Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waya dan naga sauri
kakeyi,, ya
ciro card dinshi ya bata itama ta bashi nata sukayi
sallama
ta wuce, mota ya shiga ya kalli Amirah dake gaba ya waiga
ya kalli
Afeeyah da ta cika tayi famm yace juyin mulki akayi
kenan,
ke Amirah koma gurinki itama ta dawo gurinta,
Amirah ta buďe kofar zata fita Afeeya tace saidai fa mu
zauna tare a baya, amirah tace kaji ko yaya, wallhy
tun
ďazu nake ce mata ta dawo nan taki,
kallonta yayi ta mudubi yayi dariya yace amirah
shigo muje, suna isa kofar gida ta buďe motar ta shige ba tare
da tabi
takan kayan da ya siyo musu ba,
Amirah ta kwashi nata kayan ta shige gida itama,
jabeer ya
gyara parking ya kwaso kayan ya fito dasu ya shiga
gidansu,
kwance ya sameta can karshen gadon hajja tayi ruf
da ciki
hajja na mata magana tayi banza da ita,
jabeer ya zauna bakin gadon ya gaida hajja ta amsa tace
yau kuma me kayi ma mutuniyar taka,
jabeer yayi dariya yace wallhy babu abinda nayi
mata
rigima ce kawai, Afeeya ta ďago idonta a kankance
tace har kana wallhy,
ya kalleta yace to me akayi,
tace nima bansani ba, ta mayar da kanta kan katifar
ita
kanta bata san me zata ce ya mata ba ita dai tasan
taji masifaffan zafin ganinshi da tayi da wata,
juyin duniya yayi ta faďa mishi abinda yayi mata
amma
sam taki ďago kai ma bare ta bashi amsa,
hajja taja tsaki tace tashi ka tafi ka rabu da ja'ira da
kanta zata nemeka, in ba iskanci ba babu abin da aka ma
mutum
ya hau fushi, to in kin ga dama ki fashe,,
jabeer zaiyi magana ya ji wayarshi na ringing, ya
mike da
sauri yace hajja dan Allah ki rarrasheta kafin na dawo tun
dazu Affan ke jira na, hajja tayi tsaki tace ni ban iya
wacce
ka iya ba, ya fita yana dariya. ..
Sai bayan isha suka rabu Affan ya wuce gida,
ya na sa kafarshi cikin gidansu yaji muguwar faduwar gaba,
wucewa ciki yayi a hankali jikinshi a mace ya shiga
dakin
mahaifiyarshi,
zama yayi ya dafe kanshi yana jiranta dan a
tunaninshi tana bayi ne,,
wani irin ihu yaji mai firgitarwa ya mike da sauri
yana kasa
kunne yaji daga inda ihun ya fito,
kafa kunnenshi yayi a jikin toilet yaji ba alamar
mutum a ciki, umma... umma.. ya kira sunanta sau biyu yaji
shuru
ya tura bayin,
juyawa yayi da sauri da yaga bata yana kwala
kiranta,
muryoyin mutane ya dinga ji a can saman gidansu gurin
shan iska,
a hankali ya karasa gurin yana leke a tsorace
saboda
muryoyin da yaji harda ta maza a ciki,
wani razanannan ihu ya saki haďe da faduwa kasa sumamme sakamakon abinda idanuwanshi suka
gani.....
Mrs tijjani shattima....
