Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan ne zuwanta yola na farko duk da ya kasance garin iyayenta ne shi, amma bata taba zuwa ba, sau da yawa takan rasa mai yasa iyayenta basa son koda firan garin yola ayi musu, musamman ma mum tafi tsanan mahaifar tata, lallai akwai wani abu amma kodai miye kiyayyar tayi yawa haka, dan murmushi tayi tare da fadin may be ma ba wani babban abu ya faru ba suka dauki karan tsana suka sama garin tare da watsar da danginsu gaba daya dama ance fulani nada riko, tashi tayi itama tayi toilet tayi wanka, sannan ta fito tasa kananan kaya riga da wando, tare dasa hijab dinta dan yin sallah azahar, bayan ta idar ta dauko wayanta tasa sim dinta na nigeria, kaman jira ake kiran mum dinta ya shigo wayan kin dauka tayi dan tasan indai ta dauka tasan tana yola sunanta sorry, amma da tayi tunanin rashin fadama mum din nata zai iya daga musu hankali suyi ta tunanin tana ina, dan haka kiran na tsinkewa ta tura ma mum message kamar haka..... *mum na dawo nigeria amma kiyi hakuri ina garin yola nida m samir muka zo, mum ki tayani da addu'a burina ya cika a kanshi duk da nasan kina min, tana gama rubutawa ta tura mata* koda saqon ya shiga wayan mum ihu ta saki tare da tafa hannu tana fadin lallai jawaheer yau ta wuce gonarta ta nunamin ban isa da ita ba, dad dake zaune kusa da ita yace haba bilkisu miye haka mai kuma ya faru? Kasa magana tayi sai miqa mai wayanta tayi amsa yayi shima ya karanta, salati yayi tayi tare da fadin mai yasa jawaheer zatai haka? Mum tace dole in tafi yola ina tsoran kar tarihi ya mai maita kansa, dad kallonta ya tsayayi tare da fadin koma dai miye kiyi mata addu'a sannan maganan zuwanki yola bai taso ba zanje da kaina in dauko ta, mum tace a'a tare zamu tafi, ganin yanda ta dage yasa dad fadin zasu tafi taren amma gobe da safe, mum badan taso ba dan taso su tafi yau din nan kar abunda take boyewa ya fito fili.












Washe gari tun karfe biyar su mum suka nufi airport dan mum ta matsa sosai,koda suka je airport din saida suka jira dan jirgin karfe 7 zai tashi, kallo daya zaka ma mum kasan tana cikin tashin hankali yau itace zata yola wanda a kalla shekara ishirin da wani abu da suka wuce rabonta da mahaifarta Wani irin hawaye mai zafi ne ya zubo mata a ido, shiga jirgi aka farayi suma suka tashi suka shiga, nan aka rufe jirgi ya daga zuwa garin yola.










Jawaheer tunda tayi sallah asuba, tayi wanka tasa wata doguwar riga gaba daya tun jiya bata cikin yanayi mai dadi, ta rasa dalili ga gabanta dake ta faman fadi, jin nocking tayi dan haka ta tashi jiki a sanyaye ta bude kofar murmushi ya sakar mata yayin data lumshe ido dan kamshin turarenshi ya bugan mata hanci wanda yake kara sa taji ya narkar mata da zuciya, wani irin kyau taga ya karayi yi mata sosai, duk da bawai wani canji yayi ba hasali ma riga da wando ne jikinsa kaman kullum kananan kaya, duka babu wanda yayi ma dan uwansa magana sai itace tayi karfin halin fadin morning, bai amsa ba sai hannunta daya kama sukai dakinshi tare, bayan sun shiga ya zaunar da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer maike damunki? Daga kai tayi ta kalleshi taga shima din ita yake kallo dan haka tayi saurin yin kasa dakai tare da fadin babu komai kawai.... Sai kuma tayi shuru, jin muryanshi tayi yana fadin kawai me? Tace gabana keta fadi