Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yawa ba ta ajiye, adda tace zo muje ki rakani can gidan, tashi tayi suka fita ita kuma mum ta fara shiri itama, bayan sun fita tafiya sukai mai dan nisa jawaheer tace kai adda na gaji, adda tace muje mun kusa, kan wani dutse suka je suka zauna, jawaheer tace ina gidan? Adda tace jawaheer babu inda zamu nace muzo nan ne saboda mu sami daman magana ni dake, inaso kiji kuma ki duba ki gani, jawaheer idan kika duba rayuwa yanzu ya canza a baya kinyi kuskure kin nuna ma samir kina sonshi yaki yarda ya soki kaman yanda kike sonshi, idan kika duba zaki gane tun daka sanda kika furta kina sonshi zaiga bazaki iya rayuwa ba tare dashi ba, sannan namiji yace yana sonki yata kaya balle kece kika furta mishi kalman so, aikin bani, wlh indai kika bi yanda na fada miki zai fito yace miki yana sonki, jawaheer tace me kenan? Tace matso kiji, magana ta mata a kunne, jawaheer tace amma kina ganin hakan zaiyi? Adda tace insha Allah ki gwada, tashi mu koma ma dan nasan yanzu ke ake jira, kallon agogon hannunta tayi taga 8:30 tace adda lokaci ya wuce gashi wayana yana gida, adda tace kai muyi sauri toh, suna karasawa kofar gidan taga motocin m samir a kofar gidan, gabanta taji ya fadi ance jirgin 8 za subi gashi yanzu 9 ya kusa, tana shiga ta ganshi a tsakar gidan yana kaiwa da komowa,waigowa yayi ya ganta a tsaye wani irin kallo ya mata tare da fadin daka ina kike?? Tace mun fita ne da adda, yace karfe nawa yanzu?? Tace 8:49 yace what time zamu tafi? Tace 8 yace gud tawo muje fita sukayi suka hadu da adda, ya kira security dinshi ya mishi magana yace ya fadama adda, yace adda yace in fada miki mum ta wuce saboda jawaheer ta bata lokaci suma yanzu zasu tafi a mota, nan adda taita musu addu'an sauka lfya, jawaheer tace bari in dauko kayana, riqota yayi tare da turata mota suka tafi, tace mishi kayana fah? Yace keep quite karki dameni plz, shuru tayi tana kallon sa, lokaci daya tasa kuka waigowa yayi yana kallonta, yace driver ya faka, bayan driver ya tsaya yace mishi ya dan fita, driver na fita ya janyota jikinshi tare da rungumeta ido ya lumshe yace miye haka jawaheer? Tace haka aboki ya kamata yama kawarshi mai yasa kake fushi dani? Sakinta yayi da sauri kana kallonshi zaka gane ranshi a bace yake, nanata sunan yayi aboki wato yanzu bata sona, aboki ta daukeni...........


















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 37-38
















Dago dakai tayi ta kalleshi sannan tace plz ka daina fushi dani, dan murmushi yayi tare da fadin komai ya wuce rungumeshi tayi tare da shafa mishi gashin kanshi, dariya yayi yace karki bata min gashin kai, tace sai in gyara maka, kiran driver yayi yaja suka wuce, tafiya suke kowa da abunda yake tunani, ita ta gefenta tana tunanin yaushe zai sota, yaushe zai fahinci irin son da take mishi, shiko ta gefenshi yana tunanin tunda sun bar yola babu ita babu ganin dr dama shine damuwanshi ya rasa mai yasa ya tsani dr din, dan waigowa yayi ya kalleta bacci yaga tanayi dan jiya batai bacci ba tunani ya hanata, ido ya kura mata yanda take bacci hankali kwance, yana cikin kallonta yaji ta fado jikinshi, murmushi yayi tare da kara gyarata ya mikar mata da kafa tare dasa kanta akan kafanshi, tafiya suke mota nata sharara gudu, bai taba long journey ba a mota sai yau, dan haka shima ya gaji sosai, amma yana jin dadin tafiyan, bude ido tayi taga anata gudu, tashi tayi daka jikinshi da sauri tana murmurza ido, murmushi