Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan gawar ďanshi ne da gaske ko mafarki yakeyi,
dafashi alhj basheer yayi yana zubar da hawaye yace alhj
muje kayi signn mu amshi gawarshi muje ayi mishi sutura,
alhj bara'u bai kalleshi ba yace kaima mahaifinshi kaje kayi
signn din, Allah ya amshi bakuncinshi yana gama faďin
haka ya fita,
nurse din dake tsaye a gurin ta fashe da kuka tace alhj kuje
kawai no need, Allah ya jikanshi da rahama,
nan aka gunguro gawar jabeer aka sata a ambulance suka
wuce gida cikin jimami suna kallon alhj bara'u da ya kurawa
d.l din jabeer ido,
kallon motar aka dinga yi a layin wasu suka bita dan ganin
inda zata tsaya, motar na tsayawa a kofar gidan, alhj
bara'u ya fito da sauri ya shiga ciki,
a parlor ya tarar da Abida Amirah na tsaye a kanta da
ruwan tea da magani a hannunta, kallon Amirah yayi kamar
babu abinda ya faru yace har yanzu baki shirya kin wuce
makaranta ba,
Amirah tace nayi wanka baba yanzu zan gama in---,
sallamar su malam Atiku da wadanda suka shigo da gawar
jabeer ita ta hana amirah karasawa,
da sauri Abida ta mike tabisu da ido har aka shimfiďe
gawar jabeer a kasa,
cikin firgici ta karasa kan gawar zuciyarta na dukan uku uku
ta tsuguna ta buďe fuskar da tayi faca2 da jini, runtse
idonta tayi da sauri tana fitar da wani irin numfashi tace
nasani jabeer, zuciyata ta sanar dani, Alhamdullilah da Allah
yasa aka tsinci gawarka akan lokaci, Allah ya rahamceka
jabeer, yadda ka faranta mana kayi mana biyayya Allah ya
faranta maka a cikin kabarinka dan nan ne gidanka na
gaskiya, Allah ya sanya aljanna firdausi ta zama makoma a
gareka,
ta shafa fuskarshi a hankali tace na yafe maka,
na yafe maka jabeer,
ta mike da sauri ta wuce daki alhj bara'u ya bita,
Amirah kasa gasgata gawar tayi dan gaba daya ta kasa
fahimtar abinda ake nufi, ta kalli su alhj basheer da suke
sharar hawaye tace daddy, Abba, me ya samu yaya jabeer,
alhj basheer yace Amirah addua zakuyi mishi dan wanda ya
fimu sanshi ya karbi abinshi,
Amirah ta saki kofin hannunta ta tsuguna a gabanshi tana
kuka mai tsanani tana kiran sunanshi,
da kyar alhj basheer ya rarrasheta yasa Dayyaba dake
tsaye tana kuka ta shiga da ita ciki,
Mahmud kanin Afeeyah ya shiga gida da gudu ya ajiye
biredin da ya siyo a tsakar gida ya karasa ďakin hajja,
hajja na zaune tana gyaran wake, Afeeya kuma tana
kwance jikinta ya ďau zafi sosai saboda zazzabi, fadowa
dakin mahmud yayi, hajja tace haba mahmu irin wannan
shigowar ba sallama ay sai ka tsoratani, yace hajja motar
gawa ta asibiti na gani kofar gidan alhj bara'u kuma naji
mutane suna cewa yaya jab-- Afeeya ta diro daga kan gado
tayi ma mahmud wani irin riko tace me ya sameshi,
mahmud cikin jin zafin rikon yace ban sani ba mutane
sunce sunga an fito dashi cikin jini...
.
RABO AJALI ..
3⃣2⃣
By Suleiman Bomboy
.
