Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinyar nan ta dubi salma ta
tsinka mata
mari,
Afeeyah ta durkushe ta fashe da kuka tace dan
Allah daddy
ka kaini gurin hajja, wallhy kasheni zasuyi, dukana
sukeyi
kullum, yanzu ma dukana suka gama yi har suka
yaga min
riga,
dan Allah ka kaini gurin hajja,
kafin alhj basheer yayi magana mahmud dan
suwaiba ya
shigo rike da kular abinci a hannunshi,
ta gefen ido Afeeyah ta hangoshi cikin muryar kuka
tace
mamu kai min daki ka dauko kular jiya,
alhj basheer cikin mamaki yace meye a cikin kular
nan,
Afeeyah tace abincin rana na ne,
alhj basheer cikin tashin hankali yace duk abincin
dake
gidan nan sai an kawo miki abinci daga gida,
oyizah da ta gama tsurewa tace umm al---
Afeeyah ta
katseta da sauri tace sunce abincin gidan nan ba
na
talakawa bane wai ban saba cin irin shi ba saboda
haka kar
in taba musu,
oyizah ta sankare cikin mamakin sharrin da
Afeeyah ta lafto
musu,
alhj basheer ya juya ya kalleta cikin tuhuma tayi
saurin
cewa wallhy karya take min alhj, ya za'ayi in
hanata abinci,
alhj basheer ya kalli mahmud yace kai tun yaushe
kake
kawo ma Afeeyah abinci, mahmud yace kullum
nake kawo
mata da safe da rana da daddare,
alhj basheer ya saki salati yace kin kasheni safiya,
kin tozarta ni a unguwar nan, yanzu kowa ya
gama sanin
sirikata daga gidansu ake kawo mata abinci,
oyizah tace wallhy alhj kar---rufe min baki ya fadi
cikin daga
murya,
ya dago Afeeyah ya kalli wuyan rigarta yace yi
shuru ki
share hawayenki karki kara cewa zaki je gida
sannan yau
ďinnan zan siyo miki komai na abinci ki dinga
girkawa kina
ci a dakinki,
salma cikin kuka tace daddy marin da yarinyar nan
tamin
taci bulus kenan,
alhj basheer ya juyo yakai mata wani marin a baki
yace in
mafaďin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa
bane,
yaya za'ayi Afeeyah ta iya daga hannu ta mare ki,
salma cikin kuka sosai tace na rantse da Allah
daddy ta
mareni,
ta kalli Afeeyah suka hada ido ta sakar mata
gwaloo hade
da murmushi salma ta kara tunzura tayo kanta
zata duketa
alhj basheer yace wallhy tallahi kika taba yarinyar
nan sai
na lahira ya fiki jin dadi,
oyizah dai tana tsaye kamar gunki mamakin
Afeeyah ya
hanata cewa komai, haka suwaiba,
Affan ne ya fito da gudu jin muryar mahaifinshi,
rungumeshi
yayi iya karfinshi yace daddy ka dawo,
alhj basheer yace na dawo Affan kana nan lafiya
ko,
Affan ya noke wuyanshi ya haďe rai yace daddy
nayi fushi
da Afeeyah bazan kara mata magana,
alhj basheer yayi murmushi yace me tayi maka,
Affan yace batason wasa dani kullum sai su anty
salma
suyita sata aiki ta goge can, ta goge nan, tayi girki
da yawa
kuma ita bata ci, kuma sai ta rufe kofa ta hanani
shiga
inyita bugawa taki buďewa,
alhj basheer ya harari salma da oyizah sannan ya
kalli
Afeeyah yace meyasa bakya bude mishi kofa,
oyizah tayi saurin cewa dan Allah alhj kabar
maganar nan
muje ka huta anjima sai ayita,
alhj basheer bai kalleta ba yace Afeeyah dake nake
magana,
Afeeyah ta dago kanta ta kalli oyizah da zufa ya
jikata tace
daddy saboda shan maganinshi ne na dare, kafin
lokacin
yayi nayi bacci bana sanin yana bugawa,
oyizah ta saki ajiyar zuciya a hankali..
alhj basheer yace wannan ba hujja bace daga yau
ma duk
magungunshi ke zaki dinga bashi,
Affan ya kalli oyizah yace mummy wai ita zata
dinga bani
magani?
