Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Affan da jikinshi ke kyarma
suka
wuce daki a zuciyarta tace 99days 4 the thief muje zuwa,
Allah dai ya kara bani sa'a...
Tun karfe hudu na yamma oyizah ke gurin
chummy cikin
matsananciyar damuwa tana faďa mata anyi
destroying fishpond dinta na tsafi,
dariya chummy tayi sannan ta buga kasa nan take
ya tsage
ruwa haďe da kifaye suka fara fitowa daga ciki,
saida suka
gama fitowa tsaff sannan suka haďe kansu guri ďaya,
oyizah tayi murmushin jin dadi tace ashe suna nan,
har hankali na ya kwanta, bacewarsu ba karamin
daga
hankali na yayi ba dan ba karamin taimako na
sukeyi ba, chummy tayi dariya mai karfi tace fitarsu a gidanki
tonan
asirinki ne saboda haka kisan duk yadda zakiyi ki
mayar
dasu gidan nan Affan ya dinga ganinsu kullum,
oyizah tayi tagumi tace ta yaya zan mayar dasu bayan alhj
da kanshi yace a fitar dasu,
yanzu ina komawa dasu zai fara zargin wani abu,
chummy tace karki damu, akwai abun da zan baki
kisa
mishi a abinci daga yaci shikenan ko yagansu hankalinshi
bazai kawo su bane,
oyizah tayi dariyar jin daďi tana faďin thank u my
lord,,
mikewa oyizah tayi ta shigo da wani yaron da zasu
sha jininshi a gurin meeting,
da ganin yaron kasan mugun takadiri ne dan ko
gezau baiyi
ba idonshi a soye babu alamar hawaye,
dakyar ya tsuguna a gabansu,
chummy ta harareshi sannan ta umurceshi da ya miko
mata kafafuwanshi,
tirjewa yayi yaki mikowa, babu yadda batayi ba
akan ya
miko kafafuwanshi tayi wani aikin dasu yaron nan
yaki, kwala kiran BULADUNA tayi nan suka shigo shida
abokin
aikinshi,
cikin isa ta umurcesu da su kamo yaron su kawoshi
gabanta,
da karfinsu suka fara kokarin kama shi yana tirje musu
yana tokarinsu da hannu, sai sun daukeshi sunyi
sama
dashi sai yasa iya karfinshi ya zille ya fado kasa,
daukar da sukayi mishi na karshe ne yasashi wani
irin kukan kura ya hankaďe buladuna yayi baya,
tartsasssssss sukaji dukansu suka duba gurin da
sauri,
glass din da fanne da fanna ke ciki ne yayi tarwatse
ya bullo
tun daga bayan buladuna har cikinshi, nan take ya fadi kasa
matacce, da sauri su chummy suka yo kanshi suna
kiran
sunanshi,
su kuwa su fanne cikin azama suka fito cikin glass
suka nufi gurin yaron da aka kamo da niyyar taimaka
mishi ya
gudu,
cikin tausayawa yace ku meyasa bazaku zo mu tafi
tare ba,
fanne cikin sauri tace mu matattune gawar mu ta dade a
rami kai kuwa ba'a riga an birne gangar jikinka ba
kayi
saurin komawa gida,
da sauri yace waye ya kawo ku nan,
fanna tace mahaifin mu ne Alhj sambo ministern Abuja na
yanzu,
kafin yaron yayi magana ya hango su chummy sun
doso su
suna kokarin kama su fanne,
da sauri kurwar yaron tabi ta inda su fanne suka nuna mai
ya bace daga gurin,
cikin kunan rai chummy ta ciro sandar tsafinta ta
fara nuna
su fanne dashi,
zagayen dakin suka farayi har suka kai inda kwalbar gunkin
zeenatu take,
da sauri fanne tasa hannu ta dauki kwalbar,
wani irin ihu oyizah tasa tace karki fasa, karki fasa,
zan taimakeku in maida ku gidan ku, fanna tace
fanne fasa da sauri saboda mu dama a mace muke gurin wa
zata
maida mu,
kafin chummy ta cimma fanne har ta fasa wannan
kwalbar
ta karya gunkin ciki, zama oyizah tayi a gurin tana girgiza kanta tana
fadin
shikenan, shikenan my lord,
sai da nace miki mu gama da yaran nan saboda
nasan zasu
iya zame mana matsala, yanzu nasan duk inda zeenatu
take ta farfado,
chummy bata ba oyizah amsa ba saida ta tabbatar
ta
kwantar da fanne da fanna sannan tace yau dinnan
zan gama dasu, ki kwantar da hankakinki dan sun fasa
kwalbar
a banza dan babu wanda yake tunata bare har yayi
mata
adduar da zaisa ta gama dawowa hayyacinta,,
yanzun nan zan kara yin aikin da yafi wancan akanta,
oyizah ta saki ajiyar zuciya tace nagode my lord..
