Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau din yakai maqurar da bazai iya qyaleshi ba
"Kayi haquri baba don Allah kaji?" Cewar samir da sassanyar muryarsa bayan ya maida.ganinsa ga malam salahu
"Babu komai dana,ba komai" ya amsa masa cikin nuna girmamawa yana cakude tafukan hannayensa waje daya,sannan ya motsa ya bar wajen,samir ya bishi da kallo cike da tausasawa.




"Ji mana" samir ya fadi sanda fawwaz ya gyara kwalar rigarsa yana shirin barin wajen zuwa cikin gida,dakatawa yayi fuskarsa a daure ya waiwayo yana duban samir din
"Kayi qoqari wannan ya zama karo na qarshe da irin haka zata sake faruwa takaninka da duk wani ma'aikaci na gidan nan,don mu muna girmamasu.....saboda daraja ta fifiko da tazarar shekaru da Allah ya bamu tsakaninmu dasu,banason na sake ji ko na sake gani,nan gidan akwai ɗa'a" ya qarashe maganar yana gyada kanshi,sannan ya taka zuwa wajen motarsa ya barshi a nan,cikin zuciyarsa yana jin zafi,saboda ya fuskanci maganarsa ta qarshe tamkar baqar magana yake gaya masa,gugar xana yake masa kenan?,qwafa yaja cikin ranshi yana fadin
"Idan kere na yawo,zabo na yawo....." Yasa kai zuwa cikin gidan da sassarfa,samir dake qoqarin tada motar ya bishi da kallo,abubuwa masu tarin yawa suna kaiwa da kawowa cikin qwaqwalwarsa.




Tunda ya shiga motar ya zama tamakar kurma,duk yadda jauhar taso jansa da hira bata samu damar hakan ba,gwanine idan yaso miskilanci,duk da cewa bawai halayyarsa bace,hasalima mutum ne shi mai son ababen nishadi da abinda zai sanyashi dariya,saidai a wannan karon ya ari wata halayyar ta daban.




Jawahir da dama kusan tafi kowa sanin halayyarsa,tunda ta fahimta hakan bata sakoshi cikin zancansu ba ko sau daya,kusan magana daya biyu sai jauhar ta tambaya jawahir wani abu game da samir din,duk da yaqi bata hadin kai suyi hira yadda taso har suka kawo gidan hajiya qarama.




Da fara'a ta tarbesu,kamar yadda take da karrama baqo,duk da cewa mafadaciya ce,amma tayi gadon karamci da kuma dattako gami da halin qwarai.




Sosai jauhar ta sake cikin gidan,duk da cewa hajiya qarama bata ganeta ba,amma ta karbeta kamar yadda ta karbi su najwa,saida suka kebe da samir sannan ta samu sararin tambayarsa
"Saraki wannan fa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa fuskarsa har zuwa tsakiyar kansa,yama rasa makama da kuma ta yadda zai yiwa hajiya qaraman bayani
"Kayi magana mana,sai wani faman shafa gemu kake,ko labarinsa na tambayeka?" Ta fada tana hada fuska,saiya saki murmushi yana gyara zamansa
"Yadda kika ganta nima haka naganta hajiya,saidai ita yarinyar da bakinta ta gayamin manufar zuwansu shine a hada aurena nida ita...." Shuru hajiya qarama tayi tana nazari,a yau idan samir ya tashi aure tanajin babu wanda zai kaita farinciki,koda kuwa mahaifiyar data haifeshi ne,saidai tana tsoron daga inda aka qullo masa matara auren akeso a cusa masa ita,don ko sau daya bataji zancen daga bakin yayanta ba,to amma ba zata yanke hukunci da kai ba,don haka ta gyara zama tace dashi
"Waye gwanin hadin?" Hannunsa yadan jujjuya alamun shiga rudani
"To abundai gashinan hajiya,abinda na lura daddy da mommy dukka suna son abun" faduwa gabanta yayi,haka nan a take zuciyarta taji abun bai mata ba,ta yaya za'a kawo wa samir din matar aure,kuma wai da hadin gwiwar mommy a cikin lamarin,sannnan ta zauna tana ji tana gani?,ba zata lamunta ba
"Yanzu kai wannan mai zubin ruwan askin tayi maka kenan?" Dariya ce sosai ta qwace masa,ko banza idan yazo gidan hajiyan yana samun nishadi ko na minti kadan ne,hajiyar zuma ce,ga zaqi ga harbi,saidai tana da wani baban gurbi a zuciya da kuma rayuwarsa,qoqarin daidaita kansa yayi saboda harara da yaga tana jefa masa,sannan ya tattara kalaman da zai gaya mata
"To hajiya ni ya zanyi.....,gaba kura baya sayaki,kinsan sarai yadda muke ciki da Daddy,duk abinda zan aiwatar komai kyansa kawai gani yakeyi ina yine saboda na qalubalanci ra'ayinsa,tunda naqi siyasa sai yake ganin komai ma da zanyi bashi da wani muhimmanci ko fa'ida" tsaki hajiya qarama taja ta tabe baki
"Wanna duk makircin jidda ne bana wani ba.....to idanma kana so ka fiddata daga zuciyarka tuntuni,idan kuma bata ma shiga zuciyar ba to ka hutawa ranka" tana fadar maganar ta kama kanta hadi da shan mur,batajin har abada zata sake bawa jidda wata qofa komai qanqantarta,ta yadda koma a ina samir ya samo matar aure,amma zabin kansa da kansa,bawai zabin hadin gwiwa ba,koma ya zamana zabi daga bangarenta ita daya.




Wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa,ya tabbatar mafita tazo masa,tunda hajiya qarama ta qyamaci abun to yana sanya rai babu shakka komai zai warware cikin sauqi,kuma koda laifinsa zaizo a cikin lamarin a wajen daddy,to zayazo ne da kaso mafi qanqanta.




A nan gidan ya barsu ya wuce green garden abinsa inda yayi zasu hadu da Ezekiel saboda hada takardun neman kwangila daga qarshe ma saiya turama jawahir tex kan idan sun gama abinda zasuyi su wuce gida ba yanzu zaya dawo ba.




Sannu a hankali take takawa cikin duhun magaribar,wanda ya mamaye ilahirin duniya gaba daya,ya kuma cakuda da sassanyar iskar dake nuna gabatowar lokacin sanyi kowanne lokaci.




Za'a iya cewa yawaitar duhu tafi a qauyen fiye da haske,saboda rashin wutar lantarki da basu da ita.




Iskar ke kadata daga hagunta zuwa damanta,a gajiye take tubus,ga wata bahaguwar yunwa data kwaso,kan hanyarta kenan ta komawa gida daga gidan inna,wanda matar qaninta ta haihu,ta kuma umarce taje ta yiwa mai jego kitson suna.




Da fari taqi zuwa,saida ummanta ta mata da gaske sannan ta shirya taje,saboda ranta ya baci sosai da yadda akaja baki akayi shuru,babu wanda ya shaidawa umman tasu haihuwar,saida tasu ta taso nason ayi musu kitso sannan aka nemeta,duk da kadaram kadaham suka karbeta,babu yabo babu fallasa,saidai bata yarda ko ruwan gidan ya shiga cikinta ba,bayan an gama abinci an dire mata,tace ta qoshi,daga haka inna tasa aka dauke ba'a qara mata tayi ko bi ta kanta kan taci din ba,haka ta nado yunwarta ta wuni guda tayo gida da ita.




Tana gab da isa gidansu ta hangi mutum jingine a qofar gidan nasu,ya harde hannunsa a qijri ya zubawa hanya idanu,da fari tayi tsammanin nasuru ne,saboda jiya ya dawo bayan kammala jarabawarsa,a yau kuma yace ta tsimayi zuwansa,saidai data matso kusa sosai sai taga bashi bane,don haka bata wani maida hankali kan ganin wanene ba ta tasamma wucewa zuwa soronsu.




"Ke kattume.....ke!"


Ta jiyo kiran kamar daga wata duniya ta daban,wanda hakan yadan razanata,ta waiwaya baya da sauri,sai taga yaya munzali ne,yana dosota tamkar zai tashi sama,sai qura yake tadawa kamar wanda ala bugawa kugen yaqi.




