Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inzo mum tace toh sai kin shigo ina dakina in kinzo hjy hauwa ta amsa da toh sannan suka kashe wayan.










Basu dade dayin sallama ba hjy hauwa ta shigo gidan, da sallama ta shigo dakin mum, mum ta nuna mata waje tare da fadin bismillah ga waje nan, bayan hjy hauwa ta zauna mum tace hmmm hauwa ina cikin damuwa sosai, hauwa tace mai yake faruwa bilkisu kimin bayani nan mum ta fara bama hjy hauwa labari irin abubuwan da jawaheer takeyi itama hjy hauwa salati tayi tare da fadin ikon Allah wannan wani irin sabon al'amari ne haka? Mum tace wlh kema kya fada yarinya kaman wacce tayi gamo da aljanu, hjy hauwa tace gskya nima ina tunanin haka domin inba aljanu ba babu abunda zaisa ta dinga tunanin haka Allah sarki jawaheer ,mum tace toni yanzu miye mafita? Hjy hauwa tace mafita daya shine mu kaita wajan malami ya mata ruqiya kin san akwai *BAQIN ALJANI* *sunan novel dina* da basa bayyana sai suyi tasa mutum yaita abu kaman hauka ko su hana mutum aure duk yanda akayi jawaheer tana tare dasu inko ba haka ba ai ba zata kamu da son wanda bata taba gani ba bata da tabbacin ma zai aureta ,mum tace oh ni bilkisu na shiga uku ,wlh da walaki dan jawaheer da ba haka take ba tama tsani kwallon kafa amma lokaci daya yarinya ta birkice, yanzu yaushe zamu wajan malamin? Hjy hauwa tace bari in kirashi inji yaushe yake nan, doka mai kira tayi ringing uku ya dauka bayan sun gaisa tace mlm dan Allah yaushe kake nan akwai yarinyar kawata da take da matsalan jinnu inaso mu kawota koh Allah zai sa a dace, ban san mai yace mata ba naji tace toh Allah ya kaimu sannan sukai sallama, kallon mum tayi tace yace gobe da karfe hudu mu sameshi a islamiya sannan tare da jawaheer din zamu ,mum tace Allah ya kaimu, hjy hauwa tace ameen wannan abu sai an hada da addu'a, mum tace kedai bari wlh idan kika shiga dakinta gaba daya hotan dan kwallon kafa dinne duk ta manne shi dashi sai kace abun hauka harta cup din da take amfani dashi na kwallon kafa ne duk an manna hotan yaron a jiki rannan tiles din dakinta naji tana fadin zata sa a saka mata mai hotanshi wai a cire mata na dakinta dakyar na hanata sai carpet tasa ta rufe tiles din carpet dinma mai hotan yaron, hjy hauwa tace ikon Allah jawaheer ita tata jarabawan kenan Allah sarki yarinya mai nutsuwa amma lokaci daya ta canza kiyi hKuri insha Allah gobe idan mukaje wajan mlm komai zai zo da sauki insha Allah, tashi hjy hauwa tayi tare da fadin bari in koma gida dare yayi mum tace toh ngd sai goben fita hjy hauwa tayi










Bata dade da fita ba khalil ya shigo dakin yana fadin mum ina jawaheer naje dakinta inata nocking naji shuru gashi tasa key a dakin kota fita ne? Mum tace hmmm tana ciki babu inda taje ya wuce tana can tana tunanin shirmen banzan ta data saba,khalil yace kai sis rigima dazu muka gamayi da ita wai anji mishi ciwo shine tazo tana kuka wlh mum abun sis ya fara bani tsoro fah ,nasha wasa takeyi amma naga ita dagaske takeyi ashe, anya mum ba zamu kai autarki asibitin kwakwalwa ba, hararanshi mum tayi tare da fadin ai duk kune kuka sata fara kallon wannan shirmen dariya yayi tare da fadin babu ruwana mum tunda bani nace ta kalla ba ita ta kawo kanta harta fara kallo gashi yanzu ta fini zagewa, mum ajiyan zuciya tayi tare da fadin Allah ya kyauta ya amsa da fadin ameen sannan ya tashi yana fadin mum inaso inje dubai cikin week din nan gskya, mum tace mai zaka jeyi? Dariya yayi ya fara tafiya yace indan huta mana na gaji da zama waje daya, mum tace matsalanka ce wannan tunda ga office an baka kaki zuwa kullum kafi son kaita zama gida yau baka can gobe baka can, dariya kawai yayi sannan ya fita.