Oyizah ta haďiye miyau tayi murmushi tace eh
hakan ma
yafi, Affan ya kalli Afeeyah yace zaki dinga bani
magani
dakyau yadda mummy take bani,
Afeeyah tayi murmushi ta saci kallon oyizah tace
sosai ma,
kasani ma ko in fita iya baka da kyau,
yayi tsalle ya rungumeta yace to muje mu dauko
magungunnan mukai dakin mu ko,
alhj basheer yayi dariya yace banason shirme ka
bari
mummynka zata kawo maka har ďaki,
ya kamo hannun Afeeyah yace zo muje muyi wasa
irin na
rannan,
Afeeyah tayi saurin fisge hannunta ta wuce daki
cikin jin
kunya, ya bita a baya da gudu,
alhj basheer ma daki ya wuce ba tare da ya kalli
oyizah ba,,
suwaiba tace kinga abinda nake faďa miki game da
yarinyar
nan ko,
oyizah tace uhummm kawai ta wuce daki salma ta
bita har
lokacin kuka takeyi,,, suwaibah taja gyalenta itama
tayi
waje...
Karfe huďu na yamma alhj basheer ya dawo gida
motarshi
cike da kayan abinci,
masu aikin gidan maza su suka shiga da kayan
lokacin
Oyizah na zaune a parlor tana ta tufka da
warwara, ko
kallonsu batayi ba har suka gama shigewa da
kayan suka
fita,
shigowar alhj basheer ne yasata mikewa da sauri
tana
mishi sannu da zuwa, bai amsa mata ba yace kin
kai wa
Afeeyah magungunan,
oyizah tace yanzu zan kai mata alhj, dan Allah ka
fahimceni
wallhy--yayi saurin dakatar da ita da hannu yace
babu
abinda zaki fada min in yarda,
tsakani da Allah safiya a bani amanar yarinya ku
hadu ke
da yayanki ku dinga kuntata mata,
oyizah ta fashe da kuka tace wallhy alhj sharri tayi
mana,
kaima kasan abinda zanyi da wanda bazanyi ba,
yace in ke baki mata ay yayanki na mata kuma
bakya
tsawatar musu,
Oyiza ta kara tsananta kukanta tace dan Allah kayi
hakuri
wallhy zan dauki kwakwaran mataki akan su,
dakyar alhj basheer ya hakura kuma yasa ta kira
su salma
yayi musu concrt warning akan Afeeyah...
Tun bayan magriba ta gama girkinta daidai cikinsu
ita da
Affan da tunda ya bita ďaki har lokacin bai fito ba,
bayi ta shiga tayi wanka tayi alwala ta fito ta tarar
dashi
yana game har lokacin, kwace game din tayi cikin
dabara
tace tashi muje kayi wanka,
ya noke wuyanshi yace nayi wanka da safe,
ta bata rai tace to tashi ka fitar min daga ďaki,
ya marairace fuska yace me nayi miki, tace saboda
bazan
iya zama da mai datti a ďaki ba,
ya kalli jikinshi yana zaro ido yace jikina babu datti
fa kalli,
tace ay kai bazaka ga dattin ba ni kuma gashi nan
ina gani,
in dai bazaka tashi kayi wanka ba to ka fita min a
daki
kuma karka kara min magana,
Affan ya tashi kamar zaiyi kuka ya cire rigarshi ya
turo baki
yace muje to ki zuba min ruwa, tace muje,
ya wuce bayin yana turo baki ta bishi a baya,
ba karamin cire kunya tayi wajen tsayawa ta nuna
mishi
yadda zaiyi wankan tsaki ba,
saida ta tabbatar yayi wankan tsarki da kyau dan
ta san
najasa ce dankare ajikinshi ko rashin sallah ma ay
ya
dankarar da dattin najasa a jikinshi,
yana gamawa tasa yayi wankan sabulu yanata
wasa da
ruwa a bayin yana gama wankan tasa shi yayi
alwala
dakyar, ta lallabashi ya fito daga bayin daure da
towel
ajikinshi,
saida ta gyara bayin sannan ta fito ta zauna kusa
dashi
tana kallonshi yanata dariyar jindadi dan wata
mabanbanciyar iska ya dinga ji ajikinshi mai
matukar dadi,
a hankali tace ya kaji jikinka yanzu, ko wankan
baiyi maka
dadi ba,
wani irin kallo yayi mata sannan yayi dariya yace
naji daďi
sosai kullum zaki dinga koya min irin wankan nan
ko?