Cak ta tsaya tana dakonsa har ya qaraso,abu na farko data fara ji shine saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta na hagu da dama,wanda hakan yasanya duk wata wuta ta jikinta daukewa,ta daina ganewa tsayin wasu sakanni kafin sadarwa jikinta zuwa kwanyarta ta dai daita,qara takeson saki amma kamar an riqe mata murya saboda tsananin zafi,kalamansa suka fara shiga kunnuwanta kamar saukar kibiya,wanda sai daya fara da manya manyan ashar sannan ya dora


"ashe 'yar iska ce ke tantariya?,shegiya mara mutunci kawai,yau kuma ta kaina iskanci da fitsarar taki zata biyo?,to wallahi baki isa ba,don ni ba sa'anki bane"


wani irin ciwo kalamansa suka saukar mata a zuciya,batasan sanda hawaye ya sulmiyo mata ba,tafin hannunta biyu dafe da kuncinta,a sanyaye tace




"Me nayi maka yaya?" Shuri yakai mata da qafarsa,wanda badon tayi hanzarin ja da baya ba tabbas da taji jiki




"Ni kike ma tambaya?,ashe iskancinki yakai kije har gidana ki ciwa matata mutunci ki qala mata sharrin sata?,banda ita din mai hankali ce dakai zuciya nesa kikasan me hakan zai haifar muku?,don u*****rki ni baso nayi ta kamaki tayi miki mugun duka ba inga uban daya tsaya miki ba?"


Kalmar uwarta daya fada ita tafi komai bata mata rai,zuciyarta ta fara motsawa,bakinta ya gaza dannewa




"Uwata yaya?" Ta tambayeshi tana dubansa kai tsaye




"Eh uwarki an fada,ke mai uwa ko?,dama ance idan aka zageta bakya qyalewa,to a fada don u****rki don u***rki"


"Badai uwata ba wallahi,badai uwata ba".


Gadan gadan ya yiwo kanta yana fadin


"Saidai tawa,sai tawa kike nufi?".


Kafin tayi kowanne motsai har ya iso gareta,bata ankara ba yasa qafa ya kwasheta,sai gata warwas a qasa,qugunta ya bugu da qasa,wanda ya tilasta mata qwalla qara ba tare data shirya ba saboda tsananin azaba,bai jira komai ba ya soma kai mata wani irin duka tako ina,tamkar wani mahaukacin kare,abinda ya fara jan hankalin mutane dake nesa kadan dasu suka fara tasowa.


Dukanta yake kai kace Allah ne ya aikoshi,yayin data dinga kuka mai qarfi da ihun neman dauki saboda azabar irin dukan da yake mata kamar ya samu qato dan uwanshi,mutanen farko da suka soma isowa sukayi sukayi ya bari amma ya qiya idanunsa sun rufe,har sai da hijabin dake jikinta yayi nasa wuri,data miqe ya maidata ta hanyar duka,saida wasu suka qaru,Allah yasa akwai maqocinsu malam sule,wanda yana zuwa ya hankade munzalin


"Ashe baka da hankali munzali?" Malam sule ya fada cikin fushi,yayin da munxali ke haki yana kallon kaltum dake duqe a wajen tana rusa kuka,jikinta na kakkarwa.


"Shin wai mema tayi maka kake mata irin wannan dukan kamar Allah ya aikoka?"


"Ni zata nunawa iskanci da bariki?,ka barni na qara mata"


"Idan ka kuma kai hannunka a kanta sai ranka ya baci kaji na gaya maka" cewar malam sule yana nunashi da yatsa.




Dai dai nan bilal ya qaraso wajen,saboda labarin abinda ya faru da aka kai masa can inda suke kankarar rake,tutture mutane ya shiga yi har ya isa inda kaltum ke duqe
"Yaaya"ya fada yana dagota,saiya miqa hannu ya fara da dai daita mata hijabinta sannan ya kamata suka miqe tsaye.




Idanunsa cike fal da fushi ya dubi munzali
"Indai ka zalunceta Allah ya saka mata" maganar data sanya munzalin nufoshi cikin fusata,saidai tuni aka riqeshi aka hanashi tabashi,sanda yake riqe da kaltum dake takawa da qyar yace dashi


"Ni zaka yiwa rashin kunya?,zaka gane kuskurenka kaima" shidai bilalu baiko waiwayo ba bare ya saurareshi,hankalinsa naga 'yar uwarsa dake takawa sannu sannu da qyar,hawayen ciwo da baqinciki na sauka kan fuskarta.










