Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ware miki million dari na ajiye duk sanda naga mahaifiyarki zan bata kudin, wani hawaye ne ya zubo ma jawaheer tare da fadin dad idan na tuna baku kuka haifeni ba ina shiga cikin wani hali, wlh dad zuciya na yana zafi inna tuna hakan dan Allah dad kubar tunamin, ta karasa zancen cikin kuka, ya janyota jikinshi yana bata hakuri tare da fadin jawaheer ke yata ce har gobe, murmushi tayi tare da fadin ngd dad, yace bari inzo in tafi bacci nake ji, tace toh saida safe dad, gida ta koma inda ta sami adda ta fiffito da kayan da dr ya kawo kayan tea ne manyan gwangwani dasu milo sugar kwali dasu biscuit chocolate, mum tace ashe dr yazo dubaki? Tace eh mum, mum tace wannan hidima haka Allah dai ya saka mai, adda ta amsa da ameen, jawaheer kam haushin kayan ma taji tana yi, dan me yasa zai kawo mata suma, tashi tayi ta nufi daki, bata dade da shiga ba mum ta shigo, tace mum ashe samir ya siyama su adda gida? Mum tace eh wlh gobe zamu gidan ma muga in akwai abunda yake bugata duk da abubakar yace basai ansa komai ba, amma gobe zamu mu gani, jawaheer tace Allah ya kaimu, jawaheer ta kasa bacci babu abunda take son ji sai muryan m samir tashi tayi ta fita ta kira number dinshi amma taji ance switch off, tsaki tayi ta koma daki ta kwanta sai juyi take tayi.










Washe gari tunda jawaheer tayi sallah asuba take ta kallon wayanta tana tunanin kota kira m samir ne, amma tana tunanin kaman bai dace ta kirashi yanzu ba, dan safiya ne, haka ta zauna akan dadduma harta fara bacci, bata farka ba sai wajan 9 ta ganta akan gado, murmushi tayi dan tasan mum ce ta kawota gadon, fita tayi ta nufi toilet, tana fitowa taga adda tace ga ruwan wanka nan dama yanzu zan kiraki, jawaheer tace toh yar tsohuwa, ansan ruwan tayi ta shiga toilet din, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atamfa riga da skirt ya mata bala'in kyau kaman ba itaba, adda tace kai jawaheer atamfan nan ta miki kyau amma na lura dake kaman ke bakya son irin wannan kayan kin fison kiyi ta shiga kaman ba musulma ba, dariya jawaheer tayi tace lah nice ba musulma ba? To a kunnen mai gidan, dai2 lokacin mlm ya fito yace kyaleta amarya ta kishi takeyi dariya adda tayi tace ni na yafe mata kai, jawaheer tace kaji kishin koh kaman dagaske take, dariya duka sukayi mlm yace yaushe zaku gidan? Mum tace anjima kadan abubakar muke jir..... Bata rufe baki ba saiga sallaman abubakar da m samir sun shigo, gaban jawaheer ne ya fadi kallo daya ya mata ya kawar da kanshi, gaida su mum yayi, itama jawaheer ta gaida uncle dinta, ya amsa sannan ta gaida m samir wanda ya amsa a dakile ba tare daya ko kalleta ba, mum tace ma m samir yaci abinci kuwa? Yace a'a tace ai naga alama murmushi yayi mum ta kalli jawaheer tace kema kije kici abinci kafin mu tafi, sannan ki dauko m samir kayan tea tace to, kitchen din adda ta nufa ta hada mishi kayan tea tare da soya mai akwai, falo takai mai shi daya ne a falon su mum na waje suna fira, ajiye mai tayi tare da fara kokarin hada mishi yace no leave it zanyi da kaina, sororo tayi tare da ajiye spoon din jiki a sanyaye, tana son yin magana taji yana fadin gobe zamu tafi abuja, da sauri ta dago tana kallonshi amma shi ba ita yake kallo ba, tace da wuri haka, bana tunanin zan biku gaskiya wani irin kallo ya mata da yasa tayi saurin yin qasa da kai, adda ce ta shigo tace jawaheer kuyi sauri mana, fada mishi dan