Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake masa wadda babu na biyunta,baya ga qaunae mahaifiyarsa a gareshi,wannan tunaninnm ya bashi qwarin gwiwar cira qafarsa da hanzari yabi bayansa.




Yauma gidan akwai jama'a dake ta shigowa gaisuwar sadakar uku suna fita,sai kuma wasu daga cikin 'yan uwa na kusa sosai da suke tare da ummanmu,kamar su yakumbo indo,da umma altine habi sa sauransu.


A filin tsakar gidan suke zaune saman tabarmi,a yanxun sai iya su isu,habiba da kaltumee na saman tabarma daya su biyu suna hirarsu qasa qasa,wanda su kadai sukasan me suke tattaunawa.




Sallama yayi ya shigo,suka amsa masa,masu masa sannu da zuwa sukayi masa,ya gaisa dana gaisawa,sannan ya dubi kaltume


"Ki kiramin babarku,kuzo keda ita" sai ya qara gaba yana bude dakinsa.


Jikinta a matuqar sanyayen da batasan musabbabinsa ba tun dazu ta miqe,ta shiga dakin ummanmu ta shaida mata.


Tare suka fito da ita suka nufi dakin nasa,zuciyar kaltum na wani irin bugawa da saurin da bata taba jin irin hakan ba,har kamar ana dan matsa zuciyar tata ne.


Gefan gadonsa suka cimmasa a zaune,ya baza babbar rigar jikinsa yana dakon isowarsu,gefe daya ummansu ta zauna,sai kaltun din ta bita ta zauna a jikinta tanajin jikinta yayi wani irin laushi.




Gyaran murya yayi kamar me shirin fara karatu,sannan ya dubesu,kanshi tsaye yace dasu


"Kamar yadda nace,na kuma alqawarta,to na bada auren kaltum" a tare maganar ta bugi kowannensu,kaltum da batayi shirin kallonsa ba,batasan sanda ta daga kai ta dubeshi ba.




Ya fahimci irin kallon da suke binsa dashi,a karon farko kuma yaji yadan daburce


"Eh,yau dai nima na sauke nauyin da yake kaina,na aurar da sauran 'yata data ragemin,zanyi bacci kamar kowanne uba" mamaki mai girma ya kama umma,taci gaba da kallonsa kamar wani sakarai


"Waye ka aura mata?" Dubanta yayi yana matse fuska


"To meye na gaggawa?,koma waye na aura matan ai zaku ganshi,tunda kunqi auwalu ba shikenan ba an muku abinda kuke so?" Yayi maganar cikin fada fada,saboda baiso taci gaba da tambayarsa waye mijin?,don idan hakan ta faru bashi da amsar bata,shi kansa baisan waye ya aurawa kaltum din ba,amma koma waye yasan babu abinda zai faru bazai cinyeta ba,a iya nasa dan qaramin sanin da ya yiwa duniya kenan.




Can qasan ranta umman ta saki ajiyar zuciya,tana jin fiye da rabin tashin hankalinta na kwaranyewa,saidai kuma akwai sauran fargaba a tare da ita,don batasan waye ne ya dauko ya maqalawa kaltum din ba,taji ranta yana motsawa,tausayi da bacin rai suka cakude waje daya suna karafkiya cikin ranta,kamar ba zata tankashi ba saita kasa,duban fuskar kaltum kawai ya daga hankalinta


"A wannan zamanin?,a irin wannan lokacin zaka yiwa diyarka irin wannan auren na rashin siyar daraja da mutunci?"


