Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fara cika saboda rashin kyakkyawar magudanar ruwa,tsaki samir din yaja yana kallon yadda titi ya shafe da ruwa,ya rasa aikin me gwamnati keyi?,ruwa a saman titi kamar layukan unguwanni?" Baka bambace titi da kwata?,yana daya daga cikin abinda yasa ya tsani siyasa iyaka kenan,babu komai cikinta sai yaudara da daukan alqawuran dako kusa ko alama basa iya cika koda kaso daya cikin ukunsu.


Ji yayi bazai iya ci gaba da tuqin ba,don baisan yadda zai tadda unguwarsu ya dikkon ba,bugu da qari ma ya tabbatar idan yaje zaiyi horn ne ya taso me gadin da a yanzu yake cikin dakinsa ya samawa kansa mafaka daga dukan ruwan saman,wannan tunanin yasa ya gangara a hankali hannun da yake tuqi qofar wani katafaren guest in,ba tare daya tuna inda zai ajjiye kaltum din ba.


Umarnin fitowa yayi mata bayan ya bude mata murfin motar,ta fito a hankali tana sake hade jikinta waje guda,saiya saka hannunsa saman daya kafadartata ya janyota zuwa jikinsa,abinda ya rage mata dukan ruwan,saidai kuma hakan da yayi mata tamkar ya sake jefa abun fashewa ne cikin zuciyarta,ta dinga sauke qaramar ajiyar zuciya a hankali.


Da tarba ta mutunci receptionist din ya karbeshi,ya buqaci daki biyu


"Saidai kayi haquri yallabai idan babu damuwa kuyi squatting a daki daya,babu dakuna sai wannan da ka karba yanzu guda biyun da suke ba kowa a ciki gyara ake musu,babu damar iya zama a ciki"


"Ba matsala" ya fada a hankali.


Sai daya bude mata dakin ta shiga sannan taga ya sake fita ya dawo bada jimawa ba,hannunsa dauke da wani irin akwati dan qarami me dauke da tambarin wani store,wanda manyan customers dinsu da sukayi siyaya da yawa ko me manyan kudi suke zubawa kaya a ciki.


Tana daga zaunen ya kunna heater din dakin,ya rage haske qwayayen,sannan kuma ya kunna water heater ta bandaki ya shige bayan ya tara ruwa me zafi sosai.


Har sanda ya murda qofar toilet din ya fito tana zaune a wajen jikinta a hade,duk da dumi ya fara ratsata,saidai hankalinta ya rabu biyu,ta yaya zasu kwana a dakin nan daga ita saishi?,me zata cewa jawahir idan ta tambayeta ina sukaje?,zatace mata ne sun kwana tare bayan babu wanda yasan alaqarsu?.


"Ki cire wadan nan kayan kafin sanyi ya kamaki,ki shiga toilet ki dumama jikinki da ruwan zafi" ya fada sanda yake fitowa daga toilet din sanye da sabuwar rigar wanka ta towel har qasa me budadden qirji,abinda ya bayyana tarin sumar dake kwance a qirjinsa baqa sosai mai kuma santsi.


Numfashinta ta dauke gaba daya tana sake qanqame jikinta,ruwan da yayi wanka ya sanya kowacce suma ta jikinsa kwanciya,hatta da qawataccen sajen fuskarsa mai kama da qasumba,saidai baikai qasumba fadi da cika ba.


Wani abu ta hadiye,cikin dakiya tace


"Da zaka qarasa dani gida....saboda su jawahir....." Kasa qarasawa tayi saboda ji da tayi a jikinta ita ya zubawa ido,ilai kuwa haka ne,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,yana da tabbacin batasan waye samir ba,wannan rayuwar ba irin waddanya fasaltawa kansa ko yake sha'awarta bace,inda tazo masa a matsayin matar aurensa da suka fahimci juna,duniya tasan da aurensu da ba wannan zancan ake ba a yanzu,kwata kwata wannan ba irin rayuwar auren daya tanadarwa kansa bace,saidai akwai wani qwaqqwaran bond da yakejin yana son gilmawa a tsakani,duk da haka aure duka aure ne,zai tunasar da ita abinda takeson mantawa,duk da cewa baison ya wuce gona da iri,saboda yanajin cewa gaba kadan xai bata dukkanin zabi ne.