Allah tunda baji nama yake ba, cikin sanyin murya tace ance kayi sauri muje, kai ya daga alaman yaji, tashi tayi itama ta fita waje da ido ya bita harta bace mai sannan ya lumshe ido, tana tafiya yaji abincin ya isheshi dan haka tashi yayi ya fita shima, uncle abubakar yace zaije kasuwa bada shi zasu ba, mum da adda suka shiga mota daya jawaheer da m samir kuma mota daya, sai security din dake mara musu baya, sai sharara gudu mota takeyi amma babu mai cewa komai, wayan jawaheer ne ya fara kara dan haka ta duba taga number ne, mamaki tayi toh wa yasan number dinta ita dai tasan bata kira kowa ba, har kiran ya tsinke wani kiran ya kara shigowa ta kalli m samir taga ba ita yake kallo ba dan haka ta dauka, tana dauka taji anyi mata sallama ta amsa yace nasan baki ganeni ba koh? Tace eh, yace dr ne, harga Allah ta manta ta bashi number dinta, tace eyya yaka koma gida? Yace lafiya qalau sai dai na tafi da tunaninki, tayi dan murmushi wanda a dai2 lokacin m samir ya waigo suka hada ido, wani irin kallo ya mata wanda yasa tayi saurin juyar sa kanta gefe, ci gaba tayi da wayan taji an fisge, da sauri ta waigo taga yana watsa mata wani irin kallo, yace dawa kike waya? Tace friend dina, yace ok daka yanzu in zakiyi waya a gabana karki karayin wani yare sai english, bata ce mai komai ba ya jefa mata wayan tare dayin tsaki kadan, bai kara ko kallonta ba balle ya mata magana wayanta ne ya fara kara, ganin number din dr yasa ta kashe wayan gaba daya, tafiya suke har suka karasa wani dangareren gida sukai horn mai gadi ya bude, suka shiga ciki bayan an faka suka fito, m samir yana fita baiko bi takan jawaheer ba ya nufi wajan su mum, jawaheer kam canjin da yake nuna mata ya fara damunta domin taga yana nuna halin ko in kula da ita tun jiya, amma koma dai miye yau sai taji miye dalili, shiga gidan sukayi wani dangareren falo suka shiga wanda yaji kayan more rayuwa, adda salati ta fara tana fadin ina zamu kai wannan gida? Dariya su mum suke ta mata suna fadin adda an zama yan gayu, gidan yayi bala'in haduwa gashi gidan sama, falo biyu ne a 'kasa sai daki daya a kasan, sama kuma falo daya ne sai daki uku a saman, fadin tsaruwan gidan bata bakine, adda harda hawaye tana ta sama m samir albarka tare dasu mum, tace jiba abunda muke ta kyama gashi yazo duniya ya bamu babban kyauta, haja taita mai godiya shidai murmushi yake tayi dan bai san mai take fada ba, adda tace babu abunda za'a sa a gidan hakan ya isa, mum tace shikenan dan itama taga babu abunda gidan yake bukata, haka suka fito da fadin zasu sa ranan dawowa, shiga mota sukayi dan tafiya gida, suna cikin tafiya jawaheer ta kalli m samir tace Allah ya biyaka gidan yayi kyau sosai, banza da ita yayi, ji tayi kaman tayi ihu dan takaici, ta bude baki zata kara magana taji yace mai adda take fada dazu? Dadi taji koba komai ya mata magana, tace godiya take maka tare da addu'a, dan murmushi yayi sannan yace ok, ya ciro wayanshi ya danna wasu numbers jim kadan yace dad yakake, shuru yayi sannan yace dad komai normal nan ya fara bashi labari dad din yaji dadi sosai tare da fadin ina jawaheer baice komai ba taga ya mika mata waya, amsa tayi tare da fadin hello dad yace yarinya ta yakike? Amsawa tayi tare da gaidashi nan suka taba fira tana ta dariya daka karshe sukai sallama, ta mika mai wayan sawa yayi a kunne ban san mai dad din ke fada mishi ba naji yace ok dad ba damuwa gobe zamu koma abuja muma, yana