Afeeyah na zaune tana lazumi, tunda ta idar da
sallar
la'asar bata tashi daga kan daddumar ba sai gurin
biyar, shafa addu'ar tayi ta mike ta nade daddumar
sannan ta
zauna a kasa a gefen gadonta ta tura hannunta
karkashin
gadon ta zaro zanin da ta kunshe damon nan a ciki,
a hankali ta warwareshi ta nade hannunta da leda cikin
dakewar zuciya ta fara kakkabe kasar tana kokarin
bude
bakin damon,
cikin sa'a ta budeshi sai wari yakeyi ta karkatar da
bakin ta girgizah shi, nan wata katuwar laya ta faďo kasa,
da sauri ta ajiye wannan damon ta naďeshi cikin
zanin ta
dauki layar ta warwareta,
babu abinda ta gane a cikin rubutun sai sunan
zeenatu, nade layar tayi ta mike ta fita da wannan damon ta
kulleshi
a leda takai main bolar gidan sannan ta dawo ta
kona layar
ta tattara tokar ta zubata a magudanar ruwa...
★ Magaryah Nijar★ Indo!!! tankaďen ne har yanzu baki gama ba, baki
gudun
malam ya dawo ya tarar ba'a gama abinci ba,
wane irin shashanci ne wannan,
nda tashi ki ban guri sai shegen Nawar tsiya,
indo ta turo baki ta mike tayi hanyar waje, Sallamar da akayi ne ya tsayar da ita,
da sauri ta rungumeta tana faďin "Tanti Gaje"
sannu da
zuwa,
Gaje tayi dariya tace sakan ni yar Magaryah ya na
same ku, indo tace kalau muke sai dai har lau Tanti Ayyu na
nan da
masifarta,
Gaje tayi dariya ta karasa cikin gidan tanti ayyu ta
mike tace
maraba da gaje mutan jigawa, gaje tace ina wuni Ayyu,
ayyu ta amsa tana shimfiďa mata tabarma tace ya
jigawar,
ay tun shekaran jiya muke zuba ido shuru,
Gaje tayi murmushi tace mun yi sabga ne a kazaure
dan haka baki ganni ba,
ya kokari ya kuma mai jikin an samu cigaba
kuwa--- kafin
Ayyu tayi magana wani razananen ihu ya fito daga
ďakin
majinyaciyar ya ziyarci kunnuwansu, kallon kallo suka fara yi sannan suka mike da gudu
suka
shiga dakin har suna bige juna,
zama sukayi a gefenta gaje ta fara shafa kanta tana
faďin
sannu hajiya, wani ihun ta kara saki tana faďin zasu kasheni,
zasu kashe
Affan, Gaje kije ki dauko min shi, gashi can zasu
kashe shi,
wayyo Allah nah zasu kashe min ďana,
cikin sauri Ayyu tace indo maza je ki kirah malam kice mishi
ya taho maza ta farfado...

RABO AJALI
......56 TO 59......
.
BY SULAIMAN BOMBOY.
.
Cikin sarkewar murya malam maina yace dagaske
kike
indo,
jiki na rawa indo tace walllhy kawu da gaske nake,
mikewa yayi ya gyara takalman kafarshi yayi
sallama da abokanshi suka wuce gida,
Yana shiga ya tarar har lokacin zeenatu na ihu
sosai,
da sauri ya karaso ya zauna ya umurci indo da ta
kawo
mishi ruwa, nan da nan ta fita ta kawo mishi ruwa ya jika
wani ganye ya daďe yana tofa addu'a a cikin
ruwan sannan
ya mika ma Ayyu da take rike da ita yace ta ta bata
tasha,
dakyar suka iya ďagata suka bata tana ihu tana zubarwa, a
haka har Allah yasa ya shiga cikinta,
kwantar da ita sukayi suna shafa mata ruwan tayi
wani irin
kakari haďe da amai mai yauki, tana gama aman
suka gyare mata jikinta suka kwantar da ita har lokacin
idonta a
rufe yake, saida suka tabbatar ta samu nutsuwa
sannan
suka tashi suka fita a dakin suna tattauna yadda
zasu billowa al'amarin....
