Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tashi motar suka bar airport din.




Ko a hanya ma hira suke sosai da sosai,irin hirar dake nuna yadda sukayi kewar juna,kamar ma babu kowa cikin motar saisu,da haka har suka iso gidan professor rashid.




Sanda suka danna horn sai malam datti ya dage musu qofar a maimakon malam salahu,saboda ranar ranar aikin malam salahu ce,suka gaisa a mutunce yana wa zaratan samarin barka da zuwa,fuskarsa cike da annashuwa,don sunyi kewar matasan suda tarin alkhairinsu.






*******Tun kusan bayan qarfe goma na dare yake matagugu yana juye juye,tare da fadin sunan Allah


"Cikina ummanmu,cikina....don Allah ku kaini asibiti,akwai matsala a cikin nan nawa" shine abinda bilal din yaketa fada,wanda hakan ya hana idanuwansu bacci,daga umman har kaltume,don tuni kaltume ta fara kuka tana riqe da bilal din tana jera masa sannu,hankalinta yayi matuqar tashi,saboda bata taba ganin bilal din cikin yanayi irin wannan ba na matuqar ciwo,duk da yadda wani lokaci yake da raki.




Duk wani magani da ummanmu take ganin ya kamata ta bawa bilalun ta bashi a daren,amma abun yaci tura,don babu abinda ya sauya daga matagugun da yakeyi na ciwon dake addabarsa,bugu da qari ga wani kumburi da cikin nasa yayi.




Tun babansu na sharewa harya bankada dakinsa ya fito,fada ya farayi,amma da yaga yadda bilal din yake saiya ja bakinsa ya tsuke. Ya dan zauna na mintuna kafin dare ya qara nisa,daga bisani ya tattara ya shige dakinsa ya barsu nan,lokaci lokaci yakan farka,ya leqo yaga bilal,wanda babu wani canji game da jikinsa na samun sauqi,face lafawa da ciwon yakeyi ya dawo.




Hakan ta tilasta musu suna kammala sallar asuba ummanmu da kanta ta shiga maqota,gidan malam sale mai amalanke,ta roqi alfarmar ya fitar dasu can bakin titi,inda zasu samu motar da zata kaisu asibitin cikin birni.




Babu komai malam sale yace,kasancewarsa mutum me matuqar kirki,uwa uba su kansu suna duba kirki irin na umma zuwaira,suna kuma tun alkhairinta a garesu.




"Nidai bani da ko asi,idan zaku iya zuwa to,saidai nace Allah ya kiyaye hanya" cewar malam amadu yana muzurai




"Allah zai rufa asiri" ummanmu ta fada tana duqawa gami da dago bilal,wanda gaba daya jikinsa yayi yaushi,hatta da mazagin wandonsa saida kaltum ta sake daure masa shi,sukayi masa kama kama ita da ummanmu,bayan ta tattaro 'yan kudadenta da kawu ado ya bata yace taja jari,batakai ga jan jarin ba,tana nazarin sana'ar da zatayi sa wannan lamarin ya ratso.




Babu wanda suke dashi bare suyi masa sallama,malam sale ya daukesu a amalankensa,cikin matuqar nuna tausayawa,bai saukesu ba har sai da aka samu motar da zata kaisu har bakin asibitin sannan ya taimaka musu suka sanya bilal,yana musu fata alkhairi har suka daga,sannan ya juyo cike da tausayawa,yana tuna son aiki da kazar kazar irin na bilal,amma lokaci guda kamar bashi ba,ya tuna sanda sukayi masa aikin katangar gidansa,kusan shine jigon aikin,amma daga baya ma kason da sauran suka samu na kudi shi bai samu kamarsa ba,bai kuma damu da hakan ba.






31
D/Z


*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*


08184017082
Ko kuma
09134848107




31




Daga ita har ummanmu shuru sukayi a dakin likitan,suna jiran suji bayanin da zaiyi musu,kowanne a cikinsu zuciyarsa dukan uku uku take,a haka har likitan ya dago ya dubesu.