ban taba jin irin yanayin da nakeji yau ba, murmushi yayi tare da fadin ki yawaita fadin innalillahi wa inna'ilaihira jiun, kai ta daga alaman toh sannan ya kalleta tare da fadin zamu anguwan da dad dina ya fadamin tunda bakya jin dadi ki zauna muje mu dawo, kai ta girgiza tare da tashi tace a'a tare zamu duk inda zaka a cikin kasar nan ina tare dakai,murmushi yayi tare da jan hancinta sannan yace kinyi breakfast? Kai ta girgiza alaman a'a wayan dake dakin ya kira ya fadi abunda yake bukata, bai wani dade ba aka kawo abunda yace, tea da chips nd egg aka kawo, tare sukaci sannan suka fita, motocin da aka kawo su jiya nan suka shiga inda jawaheer ta fada musu inda zasu tace guyuk in anje kuma ace gidan liman, kai tsaye driver din suka nufi hanya, hannun jawaheer na rike dana m samir yana kallon garin yanayin garin ya mishi kyau in yaga abu bai gane ba saiya tambayi jawaheer ta fada mishi, da haka har suka iso anguwan, babu laifi anguwan nada kyau, da tambaya har suka isa kofar gidan, koda suka isa jawaheer ce ta fito tace bari ta fara shiga, yace a'a tare zasu, haka suka shiga cikin gidan,babu laifi gidan yana da kyau duk da ba wani girma gareshi ba, sallama jawaheer tayi, wata yar dattijuwa ta amsa tace waye? Ku shigo, bayan sun shiga jawaheer taga tsohuwar fuskanta dauke da glass dam taji gabanta ya buga da karfi domin sak fuskan mum dinta sai dai kuma wannan tsohuwa ce ita ta girmi mum dinta sosai lokaci daya ta shiga rudani.......




















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 20














Muryan matan ne ya katse jawaheer daka duniyar tunanin data fada, tace sannunku ku karaso mana, wani karamin falo ta kaisu wanda daka gani an ware shine dan ajiye baki, falon sai kamshin turaren wuta yakeyi, jawaheer dai bin matar take tayi da ido, domin abubuwa ne fal a cikin ranta, fita tsohuwar tayi jim kadan sai gata da ruwa ta kawo musu, pure water mai sanyi, sannan ta zauna tare da fadin bismillah, m samir kallon jawaheer yayi wacce idonta nakan wannan tsohuwar,kafin yayi magana yaji matar na fadin sai dai ban shaida ku ba, cikin harshen hausa take magana, m samir bai san mai take fada ba dan haka ya kalli jawaheer tare da fadin tayi mata bayani, jawaheer tace da fatan mun sameki lfya hjy, amsawa tayi da fadin lfya qlau, sannan jawaheer tace dama mun zo neman khausar ne, da sauri matar ta tashi tare da kallon jawaheer lokaci daya kuma ta fashe da kuka tana fadin maiya kawo ku, waya turoku, mai kuka zoyi nan? Mai yasa zaku tunamin da ciwon da yake zuciya ta wanda ya kasa warkewa, kodai ku yan uwan muhd ne wanda ya bata min rayuwan yarinya, baxan taba yafe mai ba shine mutum na farko daya tarwatsa min a halina, ku tashi ku fita, m samir da bai san abunda ke faruwa ba sai kallon jawaheer yake amma yaga kaman matar fada take dan yanda take magana kadai ya isa ya nuna mishi hakan, jawaheer tace kiyi hakuri hjy wlh bada wata manufa muka zo miki ba, hasalima....... Dakata yar nan bana son jin duk wani abu da kuka zo dashi ku tafi kawai ku barni, jawaheer tace dan Allah ki saurare ni wannan da kike gani dan khausar ne kuma jikanki, gaba daya tsayawa tayi tana kallon jawaheer alaman ban san yaudara, kai jawaheer ta daga mata tare da fadin yaron muhd ne wannan a gabanki sai dai baya jin hausa, sai yaren kasar su spanish ko turanci, da