Tun a hanya kan alhj basheer ke sarawa a
zuciyarshi yana
tunanin wani abu da yayi ma rayuwarshi gibi kuma
yakeson
tuno shi, yana isa gida ya wuce ciki yana kallon ko ina na
gidan, a
hankali ya fara bin dakin zeenatu da kallo komai na
rayuwar
da sukayi a baya ya shiga dawo mishi har lokacin
da aka nemeta aka rasa, tambayar zuciyarshi ya shiga yi
akan ko
an ganta, ko ta mutu ne, meyasa kwata2 ta bace a
cikin
kwakwalwarshi,
da sauri ya karasa kofar ďakin ya murďa yaji ta a rufe,
kitchen ya wuce shi kanshi ya rasa me zaiyi a
kitchen din,
yana shiga ya tarar da oyizah tsaye tana tsiyaya
fresh milk
a kofi, wani irin kallo yayi mata wanda shi kanshi baisan
yayi shi
ba,
a hankali yace safiya ina zeenatu? har yanzu ba'a
ganta
ba? ko ta mutu ne,? saboda tsananin ruďewa saida oyizah ta kusa ajalin
glass
cup din hannunta tace alhj wace zeenatun,
alhj basheer yace zeenatu nawa kika sani a
rayuwarki,
cikin in ina tace to ni ina zan san in--- kafin ta karasa
magana wayar alhj basheer ta katseta,
da sauri ya dauka yace ina wuni baffa, daga ďaya
bangaren
ya amsa yace bashiru shin ina labarin zeenatu,
dazun nan tunaninta ya fado min bayan dogon lokaci har
yanzu babu
wani labari game da ita,
alhj basheer cikin damuwa yace tunanin da na
gama yi
kenan baffa, gaba daya na rasa yadda akayi har tunaninta
ya bace min,
Baffa yace na cire rai da ita bashiru, addu'a kawai
zanyi
mata akan Allah ya kai rahama kabarinta,
shekara uku babu amo babu labari, alhj basheer yace baffa baza'a cire rai da ita ba in
har tana
da rai, yanzu addu'a kawai zamuyi akan Allah ya
bayyana
ta in kuma bata raye Allah ya jikanta,
sun dade suna jimamawa a waya sannan suka kashe alhj
basheer ya fita daga gidan da sauri ba tare da ya
kalli
oyizah ba...
Ajiye kofin tayi da sauri ta wuce daki cikin tashin
hankali, kai kawo ta dinga yi idonta yayi jajur tace tabbas
mati ya
hake wannan damon,
cikin sauri ta bazama gurin tsafinsu domin neman
mafita...
Gidan alhj bara'u ya shiga shi kanshi yayi mamakin tsawon
shekarun da suka dauka ba tare da an nemi
zeenatu ba,
Abida harda kukanta dan kamar yadda ake shafe
rubutu a
allo haka aka shafe babin zeenatu cikin kwakwalwar
mutane,,
a ranar saida suka je gurin malamai hudu duk inda
suka je
sai anyi bincike ace tana raye amma bata cikin
hayyaci da nutsuwarta, , addu'a sosai suka baza makarantar
almajirai
da gurin malamai,
alhj basheer bai koma gida ba sai can dare gurin
11..
