Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda zata motsa dashi take motsawa,shidai kallonta kawai yake,saita zage tanata masa rawa sa waqa,tana cillashi tana cafewa,sai kuwa ya buda baki ya dinga bangala mata dariya,ta tsaya tana tayashi qaunar yaron na ratsata,tana jin kamar ita ta tsugunna ta haifeshi,habi na gefe tana musu tsiya.


"Wai ni kam inna?,tana nan da halin nan nata?" Baki habi ta tabe kafin dariya ya subuce mata


"Inna ai saura kadan a kaita gidan masu rangwamen hankali banda taimakon ummanmu......in gaya miki sata aka shiga akayi mata gagaruma,tun daga kudaden data mallaka har kadara,ke kaza wannan ba'a bar mata ba,hatta suturunta masu kyau sai da aka tsitsince,daga tafiyar sunan karime ta haihu,da inna ta dawo zaman 'yan bori ta dinga yi tana kururuwa,ke daga qarshe dai abu kamar tabi tabi,amma da yake yarinyar nan karime bata da mutunci,wallahi cewa tayi zakka ce Allah ya fitarwa innan,turmin zani wannan kasa dauka tayi ta bawa inna,bakiga kudin da umma ta dinga kashewa akanta ba,don jarinta ma sai daya tabu a sannan,amma da yake Allah ya sawa sana'ar tata albarka babu dadewa ta maida komai,ta sissiya mata kaya masu yawan gaske,sannan aka fara samo kan inna,waisai ga inna ba kunya ba tsoron Allah tana shiwa ummanmu albarka,wai dama ashe har yanzun ita irin arziqi ce?,yau gashi ta maganta mata damuwarta" baki kaltum ta tabe,son abun duniya a jinin innar yake,sam bataga amfanin soyayyar da zata nuna musu a yanzu ba.


Ana gama sallar isha'i baba ya shigo gidan,fuskarsa kamar gonar auduga yana neman kaltum din,ta gaidashi cikin girmamawa a matsayinsa na ubanta,saida daga haka babu wani walwala ko sakewa ta taso daga dakin da akayi masa ciki da falo ta dawo dakin ummansu,tayi xaton umman zatayi mata fada,amma sai taga batace da ita komai ba.


Cikin awannin da suka rage kafin su kwanta ta karanci yadda baban nasu yayi matuqar yin sanyi,babu wannan fadan babu masifa,tsakaninsa da ummansu sai kulawa da kyautatawa,don kafin su kwanta din haka ya danno musu uwar fura da tsire me kyau,yace a basu ita da habiba suci.


Sai da dare ya raba sannan suka kwanta ita da habiban,sultan na gaban kaltum ba jimawa bacci ya daukesu.


Saidai tun kiran sallar farko sukaji muryar babansu a can sama,dukkaninsu suka farka,da suka kasa kunne sai suka fahimci mafarkin bilal dai yayi yadda ya saba,don haka kowacce cikinsu ta maida kanta ta kwantar.


Basu kai ga komawa baccin ba muryar muzammilu ta karade gidan da wani irin ihu da yake kwararawa,abinda ya sanyasu tashi dafa'an suka zauna,suna jin sanda ake bude qofar sashensu,don haka suma suka miqe suka tsaya daga tsakar gida,suna jin gunjin kukansa da tambayar da ummanmu da baba ke masa


"Gobara ce,ta tashi muna bacci,ta kama gidan gaba daya ta qone,salisu da jamilu da shamsu duka an fito dasu basa motsi,asibiti xamu kaisu yanzu" Allah sarki ummanmu,duka saita rude,ta koma cikin gida ita da baba wanda ke laluben babbar rigarsa da kudade ya zuba a aljihu,ummanmu ta debo wasu ya qara musu,baban yace ta zauna suje su dawo.


Daga habiba har kaltum kwanciya suka koma sukayi,duk da kowa cikinsu yaji susa cikin ransa,kodon saboda abinda ya samu yaran,saidai gaba dayansu ba abinda ke kai kawo a ransu face irin abubuwanda muzammilu ya aikatawa,wanda ya jawo mutuwar bilalunsu.