Wani irin kallo yayi musu,wanda yake nuni da raini raini irin da kuma qyama,irin wanda aka sabawa mutanenmu 'yan uwanmu al'ummarmu ta karkara




"Baaba,yaya akayi kuka barshi haka a gida,har ciwonsa yayi tsanani haka?" Tashin hankali ne ya fito baro baro kan fuskar umman,cike da nuna damuwa ta zakuda zamanta kan kujerar tana cewa




"Likita?,me ka gani?,me yake damunsa?" Sai saya jujjuya takardar hannunsa,cikin shan qamshi sannan yace


"Eh to.....yanzu muna buqatar kuje ayi masa scanning tukunna....."




"Me kenan likita?" Ummanmu ta tambaya a rude tana kallon yadda jikin bilal din ya saki gaba daya,ya daina juye juyen,sai kallo da sauraren abinda likitan yake fada.




Goshinsa yadan sosa sannan yace


"Oh,sorry,hoton cikinsa....sannan zamu gane ainihin inda matsalar take,ayi kuma abinda ya dace" ya fada yana sakeyin wani rubutun saman takardar ya miqa mata.




Kaltum ce ta karba,sannan ta isa inda umma ke qoqarin sauko da bilal daga saman gadon,sukayi masa kama kama,ya dogara da kafadarsu suka fara tafiya don ficewa daga office din.




Tun basuyi nisa a tafiyar ba ya zame


"Bazan iya takawa ba" ya fada yana kallon ummanmu,hankalin kaltum ya sake tashi,dukkansu matane,bata tunanin zasu iya daukan bilal,har gwara ita akan ummanmu,saita dubu takardar hannunta, ayanzu burinta kawai shine sune wajen hoton a samu a gano abinda yake damunsa a cikinsa


"Ka daure bilalu muje,kaga likitannyana jiranmu" kansa ya mirgina yana ajiyar numfashi


"Bazan iya ba yaya,Allah bazan iya ba" ya fada a raunane,babu wata sauran mafita data rage musu,don haka kaltun ta miqawa ummansu takardar


"Riqe ummanmu.na goyashi"


"Anya ko zaki iya kaltum,ki barshi dai ya sake gwadawa"


"Zan iya ummanmu in sha Allahu" ta fada tana juyawa bilal bayanta,da taga taga umman ta tareshi ya shau bayan kaltum,duk da nauyin da bilal din yake dashi amma sai data ar jarumtar data shanye wannan nauyin,saidai daqyar take iya taka qafarta,hakanan kafin sukai wajen scan din ta huta ya kusa sau biyar,a haka har suka isa wajen.




Sun tadda layi,suka tambayi mutum na qarshe a wajen,suka zaunar da bilal suna tsaye a kansa




"Ruwa" ya fada qasa qasa,idanuwansa na kan al'ummar dake kai kawo,ummanmu tace kaltum din taci gaba da tsaiwa dashi,bari ta samo masa ruwan,cikin hanzari ta miqi hanya.




"Amai zanyi" bilal din ya sake fada,saita cafko wata baqar leda dake yawo a qasa kusa dasu,tana tara masa kuwa ya fara shara aman,yana aman tana kallonsa tana kuma kallon aman,hakana jama'ar dake kusa dasu,saboda wani irin baqin amai da yakeyi,harda gudaji gudaji kamar na nama ko fasashiyar mahaifa,a haka ya kammala tsaf,dai dai sanda ummamu ta dawo,ta balle pure water din data zo dasi guda uku,ya shanye biyu daga ciki.


Tafi tafi layi yazo kansu sannan suka shiga,kaltum na daga waje ummansu ce ta shiga tare da bilal din,yadda taga ya natsu ya zubawa na'urar idanu sai taji jikinta ya sanyaya haka kawai,ya daga kai suka hada ido


"Kece mamansa?" Kanta ta gyada a maimakon ta amsashi,saiya maida kansa yaci gaba da aikinsa da sauri sauri ba tare dayace da ita komai ba,yana gamawa ya linke takardar bayanan ya bata


"Kuyi hanzarin kaiwa likita wannan"
"To na gode" ta fada tana karba hannunta yana rawa,sannan ta kama bilal suka fito.