Afeeyah najin shigowarshi ta dauki hijab dinta dama ta
shirya duk yadda zatayi yau tasa daddy ya barsu su
kwana
a dakin oyizah,
wani macijin roba ta dauko ta turashi karkakashin
kujerar da Affan ke zaune hankalinshi na kan cartoon,
zama tayi kusa dashi tace manya kallon har yanzu
bai isa
ba,
yayi dariya yace yanzu za'a gama yau bana jin bacci
ina zaki naga kinsa hijab,
tace sallah na idar shine ban cire ba,
a hankali ta daura kafarta kan tashi tana mishi
waiwaiyi,
da sauri ya matsar da kafarshi ya kalli gurin dan
ganin abunda ke mishi yawo a kafa,
wani irin tsalle ya daka hade da ihu mai karfi ya
runtse
idonshi yana tsalle yana faďin wayyo daddy maciji,
Afeeyah tayi saurin dauke macijin ta boyeshi taja
hannushi a rude suka fito suna ihu tare,
da gudu daddy da oyizah suka fito suna fadin
lafiya,
Afeeyah tace daddy maciji ne a dakinmu yana can
ya shige
karkashin gado, a ruďe alhj basheer yace maciji,
Affan yace eh daddy har ya hau min kan kafata,
alhj basheer yayi hanyar dakin, Afeeyah tayi saurin
cewa
daddy karka je ya sare ka, ka bari zuwa gobe in
Allah ya kaimu sai a nemo masu wasa da macizai su
dubashi,
Alhj basheer yace hakane kuma amma a bar maciji
ya
kwana a daki, wai ni ta ina ma shigo,
Afeeyah tace nima tunanin da nakeyi kenan, alhj basheer yace yanzu dai bazaku kwana a dakin
ba zo
muje bangaren safiya ku kwana daki daya, oyizah
tayi
saurin cewa alhj dakin da na bawa Affan cike yake
da kaya a ina zasu kwana,
alhj basheer yace ba ga dakinki ba tunda ba a ciki
kike
kwana ba, yau kadai ne fa gobe zasu koma dakin
su,
oyizah ta kumbura fuska tace sam baze yiwu ba alhj, akan
me daki na privacy na in bar wata ta kwana a ciki,
alhj basheer cikin mamaki yace Afeeyan ce wata,
oyizah ta galla ma Afeeyah harara tace ba nufi na
kenan ba
alhj, alhj basheer yace na riga na gama magana suje can su
kwana, Afeeyah ta kalli oyizah tayi murmushi tace
to daddy
ko za'a bude mana can dakin umma sai mu gyara
mu
kwana a ciki, hankalin oyizah ya kara tashi dan tasan in Affan ya
shiga
wannan dakin to komai zai iya faruwa,
da sauri tace kuzo muje ku kwanta a nawa dakin,
Afeeyah tace a'a mummy kar mu takura miki da dai
munje dakin umma,
oyizah tayi mata kallon zaki sani yau cikin dare,
tace muje
babu komai,
ciki suka shige alhj basheer ya wuce side dinshi
oyizah ta kai su Afeeyah nata zuciyarta cike da mugayen
kulle kullen
data gama shiryawa akan Afeeyah...
Suna shiga dakin Afeeyah ta cire hijab dinta ta kalli
Affan
dake tsaye har lokacin a tsorace yake tace zo ka
kwanta
mana,
ya karaso gurin gadon zai hau tayi saurin tare shi tace karka
kwanta kan gadon mummy kaga ita babba ce,
muyi
kwanciyarmu a kasa ko,
ya gyada mata kai yana murmushi ya kwanta a
kasa yana kallo sama,
bayi ta shiga tayi alwala ta kare ma bayin kallo tana
gyada
kai cikin mamaki dan cike yake da magunguna da
sabulan
bleaching, fitowa tayi ta dauki hijab dinta ta kwanto
dankwalin kanta
ta shimfiďa dan bata ga dadduma a dakin ba,
sallah ta hau yi in ta idar ta kara tayar da wata
kabbarar,
tun Affan na kirga sallahr da takeyi har bacci daukeshi bata
idar ba,
☆ 2:30am ☆
Lokacin ta idar da sallolin da takeyi ta fara adduo'i
tana
neman taimakon Allah akan abin da zata aiwatar yanzu,
saida tayi addu'a sosai sannan ta mike ta cire hijab
dinta ta
rufe Affan dashi ta tofe shi da addu'a,
Saida ta tabbatar ta rufe windows din dakin sosai ta
yadda ko kuda bazai iya bi ba bare ido yaga me akeyi a
ciki,
da bismillah ta yaye zanin gadon sannan ta daga
