, badan
tsufan
shi ba da babu abinda zai hana a kirashi da jabeer
dinta....

<<<>>>
**** Part 49 to 51****
.
.
.
By SULAIMAN BOMBOY.
.
Karfe 9 na safe aka sallameta suka ďunguma zuwa
gida a
motar alhj basheer, oyizah na zaune a parlonta tana gyara farce
hankalinta sam
ba'a kwance yake ba dan
tun jiya take jiran jin mummunan labari game da
Afeeyah
amma shuru gashi har gari waye, Shigowar motar alhj basheer ne yasa ta mike ta
kwashe
kayan gyaran kumban dan taje ta tarboshi ko
zataji wani
labari a gurinshi,
tana buďe kofar parlon tayi tozali da mai taurin kashi wato
Afeeyah,
kallon mamaki ta tsaya yi mata a zuciyarta tace to
ko karya
hajja take mata yarinyar nan bata ci abincin ba,
Afeeyah ta katse mata zancen zucin da takeyi tace ina
kwana,
oyizah ta sauke ajiyar zuciya tace lafiya lau ta juya
ciki bata
ko bi takan hajja dake rike da kaya ba,
Side dinsu ta wuce tana kallon hanya ko zata ga Affan,
da bismillah ta murďa kofar dakin suka shiga ita
da hajja,
bayi ta wuce ta cire kayan jikinta tayi wanka ta
dauro
alwalar walha, ta windon bayin ta hangoshi zaune gurin fishpond idonshi kyar a cikin ruwan
baya ko
kiftawa, murmushi tayi ta fito daga bayin,
sai da tayi sallah ta shirya cikin bakar jallabiya
sannan ta
fita gurinshi, A hankali ta karasa gurin tayi saurin rufe mishi ido
da
hannunta, shafa hannun yayi cikin firgici yasa ihu
yana
ďaga kafarshi dan kar ya faďa cikin ramin kifin,
da sauri ta toshe mishi baki tana dariya tace nice matsoraci,
juyowa yayi ya kalleta nan take ya saki dariyar
farin ciki ya
rungumeta yace ina kika tafi ki barni,
ta dago fuskarshi tace ina daddy yace maka ya
kaini, ya shagwabe fuska yace mummy tace min bazan
kara
ganin ki ba, jiya suka dinga min ihu anty salma har
da duka
na,
Afeeyah tace am sorry gani na dawo daga yanzu babu
wanda zai kara maka kallon banza ma bare har ya
dukeka
tashi muje kaci abinci,
ya mike da sauri yana dariya suka wuce daki...
Da sauri oyizah ta bar gurin dan kar Afeeyah ta ganta,
wani irin bakin ciki ne yake taso mata a cikin
zuciyarta,
shin me zata ma wannan yarinyar ta daina ganinta
kwata2
a rayuwarta, a cikin yan kwanakin nan ganin yarinyar nan shine
abinda
yafi komai bakanta ranta, aiki biyu kenan tayi
akanta kuma
duk masu karfi amma basu kama ta ba,
tabbas wannan gara inyi mata me kankat, tabbas yau ne
numfashinta na karshe a duniya dan barin Afeeyah
a duniya
barazana ce a gareta dan yarinyar na neman fin
karfinta,
a tarihin rayuwar oyizah tun tana karama babu abinda ke
tsaya mata a gaba bata kau dashi ba dan haka
wannan
karan Afeeyah bata isa ta rusa sa'arta ba,
da wadannan tunanin ta karasa ďaki ta zauna
neman mafita, wani sashi na zuciyarta ya bata amsar
cewar ta
bada Afeeyah kawai su "chummy" suyi bandaro da
jinin
tsinaniyya, in ba hakan tayi ba to kuwa tana zaune
kwado zai mata kafa,,
dariya tayi cikin gamsuwar shawarar da zuciyarta
ta bata,
nan ta mike ta fara shirye2 kafin dare yayi ta
sadaukar da
jinin ďiyar ma'u da malam Atiku, To oyizah muje zuwa muga zaki iya da Afeeyah...