[5:04PM, 20/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣9⃣ By
Aysha Ya'u Kurah
A gigice oyiza da wasu maza suka saki zeenatu da babu
alamar numfashi a tare da ita ta faďi timm a kasa,
kan Affan sukayi da gudu oyizah ta ďago shi cikin
tashin
hankali tana faďin shikenan asirina ya tonu, na
shiga uku na lalace, wani bakin kato ya yarda wuka da farin
kyallen
hannunshi yace yanzu ya zamuyi kenan, dayan
cikin
dakewa yace mu gama da mamanshi sai mu dawo
kanshi, oyiza ta girgiza kanta tace Nooo mu fara dashi
tukunna
saboda kar ya farfaďo ya tona min asiri,
bakin katon da naji sun kira da "BULADUNA" yace
yanzu me
kike so mu mishi, oyizah ta runtse idonta a zuciyarta tace
"help me my lord", cikin mintina uku dabara tazo
mata ta
mike da sauri tace ku kama min shi,
cikin rashin fahimta sukace ina zaki kaishi, ta nuna
kasa da hannunta tace anan zai karasa, kunga babu wanda
zai
zargeni za'a ayi tunanin faďowa yayi by mistk,,
A tare suka haďa baki sukace Good idea, gaskiya
oyee u
are very sharp shiyasa kungiya take ji dake, tayi murmushi
tace "Lts make it snppy", kar wani yazo ya cim
mana thou
nasan ba kowa a gida,
cikin rashin imani da rashin ganin tsawon ginin
bene hawa huďu suka wurgo Affan ta kai,,
su kansu saida suka runtse idonsu saboda ganin
tsayin
gurin amma dayake zuciyarsu a kangare take nan
da nan
suka sake suka juyo gurin farin kyallen da zeenatu take,
a firgice suka haďa baki suka ce ina ta shiga,
oyizah ta kwalalo ido tana duba ko ina a gurin
amma
basuga koda sawun kafar zeenatu ba bare ita,,
hankalinsu yayi masifar tashi suka shiga duba ko'ina na cikin
gidan
amma basuga zeenatu ba, oyizah ta buga tagumi
tace to
ina ta shiga, bana tunanin da kafarta ta tashi
saboda ko sanda Affan ya ganmu Kurwarta na gurin chummy,
to waye zai dauke gangar jikinta? Buladuna yace
oyee kin
tabbatar babu kowa a gidannan,
tace babu kowa,
su farida sun fita sannan na aiki mai aikinta guri mai nisa I
don't think ta dawo kuma ko ta dawo ay baza ta
hawo nan
ba, dayan cikin kosawa yace mu tafi kawai tunda
mun
samu abinda mukeso me zamuyi da gangar jiki, buladuna
yace hakane, lets go oyee,
cikin rashin kuzari ta bisu kan buzun tsafinsu suka
bace
daga gidan..
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da chummy tace
kurwar zeenatu ko 5mints baiyi ba ta nemeshi ta
rasa,
oyizah idonta yayi jawur tace to ina yaje,? kodai ya
koma
jikinta ne, shikenan asiri na ya tonu,,, Chummy tace calm down oyee, duk inda take
yanzu
hankalinta baya jikinta, saidai tana tare da wacce
take mata
addua yanxu haka, wannan dalilin ne kadai ya
hanani dawo da ita, amma zansa suyi nesa sosai kuma zanyi
mata abin
da har ta mutu bazata taba motsi ba bare ta tashi ta
dawo
ta tona mana asiri,
oyizah ta dafe kanta tace my lord wacece wacce suke tare
yanzu ďin,
chummy tace na kasa gane ko wacece, but koma
wacece
tanada kusanci da gidan,
oyizah ta shiga kogin tunani, a zuciyarta tace to wacece
wannan za ta dauke zeenatu, ita dai tasan babu
wacce keda
kusanci da zeenatu sai Abida to ko Abida ce ta
dauke ta,
wata zuciyar tace to ta ina abida ta shigo gidan da daddare,
ta dinga tunanin da baida amsa ta kara kallon
chummy cikin
tsananin damuwa tace my lord ya akayi har ta
samu damar
guduwa,, Chummy bata iya bata amsa ba ta kalli wani katon
glass din
da ta tura Fanne da Fanna tayi kwafa cikin takaicin
abinda
sukayi mata,
dariya fanne tayi tace munci dubu sai ceto, sai dai ki rufemu
anan dan wallhy indai muna bude babu wani rai da
zai kara
salwanta a gurinku,
oyizah taji kamar zata shakesu sabo takaici amma
babu hali,
ta kalli chummy tace my lord ya kamata a gama da
yarannan if not zasu dinga bata mana aiki,
chummy tayi murmushin mugunta tace very soon
oyee,,,
saida suka gama tsaface tsafacensu sannan kowa ya bace
itama '"chummy" ta tafi gurin jigajigan matsafa na
gaba da
ita dan samo sababin lakanin tsafi...
Mrs tijjani shattima...
