Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude zata sa akwatinta taga
kaya
masu tarin yawa wadanda ba dinkakku ba harda
na bacci,
cire hijab dinta tayi ta shiga bayin dake ďakin tayi
wanka ta
fito tana tsane kanta da towel,
tsawar da aka saki tayi daidai da bude kofar ďakin,
da sauri ta waigo tana kallonshi yana kokawa da
mukullin
kofar alamun yana saurin rufeta dan kar wani ya
ganshi
......
Rabo Ajali 40 to 41
.
By sulaiman Bomboy
.
Rabo Ajali 40, 41Kallonshi Afeeyah ta tsaya yi har ya rufe kofar ya
waigo
yana mata murmushi,
kau da kanta tayi ta janyo hijab dinta tasa ta zauna a
gefen
gado, karasowa yayi yana kaďa kanshi yana dariya ya
tsuguna a gabanta ya daura hannunshi kan nata
yace
barbie yau kin dawo gidan mu ko,,
ta juyar da kanta gefe, ya taso ya zauna kusa da ita
yayi narai2 da ido yace abokina ya faďa min kullum kina
kuka
da daddare meyasa kike kuka?
Afeeyah da idonta ya ciko da kwalla ta kasa ce mishi
komai
sai kallonshi da takeyi, hannu yasa ya share hawayen da ya
digo a idonta yace ki mayar da hawayen nan dan
Allah
karkiyi kuka abokina zaice ni nasaki kuka in yazo,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka a zuciyarta tana
mai tausayawa ranar da Affan zai san jabeer ya bar
duniya,
kukan shima ya fara yi kamar karamin yaro yana
share
mata hawaye,
wata tsawar aka sake saki mai firgitarwa kamar zata rusa
gidan saboda kararta,
da sauri Affan ya shige jikinta ya kankameta haďe da
runtse
idonshi,
wani abu mai wuyar faďuwa yaji ya tsarga mishi a cikin
kwakwalwarshi,
wani irin shauki ya dinga ji a can cikin jikinshi,
shi kanshi ya kasa fassara yanayin daya shiga a
wannan
lokacin, Turashi Afeeyah ta farayi tana kokarin mikewa tasa
kaya,
kara kankameta yayi dan bayason ya daina jin
abinda
yakeji,
kallon fuskarshi tayi a hankali taga idonshi a lumshe yana
fitar da wani irin numfashi, tausayi ya bata sosai
saboda
yadda ya koma cikakken mutum a haka kafin anjima
ya
birkice ya koma tababbe, a hankali ya bude idonshi da ya fara canza kala ya
saukesu
kan nata,
da sauri ta kauda kanta tace dan Allah ka sakeni in
sa kaya
bacci nakeji, sakinta yayi cikin muryar lafiyayyan mutum yace
"muje in
tayaki sawa" cikin mamaki ta zaro manyan
idanuwanta tana
kallonshi,
murmushi yayi mata ya mike tsaye ya bude drawer ya
dauko mata cotton night gown ya mika mata,
kasa amsa tayi tana mishi kallon mamaki, ajiye rigar
yayi a
jikinta ya hura iska cikin idonta yace ko ni zan sa
miki da kaina,
tayi saurin kauda kanta ta ďauki rigar ta faďa bayi
tana
tunanin canzawarshi lokaci Guda,
tsaye ta sameshi gaban mudubi yana zana kanshi
yana dariya,
ta mudubin ya hangota ya juyo da sauri ya janyota
yace zo
kigani na iya drawing mutum a mudubi, tsaya anan
kigani,
Afeeyah ta girgiza kanta tace bacci nakeji, ya girgiza kai a shagwabe yace ni sai kin tsaya,
Afeeyah ta haďe rai ta juya ta wuce kan gado ta
kwanta,
zama yayi a kujerar dressing mirror yana kumbure2
yana
kunkuni shi a dole an mishi laifi, Ko kallonshi batayi ba tayi kwanciyarta ta shige
bargo tana
karanto adduoi,
muryarshi taji saitin kunnenta yana faďin
Niko?
