Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya najwa duban mommyn sosai,kafin tace komai mommyn tayi gaba da hanzari xuwa dakinta tana cewa


"Ina zuwa,Allah dai yasa lafiya" bata tanka ba tabi mummyn da kallo kawai,daga nan inda take tana jin sanda take murza key tana rufe qofar dakin.


Numfashi ta fidda tana kyabe baki,ita a nata ganin mommyn nata tana wahalar da kanta ne kawai,duka wadan nan hanyoyin sun mata tsaho da nisa.


Mintuna kusan goma sha biyar cikakku mommyn ta fito tana riqe da wayar a hannunta,yanayinta ya sauya kadan ba kamar sanda ta shige ba,xuba mata idanu najwa tayi tana jiran taji wani abun daga bakinta


"Dole naje ma'ajiya,kyauro yace kwanakin nan kamar suna hangen akwai matsala" wayarta ta aje gefanta sannan ta dubi mommyn


"Bazan iya bun turbar da ko da yaushe kike bi ba mommy,bani da wannan juriyar,me yasa ba zaki me gaba daya ba ki huta?,me kike jira?" Ta tambaya uwar tana kafeta da idanu.


Kai mommy ta girgiza


"Banason haqqin rai bisa wuyana,a yadda nake kallon abubuwan komai ya kusa kawo kansa da kansa qarshe ba tare da ina da wani jibi ko tuhuma akan abun ba" shuru ya sake biyo baya,kafin mommyn ta sake magana


"Ki shirya zamuje nan da kwanaki biyar"


"Ranar lahadi kenan?"


"Eh....hakane,kamar dai yadda muka saba"


"Ranar zan shiga makaranta clearance.......saidai ki zaba wani dan rakiyan,don already ma na soma qosawa da xuwan" harara mummyn ta watsa mata


"Kyaci qaniyarki,ko meye nake ba dominku nake ba" dariya najwan ta saka,cikin ranta tana jin koma meye mommyn take domin su,ya zame mata dama dole tayin,idan ma batayin ba,bata jin ita zata zauna bata yiwa kanta wani gata ba.


********** Dukka idanunta ta zuba tana kallon kaltumen sanda take maimaita karatun data gama yi mata shi yanzun nan kamar ta shekara da iyashi,sau tari takan cika da mamaki tare da shakkar anya kuwa kaltumen ba boye musu tayi ba ta iya wasu abubuwan?,wani lokaci kuma mamakin nata yakan ragu idan ta tuna cikin hirarrakin da sukeyi da biba,ta taba shaida mata,su yaran qauye mafi yawancin lokaci sunfi na birni fikira basira da kuma azanci,saboda yanayin cima da kuma muhallin da suka girma,mai wadatar korran tsirrai,wanda ke cike da wadatacciyar kuma tsaftatacciyar iska mai kyau.


Sannu a hankali yake takowa zuwa inda suke zaunen,kebantaccen waje ne da yake malale da tattausan koren grass carpet.


A nutse yake tafiya cike da ginshira,kai idan baka sanshi ba sai ka dauka wani jinin sarauta ne,komai nashi me kyau a tsare a killace cike da tsafta da kuma aji.


Qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar karbarsa,suka kuma fitar da siffar da Allah ya bashi,ta tsaho wanda ke tafe da murjewar jiki daya bayyana surar qarfi a tattare dashi sakamakon daga qarfe da yake yawan yi,iska ce ke raba turarensa mai tattausan qamshi zuwa kowacce kusurwa dake daura dashi,hakan yasa yana dab dasu jawahir ta shaqi turaren ta kuma daga kanta don tabbatarwa da kanta shi dinne.


Murmushi ta saki saiya maida mata sanda yake dab da su


"Yaya,u are welcome..."ta fada tana gyara zamanta.


Kiran sunan yaya da tayi yasa kaltume dake faman son fara hada sentence da kanta duk da karatun baiyi nisa ba ta daga kanta,idanunta ya sauka a kanshi.


Suna hada ido saita sauke nata idanun a hankali tana gyara zamanta,ba wai don zaman nata baiyi ba,hakanan kawai taji tana buqatar ta gyara din.


