Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi bacci da wuri ba ina ta tunani, tace tunani kuma? Yace eh, shuru tayi tana dan nazari shi kuma idanshi na kanta, katseta yayi da fadin ina mum? Tace tana ciki shiga yayi itama binshi tayi a baya tana shiga tayi daki, mai ta shafa cikin kayan mum ta dauko jallabiya tasa duk da ya mata yawa amma haka tasa, tana zaune tana jiyo firan mum da dan nata, uncle abubakar ya shigo, nan firan ta canza zuwa na ball, mum tace bada ita ba, jawaheer kwanciya tayi amma ba bacci takeyi ba, kawai tana tunani ne, tunda tasan basu mum bane iyayenta take jin wani iri saita tsinta kanta da rashin sakewa kusa dasu, harta dad bata sakewa in yana wajan sabanin da, wani zubin in abun nata ya tashi haka zatai ta shagwabe ma dad dinta wanda a yanzu bata jin zata iyama fira dashi kaman da, wani guntun hawaye ne ya zubo mata, babu komai a ranta sai bakin ciki tare da takaicin mai yasa basu kasance iyayenta na gaskiya ba, mum ce ta shigo dakin hannuta dauke da tray, ganin tana kuka yasa mum tayi saurin karasawa wajanta tana fadin jawaheer mai ya sameki?? Tayi saurin goge hawayen tare da fadin babu komai mum, ido mum ta kura mata tare da fadin jawaheer nasan abunda kike tunani bazai wuce kice bamu bane iyayenki, tun ranan da kika san haka kika rage yin magana damu, kika daina sakewa a gaban mu, jawaheer wlh dai dai da rana daya ban taba cireki a raina ba, har gobe ina miki kallon yar dana haifa a ciki na, mai yasa kema ba zaki daukemu a matsayin iyaye ba jawaheer?? Kuka jawaheer ta kara fashewa dashi tare da rungume mum tana fadin ba haka bane mum har gobe kune iyayena kawai ina takaicin daya kasance baku kuka haifeni ba, amma ban taba canzaku daka matsayin da kuke ba, mum tace toh kiyi shuru ga abinci kici sai kizo muje falo ayi fira dake, bata musa ba ta dauki cup din tea da white rice ns stew ta fara ci, mum tana zaune harta gama ci, duk da ba wani da yawa taci ba, amma tasha tea din da yawa, mum ta dauko mata magani tasha, sannan suka fita falo, tunda ta fito idanshi na kanta harta zauna, akan kujeran dake kallon nashi, gaida uncle abubakar tayi ya amsa tare da tambayanta ya jikin nata? Tace da sauki alhmdlh, murmushi yayi tare da fadin badai ciwon bane yasa kika rame kayan naga ya miki yawa, itama murmushin tayi wanda ya kara fito mata da kyanta, tace a'a kayan mum ne nawa yana hotel din da muka sauka, adda ce ta shigo da kayan jawaheer tana fadin ga wasu da kika canza a asibti na wanke miki su, tace lah adda wanki kuma, keda kanki? Adda tace gasu maza kije kisa sai kuje ki dauko sauran, bata musa ba ta tashi ta nufi daki dan canza kaya, jim kadan sai gata ta fito cikin hijab, ido m samir ya bita dashi dan ba karamin kyau hijab din ya mata ba, mum tayi murmushi tace jawaheer hijab na miki kyau amma bakya son sawa, murmushi tayi, tana kokarin zama taji muryan m samir na fadin muje mu dawo, dan haka bata karasa zaman ba suka fita, security din na ganinsu suka bude musu baya suka shige, kai tsaye hotel din suka nufa har suka karasa babu mai ma dan uwanshi magana, har suka shiga ciki ta nufi dakin data sauka ta fara hada kayanta tana cikin hadawa ya shigo dakin ya hade hannunshi biyu a kirjinshi ido ta dago suka hada murmushi ya sakan mata tare da nufanta ya zauna kusa da ita, ita dai bata cemai komai ba tana ta hada kayanta, hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi kirjinta ya fara bugawa da karfi fuskanta ya dago suna kallon juna ido ta rufe da sauri amma tana jin saukan numfashin shi, jin muryanshi tayi yana fadin kina fushi dani ne? Ido ta bude da sauri ganin har yanzu ita yake kallo yasa ta kara rufe idonta murmushi yayi tare da fadin sunanta jawaheer bata amsa ba haka bata bude ido ba, yace mai yasa kike fushi dani, ido ta bude tare dayin kasa da kanta, ganin haka ya kara janyota jikinshi yace fadamin, tace niba fushi nake dakai