Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu abubuwan,sannan yusufa ma ni yace babu matsala,koshi xaya yimun kayan daki,don shi a nan kurkusa yakeso ayi komai" daga haka ta janyo.ledar ta bude,awara ce mai zafi mai uban yawa,sai qunshin tsire,sai rake wanda aka gyarashi fes,aka yankashi qananu
"Kinga abinda ya kawomin" ta fada tana turawa kaltum ledar,kalla kawai tayi,saita saki murmushi tace
"An gode" yusufa yana da qoqari,yana kuma da hannun kyauta,hakanan yana da kirki kamar yadda ake cewa mamansa ma haka take,sosai kaltume ke yiwa habiba sha'awar aurensa,a yadda kowa ke yabon halayyarsa,tana sanya mata ran cewa zata dace da gidan aure in sha Allahu.




Matsantawa kaltum tayi,har sai data raba abun kashi hudu,nata dana umma dana kaltum din saina bilal,basuyi tunanin su raba da baban ba sam,saboda sun riga sunsan halayyarsa,yanzu akan wannan sai qilu ta jawo bau.


*******


Karfe biyu da minti talatin da uku na azahar ta dage labulen dakin ummansu,wadda suke ciki ita da habiba sunata sauke kayan kwalla na mahaifiyar tasu,da tayi shawarar gwara ta saukesu ta saidasu tun yanzu saboda bikinsu,tunda ba wani abu suke tsinana mata ba
"Umma na gama zan tafi"
"To Allah ya kiyaye,kina gama mata ki dawo gida,kada babanku ya rigaki dawowa"
"In sha Allahu umma bazan zauna ba"
"Saikin dawo yaya" habiba ta fada,ta amsa mata tana sauke labulen kana ta doshi qofar fita daga gidan.




A farfajiyar data hada sassan nasu ta samu baabar asiya da suke kira da baaba laure,a zaune saman tabarma,qaqashin inuwar bishiyar data baza rassanta a filin tsakar gidan,da alama sassan nata ya dauki zafi,da yake shi rana yake kallo,hatta da rumfar dake sashen idan rana ta take zafi take dauka,a nan kawai suke xama su samu iska da inuwa mai kyau,sabanin nasu sashen,da ya bawa rana baya,saidai dakunansu kawai su dauki zafin,amma banda tsakar gidansu,duk da cewar tun asali kowa a muhallinsa yake a zaune,amma baba laure sai data qalubalanci hakan,tace anyi ne da gayya ana sane aka bata nan din,saboda rana tayi mata lahani ita da yaranta.




"Yar baqa mayya" taji baba lauren ta ambata,ta sani sarai da ita take,ta tsani sunan iyaka,kuma ita ta sanya mata shi,duk sanda ta tashi taji 'yan wulaqancinta a kusa haka take kiranta,tasha ce mata
"Baba laure,ba suna bane me kyau,malam na makarantar asuba yace babu kyau mu dinga kiran junanmu da laqabi mummuna fa" saita rafka salati,tace tana son kiranta da jahila,ita zata yiwa kiɗifiri da iyayin banza da wofi,suna ne tun tana tatsitsiyarta ba xata fasa kiranta dashi ba,takan qara da cewa
"Wannan inda kinyi karatun boko Allah ne kadai masanin abinda zaki dinga yi,to sai Allah yasa wadanda ba'a so din su sukayi bokon,kuma sha maka Allahu su zasu zama madubin gidan nan,ehe" baba laure wata irin macace mai.matuqar son kanta,da son 'ya'ya,son 'ya'yan ma har yayi mata yawa,itafa duk duniya yaranta sune kawai 'ya'ya,na kowa ma ya mutu,nata ya rayu,tunda ta taba zuwa cikin gari,taga yadda ake karatun boko,gidan da taje gidan qanwar qawarta ne data haihu,taga yadda suke karatun boko,taga manyan yaran gidan yadda suke,akace mata kowanne ma'aikacine,kuma boko sukayi,shikenan tunda ta dawo ta tasa baba iliya a gaba,ta dinga shirya masa zance,tare da nusar dashi romo da amfanin karatun boko,babu jinkiri ya gamsu,ya kuma yarda,suka ganganda dukkanin kudadensu suka tasamma sanya yaransu a makarantar boko ta cikin gari.