[8:41PM, 20/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Tsaye take cikin zauren gidansu tana leken kofar
gidansu
jabeer ko zata hango shi,
tun bayan magriba take tsaye a gurin amma har
bayan isha'i bata hango inuwarshi ba,
juyawa tayi zata koma ciki kamar zatayi kuka taji an
rike
hannunta ta baya, tsayawa tayi ba tare da ta juyo
ba
hawayen da ya gama taruwa a idonta ya fara zubowa,
a hankali ya juyota ya ciro wayarshi yana haska
fuskarta,
murmushi yayi da yaga hawaye akan kumatunta
yasa
hannu ya fara share mata a hankali yace shikenan ke kuka
bashi da wuya a gurinki,
da abun kuka da wanda ba na kuka ba duk sai kin
musu
kuka, yanzu faďa min abinda aka miki,
ta kara fashewa da kukan da daga ji na shagwaba ne tace
ba kai bane--- sai kuma tayi shuru,
yayi dariya yace ba ni bane mee? Ta kauda kanta
tace ban
sani ba, ya juyo da kanta yana kallon cikin idonta
yace fadamin laifin da nayi in hukunta kaina yanzun
nan,
ta turo baki tace tun ďazu nake jiranka anan kuma
kasan
zan jiraka shine ka tafi gurin wannan kawar taka
mai kama da nunar rana,
jabeer ya kwashe da dariya yace wacece me kama
da nunar
rana?
Afeeya ta kara turo baki tace ohoo ka fini saninta,
jabeer ya kasa tsayar da dariyarshi ya kamo hannuwanta ya
hadesu guri ďaya ya sa bakinshi ya sumbace su a
hankali
haďe da lumshe idonshi, magana ya fara yi ba tare
da ya
bude idanuwanshi ba yace gurin Affan naje Afee, kinsan
babu abinda da zai hanani zuwa gurinki da wuri sai
ganin
Affan,
ta zare hannunta daya ta kai saman idonshi ta fara
jan zara zaran gashin idonshi tace ni dai ban yadda ba ka
fada min
gaskiya ko in tura hannuna cikin idonka,
ya buďe manyan idanuwanshi da sauri yace ki
makantar
dani kenan, tace eh mana sai inga da idon da zaka dinga zuwa
yawo,
yace haba Afee nah yanzu in kika makantar dani
wacece
zata aureni,
ko bakya so ki samu anty wacce zata dinga kula dake,
Afeeya tayi narai narai mayatattun idanuwanta tace
yaya
jabeer in kayi aure shikenan zan daina ganinka,
zaka daina
zuwa gurina,? zaka daina kulawa dani ko?, ya janyota jikinshi yace babu abinda zai hana
jabeer kula da
Afeeyah in dai yana raye,
bana fatan abinda zaisa rana ta faďi har inyi bacci
batare
da nasaki a idona ba, ta kara narkewa a jikinshi kamar karamar yarinya
tace to ay
in kayi aure zan daina ganinka haka hajja ta ke
cemin
kullum, da karfi yace inji hajjan, afeeyah ta gyaďa
kanta tace eh mana kullum sai ta faďa min da daddare
wai in rage
sabon da nayi da kai saboda zan sha wahala in
kayi aure,
ay nasan bazaka bari in sha wahala ba ko?
ya gyaďa mata kanshi zuciyarshi na kara zurfi a cikin
soyayyar afee,
da afeeya tafi haka da babu abinda zai hanashi
faďa mata
abinda yakeji game da ita,
girgizashi tayi yayi firgigit, tace to karkayi aure ko kuma ka
aureni sai mu zauna gida ďaya ka dinga goyani
muyi bacci
tare ko,
ya kalleta sosai yace kina sona?
ta rufe fuskarta tace sosai ma, yayi dariya ya buďe fuskarta yace da gaske kikeyi,
tace
dagaske yayana, to in ban soka ba wa zan so,
kaima ay
kana sona ko?,
yace fiye da yadda nake son kaina wifey na, ta daka tsalle tace bari inje In faďa ma hajja ta daina
min
gori, yace muje dai mu faďa mata tare ko,
tace eh hakane ta kamo hannunshi cike da murna
suka
shiga ciki... Sai goma saura ya fito daga gidansu afeeyah, zama
yayi
kan dakalin gidansu yana kiran wayar Affan dan
ya fito su
ďan rage dare,
sau huďu yana kirah ba'a ďauka ba, mikewa yayi a ranshi yace may be yayi bacci ko
kuma yana
can suna hira da umma,
dakinshi ya wuce ya kwanta yana tunanin Afeeyah,
Allah ya sani yana matukar kaunar afeeya, hakuri
kawai zaiyi ya jirata ta gama sec skool ya aureta ya maida
ita
mallakinshi ya bata duk wasu nau'in kulawa da
gata marasa
yankewa,
da wannan tunanin bacci mai cike da mafarkai yayi awon
gaba dashi....