Wurgi Afeeyah tayi da mahmud ta fita da gudu,
duk irin kiran da hajja take mata baisa ta tsaya ba,
da gudu ta shiga gidan ta tarar dasu baba ado zaune da
wasu mutane sunyi tagumi a bakin gate, da sauri ta karasa
kusa dashi tace baba ado me ya samu yayana?,
baba ado ya kauda kanshi da sauri yana share hawayen
dake zuba a idonshi, Afeeyah ta bar gurin da gudu ta shige
cikin gidan,
murďa kofar parlon tayi da karfi kamar zata balleta,
tana shiga ta dinga bin mutanen dake parlon da kallo,
ganin mutum kwance cikin jini a kasa yasa zuciyarta
bugawa da karfi,
a hankali ta fara motsa kafarta tana tafiya har ta isa
gabanshi,
tsugunawa tayi ta yaye abin da aka rufe mishi fuskarshi da
shi, gaba ďaya hanyoyin sadarwa na jikin Afeeyah suka
daina aiki sakamakon ganin fuskar jabeer,
kallonshi ta tsaya yi bata ko kiftawa,
alhj basheer ya taso ya karaso gurinta ya ďagota dakyar
dan jikinta a sake yake kamar wacce bata da rai,
zaunar da ita yayi akan kujera ya fara mata nasiha, ko
kaďan bataji abinda yake cewa ba idonta na kan jabeer da
alhj bara'u da mahaifinta ke kokarin ďaukarshi suyi mishi
wanka,
alhj basheer ya girgizata yace Afeeyah kina jina,
lumshe idonta tayi lokacin da aka fita da gawar,
alhj basheer zaiyi magana hajja ta shigo da gudu tana faďin
innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me yasamu jabeer alhj, na
shiga uku na lalace, alhj basheer yace dan Allah hajja kiyi
shuru kar gidan ya rikice adduarmu jabeer yake bukata ba
kuka,
hajja ta zauna tana kuka tana fadin kukan ne babu mai iya
hana shi fita alhj,
ta kalli Afeeyah da idonta ke lumshe har lokacin ta riketa
sosai ta kira sunanta har sau uku taji shuru,
ta girgizata da karfi tace ki bude idonki Afeeyah, nasan
abinda kikeji dan Allah kiyi tawakkali, kar wata cutar ta
kama ki,
dan Allah Afeey--- Afeeyah tace hajja me kika gani yanzu,
kuka nakeyi ko me, ba tawakkalin nayi ba,
me kukeso inyi, ku faďa min me zanyi yanzu hajja,, kome
kukace inyi zanyi walhy,
alhj basheer ya fita da sauri saboda kukan da yaci karfinshi
yasan sam Afeeyah bata cikin hayyacinta,
hajja cikin kuka tace addu'a zakiyi Afeeyah, addu'a jabeer
yake bukata,
Afeeyah ta bude idonta sosai tace hajja a ina zanyi adduar,
hajja ta rungumeta tana sheshshekar kuka tace a bakinki
zakiyi ta,
Afeeyah tayi yake tace hajja kunce kar inyi kuka, kuma ku
gashi kuna yi dan Allah kiyi shuru bari in shiga gurin ummi,
hajja ta rike hannunta suka shiga gurin Abida inda makota
suka kewayeta,
tana ganin Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa sai a lokacin
wasu hawaye masu zafi suka fito daga idonta,
Afeeyah tace ummi kuka kikeyi, daddy yace kar muyi kuka,
ta kalli Amirah tace Amirah dan Allah ki faďa min yadda
zanyi hawaye su fito a idona, Amirah ta fada jikinta tana
kuka sosai, Afeeyah tace dan Allah ku fadamin yadda zanyi,