ba, yace to mai yasa bakya son yin magana dani yau? Tace ba haka bane , yace toh miye? Dariya ta saki tare da fadin babu komai kawai bana son yin magana ne yau, yace har dani bakya son yin magana? Kai ta daga alaman eh, murmushi yayi tare da sakinta ya tashi tsaye yace ok kiyi hakuri da takura miki da nayi akan saina miki magana, in kin gama ki sameni a mota, da sauri tace to wazai fito min da kayan? Yace keda kanki mana tunda baki son a dameki, murmushi tayi tare da tashi tayi hugging dinshi ta baya tace sorry ba haka nake nufi ba, kana daya daka cikin mutane masu muhimmanci a rayuwa na, koda zan zauna daka ni sai kai bazaka taba gundura na ba, waigowa yayi tare da fadin really? Kai ta daga mai alaman eh, hancinta yaja tare da fadin zo in tayaki hada kayan, zama yayi suna ta hada kayan har suka gama, ya kira masu aikin hotel din suka fara fitar sa kayan zuwa mota, suma fita sukayi ya kalleta yace yau kinyi kyau, tace nagode, bayan sun shiga mota yace ma jawaheer ina ake saida sim? Dariya tayi tace nima ban taba zuwa state din nan ba, amma muje mtn office, tace ma driver suje mtn office yace ok, hannunta ya kamo tare da fadin kema zaki canza naki sim din, da sauri ta dago tana kallonshi tare da fadin saboda me?? Shuru ya mata ba tare daya bata amsa ba, har suka karasa mtn office, fita sukayi suka shiga wani office aka kaisu daka shi sai jawaheer, jim kadan sai ga wani ya shigo yana bama m samir hannu tare da fadin ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa yau gani gaka, m samir yayi murmushi mutumin yace plz zamu iya daukan hoto? M samir yace ok nan mutumin ya fara daukansu, sannan ya tambayi m samir mai yake so yace sim card guda biyu sannan yana son number shigen iri daya, mutumin ya dauko sim biyu ya bashi, special number karshen ne kawai ya ban banta, daya 7 daya 8, nan aka mishi register dayan ma da sunanshi akayi, har aka gama suka fito, nan mutane suka fara ihu tare da daukanshi hoto, dakyar security dinshi suka fitar dashi sukai mota, suna cikin tafiya ya kalli jawaheer yace bani wayanki? Kallonshi tayi ba tare da tace mishi komai ba kota miqa mai, hannu ya miqa mata ganin haka yasa ta bashi wayan, hannu yasa a kunnenta ya ciro dan kunnenta ya ciro abun sim din, ya cire nata yasa mata sabon daya, shima yasa daya a nashi, sai daya gama ya miqa mata wayanta tare da karya sim dinta, da ido ta bishi tana son yi mishi magana amma taga ya daure fuska ganin haka yasa tayi shuru tare da mamakin mai yasa ya mata haka, bai karayi mata magana ba har suka karasa gida, security dinshi suka fara shigar mata da kayan, itama ko kallonshi batai ba tayi cikin gida dan karya mata sim da yayi ba tare da wani dalili ba abun ya bata haushi, yana kallonta ya bita da murmushi dan yasan taji haushi, amma shi daya yasan dalilin da yasa yayi hakan, koda ta shiga a tsakar gida taga adda ita da mlm, bayan ta musu sannu da gida, tace ina mum? Adda tace ta fita ita da babanki basu dade da fita ba, m samir shima ya shigi gidan, tana ganinshi tayi ciki, adda tace toh ni yanzu bajin yaranka nake ba, ta kwada ma jawaheer kira tazo da sauri, adda tace taya zaki shige ciki bayan kin san mu bama jin turanci, fada mishi ya tayaki shigar da kayan, kallonshi tayi wanda shima itama din yake kallo yana mamakin fushin da takeyi dan an karya mata sim, tace ance wai ka tayani shigar da kaya, murmushi yayi tare da daukan akwati itama ta dauki wasu suka shigar dasu haka har suka gama kwashewa mlm ya fita daka gidan dan komawa kasuwa, itama adda ta nufi dakinta, ya rage daka m samir sai jawaheer a falo wanda sukai shuru su dukansu, tashi yayi ya matso kusa da ita, yace mai yasa kike fushi? Mai akayi miki? Tana son ta tambayeshi mai yasa ya karya mata sim amma saita kasa dan ya mata wani irin kwarjini, ganin tayi shuru yace saboda na karya miki sim kike fushi koh? Toh idan na kwace wayan fah????........
