Kai likitan yake jinjinawa sanda ya karbi bayanan yana dubawa,kansa ya daga ya dubi umma


"Baiyi amai ko sau daya ba?"


"Yayi likita yanzu babu jimawa" sai taga ya dafe goshi,ya ajjiye takardar ya dubi nurse din da a yanzu take tare dashi




"Kuje dashi a bashi gado, a daura masa drip....baaba,kuje ku nema kudin aiki dubu takwas,za'ayi masa operation ne na gaggawa,kada ya dara awa daya"




Gaba daya kamar an kwarawa jikinta ruwan sanyi haka ummanmu taji,kaltum kuwa mutuqar tsaye tayi,saboda sunfi kowa sanin cewa basu sa wannan kudi,basu kuma da hanyar samunsu,data laluba jakarta ma kudin da suka rage a ciki wanda suka taho dashi na jarin nata dubu daya ce,banda haka basu mallaki komai ba,don haka bayan an masa duk abinda likitan yace,sai ummanmu ta kalli kaltum


"Bari na fita daga waje ko zan samu wajen buga waya,na kira ado ko indo,ko Allah zaisa a dace a samu koda wani abune daga wajensu"


"To ummanmu" ta amsa mata idanunta nakan bilal,wanda nashi idanun suna kan umman


"Don Allah ummanmu kada ki dade"


Takowa tayi a hankali gabansa ta tsaya,ta kamo hannunsa da babu qarin ruwan ta riqe gam sannan tace


"Yanzun nan zan dawo in sha Allahu"


"Ayimin aikin nan ummanmu ko zanji dadin cikina"


"Da yardar Allah yau ka rabu da ciwon nan" saiya gyada kai kawai yana lumshe idanu,umma ta zame hannunta ta fice da sauri.




Kujerar roba da ake ajewa guda daya a gaban kowanne gado kaltum ta jawo ta zauna gaban bilal,duk a darare take,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa waje irin wannan,sai take ganin kamar kowa kallonta yakeyi,duk kuwa da cewa ba haka bane,kowa ta mara lafiyansa yakeyi


"Zanyi amai yaya" bilal ya sake fada,saita miqe da sauri ta sake samo masa leda,kamar aman dazu ya sakeyi,itadai kaltum ta zubawa aman ido cike da mamaki,ganin wani abu guda guda kamar hanta hanta a ciki da yake ta fita,gashi yayi wani baqi kamar ajiyayyen jini,haka ya gama ta rufe ledar taje ta yar.


Tana dawowa ta taras da wani ma'aikacin lafiya a kanshi yana dubashi,ya kammala yayi rubuce rubuce ya bata takardar,yana barin wajen yana mata bayani


"Magunguna ne,aje a siyasu yanzu" fakare tayi da takardar a hannunta tana juyata,ita da zuciyarta suna qiyasta adadin kudin maganin da babu su babu dalilinsu


A hankali ta daga idanunta,sai suka hada ido da bilal din,hannu yasa ya yafitota,ta taka a hankali zuwa gab da gadon ta sunkuya sosai daidai kansa,saboda yadda muryarsa take fita yanzu a hankali,da alama dukkan wani qarfi da kuzaru nasa ya qare


"Yaaya,inabin lawandi kudi,don Allah aje wajensa,ya bayar da kudin ayi mini aikin dasu,ni kadai nasan abinda nakeji,idan basu cika ba ko baba ne ya taimaka ya cikamin" wasu hawaye ne suka zarto mata,saita miqe tana gogesu daga fuskarta,tsananin tausayin dan uwan nata yana cika qirjinta,ta yadda har takejinnkamar ta fiddo zuciyarta waje.