Yana murmushin dake qarawa fuskarsa kyau da kwarjini yaja kujeran guda daya dake wajen,wadda da alama wani ne ya kawota ya zauna a kai


"Auta,an fara karatun kenan?" Ya fada sanda yake zama saman kujerar,qamshinsa yana mamaye wajen


"Allah yaya ka zama kudi,wahalan gani kake?" Murmushin ya sake saki,yana duqawa ya diba litattafan kaltume dake zube a wajen


"Ina wuni" ta gaidashi da siririyar muryarta,ya daga kansa daga litattafan daya fara budewa ya amsa


"Kina lafiya?"


"Lafiya qalau" ta amsa masa


"Babu wata matsala ko?" Ya kuma tambayarta a karo na biyu sanda ya buda shafin farko,itakam anan bata ga wata matsala ba,bata da rashin ci,babu rashin sha,babu rashin muhalli me kyau,matsalarta daya ce zuwa biyu,tunanin ummanta da habi dinta,sai kuma najwa da bata qaunar taga koda giftawarta,a iyaka saninta babu wani abu data taba aikata mata na kuskure ko ba dai dai ba,matsalar mummy kuma bata jinta da wani girma can,tunda a qalla tunda suke bata taba buda baki ta gaya mata wata kalma mara dadi ba,saidai kallon da take yawan yi mata yana sanyata jin tsarguwa aranta da kuma rashin sakewa,sai taji kamar an dabaibayeta.


"Babu" ta amsa masa a taqaice,tana jin wani nauyinsa da kwarjini,itakam yafi mata kama da baiwa da uban gidanta,gaba daya ta zame kalmar miji daga kansa,kallon uban gida tafi yi masa


"Ma sha Allah" ya amsa tana ci gaba da duba litatafan,wanda tun baiyi nisa ba ya soma mamaki,don bai tsammaci komai zaizo haka da sauqi ba.


Tsahon wasu mintuna sannan ya kammala dubawar,ya daga kai yana kallom jawahir


"Auta ya dalibar taki?" Murmushi ta saki tana miqawa kaltume wani littafi data gama duba mata wani dan qaramin aiki data gama duba mata


"Yaya,wannan dalibar tawa ta kusan zama malama, to my surprise duk abinda aka karanta sau daya ta gama daukeshi,abun yana bani mamaki sosai" kansa ya jinjina,alamun qarfi yana ga me qiba,tun kan yayi tambaya idanuwansa suka gane masa komai


"It means zata iya zana common entrance kenan?" Murmushi me kama da dariya tayi


"Yaya saidai placement gaskiya,wata uku na gaba fa?,karatun namu yana sauri ne fiye da tunanin me tunani"


"Good,am happy to hear that" kafin su kuma cewa wani abu daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo.


A ladabce ta gaida samir,sannan ta dubi kaltume


"Hajiya najwa tana kiranki" shuru wajen ya dauka,yayin da qirjin kaltum ya soma bugawa cikin tsoron kiran nata


"Muje na rakaki" jawahir ta fada tana miqewa


"Barta taje ta dawo,zamuyi magana dake" da baya ta dawo ta zauna badon taso ba,tafi kowa sanin halin najwan,babu lallai saboda Allah tayi kiranta,saita dubi kaltume sanda take saka wani lallausan slipper,yana cikin siyayar da jawahir tayi mata


"Jeki kaltum,amma ki dawo mu qarashe karatun yau,tunda kin iya wanda akayi" kanta ta gyada ta soma takawa a hankali tana biye da jamila data zo kiranta.


Ajiyar zuciya jawahir ta sauke sanda kaltume ta bacewa ganinta,tana juyowa suka hada ido da saraki


"Ya akayi auta?"


"Tausayinta nakeji yaya,da mahaifinka da mahaifiyarka amma a kawoka wata uwa duniya da sunan aiki,ka daina ganinsu kwata kwata,tana da hankali sosai yaya,tana da sanin ya kamata,shi yasa ko yaushe take shiga raina take burgeni" hanyar yabi da kallo kafin ya dawo da hankalinsa ga jawahir,shi kansa yana jin she needs more attention daga wajensa,har ransa yana jin zai kula rayuwarta a madadin rayuwar bilal da yayi niyyar taimaka,tunda ita dashi duka abu guda ya yisu........


"Ranki ya dade gata" jamila ta fada a ladabce tana matsawa gefe.


Waiwayowa tayi tana duba kaltume ita da sauran mutanen dake wajen,fuska a murtuke tace


"Ke,cikin dakina xaki shiga,qadangare ne ya shigomin ta window din baya ki ciremin shi,nasan ku qauyawa ba tsoronsa kuke ba mazanku da matanku" tayi maganar tana riqe da qugunta idanunta qir a kan kaltume.