fadin haka sukai sallama, kallon jawaheer yayi suka hada ido murmushi ta sakar mai tare da fadin wai mai nayi maka kake shareni? Dan tsaki yayi tare da fadin babu komai, tace toh mai yasa kake shareni? Yace haka kawai bana son damuwa, sakan baki tayi tana kallonshi wato nice damuwa ma, dan tsaki tayi wanda bata san ya fito ba jin hannunshi tayi a bakinta yaja tare da fadin wa kike ma tsaki? Kasa magana tayi dan ya riqe mata lebe, ganin yanda tayi da ido kaman zatai kuka yasa ya sakan mata bakin tare da fadin karki kara min tsaki i hate it, bata ko kalleshi ba balle yasa ran zata bashi amsa, yau ce rana ta farko daya taba bata haushi, danme zai dinga wani shareta ba tare da tamai komai ba, inda yasan yanda ta shiga cikin damuwa aida bai mata haka ba, ido ta lumshe kaman mai bacci, bini bini ya kalleta ganin kaman tayi bacci yasa ya kura mata ido tare da fadin slp beauty, tafiya mota keyi tana sharara gudu, jin tsayuwar motar ne yasa ta bude ido mai yakon ta ganta a gidan adda saita ganta a hotel din da yake kwana, kallonshi tayi suka hada ido, kawar da kanshi yayi tare da fadin muje, kaman ba zata fita ba, komai ta tuna kuma ta fito suka shiga tana biye dashi a baya, dakin da ta sauka tai niyan nufa taji ya janyota sukai dakinshi akan gadon dakin ya ajiyeta, toilet ya nufa yayi wanka jim kadan sai gashi daka shi sai towel ga kuma wani karami yana goge kanshi dashi, kallonshi tayi, tayi saurin kawar da kai, murmushi yayi tare da matsawa kusa da ita ya mika mata karamin towel din yace gashi ki gogemin, kin amsa tayi ganin haka ya kamo hannunta ya mika mata towel din, yace tashi kimin, bata tashi ba sannan bata mai komai ba, yace saboda niba saurayinki bane? Da sauri ta dago kai ganin yanda ya kafeta da ido yasa tayi saurin tashi tare da fadin zan wuce gida, kafada ya daga alaman ke kika sani, ganin yanda ya mata yasa ta fara kokarin fita har takai bakin kofa taji ya riqota tare da fadin wa yace ki tafi? Tace na gaji da zama a nan ne, yace ok to babu inda zaki yau tare zamu kwana ni dake cikin wannan dakin.......






















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 35-36
















Kallonshi tayi da sauri tare da zare ido, hada ido sukayi yayi saurin kawar dakai tare da tamke fuska, dan murmushin takaici tayi tare da kokarin jan hannunta daka nashi amma ta kasa danya riqeta tam, ganin tana son ya saketa yasa ya kara janyota jikinshi ta fado kanshi, zama sukai akan gado ya kura mata ido na wani lokaci sannan yace miye tsakaninki da dr din nan?? Da sauri ta kalleshi, ganin babu wasa a tare dashi yasa tace babu komai, yace toh mai yazo yi wajanki? Tace yazo ya gaisheni ne kawai, kai ya daga alaman yaji, sannan ya tashi tare da fadin muje muci abinci sai a kaiki gida, da sauri ta tashi kallonta yayi tare da fadin saurin me kikeyi haka? Tace inaso ne inje gida na gaji, baice mata komai ba yayi gaba itama ta bishi, fadama security din inda zasu kaishi yayi, wajan wani hadaddan cin abinci suka nufa, bayan sun zauna a private waje ta kalleshi tace mai yasa baya cin abincin hotel din? Yace hakanan, masu kawo abincin ne suka zo suka tsaya suna jiran su fadi abunda suke so, kallonta yayi yace kalan abincin da kika ci rannan nake so, dariya tayi tace ma mai kawo abincin ya kawo tuwon semo, da farfesun kaza, ita kuma ya kawo mata rice nd stew da garden salad, tafiya yayi jim kadan saiga abincin ko wanne fara cin nashi