Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Oyizah tayi
dariya sosai tace ba dole ya farfado ba,
na daďe
ina jiran wannan ranar, ta kalli ruwan sosai tace
nasan har
yakai inda nakeso yakai,
ta harari affan ta fara shafa mishi ruwan a fuska
tace kai
da samun sauki har abada Affan..
Tun daga ranar ciwo ya dawo sabo, saboda
kullum
da ihu
yake farkawa sai an mishi allurah ake samun
saukin abun, ciwon kanshi kuwa ya fara warkewa,
dan gurin da
yayi rami
ya ciko sosai,
saida yayi sati ďaya kullum ya farka da ihu yake
farkawa,
daga ya farka kafin ayi mishi allura oyizah zata
bashi
maganin da tace ruwan addu'a ne,
Watanshi ďaya a asibiti ana fama da lalura ďaya,
saidai a kawo babban likitan mahaukata gurinshi
ya dinga
mishi treatment saboda ciwon da ke kanshi,
yanzu kam ciwon yayi sauki sosai dan haka
doctor
musa ya
bada shawarar a kaishi "psychiatric" alhj basheer
sam yaki
yarda yace saidai ya fita dashi waje,
doctor musah yace hakan ma zaifi Alhj, gara ka
kaishi
wajen, akwai wani asibiti a "New Toronto,
Canada"
sunanshi
"LAKESHORE PSYCHIATRIC HOSPITAL" asibitin
sun
kware
sosai alhj, in dai waje zaka fita dashi gara ka
kaishi can,
kuma anan nigeria ma fa akwai psychiatric masu
kyau
kuma ana kula sosai, kamar su "FEDERAL NEURO
PSYCHIATRIC" dake kaduna da kuma na Lagos,
da
ma sauransu, amma tunda hankalinka yafi ga fita
dashi
din
gara ka fita dashi, mudai fatanmu a koda yaushe
shine ya
samu lfy,
, alhj basheer yace hakane doctor, nagode sosai in
shaa
Allah gobe zamu fara processing tafiyar,, doctor
musah
yace to Allah ya kaimu alhj shi kuma Allah
ya-------
doctor
musa ya kasa karasawa saboda datse harshenshi
da yayi,
ya kalli alhj basheer ya mika mishi takardun
sallama
da
reports din ciwon Affan tare da magunguna...
Watan Affan biyu a canada, oyizah ke zaune
dashi
saboda yawan tafiye tafiyen da alhj basheer keyi,
jikinshi
yayi kyau
sosai saidai duk wanda ya ganshi yaga mai tabin
hankali,
komai na yara yakeyi, ga yawan son wasa, kallon
ruwa da kifaye da sauransu,
a cikin wata biyun nan oyizah ta mallake Affan
sai
abinda
tace yayi, sam bata nuna mishi hanyar kwarai
saidai
ta
nuna mishi mara billewa, magungunan tsafi kuwa
su ke
ďawainiya dashi tun zuwansu canada,
doctors sunyi mamakin yadda akayi magungunan
da suke
bawa Affan bai mishi aiki ba,
sudai sunsan larura indai ta haukace to wacce
tafi ta affan
ma sun warkar bare tashi da suke ganinta minor,
basu san
duk magungunan da suke zuwa bashi oyizah ta
karba tace
zata bashi zubar dasu takeyi ba, wani lokacin ne
ma take bashi ba bisa ka'ida ba,
A ranar da suka cika wata biyu da sati biyu aka
sallamesu
saboda haukar affan ba ta barna bace kuma
sunga
in
oyizah tace ya zauna nan to bazai tashi ba har
sai tace ya
tashi,
wannan dalilin yasa suke ganin kamar in suka
basu isassun
magunguna nan da wasu yan watanni zai samu
sauki.. Ranar oyizah tayi murna saboda dama ta
kosa ta
koma
gida,
yawo ta fita da Affan tayi mishi siyayyar kayan
wasa da
uban yawa tana zaba tana mishi dariyar mugunta
shi kuwa
banda murna da tsalle babu abinda yakeyi,
a daren ranar suka hawo jirgi tare da alhj basheer
sai kasar
mu ta gado...