Batasan ya tsaya a gabanta ba sai da idanunta suka dauka kam xara zaran yatsun qafarsa da gashin ke kan kowanne dan yatsa ke akwance shima,kafin tayi wani motsi ya kama dukka kafadunta ya dagata,sai ya saka hannu ya zare hiraminsa ya aje gefe,jawota yayi jikinsa ya mata sasssuqar runguma,abinda ya kusa sanyata daukewar numfashinta kenan saboda jikinta daya gogi nashi,shi dinma yaji,amma ya dake,yanason ya mata tuni ne kan abinda ta manta,saiya kama zip din rigarta ya saukeshi qasa gaba daya,duk da cewa a iya nata qarfin fa cukuikuye rigar a jikinta amma hakan bai hanashi sabule mata ita ba ya hada harda bra dinta,adalci daya yayi mata tana jikinsa bazai iya kallonta ba saidai duk wata fata ta jikinta da hannunsa ya taba yana jin aiken saqo zuwa kowanne sashe na jikinsa,sai ya dauko hiramin ya rufa mata,ta kamashi kuwa tsam ta riqe tana sake lullube jikinta,ko ina na jikin nata yana rawa,qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba


"Akwai ruwa me zafi kije kiyi wanka kixo ki kwanta,idan sun tambayeki gobe,kina iya gaya musu mijinki kika biyo,naki da zunubi ko dis a wajen Allah" ya fada yana juya mata baya yana takawa zuwa gaban madubin dake fuskantosu,saidai yana iya hangenta ta madubin sanda take takawa da sauri kamar zata fadi ta durfafi bandaki.


Ta dade a tsaye tana haki tare da sauke numfashi,gaba daya ya aza mata wani irin nauyi da tsoro,bata taba kawo haka a tsakaninsu ba,duk da cewa tana jin abubuwa masu yawa dangane dashi cikin zuciyarta.......




*_A WANNAN DAREN_*




Su biyu ne rak zaune cikin dakin,duk da suna saka ran shigowar mutum na uku wato najwa.


A hankali hajiya jidda ke qarewa dakin kallo,tana qiyasta yawan dukiyar da aka sake narkawa dakin,kafin maganar hajiya shuwa ta shiga kunnenta


"Idan bakiyi wasa ba hajiya jidda kwabarki tana dab da tayi ruwa,dava tafiyata ace babu wani ci gaba da aka samu?,saima tarin koma baya dani na hango?,me yasa ba zaki kawo qarshen komai kowa ya huta ba kema ki huta?,tun kafin akai lokacin da zaki dora hannunki aka?" Murmushi mummy ta saki tana duban hajiya shuwa


"Akwai abinda nake jira da dako,banason garin sauri naje na aikata kuskuren da kika kusa aikatawa" murmushi hajiya shuwa ta saki


"Iya gidan nan kadai amma ya isheki amsa ko?" Maida mata murmushinta mummy tayi


"Eh qwarai,saidai akwai banbanci,banajin zan iya qarasawa bigiren da kike kai a yanzu" dariya sosai hajiya shuwa ta saki


"Kijimin mata.....da wanda yaci alade,da kuma wanda yaci mushe meye bambancinsu?"kai mummy ta girgiza


"Banbanci me tarin yawa kuwa,tunda ko banza shi mushe ai yankan Allah ne......".




A hankali najwa taja da baya hannunta riqe da cup din tea data hado da niyyar sha,ta taka kuma zuwa dakin da aka sauketa cikin gidan hajiya shuwa tun bayan zuwansu garin azare,wanda sukaqi zama gidan ya dikko.