Cikin jindadi suka kammala cin abincinsu na dare
wanda
hajja ta aiko musu,
bayan sun gama ta jiko maganin da kaka ya bata
ta bashi yasha dakyar yana sha yana furzarwa,
saida ta nuna mishi bacin ranta sannan ya sha da
yawa,
yana gama sha ta gyare gurin ta dawo ta zauna
suka fara
yar hira, murďa kofar suka ji anyi suka waiga suna kallonta,
da fara'a ta karaso gurinsu tace amarya da ango,
sannunku
da hutawa,
Afeeyah ta kau da kanta tace yauwa, oyizah ta
zauna gefensu tace Afeeyah ya kamata ki ďan leka gida ki
gaishesu dan gani nayi tunda kikazo gidan nan
baki shiga
ba, daga nan sai ki dan zaga da Affan yaga gari ko
ya
kikace, Afeeyah tace hakane mummy amma ay naga affan
baya
fita ko,
oyizah tace shiyasa nake so ki ďan fara fitar dashi
yayi
refreshing, Afeeyah tace to duk yadda kika ce, ta mike ta
dauko hijab
dinta tace tashi muje,
ya tashi yana kallon oyizah alamun yana so ya
tambayeta
yaje ko a'a, gyaďa mishi kai tayi alamar yaje, dariya yayi ya bi
bayan
Afeeyah suka fita,
dariyar jin dadi oyizah tayi ta rakasu har gate
sannan ta
juyo da sauri tayi dakinta ta kwaso kayan tsafinta ta nufi
side din su Afeeyah,
Tafiya takeyi da sauri saboda manta Turaren da
tasa a
ranta duk ranar da xata gida zata kaima mahifinta,
tun a parlor ta gane akwai mutum a bed room dinta,
labewa tayi ta leka a hankali,
ba karamin firgici ta shiga ba ganin oyizah tsaye a
gefen
gadonsu tana shimfiďa farin kyalle a kasan
katifarsu, da sauri ta fita daga dakin lokacin da taga ta
dauko zanin
gadon su ta mayar ta shimfidashi yadda yake,
a guje ta fita ta samu affan a inda ta barshi murya
na rawa
tace muje, ya kalleta yace ina turaren, dakyar ta saita kanta
tace muje
dai gobe zan kai mishi..
Sai goma saura suka dawo gida,
babu wanda Afeeyah ta faďa ma abin da tagani
dan ta riga ta gama kudira abinda zatayi tana komawa gida,
suna shiga ta zaunar da Affan a parlor ta kunna
mishi tv
tace kar ya tashi bari ta gyara cikin dakin,
tana shiga daki ta yaye zanin gadon da bismillah
ta ciro farin kyallen ta naďe zanin gadon ta ajiyeshi gefe
sannan ta
fito ta kalli affan tace ina zuwa bari in mayar ma
da
mummy zaninta,
yace to ya cigaba da kallon cartoon dinshi, tana fita tayi hanyar ďakin mummyn cikin sanďa
dan tasan
yanzu tana gurin daddy,
a hankali ta murďa kofar ďakin ta shiga da addua a
bakinta,
da sauri ta yaye zanin gadon tasa farin kyallen kamar
yadda taga oyizah tayi sannan ta maida zanin
gadon ta
shimfidashi yadda yake tasa kai ta fita daga ďakin
da
sauri..... .
Tana komawa daki ta tarar da Affan na gyangyaďi
a kan
kujera,
da sauri ta shiga ďaki ta canza zanin gado ta tofe
ko'ina da addu'a ta sa layun karkashin pillownta sannan ta
shiga bayi
ta ďauro alwala ta fito ta wuce parlor ta tarar har
ya bingire
a gurin yana bacci,
tashin shi tayi a hankali ta kaishi ďaki ta tofeshi da addu'a
ta rufeshi da bargo sannan ta shimfiďa dadduma
tayi raka'a
biyu,
a gurin ta zaune har pss 2 tana addu'a tana
tunanin abinda oyizah tasa mata a karkashin gurin kwanciyarta,
a zuciyarta tace koma meye ya kare miki can Allah
ya kara
tsaremu daga sharrinki,
mikewa tayi tana hamma ta hau gado ta kara
shafa addu'a sannan ta kwanta tana kara rokon Allah ya nuna
mata
guraren da akayi binne binnen nan dan alfarmar
annabi da
hasken al qur'ani....