katifar,
dakyar ta iya cire katakon dake kasan gadon
saboda nauyinsu,
a razane ta ja baya saboda hango wani makeken
rami a
karkashin gadon,
hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take fada
saboda ta matukar tsorata da ramin, zuciyarta sai bugawa
takeyi
saboda tuna ita fa xata sa hannunta cikin ramin,
girgiza kanta tayi ta fara ja baya tana fadin wallhy
bazan
iya ba, ji tayi kamar ta daki mutum a bayanta ta juyo a
razane taga
babu kowa sai muryar kaka liman dake mata yawo
cikin
kunnuwanta,
"na rokeki karki tsorata ke kadai ce garkuwar bayin Allahn
nan,
in kika tsorata babu wanda zai iya,
"in kika gansu Ruwanki ne ki barsu ko ki ciresu ki
taimaki
mahaifi da kakar abinda ke cikinki"" A hankali ta karaso gurin ramin idonta cike da
kwalla tasa
hannu ta fara ciro kulle kullen dake ciki,
gumakan dake cikin ramin uku ne, daya an soke
kanshi da
mashi, biyu kuma an haďe su guri daya an kulle, saida ta tabbatar ta fitar da komai daga cikin ramin
sannan
ta maida kayan gadon tana yi tana share zufa,
gaba daya a lokacin ta nemi tsoro ta rasa,
kwashesu tayi
cikin hijab din da ta rufama Affan ta buďe kofar dakin tayi
saurin wucewa dakinta,
kitchen ta wuce cikin dakewar zuciya ta fara
warware duk
wani kullin garin magani tana zubarwa a cikin zinc
tana kwarara mishi ruwa, haka layunma duk tayi musu,
gunkin lakan da aka hade su guri daya ta fara
warwarewa
ta sa tabarya ta dakeshi ya zama gari sannan ta
kwararar
dashi cikin zinc, dauko dayan gunkin tayi wanda akayi shi da roba,
da bismillah ta zare mashin ciki,
tana dauko wuka zata fara yankashi taji wata
guguwa mai
karfi ta bude windown kitchen din,
hannaye taga an ziro ta cikin windown tayi saurin yar da
wukar hannunta ta cilla wannan mashin bayan
cabinet,
a hankali taga gangar jikin mutum na shigowa,
da gudu tayi hanyar waje tana addu'a,
tana zuwa kofar taji an datseta da karfi, ja da baya ta fara yi tana salati tana kiran sunan
hajja,
oyizah ta gani muraran ta bullo ta cikin kofar,
zaro ido tayi murya na rawa tace m-u-mm-y,
oyizah ta buga mata wata sanda a bakinta,
rike bakin tayi tana ta nemo addu'a a bakinta ta rasa,
cikin kunan rai oyizah ta fara matsowa fuskar nan
babu
rahama tace yau sai na kasheki, daga yau kin daina
numfashi a doron kasa bare har kiyi yunkurin
shiga rayuwata,
da hannuna zan kasheki tunda duk wani abu da
nayi akanki
bana samun nasara,
ban taba haduwa da abin da ya dameni ba sai a
kanki dake da matsyacin saurayinki jabeer,
kamar yadda na kawar da jabeer da mahaifiyar
Affan kema
haka zan kawar dake kije can ki samesu dan babu
wanda
ya isa ya shiga gonata ya fita ba tare da yayi noma ba,
tayi wani huci hade da daga wannan sandar zata
buga ma
Afeeyah, da sauri ta goce ta rike sandar sosai,
nan suka fara dambe sosai har oyizah tayi nasarar
kwace sandar,
da karfi ta shiga laftar Afeeyah da ita,
ihu Afeeyah takeyi tana ja da baya saboda azaba,
wani jug ta rarumo a gefenta ta kwaďa ma oyizah
akanta,
nan jini ya fara zuba sosai, da sauri Afeeyah ta bangajeta ta kama kofar
kitchen din
tana jijjigawa tana ihu sosai kamar zata tsaga gidan,
ganin kofar taki buduwa yasata daukar wuka ta
nuna ma
oyizah dake tahowa kusa da ita tace wallhy kina matsowa
zan kashe ki,
oyizah ta goge jinin gefen idonta tayi wata irin
dariya tace
wai gawa ce ke maganar kashe me rai,
cikin kuka Afeeyah ta juya tana faďin ya Allah ka taimakeni,
tana jan kofar taji ta buďu tayi saurin fita ta datso
oyizah a
ciki,