yayi, ita kam ci take sosai dan sai yanzu ta tuna tun safe babu abunda taci suka fita, har suka gama ta tashi zasu fita ta riqe cikinta tare dayin yar kara, da sauri ya karasa wajanta tare da riqeta yana tambayanta lfya? Tace cikina ke murda min, cikin tashin hankali yace bari muje hspt, tace a'a zai daina bari in huta kad..... Bai gama sauraranta ba ya dagata cak ya fita da ita har mota yace suje hspt wani asibiti suka nufa, nan akai emergency da ita ganin yanda ya daukota yasa suka zata ko emergency ne, dr ne ya shigo dakin ya fara dubata, yace baki ci abinci da wuri ba da kika tashi ci kuma sai kika ci wani abun mai yakon ki fara shan tea, magani dr ya bata tasha, tana sha ko minti biyar batai ba cikin ya daina, sannan dr din ya sallamesu, suna mota ya kalleta yace ya cikin? Tace naji sauki sosai, ido ya kura mata can yace maganan tafiyan mu gobe saiki shirya dan da wuri zamu wuce, tace daka bari mun dan kara kwana biyu a nan, kuma banji mum tayi maganan tafiyan ba, yace dazu mukayi da ita so dan haka tace babu damuwa saiki shirya, shuru tayi ba tare data kara cewa komai ba, ita inda so samu ne ta zauna ta kara kwanaki a nan, suna karasawa kofar gida ta hango dr yana zaune akan motarshi yana danna wayanshi, m samir ya ganshi kallo daya ya mishi ya kawar dakai tare da kallonta yace sai yanzu nasan abunda yasa bakya son tafiya, nd kin dameni zaki tafi gida ashe shike jiranki, tace wlh ni ban san zai...... Shut up ya daka mata tsawa inma kin sani in baki sani ba wannan ba damuwa na bane, the only thing i hate shine karya, kince babu komai tsakaninku mai yazo yi yanzu??? Tace nima ban sani ba kuma bai cemin zaizo ba, yace bani phone dinki, mika mai tayi da sauri ya amsa ya duba yaga wayan a kashe, kallonta yayi tare da miqa mata wayan amma taki amsa ya ajiye mata a jiki tare da fadin mai yasa kika kashe wayan?? Tace hakanan kawai, yace ok tambaya na karshe miye tsakaninki da wancan dr din?? Tace babu komai yazo gaida nine ran nan, yace yanzu kuma mai yazo yi?? Tace nima ban sani ba, janyota yayi jikinshi tare da bude kofar gefenshi ya fito ita ya janyota ta fito ta kofar daya fita daura hannunshi yayi akan kafadanta tare da janyo dayan hannunta yana wasa dashi yajata suka fara tafiya, dr dake zaune m samir yace dr yakake? Dr ya dago yaga jawaheer maqale a jikin m samir nan idanshi ya canza launi dan tsabagen kishi, dakyar ya iya amsa ma m samir, sannan yaja jawaheer sukai ciki, dr kam wani irin takaici ne ya cika shi, suna shiga gidan ya saketa tare da tureta yayi ciki, binshi tayi da ido tana mamakin mai yasa yayi mata haka? Miye dan dr yazo wajanta, shiga itama tayi jiki a sanyaye ta samesu a falo har dashi, suna magana da mum ita kuma adda tana taba mlm labarin gidan, jawaheer gaidasu tayi bayan sun amsa adda tace dr yazo nemanki tun dazu, tace eh na ganshi, wani yaro ne ya shigo da kaya wai gashi a bama jawaheer inji dr, m samir jin an kira sunan jawaheer kuma ance dr ya gane sakon daka dr dinne, dan haka ya tashi da sauri ya amshi ledan, chocolate ne dasu biscuit tsaki yayi tare da bama yaron yace ya tafi dashi, yaron duk da baiji abunda yace ba ya gane ance yaje an bashi ne, mum tace ya zaka bashi bayan na jawaheer ne, yace mum kayan zaki ne kuma ita tana fama da ciwon ciki,so naga babu amfanin amsa, in kuma tana so sai in siya mata wasu, mum wani irin kallo tamai tare da fadin waya gaya maka cikinta na ciwo? Nan yaba mum