Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[30/12/2018, 21:35] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/








*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan'malikin kawo*


















Page 1








*Da sunan Allah mai rahma Mai jin qai wanda ya kara bani ikon fara rubuta wani labari bayan na kammala *TAMBARIN TALAKA* *yanda na fara lafiya Allah kasa in gama lafiya🙏*




*Wannan labarin ban yishi dancin zarafin wani koh wata ba So idan kaga abunda ke ciki yayi shige da rayuwanka badan kai nayi ba ko dan ke*




*ban yarda wani ko wata su canza Min labari tako wani siga ba duk wanda yayi haka ba tare da izini naba ban yafe ba*


















Kasar Spain kasa ce da take da mutane fararan fata wato turawa sannan ita wannan kasar yare daya takeyi wato Spanish sai wasu tsirara suke English a airport mutane ne makil anata ihu tare da gudu Wanda yaja hankalin Wanda basu san dalilin ihun ba, suma suka fara dubawa koh lafiya wani matashi ne kallo daya zaka masa kasan cewa shima bature ne jami'an tsaro ne a zagaye dashi yayin da mutane suke ta faman miki mishi paper da biro wasu kuma nata faman daukanshi hoto tafiya yakeyi yayin da yake daga musu hannu shima wata yarinya karama yaga tana miko mishi takarda da biro tsayawa yayi ya amsa tare dayi mata signing sannan ya shafa kanta ya mika mata takardan har waje mutane suka bishi inda motoci ke jiran su, daya daka cikin motar aka bude mai Ya shiga yana daga ma mutane hannu jan motar akayi Suka bar wajan, wani dangareren Gida suka nufa bayan Sun faka aka bude motar fitowa yayi ya nufi kofar shiga cikin gidan bell ya danna wata baturiya daka gani Mai aiki ce dan Tana sanye da kayan masu aiki itace ta bude kofar ganin wanda yake bakin kofar yasata saurin rungumeshi tare da fadin sannu da zuwa duk cikin yaren Spanish suke magana da Fara'a ya amsa da nagode ina Dad? Tace yana ciki yan..... Kafin ta karasa sai ga wani mutum ya fito dan dattijo da sauri ya nufi saurayin yayi hugging dinshi yana fadin My son barka da zuwa dan sakinshi yayi tare da buga kafadan shi yana fadin ina alfahari dakai murmushi saurayin yayi tare da fadin ngd Dad zama yayi akan kujeran dake falon wanda yasha kayan more rayuwa tare da fadin mai aka ajiye min? Dad yace your favorite mai aikin gidan ce ta Kawo mai coffee amsa yayi tare da fadin thank gina yana dan hadawa da turanci cikin maganan shi, Sha ya farayi sannan ya tashi ya nufi dinning inda ya bude wata hummer ya zuba abinci ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya tashi ya haura dakinshi dake gidan wai waye wannan saurayin ne..... Muhammad samir sunansa dan asalin kasar Spain ne domin a nan mahaifinshi yake dan kwallon kafa ne a laliga wanda yake bugama FC Barcelona yana daya daka cikin manyan yan kwallon da ake alfahari dashi a duniya baki daya Wanda akafi sani da m samir tun yana yaro Dad dinshi yace Mum dinshi ta rasu bai taba ganin koda hotan mum dinshi ba, abun yana damunshi sai yasa bai cika zama kasar shi ba dan yana fushi sosai idan ya tuna bai san waye mum dinshi ba, a hannun gina ya taso duk da ita ba musulma bace amma mahaifinshi na kula Dashi tun yana karami yake son buga kwallon kafa kasancewan son kwallonshi yayi yawa yasa bai wani yi karatu mai zurfi ba daka secondary Skul ya gama ya fara buga kwallon kafa duk da sai mai hanya yake samu shima Dad dinshi yana daya daka masu kudin kasar Spain sai yasa bai wani sha wuya ba wajan hayewa, da yana premier league inda yake buga ma Manchester United daka baya ya koma laliga yake buga ma Barcelona wanda aka bashi number 7 domin irin cin kwallon da yake yi number dinne ya dace Dashi sunan mahaifinshi Muhammad Ali, sai yake amfani da sunan Dad din nashi Kafin nashi, m samir matashin saurayi kwata2 shekaranshi 28 a duniya yana da kudin Dashi kanshi bai san nawa ke gareshi ba domin bayan kwallo yana business amma bashi yake kula dashi ba yana da budurwa mai suna sonia yar kasar England duk da ba musulma bace amma yana sonta kuma ita yake son aura tunda addininshi bai haramta mishi hakan ba wannan shine kadan daka labarin shi......




