22






Wucewarsu bai sanya taron jama'ar da suka taru a wajen barin wajen ba,ciki kuwa harda wasila da labarin dukan yakai mata,ta kuma garzaya don ta ganewa idanuwanta,kowa gulma tana cinsa,yana son yaji ainihin abinda ya faru don su samu abun qadarwa,sai qananun maganganu sa qus qus ke tashi a tsakaninsu,gashi munzali ya wuce fuuu cikin fushi bare su nemi jin qarin bayani daga bakinsa.




Dai dai qofar shiga da fita daga gidan suka samu ummanmu a tsaye,ga duk mai hankali duba daya zai mata ya karanci tashin hankali saman fuskarta idanuwa harma da zuciyarta,macace mai tsananin biyayya wa aurenta,bata nemi izini ba,wannan ne babban dalilinta daya sanya ta kasa fita ceton diyarta,duk da yadda takejin gunjin kukanta cikin matuqar neman taimako,inna laure da zata mata kara kuwa birki taci ta koma ta zauna tana 'yan maganganu ciki ciki,wanda ta tabbatar idan ta saurara da kyau,bana kome bane saina jin dadin irin jibgar da munzali yakewa kaltum din,ko a yanzun ma shewa take qasa qasa me cike da nishadi,saidai lauren ba itace a gaban ummanmu ba,hannun diyarta ta kamo ta taimaka mata zuwa cikin sashensu.




A hankali ta zaunar da ita,saita wuce kawa kanta tsaye zuwa rumfar da suka maida madafi tahau qoqarin kunna wuta,wannan yasa bilalu yabar abinda yake yazo ya karbi umman tasu,ya fara hada wutar da kanshi,qwalla na cika masa idanu,yau zaiwa yaya abinda itace kusan ba'a rufa sati sai tayi masa,bazai yafewa ya munzalin abinda ya yiwa yayar tasa ba,saboda baiga girman laifin data aikata wanda ya cancanci ayi mata wannan hukuncin ba,koda sata tayi bare ma ba ita tayi ba.




Umman bata iya dawowa ta zauna ba,sai taci gaba da tsaiwa a bayan bilal,ta rungume hannayenta a qirji,duk sanda tayi irin wannan tsaiwar ba shakka ranta a bace yake,koda ba zata furta kota nuna ba,har ruwa ya tafasa tana tsayen,ta juye a babban baho ta surka shi da zafinsa,tasa bilal ya kaimata gaban kaltum da har yanzu kuke take,jikinta ko ina yana mata ciwo,bilal tasa ya fita ya basu guri,sannan ta sanya kaltum din ta fitar da kayan jikinta tayi daurin qirji.




Sai data gasa mata duk inda tasan zai zame mata miki ko yayi mata zafi,kuka kam ta yishi matuqa kafin a gama gashin,sannan tasa tayi wanka da sauran.




Kafin tafito bilalu ya siyo mata man zafi kaman yadda yaga tana mulka masa,ummansu ta ajjiye mata abinci,tasa ta shafe dukka jikinta dashi sannan ta zauna ta sanyata a gaba taci abincin.




Duk wannan abun da ake batace da ita komai ba sai data gama cin abincin,muryarta cike da wani nauyi dake nuna ya taso ne tun daga qasan zuciyarta take tambayarta


"Me kika yiwa munxali,kaltume ban haneki shiga sabgarsa shida matarsa ba tun randa yaxo nemanki afujajan?"


Kuka ne ya qwacewa kaltum din,cikin muryar kuka ta amsa mata


"Wallahi ummanmu tun ranar ban qara ba,ban qara bi kota hanyar gidansa ba"


Kwashe yadda abun ya faru tayi ta gaya mata,shuru umman tayi,ranta yana suya,tanajin kamar haqurinta yana gab da gazawa,da wanne zataji?,duka tako ina wanne zata kare?,wanne hannuwanta zasu iya dauka,ida amadu yayi masu mijinta ne,mahaifinsu ne,idan inna tayi musu mahaifiyarta ce....jikokinta ne,to amma munzali fa?,saboda kawai yana a matsayin yayansu saiya kamata cikin bainar jama'a saboda tozarci da wulaqanci yayi mata irin wannan dukan?,kamar wanda ya kamata tana zina ko sata?.




Lokaci mai tsaho tana tausar kanta kafin ta samu zuciyarta ta fara sanyi,saidai bata gama direwa ba sababi masifa da tashin hankalin babansu ya biyo baya.