Roqo abune da bata taba yi ba tunda take,amma ayau zata yishi saboda ceto rayuwar dan uwanta,don gabas da yamma,kudu da arewa a yanzu batasan inda zata sama masa kudin magani ba idan bata wannan hanyar ba


"Ki kiramin ummanmu,tazo ta zauna a kusa dani" ta sake jin muryar bilal,saita juya da sauri don yi masa abinda yace din,sai kuma ga umman ta dawo




"Kin kirasu ummanmu?" Tayi tambayar tana duban yanayin umman


"Ban samu ba,amma wani bawan Allah yace na jira ya karbo wayarsa daga wajen chargy,saina koma ya kiramin.




Kai kaltum ta girgiza,tana ji lokaci yayi tsaho da yawa,tana ganin gwara ta fita su roqa,koda basu cika ba a ciki tayi kudin mota ta koma qauyensu ta amso kudin bilal din a hada a cire masa ciwon dake damunsa


"Ina zuwa ummanmu" kaltum ta fada da sauri tana bin hanyar waje,sai umman ta saki ajiyar zuciya ta maida dubata ga bilal daketa binsu da ido


"Me yasa kika tafi ummanmu?" Ya tambayeta a hankali,tana qoqari maye gurbin da kaltum ta tashi ta amsa masa


"Kayi haquri bilalu,inacan wajen nema maka kudin aiki,amma gani na dawo" saiya gyada kai yana miqa mata hannunsa


"Riqemin hannuna"


"To bilalu" ta amsa masa tana saka hannunta cikin tafin hannunsa.




Abunda baka saba ba,diri diri ta shiga yi a dan filin asibitin,ta rasa ta ina zata fara?,wa zata fara roqa?,saita fara takawa a hankali zuwa nahiyar da mutane ke zaune,wasu suna jinyar 'yan uwansu,wasu kuma dubiya suka zo.


Duk wanda ta dosa katin take miqa masa tare dayi maaa taqaitaccen bayani.


Bata taba sanin duniyarmu ta cika tab da marasa tausayi ba.....bata taba tunanin duniyarmu ta cika da nau'in jama'ar da basa jin qan junansu ba sai a ranar,mutane da yawa saidai suce Allah ya sawwaqe suma basu dashi,idan ma taci sa'a kenan an mutuntata,duk kuwa da cewa mafi yawa a cikin masu fadin hakan,ba za'a rasa kudi koda qanqani a jikinsu da zasu iya bata ba,wanda inda sunyi hakan....kadan kadan din su zasu hadu su bata yawan adadin abinda take buqatar.




Wasu daga cikin mutanen ma saidai su dauke kai,ta gama bayaninta ba tare da wani daya cikinsu yace komai ba,a haka taci gaba da jarraba sa'arta.




A hankali motar tasu ta ratso cikin asibitin,matasan zaratan samari,wadanda kudi da ilimi suka yiwa ginshiqi,samir tare da amini kuma dan uwanshi aamiru,dukkansu suna sanye da shadda,wadda aka yiwa wani nau'in dinki mai qayatarwa,wanda yayi musu kyau,ya kuma fidda sigarsu da zatin da Allah yayima kowannensu.




"Wannan wanne irin asibiti ne haka?" Amiru ya fada yana bin asibitin sa kallo,sai a sannan samir ya aje wayarsa saman cinyarsa,kasancewar bashi ke tuqin ba amiru ne,shidai yana zaune kawai a gefansa.




Ajiyar zuciya mai nauyi saraki ya sauke,tsahon wasu sakanni sannan ya magantu


"Bakaga komai ba....wannan asibitin da kima da darajarsa akan saura,bansan me shugabanninmu keyi ba,totally basu san responsibility dinsu ba,yanzu wai a irin wannan muhallin ake neman lafiyar dan adam....Allah ya kyauta" ya fada tare da bin bayan maganar tasa da tsaki bacin rai yana cikashi,saiya buda murfin motar ya zura qafarsa waje yana sake qarewa harabar asibitin kallo.