Sunajin yadda ummansu ta kasa zama,sai zirya take,babu jimawa ana idar da sallar asuba,ko addu'a ba'a kammala ba saiga baban ya dawo cikin mutuwar jiki,gaba daya yara sun rasu,biyu na muzammilu,daya da munzali,wanda wani lokaci yakan kwana a gidan,sun shaqi hayaqun gobara ne,har ya musu illa,ya toshe musu hunhunsu,fiddau kuma matarsa na can asibitin sun bata kwanciya saboda qonewa da tayi gaba daya a fuskarta.


Suna jin ummanmu na shiri tana salati,ba wadda ta bita ita da baban suka tafi,sukam sai da suka qarashe baccinsu,suka gyara mata gidan sukayi abun kari,suna aikinsu suna hira a tsakaninsu irin na 'yan uwantaka.


Kaltum na mopping habi na kallon yadda wajen keta qyalli


"Wannan abu da kyau yake,yusufa dai yace in sha Allahu muma ya kusa yi mana gyara,kamar haka zai.mayar mana da gidan,harda tiles din xai saka mana" sai kaltum tayi murmushi,habi na dakai na karatu,inama yusufa zai barta tayi karatu,ko ita da zata dauki nauyinta,koda iya matakin secondary ne,koda kaltum ta gaya mata abinda ke ranta sai tace


"Haka baaba tace dashi,to baidai amsa ba bai kuma qi ba,kawai yace akwai nisa tsakanimu,amma idan da rabo wataran zanyi,shima yana sha'awar hakan".


Wankansu sukayi tsaf suka shirya,sannan kaltum ta zabo flask mai kyau ta zubawa ummansu kayan breakfast din,sannan ta zuba musu ita da habiba da sultan,suka zauna a parlor suna karyawan,da nufin idan sun gama su wuce gidan mutuwar suyi musu gaisuwa.


Suna cin abincin suna hira,kaltum na tambayar habiba wai ina auwalu kuwa


"Hmmm,wa ya sanine?,ki cikin gidan sai suyi wata basusan ina yake ba,sai kuma ya kado sannan ake ganinsa"


"Allah ya gyara" kaltum ta fada tana duba agogon hannunta,data dago kai sai suka hada idanu da habiba,habiban ta saki murmushi


"Sai.nayita ganin kamar ba yaya kattume ta mai kitso ba,gaba daya kin canza,kin zama wata 'yar gayu sosai,kalar fatarki ta canza,hanci ido dama gashinki kamar ba naki ba,irin matan da muke gani a tv" dariya kaltum tayi


"Lallai habi,ke bakiga yadda kika koma ba?,ni na zaci fa makaranta kika koma da kika waye haka?"


"Rufin asiri ne da yusufa ya sake samu.....sannan kuma ya koyamin karatun hausa,ina iya karanta hausa da rubutawa,sai yake samomin litattafan hausar nan na soyayya nake karantawa,ashe makaranta ce guda?,kinga abubuwan dana qaru dasu wanda ada bansan dasu ba?,gaskiya da ka muke rayuwar aurenmu" cikin doki da jin dadi kaltum tace


"Kai ashe kema kinbi sahu,amma naji dadi wallahi,saboda akwai qaruwa sosai a ciki,musamman zaka tsinci darussan rayuwa masu yawa,bama irin labaran da aka tsaftace alqalami,babu batsa sai soyayya mai tsuma rai,yadda zaki zauna da miji da al'umma lafiya ki samu tsira duniya da lahira.....gaskiya inajin dadin karatun novel sosai,saboda makaranta ce guda"




Suna tsaka da wannan hirar muntasir daya zama dan gidan yanzu yayi sallama


"Kaltum kizo kiyi baqo" harara habiba ta jefa masa


"Malam kaltum take yanzu.....ka daina bata mata suna" sosai ya saki dariya yana tsokanarta,kasancewarsa mutum me barkwanci da kirki kamar mahaifinsa kawu ado,kaltum na jinsu ta miqe tana sanya hijab tare da tambayar waye


"Kamar umar,yaron mijinki" jin haka ya sanya ta biya ta kitchen,ta hada kayan breakfast tace a fara kai masa,sai bayan wasu mintuna tabi bayansa,saita sameshi zaune saman motar anan ya karya din,yaji kuma dadin abincin,don ko breakfast din samir bai barshi yayi ba ya tasoshi.