Posted by Sulaiman Bomboy
Under: RABO
[10:14AM, 21/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆21 By
Sulaiman Bomboy
Karfe 6 na asuba Alhaji basheer ya iso gida a
gajiye,
bacci sosai yakeji dan haka ya wuce ďakinshi don
ya
kwanta ya samu isashshen bacci, ya yi matukar
mamakin
rashin ganin zeenatu ta fito tarbarshi kamar
yadda
ta saba,
amma sai ya share da tunanin ko itama bacci ne
yayi gaba
da ita ko kuma dai wani abun daban amma haka
nan
zeenatu bazata taba kin fitowa tarbarshi ba ko da
kuwa
bazaii kulata ba, da wannan tunanin bacci ya
ďaukeshi...
Ihu ya dinga ji kamar a cikin mafarki, a hankali ya
buďe idonshi yaji bugun kofar da ake
ma
ďakinshi yaki tsagaitawa, da sauri ya diro daga
kan
gado
jikinshi na rawa ya bude kofar,
Salma da farida ya gani tsaye suna ihu suna kuka
suka ce
daddy Affan-- Da sauri ya katsesu yace me
yasamu
Affan
din, kasa bashi amsa sukayi sunata nuna
hannunsu saitin
kofa, da gudu ya fita waje ya'yan hanjinshi sai
kaďawa
sukeyi,
turus ya tsaya ganin masu aikin gidan da oyizah
tsaye kan
affan suna kuka jini ko ta'ina a kasa da kanshi,
wani irin ihu alhj basheer yayi haďe da karasawa
yana
girgizashi yana kuka, da kyar yake iya hado
sunan
Affan ya
kira saboda tashin hankali, daukarshi yayi bai
kula
da jini da
fashewar da tsakiyar kanshi yayi ba ya turashi
cikin mota,
binshi oyizah tayi tana kuka tace alhj ina zaka
kaishi, ya
riga fa ya mutu,
alhj basheer ya watso mata ashariyar da baisan
yadda akayi ya fadeta ba ya shiga mota yayi
asibiti da
affan,
likitoci kansu sun tsorata da ganin Affan, wani a
cikinsu
yace ranka ya dade wannan ay ya mutu,
alhj basheer yayi kanshi yace ubanka ne ya
kasheshi?
Doctorn yayi baya yace sorry alhj,
nan likitoci sukayi caa akan Affan duk da bawai
sun sa ran
yana raye ba saidai dan bala'in da alhj basheer ke
musu, Cikin ikon Allah karfe 2 na rana Affan ya
fara motsa
hannunshi, cikin mamaki doctor musa ya kura ma
hannun
ido ko gizau yake mishi, ganin ba gizau bane yasa
shi fita
kiran sauran likitocin cikin murna, alhj basheer dai
binsu yakeyi kamar zararre yana
fadin bai
mutu ba ko, dr musa ya gyada mishi kai kawai
suka wuce
dakin da Affan yake,
sai hudu suka fito kowa yayi hanyar office dinshi,
doctr musa ya kalli alhj basheer yace ka kwantar
da
hankalinka alhj muje office inyi maka bayani,,
alhj basheer ya bishi office din ba tare da ya ce
uffan ba,,
Doctor musah ya kalli alhj basheer cikin damuwa
yace alhj ka saurareni da kyau kuma duk abinda
zan faďa
maka
kasani bani nayi ba kuma ba wani bane yayi Allah
subhanahu wa ta'ala shine ya jarabceka kuma ya
jarabci
danka, saboda haka dan Allah alhj kayi tawakkali
saboda
cuta ba mutuwa bace,
alhj basheer ya share hawayen da ya zubo a
idonshi yace
faďamin komai doctor, fadamin abin da ya sami
Affan,, doctor musah ya mika mishi takardun
hotunan
kwakwalwar
da sukayi ma Affan,
ya karba hannunshi na rawa yace bazan gane
komai a ciki
ba doctor kayi min bayanin komai da baki, doctor
musah yayi ajiyar zuciya yace alhj, Affan ya
samu
"brain disorder" abin da yabamu mamakin anan
shine duk
girman ciwo da karfin buguwar nan bashi ya taba
kwakwalwar shi ba har yasamu "mental illness"
sai wani
abun daban,,,,
ya mika mishi wata takarda yace wadannan sune
ciwukan
da kwakwalwar shi ta samu
"Psychological trauma": wannan cutar may be
triggered by P.T suffered as a
child,
kamar "severe emotional", physical, or sexual
abuse;"
abinda ke kawoshi kuma shine, "a significant
early
loss", kamar the loss of a parent; and neglect...
sai kuma
"Environmental stressors":
"itama ana samunta ne a shock din mutuwa ko
macen da
aka saka, ko kuma dysfunctional family life,
sacking 4rm jobs or schools, and substance
abuse
-- it can
trigger a disorder in a person who may be at risk
for
developing a mental illness."