Afeeyah ta gyaďa kanta tace indai zaka dinga jin
magana
ba,
yace zan dinga ji sosai yanzu wani kaya zan sa, ta
mike ta
buďe drawerta ta ďauko jallabiya cikin sabbin
jallabiyoyin
da ke ďakin ta mika mishi tace tashi ka fesa turare
sai kasa
wannan rigar,
ba musu ya mike yayi yadda tace, itama ta shiga
bayi ta sa
jallabiyarta ta fito,
kallonshi tayi yana balle button din jallabiyar shi
yana
murmushi,
karasawa tayi ta karasa sa mishi tace kaga yadda
kayi kyau
ka zama cikakken mutum,
Affan yayi dariya yace dama ni ba cikakken mutum
bane,
tace a'a ni ban ce ba yanzu dai kasan me zamuyi,
ya girgiza kanshi,
a hankali tace sallah, yace wattt,
tace sallah da karfi,
juya mata baya yayi yace um um, ta dawo
gabanshi tace
baza kayi ba,
ya gyaďa mata kanshi, ta kamo hannunshi a
hankali tana
murzawa idonta cikin nashi tace dan Allah kazo
muje muyi
sallah,
kana son muyi irin wasan da mukayi rannan,? a
kasalance
ya ďaga mata kai, tace to zo muje muyi sallah kaji,
Affan ya noke wuya yana magana a shagwabe
yace
mummy tace akwai wahala,
Afeeyah tace babu wani wahala zo muje kaga
yadda akeyi
kaji,
ya fisge hannunshi yace ni bazanyi ba ki
kyaleni..... ran
Afeeyah ya baci sosai ta wuce ta barshi tsaye ta
ďauki hijab
ďinta tasa, zata tada kabbara kenan taji ya
rungumeta ta
baya..... Cikin fushi tace dalla ni sakeni in gaida
ubangijin
da ya
halicceni kuma ya raine ni da ni'imominsa,
Affan ya kwantar da kanshi a kafadarta yace ni
kike ma ihu
ko?
Tayi tsaki tace ay kai duka ne ma ya kamace ka
ba ihu ba,
ya dawo gabanta yayi narai2 da ido yace zaki iya
duka na,
tace sosai ma in dai bazaka dinga yin sallah ba,
ta tallabi fuskarshi da hannunta ta rage murya
tace kasan
falalar dake cikin yin sallah?,
Affan ya girgiza kanshi,
tace ko na fada maka bazaka gane ba,
ka faďa min duk abinda kakeso wanda yake ranka
yanzu,
ya rufe idonshi cikin murna yace ammmm inason
ganin
abokina, ya bata rai kamar zaiyi kuka yace abokina
ya gudu
ya barni ya daina zuwa guri na nayi fushi dashi,,
idon Afeeyah ya ciko da kwallah tace kar ka damu
zaizo ya
ganka, amma fa sai ka yarda kayi sallah, yace in
nayi zaizo
tace sosai ma,
Affan yace to sai kuma ina son kullum ki dinga
tayani wasa,
mu buga game tare, mu buga kwallo tare, Afeeyah
tayi
saurin cewa har abinci ma tare zamu dinga ci mu
dinga
bacci tare amma fa sai ka yarda kayi sallah,
ya daka tsalle yace yeeee zanyi,
Afeeyah tace sai me kuma,
ya bata rai yace sai kuma su anty salma, banason
suna min
ihu suna zagina wata rana harda duka na akai, in
nayi
sallah zasu daina, tace sosai ma, ai in ka yarda
kayi sallah
ko sun maka ihu zan rama maka,
yayi dariya yace yauwa barbie na to muje muyi
sallah,
ta dauko dadduma ta shimfiďa mishi duk da tasan
ba daidai
zaiyi sallar ba amma gara yayi wit tym zai fara
yinta daidai,
Guri ďaya suka tsaya ya maida hankali yana yin
duk abinda
tayi yana waige,
isha'i sukayi da shafa'i kadai banda wutiri,
saida ta gama lazimi sannan tace mishi ya ďaga
hannunshi
sama kamar yadda tayi, yayi yadda tace,
tace yauwa to duk abinda nace kace "Ameen" ya
sauke
hannunshi yace nace "Ameen" tace a'a kar ka
sauke hannun
ka ďaga hannun, yace "Ameen"
tayi dariya ta kama hannunshi tace haka zaka
barshi, ya
kuma cewa ameen,
cikin dariya ta fara karanto adduo'i yana cewa
Ameen,
inuwar mutane ta gani a kansu ta ďago da sauri ta
kallesu,
bata tsayar da addua'r ba saima sake mata salo
da tayi ta
hanyar faďin
"Auzubillahi minash shaidann rajim"
Affan yace ameen da karfi yana kallon oyizah dake
huci
fuskar nan babu annuri,
salma ta daka mishi tsawa tace tashi ka fita a
dakin nan,
jikin Affan ya fara rawa yana kokarin mikewa
Afeeyah ta
matse hannunshi ta shafa addua'r da ta idar tace
ina zaka
je,
Fareeda tace gidan uwarki zaije, tashi ka fita ko in
tattaka
ka,
Afeeyah tace ikon Allah, to dai nasan Affan baida
wani
dakin da ya wuce na matarshi,
saboda haka babu inda zashi,
oyizah cikin fushi tace kika ce me?