"Gashi inji mai gida,yace ina kawo miki kiyi qoqari ki kunna,zakuyi magana" ya fada bayan sun gaisa cikin girmamawa yana miqa mata wani kwali,tun bata bude ba ta fahimci waya ce,tayi masa sannu da qoqari tare dayi masa sallama ta juya zuwa ciki bayan ta aiko yara su kwashe kwanukan sukai mata cikin gidan.


Yana qoqarin tayar da motar samir din ya kirashi


"Na bata yanzu yanzu"
"Ok" ya fada muryasa a qasa,sannan ya kashe wayar,umar ya saki murmushi


"So,soyayya wato bata da kirki,oga an masa mugun kamu da alama" umar din ya fada yana sakin murmushi shi kadai.


Tun a parlor din ta bude kwalin ta kunna wayar,tana gama daidaituwa kamar dama jiranta yakeyi kira ya shigo,Muhammad samir yayi saving sunanshi akan wayar,batasan murmushi ya subuce mata ba,ta saki kwalin ta shige dakin ummanmu,ta haye gadonta.


Sai data daidaita numfashinta,gab da zata katse ta daga ta kara a kunneta.


Wani nannauyan numfashi taji an saki kamar wanda ya tserewa abun tsoro


"Alhamdulillah..." Ya fada cikin tattausar muryarsa,data qara zama wani cool


"Da baki daga ba na rantse da Allah yau a garinku zanyi sallar azahar" dariya da mamaki ya kama kaltun,ta fidda idanu waje ba tare data iya cewa komai ba


"Da qyar jiya na iya bacci,banyi tsammanin zan iya kaiwa safiyar yau ba babu ke a gefena.....,abu daya ne ya ragemin damuwa da nauyin da zuciyata tayi....na kwana a dakinki,naga tarin sirrikan da aka boye ba'aso samir ya sani,naga zane kala kala na fuskar samir......ashe haka kema kike sona amma kika iya cinyewa baki furta min ba" wayyo,duk da baya kusa da ita amma ji tayi kamar qasa ta tsage ta shige ciki,saita bude baki kawai bat iya cewa komai ba,kunya na dawainiya da ita,tana tuna meye da meye ma ta boye ne a ma'adanarta,ba shakka akwai tarin abubuwa masu yawa dake nuna zallar bege da soyayyar samir din


"UMMUKULSUM" yayi kiranta da cikakken sunanta,abinda bata taba ji daga bakin kowa ba saishi,sautin da ya kashe mata duk wata gaba ta jikinta,saita sake lafewa saman gadon ummanmu,kamar zata nutse a ciki


"Idan kikaci gaba da yin shurun nan....to ki tsammaci isowata nan da awa daya,kuma bazan koma ba sai da ke....."


"Am sorry" tayi hanzari fada da wani irin sound daya sashi sakin ajiyar zuciya mai nauyi.


Lokaci mai yawa suka bata kan waya,yana fallasa mata sirrin zuciyarsa,tare da narkar da ita cikin duniyar soyayyarsa,har ya sanyata itama ta dinga fallasa sirrikan zuciyarta ba tare data sani ba,batasan ta yiwa kanta barna ba sai da suka gam wayar ta fara tariyar kalaman data gaggaya masa,murmushi ta dunga yi tana juya wayar hannunta,wayace me shegen tsada,don irinta ce a hannunsa,saida habiba ta leao tayi mata magana sannan ta fito suka wuce.


Sun tadda gidan makokin a cikea dagule,duk kallo sai ya koma kansu,kowa sai ya tambaya
"Wai wannan kattume ce?" Habiba ke gyara musu


"Kulsum dai ko kaltum" cikin lokaci kadan suka zama wasu taurari su da uwarsu,kowa son rabarsu yakeyi,daqyar kaltum ta janye umma taje ta karya,sai gashi ana jira da rububin abinda taci ta rage din,kowa yana neman saura.