Idanunsa ya bubbude sosai yana hura hanci,baya so kuma baya sha'awar tayi masa wata magana,kota kawo masa tarnaqi kan hukuncin daya yanke ko misqala zarratin,don baiga uban daya isa yasashi ya janye wannan hukuncin ba


"Ke zuwaira ki fita daga ido na,ita din uban wace da bazan zaba mata miji ba?,ina cewa yarinya budurwa uba ne dama yake da haqqin zaba mata miji,shine zaki hurewa yarinya kunne ki sakata ta bijiremin?,to wallahi ta gwada,bismillah,ga fili ga me doki nan,nida ku uban wanda ya fasa" da alamu jama'a yakeson tara mata,saita miqe tana riqe da hannun kaltum zuciyarta na quna


"Ko da wanne lokaci fa zan tattarata a miqa masa ita" ya bisu da kalmar sanda umman ta kama hannun kaltum da tuni hawaye ya jiqe mata fuska,tsantsar tashin hankali kuma ya cika zuciya har saman fuskarta.


Mamaki ya kuma kama umman,wanne irin abu ne kuma haka,a daura ma yarinyar aure ba tare da tasan mijin ba,sanna ace ta shirya kowanne lokaci zata iya barin gidansu?,babu wani shiri tanadi ko sakawa rai?,mema suke dashi da zasu kaita dashi?.


Kamar yasan tunanin da takeyi saiya fiddo sadakinta daga aljihunsa,wanda sai daga baya daya nutsu ya lissafa yaga dubu arba'in da daya harda dari biyar akai,yana da yaqinin zata yi ma yarinyar kayan daki,ya lissafa ya dauki dubu ashirin ya miqa mata


"Nasan dai tunanin da kike,gashinan ayi mata wani abu dasu wanda zata tafi dasu,daga baya aje ayi mata jere"


"Amma wannan wanne irin al'amarine fisabilillahi malam?,wannan abun fa kwata kwata baiyi dai dai ba,yadda kake da haqqi a wuyanta itama tana da nata haqqin....." Saiya zaburo ya fara maganganu,maganganun da suka sanyata dole ta janye kaltum,suka fice ranta a mugun bace.




Kasa riqe kukanta kaltum tayi sanda suka koma daki,su yakumbo suna tambayar lafiya?,ganin yadda yanayin fuskarsu ya nuna zallar tashin hankali.


A karon farko bayan dukka abindanya faru,qwalla ta subuce daga idanun umman sanda take gaya musu abinda ya faru,ran yakumbo a bace ta miqe


"Haba,wannan abun yayi yawa,bari naje na sameshi,yarinyar yar tsana ce ita da za'a bada ita sadaka?,batasan miji ba miji bai santa ba?,sannan ace a shirya kowanne lokaci za'a kaita?" Harta sanya kai kawu ado ya shigo gidan,ta dubi qofar dakin amadu a kulle,da alama ya fice abinsa


"Ke kuma lafiya kamar wadda aka koro" kawu ado ya fada yana kallon fuskar yakumbo indo data cika da bacin rai


"Shigo daga ciki yaya" ta fadi tana juyawa dakin umma,saiya sanya kai shima,ya samu kujera yaja ya zauna.


A taqaice yakumbo ta labarta masa komai,sai yayi shuru yana jinjina kai,tabbas lamarin ya bugeshi ya kuma bashi mamaki,hakanan tun a hanya daya taho aka bashi labarin,saidai bai gasgata ba,ganin labarin yayi kama dana qanzan kurege.


"Da farko mu soma aiki da hankali tukunna,dukkaninmu nan amadu ya fimu iko da diyarsa kattume,hakanan a cikinmu babu wanda ya isa yaja da hukuncin daya yanke akan diyarsa koda gaban alqali akaje kuwa....saidai idan ita yarinyar taja da kanta,idan akwai abinda zamu iya cikin wannan lamarin bai wuce mu bashi shawara,mu kuma nusashe da shi ba,idan ya dauka haka mukafi so,idan bai dauka ba kuma,mataki daya zamu dauka,mu binciki halayyar yaron sana'a gami da nasabarsa,idan muka tabbatar da bashi da matsala a dukka wadan nan,sai muyi haquri,mu bi auren da addu'ar sanyawar albarkar ubangiji" a hankali zukata suka soma sauka daga bayanan da kawu ado yayi,ga duk me nisan hankali a cikinsu idan ya yiwa kalaman kallo na tsanaki,zai hango ya kuma shanshano gaskiyar zancan kawu ado,saidai ko daya zuciyar kaltum bata rusuna ba,saima tashin hankali data sake shiga dajin zancan kawu adon,yana nufin kenan a haqura a miqata ga duk wanda baban nata ya bata aurensa?,saita sake fashewa da kuka cikin tashin hankali.