Cak ya tsaida idanunsa yana dubanta waje daya sanda take kai kawo a tsakiyar asibitin,da yadda take tsaida jama'a jefi jefi,sannu sannu har ta iso dab da motarsu,sai yaga ta zagaya daga baya inda amiru ke tsaye yana amsa waya,bai waiwaya ba amma yana iya hango black face dinta ta jikin mudubi,wadda ta qara duhu da shining.


"Lafiya?" Yaji amiru ya fada,wanda bai gama wayar ba,ya dakata ne saboda tsaiwarta a wajen


"Taimaka mana zakayi fisabilllahi da kudin magani,don Allah,bamu da kowa bamu da komai sai Allah....."


"The giant,are you there?" Gyaran murya kawai samir yayi masa


"Ok,miqo wani abu" ya fada yana dariya dariya,saboda tuna wani abu da yayi,baice komai ba ya bude aljihun motar,ya ciro kudi a ciki,cikin ransa yana tambayar waye nasu a asibiti babu lafiya?.


Har zai miqawa amiru kudin saiya tuna yadda aka tabayi da ita akan sabon kudi,saiya maida,ya laluba ciki ya dace da samun wasu,sai ya miqawa amiru su gaba daya.




Har zaiyi magana da yaga yawan kudin sai kuma ya fasa,ya miqa mata,tsayawa tayi turus tana duban yawan kudin


"Ki karba mana" kanta ta girgiza


"Sunyi yawa ai" ta fada adan tsorace tana ja da baya,dariya da mamaki suka tasowa amiru amma ya dannesu


"Nawa kike so to?" Kamar ta taka da sauri tabar wajen,sai kuma ta tuna bilal yana da buqatar kudin,a hankali kamar wadda batason fadi tace


"Duka har kudin magani da kudin aikin dubu goma da dari biyar ne,na samu dubu daya,saura dubu tara da dari biyar" da boyayyar dariyarshi ya irga kudin dake hannunsa,ya zare dubu goma a ciki ya bata


"Ga dubu goma nan,dubu dayan kai sai ku sayi wani abu" hannu biyu tasa ta karba tana godiya har qasa,saita baiwa amiru tausayi,yana dariya bayan ta wuce yace sa samir


"Kaida ka kawomu nan kuma kayi zamanka kaqi ka fito,gashi na fara haduwa da mutanenka,ka ganemin yarinya?,iya abinda takeso shi zata karba?"


"Haka take" ya bashi amsa sanda yake fitowa daga cikin motar


"Ka santa ne?" Da mamaki amiru yatambayeshi


"Kusan hakanne" ya amsa masa yana gyara rigarsa data dan tattare ta baya


"Kodai daya daga cikin 'yammatan daka yone daga qauye ka yaudaresu bayan ka gama aiki?,kai....no wonder mafa naga kaqi fitowa har sai data tafi" amirun ya fada yana dariya,tilas ya sashi murmusawa,daga baya qaramar dariya ya subuce masa,har haqoransa suka bayyana,babu abinda ya tuna sai fuskar kaltume,da qwailan jikinta


"Kaci abinci amiru,amma babu laifi,zan rama ne" yana fadar haka ya danyi gaba da hanzari,amirun ya bi mashi a baya zuwa ciki,suka fara tambayar inda mai gadinsu malam salahu yace an kwantar sa dan nasa,don dama dan dama shi suka zo dubawa.


Shan gabansu da wata mace mai dan wadatar shekaru tayi yasa suka tsaya cak


"Yallabai,kune gwamnatun ta aiko da tallafi?" Ta tambayesu tana kallonsu,duban juna sukayi a tare,amiru ya dagewa samir gira kana yaja baya,alamun ba ruwansa,yaji da ita.


Murmushi samir yayi mata sannan yace


"Mune iya,me ya faru?" Zaro idanu amiru yayi jin abinda samir ya fada,ai kuwa matar ta kaikaice tana ta fadin matsalolinta,wanda kusan duka nakudi ne,sai data gama sannan ya zaro kudi masu dan dama daga aljihunsa ya bata,wayyo,zo kaga murna,kamar zata zuba ruwa a qasa tasha,tausayinta ya kama saraki,tausayin halin da takalan qasata yake ciki.