Cikin dare suka iso gida a gajiye, kowanne daki
yaje ya
kwanta banda Affan da shi a gurinshi ma safiya
ce,
zama yayi a parlor yana wasa sosai gaba daya
ya
hargitsa
parlon,
in ya kalli hanyar dakin zeenatu sai ya runtse
idonshi wasu
abubuwa su dinga gifta mishi kamar rayuwar
cartoon,
kuma sai yaga kamar harda shi a cikin cartoon
din,
tashi yayi yana kokarin zuwa kofar dakin yaji
muryar oyizah ta daka mishi tsawa,
da sauri ya dawo bayanta ya tsaya yace mummy
wannan
kofar wanene,
kamar na taba zama a ďakin, kin gani kofar ma
kamar ta drawing ko,
oyizah ta shafa kanshi tace my baby kasan meye
a
kofar
nan, ya girgiza mata kai, ta ja hannunshi ta fara
nuna mishi
kofar har zuwa hanyar steps din can saman da
ya faďo
tace duk nan gurin zaman macizai, da namun daji
ne, kana
son su cinye ka, ya noke wuyanshi ya make a
bayanta,
tace to karka kara zuwa arean gurin kaji, yace to
mummy,
ta kama hannunshi ta wuce side dinta dashi ta
sashi a wani
daki ta rufe tana kyakyata dariyar mugunta da
jindadi..
Tun karfe 12 jabeer keta fama da masu gadin
gidan akan
su bude mishi kofa sunki, dan oyizah tace kar a
kara barin
kowa ya shigo saida izininta, ran jabeer ya baci
sosai
idonshi yayi jawur, yace yanzu Halilu har ni ma
sai ku hana shiga in an
saku,
halilu yace kwarai kuwa saboda ina mutunta
aikina,
jabeer yayi kwafa kamar zai juya sai ya dawo da
karfinshi ya tura halilu ya ruga ciki da gudu suna
binshi a
baya,
da sauri alhj basheer ya fito jin hayaniyar tayi
yawa,
tsawa ya daka ma su halilu yace lafiya kuke
binshi
kamar
wani barawo, halilu yace ranka ya dade madam
ce tace kar abar
kowa ya
shigo,
alhj basheer yace jabeer ne kowa, baku san
matsayinshi a
gidannan bane, oyizah ta fito da sauri tace yi
hakuri alhj mantawa
nayi in ce
musu kar su hana jabeer shigowa,
alhj basheer yace to su sauran mutanen kuma fa
meye
dalilin hanasu shigowa, ta fara matsar kwallah
tace bana son a shigo a
dinga yi ma
affan dariya na fi son sai ya warke mutane su
ganshi,
alhj basheer ya jinjina kai cikin damuwa yace na
gamsu da bayananki, share hawayenki Allah yayi
miki abinda
kikayi
mana na alkhairi, tace ameen haďe da hararar
jabeer,
alhj basheer yace jabeer ka shiga ciki mana
abokin
naka yana ciki ai,
jabeer yasa kai ya shiga cikin parlon da sallama,
Zaune ya tarar da Affan da wasu kayan wasa a
hannunshi,
wuyanshi yasha hoda idonshi kuma kwalli, kallon
jabeer yakeyi sosai wasu abubuwa na mishi yawo
a
kwakwalwarshi,
sai da yayi minti biyar yana kallonshi sannan ya
zubar da
kayan wasan ya rungumeshi yace daddy wannan
abokina ne sosai tare muke wasa dashi, kaga
fuskarshi ma
shima
drawing dinshi akayi kamar waccan kofar,
Salma da fareeda suka kwashe da dariya harda
rike
ciki,
yayin da jabeer ya fashe da kuka haďe da
kankameshi...

Posted by SULAIMAN BOMBOY

[1:10PM, 24/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI 25◆◆
By
Aysha Ya'u Kurah
A hankali Affan ya saki jabeer yana mishi wani
irin kallo,
fuskarshi ya fara shafawa yana share mishi
hawaye yace
naji maka ciwo ne, ya ďaura hannunshi a kan
jabeer yace yi
hakuri kadaina kuka zo muje kaga kayan wasa
na, kaima
kana so ko?
jabeer ya gyada mishi kai hawaye na fita a
idonshi,
Affan ya ďan bata fuska yace to ka daina kuka
zan baka
wasu sai ka tafi dasu kaji, Jabeer ya kasa
daurewa ya saki
hannun Affan ya fita daga gidan da gudu yana
kuka sosai,
Affan ya bata rai sosai kamar zaiyi kuka ya kalli
daddy yace
daddy kaga ya tafi yana kuka ko,
kuma ay na bashi hakuri bansan zaiji ciwo ba, ka
bishi ka
dawo min dashi muyi wasa kaji,,
alhj basheer ya share kwallar da ta zubo mishi
yace zai
dawo yanzu affan yaje ya siyo maka abin dadi ne,
Affan ya daka tsalle yace daddy kace mishi ya
taho min da
sweets dinnan masu dadi,
alhj basheer yace karka damu affan je ka cigaba
da
wasanka, Affan ya gyaďa kai cike da murna ya
koma gurin
kayan wasanshi..