Koda ya shiga daki wanka yayi yasa boxer da singlet kwanciya yayi tare da daukan wayanshi yana dannawa message ne kala2 gasu nan duk bai bude ba ga wasu na kara shigowa Dan tsaki yayi domin bai san ta yanda zai fara karantawa ba inda yana tare da Sonia ne data karanta mai dialing din number dinta yayi ya kara a kunne bugu biyu ta daga tare da fadin swt hrt I miss you wen r u coming bck dariya yayi mai sauti tare da fadin Sonia yau fah nazo Spain and jiya muna tare tace kasan bana son kayi nisa Dani in baka dawo ba nan da 1 week zan zo Spain yace OK zan dawo b4 d tym kafin nan munyi match din da za'ayi inma ban dawo ba sai kizo dan nima nayi missing dinki sosai nan sukaci gaba da hira na soyayya duk cikin harshen turanci kafin suka kashe wayan.




















*NIGERIA*


Garin abuja wata matashiya ce cikin riga da wando tasa karamin gyale ta yane kanta kallo daya zaka mata kasan yar wani babban mutum ce domin cikin falon da take zaune ya isa ya nuna maka suna da dukiya yarinyar fara ce tana da tsawo amma ba sosai ba sannan kuma ba wada bace tsawonta dai normal tana da manyan ido sosai ga gashin ido kaman tasa lashes gata fara kaman kalan larabawa kyanta ya wuce duk yanda mai karatu yake tunani wani saurayi ne ya shigo falon da sauri ta tashi tana fadin Ozil dan Allah karfe nawa barce suke da wasa nasha koh 2 ne gashi nasa duk channels din da ake kwallo amma ba'a fara ba, yace toh m samir ai ba zasu nuna ba a nan nima yanzu gidan ball zani inga irin cin da za'a ma Barcelona tace haba dai muna fa da m samir taya za'a cimu dariya yayi yace haba mu madrid ai muke da yan wasa ba kuba gidan madara tace dan Allah ni mubar wannan musun muje Gidan kallon tare in yaso in mun dawo asa mana irin dish din Gidan kallon, wata mata ce ta amshe da fadin amma kam jawaeer kina da aiki dan rashin mafadi da kamun kai sai kice zaki Gidan kallon ball bayan kin san duk Maza ne a ciki babu mata? Kai kuma kabir harda biye mata koh? Baki ta turo tare da fadin mum dasu M samir za'a buga fa kuma kin san in ban ganshi ba zan shiga cikin damuwa, Mum salati tayi tare da fadin jawaeer anya ba gamo kikayi ba ki dauki son duniya ki daura ma wanda bai san dake ba bai masan da zaman ki ba may be ma bai san kasarki Nigeria ba, tace mum taya zaki ce bai san Nigeria ba bayan anayin World Cup nidai Mum mun tafi kallo sai mun dawo ta kalli kabir tace Ozil muje dan Allah tym na tafiya fita sukai suka bar Mum na jimami tare da tausayin yarta ita kuma kalan jarabawan ta kenan son dan kwallo har take fadin shi zata Aura in bashi ba babu wanda zata Aura gashi ita ba yarinya ba balle ace yarinta ne tunda yanzu tana shekara 20 dai2 a duniya zama Mum tayi tana tuna baya lokcin da jawaheer taga m samir ta rude take fadin shi zata Aura har take gaya ma dad dinta kullum tayi sallah sai tace Allah yasa ya aureta wai wacece jawaheer?........ Ku biyoni dan ji yawan comment shi zai nuna min kuna son ci gaba.....




