Katafaren dakin da sai ka zaci dakin wata hamshsqiyar ne,ranta a bace take duban tvn dake aiki a dakin,duk da cewa bata tvn take ba,hirarsu mummy ke dawo mata,ko daya bataji sun tattauna kan matsalarta ba.




shedan ke dake zafafa mata zuciya,ta fuskanci mummy tana slow ne kan abubuwa da dama,to itakam a yanzu tanajin qarfinta ya kawo,zata shiga nata yaqin,zata aiwatar da abubuwan da mummy ta kasa aiwatarwa,bata jin xata yarda ta amince....tasha dukka wata wahalar karatu saboda cikar buri da muradinta,sannan a qarshe daddy yace taje tayi aiki da kamfanin saraki a qarqashin sarakin?ba zata iya ba,kuma da sake.


Miqewa mummyn tayi tana tattaki gaban hajiya shuwa,maganganun da suka sakeyi suna mata yawo akai,hajiya shuwan kuma na binta da kallo.




Tsayin wasu mintuna mummyn ta dawo gabanta ta tsaya


"Na gamsu da dukka bayanai da hujjojinki,kuma a wannan karon ina ji a jikina zan aiwatar da tunaninki,muga kalar naki takun" kalaman da suka sanya fitar murmushi daga fuskarta hajiya shuwa,ta daga hannu tana jinjinawa mummy.


.


"Ya na ganki ke kadai?,Ina kaltum din?" Hajiya qarama ta tambayi jawahir wadda take fidda kayan jikinta da suka jiqe da ruwan sama.


Tsaiwa tayi da cire kayan,ta ta waiwayo ta dubi hajiya qarama


"Sun rigamu fitowa fa,basu iso ba kenan?"


"Nidai babu wanda na gani a cikinsu"


"Ok,bari na gama na kira ya sarakin" ta fadi tana dauko kayan da zata sauya din masu dan kauri saboda sanyin ruwan da ya ratsata,sai data gama shiryawa sannan ta zauna ta soma kiransa.


Tana shiga amma ba'a dagawa,already ya sanyata a silent ne,kaltum dake duqunqune cikin bargo tana sheqar lallausan qamshin turarensa daya kama kayansa tana iya hango hasken wayar saboda a saman kanta take a ajjiiye,saidai batason yin magana kwata kwata,tafison ya dauka tayi baccin ne kamar yadda ga zata,tun sanda ya bata rigarsa ta sanya kunya da nauyi suka cikata,saboda barin nata kayan da yayi cikin mota.


Shafa addu'arsa yayi a hankali,sannan yaja bargon daya dora saman dogayen qafafunsa ya dawo zuwa qugunsa,sannan ya zame a hankali ya kwanta a hannunsa na dama.


A hankali ya lumshe idanunsa kana ya budesu,idanunsa suka sauka a bayanta,duk da cewa baya iya hango komai na jikinta sai bargon data duqunquna har kanta da shi.


Wani numfashi mai nauyi ya sauke,yanayi irin wannan yana saukar masa da feelings sosai tun ba yanzu ba,qamshin qasa hade da sassanyar iskar damina ta dare,saiya sanya hannayensa tsakiyar gwiwoyinsa kamar maijin sanyi,haka kawai kasancewarta kusa dashi ke neman dagula lissafinsa,tsahon rayuwarsa wannan shine karo na farko daya taba hada makwanci da diya mace,yaso ya barta ta kwana a qasa kamar yadda ta zaba,saidai kuma yaga hakan bai dace ba,duba da sanyin ruwan dake sauka,ga kuma tiles da ya yiwa dakin qawanya.


Hasken wayar ya hango,wanda ya bayyana bayan walqawar walqiya a sararin samaniya,walqiyar data sanya kaltum runtse ido sosai da kuma curewa waje guda tana addu'a qasan ranta,kan Allah yasa ba tsawa za'a saki ba.