Salma da fareeda suka mike kunshe da dariya
suka wuce
daki,
suna shiga suka saketa kamar tababbu, fareeda
tace salma
kiga yadda affan ya koma kamar dan yaye, salma
tace ni ba
karamin dariya yake bani ba, ji wani kwallin da
mummy
tasa mishi a ido dan Allah, fareeda tace ay ni
yanzu na
samu film din kallo wanda zai dinga sani nishadi,
salma
tace ke ko ni, suka kara kwashewa da dariya...
Jabeer bai dawo gidansu affan ba sai can da
yamma,
idonshia kode saboda tsabar kukan da yaci,
a waje ya sameshi yana buga kwallo, affan na
ganinshi ya
rungumi kwallonshi ya rugo da gudu zai rungume
jabeer sai
kuma yaja ya tsaya saboda tunanin kar ya kara
sashi kuka
irin na dazu,
jabeer yayi murmushi ya buďe hannunshi, affan
ya kwashe
da dariya sosai ya shige jikinshi yace yanzu banji
maka
ciwo ba ko, jabeer yace ehh friend, Affan ya ďago
kanshi
yace ina abin dadin da daddy yace zaka siyomin,
jabeer yasa hannu a aljihu ya fito da chocolates
ya mika
mishi,
tsalle yayi ya dane jikin jabeer yana murna ya
karba yace
bari in nuna ma mummy dan tace duk wanda ya
bani abu in
nuna mata kafin in ci, bai jira jin abinda jabeer
zaice ba ya
ruga ciki da gudu,
jabeer ya rungume hannunshi yana girgiza kanshi
a
zuciyarshi yana kara jin tsoron Allah mai maida
bawanshi
yadda yaso a kuma lokacin da yaso,,,
Tun daga ranar kullum jabeer ya taso aiki zai
tsaya a gurin
affan suyi hirarsu yayi ta mishi shirme, in lokacin
sallah yayi
duk yadda zai buga ya raya affan yazo suje zaiki
yace sai
ya tambayi mummy, daga yaje ya tambayeta zata
hanashi
ta tsoratar dashi sosai, da taga kullum jabeer na
matsama
affan akan sallah sai ta bijiro da kokarin rabasu,
da farko tayi nasara dan kuwa ko jabeer yazo
bata barin
affan ya ganshi, da affan yaga har sati daya
baiga
abokinshi ba ya ďaga musu hankali sosai a gidan
duk irin
tsoron da mummy ta bashi bai shigeshi ba shidai
kawai a
kira mishi abokinshi abinda yake fadi kenan,
da taga kullum bashi da aiki sai kuka kuma baya
cin abinci
sai tasa masu gadi su nemo mata jabeer dan in
alhj ya
dawo ya tarar dashi a haka to bazai mata da
kyau ba..
Duk irin tururuwar da mutanen unguwa keyi a
kofar gidan
zuwa gaida affan basu samu shiga ba dan ko
kofar masu
gadi basu buďe musu,
hakan yasa mutane suka hakura da zuwa
gaisheshi saidai
in sun hadu da alhj basheer suyi mishi jaje a waje,
maganar
zeenatu kuwa banda yan'uwanta da su Abida
babu wanda
ke tunawa da ita addu'a kuwa kullum yinta sukeyi
akan
Allah ya bayyana ko gawarta ne..
Oyizah kuwa likkafa taci gaba don ba kananan
kudi takeci
da ciwon affan a guri alhj ba ,
duk bayan sati daya da kudin da yake bata da
sunan ana
ma Affan saukar alqur'ani da rubutu, amma bai
taba maida
hankali gurin ganin affan yasha rubutun a
gabanshi ba
saboda ya yarda da oyizah 100%,
haka in malam Atiku ya bashi rubutu a bawa
affan ko
jabeer ya amso mishi sai dai daddy ya bata yace
ta bashi
yana fita zata zubar dasu tayi ta musu tofin Allah
tsine...