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 31-32


















Kallonshi tayi ya sakar mata murmushi tare da daga mata gira, yace jawaheer banso ana damunki sai yasa na canza miki sim nd kuma ban san any abu da zai daga miki hankali kin san abubuwan da suka faru na sanin basu mum bane iyayenki kin san tunda maganan nan ta fito kowa zaiji, nd kuma nasa wasu za suyi ta kiranki dan suji maike faruwa, banso wani koh wata su daga miki hankali har zuwa sanda zamu gano inda iyayenki suke, hannunta biyu ya kamo ya matse tare da fadin sai yasa na karya layin, murmushi tayi tare da fadin banyi fushi ba, kawai na dan damune akan mai yasa ka karya sim din ba tare da kamin bayani ba, amma yanzu da naji komai sai naji hankalina ya kwanta komai kuma ya wuce, yace dat my sister, yaushe zamu tafi abuja? Tace ba kace sai anyi kwana biyu ba,yace yes inaso in saba da kakanninmu gashi kuma bana jin yaranku, tace bari in fara koya maka, yace yauwa amma ba'a nan ba, kizo mu tafi waje, tace ok bari in canza kaya, yace ok ki sameni mota, daki ta shiga tasa wata jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan, ta nufi dakin adda taga tana bacci dan haka ta fita kawai tana shiga mota taga anja bata cemai komai ba har suka isa wani hadaddan restaurant babu kowa sai su kadai daka gani yasa an kama mai wajan ne duka, shiga sukayi suka zauna, kallonshi tayi tace mai za muyi a nan? Yace abinci zanci kin san ba komai na iya ciba, nd ke kuma baki damu damai naci ba, tayi narai narai da ido tace nifa kasan bani da lafiya ba yau na dawo gida bama, murmushi yayi yace hakane, my baby da sauri ta dago ta kalleshi hada ido sukayi ita tana mamakin sunan daya kirata dashi, shiko yana mamakin mai yasa kullum jawaheer take kara kyau, idan yaga ta mishi kyau yanzu anjima kuma sai tafi kyau,hura mata fuska yayi tayi firgit tasa hannunta ta rufe fuska tana dariya, dai dai lokacin masu saida abincin wajan suka zo suna tambaya mai za'a kawo musu, fada musu yayi ita tace tuwon semo miyan kuka, suka tafi, basu dade ba suka kawo abincin, sannan suka roqeshi akan su dauki hoto dashi, bai musa ba haka ya tashi suka dauka, suna ta murna, zama yayi yana kallon abunda jawaheer zata ci, lokaci daya kuma yayi dariya yace jawaheer miye haka? Tace mene? Yace wannan abun da zaki ci miye? Tace tuwo, kasa fadan sunan yayi, tace ka gwada ci akwai dadi sosai, kai ya girgiza alaman a'a, murmushi tayi ta fara ci, mai yakon yaci nashi saiya tsaya kallonta yanda take ci sai yaji abun ya burgeshi, dan haka shima yasa spoon cikin tuwan yaci ido ta kura mishi, taga ya cinye ya kara ci wasa wasa sai gashi ya cinye tuwan duka, saida ya gama yace ashe akwai dadi sosai dariya tayi tace abincin mu yana da dadi, murmushi yayi sannan ya fara cin farfesun kazan da aka hado mata dashi bai wani ci da yawa ba ya ajiye tare da kallonta yace ban taba cin abinci mai yawa irin haka ba, dariya tayi tace dan wannan abincin shine mai yawa? Yace eh mana, yace toh a fara koyamin hausa, tace mai kake so ka koya?? Yace komai amma nafi son in fara koyan gaisuwa, nan ta fara koya mai gaisuwa tana fada mai da turanci saita fassara mai, sannan ta koya mai tambayan abu, da wasu yan abubuwa, murmushi yayi tare da kunna wayanshi taji magananta ashe recording yayi, kokarin kwace wayan ta farayi wai zata goge garin haka ta fada jikinshi sukai qasa, wani irin yanayi dukansu suka shiga musamman ma shi, domin kirjinta ne ke kwance akan jikinshi, ganin irin kallon da yake mata yasa ta tashi da sauru tare da fadin kayi hakuri, baice mata