Lokaci guda tsoro ya saukarwa kaltume,a duniya qadangare na daya daga cikin abinda bala'in tsoratar da ita,tund a gida basa hada hanya dashi,tun wani lokaci data yiwa inna laure laifi ta sanya mata shi a jikinta,sai dibanta akayi a sume.


Kai ta girgiza cikin rawar murya
"Wallahi ban iya cirewa ba,nima tsoronsa nake"


Zare idanu najwan tayi cikin salon masifa
"Ke ni zakiwa qarya,ku jimin yarinya da samun waje.....har a gayawa baqauye kama dabbobi,to wallahi yau saikin cireshi ko me zakiyi saidai kiyi" jin haka yasa kaltume dan ja da baya zuciyarta na bugawa tana girgixa kai


"Allah nima tsoronsa nake,da na iya dana cire miki" kafin ta ankara ta sanya hannu ta fincikota,ta kuma turata dakin ta maida qofa ta rufe.


Tsoro ne ya kamata,ta soma raba idanu,cikin rawar murya ta fara roqon najwa kan ta budeta bata iya cirewa ba,saidai tana jinta tana kuma tsaye bakin qofar dakin tana masifa tare da cin alwashin ba zata fito ba harsai ta cireshi,idan ba haka ba ta zauna a dakin,tsahon wasu mintuna amma najwan ta kafe kai da fata.


Razananniyar qara kaltum ta saki sanda qadangaren dake maqale jikin labulen ya fito yabi takan qafarta,gaba daya ta fita hayyacinta,sai kuka data saki mai qarfi.


Qarar ita taja hankalin samir da jawahir dake tattaunawa


"Yaya muryar kaltum ce fa?" Jawahir ta fada tana miqewa idanunta akan samir din,saiya miqe yace


"Muje".


Dukkaninsu darewa sukayi da ganin shigowarsa,banda najwa da tayi ta maza ta maze,sam batayi zaton yana kusa ba.


Bai kalleta ba ya isa bakin qofar dakin sanda jawahir ke tambayar najwa ba'asin abinda ke faruwa,ya murxa muqullin a nutse ya tura qofar ta bude.


Tana ganin haske bata tsaya banbamce abinda ke faruwa ba tayi hanyar da gudu,babu bata lokaci sukayi clashing,tayi kyakkyawan masauki a jikinsa.


Hannu yasa ya zareta a hankali yana jin yadd zuciyarta ke mugun bugu,saiya kama hannunta ya fiddota bakin qofar dakin ya tura qofar ya rufe,don ya fuskanci akwai abinda take tsoro cikin dakin.


A hankali ya saki hannun nata ganin yadda suke bin hannunshi dake riqe da siririn tsintsiyar hannunta da kallo,fuskarsa a matuqar dinke ya dubi najwa


"Me kika mata?" Cikin son nuna dakiya tace


"Qadangare nace ta ciremin fa kawai"


"Ce miki tayi ta iya?"


"A'ah"


"Amma meya saki turata dakin harda rufe qofa?"


"Yaya bakaga daga inda ta fito bane,har tace bata iya cire qadangare ba saboda sanabe?"


"Meye nasabar inda ta fito da iya cire qadangare?" Ya jefa mata tambayar wannan karon cikin matuqar fushi


"To ai......"


"Mtsw common keep quiet!"


"Yaya kowa fa....."


"Will you shut up ko sai na saki a dakin kema kinji yadda akeji?" Ya fada yana tura qofar dakin,wanda hakan ke nuna mata da gaske yake


"Am sorry" ta fada ba tare data shirya ba,don taga bacin ransa qarara.


Wani mugun tsaki yaja kamar xai cire harshensa,ya waiwaya ga jawahir da itama haushi da takaici ya cikata


"Ki tafi da ita dakinki"


"To yaya...." Ta amsa mishi tana kama hannun kaltume sukayi gaba,ya taka a hankali yabi bayansu ba tare da yabi takan matsalar najwan ba.


Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na quna,lallai ya tabbata mutumin nan bai qaunarta shima,tunda har zai barta da abinda take tsoro.yayi tafiyarsa,bayan yasan ko mommy bata a gida,saita juya fuuu tayi hanyar fita zuwa farfajiyar gidan,zata juyewa security nasu rabon.