Afeeya ta kalli salma tace maimata mata inaga
kamar tana
da matsalar ji,
salma cikin fushi ta kai mata naushi da sauri
Afeeyah ta
kauce tace toh fah!!, ashe dai rashin aure ba
masifa kadai
yasa ku harda harkar dabanci, fisabillihi ku ko
kunya bakwa
ji, ni bansan meyasa kuke bakin ciki dani ba dan
nayi aure
at dis age of mine, dan Allah ku barmu muci
soyayyarmu ni
da mijina zan muku addua' kuma Allah ya kawo
mashinshini
nan bada dadewa ba dan rik'ar da kukayi a gida ta
isa haka,
abun ma ni har tausayi yake bani,
babu wanda ya iya cewa komai sai kallon mamaki
da suka
bita dashi,
cikin karfin hali salma tace ina mijin yake anan da
zamuyi
bakin ciki,
ke nan har wani miji ne, wannan tababben da
baisan kanshi
ba ma bare mace,
Afeeyah tayi saurin cewa tabdijam,, ke kike ganin
tababbe,
ta rungumoshi tace ni nan namiji nake gani wanda
a cikin
maza ma sai an tona kafin asamu irinshi,
dan Allah ku fitar mana a ďaki dan naga alamar
baku san
wannan lokacin na hutawar ma'aurata bane,
fareedah ta harzuka matuka ta ajiye maganin
hannunta tayi
kan Afeeyah zata duketa oyizah tayi saurin dakatar
da ita
da hannu, tace barta fareedah wallhy sai tasan ta
faďa
muku wadannan maganganun,
kuzo mu tafi,
Afeeya tace to sai da safenku Allah ya aurar daku
ku huta
da kunci, amma fa mummy baki nuna min yadda
zan bashi
maganin ba,
oyizah kamar ta rusa ihu tasa kai ta fita ba tare
da ta bata
amsa ba,
Afeeyah ta bisu da li'ilah fi quraish ta datso kofar
ta dawo
ta kalli Affan da ya gama tsurewa tace matsoraci
to sai ka
zauna tunda dodonka ta tafi,
Affan ya zauna murya a sarke yace mummy tayi
fushi dani
ko,
Afeeyah tace batayi fushi ba bari in kawo maka
abinci kaci
sai kasha magungunanka kayi bacci kaji,
Affan ya gyaďa kanshi,
Da kanta ta bashi abinci yana gama ci yasha ruwa
da drink
ta dauko magungunan da oyizah ta kawo,
saida ta karance su tsaf ta kalli wani ruwan jarka
shi ba ja
ba shi ba maroon ba, daga kafadarta tayi tace may
be na
gargajiya ne,
na asibitin ta fara bashi duk wanda ta kai bakinshi
sai tace
yayi bismillah sannan zata zuba mishi,
tana bude na jarkar taji wani karni karni, da kyar ta
tsiyayya
a cup tace wa'iyazubillah wannan irin karni haka,
ta mika
mishi tace kayi bismillah, yana yin bismillah ya kai
bakinshi
yaji hannunshi na rawa sosai, da kyar da taimakon
Afeeyah
ya shanye maganin,
boye magungunan tayi ta gyara gurin ta dawo ta
zauna
tana mishi hirah yana kyakyata dariyah harda buga
kai a
pillow,
sun shagala sosai cikin farin ciki Afeeyah taji ana
buga
musu kofa, mikewa tayi tana mita a zuciyarta,
tana budewa taga oyizah tsaye kamar gunki,
Afeeyah taja baya tace kin dawo ne mummy,
Oyizah ta kalleta tace tambayar da ya kamata kiyi
min
kenan ni da gidan mijina, Afeeyah tayi dariya tace
to ai
wannan tambayr tafi da inyi miki shuru in kyaleki,
kuma
nima nan turakar mijina ce,
oyiza tace wallhy zan babbalaki a gidan nan in
bawa
karnuka kasusuwanki su cinye,
Afeeyah tace waii ay ko da sunci kashi da wahala
dan
wallhy kashi na taurin tsiya gareshi,
oyizah tayi shuru dan taga abinda ke neman fin
karfinta
tace kin bashi magungunan,
Afeeyah tace wannan dole ne tunda inason mijina
ya samu
sauki, oyizah tace akwai wani a jarka ki tabbatar
yasha
dama dan in jaddada miki ne yasa na dawo,
Afeeya tace karki damu in ma akwai wani ki karo
bazan
gajiya ba,
oyizah tayi tsaki ta wuce ranta a bace,
ta riga ta gama kudirawa a ranta a daren nan zata
lalata
rayuwar yarinyar nan, wallhy yau sai tasan ta tabo
ni, dan
bazan barta ba abinda ta dinga fadi kenan,,,,,
To oyizah sarkin sa'a muna miki fatan nasara
akan
Afeeyah... ...

DON ALLAH AYI MIN AFUWA AKAN RASHIN KAWO MUKU DA WURI DA BANA YI. HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON MUNA GAB DA RAFA EXAM, SO ZANDAN-ZANDAN YA DAN FARA MIN YAWA.
NA GODE DA ALFARMAR KU.
.
@RABO AJALI@
<46 TO 48>
.
BY SULIMAN BOMBOY.
.
. Tun sha biyun dare Afeeyah ke jin wasu irin
sautittika masu
ban tsoro ta windon ta,
kallon Affan tayi yana baccinshi hankali kwance,
cikin dabara ta cire hannunshi a jikinta ta gyara
mishi kwanciya ta mike a tsorace saboda sautin karuwa
yakeyi,
cikin karfin hali da dakewar zuciya ta ďaga labulen
windon
dakin,
sakin labulen tayi da sauri taja baya tana maimaita "HASBUNALLAHU WA 'NI'IMAL WAKIL" saboda
ganin wasu
halittu masu ban tsoro kewaye da windon,,,
wani kara taji an saki nan take taji ďakin da suke
ciki
yana girgiza ta ko'ina,
runtse idonta tayi tana karanto adduo'in neman
tsari,
da dai taga kamar kara girgiza ďakin akeyi sai tayi
karfin
halin buďe kofarsu cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da
ďakin oyizah, Tana zuwa kofar dakin ta kama
murfin xata bude taji
sautin
magana da karfi wanda ya sata sakin kofar bata
shirya ba, sunanta taji sosai ana kira a ďakin ta kuma ji
wannan
sautin na windon su ya dawo nan inda take tsaye,
a gigice ta leka ta windo don jin mai ambaton
sunanta cikin
wannan sigar a kuma wannan talatainin daren, tana lekawa ta hango oyizah cikin jajayen kaya
tsugune gaban "chummy,"
sai wani bakin basamude a tsaye a gafensu rike da
wani
bakin kare,
Afeeyah bata kara firgita ba sai da taga oyizah ta dauki kwaryar jini ta shanye tass sannan ta kara
daukan
wani
ungulu tana kiran sunanta dashi,
fitsari ta saki nan take saboda ganin duhu ta ko'ina
bata iya hangen gabanta, lalube ta fara yi tana addu'a da
karfi tana kiran
sunan hajja
dan ta tsorata matuka da abin da idonta ya gane
mata, ga
wannan girgizar har lokacin bata bar jinta ba, a cikin laluben taji hannunta ya taba mutum, nan
take ta
tsandara ihu haďe da faduwa kasa sumammiya,
A gigice alhj basheer da ya fito dan ganin abinda ya
samu
wutar gidan ya haskata da torch light, cikin kidima ya fara kiran sunanta yana fadin
innalillahi wa
inna ilaihir rajiun, safiya, safiya,
oyizah ta tsorata matuka da jin muryar alhj basheer
dan
tasan yayi bacci, cikin azama ta tattara kayan tsafinta ta cire na
jikinta ta
mayar da night gown din jikinta ta fito tana mutsika
ido,
alhj basheer yace safiya zo ki kama min yarinyar
nan mu