Godiyar da take zabga musu yaja hankalin mutanen wajen saika marmatso,saita hau gaya musu gwamnati ta turosu,saifa aka fara tururuwar fadar matsaloli,tun yana raba kudin aljihunsa har suka qare ya karbi na amiru,shima suka qare,daga bisani dai wanda bai samu ba sai alqawarin kawo tallafi daga baya yayi musu.


Amiru na biye dashi a baya yana kwasar dariya,shi kansa yanda sukayin ya bashi dariyar,saidai kuma tsantsar tausayinsu ya danne dariya,saiya dakata,suka jera da amiru,ya fara masa wasu bayanai da yanayi da halin da al'ummar karkara ke ciki,wanda duka ya karanci hakane a makarantar duniya,da dan shiga garuruwansu yi musu aikin da yakeyi,kafin su qarasa dakin da zasu saiga amiru yana gyada kai,sau tari shi kansa yana yaba halayya da dabi'un samir,yana kuma yaba kaifin tunani da hangen nesan da yake dashi.




A gaggauce kaltum ta tsallaka can wani wajen saida magani dake da da tazara da asibitin ta karbo dukan abinda ke rubuce jikin takardar,cikin tsananin sauri ta dawo asibitin,saboda so take akaiwa likitan kudin da wuri ya yiwa bilalunsu aiki ya huta.


Tun daga farkon qofar babban dakin ta hango ummansu zaune gaban gadon da bilalun yake kwance,ya canza yanayin kwanciyarsa ba kamae dazu ba da yayi kwanciyar hannu daya,kuma ma kamar a rufe yake yanzun,amma me yasa ummanmu ta rufeshi har saman kansa bayan tasan bashi da lafiya?,ta tambayi kanta,idanu da hankalinta a kansu har ta isa gaban gadon.


Kafin tace komai ummanmu ya dubeta,wani abu kakkaifa data hanga daga idanun ummansu,yasa dukkan wani sassan na jikinta yayi sanyi qalau,hatta maganar data furta a sanyaye tace


"Ummanmu ya samu bacci ko?" Kai ta gyada mata


"Yayi bacci kaltum,babban baccin da babu wanda yasan ranar tashinsa sai Allah,yayi kwanciyar da zai huta,irin hutun da muka gaza samar masa" kasa fahimtar maganar ummansu tayi kwata kwata,kamar ma ba hausa take mata ba,muryarta na rawa tace


"Kamar yaya ummanmu?"


"Allah ya karbi ran bilal,ina fatan kuma ya huta kenan har aljanna" batasan ledar hannunta ta fadi ba,batasan ta zame ta fadi ba ita kanta,qafarta ta bugu da qarfen gadon,abunda ta iya sani shine wani kuka data saki wanda ya amsa kuwwa a dukka ilahirin lungu da saqo na dakin,kukan da yaja hankalin dukka mutanen dakin,har ma da wadanda basusan bilal din ya rasu ba,ya kuma ja hankalin su samir dake bakin gadon dan malam salahu suna dubashi,ya waiwaya yana tuna inda yasan wannan muryar da irin kukan,sai idanunsa suka hange masa ita.


"Ya salam" ya fada yana jin qirjinsa yana bugawa,tabbas wani ne ya mutu,juyawa yayi a hankali zuwa inda take ummansu da wasu mata na qoqarin dagata tare da bata baki,bai tsaya ba sai daya isa gaban gadon,ya saka hannu ya bude rufin,saiga bilal,the hard work boy title din da yake masa.