*Maryam obam*
[31/12/2018, 14:16] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
















Page 2


















Alhaji Jibrin mai dala dan kasuwa ne na daya wanda a Nigeria ake alfahari dashi bama Nigeria ba harta kasashen waje baya siyasa duk wani Abu da akeci shi yake kawo wa babu wanda bai san sunanshi ba a Nigeria harta karamin yaro yasan Alhaji Jibrin mai dala yana daya daka cikin masu jerin masu kudin duniya za'a iya cewa yana cikin na hudu ko na uku matarshi daya hjy bilkisu yaransu uku umar shine babba yana aiki a nnpc yana da Mata sai khalil shi bashi da aure ya kammala karatun shi Oxford sai jawaheer da take karatu a nan abuja tana 2lv tana karantan English duk da dukiyar su sunyi karatun addini dan dukansu babu wanda bai sauke al'qur'ani ba da sauran littafai, mahaifinsu yana matukar ji da jawaheer baya iya musa mata ga duk abunda take bukata kodan ita daya ce Mace yarshi oho, jawaheer kyakyawa ce ajin farko gata fara Sol kaman balarabiya ga manyan ido ga lips dinta Pink gwanin Sha'awa tana da hanci dogo siriri komai dai Alhmdlh, kabir Abokin khalil ne yana zuwa Gidan suna kallon ball jawaheer bata son kwallo koh kadan gashi idan anayi su Khalil a falon Gidan suke zama su kalla wata rana jawaheer ta dawo daka lecture taga suna kallon ball zama tayi tana dan yatsina fuska a dai2 lokacin akaci kwallo khalil ya kwala ihu kallon TV din tayi taga wanda yaci kwallon gabanta ne taji yana dukan uku2 M samir taji ana ta fadi shi yaci kwallon wani irin dadi takeji da taji musulmi ne nan ta Fara tambayan Khalil waye wannan yace M samir kenan tace wani team yake yace Manchester United lokacin yana Man u bai koma barce ba, wayanta ta dauka tayi searching sunanshi a Google nan taga biography nashi da pictures dinshi ta Fara saving tun daka ranan ta fara kallon Ball kabir kuma ya zama abokinta kullum suna cikin waya yaushe za'ayi premier league sometimes ma har Gidan ball take zuwa taga koh an rubuta in Man u za suyi wasa tun bata fadin manufarta ba harta fara gaya wai ita shi zata aura Mum dinta inta fara maganan tsaki takeyi tace bata da hankali Dad dinta kam biye mata yakeyi in Mum dinta taji hakan sai tabar musu wajan dan ba zata iya jin wannan shirmen na jawaheer ba in banda abunta ina ita ina farin fata bature mai kyamar bakin fata yau koh kasar su kaje haka za suyi ta nuna maka kyama musamman ma idan suka ganka bakin fata ita gwara jawaheer dinma fara ce sol, duk wani receiver jawaheer tasa ansa a Gidan dan kawai saboda kallon ball dakinta ta manne shi da hotunan m samir duka Khalil dan Manchester United ne kabir kuma dan Madrid suna ce mai Ozil sai itama jawaheer yar Manchester United ce da M samir laliga suka siyeshi ya koma Barcelona itama tabar man u ta dawo Barcelona dan ita M samir take bi, jawaheer bata kula ko wani saurayi saboda a ce warta m samir zata Aura wannan shine labarin jawaheer bari mu dawo kan labari.




