Jawaheer tunda ta shiga daki ta rufe take ta faman aikin kuka a kasa ta kwanta akan hotan M samir tana shafa wajan fuskanshi tana fadin nasan zaka soni kaman yanda nake sonka inaji a jiki na, zanzo gareka very soon inaso ka nuna ma mum lafiya na qalau kawai sonka ne yamin yawa kazo ka aureni ka nuna ma mum baka fi karfina ba ni nasan kaine zaka aureni kazo kaba mum mamaki kaji my luv kuka ta kara saki tare da furta ina sonka sosai nasan yanzu kana cikin wani hali na ciwo amma Allah zai baka lfya inajin zafin jin ciwonka har cikin raina........ Hmmm ku biyoni muga yanda zata kaya da jawaheer a wajan mlm shin zama ta yarda taje kuwa? Dagaske aljanu gareta kaman yanda mum tace duk ku biyoni ...






















*maryam obam*
[03/01, 16:47] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 5




















KASAR SPAIN




M samir tunda aka fitar dashi daka filin kwallo aka nufi hospital dashi domin ba karamin faduwa yayi ba, koda aka nufi asabiti dashi hannunshi na rike da kafarshi yana cije baki, gocewan kashi yayi an kaishi asibiti kafin ace me har an gyara kafan nan labari ya bazu na ciwon da yaji inda masoyanshi keta jimami koda dad dinshi yazo hspt din cikin tashin hankali amma ganin yaron nashi a zaune yana waya yasa hankalinshi yadan kwanta saida ya gama wayan sannan ya kalli dad din nashi yana dan murmushi tare da fadin dad yakake dad din ya amsa da fadin my son ya kafan naka da fatan dai baka jin zafi sosai kai ya daga alaman eh duk cikin yaren spanish suke maganan, kallonshi dad din yayi sannan yace my son dawa kake waya haka? Ko wacece nasan soyayya kukeyi, dan murmushi yayi sannan yace sunanta sonia yar england ce ba kowa yasan muna soyayya ba sai yasa ba'a baza labarin ba, fuska mahaifinshi ya tamke sannan yace my son ka rabu da ita kasan bana son ka auri wacce ba musulma ba, M samir ya kalli mahaifin nashi sannan yace dad miye dalilinka bayan kasan addini na bai haramta min auran wacce ba musulma ba, baka tunanin jahadi zanyi idan na aureta tayu ta musulunta, kai dad din nashi ya girgiza alaman bazaka gane ba, sannan yace my son kasan kai fitaccene a duniya u r d world biggest celebrity zanso ace ka auri musulma domin duniya tasan kana kishin addininka ka duba ka gani yawanci celebrity musulmai basa auran musulma yawancinsu na rasa miye dalili sannan idan suka auri wacce ba musulma ba tarbiyan yaransu yakan banbanta kai yanzu da kake son auren yar england koh kasan yau idan kuka rabu yaran da kuka haifa sun zama nata? Sannan kasan daka ranan da suka koma gareta addininta za suyi kaga baka da ikon hana su, amma in musulma ce koda yar kasar england dince idan kuka rabu yaranka a wajanka zasu zauna duk da ka'idan kasarsu ce haka mace keda iko da yara amma su musulmai a wajansu ba haka bane tunda ba haka addininmu yace ba ,namiji shine shugaba ba mace ba, m samir murmushi yayi tare da girgiza kai yace dad duk da haka bana tunanin zan iya fasa auren sonia muna son junanmu and tunda tana sona duk wani abu da nace shi za tayi, dad murmushi yayi tare da fadin ba zaka fahimta ba har yanzu kai yaro ne, m samir dariya yayi tare da fadin dad next month zan cika 28 fah shima dad din dariya yayi tare da fadin koda 40 ka kai a matsayin yaro nake kallonka..... Shigowan dr ne yasa firan nasu ya tsaya dr yace ya kafan? Amsawa yayi da fadin ban san mai zance ba inajin zafi sosai ,dr yace kayi hakuri zai rage, kai ya daga alaman yaji, dr yace ga press nan da yawa suna son sanin halinda kake ciki ko zan iya fada musu halin da kake ciki? Yace miko min phone dinka bashi dr din yayi ya shiga wajan recording ya fara magana cikin harshen turanci tunda sako ne yake son bayarwa ga duniya baki daya musamman ma masoyanshi..... Ina lafiya ina kira ga masoya na da suyi hakuri nan bada dadewa ba zasu ganni, amma yanzu ina bukatan addu'a daka garegu ngd yana fadin haka yasa stop tare dayin saving ya mika ma dr din wayanshi tare da fadin kaba yan jarida din, dr din cikin jin dadi ya fita domin wannan maganan da yayi a wayanshi ba karamin kudi zai samu ba dan saida ma yan jarida zaiyi.