kaita asibiti ko numfashi bata iya yi na rasa me ya
fito da
ita cikin daren nan,
oyizah ta matso da sauri tace wace yarinya,
alhj basheer yace Afeeyah ce, kamata da sauri dan Allah,
oyizah cikin murna ta kama Afeeyah dan a
tunaninta tsafinta ne ya kamata,
suna fitowa wutar gidan ta kawo alhj basheer ya
bude
motar suka tura Afeeyah ciki, oyizah ta koma ta dauko hijab
dinta suka wuce asibiti, Tunda aka kaita asibiti a
wannan daren likitoci ke iya
kokarinsu suga ta farfaďo amma abin yaci tura,
oyizah cike da murna ta nemi guri ta zauna a
zuciyarta tace yarinya ai tunda kika shiga gona ta sai kinyi noma
wallhy, alhj basheer kuwa hankalinshi ba karamin
tashi yayi
ba dan
baisan meye ya sami yar mutane ba, safa da marwa
kadai yakeyi a cikin asibitin,
dakyar doctor musah ya lallabashi akan in shaa
Allahu
zuwa gobe zata farfado in kuma bata farfado ba sai
musan
abin yi, alhj basheer akanta ya kwana ko runtsawa baiyi
ba,
ana kiran sallar asuba yaje yayi sallah ya wuce
gidan malam atiku,
hajja a firgice ta fito idonta ya ciko da kwallah tana
tambayar wane asibiti, alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja,
safiya na
can zaune da ita ba sai kin je ba, hajja tace inaaa
aiko sai naje wallhy, ai kowane aiki
da
wakilinshi bazamu daura mata nauyin jinya ba, malam atiku yace Baba ay tunda yace kar--- tayi
saurin
katseshi tace walhi danbaba babu abinda zai
hanani zuwa
gurin hajara,
alhj basheer yace to shikenan hajja muje, tayi saurin sa takalmi jiki na rawa ta bishi,
Suna isa asibitin suka tarar oyizah na bacci Afeeyah
kuma bata farfaďo ba har lokacin,
gefenta hajja taje ta zauna tana kuka tana tofa mata
addu'a,
alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja babu
abinda zai sameta bari muje gida a kawo muku
abinci, hajja
tace to sannu alhj an gode,
alhj basheer yace haba ai yiwa kai ne nima ay yata
ce, ya kalli gurin da oyizah ke bacci ya dan bubbugata
tayi firgigit ta farka tace
"an gama komai ko"
alhj basheer yace me aka gama,
oyizah ta fara goga ido tace na dauka doctor ne,
alhj basheer yace bashi bane ki sameni a mota mu wuce gida,
dakyar ta gaida hajja sannan tabi bayan alhj
basheer
suka
wuce gida...
Alhj basheer na shiga parlor ya tarar da Affan zaune
a kasa ya haďe kai da gwiwa yana kuka sosai,
da sauri ya karasa kusa dashi ya dagoshi yace
meya
faru
dan gidan daddy, Affan ya kwanta kan jikinshi yace daddy tun dazu
nake neman Afeeyah ban ganta ba na duba ko'ina
bata
nan naje
gurin mai gadi yace kai ka dauketa ka fita da ita,
daddy ina kuka kai ta?
Oyizah tayi saurin matsowa kusa dashi tace sorry
my baby
Afeeyanka taje siyo maka abun dadi zo muje kayi
wanka
kafin ta dawo kaji, cikin rashin gamsuwa da kalamanta yace mummy
karfe nawa zata dawo,
oyizah tayi murmushi tace 10 zata dawo kaji, Affan
ya
gyada kanshi, tace yauwa baby muje kayi wanka
kasha magani ko, taja hannunshi suka wuce zuciyarta
wasai dan jiya
kadai
Afeeyah ta kusa daura mata hawan jini yanzu
kuwa
zata ci karenta babu babbaka tunda ta tafi 4 good....