Abinda yafi ďaga mata hankali yanzu shine ta
rasa inda
Affan ya ajiye takardun kadarorin da alhj ya bashi,
kullum zata zaunar dashi a siyasance tace ya
dauko mata
takardun da alhj ya bashi, cikin rashin fahimtar
abinda take
nufi zai tashi yaje ya tattaro duk takardun
dakinshi ya kawo
mata,
babu irin duban da batayi ma dakinshi da na
zeenatu ba
amma sam bata gansu ba,, gashi tana tsoron
tambayar alhj
basheer dan kar ya harbo jirginta, haka ta saduda
da
tunanin in alhj ya mutu dukiyar duk nata ne da
ya'yanta dan
ko Affan ma mallakinta ne....
Wannan shine mafarin ciwon Affan da yanzu yake
cikin
shekara ta uku cikinshi, a wannan shekarun ko
sau ďaya
affan bai taba fita da kafafuwanshi ba sai dai a
kaishi
checkup a mota tare da oyizah amma fita shi
kadai sam
bata yarda dashi ba dan ba karamin kafi tayi
mishi ba,
Salma da farida kuwa maidashi sukayi kamar toy
haka
zasu tasashi a gaba suyita dariya in yana
shirmenshi..

[8:14PM, 24/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI 26◆◆
By
SULAIMAN BOMBOY

☆ cigaban labari ☆
Gida jabeer ya tafi bayan sun gama hira da hajja
da Afee
akan lalurar Affan, yana shiga ya wuce parlon
mahaifinshi,
zaune ya samesu da ummi ya gaisar da babanshi
ya amsa
fuskarshi dauke da fara'a yace ya jikin abokin
naka, jabeer
yace alhmdullih baba, Abida ta kalleshi tace ina
Afeeyar
take shine ta tafi babu ko sallama, jabeer yace ai
ummi taga
kina bacci ne shine muka shiga gurin affan tare,
Alhj bara'u ya kalleshi sosai yace jabeer yaushe
Afeeya
zata fara jarabawa,
Jabeer yace next uppr week zasu fara, alhj Bara'u
yace
hasashena ya zama gaskiya kenan, mun zauna
da malam
atiku mun tattauna game da maganar aurenku ni
in sona ne
ma ayi kafin ta zana jarabawar, Abida tace haba
alhj ay
gaggawa ba namu bane ina laifin in sun gama da
sati ďaya,
alhj bara'u yace to koma yaushe ne Allah ya
kaimu dan na
kosa in aurar da jabeer, Abida tace kace dai ka
kosa kaga
yan jikokinka,
alhj bara'u ya kwashe da dariya yace ma jabeer
ya tashi ya
tafi, jabeer ya fita shima yana dariya..
Cikin ikon Allah aka tsayar da ranar Afeeyah da
jabeer
kamar yadda Abida tace,
murna a gurinsu ba'a cewa komai babu wanda
zai iya gane
wanda yafi murna a cikinsu,
shiri jabeer yakeyi sosai da planning din yadda
zasuyi
rayuwarsu da Sweet Afee dinshi da ya'yan da
zasu haifa
tare, duk shirin da yakeyi bai hanashi zuwa gurin
Affan ba
kullum suna tare da yamma kuma kullum sai
Affan ya
tambayeshi ina barbie dinshi,
jabeer shirme yake maida abin saboda yasan bayi
da
isashen hankali, da jabeer yaga abin na Affan
bana karewa
bane sai yake zuwa ya dauko Afee dakyar suzo
gurin Affan,
in Affan ya ganta to fa aranar murnarshi ta karu
kenan
saboda ya dinga mata shirme kenan yana kwaso
kayayyaki
yana bata wai ta tafi dasu gida,
a cikin yan kwanakin suka dan fara sabawa
kadan2, dakyar
jabeer ya fahimtar dashi cewa an kusa daura
mishi aure da
Afeeya, dariya kawai yayi yace to in kukayi aure
zaka
barmin ita anan gidan, jabeer yace sosai ma ai
anan zata
zauna, Affan yayi dariya ya kalli afeeyah yace wai
haka, ta
gyaďa mishi kai tace eh,
wani irin ihu yasa ya mike wai zaije ya fadama
mummy,
da sauri Afeeyah ta riko hannunshi ya tsaya
chakk yana jin
wani irin abu a rikon da tayi mishi,
juyowa yayi kamar me hankali ya kalleta itama
shi take
kallo haka jabeer kallonsu kawai yakeyi,
jikinta ne ya bata jabeer na kallonta tayi saurin
sakin
hannun Affan tace karka faďa ma mummy zatace
kar
abaka ni ko yaya jabeer,
jabeer ya gyada kanshi yana kallon Affan, zama
Affan yayi
yana murza hannun da Afeeyah ta rike yace to
babu abinda
zatamin in ta sani,
Afeeya ta gyada mishi kai tace baza ma tasani
ba,
jabeer yayi mamakin yadda affan yaji maganar
afeeya,
mutumin da magana in dai akan mummy ne to
babu wanda
ya isa ya tsayar dashi, kallonsu ya cigaba dayi
yadda yake
mata hira tana biye mishi suna kyakyata dariya
sai yaji daďi
a ranshi dan ko ba komai zai yi amfani da
Afeeyah ta dinga
dawo dashi hanya,
sam baiji kishin komai a ranshi ba dan yasan
Affan baida
hankali kuma ko yanada hankali ma bazaiyi kishi
ba saboda
yasan irin son da afeeyah take mishi..