zuciyata zata buga ku taimakeni inyi kuka ko zan samu
saukin nauyin da zuciyata tayi,
Alhj bara'u ne ya shigo ďakin shima idonshi jajur yace
Abida kuzo kuyi mishi addu'a an gama shiryashi,
Abida kanta a kasa tace kuje kawai rahamar ubangiji ita
kadai nake mishi fatan samu a kabarinshi, Afeeya ta mike
ta fita da gudu a tsakar gida taga gawar an shiryata cikin
likkafani,
da gudu ta karasa bata lura da mutanen da sukayi dafifi a
gurin ba ta faďa kan gawar tana shafawa,
a hankali tace yaya jabeer alkawarin da kayi min kenan,
meyasa zaka tafi ka barni, saida nace maka mu tafi tare
kaki yarda ka tafi kai kadai yanzu ka faďamin yadda za'ayi
in cigaba da rayuwa babu kai, meyasa bakayi tunanin abin
da mutuwarka zata haifar a cikin zuciyata ba, dan girman
Allah yaya jabeer ka tashi karka tafi ka barni, kai kaďai
gareni,
malam atiku ya matso kusa da ita ya dafata yace Afeeyah
Allah baya barin wani dan wani yaji daďi, Allah ba ruwanshi
da duba shakuwarku,
Allah ya kaddara--- ta katseshi ta hanyar bige hannunshi
tace wace irin kaddarace wannan, meyasa bata daukeshi
tun kafin inzo duniya ba, sai yanzu zata zo ta dauke min shi
a lokacin da nake bukatarshi,
ta mike tsaye tace abba dan Allah ka fadamin yadda zan iya
cigaba da rayuwa, kasan dai bazai yiwu ba,
malam atiku ya rungume yarshi yana kuka sosai, yace
Afeeyah nasan yadda kikeji,
ta sakeshi tana girgiza kai tace wallhy abba babu wanda
yasan yadda nakeji sai yaya jabeer,
ta kankameshi tace kai kadai kasan yadda nakeji, dan Allah
ka tashi,
duk rashin imaninka sai ka zubar ma da Afeeyah hawaye,
babu yadda ba'ayi a banbareta jikin gawar ba amma abin
ya faskara tana kwance kanshi tana sambatu babu ko ďigon
hawaye a idonta,
dago kanta tayi saboda ganin mutum yayi kneel down a
gefenta yana shafa tun daga kafar jabeer har kanshi,
kallonta yayi yana kaďa kanshi hawaye na fitowa a idonshi
yace barbie yau kwana 9 banga abokina ba, yanzu kuma
naga sun rufeshi da fararen kaya ina zasu kaishi,
kice mishi ya buďe idonshi inason muyi magana, I missd
him so much,
sai a lokacin Afeeyah ta kara maida kanta kan jabeer ta fara
kuka mai tsanani tana fadin maganganun da ita kanta bata
san suna fitowa daga bakinta ba,
Affan ma duk da baya cikin hankalinshi yaji a jikinshi wani
mummunan abu ya samu abokinshi,
da kyar aka iya banbare Afeeyah jikin gawar jabeer,
ana sashi cikin makara ta kara fashewa da kuka tana faďin
dan Allah ku dawo min dashi wallahi zai dawo gareni, dan
Allah karku fita dashi, ta dinga fisge2 jikin wadanda suka
riketa tana fadin a dawo dashi ko ya mutu a bar mata
gawarshi,
suna shashi a mota Afeeyah ta saki wani gigitaccen ihu ta
faďi kasa sumammiya....

. Allah Sarki Afeeya. Ni kaina Bomboy na tausaya mata sosai. .

◆◆ RABO AJALI ◆◆
3⃣3⃣
.
.
By Suleiman Bomboy
.
A hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai,
dishi2 take gani tayi saurin mayar dasu ta runtsesu tana
fitar da wani irin wahalallen numfashi,
muryar Anty Asiya ce yasa ta kara bude su ta kalleta,
anty Asiya ta shafa kanta idonta cike da kwalla tace sannu
Afeeyah, babu inda yake miki ciwo,
ta lumshe idonta tana girgiza kai hawaye na zuba a gefen
idonta, anty Asiya ta fara yi mata nasihar da daga ji itama
na karfin hali ne,
saida ta daďe tana mata nasiha sannan ta tashi ta fita,
da sauri safnah ta dawo gefenta ta rike hannunta tana
zubar da hawaye tace Afee,
Afeeyah ta kara runtse idonta hawaye na gangarorowa
cikinsu kamar an saki ruwan pampo,
Safnah ta kwanta a jikinta cikin muryar kuka tace don't stop
dis tears Afee let it flow nasan yadda kikeji, cry as much as
u can,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka, suka dinga yi ita da
safnah dake jin mutuwar ta ko ina a cikin jikinta,
sun daďe suna kuka kafin safnah tayi shuru ta mike tana
kallon Afee,
safnah tace Afee tashi kiyi sallah kinsan fa bakiyi azhar ba
gashi har la'asar ta wuce, dakyar Afeeyah ta gyaďa mata
kai tace shikenan safnah sun kaishi sun birne min shi ko,
shikenan ni yanzu bani da wani sauran gata a duniya ko,
dan Allah safnah ki roka min Allah in mutu in bi shi dan
wallhy bazan iya rayuwa ba,
Goggon daura ce ta shigo cikin dakin ta zauna gefensu tace
zaki iya rayuwa Afeeyah,
wannan kukan da kikeyi babu wanda zai hanaki yinshi
domin shine kadai ne zai rage miki raďađin da kikeji, ki sani
jabeer yayi mutuwar da ko wane musulmi zaiso yayita, ya
mutu a daren alhamis aka kaishi ranar jumma,a, ya mutu a
hanyarshi ta ziyara kuma da kyakykyawar niyya a
zuciyarshi,
ko wannan muka tuna ya isa yasa mu ji dadi saboda yayi
mutuwar da akeso,
tashi maza kije kiyi sallah ki karfafa zuciyarki kiyi mishi
adduar samun rahama wannan ita kaďai ce hanyar da zaki
nuna tsantsar soyayyarki gareshi yanzu,
Afeeyah ta gyaďa kanta ta mike dakyar ta shiga bayi..
Karfe biyu saura motar oyizah tayi parking a cikin gida,
tayi mamakin rashin ganin "saunanta" a waje yazo tararta
kamar yadda ya saba, ciki ta wuce cikin farin ciki tana
kwala kiran sunan Affan,
salma da farida ta tarar a parlor suka yi mata sannu da
zuwa, ta amsa haďe da zama tace ina "rakumi na" yau
banga yazo yi min oyoyo ba,
salma ta tabe baki tace yana can gidan rasuwa kinsan
Abokinshi dan girman kan nan ya wullah,, oyizah cikin
tashin hankali ta mike tace how comes ya fita daga gidan
nan,
farida tace nayi mamaki nima mummy, Alhj basheer yayi
gyaran murya ya fito daga ďaki,
oyizah ta boye tashin hankalinta tace sannu da gida "ya
hajj" yace yauwa safiya kin dawo lafiya, tace lfy lau,
ya kalli salma yace kun shiga gidan gaisuwan kuwa,
suka turo baki suka ce yanzu zamu shiga da mummy,
alhj basheer yace ya kamata bari in koma gurin zaman
makoki,
oyizah ta matso kusa dashi cikin kissa tace alhj ina ďana
yake,
alhj basheer yayi murmushi yace kice dan rigima, yana can
wai shi bazai dawo gidannan ba sai an dawo mishi da
abokinshi,
oyizah bata san sanda tace to waye ya fitar dashi daga
gidannan,
alhj basheer cikin rashin fahimta yace ban gane ba,
tayi dan murmushi tace naga ya ďade bai fita bane bana
son ya fita shi kaďai wani abun ya sameshi,
alhj basheer yace Ayya, baba ado mai gadi na fara turowa
ya taho dashi saboda yazo yayi sallama da abokinshi duk
da ba wani hankali gareshi ba,
sai baba ado ya dawo yace wai yaki zuwa daga sunzo bakin
gate sai ya juya a guje,
shine naje da kaina na ďaukoshi dakyar yana ihu ya iya
fitowa daga cikin gidannan,
saida muka shiga gidan alhj bara'u sannan ya iya buďe
idonshi, kuma kinsan ya gama tsorata da gidannan dan
kiran namun daji kawai yakeyi wai gasu nan zasu cinyeshi a
bakin gate,
oyizah da gumi ya tsatsafo mata tace ayya my baby ni na
faďa mishi in ya fita akwai animals da zasu cinyeshi
saboda ina tsoron ya fita yaje wani abu ya sameshi,
alhj basheer yace aiko ya tsorata sosai dan yace shi acan
gidan alhj bara'u zai zauna nan gidan akwai lions da
sauransu,,
oyizah ta haďiye miyau tace yanzu zanje gidan ay sai mu
dawo gida,
alhj basheer ya ďaga kafaďa yace sai kinzo,, sama oyizah
ta wuce tana huci, a zuciyarta tace alhj ya fara bata mata
aiki, shikenan ya karya wannan kafin da ta daďe da yinshi,
wanka tayi sauri tayi ta shirya suka wuce gidan rasuwa...