NIGERIA ABUJA


washe gari bayan jawaheer ta tashi bata fito daka daki ba ganin har 11 yayi bata fito ba yasa dad dinta ya nufi dakinta amma a rufe saida ya kira sunanta sannan ta tashi tazo ta bude mai kofar, rungumeshi tayi tana kuka tare da fadin dad dazu naji a news M samir ya sami gocewan kashi dad dan Allah ka kaini spain in ganshi ko zanji dan sauki, dad cikin tausayin y'ar tashi ya dagota daka jikinshi yana share mata hawayen fuskanta yace kiyi hakuri jawaheer ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin hadaki dashi indai Ambassador kasar spain na nigeria ya warke, cikin kuka tace dad koba ta hanyar ambassador ba zaka iya hadamu plz dad do something ni daya nasan mai nake ji a cikin raina dad yace shikenan my dear zansa a mana visa na kasar spain zamu tafi cikin week din nan cikin jin dadi tace i luv u dad, dariya yayi tare da fadin muje kici abinci toh ,binshi tayi suka nufi dinning zama sukayi dad da kanshi ya zuba mata abinci ta fara ci mum ta fito tagansu ta tabe baki tare da fadin Allah ya baki lfya jawaheer dad yace bata jin dadi ne? Mum tace a'a ina nufin lafiyan wannan sabon haukan da yake son kamata, tamke fuska dad yayi tare da fadin kinga bilkisu ki dinga sanin abunda zaki dinga fada akan jawaheer bana son irin abubuwan da kike mata kina nunawa kaman baki damu da ita ba,mum tace Allah ya baku hakuri nayi shuru dad yace hakan shine alkhairi jawaheer na zaune tana jinsu lokaci daya kuma ta fada duniyar tunani gata a kasar spain sun hadu da M samir ya ganta ya rude harya furta mata kalman so ido ta lumshe cikin jin dadi a hankali ta furta i luv you too wanda bata san maganan ta fito ba jin mum dinta tayi tana fadin kaga abunda nake fadama koh wlh jawaheer tayi gamo da aljanu, ya kamata ka yarda da abunda nake fadama, dad baice komai ba illa kallon jawaheer din da yake tayi cikin tausayi duk cikin yaranshi yafi son jawaheer sai yasa komai ta kawo yake dauka harya biye mata amma a gskya wannan karan shima ya fara tunanin abubuwa da dama duk da dai baya son ya nuna mata ta gane, ganin irin kallon da dad dinta yake mata irin kallo na tuhuma yasa tabar wajan da sauri, mum hannu ta tafa tana fadin oh ni bilki naga takai na, yarinya sai tayi abu kaman mai aljanu anjima kuma tayi kaman mai tabin hankali, dad yace wlh bilkisu abunda kike ma jawaheer inda badan ke kika haifeta ba da sai ince kin tsaneta ne, akan me zaki dinga danganta ta da me aljanu ko tabin hankali duk wannan maganganun da kikeyi sam bai kamaceki ba ki daina ma y'ata irin wannan munanan alkaba'in bana so, shuru mum tayi bata kara cewa komai ba dad tashi yayi tare da fadin ni na tafi villa ina da meeting da shugaban kasa, mum tace Allah ya taimaka amma dan Allah kayi hakuri bana so ka fita kana fushi dani kaji my handsome, dariya dad yayi tare da fadin kin iya zolaya bilkisu ki ganni tsoho dani kice min wani handsome cikin dariya itama tace ai a haka kullum nake ganinka, fita yayi yana fadin bari in tafi 12 dai2 zamu fara tattaunawa, har yayi nisa mum tace anjima zamu fita nida jawaheer cikin jin dadi yace ko kefa ai yana dakyau ki dinga janta a jiki sosai sai kun dawo sannan akwai kudi a wardrobe din daki na in bakya bukatan taba naki ,yana fadin haka ya wuce.