Safiyyar monday jabeer ya shirya da wuri saboda
zai kai
Afeeyah makaranta ranar zasu fara jarabawa,
a kofar gidansu ya sameta tsaye tayi kyau sosai
tana
jiranshi, kusa da ita ya kai motar ta bude ta
shiga suka
gaisa,
yace da fatan kinyi karatu ko, tace sosai ma
banyi bacci
sosai ba,
yace kedai fadi gaskiya kodai kin boyo xpo, ta
turo baki
tace kaima kasan wuce nan duk da bana zuwa
1st kasan
dai ban taba wuce 10th ba,
yayi dariya yace 3rd term ss2 dakyar na roka fa
aka barki a
10th din shine zaki wani cika min baki a faďa da
dambe ne
dai ake baki A1,
ta harareshi tace eh naji ďin, yayi dariya ya tada
motar suka
wuce yana cigaba da tsokarta, kan titin
"hausawa" ya hango
motar gidansu Affan, bai bi takanta ba bare yasan
su waye
a ciki, ya wuce ya sauke Afeeyah a skool haďe da
yi mata
adduoin samun nasara..
Yana fitowa daga layin skull dinsu ya kuma
hango motar,
wannan karan Affan ya hango a gaba da baloon a
hannunshi yana dariya mummy ta hakimce a
baya,
bin motar yayi dan yanason yaga Affan kafin ya
tafi aiki,
asibitin da ake mishi check up suka tsaya, saida
suka shiga
ciki Jabeer yayi parking, saida ya gaisa da wani
abokinshi
da suka dade basu haďu ba sannan ya shiga,
sam oyizah bata ganeshi ba saboda hankalinta a
tashe
yake da result din check up din,
jabeer yaji doctor na cewa gaskiya an gode Allah
dan zai
iya dawowa normal cikin kwanakin nan saboda
mun samu
improvement sosai, ya mika mata magani yace
wannan
maganin shine maganinshi na karshe in shaa
Allah in ya
kare komai zai zama normal,
jabeer saboda murna zaiyi magana ya bugi wata
nurse
kayanta suka zube ya durkusa ya kwashe mata
yana bata
hakuri,
yana ďagowa yaga har sun fita sun shiga mota,
binsu yayi a baya har gida,
a waje yayi parking motarshi saida ya tsaya a
waje ya kirah
office ya dau excuse sannan ya shiga ciki da
sauri,
babu kowa a parlon gidan hakan yasashi hawa
sama
saboda tsananin murna, tsayawa yayi jikin wata
kofar da
yakejin magana da karfi haďe da huci kamar
zakanya,
lekawa ya fara yi ta gurin mukulli, ya hango Affan
zaune
kan wani jan kyalle,
da sauri ya dago kanshi jikinshi na rawa ya ďeka
ta window,
oyizah ya hango da wata halitta suna magana
suna zagaye
Affan,
suna gamawa yaga an bawa oyiza wani ruwa
ance ta bawa
affan muddin yasha to bashi ba samun sauki
kuma
haukarshi zata fi ta da,
oyizah tayi dariyar jindadi tayi sujjada ga wannan
halittar
nan da nan yaga ta bace,, jabeer sai mutsike
idonshi yakeyi
a tsorace kamar a mafarki,
muryar oyizah ce ta dawo dashi hayyacinshi
waya takeyi da
esther tana faďa mata duk yadda tayi ta mayar
da Affan
haka har abin da tayi ma zeenatu,
a kidime jabeer ya fara fadin innalillahi wa inna
ilaihir rajiun,
jin tayi shuru ne yasa ya leka da sauri ya