labarin abunda ya faru da taci abinci, mum tace ai wannan ba komai bane kuma zata iya shan chocolate din, yanzu idan dr yaga yaron ya fito da kayan baziji dadi ba, yace mum wannan ba damuwan mu bane, ita kam jawaheer tana kwance akan cinyar adda ta daura akanta a kai, duk tana jin abunda suke fada tadai yi shuru ne, tana tunanin irin wannan sabon salon na samir, adda tace jawaheer abinci na kitchen fah, tace na koshi adda, mlm yace mai kika ci? Tace munci abinci kafin mu zo nan, nan mum ta basu labarin abunda ya faru da jawaheer cikin harshen hausa, nan suka fara mata sannu, shidai da ido yake ta kallonsu, dan baji yake ba amma ya dan fahimta ya gane mum ta fada musu abunda ya faru da jawaheer dinne, tashi tayi ta zauna tare da rungumo adda tace zanyi kewarki addata, banso tafiya gobe ba, adda tayi dariya tace nima haka idan aka tafi sai kuma yaushe? Ido suka hada da m samir ya sakar mata wani irin mugun kallo, tayi saurin kawar dakai tare da fadin bazan dade ba zan dawo adda ta, haka sukai ta fira daka sun hada ido dashi ya watsa mata mugun kallo, daka karshe dai tashi tayi ta shiga ciki, bata dade da shiga ba shima ya wuce, hada kayanta tayi tayi, lokaci kadan ta gama hada kayan sannan ta kwanta dan ta huta, tunawa tayi da wayanta dake kashe ta tashi ta dauko ta kunna tana kunnawa saqo ya shigo cikin wayan, budewa tayi dan taga dr ne ya mata saqon ga abunda yace nan *haba jawaheer keda nake daukanki mai hankali da nutsuwa mai yasa zaki biyema wannan farin fatan bayan kin san irin tamu tarbiyan ba irin tasu bace kalli yanda yake wani riqeki kaman wani maharraminki haba jawaheer, tunda na fara ganinki nake sonki kuma soyayyan aure nake miki bawai na wasa ba, inaso ki bani dama mu fahimci juna sannan iyaye su shiga ciki, ina fatan zaki amsa bukata ta ngd daka dr nazir* tana gama karantawa ta lumshe ido lallai dr nazir namiji ne da duk wata mace zatai burin samu a matsayin namiji sai dai ita kash m samir ya sace mata zuciyarta tare da ruhinta bata ganin kowa sai shi, ya kamata ta fadama dr nazir gaskiya.... Dan shuru tayi lokaci daya ta tashi ta fita mum ce kawai a falo, tace mum ina adda? Mum tace tana kitchen fita tayi ta nufi kitchen din inda ta sami adda na zuba dan wake a tukunya wanke hannu itama tayi tazo tana taya adda jefawa tare da fadin adda kina son danwake sosai, dariya adda tayi tace ai akwai dadi ne, jawaheer tace lallai nikam bai cika damuna ba, adda tace kin bar dadi, tace ya akayi keda mutumin naga kaman dazu yana ta miki mugun kallo sannan an aiko miki da kaya daka dr ya kyautar, nan jawaheer ta bata labarin abunda ya faru bata boye mata komai ba, adda tayi dan murmushi tace jawaheer kici gaba da kula dr tunda har yace yana sonki, tace adda shifa m samir din fa? Adda tace yace yana sonki ne?? Shuru jawaheer tayi adda tace kiban amsa mana, tace a'a bai ceba amma ina fatan yace min haka, adda tayi dan murmushi tare da fadin jawaheer ke yarinya ce har yanzu baki san mai duniya take ciki ba, kawai inason kiyi duk wani abu da nace miki indai kina son ki tabbatar da zaki sami m samir ko bazaki sameshi ba, kar ki zauna zaman jiranshi kiyi biyu babu, idan m samir yana sonki dole yayi kishin ki, inko baya sonki komai za kiyi babu ruwanshi, dan haka ji shigo da dr cikin rayuwanki sannan koda kun koma wani abu ya faru ki dinga fadamin tace toh adda ta, haka sukai ta jefa danwaken har adda ta tsame tasa musu suna fira suna ci.