Goggo ta kalli kaka liman bayan ya gama karyawa
tace sai
tafiya ko,
ya goge bakinshi yace in shaa Allahu ai yau "ta
dabo' tayi kirah, goggo tace da ka bari sai gobe saboda
akwai
daddawa da dawo da zaka tafin ma da Abida dashi,
kaka liman yace ai ciwo ko mutuwa ne kadai zai
hanani isa
ta dabo yau, Ke bazan ma iya bacci ba in banje ba,
tace to Allah dai ya tsare wannan tafiyr ta gaggawa,
yace ameen ke kike ganinta haka ni kuwa a guri na
ba
gaggawa bace saboda na dade ina sa rana banje
ba, mafarkin da nayi jiya shi ya tabbatar min da
wannan
lokacin ne lokacin sa'a a garemu, Goggo tace to
Allah ya
bada sa'ar wannan sirrintaccen aikin da ko ni kaki
yarda ka fada min,
kaka liman yayi dariya yace ameen ta liman, aikin
ne
saida
sirri, tace haka ne ai sirri a komai ma yana da kyau
Allah ya dawo daku gida lafiya, ya mike tsaye yana faďin ameen ameen,
har zaure ta rakashi inda drivernshi da alhj bara"u
ya
ajiye
mishi yake jiranshi,
saida suka sha mai a filling station sannan suka dauki
hanyar KANO TA DABO TUMBIN GIWA....
Tiryan tiryan abubuwan ke dawo mata cikin
kwakwalwarta,
a hankali ta fara motsa jikinta tana girgiza kanta,
wadannan halittun ta dinga gani kewaye da ita suna kokarin
shigewa jikinta,
wani irin ihu ta saki haďe da faďin hasbunallahu
wa
ni'imal
wakil, hajja dan Allah kizo ki taimakeni zasu kasheni,
zasu kasheni, wayyyo Allah nah, Hajja tayi saurin
katse sallar da takeyi ta yo kanta da
gudu
ta riketa, nan fa ta kara fasa wani ihun a firgice tana
fisge jikinta,
addu'a hajja ta fara karantowa da karfi tana tofah
mata,
a hankali ta bude idonta, ganin hajja ce zaune a
gabanta
yasa ta faďa jikinta tana kuka tana faďin kasheni zatayi
hajja, wallhy kasheni zasuyi, dan Allah ki gudu dani
gida,
a firgice hajja tace wacece zata kashe ki,
kafin Afeeyah tayi magana doctor musah ya shigo
dakin da sauri nurses na biye dashi a baya,
karasowa kusa da gadonta yayi yace sannu mama,
yanxu
nurse take fada min taji tana ihu,
hajja tace wallhy farkawa tayi a firgice tana ihu
bansan takamaimai abinda ke damunta ba,
doctor musah yayi gwaje gwajen da zaiyi yace dan
Allah
mama kice mata ta kula sosai ta daina yawan firgita
saboda cikinta baiyi kwarin da zai dauki hakan ba
dan bai wuce sati uku ba, Allah ma ya kiyaye cikin bai samu
matsala ba, saboda haka dan Allah a kiyaye, Hajja
cikin mamaki tace ciki doctor, doctor musah
yace
kwarai mama,
hajja tayi murmushi tace ikon Allah, To Allah ya inganta
mana, yace ameen mama ya bata magani yace in
taci abinci a bata tasha, hajja ta amsa ta mike da
sauri ta
hado
mata tea, saboda murna hajja bata kara bi takan zancen da
Afeeyah
ke mata ba,, Tana bata magani ta mike ta kabbara
sallah,
kafin ta idar su alhj bara'u suka shigo, Amirah ta
ajiye basket din abinci tayi gurin Afeeyah ta zauna tana
mata
sannu, Abida ma ta karaso cikin dakin tace ashe ta
farfado
alhj,
alhj bara'u yace saidai in yanzu ta farfado amma dazu da
muka zo da alhj basheer bata farfado ba,
Abida ta karasa kusa da ita tace sannu Afeeyah ya
jikin,
a hankali tace da sauki ummi,
Abida ta karasa kusa da hajja da ta idar da sallah ta tsuguna suka gaisa, tace hajja me suka ce yake
damun ta,
hajja tace to nidai har yanzu bansan dalilin firgicinta
ba
amma likita ya tabbatar tana dauke da karamin ciki
na sati uku,
Afeeyah tayi saurin runtse idonta saboda takaicin
fada musu da hajja tayi,
Allahu akbar alhj bara'u ya fadi yana murmushi,
Abida tace lallai Allah da iko yake, Allah ya fito
mana da