hangota ta mike
zata bawa Affan wannan ruwan,
cikin zafin nama ya murda kofar ya kabe ruwan
ya zube a
kasa, oyizah ta kalleshi a firgice tace j-a-b-e-e-r,
ya dago
Affan ya rikeshi yana mata wani mugun kallo
yace asirinki
ya tonu, muguwa azzaluma, matsafiya mai shan
jinin
alumma,
naga duk abinda kikeyi yau in shaa Allahu
karshenki yazo,
yaja hannun Affan zasu fita oyiza tace jabeer ka
dawo, ka
rufa ma kanka asiri dan wallhy babu wanda ya
isa yaga
karshena,
ka dawo ka fadi nawa zan biyaka ka rufa min
asiri,
jabeer bai saurareta ba ya fita dan a tsorace
sosai yake,
suna zuwa gate Affan ya fisge hannunshi yasa
ihu yana
faďin mummy kizo ga su lion nan zasu kamani,
ihu yakeyi
yana ja baya ya ruga ciki da gudu,
jabeer ya kalli gate din cikin mamaki dan shi
baiga komai
ba,
har zai koma ciki sai kuma ya fasa ya fita a
fusace,
Police station ya nufa yana zuwa kofar gurin ya
fara
tunanin to ina evidence yake,
Affan shi kadai ne evidence kuma bashi da
hankalin da za"a
saurareshi,
shuru ya zauna a motar yana tunanin mafita, can
ya fara
tunanin yadda zaiyi affan ya samu sauki, a
zuciyarshi yace
malamai zan tara suyi ta mishi addu'a ita kuma
oyizah zan
mata lamfa in nuna mata kamar bazan fadama
kowa ba har
sai nasan yadda nayi har Allah ya bawa Affan lfy.
[10:11PM, 24/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI 27◆◆
By
SULAIMAN BOMBOY

Juya kan motarshi yayi ya nufi gurin wani babban
malami
dake zaune a Tarauni,
saida ya jira malamin ya gama da almajirai
sannan ya
shiga suka fara zantawa,
Bayan malamin ya gama jin bayanin jabeer sai ya
jinjina kai
yace tabbas imani yayi karanci a wannan
zamanin, na dade
banji rashin imanin da har yakai wannan ba,
ya kalli jabeer yace in shaa Allahu zamu hadu mu
fadawa
Allah nan da kwana uku zuwa hudu komai zai
dai2ta kai dai
ka dauke kafarka daga gidan ka barta cikin
tunanin baka
fadama kowa dinba sannan kayi taka tsan tsan
da ita,
jabeer yace to malam nagode sosai ya ajiye musu
kudin
sadaka sannan ya mike ya fita,
Gurin malamai uku yaje a ranar duk yayi musu
bayani suma
sun dauki alkawarin yi mishi addua ba dare ba
rana,,
ranar jabeer ya yini cikin bakin ciki babu yadda
ummi da
Afeeya da hajja basuyi ya faďa musu abinda ke
damunshi
ba amma yaki fadi,
Afeeya har kuka tayi mishi duk dan ya fadi amma
bata
samu nasarar ya fada din ba,
Oyiza kuwa rasa yadda zatayi tayi, ya akayi
wannan mayen
yaron ya shigo gidannan ya hayo har sama yaji
sirrina,
kallon affan tayi da ya fara bacci saboda tsoron
abinda ya
gani a gate,
wani dogon tsaki taja a zuciyarta tana tunanin
yadda zatayi
da jabeer, yanxu tasan yama gama tona mata
asiri saboda
haka in ta dau mataki akanshi jama'a zasu
zargeta gara
tabi komai a hankali..