A waje suka ga munzali da muzammilu sunata share qwalla,muzammilu ma daya kasa jurewa kuka ya fashe dashi,baki habiba ta tabe


"Ashe dai kowa nason nasa" maganar data ja hankalin kaltum kenan,saita kada kai kawai,ta tabbatar zaluncin da suka yiwa bilal ne Allah ya nuna musu ishara.


Cikin kwanakin zaman makokin kusan umma ke dawainiyar abinci ita da baba,saboda muzammilun yanzu basu da komai,an daina jin duriyar mahaifiyarsu kwata kwata bare ta aiko musu da wani abu,wasu suce ta mutu,wasu suce an kamata tana sijin,to sanin gaibu dai sai Allah.


πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


*_DA ZAFINSU_*


*_A TSARE SUKE_*


*_SUN TANADESU_*


*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*


*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*


*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*


*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*


_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_


08184017082


_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107


*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*








65




Cike gidan yake da mutane,wasu suna shiga wasu suna fita,idan ka kalla zakayi tsammanin biki akeyi,eh....kusan bikinne saidai bashi bane,su momma ne suka yiwa garin tsinke,ita da hajiya qarama,da jawahir da biba,suka kuma kawo kayan lefen kaltum akwati dai dai har guda goma sha takwas,set shida shida different colors masu azabar kyau da tsada.


Sunzo da duk wani kayan aure na al'ada da akasan ana neman auren diya mace dashi,nema kuma irin na masu wadata da rufin asiri.


Saukar girma ummanmu tayi musu,don dama tasan da batun zuwan nasu,girki sosai akayi na alfarma,bayan lemuka da samir yasa aka kawo ruwa da sauran duka kayan buqata.


Wannan kaya da aka kawo ya hautsina qauyen dinya cikin mintuna kadan,labari ya bazu ko.ina,sai ga jama'a anata tururuwar zuwa gani,sai ka rantse da Allah wani sha'anin biki akeyi.


Kaltum kamar bata sansu ba tayi gidan habiba dauke da sultan dinta,ba kowa a gidan,don babar yusufa ma tana gidansu,da ita aka karba kayan,habiban ma tana can,sai sallamar jawahir taji.


Cikin farinciki suka rungume junansu,kamar wadanda suka dade basuga juna ba,ta bawa jawahir ruwa tayi alwala sannan tayi sallah,sai kaltum din ta zuba musu abinci cikin wanda ummanmu ta aiko musu dashi.


"Da alama bakinki fa akwai magana"


"Akwai matar the giant saraki" jawahir ta amshe ba tantama ko kwana kwana


"Bayan tafiyarki abubuwa da yawa sun faru,ciki kuwa harda yankewa najwa hukuncin daurin rai da rai da kotu tayi" tayi maganar idanunta na tara qwalla,jikin kaltum yayi sanyi itama,ta fara lallashin jawahir tare da bata baki,har ta samu tadan nutsu sannan ta dora


"Lefen aurena yana gida irin naki kuma kamar naki,Amiru ya karbi soyayyata,ya kuma nemi yardata kan zai aureni....bisa goyon bayan hajiya qarama da momma harma da daddy,bayan sun lalubi dangin mahaifina.....da farko sun doje,amma da suka bincike sosai,sai suka samu dama akwai abinda ke damunsa kafin ya rasu,cikin rubuce rubucen wasiyyar da ya bari suka samu nice,sun karbe ni sun kuma mutuntani,musamman mahaifiyar abbana,qannensa dukka maza ne,don haka babu wani cece kuce me yawa suka girmamani ba wulaqanci,saidai ya samir ya roqesu kan su boye al'amarin,saboda sunaso duniya taci gaba da kallona a matsayin diyar professor rashid azare kamar yadda take kallo na a baya......saidai nidin kunyar kallonsu nakeyi....saboda hanyar da mummy tabi ta samar dani.....abun yana min ciwo kulsum,naga matuqar qoqarin ya amiru daya bugu qirji zai aureni....." Ta qarasa maganar qwalla na sauko mata.