Kaga kenan akwai abinda ya gani ko kuma ya
sameshi cikin
waďannan abubuwan amma sam ciwon kanshi
bai
da alaka
da cutar,
Alhj basheer cikin tashin hankali yace yanzu
doctor
kana ganin Affan zai samu lafiya nan kusa,?
doctr musah cikin tausayawa yace sauki na gurin
Allah alhj,
in yazo yanzu baiyi gaggawa ba sannan in baizo
yanzu ba
baiyi jinkiri ba saboda Allah ne kadai yake iya
bada sauki a
lokacin da yaso,
sannan ina tsoron sanar dakai mostly mental
illnesses irin
wannan are caused by a combination of factors
and cannot be prevented so easily, saidai a dage
da addu'a
saboda
babu abin da ya gagari Allah kuma babu wanda
yasan gaibu
sai Shi..,
da sauri oyizah da tun shigewar su office din
doctor ta iso
ta juya cikin jin dadin ciwon da taji ya sami Affan
da
kuma
firgicin jin affan nada rai kuma zai iya samun
sauki
a koda
yaushe, kuma tasan yanzu alhj na dawowa zai
fara
tambayarta ina
zeenatu? Kuma me ya samu Affan me ya gani har
ya
haddasa mishi wannan cutar,
fita tayi daga asibitin da sauri cikin tsananin
tsoron abinda
zai je yazo, bata zame ko ina ba sai gurin
tsafinsu.....
..
[2:47PM, 22/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 22 By
Sulaiman Bomboy
Alhj basheer ya fito daga office din doctor Musah
idonshi
jajur saboda kukan da yaci, dakin da aka kwantar
da Affan ya shiga ya zauna gefenshi yana zubar
da hawaye
yana ta
tunanin yadda akayi har Affan ya faďo daga
wannan saman
nisan gaske, to wai ma me Affan ya gani da har
ya
firgita shi haka,
da sauri ya mike da ya tuno da tun asuba baisa
zeenatu a
idonshi ba, kuma ace har Affan baida lafiya
batazo
inda
yake ba, girgiza kanshi yayi a fili ko dai wani abu
ne ya
samu zeenatu, gabanshi ya faďi sosai da ya tuno
da
kalaman doctor,
jikinshi ya fara rawa ya murda kofar dakin da
affan
yake ya
fita da sauri yana fadin innalillahi a zuciyarshi, da
taimakon Allah ya isa gida, a waje yayi parking
motar
saboda tashin hankali,
yana shiga ya wuce dakinta,
babu inda bai duba ba a ďakin bai ganta ba, cikin
kiďima ya fito yana haďa sunayen mutanen gidan
yana kirah
da karfi,
da gudu suka firfito, oyizah da bata fi minti 5 da
dawowa
daga gurin tsafinsu ba ta matso kusa dashi tace
lafiya alhj, ya nuna dakin zeenatu yace ina
zeenatu take,
fareeda da
salma suka ce daddy tun jiya bamu ganta ba,
oyizah tace ni rabona da zeenatu ma ay tun ranar
da zaka
tafi mukayi maka rakiya, cikin karaji yace to ina
ta shiga,
oyizah ta dafashi tace calm down my dear muje
ka
huta ka
kira can gida kaji ko tana can,
cikin damuwa ya kalli fuskar oyizah, nan ya tsinci
kanshi da kasa yi mata musu ya bi bayanta suka
wuce gurin
dinning,
saida ta bashi abincin da ta haďasu da sinadaran
asiri
sannan ta zauna gefenshi tana matsa mishi kafa,
kallonta yayi har lokacin fuskarshi dauke da
damuwa yace
safiya ya
akayi Affan ya faďo daga wannan saman mai
nisa,
sannan me ya faru a gidannan da har ya haddasa
tabuwar
kwakwalwarshi, oyizah ta fara share hawayen
karya tace alhj nima
ban sani
ba, kowa na bangarenshi ya za'ayi insan abinda
ya
faru,
Allah sarki Affan yanzu brain dinshi ya samu
matsala, murya a dashe alhj basheer yace eh
safiya, kuma
bawai
fadowar da yayi bane ya taba brain dinshi,
hankali
tashe
kamar gaske tace to me ya sameshi,
nan ya kwashe abinda doctor ya faďa mishi ya
fada mata,
wani irin kuka ta fashe dashi harda zama a