Kwana biyar da faruwar wannan alamari oyiza taji
shuru
babu Wanda ya tinkareta,
sannan alhj basheer bai canza mata ba kamar
yadda tayi
tsammani,
hakan ya bata karfin gwiwar fara aiwatar da duk
wani
mugun nufinta saboda a tunaninta tsafinta ne ya
toshe ma
jabeer baki ya ki fadawa mutane,
Shi ko jabeer hankalinshi a tashe yake dan duk
malaman da
yasa su addu'a kowanne larura ta faďa mishi,
daga wanda
ya rasa ďanshi sai wanda yayi paralys sai kuma
wanda ya
rasa mata,
cikin tashin hankali ya dawo gida yayi tagumi
yana tunanin
mafita,
"Kaka liman" ne faďo mishi a rai nan da nan ya
kira
wayarshi,
kaka liman yasa wayar a kunnenshi ba tare da ya
duba
wanda ya kirashi ba yace "malam dan boko dan
Bara'u
jikan limamin Daura ya ta dabo,"
jabeer yayi dariya yace lafiya lau kakan dan boko
ta dabo
na gaida Daura, ya kuma tsufa da tsohuwa,
kaka liman yace tsohuwa tana can tana damun
hura kasan
bata son ayi mata kishiya,
jabeer yace kai ka isa kayi ma Goggo kishiya,
kaka liman
yace kaji ja'iri kaima fa naga auren nan zakayi
nima ina ga
cikin satin nan zan nemo wata a cikin nan nijar
auro,
jabeer ya kwashe da dariya yace gara dai ka tafi
can dan
matan nigeria sun fi karfinka, kaka liman yace
lallai baka
san wanene Abdullahi ba,
a gobe in matarka nakeson aure tana ganina
shikenan kai
kuma taka ta kare, jabeer cikin dariya yace dan
Allah karka
kasheni da sauran raina, bari in fada maka dalilin
kiran da
nayi maka,
kaka liman yace inajinka,
jabeer ya kwashe komai ya faďa mishi har larurar
malamn
duk ya faďa mishi, kaka liman ya ajiye goron
hannunshi
yace wannan ta shahara matuka jabeer, ka kirani
zuwa
karfe takwas na dare zanyi binciken duk wani
kullin da
sukayi dan sai an fara takanshi kafin a tsunduma
cikin
addua,
a wannan karan bada malami zata gwabza ba da
ni "liman
dan Baba" zata gwabza jinina da duk na wani
nawa ya fi
karfin matsafa saidai idan abun yazo da karar
kwana,
jabeer yace to zan kiraka kaka nagode sosai,
kaka liman yace ďan nema rike godiyarka in zaka
taho ka
siyomin shaddoji da kayan mata in haďa a lefe in
auro
sabuwar amarya, jabeer yayi saurin kashe wayar
yana
dariya...
Duk wasu abubuwan tsafi da kulle kulle babu
wanda kaka
liman bai gani ba, abinda ya kasa ganewa shine
na zeenatu
gata nan dai an nuna mishi ita a baccinshi bata
motsi kuma
an nuna mishi tana nan kusa dashi saidai baisan
takaimai
gurin ba,
ko da yayi ma jabeer bayani yace dole akwai
hake haken da
sai an haka sannan za'a warware abubuwa sai
hayaki da
wasu magungunan da zai haďa mishi, dan haka
ya bashi
kwana uku yazo ya sameshi sai suyi wanda
zasuyi a daura
sauran ya tafi dashi ya karasa a kano,
jabeer yaji daďi sosai ya dinga ma kaka godiya
saboda
yasan ko ba komai abokinshi zai samu lafiya
kuma zaayi
punishing oyiza 4 her deeds,
Tun daga ranar kaka liman yake aiki babu dare
ba rana duk
da ana yawan kawo mishi farmaki cikin dare haka
suke
gwabzawa har su hakura su tafi su barshi,
ranar kuwa da ya gama haďa magungunan saida
gidanshi
ya kusa rushewa saboda girgiza,
bai wani tsorata ba saboda shima hatsabibin
bafulatani ne,
a cewarshi shi a duniyar nan baiga abin tsoro ba
banda
Allah shi kadai yake tsoro a ko dayaushe amma
mutum dan
adam wanda Allah ya ara ma lokacin tsafi ko
wani abu to
ba abun tsoro bane dan idan Allah ya tashi
tarwatsasuu a
lokaci daya zaiyi ba tare da bata lokaci ba...