Koda suka isa gidan kallon ball cike yake da mutane makil duk maza jawaheer tsayawa tayi tana tunanin yanda zata shiga kallon kabir tayi tace Ozil taya zan shiga?bude kofar motar yayi tare da fadin ina zuwa fita yayi jim kadan sai gashi yace mata ta fito, fita tayi ta bishi sukai ciki Ashe Gidan kallon ball din waje2 ne akwai na yaku bayi akwai na masu hali kuma yana da girma daki daya suka zauna ita da kabir babu kowa a ciki gashi har anyi nisa, Madrid suna cin daya Barcelona kuma 0 ana 1-0 jawaheer kallo takeyi amma kaman za tayi kuka dan takaici domin su ake ci shiko kabir sune suka ci, M samir ne ya buga wata kwallo ta shige Raga ihu ta saki tare da fadin a gooooooo wow my Luv ina sonka shiko kabir shuru yayi tare dajin haushin cin da Barcelona sukayi yanzu sun dawo 1-1 har akaje half time babu wanda ya kara ci suna nan zaune ita da kabir suna fira har aka dawo, ci gaba akayi da kallo Real Madrid ne suka kara ci jawaheer kam haushi kaman ya kashe ta ana cikin haka aka buge m samir ya fadi kasa tare da rike kafar shi jawaheer bata san lokacin data fara kuka ba buguwan sosai yayi dan haka dole aka cire shi aka sa wani jawaheer ganin haka yasa ta fara kuka Dan tasan m samir ba karamin buguwa yayi ba wanda yasa har ya kasa tashi fita tayi daka Gidan kallon da gudu tana kuka tare dajin radadi cikin zuciyarta mota ta shiga kabir yazo ya sameta yana fadin haba jawaheer maiya sameki kuma kinga kun kara ci ma, tace kabir baka ga anji ma my samir ciwo ba har an cire shi mai yasa bazan yi kuka ba? Kabir yace haba jawaheer aiba wani serious ciwo bane, tace what ba serious ciwo bane kana ganin har an cire shi kuka ta kuma Saki tare da fadin dan Allah shigo mu koma Gida kabir kafin zuciya na ta buga kabir cikin tausayin kanwar tashi kuma kawarshi tunda yanzu sunfi shiri ma akan Khalil shiga motar yayi ya kunna suka tafi babu abunda kake ji sai kukan jawaheer hmmmm.


















*Maryam obam*
[01/01, 13:31] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
















Page 3


















A haka suka Isa gida yana fakawa ta fita da gudu tayi hanyar falo a hanya suka hadu da khalil tareta yayi yana fadin jawaheer kukan miye haka kufa kuka ci wasan kun cire madrid cikin kuka tace bros baka ga anji ma M samir ciwo ba, kallonta yayi na second biyar sannan yace kiyi hakuri kibar wannan kukan zai tashi a next wasa zaki ganshi dago kai tayi tace dagaske? Kai ya daga mata alaman eh yace dawa zaku buga next tace *CELTA DE VIGO* yace ok karki damu ki daina wannan kukan kabir na gefe yana kallonsu dakyar tayi shuru ta shiga ciki ido ya bita dashi yana tausayin kanwar tashi da yake ganin abun nata ya wuce tunaninshi dan shi dauka yake duk abunda take fada wasa ne amma yanzu abun ya fara bashi tsoro, kabir ne ya dafa shi tare da fadin kaga sis gaba daya hankalinta ya tashi, khalil yace ozil abun jawaheer ya fara bani tsoro fah kalla yanda take kuka dan kawai anjima M samir ciwo, kabir yace hakane amma jawaheer tana sonshi ne kaga duk abunda ya faru dashi dole taji wani iri ,khalil yace haba kabir irin wannan son yayi yawa kalla fah yanda tazo hankali tashe tana kuka, kabir yace kasan masoyi baya san ganin masoyinshi cikin wani hali, khalil tsaki yayi tare da fadin wlh abun yana ban mamaki in banda jawaheer ita da take Nigeria yar Africa ina ita ina wani bature wanda ko mutuwa za tayi bazai iya cewa yana sonta ba balle yace zai aureta haba aishi nasan bazai iya bama ace celebrity ya auri yar africa yar nigeria kuma gashi bature impossible abun kunya ne a gareshi, kawai dai sis na son daura ma kanta abunda yafi karfinta ne kawai, kabir yace haba khalil miye abun kunya a cikin SO wlh so ya wuce duk yanda kake tunani shifa so babu ruwanshi da addini launin fata, ka duba ka gani musulmi yake auran christen sannan turawa nawa ne suke auran yan africa..... Khalil ne ya dakatar dashi tare da fadin inma bature ya auri yar africa toni ban taba gani ba mutanan da suke kyamar bakar fata duk da jawaheer fara ce ita yar africa ce kuma idan suka tashi jam'u zasuyi suce bakar fata yan africa so kaga duk daya ne sannan shifa M samir duk duniya an sanshi sai kawai ace gashi yana auran yar Nigeria haba impossible mu ma bar wannan maganan kawai ,kabir yace bari kaji khalil abunda nake so ka fahimta shifa so babu ruwanshi sai kaga namiji handsome amma idan kaga matarshi sai kaji wani iri dan muni, haka sai kaga mace mai kyau amma mijinta mummuna kaman a yanka shi a boye wukan dan muni, toh kaga shi so babu ruwanshi da launin fata kyau muni kawai idan zuciya taji ta kamu toh babu ruwan mutum da duk abunda wani zaice, khalil murmushi yayi kawai tare da fadin kasan waye M samir kuwa world celebrity ne wanda ganinshi kawai tashin hankali ne sannan idan ya fito mutane zagayeshi sukeyi tako ina duk da yawan security din da suke zagaye dashi ko kasan yawan billions din da yake samu duk month banda na business dinshi da ake mai? Kabir ka daina yaudaran kanka wlh M samir yafi karfin jawaheer duk da jawaheer babu namijin da zai ganta baiyi burin auranta ba ,amma farin fata bature bazai auri jawaheer ba dan turawa suna kyaman mu sosai, kabir yace hmm khalil M samir musulmi ne bana tunanin zai kyamaci musulmai koda kuwa yan africa ne.... Khalil yace kai ni maganan nan ta isheni muje ka raka ni,kabir yace yunwa nake ji wlh ka bari inje ciki inci food din mum sai mu fita khalil tsaki ya danyi tare da fadin kazo muje mana ba dadewa zanyi ba haka kabir ya bishi suka fita tare.