da mamakinta tana bude kofar parlonta ta tarar da
oyizah da wata mata mai gebararran halitta,
runtse idonta tayi ta fara fadin hasbunallahu wa
ni'imal
wakil, la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal
zalumin,
wukar nan dake hannunta ta ďaga da niyyar buga ma
oyizah, nan tayi saurin dukawa ta kamo kafar
Afeeyah ta
daga ta sama tayi wurgi da ita ta bugu da bango da
tiles din
dakin, kara mai karfi ta saki wacce ba alhj basheer kaďai
ba har
masu gadin gidan saida suka girgiza da jinta,
tun daga wannan karar Afeeyah bata kara sanin
inda kanta
yake ba, jin Alhj basheer ya bude kofar dakinshi yasa
chummy ta
bace,,
da sauri oyizah ta yar da sandar hannunta ta
tsuguna tana
ihu a gaban Afeeyah, da gudu Alhj basheer da farida suka karaso gurin,
cikin
rudewa alhj basheer ya shiga jijjiga ta yana kiran
sunanta,
kallon oyizah yayi tana kuka sosai yace safiya me
ya sameta, cikin makirci oyizah tace nima fitowa nayi
na tarar
da ita anan tana dambe da iska, ina matsowa kusa
da ita
sai naji saukar wannan wukar a goshina,
anya alhj yarinyar nan ba matsafiya bace kuwa,? alhj basheer ya daka mata tsawa yace kamata mu
kaita
asibiti muji abin da ke damunta,
oyizah ta share hawayen karya ta kamata a
zuciyarta tana
murna dan suna zuwa asibiti zata karasa ta acan, Alhj basheer na tada mota yaji kamar muryar Affan
a gefen
glass din motar, kallonshi yayi yace Affan ka tashi
ne,
Affan ya gyaďa kanshi idonshi jajur yace daddy ina
zaku kaita,
alhj basheer yace asibiti zamu kaita yanzu zamu
dawo je ka
kwanta kaji,
bude motar yayi ya zauna a inda aka kwantar da ita
yace muje daddy,
alhj basheer yace kayi hakuri Affan ka je ka kwanta
kafin
mu dawo, Affan kamar zaiyi kuka yace daddy
bazan iya
bacci ba, oyizah cikin fushi tace ka sauka akace ko bakaji
abin da aka
ce maka bane,
kallonta yayi cikin ido hawaye na sauka cikin nashi
yace
saidai idan tare da Afeeyah zaku saukemu, oyizah zata kuma magana alhj basheer ya tada
motar yace
muje kyaleshi,
oyizah tayi kwafa dan wannan mayen ya rusa mata
plan
dinta, har suka kai asibitin idon Affan bai bar zubar da
hawaye ba,
janyoshi daddy yayi yana rarrashinshi akan ya
daina kuka
babu abinda zai sameta,
sun dan dade a tsaye kafin doctor yazo, direct ya wuce
dakin da aka kaita,
ya dade yana treatn dinta yiyi dressn ciwukan dake
jikinta,,
oyizah ma ta je wata nurse tayi mata dressn sannan
ta wuce dakin da Afeeyah take,
zaune ta samu Affan ya kwantar da kanshi akan
hannun
Afeeyah yana kuka alhj basheer na tsaye a kansu
yana
rarrashinshi, tsaki tayi a hankali ta karaso gurin tace alhj ya
kamata kuje
gida ni sai in kwana anan,
Affan yayi saurin dago kanshi ya noke wuyanshi
yace um
um nima zan kwana, oyizah tayi dariya tace ya za'ayi mai jinya yayi jinya,
kai da
ba wani isashshen lafiya gareka ba ina kai ina jinya,
Affan ya kara fashewa da kuka yace ni babu inda
zani,
alhj basheer yace to duk babu inda zamu a nan zamu
kwana, oyizah ta ja baya cikin bacin rai ta watsa ma
Affan
harara a zuciyarta tace shege mayatacce ka kusa
daina
ganinta kwata2....A tsaye suka kwana a kanta babu wanda ya
runtsa,
oyizah taki runtsawa ne saboda tana jiran su alhj
basheer
su rufe idonsu ta ida mugun nufinta akan Afeeyah,
alhj basheer kuwa yaki runtsawa ne saboda ganin Affan bai
runtsa ba kuka kawai yakeyi wanda babu wanda a
cikin su
yasan dalilin yinshi har ni da nake dauko muku
rahoto,
karfe 6 doctor ya iso, dakin Afeeyah ya shiga suka gaisa da
alhj basheer yace bata farfado ba har yanxu,