◆◆ RABO AJALI 28◆◆ By
Sulaiman Bomboy

Sati ďaya ya rage bikinsu,
lokacin yayi daidai da kammala jarabawar su Afee,
Fitowarsu kenan daga exam hall ita da safnah kowannensu
sai share zufa yakeyi, skul mosque suka wuce sukayi sallah
suka zauna bin inuwar gurin saboda gajiya, hira sukeyi duk
akan jarabawar da suka zana yau kuma ta karshe,
sai da suka fi minti talatin sannan suka mike da niyyar
tafiya gida,
a dai2 gate din fita makaranta suka tsaya ganin anyi
cincirundo kan wani yaro ďan ss2, Afeeyah tayi tsaki tace
dadina da skool dinnan son gulma dan Allah ji yadda aka
wani zagaye yaron can kowa so yakeyi yaji abinda ya
sameshi, safnah tace may be abin da ya sameshi babba ne
dan kuka yakeyi sosai gunin ban tausayi,
Afeeyah tace to Allah ya kyauta muje ko, safna tace ga
"Zulaikha Sambo" can tahowa bari tazo muji me ya faru,
Afeeya tayi tsaki tace dan Allah safnah mu tafi wato kema
kin fara son jin abinda bai shafeki ba ko,
kafin safnah tayi magana zulaikha ta karaso gurin su,
safnah tace Zully me ke faruwa a can gurin, zully tayi
fuskar tausayi tace wallhy mahaifiyar waccan yaron ce ta
rasu yanzu aka zo aka faďa mishi, safnah tace ayyah Allah
ya jikanta mutuwar mahaifiya ay babbar cuta ce tanada zafi
sosai walhy,
Afeeya da jikinta yayi sanyi tace Allah ya rahamsheta mu
kuma yasa mu cika da imani, suka amsa da ameen,
safnah tace ay mune abin tausayi Afee, gara ke tun kina
karama kika rasa taki yanzu zaiyi wuya wata mutuwa ta
girgiza ki,
zully tace kwarai kuwa,,
Afeeyah tayi murmushi tace har gobe ina tunawa da
mamana duk da bawani daďewa mukayi tare da ita ba,
wallhy kullum na kalli hotonta sai na zubar da hawaye,
mutumin dake debe min kewar tunaninta tun ina karama
shine wanda bana fatar rasa shi har karshen rayuwata,
ta kalli safnah tace kikace babu mutuwar da zata girgiza ni,
to wallhy kinji na rantse da Allah bana fatan mutuwa akan
yaya Jabeer amma ni nasan duk ranar da aka ce min ya
mutu to nima binshi zanyi in kuwa lokacina baiyi ba to
walhy ko in haukace ko in zama marar amfani,
dariya suka saka sosai safnah tace ay ke baki da hankali,
da in mutum na mutuwa ana binshi kuma Allah baya sa
dangana da duk wadanda suka rasa makusantansu suma
sun dade da mutuwa,
Afeeyah tayi tsaki tace dan Allah ya isa haka maganar
mutuwar Allah yasa mu cika da imani,
suka amsa da ameen sannan suka wuce zuciyar Afeeyah a
dagule dan ta tsani zancen mutuwa...
Ranar haka Afeeyah ta wuni sukuku,
wasu irin muggan tunanin mutuwa takeyi, da taga abin
bazai fishsheta ba sai ta ďauki qur'ani ta fara karantawa,
a haka jabeer ya tadda ita,
gaisheshi tayi haďe da ajiye alqur'anin a mazauninshi,
kusa dashi ta dawo ta zauna ta zuba mishi ruwan da hajja
ta ajiye mishi ta mika mishi tana kallonshi, kallonta yayi
shima da ya karbi ruwan yace yau naga duk kin wani natsu
ne ko wani ne ya taba min ke,
ta gyada mishi kai,
ya ajiye ruwan hannunshi yace to menene, ko kina son wani
abu ne,
ta kara girgiza kanta,
ya bata rai sosai yace akwai damuwa a fuskar nan kinada
wanda zaki faďawa da ya wuce ni,
tace um um,
yace to fada min da sauri kinji, idonta ya ciko da kwalla
muryarta na rawa tace ba komai,
hajja tace iskanci ne kawai fa da shagwabar banza yau ko
abinci bata ci ba saboda abin ya motsa,
jabeer yace dan Allah hajja kiyi shuru karki kara bata min
ranta, tashi muje waje ki faďa min kinji,
ta mike jiki a sanyaye suka fita,
a zaure suka tsaya ya kalleta yace ki mayar da kukan nan
kar ki bari ya zubo, in naji abinda ke damunki ya cancanci
kuka sai in tayaki muyi tare kinji,
ta gyada kai har lokacin kwallah na makale a cikin idonta,
yace to inajinki waye ya taba min ke,
ta shagwabe fuska tace ni ba abinda ke damuna kawai dai
ina tunanin mutuwa ne,
ta shige jikinshi sosai tace yaya jabeer ay bazaka mutu ka
barni ba ko,
ya sa hannunshi ya kankameta hade da lumshe idonshi
yace mutuwa lokaci ne Afee babu wanda yasan ranar
mutuwarshi,
ta dago kanta tace ni nasan lokacina yaya jabeer,
jabeer ya tallabi fuskarta yace

Please Login or Register in order to submit comment