Karfe hudu dai2 mum ta nufi dakin jawaheer cikin shirinta ganin jawaheer tayi tana zaune tana kallon waya nufanta tayi tana fadin jawaheer kinyi sallah kuwa? Tace mum ina fashin sallah ai, mum tace ok toh maza ki tashi ki shirya zaki raka ni, tace mum kije kawai bana jin fita yau kaina na ciwo, mum tace haba jawaheer fitan nan danke zanyi fah, tace mum ina zamu? Mum tace kedai ki tashi ki shirya ban san dogon zance, bata fuska tayi tare da fadin wlh mum kaina ciwo yake dakin bari gobe mu fita ,mun tace kin san bana son shirme koh maza ki tashi kisa hijab muje, kallon mum tayi tace hijab kuma ina zamu haka? Kodai wani ne ya rasu? Mum tace babu wanda ya rasu kawai wajan da zamu ne bana bukatan ki bini saida hijab, badan taso ba ta shirya tare da saka hijab din, mota suka shiga mum tace jawaheer ta zauna a gaba, hjy hauwa zata zauna a baya ita da mum ,bayan sun shiga driver yaja gidan hjy hauwa suka biya suka dauketa sannan suka nufi islamiyyan, hjy hauwa tace driver yayi parking bayan ya tsaida motan suka fito amma banda jawaheer mum tace jawaheer ki fito mana bude motar tayi ta fito shiga islamiyyan sukayi inda aketa karatu wani office suka shiga suka zauna babu kowa a ciki jim kadan sai ga wani mutum yazo ba wani babba bane amma kana ganinshi kasan mlm ne dan irin shigan da yayi, gaisawa sukayi sannan hjy hauwa tace mlm ga kawata nan sannan ga yarinyar nan sai a sannan jawaheer ta dago ta kalli mlm din, mum tace mlm dan Allah a mata ruqiya domin aljanu ne nake tunanin suka shigeta, jawaheer da sauri ta kalli mum din nata ta fara hawaye tare da tashi tsaye......
























*maryam obam*
[04/01, 14:50] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 6


