Sakin abun rufar yayi yayi baya yana fadin


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yana jin wani abu yana zaga kwanyarsa,bai taba tunani ko kawowa ransa haka ba,duka duka yaushe sukaje dubashi,ya daga kai ya sake kallon gawar,ko a haka cikinsa ya nuna kumburin da yayi harta saman mayafin da aka rufeshi






32
D/Z


*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*


08184017082
Ko kuma
09134848107




32


Shi ya dinga kai kawo tsakanin biyan bill din kudin bilal dana dan malam salahu,duk da cewa shi bilal nashi kudin ma ba wani masu yawa bane,saboda bai jima ba,duk motsin da zaiyi fuskar yaron yake hanga,wani tausayi yana ratsashi.


Tare da amiru suke komai,duk inda yasa qafa yana biye dashi,saidai bakinsa fal yake da tambayoyi ga sarakin game da su umman.


Bai sake shiga mamaki ba sai daya ji samir din yana bada umarnin sanya gawar bilal cikin motarsu,ya kalleshi,duk da baice komai ba,umman da kaltum daketa rusa kuka cikin wani yanayi mai matuqar ban tausayi suna daga baya,shi da samir din suna gidan gaba,malam salahu na musu addu'ar sauka qalau da samu rahama ga mamacin,samir din ya tada motar suka fice daga asibitin.


Kukanta kawai ke tashi cikin motar,ta kasa tsaida kukan ko dai dai da minti daya


"Don Allah bilal ka tashi,ka tashi kace wasa kake mana" shine abinda take fada lokaci bayan lokaci tana girgizashi,.


Sannu a hankali kukan yaci gaba da ratsa kunnuwansu,harda samir da sitiyarin motar ke hannunsa,lokaci bayan lokaci yakan ce


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" a sarari,daga bisani saiya sanya casset na karatun qur'anu,qira'ar khusari,wanda hakan ya rage kaifin kukan kaltum.


Suna isa qauyen labarin rasuwar bilal ya ratsa ko ina,kafin kace meye wannan jama'a sun fara cika gidan,habiba na daya daga cikin wadanda suka fara zuwa,sun shigo tana riqe a hannun surukarta tana gunjin kuka,tana faduwa tana tashi,tana kiran bilal din tare da fatan abunda ke faruwan ya zama mafarki,xuwanta ya sake sanyawa kaltume dake ta son bawa kanta juriya sa qwarin gwiwa saita sare,suka taru suka dinga kuka baji ba gani,sai inna da bata jima da isowa ba,tana doje daga bakin qofa tahau musu fada,fadan da badan cikin yanayi yake ba duk sai sun tsaya kallonta,saboda mamakin dama innar tasan Allah?.




Cikin abinda bai gaza awa biyu ba aka gama shirya bilal,a sannan kaltum ta sake aro juriya,ta taka tana rangaji kamar zata fadi,saboda yadda takejin iska tana yawo da ita ta fita harabar gidansun,inda abokan bilal suka cika,harda wadanda kaltum ma bata sansu ba,ba 'yan unguwar bane.




Abokinsa na kusa kusa ta kira


"Ka tambaya cikin abokanku,ko akwai wanda yake bin bilal bashi?" Kai ya kada cikin alhini


"A iya sanina babu,saidai ma wadanda bilal yakebi....amma bari na tambaya" juyawa yayi ya koma cikinsu,amsoshin dake fita daga bakunansu duka irin wadda ya bata ne daxun kafin yakai ga tambayarsu


Hawaye taji yana sauko mata,haka rayuwarsa ta qare gaba daya,ya nema da guminsa da qarfinsa,yaci iya cinsa,ya baiwa 'yan uwansa,ya bada bashi ga abokansa,koda zasu cinye bashin ba zasu biyashi ba.


Rudewa gidan yayi da koke koke,yadda gidansu ke cike damqam da mata ashe a waje abun yafi haka,mamaki ya kusan kama kowa na jama'ar da bilal ya tara,idan bakasan waye ya rasu ba,zakayi tunanin cewa wani babban mutum ne ya rasu,saboda yawan al'ummar daya samu,suna ji suna gani bayan an gama sallar ama daukeshi akayi gaba dashi,ya barsu da kuka,ya barsu da kewa,ya barsu cikin gidan da ake yunqurin korarsa,sai gashi tun ba'a koreshi ba,shi ya tattara nasa ya nasa ya tafi inda ba dawo,inda kowanne me rai zaije.