Tun ba'aje ko ina ba suka ga ba zasu iya ba,basu da sauran zabi illa su dawo dasu makarantar boko ta cikin qauyen,wadda a qalla shekara ashirin da wani abu da ginata,fiye da rabin ginin makarantar ya zube,a qarqashin biyu suke karatun,nan fa manyan yaranta maza guda biyu,munzali da muxammilu suka ce sufa ba zasuyi ba,a barsu kawai suje kudu neman kudi,juyin duniya sukaqi fafur,dole ta haqura,saita karkatar da akalar burin nata zuwa kan babbar diyarta mace wato asiya,burinta shine asiyan ta zama wata tauraruwa kuma ta musamman abar kwatance akaf fadin karkarar tasu,a lokacin da suna qananunsu,idan kowa yana fadin abinda yake sha'awar yi ko xama tsakaninsu kaltum da asiyan,idan kaltum tace zane takeso,kuma fannin zane zane takeson karanta,baba laure kan karkace tayita ɓaɓɓaka dariya,babu ma sanda taji ummansu na cewa
"To Allah yasa,Allah yasa ya zame miki alkhairi", takan ce
" ban taba ganin mutane marasa sa'a a rayuwa ba irin zuwaira da yaranta,komai.naku ku a cabe yake zuwa?,banda tohewar basira me za'ayi da wani zane?,zanen 'yan aljanu fa?tabdi,da alama a haka zaku qare ko,ni ai asiyata babu abinda ya dace da ita sai karatun aikin banki gidan kudi,ko karatun inda za'a dinga haqo man fetur,tunda ance shima abune mai daraja"umman bata taba daga kanta dai dai da rana daya ta dubeta kota dubin maganganunta ba,ko sau daya ita wannan baya a lissafinta,addu'arta.....burinta dare da rana shine su samu mazajen aure na gari,shine tabbas!.....shine dahir!....dahir din da babu gaibu a cikinsa.




Saidai abu daya da baba laure ta kasa fahimta,ta kuma kasa yiwa tufkar hanci,asiya tun tana qaramarta yarinyace maras kunya,bata da kunya ko qanqani,fadace fadace kullum yinsa akeyi da ita,dambe da maza ba sabon abu bane a wajenta,babu wanda take kunya ko tsoro,manyance a wajenta abun ba'a magana,maganganu kuwa idan tayisu saika dauka.macen aurenta ne,a sannan ana ganin a bakin mahaifiyarta da bata da kintsi take jinsu,musamman idan tayi baqi suna hirarsu,tun ana kallon abun a matsayin quruciya da tunanin zata daina,harya zame mata jiki,ta girma ta tashi a haka,sannu sannu kuma sai dabi'ar kwadayi ta shigi asiyan,wanda buri da son rayuwar jin dadi....da kuma son ganin ta kerewa duk wata sa'arta cikin qauyen suka haifar mata da hakan,dalilin kenan da ya sanya ta duqufa karatunta,duk da cewa bata da wata basira ko qwaqwalwa,idan kaga yadda take sakewa da malamanta,har wani lokaci suna wasan jakai kamar qananun yara xakayi.mamaki,wannan sake musun da takeyi ya sanya ko yaushe ita ce ke zuwa ta daya a ajinsu,don haka ma,saiya zamana bata wani damu da karatun ba,tunda zata zo ta daya,zata nunawa babarta,ita kuwa tayita tiqar rawa tana murna tare da yada habaici,shikenan tana ganin babu wani sauran damuwa,takanje makarantar sanda ta gama yawonta da xuwa duk inda zata,wanda kusan rabi amsar kudi ne daga hannun samari,wadanda saisun gama wasan banxa kamar wani miji da mata sannan su bata.




Ko sau daya baba laure bata taba damuwa da ganin gilmawar kudi a hannun asiya ba,bayan ta sani cewa....ba ita ta bata ba,ba mahaifinta ne ya bata ba,tunda dukkaninsu basu dashi,ba wata sanaa suke ko takeyi ba,amma sam hakan ba damuwarta bane,musamman idan ta tashi buqatar kudi,asiyan zata ranta mata,kota bata kyauta.