Cikin sigar lallashi da kwantar da hankali kulsum ke mata magana


"Duk abinda ya faru ya riga ya wuce jawahir,kada jiyanki tasa ki rushe gobenki,yanzu babu abinda yafi kamata dake illa ki fuskanci gobenki,sannan shi a aure.....nagartar mace na iya shafe duk wani aibu dake tattare dashi...kedin nagartacciya ce jawahir,kina da dukkan DABI'A ta qwarai,baki bari ƊABI'AR ZUCIYA na son rai da son kanta ya rinjayeki ya gurbata miki halayya da ƊABI'A ba,kina da matuqar kirki da tausayi,na tabbatar wannan yaa amiru ya kalla,Allah kadai yasan manufarsa na fiddoki a haka da yayi,wala'alla ke wannan ce taki jarrabawar nan gidan duniya,kuma nayi imanin idan kika cinyeta....zata iya zame miki silar shigarki aljanna" kalamai masu taushi tayi amfani dasu wajen kwantarwa da jawahir hankali,ta kuma samu nasarar hakan,don ta sake sosai,suka dinga hira,jawahir na bata labarin abubuwan da suke faruwa da bata nan,gidan yayi dadi sosai,ya koma kamar da,yadda momma ke bata kulawa har yafi yanda mummy ke batan,saboda lokacin mummy tana fuskantar tsangwama saboda ra'ayinsu baizo daya da mummy da jawahir ba,amma a yanzu duka babu wannan.


Ya samir kuwa tace yafara zama mara kunya ta fadi tana dariya,wallahi baya iya boye soyayyar da yake miki,kinsa momma ce taja masa kunne kan ahir dinsa yazo ya dameki?,ai inajin da ko kwana hudu vakiyi cikin qauyen nan,gaban kowa kuwa banda momma da daddy amsa waya yakeyi,shi da ya amiru kuwa yanzu baram baram jawahir ta fada tana tilliqa dariya


"Me yasa?"kulsum ta tambayeta itama tana tata dariyar tare da jin wata kewa ta mijin nata na kwarara sassan jikinta


"Yace wallahi ya samir din ya fara zaucewa,baya barinsu suyi barci,bashi da aiki sai waya" sai suka sanya dariya gaba daya.


To sai yamma lis su momma suka tashi tafiya,ciki har da 'yan uwanta daga sudan mutum biyu,sai wasu daga azare 'yan uwan daddy mutum uku suma,saidai kulsum ta kasa zuwa bare ta hada idanu dasu, momma ta dinga mita


"Shikenan samir ya shiga tsakaninmu kenan yayi mana farraqu?,to ban yarda ba,da sake" da kanta tayi tattaki har gidan habi ta ganta sannan sukayi sallama,saidai jawahir ta roqi momma ta barta,sa dawo tare da kulsum din.


Hakan kuwa akayi,a nan qauyen suka barta,tare da ita suka dinga zagaya dangi,har gidan inna,wadda ta fashe da kuka sanda taga uban kabakin da su momma suka ajjiye mata a matsayinta na kakar kulsum,saboda momman tace duk wani daya danganci kulsum sai yaci arziqinta ya kuma ya qara,kulsum mutum ce,kulsum nagartacciyar mace ce mai kyakkyawar zuciya,wadda kudi ko dukiya ko wani qyale qyale na rayuwa bai dameta ba,sanda zata tafi saiga innar ta zube tana roqarta gafara


"Basai kin nema gafarata ba inna,badai abun duniya kikeso ba,kuma gashi an baki,zaki iya ci gaba da tsinema muda ummanmu" sarai innar ra gane magana ta gaya mata a fakaice,to amma tasan yaran sunyi haquri,sun kuma yi kawaici,kome zata fada kuwa,ita a yanzu nadamarta hade da kunya take,ashe wanda ka raina watarana shine zaiji qanka ya rufa maka asiri?,ashe RABON BAWA DA ARZIQI MUTUWA ce?.


"Allah ya yafemu gaba daya" itace kalmar qarshe da kulsum tayi mata suka baro gidan.


"To haka kawu ado yakumbo indo da umma suwaiba,kaf dangi 'yan uwa abokan arxiqi babu wanda baice HAIHUWA TAYI RANA ba akan su kulsum din,abun sai son barka da godiya ga Allah S W T wanda yake azurta bawa a sanda yaso.