*******A nutse yake shiryawa duk da cewa yayi nisa a tunanin da yakeyi,har ya gama shirinsa tsaf,ya dawo a hankali ya zauna gefam katifa yana jan kayan breakfast dake saman wani babban tray da niyyar yin break aamiru na zaune saman wani stool yana dubanshi,hannayensa goye a qirijinsa.


Hannayen nasa ya saki yana sauke ajiyar zuciya,fuskarsa da alamun damuwa yace


"Am asking you since yesterday.....ya zakayi da auren nan,bakace min komai ba" kamar ko yaushe harara ya watsa masa yana hada tea din,sai daya kammala ya riqe kofin a hannunsa zaikai baki sannan yace cikin wani irin soft voice


"Da zaka dameni duk ba kaine ka jawo komai ba?,dana sani ma na qyaleka,idan yaso in ka koma hajiya qarama tayi banda da namanka" duk da tasirin damuwar dake tattare dashi amma sai daya daara,kana ya koma ya daidata zamansa sosai,cikin seriousness yace


"Am bother to ask you ne saboda hajiya qaraman da kuma boss professor,but u are feeling bossy,sai wani jamin aji kakeyi"


"An ja makan,idan kaji haushi ka barni da matsalata" kafada amirun ya dage


"Kome zakace zan dauka,saboda bamu saba hadiye damuwoyinmu mu kadai ba" qaramin murmushi ya subucewa saraki,saiya aje cup din a gabansa,ya hade yatsunsa waje guda yana kallon amirun


"Wani abun mamaki,ban dauki wannan abun daya faru a bakin komai ba,but amma sai naketa jin nauyinsa a kaina tun jiyan?" Shuru ya ratsa tsakani,amiru ya saki ajiyar zuciya,muryarsa tayi sanyi fiye da dazu


"Ni kaina gaba daya tunani na ya qare akan yadda wannan al'amarin zai warware....ni inaga.....me zai hana ka qara ko one week ne,ka more sadakinka kawai,daga nan ka rubuta masa takardarta kawai ka maidata gida?" Wanu banzan kallo ya jefa masa


"Kana tunanin zan iya hada jiki da wannan yarinyar?,kai anaka tunanin yarinyar ma dukanta ta isa wani moro ne?" Kai ya kada
"Ba haka nakeson matata ta kasance ba,baya ga haka ta yaya zan cutar musu yarinya?,na karbe mata darajarta kuma na rabu da ita alhalin bata yimin komai ba?"


Gira amiru ya dage
"Ok,kawai ka gama bude school din muyi tafiyarmu,dole idan suka gaji da nemanka su warware abinsu su ba wani" fuska saraki ya matse yana dubansa


"Ya kakeson canzawa daga amirun dana sani ne?,ka manta who iam?" Shuru ya sake biyo baya,idanunsa ya janye ya dauki cup dinsa ya sake kurban tea sannan yace


"Zanje kawai na basu haquri kan ban shirya ba na karbi aurenta,zan rubuta mata takardarta na bata kawai shikenan an wuce gurin,ba wani yaudara ko kwana kwana" kai amiru yake jinjinawa,yasan halin samir,dama ba zaya dauki shawararsa ba,yana tarar komai gaba da gaba ne,bai iya boye boye ko qumbiya qumbiya ba,idan kuwa har kaga yayi hakan,to ba qaramin abu bane.