A hankali baba lauren ta fahimta samari ne ke yiwa 'yarta hidima,a maimakon shiga tashin hankali a matsayinta na uwa,tsaurara bincike da yanke duk wata alaqa,saita hau murna,ranar kamar zata taka kan shege,ta yiwa yarta kirari a filin tsakar gidan nasu
"Kaga diyar da ba'a haifi kamarta ba kaf fadin qauyen ƊINYA,yarinya mai farinjini tamkar daren sallah,ah....ashe nidai na haifi mai sharen min hawayena ban sani ba,daa na qwallafa raina akan wadancan sakarkarun su muxammilu,wadanda saisunga dama zasu waiwayo gida su bani abinda sukaga dama,Allah ya karemin ke,ya tsole idanun maqiya" dukka wadan nan maganganun ta yisu ne sanda asiyan ta miqa mata danƙwaleliyar gasashshiyar kaza sukutum da guda,da sassanyar fanta,dukkan maganganunta kuma da umma take,wadda ta fito tana kwashe shanyar kayansu da habiba ta manta bata kwashe ba.




Bata ce komai ba sai data gama ta kaisu sassansu sannan ta dawo inda baba laure take,ta yanke gaya mata gaskiya ne saboda girman zumunci da zaman tare,sannan ko banza JININ YARANSU DAYA,ko banza basu isa su cire jinin su asiya daga nasu bilal ba,har abada duniya ba zata daina kiransu da sunan 'YAN UWA BA!,ba tun yau ba,tasha jin gulmammaki akan asiyan da irin abubuwan da takeyi,sai Allah ya nuna mata sau biyu itama,amma bata taba tunkarar baba lauren ba,a tunaninta na kada ta daga mata hankali,tana shawarar kiran asiyan tayi.mata fada sai kuma akayi haka.




Fara nade ledarta tayi ganin tahowar umman,duk da ta sani cewa ita din sam ba makwadaiciya bace,hasalima tana cika da mamakin yadda take da haquri da kuma wadatar zuci,duk da bata da komai,hakanan mijinta baya kula da ita,amma hakan bai sauya dabi'a ko halayyarta ba
"Laure,ni a nawa tunanin,wannan abun da kikayi bashi ya kamata kiyi ba,ke uwace mace,wanda tasan ciwon yaranta,ya kamata ki fara sanin dawa dawa asiya ke tare dasu?,meye alaqar dake tsakaninsu?,idan aurenta suke da niyyar yi....."
"Dakata zuwaira" baba lauren ta tsaidata
"Babu alaqar dake tsakaninsu saita alkhairi,yarinyata kintsatsiya ce,kuma na yarda da tarbiyyarta,don haka kada.kizo min da wani qabli da ba'adi,farinjinin samari ne dai kawai da Allah ya bata,kuma koni ban isa na dakushe ba" saita kwashe kayanta tayi sassanta tana mita,zucuyarta baqiqqirin,kawai gani take babu wani babu wata,baqinciki zuwaira take tsagoransa,tunda ita kaltum kusan duk wanda yazo tafiya yake,habiba kuma a sannan bata tsaiwa da kowa,don tana ganin tayi quruciya,duk da cewa a qauye suke,amma ita tarbiyya idan za'a bada ita,babu alfanun duba yanayin muhalli,a bada ita kawai yadda ya dace,wannan shine abinda ke wakana a tsakaninsu da kalar halayyar asiya da.mahaifiyarta,wanda sannu a hankali abunda asiyan takeyi yake bunqasa ba tare da sanin lauren ba,tunda tun a karon farko taga goyon baya qarara daga mahaifiyartata,babu bincike ko.matsantawa cikin lamuranta,kudi takeso.....kuma tana kawo mata su,shikenan an wuce wajen 👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽.



"Ke 'yar baqa dake nake" baba lauren ta sake fada cikin daga murya,sai kaltum ta dakata,ta waiwayo tana duban baban,ko kafin lauren ta sake samun sukunun yin magana saita jiyo sautin bilal tun daga zaurensu,hakan yaja hankalinta zuwa zauren da hanzari ba tare data sake sauraren lauren ba.




Tabbas bilal ne,ya shigo futu futu dashi kamar wanda aka turbuda a qasa,yana dingisawa yayin da hawaye ke wanke masa fuska.