Niko? Ya faďi haka yafi sau goma Afeeyah tayi tsaki ta yaye
bargon zata fara masifa hawayen da ta gani kwance
a
kuncinshi ya hanata, ta kalleshi murya a tausashe
tace me
nayi maka kake kuka, ya kwanta kan cinyarta yace bake bace kika ki
tsayawa inyi
drawing dinki ba kuma kika tafi kika barni baki bani
hakuri
ba,
sai na fadama abokina ince barbien shi ta daina kirki yanzu,
Afeeyah tasa hannu ta share mishi hawaye tace kayi
hakuri
gobe zan tsaya yanzu bacci nakeji,
Affan ya ďago kanshi ya kalleta cikin ido yace ni
bana jin bacci zaki rarrasheni inyi bacci,
Afeeyah ta dafe kanta kwalla ta cika idonta a
zuciyarta tace
ni kuma kaddara ta kenan, kwanciya tayi ba tare da
ta bashi
amsa ba tana hawaye tana hango da yanzu fa tana gidan
masoyinta abin kaunarta jabeer,
hawa gadon Affan yayi ya kwantar da kanshi a
bayanta,
nan ta fashe da wani irin kukan da yasashi saurin
kankameta yana rarrashinta, runtse idonshi yayi yana sake jin abin da yaji dazu,
a hankali kwakwalwarshi ta fara daukar caji ya shiga
shinshina jikinta yana lumlumshe ido,
kara matseta yayi lokacin da hannunshi ya sauka
kan
kirjinta a take ya saki ajiyar zuciya yana wani irin nishi,
cire hannunshi ta fara kokarin yi ta kasa saboda irin
rikon
da yayi mata, yafi minti biyar a haka yana sauke
ajiyar
zuciya yana sauraron kukanta da yake jinshi kamar waka a
wannan lokacin,
mirginowa yayi ya ďago fuskarta idonta a rufe ya
fara share
mata hawaye haďe da bata hakuri,
bata bude idonta ba kuma bata tsayar da hawayen ba,
kwantowa yayi ya haďa fuskarshi da tata yana
gogawa a
hankali,
cikin kuka ta bude baki zata fara masifah yayi saurin
tura bakinshi cikin nata,
duk yadda taso fitar da bakinshi ta kasa saboda sam
ya
hanata damar hakan,
wani irin rikitaccan alamari ta dinga gani a tare da
wanda tasan bashi da isashshen lafiyar kwakwalwa,
Shi kuwa Affan sam baya cikin hayyacinshi bare ya
tantace
a tsakanin duniyar mahaukata ko a ta lafiyayyu
yake,
babu inda baya rawa a jikinshi, gani yakeyi kamar duk cikin
wasa yakeyin abinda yakeyi sam ya kasa tsayawa da
wannan wasan saboda ba kananan abubuwa yakeji
na
shauki a cikin jinin jikinshi ba,
a wannan lokacin duk iya kokarin turashi hade da kukan da
Afeeyah takeyi bai sa ya daina ba saima shiga yin
wasu
abubuwa na daban da yayi dan a yadda yakejin
kanshi in
har ya daina wasannan da yakeyi to tabbas zai iya rasa
ranshi,
wani irin kuka Afeeyah takeyi na takaici da bakar
azaba
tana kiran sunan jabeer dan abubuwan da Affan
yake mata sun zarce tunaninta,
"Ni kaina danake dauko rahoto saida na tsorata nayi
fitar
da babu shiri harda buge kafa saboda sauri dan
Affan ya
matukar tsoratani yadda ya dinga sarrafa Afeeyah kamar
cikakken mai hankali"
A bakin kofar na tsaya ina jiyo muku kukan Afeeyah
wanda
takeyinshi kamar ana yankata, sai karar ruwan sama
da ake tsugashi kamar da bakin kwarya,,
barin kofar ďakin nayi na juya gurin da nake jiyo
magana
kasa2,
a hankali na karasa side din mummy wacce ta fito
daga dakin alhj basheer,
tsaye na same ta a bakin kofar dakin da ta bawa
Affan
tana magana ita kadai tana fadin ina yaron nan ya
shiga,
kardai yaron nan gurin yarinyar nan ya tafi, cikin bacin rai
tayi kwafa ta kama hanyar side din Affan......Muryar alhj basheer taji da karfi yana faďin ina tea
din yake
ne safiya,