Ko sallama bai samu zarafin yi musu ba sai qwala kiran sunan kaltume!....kaltume!!!!..




Tana daga zaune ta amsa masa don ba zata iya miqewa cikin hanzari ba,kafin wasu sakanni ya bayyana cikin gidan


"Ni na banu na lalace,wannan wacce irin diyar jaraba Allah ya jarabceni da ita?,don ubanki munzali sa'an wasanki ne?,ba sbine madadina ba randa bani?,kin dauki baqar hudubar uwarki kin fara muna musu 'yan ubanci ko?,wallahi wallahi kaltume ki fita daga idanuna,kiyi qoqarin da hannuna bazai kai jikinki ba,kinsan Allah?,duk sanda kika bari hannuna yakai jikinki saina qarar miki da numfashi".


Sosai furucin ya sauka zuciyar ummanmu,a wannan karon ta gaza shuru


"Malam....ka daina fadar haka,idan ka fada da bakin mala'iku fa?"


"Da zan fada da bakin nasu ai da nafi kowa murna,me za'ayi da yarinya irinta?,to na soma gajiya,kuma wallahi aka kaini bango ran kowa saiya baci a gidan nan,kowa bazaiji da dadi ba,kin taramin jama'a qofar gida saboda dai ni a tozartani?,kamar ni kadai ne me 'ya'ya a duk garin nan?,to idan xaku shiga hankalinku ku shiga,in ba haka ba zanbi takan kowa a cikinku,ai ba gagarata kukayi ba" daga haka yayi gaba kamar zaiyi ball da qafar umma dake miqe.




Shuru ne ya ratsa wajen na wasu sakanni 'yan kadan,kafin kaltum takasa jure abinda take ji ta saki kuka me sauti,sai umman ta kasa hanata,ta miqe tayi daki,tabar bilalu da rarrashi.




********Washegari wani abun mamaki sai 'yan dubiya suka dinga shigowa gida nasu,wannan na fita wannan na shiga,kowa ya shigo abinda zaice shine


"Allah ya kiyaye gaba,ya sawwaqe".


Da amin umma ke amsawa,tun tana irga wadanda suka shigo har ta daina,saidai tana jiyo inna laure daga can babbar farfajiyar gidan tana 'yan waqe waqenta cikin madaukakin sauti,da alama ma abun shinfida ta zauna kamar me karbar gaisuwa,duk kuma wanda ya fita daga wajen ummanmu sai yaja birki wajen inna laure,mafi qaranci mutum ya kwashe minti talatin kafin suji fitarsa yana yiwa inna laure sallama,ranar haka suka wuni har dare,abun ya yita basu mamaki,saida cikinsu babu wanda yayi maganar da dan uwansa.




*********A wata washegarin misalin qarfe shida na safe tana kwance kan shimfidarta tana jiyo motsin umma a tsakar gidan nasu,duk kuwa da yadda iska ke kadawa.


Lokaci lokaci takanyi juyi a hankali saboda yadda har a sannan wasu sassa na jikinta ke ciwo,musamman qugunta daya bugu,a duniya ya washi ta tashi cikin lalurar da zata hanata taimakawa ummanta,kota kama mata wasu ayyuka,a rayuwarta tana bala'in tausayin uammansu,tunda ta taso ta sameta ne cikin haquri da rayuwa,haquri da halin duniya,haquri da mutanen da take mu'amala dasu,mutanen da take jin dadinsu dai dai kune,wata irin bahaguwar rayuwa mara dadi,wadda babu wata walwala ko nishadi a cikinta ko kadan.




Sama sama take jiyo sallama daga tsakar gidan nasu,tana jin ummansu dake duqe can bakin magangara tana wanke kwanukan abinci tana amsa gaisuwar da akeyi mata,saidai kaltum din bata dauki muryar ko wacece ba,sai taja tsaki,ta gayara kwanciyarta,tana fatan ba 'yan dubiya bane.