Koda jawaheer ta shiga cikin falon gidan taga mum dinta da dad da gudu ta fada jikin dad din nata tana kuka cikin damuwa iyayen nata suke tambayanta ko lfya mai aka mata? Cikin kuka tace dad anjima M samir ciwo mum tsaki tayi tare da kawar dakai daka kallonsu da takeyi dan tasha ko wani abu aka mata da farko ashe shirmenta ne data saba dan haka mum take daukan duk wani abu nata indai akan M samir ne, dad ya kalli mum yace haba bilkisu mai yasa kike irin haka kina ganin yarinya ta shigo cikin wannan halin sai ki dinga sakar mata tsaki ,tace toh mai zance? Indai akan wannan shirmen ne na jawaheer bani da abun cewa sai dai tsakin yarinya kullum bata da aiki sai fadin M samir M samir haba dan Allah ,jawaheer jin haka yasa ta kara fashewa da kuka dad yace yakuri J ki kyale mum dinki sannan M samir zai tashi insha Allah cikin shagwaba tace dad dagaske? Kai ya daga ya kuma cewa insha Allah, hawayen fuskanta ta goge tare da fadin dad dan Allah yaushe zaka hadani dashi? Murmushi yayi tare da fadin Ambassador dinmu na kasar Spain bashi da lafiya yana asibiti munyi magana idan ya warke zai fadamin sai ya hadaku dariya ta saki tare da fadin kai dad ina sonka sosai dad idan ya ganni zaiji yana sona kuwa? Mum tsaki tayi ta tashi tabar wajan dan takaici shiko dad ci gaba yayi da sauraran yar tashi yace sosai kuwa ai nasan idan ya ganki saiya rude sosai dan babu wanda zaiga my daughter yace bata mai kyau ba ,jawaheer cikin jin dadi tace dad kaga idan muka hadu ina gama skul sai ayi bikin mu koh?dariya dad yayi yace duk yanda kika tsara hakan za'ayi tashi dad yayi tare da fadin bari in fita ina da meeting karfe 6 kice ma mum dinki na fita tace ok dad take care yace i will my dear fita yayi ita kuma ta nufi dakin mum din nata ,a zaune taga mum tayi tagumi jawaheer tace mum lfya kuwa? Mum ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yauwa zo nan ki zauna bayan jawaheer ta zauna kusa da mum take cewa dad yace in fada miki ya fita,kai mum ta daga alaman toh, sannan ta kalli yar tata tace jawaheer wai yaushe zaki gane kin girma ne? Yaushe zaki farka daka wannan mahaukacin mafarkin da kikeyi ne? Shifa wannan mutumin da kike hauka a kanshi bai sanki ba yau ki duba shekarunki ishirin a duniya amma baki da saurayi tsayayye duk masu sonki in sunzo sai ki koresu yaushe zaki fahimci cewa shi wanda kike hauka a kansa bazai iya auranki ba..... Kukan jawaheer din ne yasa mum yin shiru tana kallonta cikin kuka tace mum ba mafarki nakeyi ba Mum kema kin san M samir gaskiya ne yana cikin duniyar mu kinga mum shiba mafarki bane mum bana jin zan iya auran ko wani namiji inba M samir ba wlh mum shi nake so inama zan iya nunama duniya zuciya ta taga irin son da nake mishi mum ko kin san idan ban sami M samir ba zaku iya rasani mum wlh ina cikin hayyacina tsantsar sonshi ne yasa nake duk wannan abun mum ki fahimce ni..... Salati mum ta saki tare da fadin nashiga uku wlh jawaheer kin samu tabin kwakwalwa..... Tace mum lafiya na qalau babu abunda ya sami kwakwalwa na ,mum cikin tausayi tace inko babu abunda ya sami kwakwalwanki toh wlh kinyi gamo ne cikin biyun nan dole akwai daya ban taba ganin irin wannan masifan ba dan Allah jawaheer ki cire wannan abun indai kina so in tabbatar da kina cikin hankalinki, kuka jawaheer ta kuma saki tare da fadin mum nayi kokarin inyi hakan amma na kasa mum idan ban auri M samir ba mum bana tunanin iya ci gaba da rayuwa na mari mum ta sakar mata ji kake tas.......