dirshan
a kasa
tana faďin mun shiga uku, yanzu shikenan Affan
ya
haukace,
alhj basheer ya shiga rarrashinta yana faďin
addu'a zamuyi
mishi safiya,
dakyar oyizah tayi shuru tace ni alhj babban
tashin
hankalina shine rashin ganin zeenatu,
Allah yasa ba wasu mugayen bane suka saceta
suka wurgo Affan daga sama, hankalin alhj
basheer ya tashi da
jin
furucin oyiza,
ya kalleta yace da zeenatu tayi musu me zasu
saceta,
oyizah tace Alhj ka manta muna cikin zamanin da
ba sai
kayi ma wani komai ba zai maka mugun illah,
nidai
gobe
kabi jirgin safe kabar kulawar Affan a gurina kaje
can
cameroon ka dubata dan wannan abun yafi karfin
waya,
alhj basheer ya share zufar goshinshi yace kin
kawo
shawara mai kyau safiya, amma--- ta katseshi
da
sauri tace
na fada maka zan kula da Affan fiye da yadda
zaka kula
dashi, kai dai ka tafi nemanta dan hakkinta na
wuyanka,
cikin jindadin tsararrun kalaman oyizah alhj
basheer yace
nagode sosai safiya, Allah ya kaimu goben, tace
ameen
yanzu kaje ka kwanta ni zan tafi gurin Affan din
in
ta kama
ma sai in kwana, alhj basheer yaji dadi sosai a
ranshi ya
dinga shi mata albarka.. Ďaki oyiza ta wuce
zuciyarta wasai yanzu gida zai
dawo
karkashin ikonta,
wani kulli mai kyalli ta kwance ta fito da babyn
"Mutum
mutumi" an soke kanshi da mashi, Kallon babyn
tayi hade
da kwashewa da dariya tace Affan kai da
warkewa
har
abada, haka zaka dawwama cikin hauka har ka
mutu kamar
yadda babyn nan take haka zaka kasance sai
yadda nayi
dakai,
ta mike ta daga karkashin gadonta inda ta dade
da
haka
wani ramin sihiri ta kara tona gefen ramin ta kira
sunan Affan sau uku sannan ta tura babyn ciki
tana
dariyar
mugunta,
ta kalli wata laya ta kara saka wata dariyar tace
wannan
naki ne zeenatu, ba yanzu zanyi aikin ba sai an
gaji da
nemanki, ta mayar da layar cikin daurinta sannan
ta
loda
magunguna hade da turarukan tsafi a jakarta ta
shirya
wucewa asibitin.. Tun asuba jabeer ke neman
wayar Affan ba'a
dauka ba,
daga karshe ma jin wayar yayi akashe,
gurin karfe 8 yaso shiga ya dubashi sai wani
muhimmin aiki
ya taso mishi a office ya wuce, bai dawo gida ba
sai bayan magriba, saida ya fara
shiga
gurin Afeeyah suka dan taba hirah sama2 sukaci
abinci tare
kamar yadda suka saba sannan ya mike jikinshi a
sanyaye saboda rashin jin muryar amininshi yau
tru out,
abinda bai taba faruwa ba tun tasowarsu dan ko
tafiya
dayayayi to suna manne a waya, sallama yayi
ma
hajja da
afeeyah ya fita ya isa kofar gidan su Affan, tun a
gate mai gadi ya sanar dashi abinda yake
faruwa,
kiriss ya rage jabeer ya faďi saboda tashin
hankali,
da kyar
ya daidaita kanshi ya karasa cikin gidan, babu
wanda ya samu a ciki sai farida dake waya tana
kyakyata
dariya,
murya na rawa yace Fa-re-da- wani asibiti aka
kwantar da
Affan, sai da ta kalleshi sama da kasa sannan ta
ajiye wayarta, cikin masifa tace haddar sunan
asibitoci
aka kawo
ni yi duniya,
cikin bacin rai jabeer yace "oops" na manta fa
da'kikiya
kamarki wacce bazata iya haddar sunanta ba
bare asibitin
da aka rubuta shi da turanci saboda masu ilimi
su
gane,
farida ta mike a fusace zata fara bala'i karar
bugun
kofa ya
hanata, jabeer ya kalli daddy suka gaisa sama2
yace daddy
wani
asibiti affan yake, daddy yace muje jabeer nima
can
zanje
nan "Arewa surgery" ne,
jabeer ya harari fareeda ta gefen ido yayi kwafa
ya bi bayan
dady...