Ke dai kinji kunya wallahi, mutum yayi ta tusa sai kace bodari gaba ďaya
kinyi
polluting iskar ďaki,,, salma ke magana da karfi
hancinta a
toshe ta doshi parlor,
fareeda ta biyota tana dariya tace ashe ba dadi kullum kike
kumbura min ciki cikin dare,
salma tayi tsaki ta zauna tace wallhy bana irin
wannan haba
wannan irin tusa haka sai kace ana kwasar kashi,
fareedah ta kwashe da dariya ta koma daki tana faďin oho
dai in kinga dama ki dawo ďaki ki kwanta dan 12
ta wuce,
salma tace wallhy bazan kwana a dakin nan ba
dan bansan
wace iri zaki kuma saki cikin dare ba, fareeda ta shige ďaki tana dariya,
mikewa salma tayi ta leka dakin da affan yake
kwana
taganshi kaca2 tayi tsaki ta wuce dakin oyizah,
da murnarta ta shige ďakin ganin mummy bata
ciki, kwanciya tayi akan gadon ta cigaba da chattn din
da takeyi,
sai gurin biyu na dare bacci yayi gaba da ita...
Tun asuba esther ke kiran wayar oyizah bata ďaga
ba
saboda wani nannauyan bacci da yayi gaba da ita, sai gurin bakwai da rabi ta tashi babu sallah bare
salati,
agogon gefenta tayi saurin kallo taga 7:34 da sauri
ta diro
daga gado tana mamakin baccin da ya dauketa
har ya hanata zuwa shan jinin matsiyaciyar yarinyar nan,
karar shigowar kira wayarta ne yasata saurin
dagawa tace
morning esther, jiya bacci ya hanani zuwa meeting,
esther tace haba ay ni tunda naga ban ganki nasan
kina can kina shegen baccinki, amma oyeee meyasa kikayi
haka,
meyasa kika bada jinin yari---- oyizah tayi saurin
katseta
tana dariya tace badai an gama komai kuma kun
riga kun koshi da jinin ba, to ay shikenan,
esther cikin damuwa tace oyizah me tayi miki haka
da zafi
har kikayi sacrificn dinta 4 no reason,
oyizah tace meye ma bata min ba yarinyar nan,
kedai zamuyi magana bari inje mu fara shirye shiryen
jana'izah, esther tace to sai munyi waya,
oyizah ta kashe wayar ta shiga bayi ta wanke
fuskarta cikin
farin cikin ta yar da kwallon mangwaro ta huta da
kuda, a zuciyarta tace yanzu ne zan kara daure alhj da
Affan ta
yadda su da dukiyarsu zata dawo karkashin iko na
gaba
ďaya, bazan kara yarda a auro ma affan mace ba
bare ma har ta zame min damuwa,
Tana fitowa ta wuce parlor inda alhj basheer ke
kallon
news,
saida ta gaisheshi sannan tace bari inje in dubo
lafiyar Su Affan sai in kawo maka break ko,
yayi murmushin jin dadi yace ya kamata kam
saboda mai
larurar ciki,
ta shafi fuskarshi tana dariya tace su alhj ana ji da
wannan jikan, yace sosai ma,
Allah dai ya fito min da ita ko shi lafiya,
oyizah ta kaurara dariyarta tace ya Hajjjj kenan
sannan ta
wuce side din su Affan..
Da izzarta ta buďe kofar tana murmushi, bata samu kowa a
parlon ba dan haka ta tura kanta bedroom ďin,
zaro ido tayi cikin firgici saboda ganin Affan
kishingiďe da
towel a jikinshi Afeeyah na zaune da night gown a
gefenshi tana mishi gyaran fuska suna kallon juna suna
murmushi,
A-f-e-e-yah oyizah ta faďi bakinta na rawa,
Afeeyah ta mike
tana gyara gashin kanta tace naaaam ina kwana
mummy, oyizah bata iya amsawa ba sai ma fita da tayi
dasauri
kamar zararriya,
tana gab da shiga dakin alhj basheer dan daukar
wayarta ta
kira esther taji ihun farida a ďakinta, da sauri ta juyo ta karaso ďakin dan ganin abin da
take ma
ihuu.....
.