komai ba harya tashi sannan yace baki ji ciwo ba? Kai ta daga mishi alaman eh, cikin sanyin murya tace muje gida dare ya farayi, tashi yayi yace muje, mota suka shiga aka sauketa kaman bazai fita ba komai ya tuna oho ya fito har kofan gidan ya kaita sannan yace mata saida safe, bata bashi amsaba ta shige, a falo ta tarar dasu mum harda dad, mum tana ganinta tace jawaheer daka ina kike maiya sami wayanki? Tace mum muna tare da m samir sannan na canza number ne, ido dad ya bita dashi yace saboda me kika canza number kuma baki bamu ba, tace dad m samir ya siya mana dazu nan ta fada musu number din suka saka, dad yace zai tafi hotel din daya sauka mum ta rakashi jawaheer kuma tayi dakin da take kwana ita da mum.










M samir koda ya isa an kira sallah isha'i dan haka saida yayi sallah sannan yayi wanka ya kwanta, amma kuma sai me?? Tunanin jawaheer ne cike a ranshi, musamman dazu data fado mishi jiki ido ya lumshe tare da fadin maike damuna? Kanwata ce da sauri yace no bazan iya ba kanwata ce kawai sabuwan da mukayi ne yasa nake jin wani abu but zanyi dan nesa da ita, duk yanda yaso ya cire tunanin jawaheer ya kasa daka karshe recording din da yayi ya kunna yana jin muryanta yana dariya har bacci ya daukeshi.












Itama ta gefen jawaheer tunanin nashi tai tayi ga wani irin azabban sonshi dake kara shiganta, Allah ya sani tana hakuri da irin son da take mishi amma ya kasa fahimta wani lokacin har tunani take inda zaice ta bashi jikinta zata iya bashi dan dai kawai yasan tana sonshi, duk da wani lokacin tana kokarin cire shi a ranta amma ina abun ya gagara sai dai kullum tayi sallah tana roqan Allah mafi alkhairi.










Washe gari da safe jawaheer ta tashi da wuri, ita ta share tsakar gidan tare da hada kayan wanke wanke ta wanke su tas, adda ta fito tace jawaheer keda baki da lafiya inake ina aiki? Mai makon ta bata amsa saita gaidata da fadin ina kwana adda, murmushi adda tayi tace lfya ya karfin jikin naki? Tace alhmdlh naji sauki, adda tace haka akeso Allah ya kara mana lfya, tace ameen yar tsohuwa, dariya adda tayi tace aina fiki kyan jiki, jawaheer tace wa tab aida ban sami samari ba, adda tace ina samarin tunda kika zo banji anyi sallama ba, niko sanda ina budurwa zo kiga layi, jawaheer dariya take tayi tana fadin ba wani layi kakana kadai ke zuwa inna aureshi nasa ya sallameki dan kin mai tsufa, mum ce ta fito tana dariya tare da fadin ina kwana adda, adda ta amsa cikin fara'a tare da fadin kinga yar nema sauki ya samu zata damemu da surutu, mum dariya tayi dan harga Allah taji dadin yanda jawaheer ta sake yau har take ta fira, wanda rabonta data sake irin haka tunda tasan basu bane iyayenta amma yau gashi tana ta surutu, mum tace adda ina zan sami waina shi nake son ci yau, adda tace shine tun jiya baki magana ba aida anyi yau,kira abubakar ya siyo miki, tace toh daki ta koma ta dauko wayanta ta kira abubakar, sannan ta dawo tsakar gida inna adda da jawaheer keta kulla alale, suna fira, ita hannu tasa ta taya su, har suka gama jawaheer ta daura akan murhu, har alalan yayi suka faraci amma banda mum dan tana jiran waina, sallaman abubakar ne yasa su duka suka daga kai, amsawa sukayi sannan ya shigo ya ajiye cooler din tare da gaida adda, itama mum gaidashi tayi sannan itama jawaheer, bayan ya amsa yake tambayan jawaheer ina m samir bai zo bane? Tace eh bai zo ba uncle, murmushi yayi tare da fadin bari inje in shirya yau yace yawo zamu tare, mum tace yadai kamata shima yaga gari da irin al'adunsu, harya tashi zai fita ya dawi tare da tambayan ina mlm mahaifinsu