ya sakar mata, tace har yanzu bamu kai ba? Kai ya daga mata alaman eh, tace kai wlh na gaji gaskiya da nisa, murmushi yayi tare da fadin matso nan, matsawa tayi kusa dashi yasa hannunshi akan kafadanta yace kefa kinyi bacci bai kamata kiga nisan wajan ba, tace ni nasha ina tashi zan ganni a gida, dariya yayi yace oh i see sai yasa kikai bacci, kai ta girgiza alaman a'a, yace toh miye? Tace jiya banyi bacci ba sai yasa nayi yanzu, kallonta yayi yace maiya hanaki bacci?tace babu komai kawai dai bana jine, shuru yayi tare da aiya nawa cikin ransa kodai tana tunanin wannan dr din ne? Tsaki yayi mara sauti amma duk da haka taji, dago kai tayi da sauri ta kalleshi ganin ya tamke fuska yasa tasa hannunta tana shafa mishi fuskan tare da fadin miye kuma? Hannunta ya cire daka fuskan nashi tare da fadin babu komai, bata kara cewa komai ba har suka zo wani kauye da ake ta siyar da abubuwa, tace driver dan faka, driver tsayawa yayi a gefen titi, kallonta yayi yace mai za kiyi tace yunwa nake ji abu zan siya, yace nop ki bashi ya amso miki, tace ai ban san mai zan siya ba saina fita na gani, kallon wajan ya farayi yana dubawa, tsaki yayi tare da cema driver yaja motar su wuce, driver ya tada motar suka tafi, tace ya zamu tafi ban siya komai ba, yace saboda abun wajan bai min ba, tace nifa yunwa nake ji, yace sorry in naga wajan da yayi min sai a tsaya kici, kai ta daga alaman toh, tafiya suke tayi babu wanda ya kara magana, har suka shiga cikin wani gari yace driver ya tsaya, bashi kudi yayi yace ya siyo mata kaza da drinks, amsa yayi ya fita jim kadan sai gashi ya kawo kaji har guda biyar, da drinks da yawa, amsa tayi ta fara budewa kudi ya kara ma driver yace kuma kuje kuci abinci tare da sauran security din, yace ok, bude kazan tayi tace kai yayi yawa, fara ci tayi tare da miqa mai kai ya girgiza tare da fadin nop bana ci, bata fuska tayi tace in baka ciba nima zan daina ci, kafada ya daga alaman bai dameni ba, ganin haka yasa ta ajiye naman wai tayi fushi, murmushi yayi tare da daukan naman yasa mata a baki ta kawar dakai yace plz kici ban san taurin kai, daukan naman tayi shima takai mai wajan baki ya kawar dakai ta kara matsawa kusa dashi zata bashi ya janyota jikinshi wanda yasa bakinta ya mannu a nashi, dukansu tsayawa sukai cak, sunyi wajan minti daya kafin ya danja baya, da sauri itama ta matsa tare dajin wani iri, shuru dukansu sukayi na wani lokaci sannan taji muryanshi yana fadin muci, bata musa ba suka fara ci, har driver ya dawo suka tafi baka jin karan komai sai wakan nicki minaj, sai wajan karfe hudu suka karaso garin abuja, tana ganin sun shigo taji wani irin dadi, gida suka nufa da sauri ta fita suka ci karo da khalil wani irin runguma sukai ma juna na murnan ganin juna, khalil yace sis sake ni mana inje inga samir, tace babu ruwana dakai dariya yayi yace sorry sis ai nafi jin dadin ganinki akanshi, dariya tayi tace mai wayau, sakinshi tayi ya nufi m samir dake tsaye yana kallonsu yana dariya hugging dinshi yayi tare da fadin bros u r wlcm, m samir yace thanks, ya umar ne ya fito shima cikin murna yayi hugging m samir sannan suka shiga ciki, jawaheer dakinta ta nufa tana shiga tayi toilet dan tayi wanka, bayan tayi wanka ta fito tasa wani wando 3quater da wata top mai bala'in kyau ta fito falo ta gansu su duka suna ta fira hawaye ne ya zubo mata tunawa da tayi bata hada komai dasu ba, wani irin zafi takeji daka zuciyarta, juyawa tayi zata koma daki dad ya kirata tsayawa tayi cak dan haka