Hannu ya miqa ta saman kanta zai janyo wayar,dai dai sanda qarar tartsatsin walqiya mai qarfi ya baje a fadin duniya ya sauka zuwa kunnen kowanne abu me rai dake sararin subhana.


"Alhamdulillahil lazi yusabbihur ra'adu bi hamdih,wal mala'ikatu min khifatihi" saraki ya fada a hankali yana dan runtse ido saboda qarar tsawar,sannan ya bude idanun nasa a hankali ya sauke a kanta.


Baiyi tsammanin cewa batayi bacci ba saida aka saki tsawar yaji yanda ta firgita,har kuma bayan shudewr tsawar yana iya jin yadda ta sake tattarewa waje daya,bai fasa dauko wayar ba,ya budeta ya shiga app din karatun qur'ani,qira'ar shaik abdur rahmani assudais,ya kunna suratul baqra,ya sanya volume dinta saisa saisa (indai har zaki iya kwana da waya saman kanki bayan kin gama danne dannenki,to yana da kyau ki koyi sanya karatun qur'ani cikin dakinki sanda zaki kwanta bacci,cikin qaramin volume ba mai yawa ba,hakan yana taimakawa wajen yin bacci me dadi mai kuma cike da nutsuwa,uwa uba ga tsaro da zaya baki daga dukkan sharri,koda bunu chargy indai akwai wuta,jonata a socket,ki kunna qur'anin,yana playing tana chargy,zaki mamakin yadda wayarki zata cika da wuri,ga kuma qur'anin yana yi har safiya,koda chargynki ya kusa qarewa kika kunna,wani hukuncin Allah wayar bata mutuwa,tana kaiwa har safiya yanayi,Allah ya bamu albarkacin qur'ani mai girma,alfarmar shugaba S A W👏🏽👏🏽).



Saman kansu ya sanya wayar,ya raba a hankali zuwa bayanta ya kwantar da jikinsa,idanunta ta lumshe gaba daya zuciyarta ta soma gudu yadda ta saba a duk sanda ya rabota....lokacin data jishi cikin bargon da take,hannunsa saman ruwan cikinta,muryarsa can qasa kamar meyin rada yana cewa


"You are safe..... good night" cikin son yin aiki da maganarsa ta rufe idonta a hankali tana sauke numfashi,dumin kowanne na ratsa dan uwansa yana haifar masa da wani yanayi na daban.........


_to sai ince asuba ta gari kalsam_




53
DZ




"Ina hanya,yanzu zamu iso,koma meye idan nazo ka tambaya" abunda ya fada kenan sanda yake jingine da motarsa a farfajiyar gidan saukar baqin,saiya latse wayar kawai sanda yaji amirun nason masa cari,ya soma sanya wayar a aljihun wandon shaddarsa,lokaci guda kuma yana daga kansa.


A kanta idanunsa suka sauka,tana sanya da atamfa riga da zani,sai mayafi wanda yayi matuqar dacewa da kayan jikinta.


Kyakkyawar kalar fatarta ta haska tarwai cikin kalolin kayan jkinta,kwantaccen gashinta me santsi ya fiti ta gefe da gefan kunnenta,da kuma qeyarta inda ta nadeshi kamar alkaki.


Baisan sanda ajiyar zuciya ta kubce masa ba,yana tuna yadda hannunsa ya dinga yawo a jikinta daren jiya cikin mafarkinsa,wani abu ya tsarga masa sanda ta daga fararen idanunta suka sauka akansa,saiya sanya hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana qyara tsaiwarshi da kyau.


Faduwar gaba taji sosai,karon farko data ganshi da shigar da bata taba ganinsa da ita ba,shigar shadda fara sol sai maiqo da walqiya takeyi,wadda akayi mata aikin zare baqi,takalmi sau ciki wanda shima yake nashi kalar qyallin,hannunsa sanye da Rolex me asalin tsadan,sumar kanshi wadda bata da wani yawa sai sheqi takeyi saboda hularshi dake aje saman motar bai sanya ba.