Ita ko daya dubiyar da aka dinga zuwa din nafa burgeta ba,saboda magi akasarin mutanen da suka shigo din babu wani abu dake hadasu da ita,wasu ko gaisuwa bata shiga tsakaninsu,wasunsu ma bata gama wayewa da fuskarsu ba,saboda tun asali ita din bame shige shige bace,koda yaushe tana maqale jikin ummanta,tana da ƙawa zuci da kuma ƙulafucin uwa,kuma kusan duka haka yaran umman tasu take,saboda itadin macace mai tausasawa ga yaranta,ta iya bi da damuwar kowannensu.




Tsaiwa taji anyi daga bakin qofar dakin ana cire takalmi kafin daha bisani ayi sallama a shigo ciki,sai a sannan ta daga kanta tana duban me shigowar,lantana ce,mamaki yadan kama kaltum,saboda lantanar bata tana shigowa gidansu a irin wannan lokaci ba,dole ta miqe daga lullubar da tayi da wani tsohon xaninta data maida abun rufa tana amsa sallamar lantana.


Gefan kaltum din ta qaraso,tana zama tana furta kalmar
"Sannu kattume" dan murmusawa tayi cikin qarfin hali,saboda sam batajin murmushin a zuciyarta


"Yauwa lantana"


"Yaya jikin naki?" Lantana ta tambayeta


"Alhamdulillahi,da sauqi"


"To Allah ya rufa asiri"


"Amin lantana,na gode" kaltum ta amsa mata.




Shuru ne ya biyo baya,cikinsu babu wanda yace wani abu,daga bisani lantanar ta sauke ajiyar zuciya


"Waime ya hadaki da munzali yayi miki irin wannan dukan kaltume?" Lantana ta fada fuskarta qunshe da alhini da damuwa.


Ajiyar zuciya kaltum ta saki,tana jin zafin irin yadda ya munzalin yayi mata bainar jama'a,inda cikin gidansu ne gaban mahaifiyarta ya daketa irin hakan da da sauqi,bata boyewa lantana komai ba ta labarta mata,sai taga lantanar tayi qasa da kai bayan ya dafe kuncinta da hannu daya.


Zuciyar kaltum cike da tamabaya take dubanta,bakinta ya gaza shuru


"Lafiya lantana?" A hankali ta dago ta dubi kaltum


"Don Allah wai me kika yiwa wasila ne a rayuwa me zafi haka data zabi ta saka miki ta wannan hanyar?" Kasa gane kan maganar tayi,saita zabi taci gaba da kallon lantana ko zatayi mata bayani,ganin hakan ya sanya ta gyara zamanta,ta dora dukka idanunta da hakalinta kan kaltum


"A iya sanina a abinda ya faru....na riga wasila zuwa wajen ma,saidai babu yadda zanyi na qwaceki daga hannun munzali,saboda idanunsa sun rufe,kuma wadanda suka fini shekaru ma sunyi sunyi ya bari yaqi.....amma kuma bayan komai ya lafa muna shirin barin wajen......kawai sai wasila ta fara wasu maganganu da suka jawo hankalin mutane kanta,wai ai dama ta gaya miki,ki daina duka abubuwan da kike,saboda ta sani cewa idan wasu sunyi sunci riba,ke din duka zakici hannun 'yan gidanku,yanzu wa gari ya waya?' "kowa dai bai gane abinda take magana a kansa ba,don haka wasu suka takura da tambayarta meke faruwa?,ta fara cewa ita ba za'aji mutuwar sarki a bakinta ba,wasu suka tafi,wasu suka matsantsa saboda sunsan baki da makusanciyar qawa irinta,budar bakin wasila......" Sai kalaman lantana suka tsaya a wajen,tana jin nauyin qarasa gayawa kaltumen abinda ya faru,tana jin nauyi,don ita kanta ba qaramin razana tayi ba dajin labarin da wasilar ta qirqiro cikin qaramin lokaci ba,don har ga Alla sam bata yarda ba,hankalinta bai dauka cewa hakan zata faru ba


"Me tace lantana?" Kaltum ta tambayeta a sanyaye,haka nan tun kafin taji komai taji gabanta yana faduwa.




Daga ido lantana tayi ta dubi kaltum
"Kiyi haquri,ya zama dole ne na gaya miki,tun jiya naso zuwa,amma naga gidan nan ya cika da 'yan gulma,masu zuwa dubiyar qarya......wai cewa tayi cikin shege kikayi,labari yakai kunnen ya munzali,ita kika fara gayawa tace ba ruwanta....babban abun baqincikin shine,duk wanda yazo dubiyar ya biya ta wajen inna laure don tabbatar da gaskiyar lamarin saita bashi tabbaci,ta kuma dora da nata bayanin qanzon kuregen".