ya tashi ya nufi inda take, ya janyota jikinshi tare da fadin ina zaki, tace zani daki ne dad, yace no muje, kaita yayi har wajansu ta zauna kowa idanshi na kanta, tausayinta suke ji sosai, ga hawayen da take son boyewa ya kara zubowa, khalil yace sis miye haka? Bata bashi amsa ba sai kuka data saki tare da fadin mum plz muga kwalin da aka baku ni, kowa ya tausaya mata da turanci take magana kowa dake falon yaji mugun tausayinta, mum cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi dakinta sai gata da kwali, miqa ma jawaheer tayi ta riqe kwalin tana kuka, budewa tayi taga international passport, dauka tayi taga wasu abubuwa akai budewa tayi tana kuka wani dan karamin passport ne ya fito, da sauri ta dauka tana kallon hotan fuskan matan sak mata da sauri ta nuna ma mum tana fadin mum kalla ki gani da sauri mum ta amsa tace wlh itace ta bamu ke jawaheer itace kuma duk yanda akayi mahaifiyarki ce dan ga kaman ku nan, ci gaba tayi da duba kayan ta dauko wasu riga da wando masu kyan gaske tana kallo, mum tace wannan sune kayan data bamu ke sune lokacin a jikin ki, rungume kayan tayi tana kuka mai ban tausayi m samir dake zaune yana kallonta cike da tausayi ya tashi ya nufeta tare da goge mata hawayen yace jawaheer kiyi hakuri ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin haduwa da mum dinki bada dadewa ba wannan nauyin yana kaina, kuka ta kuma saki tare dayin hugging dinshi duk wanda ke falon saida tausayin jawaheer ya tsargo mai cikin zuciya, musamman khalil da sukafi sabawa dashi lokacin da yaji ba kanwar shi bace yayi takaici sosai dan yana son jawaheer, m samir amsan kwalin yayi tare da fadin mum a nan zan zauna ina daki na? Mum ta kalli jawaheer tace jawaheer kaishi dakin kusa dana khalil, mum tayi hakan ne dan jawaheer ta daina kukan, tashi tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya, bayan sunje kofar dakin taja jiki ta tsaya tare da nuna mai kofar da hannu alaman ga dakin nan, murmushi yayi tare da fadin tare zamu shiga, batai magana ba ta bude kofar ta shiga shima ya shigo, dakin akwai komai a ciki ga kamshi dake tashi daka ganin mum dazu tasa akasa komai dan tasan da babu komai a dakin, kallonta yayi yace wow dakin yayi kyau bari inyi wanka ki zauna ki jirani, kai ta daga mai alaman toh, yana shiga ta fita waje dakinta ta nufa ta kwanta tana kuka mai cin rai, yanzu basu mum bane suka haifeta ji take abun ya dawo mata sabo, musamman da taga bros umar khalil ga mum ga dad ga samir, amma ita bata hada komai dasu ba, mai yasa haka ya faru da ita mai yasa mum dinta ta bada ita, lallai tana bukatar jin amsa ada bata da burib haduwa da mum dinta amma a yanzu tana so, tashi tayi da sauri ta dauko wasu takardu tasa a jaka tare da daukan key din mota, har zata fita ta tsaya ta koma ta nufi wardrobe dinta ta dauko wata doguwar rigan atamfa tasa tare da yafa gyale akanta karami fita tayi ta nufi dakin m samir tare da fatan Allah yasa bai fito daka wanka ba, shiga tayi tako ci sa'a bai fito ba wajan kwalin ta nufa ta bude tare da kwashe kayan dake ciki tana kokarin fita taji ya kira sunanta da jawaheer tsayawa tayi cak, ba tare data waigo ba, ganin bata waigo ba yasa ya fara matsowa kusa da ita ji tayi ya riqota ta baya tare da juyo da ita, kallonta ya tsaya yi sannan yace wannan kayan fah? Mai zaki dasu? Kallonta ya kumayi daka sama har qasa sannn yace ina kuma kikë shrin zuwa? Wani irin hawaye ne ya gangaro mata sannan tace zan tafi zan tafi gaba daya zanje neman