Hardewa taji ta fara yi saboda takalman qafarta masu dan tsinin dunduniya da sukayi mata kyau suka kuma sake qawata kwalliyarta.


Tana dab da isowa inda yake ya sanya hannunsa saman motar ya.janyo hularsa ya aza a kansa,har a sannan bai fasa kallonta ba.


"Kinyi kyau" kalmar data subuce masa a bakinsa kamar fitar kibiya,hakan ya qara aza mata nauyinsa.


A hankali ya kutsa da motar cikin layin gidan ya dikko,duk kuwa da saurin da ya dinga yi amma hakan baisa ya iso a sanda yaso ba,saboda wani laziness da yakeji a jikinsa gaba daya,a hankali ya dannan wani madanni dake gefansa ya dage dukka gilasan motar sama sanda yake yiwa motar gun tsaiwa,hannu tasa zata bude motar


"Wait" taji ya fada,hakan yasa ta tsaya din kamar yadda ya buqata,ta qagauta ne su raba jaha,don ita kadai tasan wanne yanayi take riskar kanta a ciki duk sanda suka kadaice irin haka,wani mugun nauyi da kunyarsa takeji fiye da kowanne lokaci.


Wayarsa ya ciro ya dannan numbers din jawahir, ringing biyu ta daga,zata barke masa da surutun nan nata ya dakatar da ita,yace ta fito ya sameshi a waje,sannan ya aje wayar .


Daga nesa ya hangi fitowarta,tayi duru duru tana nemansu,saiya dan danna mata horn sannan ya bude motar ya fita,dai dai nan ta iso,saiya dan saka kansa kadan yace da kaltum din ta fito.


"Wai a ina kuka kwana kaltum?" Ta tambayi kaltum din cikin mamaki da kokwanto,saidai kafin tace komai samir din ya tsaidata


"Ba'a sani ba tambaya,ku wuce muje" bata qara tambayar ba,saidai tana mata susa a rai,tare da tambayar kanta inda sukaje suka kwana,kuma su biyu,ba muharraman juna ba,duk da cewa ta yarda da hali da dabi'ar yayan nata,dama ta kaltum din.


Suna gaba yana biye dasu a baya,duk da jama'a na tsaidashi suna gaisawa,duk inda ya wulga sai ya dauki hankalin jama'a,farinji da kwarjini gareshi,uwa uba yadda yake kyautatawa al'umma ya siya masa soyayyar jama'a me yawan gaske,a haka suka isa babban falon yadikko,wanda yalwar gidan da wadatar guraren zama ya sanya babu yawaitar mutane,kusan suna dakuna......


"A ina kika samo wannan beb din......ban santa ba a cikin danginmu" daya daga cikin samarin dake xaune a falon ya fada,abinda kuma kunnuwan samir suka jiye masa sanda yake shigowa,idonsa ya sauka kan yaron wanda ake kira da muntasir.


Sallamarsa yasa maganar da yake shirin yi ta yanke,duka suka waiwaya,sannan suka miqe cikin nuna girmamawa suna masa sannu da zuwa kafin su fara gaidashi.


Fuskarsa a hade tsam ya kalli jawahir


"Ina mummy?"


"A gidan haj shuwa ta kwana,amma munyi waya tace min ta taho,duk yadda akayi ta kusan qarasowa" ido ya lumshe kana ya bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,haka kawai cikin zuciyarsa jininsa baya son matar,kuma bazai iya tuna wani laifi data taba yi masa ba,koda na kallon banza kuwa


"Ki rakata wajen hajiya qarama"


"To" ta amsa masa tana yin gaba,kaltum tabi bayanta,saiya tsinci kansa da rakasu da ido.