sai a sannan ta tuno da abinda ya fito da ita daga
dakin har
taga kofar Affan a bude, hanyar kitchen ta nufa cikin gaggawa ta hado mishi
tea ta
koma dakin ta mika mishi, ya dafe kanshi yace ina
maganin,
da sauri tace ba kai ka ajiyeshi ba,
yayi tsaki yace na manta inda na ajiyeshi duba min ko cikin
drawer ko kan mudubi, cikin bacin rai oyizah ta fara
duba
maganin da kyar ta ganoshi a drawer gefen
gadonshi ta
mika mishi da sauri, ya kalleta yace yau ko ballo min maganin baza'ayi ba,
ta amsa ta babbalo mishi ta mika mishi tayi hanyar
kofa,
Alhj basheer yace wai ina zaki je ne kiketa sauri
haka,
juyowa tayi tace umm na manta ban bawa Affan maganinshi ba, yayi murmushi yace karki damu
dazu da
kuna gurin Amarya na shiga na bashi,
oyizah tace ka tabbatar dai2 ka bashi,
alhj basheer yace kwarai kuwa dawo kiyi min tausa,
oyizah ta dawo ranta a bace ta fara mishi tausa tana tunanin abinda ya kai Affan dakin da aka kai
amarya,
wasu irin tunani ta dinga yi dan tasan illar
kebantuwar mace
da namiji a guri,
wani irin ihu tayi ta diro a gado tana fadin alhj na daura
ruwan zafin tea a gas na manta ban kashe ba,
sakkowa
yayi jiki na rawa yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
bari inje in duba, tace koma ka kwanta alhj ka riga
kasha magani, hanyar kofa yayi yace wani irin magani ay
gara inje
in duba kar kije wani abun ya sameki,
dafe kanta tayi lokacin daya fita tana sake tunanin
hanyar
da zata bi, waya ta dauko da sauri ta shiga kiran salma, numbr
busy
aka dinga sa mata tayi tsaki ta kira farida taji a kashe,
wurgi tayi da wayar tace wadannan tambadaddun
kuma
wayarsu taki shiga, yanzu ni ya zanyi, muryar alhj basheer taji akanta
yace
safiya kin tsoratani wallhy, gas a kashe yake,
ta dafe kanta tace lallai tsufa ya fara zuwa min sai
naga
kamar ban kashe ba, yayi murmushi ya zauna haďe da
rungumeta yace baki ma kunna ba a flask kika dibi
ruwan,
tace hakane shaff na manta ne wallhy,
nan alhj basheer ya shiga faranta ranshi a jikin
oyizah sakin jikinta tayi suka faranta ran juna duk da bataso
hakan ba...
Asubar fari oyizah ta farka a gigice sakamakon
mafarkin
da tayi,
ko wanka batayi ba ta fita tayi dakin Affan, buga kofar takeyi kamar zata ballata tana kiran
sunanshi,
cikin bacci Afeeyah taji bugun kofar ta mike a
hankali ta
fara ture Affan da ya cikwikwiyeta hawaye kwance a
gefen idonshi, kara matse jikinshi yayi da nata yana
sheshekar
kuka haďe da ajiyar zuciya, ba karamin tausayi ya
bata ba
duk da itama abar tausayin ce saboda irin azabar da
tasha, bugun da mummy kema kofar ya karu muryarta ta
cika
cikin gidan tana masifa tana fadin in Affan bazai
bude ba
dan uwarki da ubanki ke bazaki bude ba,
Afeeyah ta fara kokarin yi mishi dabara ta cire hannunshi ta
dan turashi tasa pillow a gurin ta daura hannun kan
pillown
taja bargo ta rufa mishi,
hijab dinta taja tana tafiya dakyar ta karasa kofar
dakin da oyizah ke jijjigawa kamar zata ballata,
murda kofar tayi taja ta tsaya,
da karfi oyizah ta hankado kofar har saida ta sameta,
kallon Afeeyah ta tsaya yi daga sama har kasa tana
hararrta, ta janyo hijab dinta da karfi tayi wurgi dashi
tabi duk jikinta da kallo,
cikin fushi tace a ina kika kwana,
Afeeyah baki na rawa tace a-a-a- -- sambatun Affan
ya
katseta yana kiran sunanta yana fadin wasu