alhj basheer yace ko motsi bata yi ba doctor da
fatan dai ba
wata gagarumar matsala bace,
doctor musah ya bude idonta a hankali yace buguwa ce
kawai tayi sai wadannan ciwukan,
ya akayi ta samu wadannan raunin haka alhj,
alhj basheer cikin damuwa yace ina ganin gamo
tayi cikin
dare dan ni ihunta kawai naji na fito na sameta a sume ina
fatan dai bai taba lafiyar cikinta ba ko doctor,
doctor musah yace dakyar ne alhj dan buguwar a
kai tayi
amma anjima zanyi scanning dan tabbatar da
lafiyar shi, alhj basheer yace Allah yasa muji alkhairi, doctor
musa
yace Ameen alhj sannan ya fita,
oyizah tace alhj ya kamata ku tafi gida kuje kuyi
wanka sai
ku kawo mana abin kari ko, alhj basheer ya dafa kan Affan yace tashi muje gida
ka dan
yi bacci ka huta anjima sai mu dawo,
Affan ya ďago idonshi da ya kumbura ya girgiza
kanshi
yace kaje daddy, alhj basheer yace haba Affan baka ganin yadda
idonka yayi
nasan ka gaji kuma bacci kakeji, kayi hakuri kazo
muje kaji,
Affan ya mike yana murza idonshi ya fita ba tare da
ya kalle su ba,
saida alhj ya dan dade a ciki sannan ya fito ya samu
Affan
a mota ya daura kanshi kan murfin kofar,
shiga yayi ya tada motar suka wuce...
Suna fita oyizah rufo kofar ta dawo gurin Afeeyah tana
dariyar murna,
pillown kan Afeeyah ta cire tana fadin yau taki ta
kare,
yau zan karar da duk wata matsalata in huta da
bakin ciki, tana daura pillown kan Afeeyah taji an murďa
kofar,
da sauri ta zauna ta zame pillown tana dariya tace
doctor
ka dawo,
doctor musah ya kalleta sosai yace eh na dawo, nazo daukarta muje ayi mata scanning daga nan
zata wuce
resting room,
zaifi kyau ki tafi gida hajiya saboda bama yarda
kowa ya
shiga dakin hutu in ba likita ko nurse ba, oyizah tayi mishi wani irin kallo tace kana nufin ita
kadai
xamu bari a asibitin babu wanda zaiyi jinyarta sai
kace
marar gata,
doctor musah yace haka ka'idar take hajiya baki ga conditn
din da take ciki ba, oyizah ta fara masifah tace
wallhy baka
isa ba, babu inda zaka kaita haka kawai zaka wani
zo kayi
min iyayi anan, to anan zaka barta tunda ko ina ka kaita Allah ne
zai bata
lafiya ba kai ba,
yayi mata wani irin kallo sannan yasa aka shigo da
wani
gado yace hajiya aiki na nakeyi tunda ba ke kike biyana ba
dan Allah ki barni inyi aiki na,
ya kalli nurses din yace ku daura ta muje, suka
kinkimeta
suka daurata akan gadon,
rike gadon oyizah tayi tana ta bala'i tana wallhy baza'a tafi
da ita ko ina ba,
mutane suka taru a gurin anata bata hakuri amma
tace ita
sam babu inda za'a tafi da ita,
doctor musah da kanshi ya amshi gadon yasa iya karfinshi
ya fara turawa oyizah na binsu tana bala'i kamar
zararriya,
dr musa bai tsaya a ko ina ba sai office dinshi, da
karfi ya
bude kofar ya tura gadon haďe da bangajeta ta fadi kasa
yayi saurin shigewa ya datso kofar,,
wani sabon bala'i oyizah ta dasa ta dinga masifa
cikin daga
murya,
babu wanda ya kalleta a asibitin kowa harkar gabanshi
yakeyi saboda su a ganinsu mahaukaciya ce in ba
mahaukaci ba waye zaiyi wannan daga cewa za'a
kai
patient resting room,
ita kuwa oyizah musabbabin tashin hankalinta shine yanzu
Afeeyah tasan ita wacece in har tabar Afeeyah ta
kara
kwana a doron kasa to tabbas asirinta zai tonu dan
zata iya
farkawa a ko da yaushe, (oyizah bata san ba tun yau Afeeyah tasan ko
wacece ita
ba, kuma bata san bayan Afeeyah akwai mutanen
da suka
san ko wacece ita kuma suna nan tunkarota cikin
kankanin lokaci )
sai da ta gaji da masifar dan kanta sannan ta wuce
gida
cikin kunan rai...