Yakumbo indo ita ta dauke kulsum da jawahir ta ajjiye gidanta ta fara tsumasu,gyara na gaske take musu musamman kulsum da take ganin 'yar hannu ce,batasan komai bai gudana ba,har sai wani dare an hadu ana hira,kwanaki bakwai da suka rage su koma gida ayi walimar da za'a raka amare gidajensu,da ita da fatsima da karima wadda a yanzu itama ta sauko take kuma jin kunyar abinda suka yiwa kulsum din a baya,ashe arziqinta yaci uban nasu,gefe ga jawahir da habi dake baiwa danga nono,karime ke tsokanarta kada fa ta koma asake sabon gashi yawa sabuwar amaryar da aka kawo yau yau.


Yatsina fuska tayi tana dubanta
"To da mecece?,kar nake a leda,babu wani abu daya gudana" dariya suka sanya gaba daya,habi ta kama baki ta kasa magana,jawahir tace


"Allah ya samir ya gama hure miki kunne,ya koya miki rashin kunya"


"To meye laifinsa?,yama yi qoqari ai" shewar suka sake saki


"Zaki bayani da babban baqi wallahi,don indai wannan mijin naki ne a yadda dai na ganshi ko.....hmmmm" dukkansu suka sake saka dariya,sai kuma tsoro ya dan tsarga mata,ta basar da zancan aka shiga wata hirar.




Da magariba bayan sun bar gidan habi tayo wajen ummanta,sai umman ta kama hannunta zuwa qofar wani daki,ta tura ya bude,cike fal dakin yake da kayan jeren cikin gida da kayan qyale qyale,masu kyau masu tsada kuma na zamani


"Ki duba da kanki kaltum,kar kiji kunya,idan akwai abinda babu kiyi magana za'a siyoshi kafin ku tafi" idanunta cike fal da qwallar qaunar da umman nata ke mata


"Ummanmu....duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata


"Nakine kaltum,duka abunda na mallaka a duniya naku ne keda habi,saboda bani da kwafinku" rungume umman nata tayi a jikinta sosai,tayi kuka tayi kuka,tayiwa bilalu addu'a,sannan tana tsaye aka dinga fito da kayan tana gani.


Komai yaji yayi daidai,babu wani abu da babu shi koda kuwa ina za'a kaita a aure,sun jima suna hira da ummansu har zuwa sanda babansu ya shigo,bakinsa dauke da sallama,kai bakace shi bane.


Sannu da zuwa tayi masa ta miqe zata shige daka kamar yadda suka saba a baya


"Kulsumu" taji yayi kiranta,saita tsaya cak


"Zo nan" ya kirayeta,ta dawo da baya,tazo gabansa ta tsugunna


"Fushi kike dani har yanzu ko?" Yayi maganar muryarsa na rawa,saiga hawaye na sauka,abinda ya daga hankalin kaltum kenan,ta girgiza kai da hanzari


"A'ah baba"
"Idan ma kinyi ai bakiyi laifi ba,amma ina roqonki don girman Allah ki yafeni,bana buqatar komai daga wajenki banda yafiyar,koda bazan tsira da komai ba a rayuwata ba damuwata bace indai na tsira da yafiyarku"


"Ban riqeka ba baba,kai kayi silar kawoni duniya,na yafe maka,kuma kaima ka yafemin idan na taba bata maka" adaren su ukun suka zauna sukayi hirar da suka kafa tarihi,irin hirar da tun haihuwarta basu taba ba.




Ana ya gobe zasu tafi saiga lantana Allah ya kawota ita da nasuru,da fari kunyar kulsum ta dunga ji tana buya,wai kada taga kamar taci amanarta,saida zasu fita da yammaci xasu karbo wasu kaya wajen yakumbo indo,tayi wa lantana ba zata ta fada gidanta,sun sameta tana ta ware tsarabar doya da manja da dankalin turawa da takanyo,ta saukesu da ruwan da lemon roba cikin mutantawa da kuma jin kunya,xata fice kulsum tayi caraf ta damqota