Sanin cewa koda ya sake cewa wani abun,hakan bazaisa samir ya sauka daga ra'ayinsa ba,saiya miqe yaci gaba da shiryawa,dai dai sannan umar yayi sallama ya shigo


"Ka dauki kayanmu duka ka saka a booth,get ready....ana gama bukin bude makarantar gida zamu wuce direct,ya kamata nayi facing my agendas"


"Ok sir" umar ya fada yana jan babbar jakarsa daya zuba komai nasa a ciki yayi waje da ita.




Taro akayi sosai na bude babbar makarantar primary da secondary ta me tafasa,wadda aka canzawa suna,kamar yadda samir din yakeyi a duk sanda yayi wani aiki.


Bangaren primary daban,na secondary daban,ga bandakuna da offices na malamai,abun dai masha Allah gwanin sha'awa,za'a iya gabatar da karatun boko da kuma islamiya duka a ciki.


Duk wani motsinsa yaro daya ya tsaye masa a rai wato bilal,ya dinga kallon guraben dayafi yin aiki a guraren,a irin wannan ranar yayi masa tanadin abubuwa masu yawa da zasu inganta masa rayuwa,saboda yadda ya karanci yana da buri kan yayarsa da mahaifiyarsa,saidai tsarin ubangijinya danne,ya kuma shafe tsarun dukkan wani me tsari.




Farincikin daya gani saman fuskar al'ummar mabuqata,talakawa bayin Allah shi ya dasa nasa farincikin da walwala kan tasa fuskar,har cikin zuciyarsa ya dinga jin farinciki da nishadi,he believes a rayuwa babu abinda yafi ka farantawa wanda yake da buqata ta hanyar biya masa tasa buqatar,yana jin abu daya ne a yanzu ya rageshi a duniya,RASHIN UWA MAHAIFIYA DAURA DASHI,KO TANA INA???,itace tambayar da yake yawan yiwa kansa,yana da tabbacin tana raye,saboda karo na barkatai da yasha yin mafarkinta tana gaya masa cewa tana raye,amma wani SHAMAKI data sanyawa zuciyarsa yasa ya kasa yunqurin komai wajen isa gareta.




*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*


*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*


*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*


*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*


*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*


*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*


*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*


*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*


*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*


*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*


*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*


2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000


*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*


09134848107


*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar












34


Kamar wadda ta tashi jinya haka take tafiya salalo salalo zuwa sashen kawu iliya,hannunta dauke da botikin qarfen inna laure da umma ta bata takai mata,yara suka kawo nan sashen ta suka ajjiye.


Sau biyu tana sallama,saidai kallo daya asiya dake tsakar gida saman kujera 'yar tsuguno fesa kwalliya tayi mata ta baiwa banza ajiyarta taci gaba da kwalliyarta,tana sa ye da wani tsalelen lace,har sai da inna laure dake daki ta fito,tana sanya slippers dinta da asiyance ma ta siya mata


"Au...au ashe amarya ce,amarya manya,amarsu kin sha qamshi,amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida" kamar hadin baki sai suka kwashe da dariya gaba dayansu,asiya ta fara tsaida tata dariyar


"Ni wallahi Allah har mamaki nake ma yadda kattume ta fito tatsatsanmu,kaf yaran gidan nan babu wanda ya kaita baqi da muni,kiyi haquri fa gaskiyata nake fada,koda yake ma ke da kika kusan tafiyarmi gidan miji....au na manta ban miki Allah ya sanya alkhairi ba,kada ace kana baqinciki,duk da ma kafi qarfin ka yiwa mutum baqinciki,Allah ya sanya alheri,ya kawo tsala tsalan yara" dariya suka sake kecewa da ita


"Ga munu ga talauci,ta ina tsala tsalan yara zasu samu?,don nasan duk wanda ya dauketa dai ajin rayuwarsu daya,tun daga suffa zuwa wadata,ai yara tsala tsala saiku a gidan alhaji uba" farrrr asiya tayi da idanu,kafin su sake cewa wani abu kaltum ta ajjiye botikin ta juya da hanzari,duk yadda taso maida amsa amma ta gagara,kalamansu sun mata muni sosai da bazata iya juresu ba.