Cikin ruďewa ta isa gaban gadon tana fadin ke
lafiya, ihun me kikeyi,
Fareedah ta kasa magana sai nuna salma takeyi
da hannu
tana kuka sosai,
a firgice oyizah ta fara girgiza salma tana kiran
sunanta, wani irin ihu ta saki haďe da zama a kasa tana
faďin
wayyyo salma,
da gudu alhj basheer ya shigo ďakin yana faďin me
ya faru,
oyixah cikin ihu tace salma, salma--- yace salma me, tace
salma ta mutu alhj,
karasawa gaban gadon yayi kirjinshi na bugawa da
karfi ya
ďagota yana dubata,
sakinta yayi da ya tabbatar bata rai ya shiga fadin innalillahi
wa inna ilaihir rajiun,
oyizah ta mike kamar zararriya tace alhj ka
tasheta wallhy
karka bari ta mutu,
wayyyo na shiga uku na lalace, alhj basheer ya daka mata tsawa yace wani irin
hauka ne
wannan, waye ya isa da dawo da matacce,
oyizah ta kara rusa ihu tana faďin wallhy sai ta
dawo salma
bazata mutu yanxu ba, tsaki alhj basheer yaja ya tashi ya fita daga ďakin
hankali
tashe,
ihun suka cigaba dayi ita da farida suna kuka suna
jijjiga
salma suna faďin ta tashi, Ihun da sukeyi ne ya janyo hankalin Afeeyah dake
zaune
suna karyawa ita da Affan,
da sauri ta mike tace ya karasa bari ta duba taga
ihun me
akeyi, tana fita tayi hanyar dakin mummy dan nan takejin
ihun,
sankarewa tayi da ta shigo dakin ta hango salma
kwance
inda ta shimfida wannan farin kyallen,
innalillahi kawai take maimaitawa a zuciyarta, sam ta kasa karasawa gurin saboda tsoro,
a zuciyarta tace yanzu da ni ce zan mutu, meyasa
matar
nan takeso ta kashe ni,
wani irin kuka ta fashe dashi ta ruga dakinta da
gudu a zuciyarta tana dana sanin sa farin kyallen a gurin,
da tasan na mutuwa ne da ta daukeshi ta konashi
bata
shimfiďa wani ya hau ya mutu ba,
kuka sosai takeyi tana fadin shikenan nayi kisan
kai, da sauri Affan ya matso kusa da ita yana
tambayarta
abinda ya faru,
bata bashi amsa ba ta shige can cikin daki ta
dauki wayarta
ta kira kaka liman, ringing biyu wayar tayi ya dauka,
cikin muryar kuka ta gaisheshi ya amsa yace lafiya
me ya
faru, ta kara fashewa da kuka tace kaka nayi kisan
kai,
wallhy bansan abun mutuwa bane, na dauka wani tsafin
tayi dan ta nakasa mu ashe na mutuwa ne, kaka
liman yace
nutsu ki fada min komai yadda yake dan bana
fahimtar abin
da kike fadi, nan ta tsagaita kukanta ta faďa mishi duk abinda
ya faru,
kaka liman yayi ajiyar zuciya yace kwantar da
hankalinki
Allah baya kama mutum da laifin da bai sani ba,
lallai Allah na tare dake Afeeyah shiyasa har ya nuna miki
wannan
mummnan alamarin ya kuma baki basirar ki mayar
mata da
kaidinta,
wannan aya ce Allah ya saukar gareta in har tana da
hankali,
har gurin Allah baki da laifi dan ba ke kika kasheta
ba
uwarta ce ta kasheta,
ki dage ki cigaba da addu'a saboda yanzu ne zata kara
karfin tsafinta in har tasan kaikayi ne ya koma kan
mashekiya,
Afeeyah ta share hawayenta tace to nagode kaka
dan Allah
ka cigaba da yi min addu'a dan wallhy abubuwan tsoro suke
bani,
kaka liman yace babu komai jikata addu'a kullum
munayi
saidai akara bude wuta, Allah ya dauraki bisa
kanta, Afeeyah tace ameen sannan ta kashe wayar ta fita
ta wuce
gurin gawar salma....