kalmomi na shauki haďe da matse pillow a jikinshi,
oyizah tayi saurin kallon inda yake ta karasa ta cire
bargon
da Afeeyah ta rufa mishi,
wani irin ihu ta saki hade da mayar da bargon tace
na shiga uku, me kikayi mishi naga babu kaya a jikinshi,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na tsere
cikin
idonta,
oyizah cikin hassala ta shakota tace yau sai kin fada
min abinda kikayi mishi, yaudarar mahaukacin nan
kikayi kika
mishi fyade ko me,
Afeeyah ta kara sautin kukanta tace wallhi babu
abinda na
mishi, oyizah ta tsinka mata mari tace karya kikeyi dan
uwarki,
ga shi nan babu wando a jikinshi kema kuma kalli
yadda
kike kin kasa tsayuwa da kyau,
Afeeyah ta kasa magana sai kuka kawai takeyi, nan mummy ta cigaba da magana cikin ficewar
hayyaci
tana dukan Afeeyah,
ihun Afeeyah ne ya tada Affan daga bacci ya mike da
sauri
ganin oyizah tana dukanta, baibi takan daukar wando ba ya
diro daga kan gadon yasa duk iya karfinshi ya turata
ta faďi
kasa ya dago Afeeyah yace yi hakuri barbie me
kikayi mata,
Ta runste idonta da sauri ta dakko wando ta mika mishi ya
karba ya fara sawa,
oyizah na huci ta mike ta karaso gurinshi ta
daukeshi da
mari har sau biyu tace dan ubanka ni zaka ture
saboda wannan kodadiyyar matar, Affan ya rike kuncinshi
ya
kumburo baki yana hawaye yace mummy ni kika
mara,
tace zan maka abinda yafi mari indai har kace zaka
fara bijire min,
ta kalli Afeeyah tace Affan bai taba min musu ba, bai
taba
bata min rai ba kullum yana kaffa2 dani amma gashi
daga
zuwanki Affan har tureni yayi na fađi kasa, yau sai na miki dukan tashin hankali inga uban da
ya tsaya
miki,
da sauri Affan ya shiga tsakiya yana kuka yace
mummy ni
ki dukeni dan Allah ki kyaleta jiya fa naji mata ciwo, wayyyyyo oyizah ta faďi ta hankaďashi gefe tayi kan
Afeeyah dake ja da baya da kyar,
tana cimmata ta daga hannu zata fara dukanta alhj
basheer
ya shigo da sauri yace lafiya me yake faruwa anan,
Da gudu Affan yayi gurin daddy yana kuka yace mummy ce
zata duki barbie na daddy dan Allah ka hana ta bata
da
lafiya jiya muna wasa naji mata ciwo a---- alhj
basheer yayi
saurin toshe bakinshi yace ya isa haka, oyizah ta kirkiri dariya ta sauke hannunta kan
Afeeyah tana
shafawa tace wa yace maka dukanta zanyi,
alhj yarinyar nan taji ciwo sosai shine nake son in
kaita bayi
in mata wanka shine fa take kuka shi kuma ya dauka
dukanta nakeyi, alhj basheer cikin mamaki yace
sannu
Afeeyah,
tashi kije bayi dan Allah kiyi hakuri kinga yanayinshi
komai baya yinshi a hankali,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka tace dan Allah ka
kaini
gurin hajja,
alhj basheer yace kiyi hakuri zan je in kira miki ita in
gari ya waye kinji,
yanzu tashi kije mummynku ta miki wanka,
Afeeyah tayi saurin girgiza kanta tace wallhy zan iya,
alhj basheer yace to safiya zo muje ki hado mata
abinci,
ya tura keyar Affan dake kallon Afeeyah shima yana kukan..
Toilet Afeeyah ta shige da sauri tasa key ta sirka
ruwan zafi
ta shiga ta zauna tana kuka sosai tana kiran hajja da
jabeer,
saida tafi minti talatin a bayi sannan ta fito a zuciyarta tana
tunanin to yanzu waye zaisa Affan yayi wankan
tsarki,
Ďaga kafadarta tayi tasa ma dakin key tayi sallah tayi
adduo'i sannan ta hau gado ta kwanta tana tunano
alamuran da suka kasance tsakaninta da tababben mijinta..