mahaifiyata lokacin da nake yola banji ina son ganinta ba, amma dawowa na nan gidan yau yasa naji ina son haduwa da ita, yau nasan miye iyaye bazan iya zama a nan ba dole in tafi in nemot..... Janyota yayi jikinshi tare da toshe mata baki yace ya isa haka jawaheer ya isa haka, karki kara tunanin barin nan gidan, kina tunanin kinyi adalci kenan yasu mum za suji in suka ga bakya nan?? Kinyi tunanin haka? Tace karka dakatar dani ka barni dan Allah yace jawaheer mai kike tunani kin san halin da kowa zai shiga kuwa? Nima kaina kin taba tunanin wani hali zan shiga idan aka nemeki aka rasa? Da sauri ta dago dakai suka hada ido lokaci daya kuma ta fashe da kuka tare da fadin koda na tafi kuna raina har abad......... Shhhhhhhhh ya dakatar da ita tare da fadin okey na fahimta amma kafin ki tafi inaso ki fadamin wani irin so kike min dahar kike tunanin barina gaba daya saboda wani dalili?? Zaki iya nesa da abunda kike so ba tare da kin sameshi ba?? Kasa magana tayi sai kuka da take tayi, shima shurun yayi tare dayin hugging dinta sosai yana mai jin kukan nata har cikin ranshi, ido ya lumshe ya rasa mai yasa yake jin abubuwa da dama akan jawaheer wanda baya ji akan ko wata mace, ko sonia da sukai zama tare na lokaci mai tsawo baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a halin yanzu sakinta yayi tare da janyota suka zauna akan gadon dakin yace jawaheer kiyi shuru kibar wannan kukan, nayi miki alkawarin neman miki mum dinki jibi zan koma spain muna da wasa bazan dawo kasar nan ba har sai na nemo miki mum dinki, inaso kimin alkawari ba zaki kara tunanin barin gidan nan ba, kai ta daga cikin kuka alaman eh, tare da rungumeshi tana fadin nagode sosai Allah ya baka abunda kake so, a hankali yace ke nake so jawaheer..........






















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 39-40
















Da sauri ta dago kai ta kalle shi, murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer u r my sister bani da wata yar uwa mace sai ke, so kinga dole in soki, ajiye ajiyan zuciya tayi tare da lumshe ido dan ba haja tai zatan jiba, tashi tayi tare da fadin saida safe, shima tashin yayi yace sis bacci yanzu miye time? Tace na gaji ne sosai, yace ok good night, fita tayi ya bita da ido harta rufe mai kofar sannan ya lumshe ido tare da buga hannunshi akan dayan hannun yace damn, shima kwanciyan yayi tare da tunanin jawaheer din tare da alkawarin neman mata mum dinta a duk inda take a fadin kasar nan.












Koda ta shiga daki kuka ta fashe dashi tare da fadin lallai na yarda m samir bazai taba sona ba, Allah ka jarabceni da son wanda baya sona amma ina roqanka kasa in cinye wannan jarabawan, shuru tayi tare da fadin lallai wannan shine maganin matsalata, wannan ne karo na farko data taba tunanin tayi aure ko zata cire m samir a ranta, lallai shine mafita amma komai zanyi sai naga mum dina zanyi aure inyi nesa dashi gaba daya da wannan tunanin bacci yayi gaba da ita.










Washe gari m samir tun karfe 7 ya fita shida khalil da security dinshi, direct wajan hukumar shiga da fice suka nufa, inda suka basu international passport din mum din jawaheer, tare da kudi masu yawa akan su nemo bayanai akanta, ce musu sukayi su dawo nan da sati daya, hakan akayi suka tafi bayan yawan mutanen da suke ta cincirindon son daukan hoto da samir dakyar dai suka shiga mota suka bar wajan akan nanda sati daya zasu dawo ko kuma su zasu nemeshi sun daiyi exchanging number, yawo suka dinga yi ranan.