Shiko m samir ya rasa dalilin da yasa ya tsani dr, shidai abu daya ya sani bawai yana son jawaheer bane, kawai yana tausaya nata ne, dan shuru yayi lokaci daya kuma yace ba haka bane, kawai bana sonta da dr dinne dan ban yarda da hankalinsa ba, daukan wayanshi yayi ya doka mata kira, ringing biyu ta dauka, yace mata kin gama shirin mamaki tambayar tashi ya bata tasan dai dazu yana ta nuna mata halin ko in kula, yanzu kuma yana tambaya waiko ta shirya, tace eh na shirya komai duk da basan komawa nake gobe ba, yace saboda wannan dan iskan dr din koh?? Jawaheer ina tunaninki yake wai yaushe ma kika fara sonshi ne?? Shuru tamai tana jin ikon Allah daka cewa bata son komawa ya hakikance yana ta zagin mutum wanda baisan maike faruwa ba, tace kana cin hakkinsa domin shi bai san maike faruw....... Wani irin tsawa ya mata tare da fadin yimin shuru ban san haka kike ba, da tun farko ban daukeki a matsayin friend ba, wani irin takaici taji lokaci daya maganan da bata zata, zata fito ba taji ta fada nima fa budurwanka bace kace ni kawarka ce ina da right in kula duk wanda naga dama, jin ya kashe wayan yasa ta fara tunanin maita fada mishi haka, daura hannu tayi akai tana kuka tare da fadin Allah yasa ba fushi yayi da ita ba, daukan wayan ta tayi ta kirashi amma saiya saka mata busy alaman ya kashe wayan, daka karshe ma data kara kira sai taji switch off, kuka ta saki mai karfi mum dake kwance kusa da ita tana bacci ta farka tare da tanbayan lfya jawaheer? Tace mum wlh ina son m samir ban son in rasa shi, mum ta janyota jikinta tana fadin kiyi hakuri jawaheer idan Allah yasa shi zaki aura dole ya zama mijinki ance matar mutum kabarinshi, tace hakane mum, in ban sami m samir ba zan iya shiga cikin wani hal...... Toshe mata baki mum tayi tana ta rarrashinta, dakyar tayi shuru amma maganan bacci kam babu shi, dan ya gudu yanda taga dare haka taga safiya, tunda tayi sallah asuba, ta nufi dakin adda, adda tace jawaheer lafiya naga kaman idanki a kumbure? Kuka ta fara tare daba adda labarin abunda ya faru, adda tace ai gaskiya kika fada mishi baki Karya ba, aishi ba saurayinki bane, dan haka dole ji tsaya da wasu, jawaheer tace haba adda nifa shi nake so, adda tayi tsaki tare da fadin ai sai kiyi ta son nashi, kina son mutum yana miki wulakanci dan yaga ya hadu, shima yanda ya hadu haka kema kika hadu, babu namijin da zai ganki yaji bai sha'awar ya mallakeki, dan haka wlh kima cireshi a ranki tun kafin ya sa miki ciwon zuciya, gwara ki nemi mai sonki kibar wanda baya sonki, jawaheer cikin kuka tace adda bana son wannan magan ganun naki basu da dadin ji wlh, adda dariya tayi tare da fadin kaji ja'ira gaskiyan ne baki so? Tace adda taya zan cirshi a raina bayan kin san ba abu bane mai yihuwa? Adda tace ina zaune zanji kince kin cireshi a ranki amma fah kar kice na miki baki, kallon adda tayi sororo tace kaman ya adda? Adda tace nan gaba zaki gani badai namiji bane shi, jawaheer tashi tayi ta fita alaman taji haushin maganan adda, dariya adda tayi tace kai Allah ya yaye miki yarinya sai kace a kanfa aka fara soyayya ita ko zuciya ma taki yi, shiba sonta yake ba amma ta like mai, dakinsu jawaheer ta shiga taga mum na hada kaya mum tace yauwa jirgin 8 za mubi kizo ki shirya, jiki a sanyaye tace toh fita tayi ta nufi toilet tayi wanka da ruwan sanyi dan garin ana dan zafi, fitowa tayi ta fara shiri cikin wata doguwar riga na less yayi mata mugun kyau, duk da batai makeup ba, ta daura dankwali irin ture kaga tsiya ta yafa wani karamin gyale, sannan ta fita falo, inda adda tasa musu abinci kunu da alale da farfesun kayan ciki, zama sukai suna ci amma ita kam jawaheer tunani take saida mun ta lura da ita tace jawaheer tayi firgit mum ta girgiza kai tare da fadin kici abinci mana, bata ce komai ba ta fara ci, bata wani ci

Please Login or Register in order to submit comment