Kafin karfe 10 angama shirya salma cikin suturarta
za'a
kaita gidanta na gaskiya, har lokacin oyizah bata bar ihu ba sai sambatu
takeyi tana
fadin wallhy babu inda za'a kai mata ya, babu
wanda ya isa
yaje ya binne mata 'ya a rami,
sosai ta fita hayyacinta tun kukan na fitowa har ya daina
fitowa,
dakyar aka fita da gawar salma daga gidan, sai da
oyizah
ta suma sai uku saboda tashin hankali,
tana farfadowa ta shiga tsine ma mutanen gurin tana fadin
ita fa yarta bata mutu ba dan ko ciwon kai batayi
ba,
Da mutane suka ga abin nata jahilci ne sai suka
watse suka
barta da kukan takaici, Bayan azahar esther ta kara kiran oyizah,
cikin kuka oyizah ta ďauka tana faďin esther salma
ta mutu,
batayi ciwon komai ba, ko mura ba tayi ba lafiya
lau muka
rabu jiya da daddare,, esther tayi dariya tace kin iya acting oyizah halan
kina cikin
taron mutane ne,
oyizah cikin ihu tace wane irin acting ina fada miki
yau da
safe mun tashi ba salma shine har kike dariya, esther tace to ay abin naki ne,
ki bada yarinya da hannunki sannan kizo kina
kuka,
oyizah ta zaro ido tace wace yarinya,
esther tace salma mana,
salma kika kawo jiya, kinsan kuwa saboda hakan da kikayi har mukami
aka kara
miki saboda kin kawo yarki wacce kika fi so dalilin
da yasa
na kara kiranki kenan dan inyi miki albishir,
oyizah ta saki wata kara mai rikirtarwa ta mike ta shige ďaki
tace esther jinin salma kuka sha,
esther tace wai ko kin haukace ne,
har kiranki fa nayi da safe kikace kina sane kika
bayar,
oyizah tace wayyyo na shiga uku, ni ba salma na bayar ba Afeeyah na bayar, ya
za'ayi in
bada salma,
esther tace ha'a to ya akayi muka ga salma,
oyizah tayi wurgi da wayar hannunta ta yaye zanin
gadonta, nan tayi arba da farin kyalle,
cikin firgici ta fara shafa kyallen tana fadin ya
akayi wannan
kyallen yazo nan gurin, waye ya kawo wannan
kyallen nan,?
waye ya kashe min salmata ta fadi cikin karaji,? da sauri farida ta shigo dakin ta riketa tana
rarrashinta tace
mummy dan Allah ki daina wannan ihun kinga
mutane suna
ta kara yawa,
oyiza ta hankaďa ta tace sun ci kutumar ubansu mutanen,
nan ta fara zage2 tana tsinewa mutanen da suka
zo mata
gaisuwa cikin ficewar hayyaci,
saida farida ta kirah alhj basheer yazo ya lallabata
da kyar sannan tayi shuru tana ajiyar zuciya,
gaba ďaya ta dauki tunaninta kacokan ta maida
shi gurin
gano yadda akayi abin da ta shimfiďa ma Afeeyah
ya dawo
dakinta, yanzu su chummy basuyi ma diyarta lamuni ba
suka zuke jininta ba tare da sun tambayeta ba,
lallai sun taro match dan wallhy sai tasan yadda
akayi
wannan kyallen ya dawo dakinta sannan kuma sai
ta nuna ma su chummy bacin ranta,,
Tun ranar da salma ta mutu nutsuwa tayi ma
oyizah
tawaye,
kullum cikin mafarke2 take tana bakin cikin yadda
akayi aka bada ďiyarta a cikin kungiyarsu ita kuma shegiyar
kungiyar
mai lakabin sabo da kaza baya hana a yanka ta, in
ba haka
ba ay sunsan yadda takeson yayanta kamar yar
ranta, a ranar da akayi uku ne ta fara shirin zuwa gurin
meeting
dan ta warware musu kuma a binciko mata dalilin
da yasa
wannan farin kyallen ya koma ďakinta.....

RABO AJALI
52 TO 55
.
BY SULAIMAN BOMBOY.
.
.
Karfe biyun dare suka hadu a gurin meeting kamar
yadda
suka saba,
oyizah na zaune gaban chummy bayan ta gama
masifarta
sai cika takeyi tana batsewa, Chummy ta dafa kanta tace oyeee naji duk bayanan
ki
, kuma na fahimci fushinki, amma kinsan mu nan
duk
wanda aka kawo baya tafiya ba tare da munsha
jinin shi ba ko,
mistake din daga gareki yake tunda ke kika
shimfiďa farin
kyallen,
oyizah cikin fushi tace ba a dakina na shimfiďa ba
my lord a dakin yarinyar da na bada anan na shimfiďa
bansan yadda
akayi ya dawo ďakina ba,
alhj sambo ya kalleta yace haba oyizah dan kin
bada yarki
daya shine kike ta wannan fushin, ni yayana biyu na bayar da kannena biyu da nake
matukar
so,
a hassale oyizah tace abin da kake nema ne dole
sai kayi
wannan sacrifice din, ni ay na riga na bada nawa wannan kyauta na
bayar
saboda kungiya taji dadi,
esther tace calm down oyee,
chummy tace barta ta cigaba,
ta manta duk abinda kungiya tayi mata

Please Login or Register in order to submit comment