A rude ta nufeshi ta kama kafadunsa tana kallonsa
"Kai bilal?,meye haka?,lafiya me ya sameka?" Muryarsa a dakushe ya soma magana da qyar
"Su musbahu ne,mun gama aiki an biyamu kudinmu,shine suka ce wai ba zasu raba dani ba,ni kuma nace saboda me,wallahi saisun bani kudina tunda haqqina ne,shine suka taru suka yimin duka,kuma don nace zan tona musu asiri ne,muna kwabin qasa suka kwashe kayan aikin suka boye,wai idan muka gama aikin zasu je su siyar su qara samun yawan kudin aikin" sosai ran kaltum ya baci,ba wanannan ne karon farko da suka fara dukan bilal ba,bama su ba,wasu mutanen da yawa cikin qauyen,saboda suna ganin kamar bashi da wani gata ko galihu,bata iya tanka masa da komai ba ta kamashi suka koma cikin gidan,tana jin baba laure tana dariya
"Oh...aikin qwadago badai wuya ba,toh...mudai namu rabon yana jikin biro da takarda in sha Allahu,daga me yawon qwadago sai me gawon kitse sumar jama'a,suma dake cike da datti da annakiya,kai....itadai zuwaira bata iya haihuwa ba....hhhhhh" ta qarashe da dariyar dake nuna cikar nishadi da farinciki.




Har tasa qafa sashensu saita tsaya cak saboda kalaman da kunnenta suka dauko mata,uwa uba dariya ta biyo baya daga bakin lauren da baquwarta abu,wadda kusan kome ke wanzuwa na samun goyon baya da asiya tayi da shawarar zainabun ce,wadda a kullum ita ke nunwa baba laure 'yarta me sa'a ce,ta barta,kada ta toshe musu kafar samu,duk maganar da mutane zasuyi zallar baqinciki ne,abun ke dorasu akan komai.




Kaltum din zata iya jurewa komai amma banda taba qima da mutuncin mahaifiyarta,taba qimar mahaifiyarta shine abu na qarshe da mutum zai mata,koda kuwa shi waye,don haka saita saki bilal,ta dawo da baya,yayin da laure ta zuba mata idanu zuciyarta cike fal da taraddadin kada kaltum din ta yarfata,tunda tafi kowa sanin halinta kan mahaifiyarta.




Bata tsaya ba kuwa sai data isa gabansu,idanunta cikin na baba lauren ta maida mata amsar data tashi hankalin baba laure
"Ummata itace kuwa ta iya haihuwa,tunda ta haifi tsaftatattun 'ya'ya,babu me yawon bin maza.....babu kuma wanda ta bazama duniyar qabilu da arna neman abun duniya,yaranta na killace gabanta tana qoqarin basu tarbiyya da kulawa,duk da tsananun babunta,don haka babu haihuwar datafi wannan sa'a" saita juya abinta,tana sake dannar zuciyarta,saboda tana jin amsar data bayar dinma kamar bata isa ba,kamar bata isa ta wanke mata hucin da zuciyarta ke fitarwa ba.








06




*Kiji tsoron Allah☝🏽,karka/karki taba haqqin wasu,saboda akwai ranar biya,randa baka da abun biyan🤌🏾*
*KI TUNTUBA WADAN NAN NUMBERS DIN DON SAMUN DAMAR KARANTA NAKI HANKALI KWANCE*


08184017082
KO KUMA
09134848107
____________________________
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_


_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_


_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_


_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_


_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_


https://youtube.com/c/sudaiskura


_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._


_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_
______________________________






"Kambu" ta furta da qarfi,wani irin zabura baba laure tayi ta durfafi kaltum dake niyyar shigewa sashensu,kafin ta ankara harta shaqo wuyanta ta fisgota baya
"Ni kike zagi don u****rki kaltume?" Ta fada cikin hargowa da daga murya
"Kibar zagarmin uwa baba"
"An zagetan....ko zaki rama mata ne 'ya'yan kuka?" Ta sake fadi hannunta riqe da bayan hijabin kaltum,wanda tuni ya feke sanadiyyar fisgotan da tayi,dubanta take ranta na sake baci,yana kuma raya mata abubuwa da yawa akan baba lauren,batason tayi rashin kunya,kota aikata abinda zai sanya ran ummanta ya baci....kafin tayi tunani na gaba ruwan ashar ya fara fitowa daga bakin lauren,wanda ya sanya umma fitowa daga daki kusan a tare ita da habiba bayan sun saki aikin da sukeyi.




Abinda ta gani din ya bata mamaki,laure riqe da hijabin kaltum tana dura mata ashariya,abu na tsaye abinta tana kallonsu hankalinta kwance.




Cikin sanyin nan nata ta qaraso tana duban laure,bayan ta dauke kanta daga irin ruqon da lauren ta yiwa diyarta
"Lafiya laure?,me ya faru?"
"Bani zaki tambaya ba,tunda kin fini sanin komai,qila ma ke kika aikota tazo ta zageni"cikin mamaki umman tace
"Zagi kuma?,kaltum?,ban baku irin wannan tarbiyyar ba" ta fada cikin takaici tana girgiza kai,ran kaltum ya baci,qiri qiri zata mata sharri ta bata ran mahaifiyarta,bayan itace silar faruwar komai?,saita fincike hijabinta daga hannun lauren,wanda hakan yasanya yagewar da yayi ya dadu,ranta a bace tace da umman
"Don Allah umma kada ranki ya baci,ki koma ciki kawai ki zauna,ni ban zageta ba na rantse da Allah,magana ta gaya miki ni kuma na gaya mata zahirin abinda ke faruwa,wanda ita batasan dashi ba" anzo wajen umman ta fada a ranta,har kullum idan kaji fadan kaltum dama ko waye to an taba tane,bata fiya fada akan karan kanta ba,ta rasa yadda zatayi ta rabata da wannan dabi'ar,saidai wasu daga cikin mutanenta na yawan gaya mata,kaltum din haka take,haka Allah ya halicci wasu bayinsa,me kishin uwace,ba yadda zatayi da ita
"Yimin shuru!,ni nafi kowacce halitta ne a duniya da ba za'a zageni ba?,annabin Allah ma aka zageshi wanda akayi duniya da lahira saboda shi,bare ni da ba kowan kowa ba?"
"Don Allah ummanmu kizo mu wuce mu qarasa aikinmu" habiba ta fada cikin yanayin bacin rai,duk da rashin son maganarta sai data tanka,saboda ranta baqaramin baci yake ba idan har taga ana yiwa kaltum din fada alhalin ita keda gaskiya,mawuyacine kaga tana fada da wani a sanadinta,saidai a sanadin uwa ko 'yan uwanta,ko kazo mata da rainin hankalin da ba zata iya dauka ba.




Maganar habiban saita harzuqa laure tahau zage zagen umman ta haifa marasa albarkar yara,ana fara haka habiba taja hannun kaltum don kada a sake batacciya zuwa ciki,babu jimawa umman ta biyo bayansu,bayan tayi tayi da lauren tayi haquri amma ta qiya,wanda sai data kwashi tijararta iyakar yadda ranta yayi mata sannan abu ta janyeta zuwa sashenta ta dora a can.




Kaltum din na zaune gefe tana qoqarin saisaita kanta tana kallon yadda umman ta hadawa bilal ruwan zafi yake gasa jikinsa,sannan ta sanyashi ya shiga wanka,sai daya shiga wankan sannan ta waiwayo ya dubeta
"Allah ya shirya min ke,ya kuma sawwaqe miki,shidai haquri maganin zaman duniya ne,kuma riba gareshi,ki tashi ki wuce inda zaki,bance kuma ki sake kula kowa ba,koda su musbahu kika gamu dasu bance ki musu zancan bilal ba" daga haka ta sanya kanta cikin dakin,sai kaltum din ta miqe,don itama zaman gidan ji tayi ya soma yi mata zafi,ta taka ta fice,har a sannan tanajin tashin maganganu daga sashen baba iliya,duk da baka gane ainihin me ake cewa.




Harta xarta gidansu wasila saita yanke ta biya tacan ta rakata gidan kitson,da yake wani lokaci tana rakata,kuma wasilan na yawan qorafin yadda kullum itace a tafe gidansu kaltum din,amma ita ko kara batayi ta zo mata saida dalili.




Taje kuwa a sa'a,donta isketa fes da kwalliyarta,da yake suna da yan uwa a cikin gari da suke bata kwancen kaya,ita kuma tayita gayunta da qwalisa dasu,tasha yiwa kaltum tayin wasu ma kan ta bata kyauta,amma sai tace aah,nata sun isheta,duk da cewa a kode suke,amma bata taba sha'awar karba ba,ta samo wannan qwarin gwiwar da wadatar zucin daga wajen mahaifiyarta
"Qawata irin wannan shan kyau haka?" Kaltum ta fada wasilan na bata sha'awa,irin yadda ta samu kulawa daga wajen mahaifinta,duk da cewa tana talla amma ba talauci ne yasa take tallan ba,kawai sabo ne da kuma yanayin al'adarsu ta shegen neman kudi,ji take inama itace wasilar,wadda bata da wata matsala a rayuwarta.