Ta kalli mum tace mum mai hakan ke nufi? Mum kallon aljanu kike min kuka ta saki mai karfi tare da fadin mum nifa lafiya na qalau bani da komai kaman yanda kike tunani kallon mlm din tayi tace mlm ka kalleni dakyau nayi kama damai aljanu ko tabin hankali? Matsowa tayi kusa da mlm ya danyi baya kadan tare da fadin auzubillah karki matso kusa dani haram, mum ta tashi ta rikota tare da fadin zoki zauna jawaheer kwace jikinta tayi daka na mum tace mum bazan iya zama ba, amma inaso mlm ya cire miki zargin da kike min yanzu, kallon mlm tayi da yayi shuru yana kallon ikon Allah, tace mlm mai zaka min ka nuna ma mum dina ni lafiya na qalau, mlm yayi gyaran murya tare da fadin da farko dai ki zauna zanyi miki yan tambayoyi kadan, zama tayi akan kujera tare da kallon mlm tace inaji, mlm yace ya sunanki? Tace jawaheer, kai ya daga alaman yaji yace kina mafarkin ruwa ko wani yana saduwa dake kai ta girgiza alaman a'a, yaci gaba da tambaya kina mafarkin gaki a daji ko kuma ana binki tace a'a, nan dai yaita mata tambayoyi tana bashi amsa harya gama ya dauko wani magani ya bata yace tasha, bata musa ba ta amsa tasha bayan ta shanye tace mlm shikenan? Yace eh an gama, tace mlm bari kaji wani abu kasan miye matsalata? Shuru yayi ba tare da yace mata komai ba tace mlm Allah ya jarabceni dason wani mutum wanda badan nan kasar bane dan kwallon kafa ne nasan zaka iya saninshi sunanshi M samir, mlm a kullum inna kwanta ina ganinshi yana kuka tare da fadamin yana da wata matsala amma idan abun ya fito kar in gujeshi duk wuya in zauna dashi sannan yamin zai aureni duk wuya yace in daure ni tashi ce, ban taba fadama kowa wannan ba kullum sonshi na karuwa a raina duk da a kullum ina kokarin in cireshi a raina amma na kasa, abun kaman kara karuwa yakeyi kullum tun bana iya fadama iyayena harna fara fada musu abunda ke cikin raina dady dina ya fahimceni amma ita mum dina ta kasa itace mahaifiyata ita ya kamata tafi kowa fahimta na tasan wani hali nake ciki ya nake ji, amma mum ta kasa fahimta na saita fara min kallon aljanu da tabin hankali wanda hakan yana batamin rai mum dina tana nesa dani wanda hakan yasa nafi sabawa da dad dina akan mum dina shuru tayi domin kukan da yazo mata lokaci daya, wajan yayi shuru na wajan second biyar sannan taci gaba da fadin kiyi hakuri mum ina fadin hakane dan kisan abunda yake damuna, ban taba soyayya ba sai akan M samir duk da bai san inayi ba, sometimes nakan so incire abun a rai na har inyi kokarin sauraran wasu amma na kasa, tashi tayi tace mlm nasan kai zaka iya fahimta na wlh bana tare da wani cuta illa ciwon so wanda nasan idan ban sami abunda nake soba zai iya zama ajalina, nasha kallo a fina finai irin abubuwan da so yake haifar wa dariya nakeyi ko ince karya ko hauka, domin ina tunanin hakan bazai taba faruwa da gaske ba, ashe ba haka bane, yau gashi abunda nake ma dariya nake ganin karya ne gashi ya faru a kaina har nima ana min kallon mara hankali, ni nasan wannan yana cikin jarabawan rayuwa na, mlm pls make my mum to understand dat i dnt have any jin tana fadin haka ta fita, duka da ido suka bita mum kasa magana tayi mlm yace hjy yarinyarki bata da aljanu kaman yanda kike zargi sannan bana tunanin tana da tabin hankali lafiyanta qalau, kawai tsabar son mutumin nan ne yasa mata take haka which kuma abunda na fahimta kaman bata da kawaye wanda take fada musu matsalanta ku take fadama wa amma dad dinta yana fahimta har yake biye mata amma ke kina nuna mata kaman ta sami tabuwa, kuma ita a nata ganin kune ya kamata kusan wani hali take ciki tunda kune iyayenta, hjy ya kamata ki dinga janta a jiki kina bata shawar wari wanda zata fahimta koda tana firan dan ball din da takeso ki daina nuna mata kyara hakan yakan sa yaro ya tsani kanshi yaga kaman iyayenshi sun tsaneshi yana da kyau ka maida danka abokinka ta yanda zaku dinga bama juna shawara jan yaro a jiki yana sa komai zaiyi saiya fadama iyayenshi sannan nunama yaro kyara yana sa ya dinga boye abubuwa da yawa wanda in ba'ayi wasa ba nan gaba za'ayi dana sani wanda ba'a fata, jikin mum yayi sanyi tace ngd mlm tabbas hakane jawaheer bata da kawa ko daya na tabbata inda tana da kawa da tare zasu dinga shawara rashin kawar ne yasa take fada mana ni kuma sai inki fahimta in dinka mata kallon hauka, mlm kasan ba komai iyaye suke dauka ba amma yanzu da naji maganan ka na fahimci komai yaronka ya fada maka koda shirme ne ka nuna masa kulawa akai, nan suka ma mlm godiya tare da bashi kudi yaki amsa yace dan Allah yayi baya bukatan kudi saida mum tace babu kyau maida hannun kyauta sannan ya amsa suka wuce, a mota suka sami jawaheer tana ta kuka, mum cikin tausayin yar tata suka karasa motar bayan sun shiga mum tace jawaheer kiyi hakuri kibar wannan kukan batai shuru ba har suka sauke hjy hauwa suka wuce bayan sun shiga gida da sauri jawaheer ta shiga gida tana kuka a falo taga dad dinta nufanshi tayi tana sauke ajiyan zuciya, cikin damuwa yake tambayanta mai aka mata? Bata bashi amsa ba sai kukan da take tayi mum ce ta shigo falon ganin dad yace bilkisu mai aka mata haka? Kodai wannan magan ganun naki kike ta fada mata? Hjy bilkisu cikin damuwa tace kayi hakuri da abunda zan fada maka yanzu inaso kamin adalci sannan ka fahimce ni, wlh nayi hakan ne dan ina zargi amma daka baya saina fahimci kuskurena, munje wajan wani mlm ne a islamiya domin ina zargin aljanu jawaheer take dasu, dad yace what? mum tace kayi hakuri ka gama saurara na shuru yayi amma fuskanshi a tamke nan mum ta bashi labarin abunda ya faru, dad baice komai ba sai kama hannun jawaheer da yayi yace tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci sannan ki fara shiri jibi zamu tashi zuwa spain bata san lokacin data tashi ba dan murna lokaci daya kuma tace dad r u serious? murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer bana daukan abunki da wasa komai naki inaso inyi miki yanda kike so hugging dad dinta tayi tare da furta u r d best dad in d world tana fadin haka ta nufi dakinta.