Tun a kofar gida inda maza sukayi dafifi ana karbar
gaisuwa gaban oyizah ya faďi saboda haďa ido da tayi da
wani tsoho mai matsanancin kama da jabeer,
saidai shi ya tsufa sosai, maida kanta tayi gurin Affan da ya
lafe jikin tsohon yana tsotson hannu idonshi a lumshe,
dakyar ta iya gaisar da mutanen gurin saboda irin kallon da
tsohon nan ke mata,
cikin gida suka shige ita da yayanta sai a sannan hankalinta
ya kwanta,
bayan tayi gaisuwa sama2 sai suka fito ta tsaya daga ciki
ta aika farida ta kira mata Affan,
farida ta wuce ta keta gurin mazan saboda rashin kunya
tasa hannu zata fara bubbuga affan,
da sauri tsohon nan ya tare hannunta yace ke lafiyarki,
ta tsaya kerere tace mummy ce tace in kirashi mu tafi gida,
ya kalleta sosai yace kice wai bacci yakeyi,
farida ta turo baki ta juya taje ta faďa ma oyizah sakon
wannan tsohon,
hankalin oyizah ya kara tashi tace kuzo muje, suka fito, har
ta fara tahowa gurin da suke sai ta canza hanya,
farida tace mummy gasu can fa,
oyizah tace kuzo mu tafi anjima zan sa a kirashi,
sai a lokacin kaka liman ya ganeta, a zuciyarshi yace
tabbas bazaki iya hada ido dani ba dan mugu na tsoron
kwayar idona, ya shafa kan Affan a zuciyarshi yana kitsa
abubuwan da zaiyi ta karkashin kasa ba tare da wani ya
sani ba bare ta kara ajalinshi....
Oyizah na shiga gida ta fara safah da marwah tana sake2 a
zuciyarta,
fitar Affan daga cikin gidannan ba karamin tashin hankali
bane a gareta,
to wani tsoho ne wannan da ya firgita ganinta kamar wani
aljani, yanzu shikenan Affan yana can gurin dubban mutane
kuma tasan dole wasu zasuyi mishi addu'a,
Noooo bazai yiwu ba ta fadi da karfi haďe da tashi ta kara
fita daga gidan....

◆◆ RABO AJALI ◆◆
3⃣4⃣
By Suleiman Bomboy

Tun kafin ta karasa take kiran wayavr alhj basheer bai ďauka
ba saboda suna addu'a a gurin zaman makoki, tana
karasawa taga maza sun kara yawa a gurin ta kalli gurin da
tsoho da Affan suke bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta wuce cikin gidan kamar zata rusa ihu,
a waje ta tarar da Amirah ta rako yan makarantarsu tace
"ke" ina Affan yake,
Amirah ta fara waige2 sannan ta juyo ta cigaba da magana
da kawayenta,
oyizah ta hassala tace ba da ke nake magana ba Amirah,
Amirah tace ay bansan dani kike ba naji kamar "ke" kikace,
yana ďakin yaya jabeer,
oyizah ta harareta a hankali tace mara kunyar banza, ta
wuce dakin jabeer,
Kwance ta sameshi ya kura wa makeken hoton jabeer ido
baya ko kiftawa,
cikin fushi tasa hannu ta make kanshi da karfi,
a zabure ya mike yana kallonta,
hararshi tayi tace wuce muje gida, bai ďauke idonshi a
kanta ba ya girgiza mata kai alamar baza shi ba,
oyizah hassala matuka tace ni kake ma musu Affan,
ya kara marairaicewa yace ni abokina nake jira,
ta damko hannunshi tace dan ubanka wa ya faďa maka