Muntasir ya tabo dan uwansa


"Kaga guy din nan,ashe shima ya iya kallon mata?" Boyayyar dariyar ciki ya sake


"Waye baison mace dama?,aisu sunfi qarfin zuciya da qwaqwalwar kowa,saidai idan bai samu ba,bare wannan....ta wanku fa,kalar fatarta ta musammance wlh,ga wani kyau mai sanyi alaji,wanda saita matsoka kake ganinsa",dif sukayi sanda ya waiwayo ya dubesu,don kalamansu na qarshe sun shiga kunnensa,baisan me yake taba zuciyarsa ba duk sanda sukayi magana irin wanann,dukansu ba sa'ansa a cikinsu,don haka ya miqe ya nufi bangaren dakin ya dikko don su gaisa,tun kafin daddy ya qaraso yaji basu gaisa din ba.


Fara'a fal fuskar hajiya qarama,farincikin ganin kaltum ya bayyana sosai


"Lale maraba da diyata,ina nan inata kewarki,dama yanzu nake shirin kiran saraki naji can gidan abokin nasa zaku yita zama ne?,sai amirun yacemin matar abokince bata jin dadi sosai,kin dan tsaya kin taimaka mata ta kintsa gidan" itadai murmushi kawai take,kanta a qasa tana jinjina yadda amiru ya iya tsara irin wannan qaryar,duk da tayi mata dai dai,don bata da kowacce amsa da xata bata.




"bari naje mu qarasa packaging abincin 'yan daurin aure.....ina zuwa kaltum" ta fada tana juyawa gami da ficewa daga dakin,zuciyarta dai na tantamar labarin da amiru ya bawa haj qaraman kan rashin kwanansu gida,tunda a gabanta ne yake neman shima inda suka shiga,ture batun tayi,sabida batason baiwa shaidan qofa akansu,ta yarda da kowa a cikinsu.




Sai data zauna sosai sannan ta daga kai da niyyar gaida hajiya qarama,saidai gaisuwar taso.maqale mata a maqogaro,saboda sauka da idanunta sukayi kan wani hoto dake maqale a bangon dakin da yake tamkar na hajiya qaraman,saboda duk sanda tafiya ta kawosu azare a nan take sauka,idan zata tafi kuma ta rufe ta bawa ya dikko maqullin.




Hoto ne dauke da taswirar fuskar matar dake a jikin hoton data taho dashi zuwa azare,wanda tayi masa duban duniya amma ta rasa inda ta yada shi,gabansa kadan wani hoton ne irinsa,tana sanye da atamfa da akayi mata riga da xani,ta yane jikinta da mayafin atamfar,wadda ta haskata ta kuma fidda kyanta sosai.


Tattaro kalaman bakinta tayi tana gaida hajiya qarama,amsa mata tayi tana waiwaya bayanta don duba abindan ya dauki hankalin kaltum din haka,sai taga hotunan,hotunan da a kullum idan ta kallesu sai taji wani abu mai qarfi ya motsa mata,takan ji karyewa zuciya qwarai,har yau zuciyarta ta kasa gasgata abinda aka fada akan raihana,har yau ta kasa jin nutsuwa da kalaman da akayi a kanta,har yau zuciyarta tana gaya mata cewa tana raye.


"Suna kama ne da samir?" Hajiya qarama tayi mata tambayar tana murmushi gami da duban fuskar kaltum,maganar hajiya qarama ya sanyata janye idanunta daga kan hoton,murmushi yana subucewa daga fuskarta ta girgiza kai gami da saukar da kan nata qasa.