Jawaheer kam tunda ta tashi tayi wanka, tasa wata atamfa mai ruwan ja da ash yayi kyau atamfar anyi dinkin riga da skirt saiya fito mata da surarta das a jikin kayan tayi bala'in kyau duk da ba makeup a fuskanta, wani karamin gyale ta yafa ta fito ta sami mum ita daya a falo, tace ina kwana mum? Amsawa mum tayi cikin sakin fuska tare da tambayanta ya gajiyan hanya, tace alhmdlh mum hanya babu dadi, mum tace ina zaki naga kaman fita za kiyi, tace eh mum yau zan shiga skul mun koma tun last week, mum tace kai jawaheer kina wasa da karatu tun last week kuka koma shine kikai shuru baki fara zuwa ba, yanzu kin san lecture nawa kikai missing? Tace mum karki damu attendance ne matsalan kuma nasa ana daukan min, mum tace toh shikenan dan Allah ki daina wasa kije kici wani abu kafin ki tafi, tace mum zanci a skul, babu yanda mum batayi ba amma taki ci tace bata jin yunwa, fita tayi ta wuce daya daka cikin motar gidan ta shiga mai kiran prado, ita da kanta take tukin har cikin makarantar,faka motarta tayi sannan ta nufi department dinsu, tun daka nesa ta hango yan class din nasu daka gani akwai lecturer a ciki domin duk sun bada hankalinsu wajan kallon waje daya, tana isa kam taga lecturer ne a ciki, dan haka ta shiga cikin sanyin jiki, kallonta lecturer din yayi kaman zaiyi mata magana sai kuma ya fasa, ji yayi tace mishi morning amsawa yayi sannan ta nemi waje ta zauna, kowa yayi mamakin dabai koreta ba dan yau kwananshi uku da fara basu darasi sannan duk wanda yazo idan ya shiga baya bari ya zauna, bayan jawaheer ta zauna ya kuma kallonta tare da sakin murmushin dashi kanshi bai san yayi ba, ganin itama ta mayar mai da martani yasa ya gane abun da yayi, da yake ya iya duniyanci saiya basar yaci gaba da lecture har lokacinsa yayi, sannan ya kalli jawaheer yace daka yau karki kara shigo min class indai na rigaki shigowa, kai ta daga alaman naji, sannan ya fita, tsaki tayi tare da dauko wayanta tana dan dannawa, kiran dr ne ya shigo kaman ba zata dauka ba, komai ta tuna kuma ta dauka tare da fadin hello, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin jawaheer wai nayi laifi ne aka daina daukan waya ta? Uhm kawai tace yaci gaba da fadin jawaheer naje adda tace min wai kin koma jiya, shine ko sallama babu, tace kayi hakuri tafiyan ne yazo a bazata, yace bakomai da fatan anga sako na, dan shuru tayi kafin tace uhm, murmushi yayi sannan yace ina fatan za'a bani dama? Tace Allah ya taimaka ya shige mana gaba, wani irin dadi yaji tare da fadin kenan an bani dama, kai yau ina farin ciki Allah ya dai daita mu, bata ce komai ba sai murmushi da tayi, wani lecturer ne ya shigo tace ina zuwa zamu fara lecture yace ok tare da kashe wayan, sai lecture ake musu amma ita sam bata san mai ake fada ba, domin tayi nisa cikin duniyar tunani ba komai take tunani ba sai na amince ma dr akan yaci gaba da nemanta har Allah yasa su fahimci juna tayi hakan ne da zuciya daya domin tana da burin ta sami miji tayi aure dan ta cire m samir a ranta duk da tun jiya take ta kokarin tusa ma kanta kin shi amma hakan ya faskara, lallai koda banga mum dina ba indai muka fahimci juna dole inyi aure in huta, ji tayi ana mata magana, wata yarinya ce kana ganinta kasan suma suna da arziki, jawaheer firgit tayi taga lecturer din ya fita tace kai ashe har an gama, yarinyar tayi murmushi tare da fadin sunana zarah, yau na fara zuwa lecture saboda nayi ciwo sai nayi differing da yanzu ina 3lv amma yanzu ina 2lv, jawaheer tace Allah sarki Allah ya baki lfya, murmushi zarah tayi tare da fadin baki fadamin sunanki ba, tace jawaheer murmushi zarah tayi tace suna mai dadi zarah ta amshi no din jawaheer tare