kenan, adda tace yana bacci, yace mai gari jiya ya ganni yake tambaya na wai dagaske khausar ta dawo gari, nace mishi eh yace shine mlm bai fada mishi ba, nace toh nima ban san dalilin hakan ba nayi tafiya ta, mum tayi dan murmushin takaici tare da fadin naga kasar nan ta kowa ce kuma kowa zai iya zuwa inda yake so, koda can baya rashin sanin yanci nane yasa akamin haka, adda tace Allah dai ya kyauta suka amsa da ameen, sannan abubakar ya fita, jawaheer kam bayan ta tattare kayan da suka ci abinci ta wanke daki ta koma tayi kwanciyanta tare da tunanin m samir, haka taita zama a daki har wajan karfe daya ta fito tayi alwala ta koma tayi sallah, bayan ta idar taji mum na kiranta fita tayi tace mum gani, mum tace kije kici abinci mana, kin shige daki ko dai jikin ne? Tace a'a mum tashi tayi taje ta zuba abinci kadan ta zauna kusa da mum tana ci tana tunanin ina ma mum ce mamanta ta gaskiya da tafi kowa farin ciki, ajiye abincin tayi dan taji yana mata daci, mum tace badai wai har kin koshi ba? Tace eh mum bana jin yunwa sosai, shuru mum tayi dan tasan halin jawaheer ba'a matsa mata akan abu yanzu ta fara kuka, jawaheer damuwa ya mata yawa na rashin ganin m samir haka taita zama har yamma amma shuru bai leqo gidan ba, har mum da dad suka fita koda dad yazo yace ta bisu taki yarda ta bisu tace suje, tana zaune a falo adda ta zauna kusa da ita, duk tana lura da jawaheer tace jawaheer nikam wani irin so kikema wannan yaron haka? Jawaheer tayi dan murmushi tare da fadin adda niwa nake so? Adda tayi dariyan manya tace kaji ja'ira, bayan keda bakinki kin fada munji ko kin manta ne? Jawaheer tace kai ku tsofaffin nan bakwa mantuwa wlh, adda tace jawaheer naga kaman shi bawai yana sonki bane, irin yanda ke kike sonshi, amma zan baki shawara duk da nasan miye so ya kuma akeji dan nima auran so nayi duk da a lokacin ba'ayi, hada ku akeyi sai akaci sa'a muna son juna, ya kamata kibama wani namiji dama dan ya shiga cikin rayuwanki sannan ki nunama samir kema a matsayin dan uwa yake a wajanki yanda shima yake nunawa, ji jaraba wannan abun guda biyu idan kikayi zan kara miki wasu, jawaheer tayi dariya tace zan gwada yar tsohuwa suna zaune kam sai gashi wani yaro yayi sallama, wai ana kiran jawaheer, kallon juna sukayi ita da adda, sannan adda tace kaje kace tana zuwa, yaron ya fita jawaheer tace adda taya zani bayan ban san ko waye bane? Adda tace sai yasa nace kije ki gani, tashi tayi daka ita sai dogon wando da top amma yakai mata giwa sai wani dan shara sharan gyale ta yane kanta dashi, fita tayi taga wata mota kiran matrix tsayawa tayi sai taga an bude motar wannan dr din ta gani wanda ya dubata a asibiti, da murmushi akan fuskanshi yace bismillah ki shigo ciki mana, tace nan ma ya isa ai yace ba mutunci bane mu tsaya a waje...... Hasken mota ne ya hasko su, motocin m samir ne da security dinshi tun daka nesa ya hangosu suna tsaye, bayan motar ta tsaya ya fito zai wuce dr yace m samir tsayawa yayi tare da fadin dr ya aiki? Dr yace lfya tare da miga mai hannu suka gaisa hada ido sukayi da jawaheer wani irin kallo ya mata mai kama da harara, sannan ya shige ciki, dr yace shigo muyi magana, jiki a sanyaye ta shiga ciki,yace nazo inji ya jikin ki? Tace na warke nan ya fara mata surutai wanda gaba daya bama jinsa take ba, shiko m samir yana shiga yaga babu kowa sai adda ya gaidata da hausa tana ta mamaki tare sa fadin sai anjima kallo ta bishi dashi dan mamaki harya fice bata ce komai ba, koda ya fita yaga sun shige mota tsaki yayi tare da kawar da kanshi gefe ya shige mota akaja suka bar wajan.......






