wanda ya mutu yana dawowa, wuce muje kafin in ji maka
ciwo,
ya noke wuya yace ni bazan tafi ko ina ba,
ta janyoshi da karfi ta hankaďo shi waje,
wani irin ihu ya saka ya ruga bayan Asiya da ke tahowa
gurin,
Asiya ta rikeshi tace me ya sameka Affan, Affan ya shige
bayanta yana nuna mummy da ta taho tana huci kamar
kumurci, tana karasowa ta kai hannu zata kara rikeshi ya
kara sa ihun da ya maido da hankalin mutane da yawa
gurinsu,
Asiya tace me yayi miki ne wai,
oyizah ta harareta zata kara rikeshi Asiyah ta rike hannunta
tace wai me yake faruwa ne, ki kyaleshi mana ko dole ne,
oyizah ta shaka sosai ta kalli yawan mutanen dake gurin
zuciyarta na zafi saboda ganin Affan ya fara mata musu,
ta kalli Affan fuskar nan babu annuri tace ka wuce muje
gida, Affan ya noke wuya yace ni babu inda zani,
Abida da rabon da tasa Affan a idonta tun kafin ya fara
ciwo ta fito ta riko hannunshi tace zo muje ciki,, kaci abinci
ko,?
ya gyada kanshi tace to zo muje anjima abokinka zai dawo
sai ya rakaka gida kaji,
ya kara gyaďa kanshi cikin murna suka fara tafiya,
da sauri oyizah tasha gaban Abida tace sakeshi tunda babu
abinda kika haďa dashi,
Abida tayi mata kallon banza tabi ta gefenta ta tura Affan
gaba suka wuce yana waigen mummy dake mishi wani irin
kallo, masifa ta fara yi tana zage2 kamar tababbiya dan
gani takeyi zasu bawa Affan maganin da zai maido mishi
da hankalinshi ya tona mata asiri, dakyar suwaiba ta
rarrasheta suka wuce gida suna kulla munafurcinsu..
Kuka sosai oyizah keyi a gaban alhj basheer akan ita a
dawo mata da ďanta,
ta share hawayenta tace shekara uku kenan ina wahala
dashi sai yanzu zaka barshi can wani guri kace ya kwana,
wallhy alhj bazan iya yin bacci ba yau in affan bai dawo
gida ba,
alhj basheer ya juyo yace haba safiya, na yau dai kaďai sai
kace wanda zai zauna a can dindindin,
ta harzuka tace kasan abinda zasu bashi yau ďin,
yace kamar yaya abinda zasu bashi, me zasu bashi kuwa,
oyizah ta saita kanta tace ina nufin kasan baya cin komai in
ba ni na bashi da kaina ba, ta kara fashewa da kuka tace
yanzu Allah kaďai yasan yunwar da yakeji,
alhj basheer cikin jin dadin kulawarta ga danshi yace karki
damu safiya Affan na can cikin koshin lafiya kuma yaci
abinci sosai dan abin har mamaki ya bani,
kuma kinsan ďan zaman nan da yayi a gurin makoki yau
har sallah yayi da kanshi saboda ganin mutane nayi,
oyizah ta mike cikin kidima tace alhj kana yi wa Allah kaje
ka dawo min da ďana,
alhj basheer yace wai bakiji abinda nace miki bane, ki bari
zuwa gobe mana,
ta girgiza kanta ta wuce ciki tana kuka tana faďin dan kaga
na damu dashi ne shiyasa kake nuna min ba ni na haifeshi
ba,
alhj basheer yayi murmushi a zuciyarshi yana kara jin son
oyizah saboda yadda take nuna kulawarta ga Affan. ..
