Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu Allah yayi masa,tafiya koda ta sati daya ne bai iya tafiya ba tare da kulsum din tasa ba,momma tace ita abun ya isheta,ba za'a yita mata jele da yara ba,su din dai da sukaga zasu iya sai sun dawo,Allah raka taki gona,ummanmu kuma ta goyi bayan momma,wani lokaci shima amirun idan ya tashi nashi abun sai hajiya qarama momma ko ummanmu s karbesu,hakan ya sanya yaran suka shaqu sosai da kakanninsu.


Murmushi tayi ta daga video call din da take mata,ta maqale wayar yadda zata ganta sosai,ta amsa wayar bayan ta janyo mai ta fara shafawa.

Sai data fara da yiwa kulsum da samir tsiya kamar yadda suka saba koda yaushe sannan ta dora


"Kozu ku karbi yaran nan,muma zamu tafi namu honey moon din" dariya sosai ta kulsum ta saki


"Sharrin da zakiyi mana kenan?"
"Eh mana,jiya har sun fara maganarku wallahi,jiya da mukayi magana da ummanmu bakiga fadan da tayi ba,wai takardar meye da itama sai an mata wannan takakkar an karbota"


"Tayi haquri,an karbo certificate dazu,abinda ya rage mana tahowa,kuma ina tunanin a satin nan zamu taho"


"Ya daifi gaskiya" ta fada tana hararta,dariya kulsum ta sakeyi


"Lallabani yarinya,idan ba haka ba kamar a kunnen yayanki abinda kikamin"


"An gaya miki yanzu ina tsoro?,nima fa ina da me taremin din nan,kawai kara muke muku ni da hubby na,amma tunda abu 'yar hakan....."


Qarar bude qofar dakin da jawahir taji ya sanya ta saurin katse maganar da takeyi,don ta tabbatar saraki ne ya shigo,ta goce tana dariya,ta jonasu da yaransu.


Kyawawan twins guda biyu,identical twins ma kuwa,masu kama da mahaifinsu sak,irin jinin professor rashid,wanda a idanu zaka basu shekara takwas,saidai shekararsu biyar biyar kacal,bayan auren iyayensu da shekara biyu Allah ya albarkacesu da samunsu.


A hankali ya qaraso bayanta sanda take magana da yaran,tunda ya shigo tayi matuqar daukar hankalinsa,saboda wani qyalli da kyau da fatarta ta qarayi.


Dab da bayanta ya tsaya,ya dora habarsa saman kanta,kasancewar ya fita tsaho,murna ta kama yaran kamar su shigo ta wayar.


Taso zamewa ta qarasa shirinta,saboda tasan hirarsa da yaransa bame qarewa bace,amma ya hanata,ko yaya tayi gefe zata goce sai ya tarota,daga qarshe da qafafunta suka gaji da tsaiwa tilas ta sulale a jikinsa ta kwanta,tana ta murmushi tana sauraren hirarsu,har sai da wayar jawahir din ta saka low battery sannan aka haqura,ya dangwala yatsansa ya kashe kiran,saiya maida hankalinsa kanta.


Dagota yayi gaba daya ya dorata saman madubin yana fuskantarta,itama idanunta saman fuskarsa,ido daya ta kashe masa tana murmushi,saiya kama kumatunta yaja


"Yau akwai jan magana kenan" wannan shine salon furucin da sukewa juna a irin wannan lokacin,kai ta gyada sannan tace


"Amma yaran nan fa....."


"I know,nima nayi kewarsu,naso ki rakani kallon wasan polo,but na fasa,ina buqatar jin dumin yarana.....sai me kuma?" Kafadunta duka ta kada


"Babu"


"Ni kuma akwai"


"Yes sir....ina saurarenka"


"Me yasa kikayi rejecting duk wata gayyata ta daukarki aiki da manyan kamfanoni suka miqo gareki? Bayan kina da right nayin mu'amala da kowa ta fannin zanenki" Qawataccen murmushin daya sake narka masa zuciya ta saki,sannan tamiqa santala santalan hannayenta ta dorasu saman kafadarsa,ta sake matsowa dashi sosai dab da ita,har ya zamana suna musayar numfashi


"Kaine baban kamfani na,kaine arziqi na,kaine kuma jarina......a yanzu bazan iya aiki qarqashin kowa ba sai kai,saboda babu wani abu da nake da buqatarsa a duniya da ban samu ba.....hakanan duk abinda zan buqata a gaba nasan da cewa zan sameshi IN SHA ALLAH,sabida ina tare da jarumin namiji,mijin da yafi na kowa" dire maganarta yayi daidai da daukarta caraf daga saman madubin yayi gado da ita,salon yadda take masa maganar salone da bazai iya kaucewa tarkonta ko haquri da ita ba.




*_TO NIDAI DAGA NAN NA FICE NA BASU WAJE,KUMA ANAN LITTAFIN DABI'AR ZUCIYA YA DAKATA,KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA,YA BAMU LADAN DAKE CIKI_*


*_DABI'AR ZUCIYA ce son rai_*


*_DABI'AR ZUCIYA ce son kai_*


*_duk kuma wanda ya biye ma wadan nan abubuwan yana tare da nadama da dana sani,kana da iko da damar da zaka iya DABI'ANTAR DA ZUCIYARKA KAN KYAKKYAWAN AIKI,qarfi bawai a jiki kawai yake ba,a'ah qarfi yana ga mutumin dake iya mallaka da kuma sarrafa zuciyarsa_*


*_Annabi S A W yana cewa akwai wata tsoka jikin mutum,idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci kuma dukkan jiki ya baci,yace ku saurara itace ZUCIYA,ALLAH YA BAMU TSARKIN ZUCIYA_*🤲🏽🤲🏽



*_BAZAN RUFE BA SAI NA MIQA GODIYA GA 'YAN AMANAR ZAFAFA,WANDA BASA GAJIYA DA SIYAN LITTAFINMU,ALQAWARIN ALLAH YAKAI MUKU A KODA YAUSHE,ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRI,YA KUMA SAKE HADAMU A WANI SABON KAFCEN NA GABA IN SHA ALLAH_*


*_DUK INDA AKAGA WANI KUSKURE,TO AJIZANCI NE IRIN NA DAM ADAM,WANDA YAKE TARA BAI CIKA GOMA BA_*


*_FA SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASHAHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment