Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kalli qawataccen gidan da sunan gidan mahaifanta,kamar ba'a karkarar ba,ko ina tiles da tiles,ga ruwan famfo ga wutar solar inverter,fankoki kota ina?,fakadeden tsakar gida da yasha tiles aka qawatashi da shuke shuke,ga yalwataccen kitchen irin na zamani,ga dan qaramin gas,abun kamar a mafarki?,bayan maka makan dakuna dake tsakar gidan,duk da bata bude ba batasan meye a ciki ba,kai koda a cikin garin ba kowa zai dace da irin wannan gidan ba.


Har samir ya shigo suka gama gaisawa da ummansu tana cikin duniyar tunanin wanda ya yiwa rayuwar ummansu wannan baban aikin,umman tasu ta qara qiba tayi wani shar da ita,idan ta hada umman data bari lokacin aurenta data yanzu sai kace uwace da 'yarta,babu wani gami ko kadan.


Bayan sun gama gaisawa umman ta qwalawa muntasir da shigowarsa gidan kenan kira,murna da mamakin ganin kaltum din ya cikashi,ta bashi key


"Ka bude masa dakin can hanyar soro,yadan huta kafin su wuce,ai baya juyawa ba daga zuwansu" ummanmu ta fada bayan ta yiwa samir magana ya dakata da zancan tafiya tun yanzu,muntasir ya karbi muqullin cikin murna ya fice.


Nannauyar ajiyar zuciya kaltum ta saki,tabi habi da kallo wadda ke ajjiye fulasan abinci masu kyau a gabanta da batasan inda suka samo fulasai masu kyau haka ba,habi din tata ta cika ta zama babbar mace,tayi qiba sosai,kamar ba 'yqr ficikar habi din data tafi ta bari ba,tayi adonta cikin wani lace mai kyau,da alama tana samun kulawa daga wajen mijinta yadda ya kamata.


"Ina dana ko 'yata da ban sansu ba?" Kaltum ta jefawa habi tambayar,saita dago kai,suka hada idanu,suka sakarwa juna murmushin dake cike da qauna irin ta 'yan uwantaka


"Yaya kaltume,ki fara sallamar dan aljannar mijinki din nan tukunna,yau kwanan hira zamuyi" saita dan dubeta


"Ki baro yusufan a gida?"


"Baya nan ma,ya tafi Lagos,kuma koda ya nan shi da kansa zaice nazo na kwana din"


"Lallai yusufa,likkafa ce taci gaba haka?"


"Duk ya sanadin mijinki ne ai,arziqinku muke ci" ta amsawa kaltum,duk da maganar ta daure mata kai amma haka ta duqa ta dauki kwandon,sannan ta fice tabar su ummanmu suna binta da kallo,kowa zuciyarsa fes qal,suna mamakin yadda kaltumen ta sauya gaba daya,kai baka ce ita bace.


Zata fita taci karo da wata mata na shigowa,idanu jage jage da hawaye tana sharbar qwalla,sai taja da baya don bata hanya,saboda ganinta riqe da yaro ga kaya ga kuma tsohon ciki.


Data sake dubawa sai taga ashe asiya ce,mamaki sosai ya kasheta,asiyan ce haka?,yarkace yarkace cikin tsumma?,itama asiyan idanu ta zuba mata,amma sam zuciyarta taqi yarda cewa kaltum din ce,don haka ta gwada kiran sunanta,jin ta amsa saita zabura,sannan da sauri ta qara gaba zuwa sashensu tana waigenta tare da qoqarin boye hawayenta.


Mamaki ya cikata sanda take ajjiye kayan abincin data jiyo muryar samir a qofar gidan tare da muryoyin jama'a,ko data leqa,sai taga qofar gidan nasu cike yake da al'umma,samir na cikinsu,daga gefe daya kuma wasu kaya ne aka sauke,da alamu kuma wannan al'ummar za'a rabawa,don kowa ka kalli fuskarsa cike yake da farinciki.


Idaunta ta maida kan samir,ta zuba mishi idanu tana masa kallon qurilla,irin kallon da bata iya masa matuqar yana tsaye a waje gata gashi,yadda yake ta haba haba da mutanen kawai zai alamta maka he's so simple man,bashi da qyamata,hakanan bai dauki duniya da fadi ba,kuma yadda suke gaisawan kadai xai gaya maka sabo sukayi,ba iya na yau ba kadai.


Ci gaba tayi da morewa kallonsa,duk inda ya matsa idanunta suna biye dashi,daga bisani ma saita zauna saman wata 'yar kujera stool dab da window din tana bibiyar duka motsinsa da idanunta,murmushi na qwace mata lokaci zuwa lokaci,har zuwa sanda taga sun fara rabon kayan,yana miqa wani abu a envelope da tafi kyautata zaton kudi ne,ana dorawa kowa saman kayan.


Komai da yakeyi yana yinsa ne cikin nutsuwa,cikar haiba da kamala,zuciyarta ta dinga qara gudu saboda yadda yake sake burgeta da shiga ranta,ganin bai qyamaci al'ummarta ba.


Hayaniya ce ta tashi daga can baya,harta qaraso inda samir yake tsaye,da alama kuma duka akan rabon abincin ne,matar da suketa tarewa ta qaraso,data duba da kyau sai taga wasilarta ce data shige dazu,wasilar da ayanzu tafi kama da mahaukaciya tuburan.


Idanu ta zuba mata daga inda take tsaye,mamakin abinda ya samu wasilan takeyi data sauya haka gaba daya,saika dauka kakar kaltum ce bawai sa'anni suke ba,banda ma tayi mata farin sani ba zata shaidata ba,tana tsaye taga samir din ya sanya an loda mata abincin me yawa ya bada umarnin a daukar mata,sannan ya fidda envelope din guda uku ya miqa mata,tana hangen sanda ta durqusa har qasa tana godiya,yayi mata alama da hannu ta tashi,yayi taku uku ya koma cikin mutanen yana ci gaba da kula da yadda ake gabatar da rabon.


Kamar wanda aka gayawa ko kuma wanda jikinsa ya bashi,saiya waiwaya saitin window din sanda yake qoqarin jingina da itaciyar dake wajen,karaf idanunsu suka hadu,sai taja baya da wani mugun sauri cikin faduwar gaba.


Sarai ya ganta,sai ya saki wani miskilin murmushi,ya kirayi umar daga inda yake,ya danyi magana dashi na wasu mintuna sannan ya juya ya fara takawa zuwa cikin gidan.




Da sauri sauri tayi hanyar fita,saidai yana sako kai itama tana sanyo nata,abinda ya basu damar yin karo kenan da juna,sai yaci gaba da tafiya zuwa ciki,yana korata da baya a baya zuwa cikin dakin,kana ya sanya qafarsa daya ya maida qofar ta bame,bai barta ba har sai da suka dagana da bangon dakin,takai qarshe,sai ya sanya hannunsa daya ya dafe bangon dakin,idanunsa akan kyakkyawar fuskarta,bugun zuciyarta ya qaru saboda yadda take iya jin saukar numfashinsa saman fuskarta


"Meye hukuncin mutumin daka kama yana satar kallonka?" Kunya da nauyinsa suka rugo suka dabaibayeta,ta kasa magana,ganin bata tanka ba sai ya qara matsarta sosai,tayi gefe zata goce,ya tarota ta hanyar sanya daya hannun nasa ya sake dafe bangon,ya sakata a tsakiya kenan


"Babu inda zaki motsa daga nan,saikin bani amsa" a dan tsorace ta kalleshi,tana iya jiyo hayaniyar mutane har yanzu daga waje,kada wani ya shigo dakin ya samesu a haka


"Ni ba kai nake kallo ba" ya saki da qaramin murmushin gefen baki,yana tuna wasu abubuwa da suka shude,kaltum me tsiwa,kaltum mara tsoro,gata yau gaba daya ta sukurkuce tsakanin hannayensa,tun baikai ga tabata bama


"To wa kike kalla idan bani ba?"


"Yan garinmu" tayi hanzarin bashi amsa,waiko hakan zaisa ya kubuta,fuska ya bata sosai


"Wasu mazan kike kallo ma ba mijinki ba?.....lallai sai na hukuntaki" yana kaiwa nan ya tallafo kanta,ya kuma hade bakinsu waje guda.


Wani salon tsotsa yakewa lips dinta,har sai da sukaso sakwarkwacewa gaba dayansu,dama ga sauran dafin jiya da bai gama barin jikinsu ba.


Baya ya koma a hankali ya zauna dabas a qasa,banda cikin tahowar kaltum din akwai umarnin momma da baisan hikimarta na yin hakan ba,da babu shakka bazai iya tafiya ya barta ba,bazai iya nesa da itaba na wasu kwanaki.


Sai da nutsuwarsu ta daidaita sannan ya karbi zuba abincin da kansa,yace ta zauna gabansa kawai yayita kallonta ya wadatar,ya fuskanci zallar soyayyarsa ke ci mata zuciya,amma batasan ya zata sake dashi ba,don haka bai barta ba a sannan sai daya samo kanta da kaso sittin cikin dari,yana cin abincin da bata tsammaci xaici ba yana janta da hira,har tazo ta iya maida masa.


Sake kallon agogon hannunsa yayi,qarfe uku na rana,a qalla sun shafe kusan minti ashirin xaune cikin motar kawai yana kallonta,bayan ta fito ne kawai da sunan yi masa rakiya.


Numfashi ya sake ja yana dubanta,sai ya kamo hannuwanta zuwa cikin nashi yana murxa tafin hannun nata,abinda yasa ta dunqule jikinta waje guda,kwanakin nan gaba daya wani dafi yake saukarwa jikinta,wanda mutum bai isa ya kauce masa ba.




"Suna jiranka fa,kamar sun gaji" tayi jarumtar fada sanda take hango tsaiwarsu murtala ta baqin gilashin motar da suke ciki ita da sarakin


"Zan tafi.....amma,sai kinyimun abu daya" wannan karon samun kanta tayi da sanya qwayar idanunta cikin nasa,har cikin jiki da jininta itama cikin wadan nan daqiqun takejin cewa zatayi kewarsa,kamar kada ta barshi ya tafi


"Ya salam..... what a beautiful eyes..... kada ki zubamin dafin da zan kasa tafiya na barki mana" tattausan murmushi ma cakude da kunya ya sauka saman fuska da lebanta,sai ta sadda kanta,amma kafin ta gama saukarwar ya kama fuskarta ya dago zuwa gareshi


"Nooo......ki barni na kalla na mitunan da suka ragemin na tafi" fararen idanun nata ta zaro


"Mintuna kuma?"
"Yes....so kike na tafi ko?" Kasa amsa masa tayi,saita maye gurbin amsar da murmushi


"Is okay,nasan kinyi missing ummanmu.....but before na tafin, give me a kiss" ya fada yana miqa mata tausasan labbunansa sirara masu taushi da sanyi" sake fito da idanun nata tayi waje tana girgiza kai alamun a'ah,sai shima ya fitar mata da nasa idanun


"Just do it....idan ba haka ba kuwa,zamuyita zama anan"kafin ya rufe bakinsa tayi saurin dora nata bakin ta manna masa kiss din mai tsaho kuwa,wani numfashi mai nauyi yaja,ya koma da baya ya zube cikin kujerar yana shafa qirjinsa,bata ankara ba yasa hannunsa daya ya fuzgota cikin jikin nasa,tsahon wasu mintuna har sai da nutsuwarsa ta daidaita.


Hannunta ya kamo ya saka mata sabbin kudi masu kauri yana cewa


"Wannan dai kyautace daga mijinki,don naga alama fada kike da sabbin kudi...... don't say no" dariya da kunya suka cikata,cike da girmamawa tayi masa godiya,ya fito da kansa ya bude mata qofar motar,yana tsaye yana binta da kallo har sai data shige gidan,sannan a sanyaye ya kada kai ya koma cikin motar,su umar dake tsaye gefe suna gulmar kallon da yake binta dashi,suna masa tsiya da dariyar ba sabon ba,suka shige motar


"Ku kuka da kanku akan gulmata,ku kuma dauke idanunka daga kan matata,if not, I'll definitely deal with you" saraki ya fada fuskarsa a washe,saidai kuma akwai alamun da zai nuna maka shi dinne boss.


"Sorry sir" suka fada cike da mamakin yadda akayi ya fahimci gulmarsa suke,sai kowa ya shiga taitayinsa,suka tada motocin.


πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


*_DA ZAFINSU_*


*_A TSARE SUKE_*


*_SUN TANADESU_*


*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*


*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*


*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*


*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*


_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_


08184017082


_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107


*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*




64


Farincikin data tsinci kanta a ranar bazai misaltu ba,gata ga ummanta,ga kuma habi dinta,bata manta da bilalu ba,sai data kokawa rashinsa a dai dai wannan lokacin.


Hira iya hira,labarai rankatakaf na abubuwan da suka faru cikin gidan dana qauyen sanda bata nan sai da habiba ta sauke matashi,ko abinci saida ummansu tayi da gaske sannan ta tsaya taci.


Habiba da umman sun fara mata ne da labarin abinda ya faru cikin gidan,bayan tafiyarta ummanta ta shiga damuwa qwarai,saboda rashin sanin taqamaimen inda aka kaita,sanda kawu as ya shaida mata ya karbi address na samir ta dan samu sauqi cikin ranta na wasu lokuta,daga bisani kuma kwanciyar hankalin ta wargaje,saboda jin an debi watanni shuru babu kaltum din babu labarinta,gefe guda kuma inna laure tana murza tsiyarta,tare da baza habaici akan auren kaltum,saidai cikin hikimar Allah,data durfafi tashin dare tana kaiwa Allah kukanta,sai ya sanya mata dangana,ya fidda mata damuwa,har ma tayi mafarkin kaltum din sau biyu cikin kyakkyawan yanayi a wasu darare guda biyu bayan ta gama sallar bacci ya dauketa,abinda ya sake sanya mata kwanciyar hankali kenan.




Babu dadewa sai ga wata qungiya me suna professor rashid women aid forum,wadda tazo rabon jari ga matan karkarar,ummanmu bataje ba,amma sai gashi anzo har gida an kawo mata nata tallafin jarin me tsoka,wanda kusan yafi na kowacce mace yawa,suka dinga qara mata kudin da kadan da kadan,ta cika da mamaki da kuma tsoro,daga bisani zuwan qarshe da suka kawo.mata tace ba zata karba ba,saiga samir yazo da kanshi,ya bayyana mata kansa,bai boye mata komai ba,saboda yace yasan ita din uwace,tsayayya jajirtatta,kuma a soyayyar uwa da yarta tabbas hankalinta bazai taba kwanciya ba idan batasan inda diyarta take ba,saidai bai bayyana mata yadda zaman aurensu yake da kaltum ba.


Sosai hankalin umman ya kwanta,ta kuma samu salama mai tarin yawa,taja bakinta ta rufe kuma,bata gayawa kowa waye samir din ba,saidai kuma tun daga wannan lokacin ya dauke musu nauyin ci da sha,gefe daya ga sana'ar ummanmu nata habaka,kasancewarta dama mace mai tarin kirki tun da can,tun mijinta malam amadu nada dukiya,kasancewarsa mutum me arziqi ada,bayan aurensu ya soma tsiyacewa,mutane suka fara cewa ya auri mai farar qafa.


Tun baya dauka har ya soma yarda,abinda yasa ya tsaneta ya tsan gwameta kenan ita da yaran.


Abun mamakin da ya faru a lokacin shine,yadda hankalin malam.amadu ya fara tashi,saboda jita jita da laure ke yadawa cewar anya ba kudin diyarsu sukeci ba kuwa?,sai a sannan ya fara tada hankalinsa nason sanin inda ya miqa kaltum din,ummansu tana kallonsa bata ce masa ta tafas ba,haka zai qaraci zirgillonsa kullum rana yana zuba idanun ganin samir ya kaishi inda diyarsa take,ko sau daya ummansu bata taba tanka masa ba.


Ba jimawa kuma sai ya fara wani zabura,yana tsaka da barci sai aga ya farka a firgice ya fito da gudu yana kiran sunan bilalu,yana hirji kan bilalun ya yafe masa,gaba daya sai ya koma wani firgitacce,ko baccin rana baya samun yi bare na dare,daya fara gyangyadawa zai farka a firgice.


Da farko ance masa wai fatalwa ce,umma ta kafe kai da fata kan cewa ba ita bace ba,danta bazai taba fatalwa ba,tunda ma ai saiya kwanta bacci yake ganinsa,daga bisani da suka samu wani malami masanin addini sosai,yayi masa bayanin komai,sai ya tabbatar masa haqqin bilalun ke bibiyarsa,ya bashi shawarar ya tuba ga Allah,ya kuma yawaita sadaqa wa bilalun,da ziyartarsa duk ranar juma'a idan hakan zata yiwu.


Da taimakon wadan nan addu'o'in ya fara samun salama,sai ya jima baiyi mafarkin ba,saidai gaba daya yayi laushi ya kuma canza,bashi da buri da addu'a koda yaushe illa addu'ar Allah ya bayyana kaltum din.


Ana tsaka da wannan samir din ya dawo da plan na canza musu ginin gidan gaba daya,saidai hassada da qyashi suka sanya laure d kawo iliya cewa basuso,yarsu asiya wadda tayi aure tace zaa canza musu suma.


A sannan asiyan tayi irin auren da suke burin tayin,alhj dauda ya kashe mata kudi kamar baisan zafinsu ba,sunata murna da alfaharin sun kafa tarihi cikin qauyen,bayan ya musu romon bakan suna zuwa asiya zataci gaba da karatu,saita zama babbar likita,duk kuwa da cewa basusan kowa nasa ba,amma su murna suke yarsu tayi goshin da kaf fadin qauyen babu wanda yayi irinsa.


Baibi ta kansu ba ya gyara sashensu kaltum din,saidai bai duba halayyarsu ba yayi musu kwaskwarima kamar yadda ya yiwa maqotan.


Tun tafiya batayi nisa ba jikinsu yayi sanyi da lamarin asiya,saboda tunda taje gidan alhj dauda cikin wahala da wulaqanci take,bata da wani girma ko kima,saboda sun gama watsewarsu a waje kafin auren,don haka ko a gaban 'ya'yansa da matansa guda uku data taras goranta mata yakeyi.


Ashe alhj dauda inuwar giginya ne shi,na nesa kasha dadinta,kowacce mace a gidansa ita kewa kanta komai,idan yaranki kuma sun tasa suyi miki,daga qarshe dai sai ya zamana laure ita ke ciyar da asiya dake aure wani gidan,sun dinke bakinsu saboda gudun dariyar jama'a,ta zauna duk da wannan wahalar da take ciki,saidai zancan duniya baya buya,kamar yadda dadi da wuya basa buya,tuni zance ya fantsama,saidai an kawo idanu an zuba musu,ana jiran ranar da zata fashe.




Babu jimawa ciki ya bayyana a jikin asiya,nan alhj dauda yayi tsalle yace ba dashi ba,ba kuma a gidansa ba,don shi bai aurota don ta haihu ba,ya aurota ne don ya huta da ita,abinda ya dagawa inna laure hankali kenan,saboda sun kama shirya plan na asiyan tayita haihuwa,kodon kwadayin abinda alhj dauda ya tara,da qyar aka ciyo kansa,bayan yarjejeniyar cewa bazaiyiwa asiya komai ba,data haihun kuwa haka akayi,laure ce tayi komai kamar ita tayi cikin,aka rufa akaci gaba da zama a haka,ba dadewa kuwa wani cikin ya sake bayyana,sai fa aka koma 'yar gidan jiya,kullum asiyan na tafe a hanya,wadanda ake boyewa kar su san komai tuni komai ya gama bayyana,a haka ake,har zuwa jiya da hukumar NDLEA ta kawo samame gidan ta cafke alhj dauda,ashe tsohon dan safara da saida muggan qwayoyine,wannan ne abinda ya kawo asiya gida abirkice,gashi batasan wani dangi nasa ko daya ba,na kusa ko na nesa,matansa kuwa ba zaman lafiya sukayi ba bare ta tambayi wata arziqi ta gaya mata,ita sai taga ma sam cikinsu ba wanda ya damu,kowa sabgarsa yaci gaba dayi,aka tattarata aka watsar,don dama kusan kamar kowa ya tsaneta cikin gidan,kamar mujiya,babu me mu'amala da ita.


Malam amadu da yusufa mijin habiba kuwa,rumfa guda biyu cikin babbar kasuwa samir ya siya musu,ya zuba musu jari me kauri a ciki suna juyawa,idan kayansu sun qare,yusufa zai tattaki har jahar Lagos yayi musu sari,rayuwa tayi albarka,saidai har yanzu tabon mutuwar bilalu na taba amadu,da mafarkinsa da yakanyi jefi jefi,sai kuma burin ganin kaltum,wanda kunyar abinda ya aikata ya hanashi tambayar samir kaltum din.


Ita kuwa wasila,tun randa aka kaita gidan nasuru,sati daya kacal nasurun ya tsallake yabar garin nan ba'a sake jin labarinsa ba,tun lantai babarsa na ganin xai gaji ya dangana ya dawo har abun ya fara damunta,yayin da wasila kuma ta miqe qafa,tana cewa zama daram,duk inda yaje zai dawo ma,ita ba zatayi zuciya ba,hakanan ba zata gaji ba,sai ya zamana lantai ke ci da ita.


A zaton lantai zata zauna da ita kamar uwarta,sai taga ba haka bane,cangal wasila bata iya mata,saidai taci tasha ta qoshi,ta tara qawaye susha hira da shewarsu,kamar ba itace wadda mijinta ya bace ba.


Lantai bata da haquri,don haka ta yuwa wasila kaca kaca kan abinda take,nan fa wasilan ta tsiri fushu da maidawa lantai maganganu,daga bisani ma sai lantai taga ta tsira fita unguwa,tun safe sai dare,ta kuma dawo da abubuwan arziqinta taci tayi hani'an ta kwanta abinta,tama daina cin abincin lantai din,tace idan ma saboda shi take uzzura mata.


Sai zaman gidan ya koma kamar na kishiya da kishiya,idan kaga lantai da wasila ana cashewa zaka dauka kishiya da kishiya ne,haka suke zaune.


Sannu a hankali wasila ta fara mulka wata uwar qiba ta tashin hankali,tayi dimimi abinta,sai hankula suka fara dawowa kanta,zargin ciki ya tabbata akanta,koda lantai ta tuhumeta.....sai ta shaida mata eh tabbas ciki ne da ita,kuma cikin nasuru,abunda lantai ta musashi kenan,saboda tunda aka kawo wasila nasurun bai taba kwana a sashen bama,yana tsohon dakinsa,har zuwa sanda ya tsallake ya tafi ya barsu.


Sanda lantai ta musa gagarumar rigima ta barke,ita tana ba cikin danta bane,wasila na cewa dole ta musa tunda ita ke tayasu kwana a daki,daga qarshe dai aka yanke zuwa cikin gari ayo scanning,wasila batasan meye ba,tace aje din ayi,saime?,ko shi akayi zai nuna ciki na nasuru ne,su kwano za'ayi ayi.


Anayin scanning kuwa ya bayyana watannin ciki,tafiyar nasuru wata shida kenan,shi kuma ciki wata uku,tun daga nan jikin iyayen wasila yayi sanyi,ita kuma ta dage kan hakane,ana tsaka da wannan rigimar Allah ya jeho da nasuru,suka bayyana gaban mai gari,ya kafe wasila da idanu yana mamakin qarfin halinta,cikin bacin rai yake bayyana gaskiyarsa,sai wasila ta fashe da kuka tana fadin,tabbas ciki ba nasa bane,ciki na wani dan maqwafcin qauyensu ne,wata barratu cikin qawayenta ita ta bata shawarar cewa,taje kawai tasha sabgarta,tunda tana da aure yanzu babu me ganewa,koda ta samu ciki akwai na nasuru ne tunda shine mijinta,ta dnga samun 'yan kudaden da zata kashe sabgar gabanta,basai uwar miji ta bata ba,tunda miji ya ajjiye ta ya tafi,me zata zauna yi itama.


Hankalin kowa ya tashi a wajen,iyayenta suka dinga kuka suna tsine mata,sai da me gari ya tsawata musu,a take anan nasuru ya rattaba mata saki uku,bayan wasu watanni tana gidansu da suka juya mata baya suma,nasuru ya aure lantana qawar kaltum,ya dauki matarsa suka wulla ibadan inda yake neman kudi.


Cikin naquda wasila ta hadu da jijjiga eclampsia,wannan yadan taba mata qwaqwalwa,ta haifi danta namiji,amma yazo babu rai saboda wahalar da yasha a ciki,haka iyayen wasilan suka fara nema mata magani,saidai sunyi saunyi harsun gaji sun watsar,bata warke ba saidai ta samu sauqi,wannan tabban guda biyu yasa tarasa me aurenta,bayan rasuwar mahaifiyarta taci gaba da rayuwa ita kadai cikin gidansu,ita ke dawainiya da kanta da komai nata,tausayinta ya sanya ummanmu ta dauke mata abincin rana dana dare,hakanan kuma takan aika mata dan kudin batarwa,kullum tazo gidan cikin nadama da neman yafiyar kaltum take,takan ce jifa tayi,ya kuma dawo ya sameta tsakiyar kanta.


Cikin matuqar sanyi da mutuwar jiki kaltum tace
"Allah ya kyauta,ya rufa mana asiri,ya rabamu da sbarrin zukatanmu da kawunanmu" tabbas zalunci abun tsoro ne,kuma tun a nan gidan duniya Allah ke sakayyarsa,babu daga qafa,babu jinkiri,lallai Allah baya son zalunci,kuma baya jinkiri wajen ramawa wanda aka zalunta.


A iya wunin ranar kadai kaltum ta tabbatarwa da kanta lallai sabuwar rayuwa ta zowa ummanta,mutane maqota wannan ta shiga waccar ta fita,kowa tazo ganin kaltum,tare da godiya kan kabakin arziqin da samir ya saukewa kowa,kafin kace meye wannan gida ya cika da abinci,kwano kala kala,kowacce da kalar abinda zata kawo.


Ko can dama ummansun mutum ce ta mutane,tana da kirki da kuma hannun kyauta sun suna da shi,abun hannunta bai tsone mata idanu ba,don haka ko a yanzun ma abun bai zame mata sabo ba,tana da hidima da jama'q,duk sanda wani cikinsu ita ko habi wani ya miqe sai kaltum din ta bisu da kallo,farinciki na ratsata na yadda sukayi kyau suka murje,rayuwar tayi kyau fiye da yadda tayi hasashe,kowaccensu sanye da sutura ta rufin asiri gwanin sha'awa.


Har magariba suna zaune ana abu daya,abinci kuwa har kaltum ta rasa wanne zataci a ciki,don har babar lantana sai data aiko da nata,bayan sun idar da magariba aka kawo yaron habi,sultan,yaron fes dashi sai qamshi yake,kyakkyawan bafulatanin yaro me kama da ubansa,bul bul dashi,da alama yana samun kulawa da soyayya daga mahaifinsa.


Shida uwar mijin habi din sukazo,tunda dama yana wajenta,a wajenta ya wuni,kuma dama ko suna gida ma wajenta take wunin,yadda taqe qaunar yusufa da habi haka soyayyar ta koma kan yaron.


Suka gaisa da kaltum cikin girmamawa,tayi mata godiyar abun alkhairin da samir yayi wa yaronta yusufa,kunyar baban ta kamata,macace ta gari,wadda bata qyamaci hada zuri'a dasu ba sanda kowa yake gudunsu,taso 'yar uwarta,ta mutuntata qwarai,ta nuna mata soyayya,sun kuma riqeta da girma da mutunci


"Baba da kin bari nazo da kaina ma ai" ta fada tana murmushi,itama murmushin tayi


"A'ah kaltume.....wannan abun alkhairin yafi qarfin sai ke kinxo za'a miki godiya".


A ranar duk sanda ta rufe idanunta muryoyin jama'a daketa mata godiya ke yawo a kanta,wai yau itace dimbun mutane ke mata godiya tare da son rabarta?,kowa yana farincikin samun wani alkhairi ta qarqashinta?.


Sultan dan habi yana jikinta,duk

Please Login or Register in order to submit comment