.: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 23 By
Sulaiman Bombou
Kuka sosai jabeer yayi da yaga yadda Affan ya
koma,
zama yayi gefenshi yasa hannunshi cikin nashi
yana karanto adduo'i yana tofa mishi,
oyizah ta harareshi tace dan Allah malam ya isa
haka kar
miyan ka ya jikashi ya farka lokacin farkawarshi
baiyi ba,
daddy yace addu'a fa yake mishi safiya, oyizah ta
marairaice tace doctors ne suka hana alhj
nima
dazu ina mishi addu'a suka hana ni,
jabeer ya waigo ya kalli daddy idonshi a kumbure
yace
daddy ina umma,? alhj basheer yayi jugum
sannan ya fada ma jabeer
komai
game da zeenatu,
a rude jabeer ya mike yace daddy shine ba'a
dauki
mataki
ba tun dazu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
alhj basheer yace nasan bazata wuce gida ba
gobe
da
sassafe zan tafi,
jabeer yace da nan ya kamata a fara daddy, in
har
bata nan sai a tafi can,
oyizah ta harareshi ta wutsiyar ido sannan tace
hakane alhj
kai kaje cameroon din mu sai mu fara nemanta
anan ko
jabeer, jabeer bai kalleta ba yasa kai ya fita
zuciyarshi
kamar zata
buga saboda tashin hankali..
Washe gari tun asuba jabeer ya bar asibitin ya
isa
gida,
nan suka shiga binciken duk gidajen aminansu na
kusa da
na nesa shi da Abida da tun jiya bata runtsa ba
da
jabeer
ya faďa mata wannan mummunan labarin,
babu inda basu shiga ba amma babu labari,
jabeer ya zarce gurin yan sanda ya sanar musu
sannan ya
koma asibiti,,
yana shiga ya tarar da oyizah zaune gefen Affan
tana
shaka mishi turare a hancinshi, tana ganin jabeer
ta
mike da sauri tace jabeer ka dawo,
kaga turare ne aka bani ance yana healing ciwon
kwakwalwa in ana shakawa mutum shine nake
gwada
mishi,
jabeer yace uhum kawai ya zauna gefenshi yana
kallonshi
yana mishi addu'ar da oyizah ta tsani ganin ana
mishi,
a zuciyarta tace tabbas in bata katange Affan
daga
adduo'in
mutane ba wata rana tana zaune adduar zatayi
tasiri
akanshi,, ta kalli Affan tayi kwafa ta maida
turaren
jaka ta
fita daga asibitin..
A can cameroon kuwa tashin hankalin da suka
shiga bazai misaltu ba,
dan kuka sunci shi da aka gama duba guraren
dangi ba'a
sameta ba,
alhj basheer kanshi kasa tsayar da kukanshi yayi
yanata kiran sunanta kamar zautacce yana fađin
ina kika
shiga ne
zeenatu,
da kyar Baffan zeenatu ya rarrasheshi da bashi
baki akan
suyi ta addu'a, ko gawarta ne Allah ya bayyana,
Washe gari tare da su yadikko aka taho duba
Affan,
sun jima tsaye akanshi cikin tausayawa amma fa
babu
wanda a cikinsu ya iya budar baki yayi mishi
addu'a, "saidai kawai suce sannu Affan cuta ba
mutuwa
bane, wata
rana sai labari sai kuga kamar baiyi ciwon ba,"
wadannan kalmomin su kadai duk wanda yaji
Affan baida
lafiya yake iya faďi, JABEER BARA'U DAURA shi
kaďaine yake yin addu'a
sosai
akan Affan,
hakan ba karamin ďaga hankalin oyizah yakeyi ba
dan tayi
duk wani abun da zatayi na tsafi akan jabeer
amma ta
kasa,
tabbas tasan jinin jabeer ya fi karfinta dan haka
ta
kudira a
ranta Affan na komawa gida zata hana duk wani
mahaluki zuwa dubashi bare har ya samu damar
yi mishi
addu'a,
sannan shima Affan din zata san yadda zatayi ta
daure
kafarshi a cikin gida ya zamana ko wajen gate
bazai iya taka kafarshi ba,
da wannan tunanin oyizah ta ďan samu relief...