A qafa suka tako shida amirun,tun daga makarantar har zuwa qofar gidansu kaltum,amirun yanata mitar yasa takalmansu duk sunyi qura,me yasa bazai bari a qaraso dasu a mota,bai kulashi ba har suka qaraso qofar gidan.




Qarqashin bishiyar dake basa iska a wajen ba kowa sai kawu ado da babban dan yakumbo indo,a nutse suka qarasa da sallamarsu,saiya miqe daga kashingidar da shi kawu adon yayi ya zauna sosai yana amsa sallamar,tare da basu damar zama.




Takalmansu suka tube sannan suka zauna din,sukayi musabaha mai cakude da gaisuwa ya amsa musu,shuru ya ratsa na sakanni,sai amiru yace


"Wajen mai gidan mukazo"
"Wanne daga ciki?"kawu ado ya tambaya yana kallonsu sosai,sabida baqin fuska ne a wajensa


"Baban kal.....kal" samir ya fadi yana kakarewa,saboda son tuna sunan da yake qoqarin yi


"Baban kaltume?" Kawu ado ya qarasa masa,sai amiru ya gyada kansa yana cewa eh


"Ko kaine mijin kaltumen?" Kawu ado ya tambaya yana duban amiru,sai yadan daririce,hakan yasa samir ya nuna kansa


"Nine" kallonsa ya dauke daga kan amiru ya maida ga samir yana qare masa kallo,gami da fadin


"Ma sha Allahu,sannunku dan samari,dama ina bidar ganinka kuwa" kawu ado ya fada yana gyara zamansa sosai.


Kwarjini yadan yiwa samir din ganin yadda kamalarsa ta sake fitowa bayan ya zauna sosai yana fuskantarsu,sai shima ya gyara zamansa yana cewa


"Ma sha Allah,nima magana ce ke tafe dani dama"


"To bismillah mana" kawu ado ya bashi dama


"A'ah baba,ba damuwa,ina saurarenka".


"To alhmadlh,nasan dai baka sanni ba,bakuma kasan alaqata da kattume ba,kattume kamar diya take a wajena,diyar yayata ce,banu wani boye boye a tsakaninmu,tunda an riga da an zama daya,duk da dai kai din da alama baquwar fuska ne,to amma kattume marainiya ce duk da tana da uba,sannan ita da dan uwanta gaba daya rayuwarsu ta kawo yadda take akaine a yanzu aboda huwacewar ubangiji kawai,yarinya ce da gwara wani marayan da ita,don Allah,don son annabi,ka riqeta bisa gaskiya da amana,saboda tasha wahalar rayuwa,tun batakai haka ba take ci da kanta danuwarta dama qannenta,tana buqatar matallafi,tana buqatar bangon da zata jingina dashi,munso yi mata hakan,amma bamu samu hadin kai daga wajen ubanta ba,sai muka rakata da addu'a,saboda munsan cewa ita din diya macace,kuma komai daren dadewa zata samu miji ne tayi aure,wala'alla wannan shine silar hutawarta daga dukkan wani qunci da matsi,ka duba darajar fiyayyen halitta kayi mata ruqo na mutunci da adalci.....kai din asalin da inane?" Ya zarce da tambayar samir,bayan yakai qarshen kalamansa da suka sauke duk wani shiri na samir din ba tare daya shirya hakan ba,ya buda baki da niyyar magana hayaniyar yaran data tunkarosu ta mamaye wajen,hayaniyar taja hankalinsu,ya daga kai yana duban yaran da suka taso wani saurayi a gaba


"Kaga da wanda akayi shirin bata nan,Allah ya dubu irin maraici da girman biyayyarta ga mahaifiyarta ya musanya mata,tunda kai din muna kyautata maka zaton alkhairi"