Alhj basheer kuwa bayan ya je ya dauko hajja ya
kaita har
dakin Afeeyah da kanshi, ya fito waje yana mamakin
alamarin da ya kasance tsakanin mahaukacin danshi
da matarshi,,
shin dama mahaukaci wanda ke da matsala a
kwakwalwarshi yana iya saduwa da mace ko dai ita
Afeeyar
ce ta sadu dashi,
tambayoyi marasa amsa ya dinga yi wa kanshi sai daga
karshe ya samo mafitar yaje gurin doctr musa ya
tambayeshi yadda abin yake,,
Dariya sosai doctor musah yayi bayan ya gama jin
bayanin
alhj basheer, ya kalleshi sosai yace alhj tambayarka zanyi, bawai
ina
nufin danka na daga cikin wadannan halittun bane
saidai
dan in gamsar da kai ka fita daga kokwanto,
alhj basheer yace ina jinka doctor,, doctor musah yace shin alhj Allahn da ya halicci
dabba da
mutum da me ya bambantasu,
Alhj basheer yace "hankali"
doctor musah yace good, kaga dabba bata da
hankali amma tanada halittar sha'awa a tare da ita,
komin kankantar dabba akwai wannan halittar ta
sha'awa a
tare da ita wanda idan wannan sha'awar ta motsa
dole sai
sun samu mahaďin da zai lafar dashi,, dabba kenan bare dan Adam mai karfin sha'awa,
a jin sha'awa babu babba babu yaro, babu mai
hankali babu
mahaukaci,
kowa nada wannan halittar a jikinshi,
mahaukacin da yafi Affan ma yana iya saduwa da mace
bare shi da haukarshi ta masu lafiya ce,,
ina mamakin yadda har yanzu Affan bai daina
abubuwan
marasa hankali ba saboda brain dinshi is normal
yanzu sai abin da ba'a rasa ba,, saboda haka alhj karka damu
wannan abun da yayi is normall saidai ita yarinyar ya
kamata ta daina mishi gardama ta bashi hadin kai if
not zai
dinga ji mata ciwon da baisan yaji ba tunda baya
cikin hankalinshi,,
Sannan kwakwalwarshi zata dinga charge if yana
feeling
wannan current din, babu mamaki in Allah ya
taimaka ta
dalilin hakan brain dinshi ya zama normal gaba ďaya, Alhj
basheer yayi murmushi yace Allah yasa, doctor
musah yace
Ameen alhj, da fatan kuna bashi magungunanshi
akan
ka'ida, Alhj basheer yace kwarai kuwa doctor, nan suka
cigaba da hira yayi ta warware mishi abubuwan da
masu
irin ciwon Affan zasu iya yi da wanda bazasu iya ba...

♥♥RABO AJALI♥♥
♡♡♡42 TO 45♡♡♡
. .
By SULAIMAN BOMBOY.
.
A can gida kuwa Afeeyah na kwance kan cinyar
hajja tana
kuka sosai tana fada mata abinda ya faru
tsakaninta da
Affan da su oyizah,
a hankali ta ďago kanta tace hajja ni tsoro Affan
dinnan
yake bani wallhy, sai yayi magana kamar me
hankali kuma
sai ya juye mahaukaci,
sannan hajja mahaukaci ma na iya yin abinda yayi
min,
hajja ta share hawayenta tace zai iya Afeeyah
tunda yanada
duk wata halittar da muke dashi kwakwalwa ce
kadai ta
samu matsala,
Afeeya ta koma ta kwanta tace hajja to ya zaiyi
yayi wanka
yayi sallah,
hajja tace wannan ne kuma bansani ba,
tashi muyi magana kuma ki share wannan
hawayen ki
saurareni sosai,
Afeeyah ta mike zaune tana share hawayenta tace
ina jinki
hajja, hajja ta kalleta sosai tace Afeeyah kuka
yanzu ba
naki bane, daga yadda kika bani labarin abinda
safiya tayi
muku ke da Affan na ďago wasu abubuwan da ke
yarinta ya
hanaki dagowa,
tabbas rayuwar yaron nan na cikin haďarin da
bashi da
mataimaki sai Allah sai kuma ke da Allahn ya
bashi a
matsayin garkuwa,
"Hajara"
yau na kiraki da ainihin sunanki saboda inason in
karfafa
miki gwiwa dan naga kin shagwaba kanki da
sunan da
jabeer ya shagwaba ki dashi, dole ki jajirce kiyi
amfani da
damar
da Allah ya baki gurin kwatowa wannan yaran
yancinshi,
dole kisa shi a hanya ki dinga nuna mishi hanyoyin
bi masu
kyau da marasa kyau,
dole ko yaya ne ki fara koyawa kanki sonshi dan
sonshi
bashi zaisa ki manta da jabeer ba,
dole duk inda yasa kafarshi kema kisata saboda
kuyi
shakuwar da duk abinda kika ce mishi yayi zaiyi ba
musu,
sannan Addu'a, dole ki jajirce ki yawaita addu'a
domin itace
makaminki a yanzu, dole kuma kiyi hakuri da duk
abinda
za'ayi miki saboda mai hakuri shi keda nasara a
ko da
yaushe,
kina jina ko,
Afeeya ta gyada kanta tace ina jinki hajja,
kafin hajja ta buďe baki ta sake wata magana
sukaji an
tokari kofar dakin da kafa,
da sauri Afeeya ta ďago tana gyara dankwallin