Kallon mum dad yayi yace bilkisu na rasa mai yasa gaba daya kika canza bakya jin duk maganan dana fada miki, yanxu kinji dai abunda mlm din yace Allah yasa ki dauka kiyi amfani dashi, tace kayi hakuri insha Allah komai ya wuce sannan wannan abunda ya sami jawaheer na jarabawa zan kara dagewa wajan roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwa, yace yauwa ko kefa, dan murmushi tayi tare da fadin kasan ita daya ce yarinya ta mace duk wannan abunda kaga inayi duk sonta yaja hakan tunda babu mai so yaga nashi ya shiga wani hali, dad yace hakane sai muyi ta addu'a sannan tare na mana visa harda ke zamu tafi jibi da khalil mum tace tafiyan family ne kenan gaba daya dariya dad yayi yace mun dade bamuyi irin tafiyan nan ba gaba dayan mu, tunda muka dawo daka saudiya bamu kara fita mu duka ba naso muje harda umar babban dansu kenan, amma yace shima zaiyi tafiya, mum tace Allah ya taimaka, ya amsa da ameen...... Toh jawaheer za'a spain koya zata kaya???






















*maryam obam*
[06/01, 01:05] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 7






















Jawaheer shiri take sosai domin tafiya spain ko abinci bata iya samu taci dan murna sai dad yayi dagaske take ci, kaman yanda dad yace jibi zasu tafi hakan ta faru domin dai rana bata karya inji masu iya magana, yau jirginsu ya daga zuwa kasar spain.....








Su jawaheer an sauka a kasar spain tunda suka sauka ta lumshe ido tana jin wani irin nishadi tare da farin ciki sai take ganin kaman gata ga M samir nan, wata katuwar mota ce taxo ta daukesu da kayansu wani gida suka nufa gidan sama, bayan sun karasa gidan suka shiga komai na gidan an rufe da farin kyalle saboda kura cirewa sukayi suka zauna a kujeran falon, hjy bilkisu ta kalli mijin nata tace wannan gidan fah nadai san baka da gida a kasar nan, murmushi yayi tare da fadin saboda jawaheer na siya, munyi waya da ambassador akan ina son gida a kasar nan shine ya hadani da wani kin san shi yana asibiti, toh wannan gidan ma mutumin yace nayi sa'a harta yan kasar sun kasa siyan gidan dan yayi kudi da yawa, mum tace ah lallai kam ai dole dan gidan ya hadu gskya duk da banga ko ina ba, jawaheer ta tashi tare da fadin bari inga gidan khalil shima binta yayi nan sukai ta zagaya gidan wanda yasha kayan more rayuwa ga gidan kato a kalla dakuna sun kai bakwai a gidan, mum tace ma dad naga su turawa basa

Please Login or Register in order to submit comment