*comment dinku yana min kadan sannan plz sharhi nake bukata ba thx ba dan yana da matukar amfani*


















*maryam obam*
[02/01, 14:23] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
















Page 4














Rike wajan tayi tana hawaye mum tace jawaheer ki farka daka wannan mafarkin da bazai taba zama gskya ba, keba yarinya bace ki daina yaudaran kanki kuka mum ta saki itama ta fara magana cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi tace jawaheer ke daya ce y'ata mace ina sonki fiye da yanda kike tunani bana son duk wani abu da zai saki cikin damuwa koya taba lafiyanki nafi kowa son inga yau kin sami abunda kike so amma wannan abunda kike so bamai yihuwa bane dan Allah jawaheer ki cire wannan kwallon a ranki da shi dan kwallon da kike so ki nutsu ki fitar da miji cikin manemanki kiyi aure idan kikayi aure hankalinki zai kwanta zaki manta da wani M samir, kai jawaheer ta fara girgizawa tare da fadin kiyi hakuri mum inama zan iya hakan da nayi farin ciki Allah ya sakamin son M samir bana iya ganin zan iya rayuwa da wani namiji inba shiba mum ki fahimce ni ban taba kin duk wani abu da kika fadamin ba wannan yafi karfina ne son M samir a jini na yake wlh mum Allah shine daya koh toh idan ban sami M samir ba zan iya mutuwa tana fadin haka ta tashi tabar dakin mum din nata da gudu tana kuka itama mum din kuka ta saki tare da fadin wlh jawaheer tayi gamo dole insa ayi mata addu'a na shiga uku wannan wani irin bala'i ne ita kuma irin tata jarabawan kenan son bature wanda suke kyamar yan africa suke kiran yan africa animals mum daukan wayanta tayi ta kira maman kabir hjy hauwa, bayan ta dauka suka gaisa hjy hauwa tace bilkisu lfya kuwa naji muryanki kaman kina cikin damuwa? Tace hmmm hauwa kedai bari kawai wlh jawaheer tana son sani cikin damuwa maganan nan bata waya bace kina gida yanzu in shigo? Hjy hauwa tace ina nan ki bari bari ni

Please Login or Register in order to submit comment