kanta,
hajja ta kalli oyizah dake musu kallon raini tace
ina kwana
safiya,
oyizah ta kirne fuska tace bamu haďu dashi a
hanya ba,
hajja ta kauda kanta, salma ta karaso tace ma
Afeeyah kee,
kinsan karfe nawa yanzu,
Afeeyah tace a'a, salma tace dan ubanki jiya me
mummy
tace miki,
oyizah tace ai ta manta da abinda nace mata
tunda ta
kauda budurcinta a gurin tababbe,
salma tace hmm lallai, naga alama mummy,
ta kalli Afeeya tace wallhy kafin 11 ki tabbatar kin
kammala
komai na gidan nan in ba haka ba na rantse da
Allah sai
jikinki yayi tsami,
oyizah tace ay ni bani da bakin magana ki ji da ita
dan in
har nace zan sauke fushi na akanta to wallhy
dakyar zan
barta da rai,
salma tace ay dama mummy bai kamata ki dinga
kulata ba
mun isheta dan tasan babu sa'anta a gidannan, ko
shi garan
mijin nata bai isa ya hanamu yin komai akanta ba,
Afeeyah ta mike dakyar tace ma hajja tana zuwa,
hajja tace muje in tayaki,
Afeeyah tace haba hajja zauna yanzu zan gama,
hajja ta maida kwallar idonta tace to Afeeya,
hijab ta ďauka tabi ta gefensu ta wuce ta barsu
tsaye
sunata habaici suna zaginta,
kitchen ta shiga ta tarar dashi kaca2, nan ta shiga
gyarashi
ta haďe kayan wanke2 tayi ta gyara ko'ina tayi
mopping,
tana gamawa taji muryar farida a bayanta, da sauri
ta
waiga ta kalleta tace na'am me kikace,
farida ta harareta tace ance ki daura rice nd stew 4
lunch
akwai komai na amfani ki duba zaki gani sannan ki
haďa
min corslw,,
salma kuma tace ki soya mata plantain ki kawo
mata
yanzu,
Afeeyah ta gyada kanta ta wuce store din da ta
hango
kayan abinci,
saida ta daura white rice sannan ta bare plantain,
ta daura
shi a wuta ta soya,
ba karamin wulakanci sukayi mata ba da ta kai ma
salma
plantain din,
Ko kallansu batayi ba ta juya ta koma kitchen ta
cigaba da
aikinta,
sai sha biyu saura ta gama komai ta gyare ko'ina
sannan ta
wuce parlor da niyyar gyarawa,
Zaune ta sameshi a parlon yana buga game yana
ihu shi
kaďai,
bata kalleshi ba ta fara gyara cikin parlon, buruntu
yaji ya
waigo ya kura mata ido yana dariya,
sam bata lura ya ganta ba tana can tana kakkabe
kujeru,
rungumeta taji yayi ta baya yana faďin yeeeee na
ganta,
Afeeyah tace dan Allah sakeni aiki nakeyi,
ya saketa ya zagayo yana kallonta yace har yanzu
fushi
kikeyi dani,
ta dauki remote ta kaishi mazauninshi ba tare da
ta kalleshi
ba,
binta yayi a baya yace ki yi hakuri ni bansan zaki ji
ciw--
dan son annabi ka kyaleni kaje ka cigaba da game
dinka
haba ta fadi da karfi rai a bace,
hanyar waje yayi kanshi a kasa kamar zaiyi kuka,
Kallo ta bishi dashi har ya fita sannan taja tsaki a
hankali ta
cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali dan har
ta gama
bai dawo ba,
ďaki ta koma tana haki saboda yunwar da takeji ta
samu
hajja a kan dadduma ta idar da sallah,
zubewa tayi a jikinta tana maida numfashi tace
hajja yunwa
nakeji, dan Allah ki samo min wani abu inci a gida,
hajja ta shafa addua tace ke kuwa duk girkin nan
da kikayi
bakici ko kadan ba,
Afeeyah tace umm banason abinda za'a kira uwata
da
ubana a zaga,
hajja tayi murmushi a zuciyarta tace lallai mutuwar
jabeer
ta kashe zuciyar yarinyar nan,
ta kalleta tace kinyi dai2 kici gaba da hakuri wata
rana sai
labari,
bari inje in kawo miki abinci a gida,
Afeeyah tace to hajja bari inyi sallah kafin ki dawo,
Ta windon bayi ta hangoshi zaune yayi tagumi
yana kallon
ramin kifi, da ganinshi kasan baya cikin walwala,
tsaki tayi ta cigaba da alwalarta ta fito tayi sallah,
tunanin maganganun da hajja tayi mata ta dinga yi
sannan
ta tuno da abinda tayi mishi dazun da kuma bacin
ran da ta
karanta a fuskarshi,
mikewa tayi ta naďe daddumar ta fito tana neman
hanyar
da zata sada ta da gurin kiwon kifin,
da kyar ta gano hanyar ta karasa gurin ta zauna,
sam
baisan tazo gurin ba ta waiga gurin da taga
abincinsu ta
ďiba ta watsa musu,
da sauri Affan ya waigo suka haďa ido ya kauda
kanshi ya
juya mata baya, murmushi ta kirkiro tace kayi
hakuri,
dazu banaso ka hanani yin aiki ne shiyasa,
ya noke wuyanshi yace naki yin hakurin,
ta kamo hannunshi a hankali tace Niko?