Murmushi wasila tayi
"Kwalliyar bakarabe ce,yanzun nan ya tafi,Allah ne yayi ba zaku gamu ba" murmushi tayi tana dosana da wani dutse da mutan gidan ke zama kansa idan zasuyi alwala,sannan ta saki murmushi
"Kullum.zancanki kenan,idan kinaso mu hadu ai takanas zaki aiko kirana duk randa yazo" wannan ba shine karon farko ba,don tunda wasila ta hadu da balaraben take baiwa kaltum labari,bata taba hadasu ba,saidai idan yazo ya tafi ta bata labari dariya wasila tayi
"To kiyi haquri,zuwa na gaba in sha maka Allahu zan aika kizo kafin ma ya qaraso"
"To Allah yasa"ta fadi cikin rashin baiwa zancan muhimmanci
"Rakani kitso zakiyi dorawa don Allah"
"To bari na gayawa babarmu" ta fada wasilan tana wucewa ciki da ledar hannunta,da alama balaraben ne y kawo mata wani abun.




Bata fi minti uku ba ta fito tana ware mayafinta ta yafa saman kanta
"Muje" tayi gaba kaltum na biye da ita a baya.




Duk da yake ranta na abace ne amma tayi qoqarin sakin fuskarta,suna tafe suna hira da wasilan,wanda hakan yadan rage damuwar dake ranta,duk da komai yana nan daram cikin zuciyarta.




Basuyi nisa ba ta hango nasiru tun daga nesa,shi dinma ya ganta,hakan ya sanya ya saki fuskarsa sosai yana jifanta da fara'a tun kafin ya riskosu.




"Kinga wancan....dan bokon garin nan,sai murmushi yake mana" wasila ta fada tana washe baki,idanunta akan kaltum,shuru kaltum din tayi ba tare data ce komai ba,don nasirun yana gab dasu.




Bai wuce minti daya ba kuwa ya riskesu,idanunsa akan kaltum din,har yanzu murmushi yake
"Gimbiyata.....sai ina haka da ranar nan,anya kuwa kina jin zafin rana?" Murmushi itama ta saki,ba laifi nasurun ya iya magana ta nutsuwa kuma a tsare
"Dole ce ta sanya hakan....,ina yini"
"Lafiya lau gimbiyata....ina fatan kin wuni lafiya"
"Lafiya qalau....." Saita waiwaya ta dubi wasila wadda ta zuba musu idanu tana kallonsu cikin mamaki
"Ga wasila nan,qawata ce,kuma aminiyata,ku gaisa" da murmushi ya dubi wasila
"Barka da warhaka hajiya wasila" qoqari tayi ta saita yanayin fuskarta sannan ta sake muryarta sosai
"Yauwa....barka kadai,nasuru ko?" Kaiya gyada
"Haka ne,ashe kinsan sunana" murmushi ta saki
"Na sani mana,ai kusan yammatan qauyen nan dai dai kune wadanda basusan sunanka ba,saboda banbamta da kayi dasu ta fannin ilimi" fuskarsa yadan motsa a mamakance
"Amma kuma cikin yammatan banda kaltum..." Saiya waiwaya yana dubanta,kafin ya dawo da kansa ga wasila
"Sanda na santa ita bata sanni ba,har sai dana gabatar da kaina dakuma sunana" dan tabe baki wasila tayi
"Idan ana magana ba'a sanyawa da kaltume,saboda kifin rijiya ce ita,daga daki sai tsakar gida,babu inda ta sani,ba wanda ta sani" murmushin farinciki ya saki
"Ma sha Allah,haka akeson mace ta zama ai" kafin wani cikinsu ya sake cewa wani abu kaltum din ta magantu
"Inaga zamu wuce,sauri nakeyi,nabar mutane suna jirana" saiya waiwaya ya maida hankalinsa gareta
"To shikenan....amma yau zan samu ganinki?" Kaita kada
"Gaskiya bana jin...."
"To gobe fa?"
"Allah ya kaimu" ta fada tana fara yin gaba,wanda hakan ya sanya wasila biyota suna sallama da nasiru.