Wani irin abu taji yana yamutsawa saman kanta,wani sanyi ya saukar mata tun daga saman kanta har qafafunta,tana daga zaune amma ji take kamar ana dawafi da ita,saita lumshe idanuwanta tana kiran ya Allahu,ya Allahu,tausayinta ya kama lantana,cikin salo na rarrashi tace


"Kada ki damu katume da abinda kikasan baki aikata ba,baki isa ki iyawa mutum ko ki burgeshi ba" sannu a hankali ta bude idanuwanta tana duban lantana


"Tabbas haka yake,na gode lantana da qaunar da kike min saboda Allah,su kuma.....amma babu komai,akwai Allah.....ya ubangiji kana kallo.....Allah kaine shaida" daga haka bata sake cewa komai ba.




Cikin hikima lantana take bata baki har na wasu lokuta kafin tayi mata sallama,bayan ta bata shawarar duk wanda yazo dubiya kada ta sake fita,su qaraci gulmarsu su koma.




Ita kadai cikin dakin,tana jinta kamar wadda aka haqa rami aka zurata iya wuya,labarin da lantana tazo mata dashi ke yawo a kanta,sai data fada din sannan ta tuna irin yadda duk wanda ya shigo yake mata wani kallo da bata fahimci dalilin yinsa ba sai yanzu,qwalla ce ta silalo mata duk da yadda take qoqarin riqeta,ta kuma sanya hannunta da sauri tana ta qoqarin shareta sanda taji ummansu na shigowa dakin tana tambayarta bata tashi bane?


"Na tashi ummanmu" dai dai sanda ya daga labulen,dan tsaiwa tayi na sakanni tana kallonta,sai kuma tace


"Ki tashi ki saka ruwan zafi a jikinki,kizo ki sanyawa cikinki wani abun"


"To ummanmu" ta amsa tana qas da kanta tare da yunqurin miqewa.




Rana batayi nisa ba 'yan dubiya suka fara shigowa,a hankali cikin hikima da nutsuwa take karantar duk matar data shigo,saita fara tabbatara da zancan lantana,duk da cewa tayi yunqurin yin zamanta cikin daki taqi fitowa koda anzo,sai kuma wata zuciyar ta gaya mata,yin hakan tamkar tana tabbatar da zargin dake cikin zukatan mutanen,don idan wani ya fahimta.....wani cewa zaiyi da gaske cikin shegen tayi take buya bata son a ganta.




Yadda jama'a ke kallonta yayi bala'in kadata,bata taba tsammanin akwai wani qunci a duniya sama da wanda suka ciki ba sai a wannan karon,dama aminta da qawance yana juyewa ya zama sharri mai girma da nauyi haka?,dama qauna da soyayya tana jirkita ta koma mummunar sakayya irin wannan?,babu wata daqiqa da zata kubce mata ba tare da abun yana mata yawo cikin qwaqwalwarta ba,wai wasilanta?,wasilan da suke kuka tare suyi dariya tare,wasilan da take gayawa sirrinta,wasilan da suke shawara tare,su kashe su kuma bunne tare,to wai shin meta aikata mata data cancanci sakayya mafi muni irin wanna?,tambayar data dinga yiwa kanta da kanta kenan,saidai ta gaza gano amsar tambayar tata.




Sati gida cur tayi tana jinyar jikinta kafin ta warware,a tsahon satin bata ga koda gilmawar mai kama da wasila cikin gidan ba bare ita,sai tarin qawayenta da kullum ke kaw mata zancan abinda wasila keta yamadidi dashi.




Dakatar dasu tayi,ta kuma shaida musu batason ji,saboda jin bashi da wani amfani,hakanan babu wani magani da zaiyi mata,face baqin wasila da zata dinga gani.




Randa ta cika satin misalin sha daya na rana,tana tsakar gida tana tsince musu busashshen zogale da suke shirin yin miyar zogale ayau din,cikin shinkafar da yakumbo indo ta ajjiyr musu,har zuwa yau kuma suke amfanarta.




Alamun sauti kamar na kuka datake jiyowa kamar daga nesa kadan da inda take yasa

Please Login or Register in order to submit comment