A hankali ya daga idonsa yana dubansa,shine wannan saurayin daya kubutar da ita daga hannunsa


"Meye alaqarsu?" Ya samu kansa da tambayar kawu ado sanda yaga auwalun ya shige cikin gidan,bayan badaru dan yakumbo indo ya kora gayyar yaran


"Dan qanin babanta ne,kuma ba haka suka so ba,don ko a yau auren kattume ya mutu sai sunsan yadda sukayi suka liqa mata shi" ya fada cike da takaici,shuru yadan sake giftawa,saiya sake maimaita tambayarsa


"Yaro dan inane kai?" Kansa yadan saddar qasa,yana tunanin yadda zai yiwa mutumin dake a karkara irin wannan bayanin mahaifinsa


"Ni dan garin azaren jihar bauchi ce,amma kuma a kano nake zaune,anan na taso"


"To...to ma sha Allah,to ta yaya yaro zamu iya samunka kenan?" Shuru ya sake biyo baya kafin ya samu abun fada


"Unguwar makwarari,duk wanda ka tambaya gidan malam nura zai kaika,ka cewa malam nura kana neman samir ko saraki,zai kawoka inda nake"


"Samir,saraki....to to....to shikenan,babu damuwa" ya fada yana jin gamsuwa a ransa,bayan ya hada wannan bayanan,da kuma bayanin da malam amadu yayi masa a tsaitsaye kan cewa su aka turo sukayi ginin makarantar da ake budewa yau,haka kawai yakejin wata gamsuwa da nutsuwa kan yaron,yasan unguwar daya fada din,yakan shiga cikin gari,kuma yana da abokima a anguwar,dake zuwa sari wajensa duk qarshen wata na kayan hatsi.


"To malam samiru banji naka batun da kazo dashi ba".




Shuru ya danyi,yana jin dukkan wani bayani da quduri nasa da yazo dashi yana saraya gami da bin iska,tamkar bayanin da kawu ado yayi masa ya warware komai daki daki ne,sai yaji nauyin mutumin,a yadda kamalarsa take,da irin roqon daya dinga masa da fatan alkhairi,yanzu shi kuma ya buda baki yace yazo sakin diyarsa ne?.


Muryar malam amadu ta ratsa tsakiyar tunaninsa ta tsinka zaren


"Tun yaushe kuka iso malam muhammadu?,kada dai ace daukar yarinyar nan kukazo yi aka barku a nan?" Kallon takaici kawu ado yake bin malam amadu dashi,shi sam.bai damu da sanin komai akan yaron ba?,sai qoqarin cusa masa yarinya yake kamar yar tsuntuwa ba diyar cikinsa ba


"Amm....malam amadu,ni a ganina daukar yarinyar nan yana da buqatar nutsuwa ko kuwa?" Dubansa yayi


"Wacce nutsuwa kuma?,bazai wuce kuce siyayyar kaya ba,yo ku basu kudin kayan mana,sayi siyayyarsu su siya abinda ransu keso,kabar yaro ya dauki matarsa,daga baya maje muga waje" .


A sannan inda ya lura da kyau wani kallo samir ke binsa dashi,ya yadda ya amince ya kuma yi imanin lallai yarinyar batayi sa'a da kuma dacen uba ba,yasan tsaf zai bata ran kamilin mutumin da ya shaida musu suna kawu ado,don haka ya shiga maganar


"Kawu,inaga a barta din kamar yadda kace,idan naje gida na dawo sainazo na dauketan" murmushin takaici kawu ado ya saki


"Babu komai malam samir.....bari amusu magana,ku tafi din,Allah ya tsare hanya,ya baku zaman lafiya" kafin ya dire wannan kalaman ma tuni malam amadu yayi ciki,ransa a bace yana mitar ana shiga gonarsa,shida iyalansa amma ana musu shishshigi?.