Shuru ne ya ratsa dakin na wasu sakanni kamar ba kowa a dakin,ajiyar zuciyar da haj qarama ta sauke yasa kaltum kallonta,suka hada ido,sai hajiya qaraman fa gyara zamanta


"Shekara kusan ashirin da takwas,amma har yau zuciyata ta kasa gasgata bacewar raihana.....wadda ta bace rana tsaka,sama ko qasa,a lokacin samir nada shekara biyar a duniya,bayan ana tsaka da wata hatsaniya,ba'a gama kamo bakin zaren ba,a yadda jidda tace.....a gaban samir akayi,tace ne ta gaji da zama da rashid,dama kara take mishi,ita ba sa'ar aurensa bace,akwai maza da yawa dama dake dakon fitowarta,ta bashi wata wasiqa data tabbatar da dukka abinda ta fadi cewa raihana tace,kuma tabbas kowa yasan rubutun na raihana ne,hatta da 'yan uwanta sun tabbatar da hakan.


Hatsaniyar da ake tsaka da yi da kuma wannan abun daya faru ya haifar da gagarumar tsanar raihana a zuciyar rashid,abinda yasa ya karkade hannunsa daga batun nemanta,wannan ne kuma ya hasala danginta,wadanda 'yan asalin qasar sudan ne,sukaga koba komai ai matarsa ce,kuma shine silar zuwanta qasar nan,bugu da qari su basu da ido a nigeria,shine zai shige musu gaba waje batun neman raihana,amma ya qeqasa qasa yaqi,yace dama can yana da hujjojin dake nuna cewa ita din bibiyar maza take,haquri yayi da ita,maimakon ya zauna a duba matsalar batanta,sai saki da ya rubuta mata ya baiwa 'yan uwanta takardar,yace idan sun ganta su wuce da ita qasarsu" shuru hajiya qarama tayi tana sauke numfashi,da alama har kwanan gobe abun yana tabata bai wanke daga zuciyarta ba,yayin data jefa kaltum cikin zuzzurfan tunani.


"Tun kawo raihana qasar nan babu wanda ta shaqu dashi irina,hasalima a sannan tare muka qarasa karatu ni da ita,bani da aminiya kamarta saboda mu biyu mahaifiyarmu ta haifa,kamar yadda nima ta maidani 'yar uwarta,a sannan ina gidana,ni naso karbar baquncin dangin raihana da suka shiga nemanta babu ji babu gani,amma saboda fusatar da sukayi sukaqi sauka,suka kama hotel.....lamarin da yayi matuqar girgiza mu shine,iyakar nema me sunan nema mun yiwa raihana amma babu ita babu dalilinta,cigiya kafafen yada labarai babu inda ba'a kai ba shuru maqatau,yan uwanta sun share watanni suna nema amma babu nasara,har suka koma qasarsu suna zuwa lokaci bayan lokaci amma har yau da nake baki labarin nan babu labarinta,wannan daliline yasa muka saddaqar cewa an sace raihana ne an kuma kasheta,amma inda tana raye ko da bata kawo kanta ba yadda cigiyarta ta watsu a na qasar dama waje....ba shakka ba za'a rasa wanda zai kawo rahoton ganinta a wani waje ba...."




Yan uwa raihana sun jima da sarewa,sunma tattara sun bar koda leqo qasar nan,lefin rashid ya sanya suka daina koda waiwayar samir,wanda shima bansan dalilin daya sanya tun tashinsa bai sha'awar yaje dangin mahaifiyarsa ba,tun ina masa maganar lokaci bayan lokaci nima harna haqura na qyale.....tabbas jikina har yau yana bani jidda tana da hannu kan bacewa da mutuwar raihana,har yanzu na kasa jin qaunarta a raina....kuma zuciyata ta kasa gamsuwa da soyayyar da take nunawa samir" maganar hajiya qaraman ta katse,da alama tana hadiyar dacin daya taso mata ne.


Dubanta kaltum keyi,itama tana jin wani abu cikin zuciyarta,tana kuma sake kallom hoton dake maqale,ba shakka itace a jikin hoton biba data dauko,to meye alaqar biba da mahaifiyar samir din?,meye haka yayi tasiri a ran samir daya sanya ya nesanta da dangin mamarshi?,meye alaqar matar dake gidan masu lalurar hankali da wannan matar?,tabbas akwai kamanni a tsakaninsu,saidai akwai wasi banbamce banbamce kuma data kasa ganesu,meye alaqarta da mummy harta ziyarceta a wanacan lokacin?.