yayi murmushi haďi da fari da ido kamar yana
kallonta
sannan ya kara haďe rai yace eh ďin,
tace to juyo kaga wani abu,
ya juyo yana turo baki yace meye?
tayi murmushi tace fushin fuskarka zan nuna
maka,
ta nuna bakinshi da hannu tace kaga yadda
bakinka yayi
babba, sannan fuskarka tayi katuwa saboda fushi,
ya kara turo bakin yayi kasa da idonshi yace to
bake bace
kike min ihu,
tace to ai zan daina nace maka,
yayi murmushi kadan yace yaushe zaki daina, tace
yanzun
nan, ya wangale baki ya rungumeta yana dariya
sosai yace
yauwa barbie na, to tashi muje can ki tayani buga
kwallo,
tace a'a yanzu dai inaso insan ko kayi wankan
tsarki,
yace eh nayi wanka sosai jikina yanata kumfa,
yanata kumfa,
yanata kumfa na koma fari sosai,
tayi dariya tace to sallah fa,
nan ya kirne fuska yace ai ni bana sallah, Afeeyah
ta
kwalalo ido waje tace la haulu, baka sallah,
saboda me,?
Kafin yayi magana sukaji muryar oyizah a bayansu
tana
cewa saboda ubanki bai koya mishi ba..... Afeeyah
ta sunkuyar da kanta da sauri kirjinta na
dukan
uku2,
Affan ya kalli oyizah yace mummy dama saboda
babanta
bai koyamin ba shiyasa bana yi,
oyizah ta mika mishi cup din hannunta tace amshi
maganinka kasha rabu da wannan kinibabbiyar,
Affan ya karbi ruwan asirin da ya saba sha kullum
ya fara
sha ya miko ma Afeeyah yace kema zaki sha,
Afeeyah ta
girgiza kanta ta mike zata wuce oyizah ta janyo
hijabinta
tace dawo nan ban gama dake ba, ta kalli Affan
tace tashi
ka kai cup din kitchen sai kaje kayi wasanka, Affan
ya mike
yana yafito Afeeyah da hannu yana cewa zo muje
ki tayani
buga game,
oyizah tace a'a jeka kayi wasanka zata zo ta
sameka,
ya wuce da gudu yana dago ma Afeeyah hannu,
Wani irin kallo oyizah tayi ma Afeeyah sannan tace
jiya me
nace miki game da Affan,,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa tace dan Allah
kiyi
hakuri,
oyizah taja kunnenta da karfi tace hakurin uban
me kike
bani, bance miki kar ki shishshige ma Affan ba?
bance miki
karki shiga rayuwarshi ba, ohhh wato kema zaki
fara
tursasashi akan sallah kamar yadda ďan iskan
saurayinki
yayi ko?
Afeeyah ta runtse idonta zuciyarta na zafi saboda
kiran
jabeer dan iska da oyizah tayi,
Rankwashi mai karfi ta sakar mata akai tace zan
miki
kashedin karshe,
kashedin da idan kika ďauka kin tseratar da kanki
daga
fushi na,
anyi na farko anyi na karshe tsakaninki da Affan,
kin
fahimci abinda nake nufi ko sai na warware miki?