Cikin dare a ranar ta kasa bacci,ganin komai take kamar wani wasan kwaikwayo,kamar wani wasa ne bilal din yake musu,kamar yaje ne zai dawo musu,ta dinga juyi tana kuka,yayin da gefe guda kuma abinda ya faru a wunin duka ya dinga dawo mata,yadda su ya munzali da muzammilu suka dinga rawar qafa wajen hada gawar bilal,sune kawo turare sune kawo sabulu da likkafani,idan ka gani kai ba zakace sune sila ko muzajar mutuwarsa ba,Allah ya sani,ba zata iya gogewa ba,ba zata iya hana kanta kallonsu a matsayin wadanda sukayi sila ko sanadiyyar tafiyar bilalunsu zuwa qiyama ba.


Sai kuma ta hango fuskar mahaifinsu,yadda yaye tsugunne gaban gawar bilal,gawar da sai da aka gama hada bilal din sannan ubangiji ya bashi ikon qarasowa,don bai samu labari da wuri ba,saboda a ranar yayi sammakon zuwa wani waje.


Ganin juyin bana qare bane saita miqe don ta dauro alwala,sai sukaci karo da ummanta,da alama itama baccin ya gagareta ne,batasan sanda wani sabon kukan ya qwace mata ba


"Da kika ce abar habiba ta zauna,da haka zaku zauna kenan ke da ita kuyita yi masa kuka?,kukan da bashi da wani amfani ko rana a wajensa?" Abinda umman tace kenan tana cika buta da ruwa don daura alwala.


To cikin kwanakin zaman makokin abubuwa da yawa sun faru,sunga jama'a masu yawa,wadanda basu tsmmatarwa bilal din ba,jama'a masu kamala da mutunci,wadanda zaka zaci ba zasu zo gun jana'izar yaro ba,yaron ma mata gata irin bilal,amma sai gasu,kowa yazo kuma saiya koka kan rasuwar yaron,saboda yadda kusan kowa ke amfanar sa,bashi da qyuya ko san jiki ko kadan,baisan rashin kunya ko fitsara ba ko kadan,girmama kowa yake,hakanan bashi da abokin fada.


Kudadensa da mutane suka kakkarba bashi masu tsoron Allah suka dinga kawowa ummanmu da kaltum sunyi mamaki,saboda wani ma basuyi tunanin bashi zai shiga tsakaninsu ba,yawan kudin da suka riqe sai yanzu suke biya,inda a zamanin da yake raye suka biyashin,babu shakka da sun isa ya kafa qaramar sana'a,da bai mutu cikin wahalar daya mutu ba,da bai mutu yana neman kudin da za'a masa aiki ba.


Yawan mutanen da suke zuwa gaisuwa ba shakka banda taimakon Allah,da kuma taimakon kawu ado da gwaggo indo da basusan da abinda zasu ci dasu ba,saidai a taimakon wadan nan bayin Allahn aka dinga dafa abinci ana ci.


Inna kuwa rabonta da gidan tun randa aka dauki gawar bilal,bayan an dawo daga binneshi,kawu ado yasa aka sauke buhun shinkafa babba dana wake,saita hau cewa a diba mata,wannan ai ya yiwa zuwaira da ahalinta yawa,ta dauko babbar qatuwar leda baqa ta buda bakinta.


Ran wasu daga cikin 'yan uwa ya baci,amma saboda kowa yana shakkarta,saboda masifarta da bala'i yasa aka rasa mai tanka mata,sai wasu daga cikin jikokinta da suka fara qananun maganganu.


Ganin da gaske take yasa yakumbo indo ta murje idanunta tayi mata magana


"Inna,wannan kayan abincinfa ba dafawa akace a dinga

Please Login or Register in order to submit comment