Oyizah taci kuka a wannan daren dan ta hakikance wasu
daga cikin abubuwan da tayi ma Affan sun warware, tunda
har Affan ke iya mata musu kuma har yayi sallah,
wani irin ihun takaici tayi da ta kara tuno da Affan na can
gidansu jabeer kuma Allah kaďai yasan abinda zasu
bashi..... ◆◆ RABO AJALI ◆◆
3⃣5⃣
By Suleiman Bomboy

Washe gari tun asuba oyizah taje gurin alhj basheer ido
luhu2 saboda kuka da rashin bacci,
gaba ďaya ta rasa abinda zata yi a wannan daren saboda
bata san ta inda zata fara ba tunda Affan baya gabanta,
alhj basheer ya ďago ya kalleta cikin bacci yace safiya
lafiya, tace alhj naga kai baccinka ma kakeyi baka damu da
yaron nan ba, ko bacci banyi ba saboda nasan da kyar in ya
iya yin bacci,
alhj basheer yayi mika haďe da salati yace lafiyarshi kalau
safiya yau a masallaci ma na samesu tare da kaka
mahaifin alhj bara'u, rike ciki oyizah tayi hankali tashe tace
a masallacin suka kwana?
Alhj basheer yace a'a sallahr asuba suka je, oyizah ta
zauna dabass a kan gadon ta marairaice tace alhj inda zaka
san irin missing din Affan da nakeyi da baka barshi ya
kwana a wani guri ba, wallhy jiya banyi bacci ba dan daga
na rufe ido shi kaďai nake gani,
kasan yadda na shaku dashi kuma nake jin tausayinshi, dan
Allah ka tashi kaje ka dawo min dashi,
alhj basheer ya tausaya mata dan yasan tana iya kokarinta
akanshi yace to bari in yi wanka zanje in dawo miki dashi,
ta saki wata dariyar murna tace nagode alhj bari in je in
shirya mishi favourite break dinshi,
alhj basheer yayi dariya ya koma ya kwanta,
Daki oyizah ta koma cikin murna tace wannan karan mai
gaba ďaya zanyi akan yaronnan dan bazai yiwu su dinga
daga min hankali ba, gara in kashe shi ya bi abokinshi in
huta da zulumi,
wata zuciyar ta haneta da sauri tace in kika kasheshi yanzu
tayaya zaki samu dukiyoyin da alhj ya mallaka mishi,
sannan in kika kasheshi hankalin mutane zai dawo kanki su
zarge ki, gara kibi komai a hankali ki kara tsaurarawa
akanshi ki maida shi mara amfani,
da wannan tunanin tayi yan tsaface tsafacenta na gaďo
sannan ta wuce kitchen shiryawa Affan break...
Karfe 9 da kwata alhj basheer ya iso gidan rasuwar,
zaune ya samesu a cikin parlor sunyi shuru sai muryar
Affan kadai akeji yana ma kaka liman hirar shirme,
dariya kawai kaka liman keyi yana tausayawa halin da
Affan ke ciki,
da sallama alhj basheer ya shigo parlon ya tsuguna ya
gaida kaka liman sannan suka gaisa da alhj bara'u,
alhj basheer ya kalli Affan yace ka tashi lafy,
Affan ya gyaďa mishi kai yace sosai ma tare da kaka
mukayi bacci shi ya tashe ni yasa nayi wanka ya bani abinci
ko kaka?,
kaka liman yayi murmushi yace kwarai dan kaka,
alhj basheer yace kace yau kai ďan gata ne, to tashi mu tafi
gida mummynka na can tana missing dinka,
Affan ya noke wuya yace ni bazan je gida ba, alhj basheer
yayi murmushi yace meyasa? Affan yace saboda har yanzu
abokina bai dawo ba,
alhj basheer yace ay yana can gida yana jiranka kuyi wasa,
Affan ya waro ido waje yace dagaske daddy, alhj basheer
ya gyaďa kanshi yace dagaske nake,
Affan ya kalli kaka liman yace wai haka kaka, kaka liman
yayi dariya yace haka ne,
Affan ya tashi da sauri yace muje daddy,
alhj basheer ya mike ya rike hannunshi yayi sallama da su
kaka liman suka fito tare da alhj bara'u,