"Na jima banyi wannan maganar da wani ba sai ke kaltum,bansan me yasa ba hakanan naji ina sha'awar baki wannan labarin,qila zaki tayamu da addu'a,addu'ar da har kullum mu masoya raihana mukeyi,kan koda kabarinta ne Allah ya nuna mana shi" qas tayi da kanta tana jin tunaninta na hautsinawa,yana son hada mata fuskokin nan uku waje daya


"Allah ya shiga lamarin?"


"Amin don nabiyyur rahmati" hajiya qarama ta amsa tana janyo wayarta,yayin da kaltum taci gaba da son daidaita makamar wadan nan zantukan da dukka hasashen zuciyarta a mizani guda,yadda zasu bata cikakken bayanin da take so.


"To ya rashid kodai suna hanya har yanzu bai qaraso ba?,gashi an kusa fara daurin auren,kuma wayarshi a kashe" hajiya qarama tayi maganar tana sauke wayar daga kunnenta,saita tashi ta na nufar qofar fita daga dakin.


A babban falon ya dikko sukaci karo da mummy,wadda ke keto falon cikin shigar alfarma ta wani baqin material daya haskata sosai,sai sheqin duwatsun da aka masa qawanya dasu yakeyi,tun daga wuyanta zuwa hannunta designers ne na jewelry daketa sheqi suma,bayanta kuma photocopy din tata ce wato najwa biye da ita,tana hura hanci tare da yiwa kowa kallon daya daya,kusan wannan din halayyarta ce,kada ma taga 'yan son zuciya da neman gindi zama....hadi da masu ganin kimar mummyn saboda yawan kyautarta na miqa gaisuwa da girmamawa.




Cikin salon nan nata da koda yaushe take amfani da shi wato fara'a da sakin fuska take amsawa kowa,kafin ta maida hankalinta ga hajiya qarama ta soma gaidata,ba tare data damu da cewa ita dince matar yaya ba,ita ya kamata ta gaida.


Kamar ko yaushe ta amsa mata babu yabo ba fallasa,tayi gaba zuwa dakin ya dikko,mummyn na biye da ita a baya.


Tsohuwa ce sosai,don gaba daya kanta ya cika da furfura,saidai kuma yadda tayi quruciya me cike da nagarta da bin Alla sai tsufan nata yaxo mata da kyau,bata rasa baqora ba kamar yadda bata rasa hankalinta ba,hannu biyu ta karbi mummy kamar ko yaushe,saboda yadda mummyn ta maidata,kamar itace ta tsugunna ta haifi professor rashid.


Hajiya qarama na daga gefe tana ta gwada wayar professor din amma still dai taqi shiga,saboda sun riga da sunyi magana da ita kan cewar,zai iso nan da awa biyu ne,akwai ganawar da zasuyi shi da ita da ya dikko kan auren samir.


Tsaki ta danja sai duka suka kalleta


"Ya dikko na kasa samun yaya rashid,bansan ko matsalar network bane irin na qasar nan"


"Muna daya ashe,nima tunda na fito daga gidan hajiya shuwa nake gwada kiran nasa amma ban sameshi ba" mummy ta fada fuskarta na nuna damuwa,ajiyar zuciya hajiya qarama ta saki,ta duba agogo


"Amma yaci ace ma ya qaraso,indai ba fasa zuwan yayi ba"


"To Allah yasa lafiya" yadikko ta fada


"Ameen" duka suka amsa a kusan tare.


Ba kasafai ta fiya zama waje daya ita da mummy ba,amma wannan karon sai ta kasa tashi,taci gaba da zama a wajen.


Turo qofar da akayi ya sanyasu daga kai,kowa ya bawa qofar hankalinsa.




Please Login or Register in order to submit comment