Sati biyu suka wuce babu zeenatu babu labarinta,
haka Affan bai farfaďo ba kullum yana kwance
cikin
oxygen, Oyizah ta kalli alhj basheer da yake cikin
damuwa
har
yanxu, tace ranka ya ďade ya kamata ka cire duk
wata
damuwa aranka, duk inda zeenatu take--- yayi
saurin katseta yace na manta da batun zeenatu a
wayewar garin
yau saboda zeenatu ba yarinya bace duk inda
take
zata iya
kula da kanta koda kuwa saceta akayi,
ni yanzu ciwon Affan ne kaďai ke damuna day nd
nyt,
oyizah tayi murmushi a zuciyarta tace aiki yayi,
ta
tuno
sanda zata tura layar cikin bakin gawar "Damo"
saida ta
tsorata taso ta bar aikin, ashe nasara ne ya
hanata barinshi,,
ta kalli alhj basheer idonta ya ciko da kwalla, tace
karka
damu alhj Affan zai samu sauki tunda yana
karkashin
kulawar likitoci, zeenatu fa babu wanda yasan
inda take,
tsawa mai karfi ya daka mata yace nace ki daina
kawo min
maganar zeenatu nan gurin,
oyizah ta mike sum2 ta wuce ďaki tana kukan
munafurci.. Tsalle ta dingayi da ta shiga ďaki
murna kamar zai
kasheta,
yanzu abinda ya rage mata shine tasan inda
Affan
ya ajiye
kadarorin da alhj ya mallaka mishi....

◆◆ RABO AJALI ◆◆24
Ranar wata jumma'a bayan an sauko daga sallah
jabeer
asibiti ya wuce saboda nan ne gurin zama da
kwananshi, duk da irin kyarar da oyizah ke mishi
hakan bai
hanashi
zuwa ba,, addu'a sosai yayi ma Affan a masallaci,
yana shiga cikin asibitin ya tarar babu kowa
gurinshi kuma
yaga kamar bakinshi na motsawa, da sauri jabeer
ya naďe carbin hannunshi ya
karasa kusa
dashi, ya rike hannunshi yasa kunnenshi saitin
bakinshi,
R-u-w-a yaji yana fada muryarshi na rawa,
jabeer ya mike da azama yaje ya kira doctor suka
shigo tare
da sauri,
doctor ya gama duba Affan sannan ya kalli jabeer
yace dan
bashi ruwa kaďan,
jabeer jiki na rawa ya balle murfin Faro ya tsiyaya
kadan a
ciki saida yayi addu'a sosai a cikin ruwan sannan
ya matsa
kusa da Affan da har lokacin bai bude ido ba sai
kiran ruwa
da yakeyi, buďe bakinshi yayi zai fara zuba ruwan
aciki
oyizah ta shigo da sauri ta kabe glass cup din ya
fadi ya
fashe,
cikin masifa tace baka da hankali ne zaka bashi
wannan ruwan daga cewa a bashi,
doctr musah yace hajiya ruwan is pure ni nace ya
bashi,
oyizah ta fito da wani ruwa a cikin gora tace
wannan ruwan
alhj ya bani kafin ya tafi yace duk sanda ya
farfaďo a
tabbatar shi ya fara sha saboda ruwan addu'a ne
da ya
amsoshi daga cameroon,
jabeer da ya cika yayi famm yaja dogon tsaki ya
fita
ya bar asibitin gaba ďaya,
doctr musa ya ba oyizah da ke sharar kwallar
munafurci
hakuri yace bamu san akwai adduar da za'a
bashi
bane da
bamuyi gangancin bashi ruwa ba, tace babu
komai doctor, yanzu zan iya bashi
kenan,
doctr musah yace eh hajiya, nan oyizah tayi
murmushi ta
gefe ta zauna ta bude bakin Affan ta tsirara mishi
ruwan da yasa shi sakin razananen ihu, da sauri
ta mike da ta
tabbatar da ya hadiye ta matsa baya tana kuka
tana
fadin
doctr dubashi,
da kyar doctor musah ya samu yayi mishi allurar
da
tasashi bacci ihun ya lafa,
ya waigo ya kalli oyizah yace hajiya I think ruwan
adduar
nan yasashi ya farfado gaba daya saidai kuma
yanzu ne
za'a fara jinyar, yasa kai ya fita..

Please Login or Register in order to submit comment