a bakin gate suka haďu da hajja rike da katuwar kular
abincin sadaka,
da gudu Affan yaje gurin ta yana kokarin karbar kular
hannunta, kauda kular tayi tana dariya tace bazaka iya ba
Affan,
su alhj basheer suna dariya suka tsuguna suka gaisheta ta
amsa haďe da kara yi musu gaisuwa,
alhj Bara'u yace ina Afeeyah dafatan jikin nata da sauki,
Hajja tace hmm sai dai addu'a tana can tun jiya take abu
ďaya yanzu na baro mahaifinta yana mata rubutu,
alhj basheer yace kuka fa dole ne hajja shakuwar zaku
duba, kai mutuwa, mutuwa mai yankan kauna,
Affan yace daddy Afeeyah ce ke kuka, alhj basheer ya
gyada mishi kai,
Affan ya bata rai kamar zaiyi kuka yace daddy tun jiya fa
take kuka kaje ka rarrasheta kace tazo muje gidanmu taga
abokina muyi wasa tare,
alhj basheer yace to yanzu dai muje gida anjima zan je in
rarrasheta sai in kawo maka ita gidan kaji,
Affan yayi dariya sosai yace gaba daya zata dawo gidan
mu ko?, dama jabeer yace zai bani ita in ya aureta kuma
kaima kace zaka aura min ita ay ko,?
sukayi dariya dukkansu alhj basheer yace eh zan aura maka
ita wuce muje, ya fita yana tsallen murna,
sun kusa karasawa gidan ya rungume daddy yace daddy ka
goyani kar inga lions, alhj basheer yace babu abinda zaka
gani buďe idonka nasa an cire su, a hankali ya buďe idon
yaga babu abubuwan da ya saba gani a kofar gidan, a
tsorace ya shiga gidan yana zazzare ido,
jiki na rawa oyizah ta fito ta rungumeshi tana faďin oyoyo
Affan ďina, nayi missing dinka ďana,
alhj basheer yayi dariya yace ai da kyar ya yarda ya biyo ni
saida na ce mishi jabeer na nan gidan sannan,
oyizah tayi murmurshin mugunta tace muje ciki kaci abinci
sai in nuna maka abokin naka, Affan yayi dariya ya bita
suka shiga ciki,
Special break ta haďa mishi wanda yaji magunguna,
zaunar dashi tayi ta cika gabanshi da abinci ta diba a cokali
zata fara bashi ya kauda kanshi yana rike ciki yace mummy
munci abinci sosai tare da kaka har da kosai ma mai dadi,
oyizah ta ajiye cokalin ta saci kallon alhj basheer da
hankalinshi ke kan TV sannan ta kalli Affan tace haba baby
na, baka so kaga abokin naka kenan Affan da sauri yace
inaso mummy, tace oya open ur mouth kayi ko 1bs ne,
ya buďe bakinshi ta ďebo zata zuba mishi ya kara kauda
kanshi da sauri yace ina zuwa mummy kaka liman yace in
zanci abinci in dinga yin bismillah, da karfi yace "bismillah",
oyizah ta buge bakinshi da karfi ba tare da tasan tayi ba,
washhhh Affan ya faďi da karfi yana kallonta idonshi ya
fara kawo ruwa yace mummy me na miki,
ta dafe kanta tace Affan wadannan mutanen sun koya maka
abubuwan da zai kasheka,
Affan ya fito da ido waje yace "kasheni" mummy?
Ta rage murya tace yess,
kaga wannan bismillahr da yace kayi, to daga ka kuma
yinta zaka mutu,
Affan yace to ai jiya munyi sosai harda wani karatu ma duk
munyi kuma ban mutu ba,
oyizah ta mike ta riko hannunshi tace zo muje in fada maka
wata magana,
ya mike ya bita daki ta zaunar dashi gefen gado ta fara
tsoratar dashi sosai akan sallah da wasu abubuwan da
kaka liman ya koya mishi sannan tace mishi kasan inda
abokinka yake, ya girgiza mata kai cikin tsoro tace to ya
mutu kaga irin mutuwar da akeyi a cikin film mutum ya fadi
ya

Please Login or Register in order to submit comment