D/Z
40




A hankali kowannensu yake kaiwa cikinsa a bincin,yayin da kowanne hannunsa yake dauke da wayarsa,table din yau fayau yake,saboda babu kowa a kai,daga mummyn sai najwa.


Wayar hannunta mummy ta ajjiye a gefanta,ta dora idanunta a kan najwa


"Ina jawahir ne?"


"Tana daki" ta amsa mata tana ci gaba da danna waya


"Me yake damun yarinyar nan ne?,kwanakin nan duka ta daina zaman cin abinci?" Fuska najwa ta yamutse ta ajiye wayar itma a gefan plate dinta


"Ina gaya miki mummy yarinyar nan bata da hankali,duk sanda zanyi mata magana saiki hanani,kinsan abinda yasa ta daina cin abinci damu?,saboda waccar banzar 'yar qauyen mai aikin,tare suke cin abinci cikin daki,kuma kina zaune an maida miki yarinyar baiwa,ita kewa yarinyar can karatu,ni wallahi badan badan ba da sai nace jawahir ba jinina bace"


"Ke!....kul!..." Mummyn ta fada cikin hanzari da muryar tsawa tana duban najwa


"Kada na kuma jin irin wannan furucin daga bakinki,jawahir jininki ce halak malak" baki najwa ta sake tana bin mummy da kallo


"Bakiji abinda nace miki ba?,nace kada na qara jin wannan kalmar daga bakinki"


"Naji" ta amsa,fuskarta ta fara nuna fushin nan nata da bata iya boyeshi duk sa'adda aka bata mata rai,tana daukar cokali taci gaba da cin abincinta,yayin da mummy ta sake daukar wayarta tana laluben number jawahir.


A daidai lokacin suna zaune saman carpet din dakin jawahir din,wanda tun ranar da saraki yace suje dakinta bata bar kaltumen ta koma dakinta ba,anan suke kwana,saidai jawahir din tana boyewa bata bari mummy ta fuskanta ba.


Mayukan data siyawa kaltum take daddagawa,sai data gama ta waiwayo tana dubanta,cikin yanayin jin haushi tace


"Ai wallahi tunda na kalli fatarki naga bata fara komai ba nasan baki amfani dasu,kinsan tsada da kyan mayukan na kaltum?" Kai ta girgixa


"Ni wallahi tsoron koilin nake,banason bilicin,masu yima qyanqyaminsu nake,asiyata tana yi,amma ko hanya banason mu hada,tasha yimin ba'a da tsokanata,wai ni baqa ce,amma ni bana damuwa kwata kwata,saboda nasan haka Allah yakeson ganina,kuma tunda ya bani baiwar ji da gani,ya bani hankali,ya bani idanu da qafafuwa to nafi mutum miliyan dasu wannan ma suke nema" murmushi jawahir tayi,sau tari tana tsintar kyawawan dabi'u daga kaltum din


"Maganarki haka take, black is beauty ni a wajena,ke kyakkyawa ce kaltum" ta fada tana kallonta,zaro idanu kaltum tayi itama tana duban jawahir,fuskarta da zuciyarta cike fal da mamakin kalamanta,saboda ita din ce mutum ta farko data fara gaya mata wannan kalmar,ko da yaushe saidai ace habiba ko asiya sune masu kyau a gidansu,saboda sun fita hasken fata,amma itakam bata taba jin wanda ya gaya mta hakan ba sai yau.


Ta lura da tarin mamakin dake qunshe a fuskar kaltume,saita sanya dariya kafin ta tsaya


"Wai mamaki kike?,da gaske nake ke kyakkyawa ce"


"Ki daina fada don Allah,sai naga kamar kinamin ba'a ne" ta fada tana shafa 'yar kewayayyar fuskarta,tare da shafo zara zaran gashin idanunta masu tsaho,da a wadansu lokuta take jin suke rage kyan fuskarta


"Kaltum,irinku ne masu boyayyen kyan da ba kasafai aka fiya ganinsa ta farat daya ba,sai sanda suka sake girma,suka kula da kansu,a sannan kyau mai ban mamaki yake bayyana daga jikinsu,fari tsaho ko sirantaka ba shine kyau ba,kowacce mace kyakkyawa ce ta irin hanyar da Allah S W T ya halicceta,amma ina me tabbatar miki ke.din kina daga sahun kyawawan mata,ina kuma da yaqinin nan gaba maza sai sunyi gware a kanki"


Idanu kaltum din ta sake fiddowa,wadanne mazan?,badai mazan irin wannan garin da take gani ba,saidai mazan qauyensu. Jawahir ta sake katse mata tunaninta ta hanyar cewa


"Wannan man dana siyo,bana komai bane,baya saka hasken fata,bazan ma yarda ki shafa ba idan muna tare,saboda ya saraki ya taba gayamin shafa man da zai sanya mutum hasken fata haramunne haramunne haramun ne......,kuma duk wadda takeyi ta shirya gamuwa da fushin ubangiji matuqar bata tuba ta daina ba,kuma dabi'a ce da shaidan yayi alqawarin dama sai ya sanya mata sun yita ita da qarin gashi" saita miqe ta soma bare ledar jikin mayukan tana dorawa saman mudubi


"Daga yau sune man shafawarki.....gana gyaran gashi ma.....wait...." Ta fada tana waiwayowa


"Ni ban taba ganin kanki bama fa kaltum,ya kike iya wuni ki kwana da dan kwali?" Murmushi tayi tana sake janyo dankwalinta tana rufe kanta,batason kowa yaga kan nata,saboda tsufa da kitsonta yayi,ranar da taso tsefewa a ranar suka tashi da kai bilalu asibiti,abinda ya hana tsifar kenan har yau,sai taji qwalla ta cika mata idanu


"Allah sarki bilalu,yana can qarqashin qasa a kwance" wannan tunanin ya qara yawan qwallarta,sai tayi qasa da idanuwanta,wanda kiran wayar mummy ya hana jawahir ganin hawayen


"Gani nan" ta fada tana katse wayar,saita duba sashen da kaltum ke zaune


"Zanje na dawo mummy na kirana,shima man wankin kan nan yana sake gyara gashi,idan ya karbeki ma har tsahon gashi yake qarawa,Allah kafin lokacin shigarki makaranta dole ki fara amfani dasu don kada su rainaki,nasan ya samir private zai kaiki,ba kasafai yakesaka mutum a government school ba" daga haka ta fice daga dakin.


"Ni dinma ba kowa bace,yadda kika daukeni jawa(haka take kiranta) ba haka bane,ban samu dukka wannan darajar a gidan uban daya haifeni ba,saidai na gaji,na gaji" ta fada tana kifa kanta saman cinyarta,hawayen da take riqewa suka fara zuba,jinta take a wani irin takure,ta gaji da zaman gidan,ta gaji da kewar ummanta da takeyi da habibanta,tana kewar dakin kwananta duk da nan ya ninka shi sau babu iyaka,amma tana kewarsa,tana kewar qauyensu qwarai.


Yadda mummy ta zuba mata idanu har ta qaraso ya tabbatar mata akwai damuwa,tun kafin takai ga zama ta balbaleta da fada,abinda ta jima bataji tayi mata ba


"Izinin waye kika nema da xaki fara koyawa yarinya karatu haka siddan,daga zuwanta gidan,ba'asan wacece ba ita?,ko yau ta cutar dake ta gudu babu inda zamu sameta,saboda bamu da tabbacin asalinta?da zaki dauketa ki kaita dakin kwananki ku dinga kwana tare,dakin kwananki fa jawahir?,anya kuwa kina tunawa da waye ubanki da kike hada matsayinki dana wasu?" Fuskar mommy take kallo tana mamakin yau kalaman dake fita daga bakinta,baya koda yaushe ita mai son taimako ce da jan mutane a jiki gami da faran faran dasu,gwiwa a sanyaye tace


"Mommy kece kuwa?" Idanunta ta lumshe tana qoqarin cooling down kanta,tare da controlling fushinta,batasan ta fidda maganganu haka ba


"Tunzurani kike son yi jawahir na soma aikata halin da ba nawa ba" ajiyar zuciya jawahir din ta sauke,ta gyara tsaiwarta


"Mummy,ya samir ne yace na koya mata karatu,kuma shine yace na kaita dakina,kuma mummy itama ta fara koyamin karatun islamiya,tana da karatun addini,zaki mamaki sosai idan kikaga yadda ta iya....."


"Ya isa,jeki" mummyn ta katseta sanda samir yake takowa cikij falon


"Thank you mummy" ta fada tana jin dadin yadda bata ja abun da yawa ba,tafi zargin ma najwa ce ta zugata,don haka ta wuce najwan tana yar waqarta.


Yana isowa wajen kwarjininsa ya mamaye gurin,fuskarta da mayalwaciyar fara'a kamar kullum tace


"Barka da fitowa son" tana gyara masa kujerar dake daura da ita,yana gyarawa kansa wata kujerar tare da shirin zama ya amsa


"Yauwa mummy" saiya soma gaidata bayan ya zauna,najwa ta gaidashi tana sauri ta kammala tabar wajen,abu guda dayan da take mtuqar jin haushinsa shine yadda kwarjininsa yake bugar da ita,sau tari shike mata burki kan abubuwa da yawa da take da burin aiwatarwa.


Umarni mommy ta bata tayi saving dinsa,ta miqe ta hada masa komai,sannan ta kwashe wayoyinta tabar wajen


"Samir,me yasa ne kwanakin nan kamar kana aiwatar da abubuwanka gaba gadi ba tare da sanina ko izini na ba?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi daga kai ya dubeta,idanuwansa daya zuba mata ya sanyata gyara maganar


"Duka masu aikin gidan nan qarqashina suke,nice ahaqqu da cinsu shansu da suturarsu,to amma ita wannan yarinyar ka dauki kudinka da kanka kayi mata abinda nice zanyishi,why son?" Ta qarashe tana fidda boyayyen numfashi,yau batasan mene yahau kanta take sakin magana haka anyhow ba.


Ci gaba da cin abincinsa yayi kafin yace


"Ita na daukota ne daga gaban iyayenta da sunan amana,so dole kinga nima na kula da wasu abubuwan,amana ba abune qarami ba"


"Qwarai kuwa son,kayi gaskiya,dole ne kowanne mutum ya dinga kula da amana,kuma tunda haka ne nima zan tayaka in sha Allah" ta fada tana murmushi sosai kan fuskarta,saidai can qasan zuciyarta tana kallon haka kamar ragin matsayine a gareta,amma koma meye zatayi amfani da fikirarta kamar kullum,komai yaci gaba da gudana a qarqashinta.


"I called daddy several times amma bana samunshi,akwai wani specific line daya kiraki dashi?" Wayarta tadan kalla sannan tace


"Oh god.....tunda yaje bakuyi waya ba son?" Kansa ya gyada,fuskarta cike da damuwa tana jawo wayarta gabanta tace


"Bai kamata ba, that's why ko yaushe yake kallonka a matsayin wanda bai damu da al'amuransa ba,pls put the digits ka kirashi yanzun nan" ta fada tana buda wasu shiryayyun numbers ta fara gaya masa yana rubutawa.


Sai daya gama jerasu tsaf ya sake kallonsu,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fara gwada kiran,a take na'ura ta gaya masa cewa a kashe wayar take


"Maybe he is busy shi yasa ya kashe wayar,but please try to call him again"


"Ok"ya amsa yana yunqurin aje wayar,dai dai sanda amiru ya shigo,a shirye tsaf dashi,kamar yadda ta lura shima samir din yayi ado ne cikin wata shadda da suke iri daya sak data amiru,dinkin matasan yanzu qaramin hannu,haka tsahon rigar bai wuce cinyarsa ba.




Da fara'ar shima ta amsa gaisuwarshi tana masa tayin zama yaci abincin,saidai shi ya kada kansa


"Sauri muke mummy,man,mu suke jira fa"


"Sai ina haka 'yan samari?hala surukan nawa zaku ganomin" Ta tambayesu tana murmushi


"Zamu daukarwa abokinmu amarya ne" samir daya miqe daga kan abincin ya bata amsa yana goge hannunsa da tissue


"Allah ya bada sa'a,saikun dawo" ta rakasu da addu'a sanda suke ficewa,idanunta na kan amiru,saita koma ta zauna,taja wayarta tana neman wata number,tana jin a yau ya kamata ta tada zancan,bai kamata tayi sake akansa har haka ba,kamar yadda hajiya kulu ta shawarceta.


"Pls kayi tuqi da kyau mu isa on time,wai me yasa kake hakanne,baka kyautawa IB bafa,tunda aka fara bikin nan babu abinda kaje masa,yau dinma kuma kana wani yanga akan titi kamar ba zamuje ba"


"Nayi maka kama da mara aikinyi da zan yita zaryan bikin abokai?" Ya fada tana dan jefawa amir harara,duka amiru yakai masa a kafadarsa yana dariya


"Allah ya sakamin,nine mai kama da marasa aikinyin kenan ko?,na gode"


"Wa yasani,abu a duhu" ya fada yana qaramar dariya,sannan ya qarawa motar wuta kamar yadda aboki kuma dan uwan nasa ke so.


Kamar kowanne qofar gidan amare sanda ake shirin daukar amarya,shima wannan a cike yake da motocin dake jere bisa tsari,yammata kowacce na nufar motar datafi kusa da ita.


Amiru ya sanya hannu zai bude motar saraki ya tsaidashi


"Me zaka fita kuma kayi,just ka bari ma hadu dasu a can"


"No,kasan yanzu an canza tsari saboda rashin tsoro,sai anyi marking motarmu a cikin masu kai amarya"


"Ok.....but pls" yayi maganar idanunsa nakan gungun wasu 'yammata dake tsaye,da alama suna laluben motocin dq zasu hau ne


"Kada ka kwasomin yaran can masu rawar kan tsiya,a bani dattawan mutane" harara amiru ya jefa masa


"To baba na" saiya saka qafa zai fice


"Am telling you ne....duk wadda tayimin rawar kai saita fice" daga haka amiru ya rufe masa qofar yayi gaba.


Mintuna kusan goma yaji ana knocking Glass din motar,ya daga kansa a hankali ya sauke glass din


"Saraki...... best friend din amarya zata dauka pls,bata jin dadi ne sosai" qaramin tsaki yaja yana mita qasan ransa,me yafi lafiya dadi ne wai?,amma su mata akan kai amarya basa ji basa gani sai sunje,kafin ya gama mitarsa ma amiru ya buda gaban motar,ta shigo a hankali,dai dai sannan ya buda murfin motar shi kuma ya fice ta side dinsa.


Sai data zauna sosai qamshin daya cika motar ya soma shiga hancinta,da alama na turaren mamallakin motar ne,wani qamshi mai taushi da dadi,sai ta waiwaya ta dubi drivern,take ta lumshe idanu,ta dora kanta saman qafafunta tana jiyo hayaniyar yammatan daga waje.


Minti kusan goma taji wasu mata an bude musu murfin baya sun shigo,daga muryoyinsu tasan cewa dattijaine,ci gaba tayi da kwanciya har sanda taji an sake bude mazaunun driver an shigo


"Bismillah" ya furta,muryar data ja hankalinta,har ta dago da kanta tana dubansa,suka hada ido,ya janye nashi idanun yana tayar da motar,yayin data lumshe ido tana jin kanta ya sake wani sarawa.


Ta nemeshi har ta gaji,layin data taba ganinsa tayi bulayin nemansa a fakaice amma bata sake ganinsa ba,number daya bata idan ta shiga ba'a dagawa,abinda bata sani ba shine ba kasafai jawahir ke daga baquwar number ba,yau sai gashi dab da ita,amma yadda taji ciwon kanta yana qaruwa ya hanata yin komai ko cewa komai,sai komawa da tayi luf ta sake kwantar da kanta saman cinyarta tana shaqar daddan qamshi,wanda zata iya cewa hancinta bai taba shaqar mata turare mai dadin wannan ba.




*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*


*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*


*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*


*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*


*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*


*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*


*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*


*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*


*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*


*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*


*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*


2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000


*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*


09134848107


*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar










41




Tunda suka tafi hankalinsa naga titi,tuqinsa kawai a hankali cike da nutsuwa har suka kawo gidan amaren,jama'ar daya debo suka fita,saidai mubina ta kasa koda motsawa,saboda yadda kan mata ciwo ainun,ya kuma qaru ke ciwon saboda saraki,wanda baisan meke faruwa ba,don suna zuwa bayan ya kashe motar ya fice daga ciki shima.


Baisan tana ciki ba sai sanda zasu koma,da yake wadanda ya debo din ba komawa zasuyi ba,amiru ya bude gaban da niyyar shiga ya ganta,ya shaidata don haka ya tambaya,da qyar ta iya amsa mishi


"Please saraki ka daure mu ajeta koda pharmacy ne ta amshi magani,daga nan ta kira wani ko daga gida ne ya maidata gida" yace da samir sanda yake tada motar,shuru ya masa bai amsa masa ba,ya fara tuqinsa abinsa.


A bakin wani madaidaicin private hospital ya tsaida motar,yayi horn sau biyu mai gadi ya taso ya bude masa ya saka motar ciki


"Ho samir" amiru ya

Please Login or Register in order to submit comment