wannan zazzafan rabon lafiya, Hajja taji tausayin
Abida sosai a hankali tace Ameen,
nan suka cigaba da yar hirarsu ta manya duk akan
cikin,
Afeeyah dai tunda ta runtse idonta bata bude ba har
suka
tafi,,, Alhj basheer ma da yazo doctor musah ya
faďa mishi
ba
karamin farin ciki yayi ba,, bai wani dade a asibitin ba ya wuce gida dan kai
ma
su
safiya albishir,,, Da murnarshi ya shiga gidan, tun
kafin ya karasa
cikin parlon yake kwala ma oyizah kirah,
da sauri ta fito tana faďin alhj lafiya,
yayi dariya yace lafiya lau safiya albishirinki,
gabanta
ya faďi da taga yana dariya dan ta dauka kiran
fađin mutuwar
Afeeyah yakeyi mata,
a hankali tace goro, yace kin kusa samun miji ko
kishiya,
cikin rashin fahimta tace ban gane ba alhj, yayi
dariya yace ay dama bazaki gane ba tunda ba bahaushiya bace
ke,
to ina nufin kin kusa samun jika,
oyizah ta haďiye miyau dakyar tace kana ta min
magana a cukurkuďe a gurin wa zan samu jika,
alhj basheer yace kina da wani dan da ya wuce Affan
ne,
oyizah ta saki baki tace ciki matarshi ke dashi,
yace kwarai kuwa, kinga rabo ko,
ranar da aka sa aurenta da jabeer a ranar aka
daura auren da Affan kuma a ranar Rabo ya rantse kanshi,
oyizah da zufa ke keto mata ta ko'ina tace umm
hakane
yanzu ta farfaďo kenan,
alhj basheer yace garau ma tana can na barta a
zaune, oyizah ta mike tace to bari a haďa mata abinci a kai
mata
ko,
alhj basheer yace ya kamata kam, ki haďa mata
duk
wani abun da kika san me ciki na bukata in ma babu ayi
min
magana dan Allah, oyizah ta wuce tace to,
Zama tayi a kasa a dakinta ta zuba uban tagumi
tana
tunanin yadda akayi ta samu failure a aikin jiya, da kuma yadda akayi har ciki ya shiga jikin yarinyar
nan,
inaaa bazai yiwu ba dole cikin nan ya fita, dole ne in
kashe
yarinyar nan dan wallahi bazan yarda ta sake
dawowa gidan nan ba, mikewa tayi zubur ta wuce kitchen ta shiga
shirya
abinci
daidai cin mutum daya, tana yi tana zancen zuci dan
bata
taba yin aiki irin haka ta samu failure ba.. Gab da la'asar kaka liman ya bayyana a asibitin, a
zaune ya samesu hajja ta tasa mata abinci a gaba
tana ci,
fuskar hajja dauke da fara'a ta gaishe shi ya amsa
yana
kallon Afeeyah, Afeeyah ta sunkuyar da kanta ta gaishe shi ya
amsa yana
murmushi yace ya jikin kuma,
Afeeyah tace da sauki, ya zauna a kan kujera yace
to
Allah ya karo sauki, suka ce ameen ita da hajja,
saida suka dau kusan minti biyu shuru sannan ya
kalli hajja
yace dan Allah hajja in bazaki damu ba ko zaki dan
bamu
guri, Hajja ta mike tace haba babu komai wallhy ta fita
daga dakin,
Bayan fitar hajja da kamar minti uku kaka liman ya
kalleta
yace ya mai gidan naki,
Afeeyah tace yana nan lafiya kaka, kaka liman yace lafiyar ciki ko ta waje, Afeeyah ta
dago cikin rashin fahimta tace ban gane
ba
kaka, yace ina nufin wace irin lafy, lafiyar koshin
lafiya ko
kuma ta duka harda kwakwalwa, Afeeyah tace lafyr koshi kaka, sannan lafiyar
kwakwalwarshi ma ina tantama akanta,
wani lokacin in yayi abu kamar cikakken me lafy
baya
mintina kuma sai ya koma kamar da,
kaka liman yace to yaya kika fahimci mutanen gidan,
ina nufin a tunaninki wane irin zama sukeyi da
yaron
nan, kina
ganin suna kaunarshi tsakan--- sammm ta katse
kaka liman, tace muguwar tsana sukayi mishi wallhy,
amma a gaban daddy sai su nuna basu da
kamarshi, sannan kaka bata barinshi yayi sallah,
duk wata
ibada bata
barinshi yayi, sannan kaka jiya da dadd--- yayi saurin
katseta yace tambaya daya nayi miki,

Please Login or Register in order to submit comment