Yasan komai yana iya faruwa a cikin gidan,don haka da murmushi saman fuskarsa ya miqe


"Ina zuwa,kuyi haquri don Allah bari a fito da ita,kunsan sha'anin mata,kada suje su bata muku lokaci" a hankali amiru ya gyada wuyansa da yakeji kamar an sauke masa guduma,yayi alamar to,yabi kawu amadu da kallo sanda ya shige cikin gidan yana saba babbar rigarsa.




Sai daya shige ya maido dubansa ga samir,magana yakeson masa amma wanzuwar badaru a wajen ya hanashi magana,bashi kuma da tabbacin ko yaqinin baya jin turanci ko qanqani bare ya juya harshe,saboda ya ganshi fes dashi fiye da yanayin sauran samarin qauyen,yasan kuwa bazai rasa karatu a tattare dashi ba,sai shuru yaci gaba da sukwane musu lokacin,amiru cike da mamakin samir din daya ruguza duk wani abu da yace masa zai aiwatar,kuma ko sau daya bai kalleshi ba bare yayi masa nuni kan ya taso su kebe suyi magana kafin a kai ga fitowa da yarinyar.


Tana daga dakinsu,amma sallama guda daya tak ta mahaifinsu ta haifar mata da wata mummunar faduwar gaba data hanata zama,saita miqe tsaye cak ta tsaya sanda taji yana maganarsa gaba gadi a tsakar gida


"Ke zuwaira..…ku shirya yarinyar nan,mijinta yana waje yana jiranta zasu tafi,kuyi maza maza ku hanzarta" a hankali ta daga kai ta dubi mijin nata,tana jin yadda zallar rashina adalcinsa yakai mata ko ina ma rayuwarta,bazai sauya ba,babu abinda zai sauyashi,saidai ta sani cewa ta roqi Allah,koma meye zai shigo rayuwar kaltum din yazo mata da sauqin da babu wanda ya zata a cikinsu


"Dake fa nake magana,ku hanzarta da Alla kada kubar mutane suna jiranku" daga haka ya juya hankalinsa kwance ya nufi cikin dakinsa.


Tsam ta miqe daga durquson da tayo gaban murhu tana shirya itace,saboda girkin da takeson ta dora musu,sakamakon yadda kaltume din gaba daya ta koma bata iya tsinana komai,mayafinta dake kan igiya ta janyo ta sanya,sannan ta kutsa kai ta fito ainihin babban tsakar gidansu.


Tana niyyar zarcewa zuwa waje tanimu dan maqotansu daya fito daga sashen inna laure ya fito


"Yauwa tanimu,leqa daga waje qofar gida,idan kaga baqin fuska kace musu anason magana da mijin kaltume" tace da yaron


"Nama sanhi ai,ogan ginin makarantar mai tafasa ne"ya amsa mata,saita dafa kansa


"Yauwa,yi maza ka kiramin shi" ya cilla kuwa da gudunsa yayi waje,yayin daya barta da juya maganar tasa,indai hakane kenan yana nufin uban gidan su bilalu ne?,ya akayi har yaje ya karbi auren kaltume da hannunsa da kuma amincewarsa?,tambayar data tsaya mata kenan a rai.


Dan jim samir yayi yana juya kiran da aka masa daga cikin gidan,yana kuma jinjina kalmar mijin kaltume da aka kirashi dashi,sai yaji kalmar shi kansa tayi masa nauyi qwarai,sai kuma ya miqe yana zura takalmansa,cikin tafiya ta nutsuwa ya kutsa kai cikin soron,yana kallon zaizayayyar katangar gidan,yana sake girmama ubangiji da yayo mu mabambanta,hakanan ya bambanta mu cikin rayuwa wadata da samu da kuma jin dadi.


Tunda ya doso soron ta zuba mishi idanu a fakaice,tabbas shi dinne,duk da gani daya tak ta taba yi masa amma ta shaidashi,duk wani karatu irin na hankali nazari da kuma lissafi daya kamata kayi akan mutum tayi namijin qoqarin yi a kansa kafin ya cimmata.