, Afeeyah tayi shuru kirjinta na tsananta bugawa,
oyizah tace to ina nufin kwana ďaki daya ke da
shi, anyi ta
yanke ta gille tsakaninku,
wallhy kinji na rantse duk ranar da kika kara yarda
Affan ya
shigo dakinki har kika barshi ya kwana, hmmm
faďin
hukuncin da zan miki ma bata baki ne kina jina
ko?
Afeeyah ta gyaďa kanta tace eh inaji, oyizah ta
saki hijab
dinta ta kara kai mata duka a kai tace bace min a
gaba ko in
illata ki, da sauri Afeeyah ta wuce daki tana
kuka******
Bayan hajja ta gama rarrashinta ta zuba mata
abinci ta
karba ta fara turawa da sauri saboda azabar
yunwar da
takeji,
cikin tausayawa hajja ta fara bata baki cikin hikima
da
kalamai masu taushi,
sai da ta tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan
ta tashi
tafi gida cike da tausayin yar jikarta da ta fara
dandana
rayuwar duniya, dan da sam Afeeyah bata san
bacin rai ba
kullum cikin farin ciki take in ka ganta tana kuka to
na
shagwaba ne, babu wanda zai taka ta ta barshi
bare har ya
daura mata bacin rai duk wanda yayi mata take
zata mayar
mishi ta wuce hankalinta kwance..
Haka rayuwar Afeeyah ta kasance cikin kunci da
bauta,
wulakanci kala2 babu wanda bata gani,
sam bata bari Affan ya ganta ko yazo yana
bubbuga kofarta
bata budewa,
ba karamin tausayi yake bata ba in ya fara buga
kofar dan
baya bugun hankali yana bugata yana ihu wani
lokacin ma
harda kukanshi,
abinci kuwa saidai hajja ta kawo mata dan bata
nasu,
duk wannan wainar da ake toyawa alhj basheer bai
sani ba
saboda baya gari,
A ranar da ta cika sati uku a gidan tana tsaye tana
mopping
dining room,
oyizah da suwaiba suna zaune cikin parlon suna
gulmarta,
suwaiba tace lallai yarinyar nan ashe duk iskancin
da take
mana guri ta samu,
ji yadda take muku bauta kuma duk zagin da kuke
mata ta
kasa tabuka komai,
oyizah tayi dariya tace ay wargi ma guri ya samu,
ni yaushe kamar wannan yarinyar zata tsaya min a
gaba, ai
wallhi kema suwaiba harda laifinki,
suwaiba tace ai da dinma daurin gindi ta samu to
yanzu mai
shagwabatan ya mutu shiyasa shegen bakinta ya
mutu,
oyizah tace ai ko shugaban kasa ne ya tsaya mata
bata isa
ta min ba bare wannan tsinannan yaron mai
shegen girman
kan tsiya..
Afeeyah ta yar da mop din hannunta ta runtse
idonta
zuciyarta na tafarfasa,
muryar salma taji a bayanta cikin isa da gadara
tace
kee..
je kiyi min pepper soup mai yaji sosai yanzu nan ki
kawo
min,
Afeeyah bata juyo ta kalleta ba ta tsalleke ruwan
da take
mopping dashi ta kama hanyar side dinta,
da sauri salma ta bita tana huci taja rigarta ta
baya har
saida wuyan ya yage tace ke dan uban--- Afeeyah
ta juyo
cikin azama ta dauketa da gigitaccen marin da ya
hanata
karasawa yasata sakin Afeeyah bata shirya ba.... A
firgice oyizah da suwaiba suka yo kan salma
dake rike da
kunci idonta yayi jajur,
fuskarta oyizah ta ďago tana shafawa ta kalli
Afeeyah
murya a sarke tace m-ari,
suwaibah ta jinjina kai a munafurce tace tabdijam,
lallai
yarinyar da tsaurin ido kike, ki kalli girman salma ki
dauketa
da irin wannan marin,
Afeeyah taja tsaki ta juya zata wuce oyizah ta saki
salma ta
janyota da karfi tana huci,
ihun da Afeeyah ta saki yayi daidai da shigowar
alhj
basheer parlon,
da sauri ya karaso yace subhanallahi lafiya safiya,
me tayi
miki,
oyizah ta saki Afeeyah da sauri ta juyo ta fara
hawaye tace
alhj ace kamar

Please Login or Register in order to submit comment