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 33-34














Jawaheer kam bata Jin komai na abunda dr yake fada mata, shima kaman ya lura da hakan yasa yace mata bari ya barta yaga kaman ta gaji, hakan ya mata dadi yace ta bashi number dinta, bashi tayi sannan ya bata ledoji manya guda biyu daya kawo mata, amsa tayi tare dayi mishi godiya sannan ta fita tayi gida, a falo ta tarar da adda tana cin danwake, zama tayi kusa da adda tace adda samir yazo naga bai dade ba ya fita, adda tace hmm aini yau yaban mamaki, kinji hausa gaidani yayi da hausa harda cemin saida safe, jawaheer kam shuru tayi tana tunanin mai yasa ya tafi bai bari ta shigo ba, jin adda tayi ta katse mata tunani da fadin nasan ya ganki keda wani koh? Tace eh adda wannan dr din nanne yazo dubani, kinga yanda ya sakar min harara nan taba adda labarin abunda ya faru, adda tayi murmushi tace jawaheer inaso ki nutsu ki bama wannan dr din lokacinki dan ki nuna ma m samir kema fah akwai masu sonki, jawaheer tace adda shifa dr gaidani yazo yi ba sona yace yakeyi ba, adda tace aida haka zai fada miki, kedai kawai kiyi abunda nace..... Sallaman mum ne ya katse musu firan da sukeyi, jawaheer da fara'a tace mum har kun dawo sannu da zuwa, mum ta amsa tare da fadin dad dinki yace kije yana waje, tashi tayi ta fita ta sami dad a mota, dad yace jawaheer gobe ni zan koma ko akwai abunda kike bukata? Tace a'a dad babu komai sai dai ina son ka canza masu adda gida inda hali, dad yayi murmushi yace naso nayi hakan amma m samir ya rigani dan dazu abubakar yake fadamin fitan da sukayi gida yaje ya siyan musu cikin adamawa, abubakar yace gidan babba ne akwai komai da komai domin gidan wani barawon gwamnati ne wanda ya saci kudi shine gwamnati ta kama gidan ta saida, jawaheer tace kai Allah ya saka mishi da alkhairi, dad ya amsa da ameen, sannan yace an fara biyan kudin aikin haji, zan biya musu sai yasa zan koma ma gobe, sannan ina aiyuka, jawaheer tace Allah ya saka maka da alkhairi dad, murmushi yayi tare da kara son yar tashi ba ita yama abu ba amma tana ta godiya, kudi ya dauko ya bata ta amsa tare da fadin dad nida transfer kamin ma da yafi, dad yace toh riqe wannan din bari in miki transfer din ma, nan ya mata transfer tace kai dad kudin yayi yawa, yace jawaheer kudin da nayi ta sanadinki ne in baki ciba wa zaici, sannan million dari din da mum dinki ta bani lokacin data miqa mana ke, dasu na fara sana'a har nayi mugun arziki inada kalan kudin wajan sau million, na

Please Login or Register in order to submit comment