Tana isa gida ta faďa ma alhj karya da gaskiya akan
abun da doctor musah yayi mata,
alhj basheer yace safiya mutumin nan fa aikin shi
ne ya fiki
sanin abinda ya dace, oyizah tace babu abinda ya
sani alhj
kawai mu canza mata asibiti, alhj basheer ya girgiza kanshi yace babu inda zan
kaita a
can zata zauna har Allah ya bata lafiya,
in ma yace kar wanda ya kara zuwa gurinta to na
yarda dan
nasan zai kula da ita sosai, oyizah ta tsaya tana kallon alhj
basheer tana huci kamar bakar zakanya,
mikewa yayi ya fita daga gidan gaba ďaya ya barta
tsaye
kamar zata kurma ihu..Kwanan Afeeyah uku a asibiti bata farfaďo ba, a
cewar
doctors buguwa tayi sosai kuma suna iyakacin
kokarinsu
gurin ganin ta farfaďo nan da yan kwanaki,
babu wanda ke zuwa dubata daga gida sai alhj basheer da
Affan da har wannan ranar bai bar zubar da
hawaye ba,
ba karamin damuwa alhj basheer yakeyi ba akan
yawan
kukan Affan, gani yakeyi kamar yin kukan yanada nasaba da
ciwonshi,
saida doctor musah ya kwantar mishi da hankali
yace babu
abinda ke damunshi may be ciwon matarshi ne ke
sashi yawan kuka,
alhj yayi dariya da dr musa ya fada mishi haka, yace
yanzu
wannan da kwakwalwrshi bata da amfani har yake
iya yin
kuka dan wani nashi baida lafiya, kenan yasan zafin ciwo
kuma yasan meye damuwa,,
doctor musah yace me zai hanashi yin kuka, alhj ni
fa har
yanzu kana bani mamaki akan wasu abubuwa da
ka kasa fahimt-- wani irin kallo Affan yayi ma doctor musah
nan da
nan yayi saurin canza magana yace kamar ciwon
Affan ka
kasa fahimtar kullum yana samun cigaba dan wani
lokacin yakanyi abubuwa irin na masu hankali,
alhj basheer yayi murmushi yace hakane doctor,
Allah dai
ya kara bashi lafiya,
dr musah yace ameen alhj, mikewa alhj basheer
yayi yace to mu zamu wuce dan inada inda zani,
dr musah yace to sai anjima alhj, nan suka fita dr
musah ya
bi Affan da kallon mamaki...
Affan ne zaune a kan kujera a palour ya haďa kai
da gwiwa yana kuka sosai harda sheshsheka,
mamakin al'amarin nayi a zuciyata nace shi kuwa
wannan
tababben ko kukan me yake yawan yi tun ranar da
aka kai
Afeeyah asibiti oho,, a hankali naji yana faďin sai na dauki fansar
kisarku, bazan
kyale duk wanda yakeda hannu a cikin kisan ku
ba, wannan
yakin ni zan karasa shi cikin kankanin lokaci in
shaa Allahu, sosai yake kuka yana faďin wadannan kalaman,
cikin kidima na kureshi da ido a zuciyata nace anya
wannan
bai samu sauki ba,
anya ba basaja yakeyi ba kuwa?,
Da sauri na maida computer cikin kwakwalwrta baya zuwa
ranar da Afeeyah ta aiwatar da ayukanta na karshe
wanda
yayi sanadiyyar zuwanta asibiti,
da sauri na ciro yar makallaliyar camerar da ke
makale a dakin oyizah na kunna,
cikin mamaki na fara dauko muku rahoton abin da
ke ciki,
da naso in

Please Login or Register in order to submit comment