Shuru ne ya ratsa tafiyar tasu ya maye gurbin hirar da suka dinga yi a daxun,zuwa wani lokaci kaltum ta ankara,ta waiwaya ta dubi wasila,sai taga kamar yanayi fuskarta akwai damuwa,dama kuma ita ke qoqarin sanyo hirar tun daxu,kaltum din tayata kawai takeyi
"Lafiya dai ko wasila?" Da sauri ta dubi kaltum din,sai tayi murmushi tana kada kai
"Lafiya qalau...."
"Naga kamar damuwa a fuskarki,wadda babu ita a dazun" shuru ta danyi kafin ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta fara magana a hankali
"Gaskiya bazan boye miki ba kaltume,banji dadin yadda kika boyemin soyayyarki da nasuru ba,a matsayina na aminiyarki,ace kun fara soyayya da nasuru amma ni ban sani ba,badon idanuna sun gani ba da sai yaushe kenan zan sani?" Hannun wasila ta kama tana murmushi
"Haba qawata,ba'a wani dade bafa sosai" hannun nata tadan zame da qarfi
"Ni ba abunda zaki gayamin,tunda ko na kwana daya ne aiya kamata na sani ko?" Dan jimm kaltum tayi tana mamaki,saita sake cewa
"Kiyi haquri wasila,bansan zakiji babu dadi ba,amma hakan ba zata sake faruwa ba"
"Shikenan,ya wuce" ta fada muryarta can qasa sosai,daga haka sukaci gaba da tafiya,saidai har a yanzun ma tafiyar kurame ce ba kamae dazun ba,hakan yasa kaltum take ganin kamar hucewa ne wasilan har yanxu batayi ba,don haka ta dinga qoqarin sanyo hira a tsakaninsu,da haka suka qaraso gidan.




Jan tunga wasila tayi tana duban kaltum
"Kaltume...kamowa zanyi gida fa" cike da mamaki kaltum ke kallonta
"Gida kamar yaya?,lafiya?" Fuskarta tadan yamutsa kadan
"Banajin dadin jikina ne"
"To.....baya bata da kadan" kaltum ta fada tana dan yin jim sannan ta dora
"Shikenan,Allah ya sawwaqe,ki koma din ki samu ki kwanta ki huta,idan na dawo zan biyo ta gidan na ganki,Allah ya sawwaqe" tana nan a tsaye har sai da wasila ta bace sannan ta saka kai gidan,zuciyarta duk babu dadi,musamman yadda suka taho tare kuma lokaci daya irin haka ta faru.




Data gama kitson sai data biya ta gidansu wasilan kamar yadda tayi alqawari,Saidai ance mata bacci take,don haka ta yiwa babarsu sallama ta wuce zuwa gida.




*_BAYAN WANNI BIYU_*




A inda suka saba zama koda yaushe cikin tsakar gidan nasu suke zaune bayan sun idar da sallar magariba,ummansu na saman tabarma ita da habiba,kowanne lazumi yake,yayin da kaltum ta shimfida sallaya tayi tata sallar,kuma tuni ta idar,rashin wani abu da zatayi ya sanyata dauko pencil ruler da farar fefa da usaina 'yar maqotansu ta bata kyauta,ta zauna sosai saman daddumar yadda zataji dadi,saita zubawa takardar idanu tana tunani,xane takeso tayi,saidai ya rasa me zata zana,murmushi ta saki samda zuciyarta ta bata shawarar zana duk abu na farko da yazo kanta,sai ta sake sakin murmushi karo.na biyu,ta duqa a hankali ta ware takardar ta soma zanen cike da nishadi,tana kuma rayawa a ranta,daga wannan karon duk abinda ta zana din zata dinga ajjiyewa ne,tana gani itama tana tunawa,bata mantawa,cikin irin hirarrakin da sukeyi da nasuru,sanda ya taba ganin wani qaramin gida irin nasu na karkara data zanawa 'yar maqocinsu,ya shaida mata cewa shi kansa zanen wani babban ilimi ne me zaman kansa da ake karatu a kansa,sai tayita mamaki tana jinjina abun,hakanan saita

Please Login or Register in order to submit comment