da fadin in akwai lecture zata dinga fada mata, sannan tace duk abunda jawaheer bata gane ba ita zata dinga nuna mata, nan jawaheer tayi godiya tare da fadin an gama lecture din yanzu? Zarah tace a'a akwai wanda zai zo karfe hudu, jawaheer tace kai bari inje inci wani abu yunwa nake ji, zarah tace muje tare toh, fita sukayi tare suka je wani restaurant a cikin skul din, fried rice jawaheer tace a bata, ita kam zarah snacks ta amsa da drinks suna ci suna fira har suka gama, fita sukayi suka zauna wajan wata bishiya ko wacce na danna wayarta, wayan jawaheer aka fisge daka hannunta da sauri ta dago taga ko waye khalil ta gani dariya tayi tare da fadin bros mai kazo yi? Yace zo muje ki gani, zarah ta dago kai tare da kallon khalil gaidashi tayi jawaheer tace bros dina ne, tace ashe yayanmu ne, dariya yayi sannan yace ma jawaheer ga mota can kije ana jiranki ni bari in zauna a nan muyi fira da zarah, dariya tayi sannan ta nufi motar dan a zaton ta dad ne, tana budewa taga m samir zama tayi a cikin motar tare da rufewa shine a mazaunin driver daka gani shine ya tuka motar, kallonta yayi tare da fadin baki so gani na ba koh? Tace a'a , yace mai yasa kika daure fuska? Tace babu komai, murmushi yayi tare da fadin jawaheer yau baki damu da inda na shiga ba, baki kira niba, tace bani da abunda zance maka ne, yace ok toh bari in tafi, bata bude kofar ba sannan bata motsa ba, ya kuma cewa zan tafi, kallonshi tayi da idonta daya rine kadan kawai take jira tayi kuka, janyota yayi jikinsa yace karki sake kice zaki fito da wannan hawayen, jawaheer na rasa mai yasa ko kadan bana son ganinki cikin damuwa, bana son inyi nesa dake na saba dake cikin lokaci kadan, gobe zan tafi inaso plz koda na tafi kici gaba da riqemin kanki karki bama kowa daman shiga rayuwanki, dagowa tayi ta kalleshi dan bata gane mai yake nufi ba, murmushi yayi tare da fadin nan gaba kadan zaki fahimta abunda nake nufi, but yanzu ina son ki riqemin kanki ban son ko wani namiji ya shigo cikin rayuwanki, naso mu tafi tare sai naga koda munje banda tym nd ban son in barki cikin kadaici, shuru tayi tana tunani toh mai yake nufi kar inbar wani ya shiga rayuwa na? So yake in zauna banyi aure ba..... Katseta yayi da fadin zanyi missing dinki sosai, murmushi tayi tare da fadin nima haka, yace taya zan gane? Murmushi tayi tare da fadin komai kaji na fada a kanka dagaske nake kuma hakan nake ji, a musulunce mace zata iya fadama namiji tana son shi, amma a al'adance abun kunya ne, samir a kasar ku na fada maka ina sonka, amma ka nunamin inyi hakuri naji kuma nayi duk da ban cire raiba, amma a yanz..... Shuru tayi yace yanzu me?? Na hakura dakai ina son nima in sami mai sona inyi aure bada dadewa ba, kallonta yayi yana dan nazari kafin yace zaki iya auran namijin da baya sonki? Tace zan iya indai ni ina sonshi, murmushi yayi tare da fadin mai kike tunanin zai faru bayan auren? Tace zaman hakuri, yace har zuwa wani lokaci zaki ta zaman hakuri dashi, tace bazan iya sani ba, amma idan hakan ya faru zuciyata zata yanke a lokacin, yace ok naji zaki iya aurena bayan kin san bana sonki? Wani irin hawaye ga zubo mata, tace zan iya burina a kullum in kasance dakai a koda yaushe, yace jawaheer shikenan nayi miki alkawarin zan aureki amma inaso ki sani ban taba kallonki a matsayin budurwa taba, sai yar uwata, inaso kiyi tunani akai indai kin amince nanda wata biyu za muyi aure in kuma baki aminceba shikenan kiyi tunani akai, shuru tayi na wani lokaci sannan tace bana tunani akan sonka a kullum tunani na shine in sameka a matsayin miji dan haka na amince, yace ok zan fadama dad yau sai

Please Login or Register in order to submit comment