A zahiri bata ga wata siffa ta tawaya ko siffar da zata nuna maka cewa akwai wani matsala dangane da dabi'a da kuma halayyar mutum ba,duk da kuwa cewa bawai ta sanshi bane sani na dabi'a da halayya ba,to amma kuma....data dauko wanna nazarin ta hada da labarai da bilal je basu a lokacin da yake raye dangane da halayya da dabi'unsa,sai taji wani sashe na zuciyarta yana mata sanyi da haske,duk dadai ta hangi tarin tazara da kuma bambanci a tsakaninsu,ta kasa jin nutsuwar cewa shida kansa ya zabi diyarta kaltume,ba zata bari ta yaudari kanta ba,wannan sam baiyi zubi ko suffar irin mutanensu ba,akwai alamun tazara da bambancin duniyar rayuwa a tsakaninsu.


Shuru ne ya ratsa tsakaninsu bayan gaisuwar data gilma,umman ta tattara dukkan kalaman bakinta sannan ta motsa cikin yanayi na nutsuwa irin na uwa


"Duk da cewa babu wanda ya gayamin ko mukayi maganar dashi,amma zuciyata ta kasa yarda gasgatawa ko kuma gamsuwa akan cewa kaine da kanka ka zabi kaltume na amatsayin matar da zaka aura,banbamcin yanayi da kuma yadda aka bada tallanta ko ince sadakarta ya gayamin haka,zuciyata tafi gayamin cewa......ka karba auren kaltum ne saboda wala'alla tausayi taimako ko kuma wani abu daya shafi hakan,toh....koma meye,nidai zan roqeka,koda ka auri kaltum ne don ka nesantata da rayuwarmu zuwa wani lokaci,zan gode maka,aqalla zata samu wani sukuni na taqaitaccen lokaci da muka gasa samar mata....zan kuma roqi alfarmarka akan ka riqemin ita amana,ka kulamin da rayuwarta,nayi yaqini da kuma imani da Allah,tunda har na roqeshi,na kuma nemi zabinsa,toba shakka abinda ya aiwatar a yanzu akan kaltum dai dai ne,kuma ina saka ran alkhairi ne ga rayuwarta,ban damu ba,koma daga ina kake?,koma daga ina ka fito,nasan cewa ubangiji baiyi koma meye ba domin wofantar da addu'ata ba,ALQAWARIN ALLAH NE cewa,bawansa bazai taba daga hannunsa ya roqeshi ba,shi kuma ya dawo masa da hannunsa haka ba tare daya amsa masa ba,ko a kusa,ko a nesa,kaje da kaltum amma bisa ruqo na amana".


Kowanne gefe idan ya juya sai yaji ya kasa amayar musu da dalilin xuwansa,baizo don ya tafi da diyarsu ba,yazo ne saboda ya warware igiyar data dauru a kanta dalilin amiru,amirun dashi kansa ya aiwatar da komai bisa wasa,wasan da yayi kama da ganganci sak!.


A hankali umma ta yaye labulen dakin,zuwa sannan ta jima ta suman tsaye,fuskarta tayi sharkaf da hawaye,tamaqale jikin bango sai kace mai shirin tsagashi ta wuce ta ciki.


Tun umman bata qaraso ba ita ta isa gareta a sukwane ta fada jikinta


"Ummanmu...ummanmu" sai kuma ta kasa furta komai,cikin wata irin dakiya tace


"Ya isa,a ko ina kike Allah yana tare dake,hakanan kina tare da addu'ata da izinin ubangiji" data daga kai ta kalli ummantata,sai dakiyar umman ta bata tsoro da mamaki,ta bita da kallo sanda take isa inda take tara kayan sawarta ta fara hada mata waje daya


"Ummanmu,bamuyi sallama da habi ba"

Please Login or Register in order to submit comment