"Na kamaki,waini lanatana kikejin kunya?,me kika yimin banda alheri?" Kanta ta sadda qasa,saidai yadda kulsum din keta dibanta da tuna mata da rayuwarsu ta baya ya tabbatar mata babu komai a ranta kulsum din,daga qarshe ta shaida mata ita dadi ma taji data auri nasurun,saboda sun dace matuqa,sukayi sallama ta hada mata doya da yawa tace ta kaiwa ummanmu,dama kuma ta saba kai mata duk sanda ta dawo,ba zata samu zuwa walimae tarewar kulsum din ba saboda tayi nauyi,amma ta karbi address dinta,ta tabbatar mata da cewa tana nan zuwa in sha Allah duk sanda suka shiga garin.


Kudin da tazo dasu taga sam babu wata buqata da ummanta ko babanta ke dashi,saita rabasu gida hudu,kaso biyu ta bawa habi wadda keta tunanin irin san'ar daya kamata tayi,ta bata shawarar sarar atamfofi da hijabai,kaso daya ta aikawa da wasila,daya kashin kuma ta aikawa da asiya,duk da tana tunanin ba zata karba ba,saiga asiyan da kanta tazo godiya,inna laure ta rakota,saida suka gama godiyar asiya ta fashe da kuka,suna neman gafarar ta,bata wani tsaya batama kanta lokaci ba tace ta yafe mata,sabida ta riga ta wucen wajen ita.


Bata jima da fita ba wasila tazo da nata kukan da neman gafara,itama cewa tayi ta yafe matan,saboda ubangiji ya ruga daya hukunta kowa dai dai da laifinsa,to me yayi saura?.




******** Cike da wata irin nutsuwa me ratsa zuciya gangar jiki da ruhi yake rufe kowanne sashe na gidan,har zuwa sanda yakai ga qofar qarshe wadda zata sadashi da ainihin falon gidan,saiya daga kansa a hankali yana kallon sama,wadda ta hada hadari me kyau daya fara feso yayyafi yas yas a jejjere me dan yawa.


"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" shine abinda ya furta,bayan samun kansa da yayi tsakiyar falon gidansa da yake mallakinsa,wanda tako ina qamshi yake fitarwa mai taushi da dadi,komai kuma na falon kalar fari ne da light ash.


Tafiya yaci gaba dayi yana sanya hannunsa yana fidda babbar rigar jikinsa ya riqeta a hannunsa,komai na jikinsa farine qal kamar hannu bai taba tabashi ba,tun daga samansa har qasa.


A hankali ya tura qofar dakin da yake da tabbacin a ciki take a zaune,dakine wanda babanta yayi mata komai na ciki,bayan dakin da umman ta ta shirya mata,da kuma wanda shi karan kansa samir din yayi mata,amma sai ta zabi zama ana babanta,saboda tasan cewa da uba ake ado.


Maida qofar yayi ya rufe,fuskarsa na fidda wani yalwataccen murmushi,sallama yayi da tattausan muryarsa data qara laushi,tun daga bakin qofar ya tsugunna ya zare takalminsa,safa kawai ta rage,sannan ya miqe a nutse,idanuwansa a kanta ya soma takawa zuwa inda take zaune,duqunqune cikin fararen tufafin lace mai taushi,da sassalkan mayafi mai ado irin na jikin lace din.


Waiwaya yayi ya hangi wata dunqulalliyar kujera ta cusion,ya sanya hannu ya janyota zuwa gaban gadon inda take zaune,gab da ita,gwiwoyinsu na gogar na juna,hannunsa ya sanya ya lalubo hannayenta ya riqesu ga cikin nasa,sannan ya sake maimaita sallamar da yayi dazun.


Da dasashiyar muryarta mai sanyi ta masa masa,ta sanya hannu a hankali ya zare mayafin data rufe kanta dashi


"Look" ya fada yana ci gaba da tsura mata idanu,wani shegen dinki akayima lace din kamar qasar arna,saidai ya qayatar dashi matuqa,ya kuma ja hankalinsa


"Karki fara karya alqawari tun yanzu..... please ummu kulsum" ta tuna dukkan wani alqawari data dauka masa a shekaran jiya,hanyarsu ta zuwa gidan qunshi,yabi

Please Login or Register in order to submit comment