sauri ta rungume m samir tana kuka tare da fadin ina kaje wajan shekaru ishirin da suka wuce a ina ka rayu, m samir farin ciki ne fal cikinsa tunda yaga ta rungumeshi alaman sunyi nasara kenan, kuma ya tabbata zaiga mum dinshi yanzu, sakin m samir tayi sannan ta kalli jawaheer tace yar nan fadamin a ina ya taso, nan jawaheer ta fara bata labarin abunda ya faru wanda dad din m samir din ya fada mishi da yanda abubuwa suka faru a baya tare da satoshi da yayi har ya girma a wajanshi, kuka ta kuma saki tare da fadin lallai muhd shine silan tarwatsa min dangina, amma babu komai munyi imani da kaddara wanda a wancan lokacin muka kasa fahimta, shigowan su mum gidan yasa jawaheer da tsohuwar suka fita shima m samir ya rufa musu baya, jawaheer tace mum dad mai kuka zoyi nan? Mum kam kuka takeyi yayin da matar itama take kuka tana fadin bilkisu dama kina raye, gaba daya jawaheer ta shiga rudani sosai dan haka ta matsa wajan dad dinta tana fadin dad maike faruwa ne? Dama sun san juna ne? Dad bai iya magana ba balle ya iya bata amsa, matar ta kamo hannun m samir ta hada dana hjy bilkisu tace ga danki nan bilkisu, jawaheer wani irin duhu ta gani ya rufe mata ido hannu ta daga tana fadin dama yaya nane kai jini nane kai mum dinmu daya ash..... Tif tayi kasa sumamma da sauri sukayi kanta suna fadin jawaheer musamman ma m samir da yafi kowa rudewa lokaci daya domin duk maganan da sukeyi babu abunda ya fahimta dan da hausa sukeyi sai dai ya gane mum itace mum dinshi, ruwa tsohuwar ta dibo ta fara yayyafa ma jawaheer amma ko motsi batayi ba, dan haka hankalinsu ya kuma tashi sosai dad ne yayi karfin halin fadin mu kaita hspt, jin an fadi hspt yasa m samir ya fahimta dan haka ya dauketa cak sukai mota ya shigar da ita yace ma security dinshi suje hspt mafi kusa, tafiya kadan sukayi suka isa wani asibiti inda akai emergency da ita domin ceto rayuwanta, mum babu abunda take sai kuka tare da fadin jawaheer insha Allan babu abunda zai sameki kuka take sosai gaba daya ta kasa zama, shiko m samir gaba daya ya rasa maike mishi dadi, ganin irin kukan da mum take yasa ya nufeta yana bata hakuri lokaci daya ta janyo m samir ta rungumeshi tana kuka mai cin rai, yau ya kamata ace ranan farin ciki ne a rayuwanta amma kash abubuwa sun jagule, ga danta Allah ya hadasu, ga jawaheer a asibiti rai a hannun Allah, sunyi wajan awa daya kafin dr ya fito da sauri m samir ya nufeshi yana tambayan ya jikin nata, yace suje office dinshi, binshi sukayi har office dr din sai kallon m samir yake yana mamaki kaman ya sanshi m samir ne ya katseshi da fadin dr ya jikin nata? Dr yace munyi iya kokarin mu sauran sai a barma Allah, dan harta farka tana fadin ashe yayana ne shikenan burina bazai cika ba, nono daya muka sha...... Tana cikin fadin haka ta kara suma ko numfashi baya fita amma yanzu mun sa mata oxygen numfashin ya fara fita, gaskiya tana cikin mugun damuwa wanda ba'a so mutum yakai irinshi domin sai anyi sa'an gaske mutum yake tashi idan yayi irin wannan abun, dayan biyu ne ko ka tashi da ciwon barin jiki ko kuma zuciyarka ta buga ka mutu, yanzu dai sai mu jira ta farka mu gani, hankalinsu gaba daya ya tashi m samir wani irin son jawaheer yaji yana shiganshi wanda bai taba jin irinshi ba sai a yanzu amma yana ganin hakan a matsayin dan tana kanwarsa ne jininsa wanda saida dr yayi bayani ya fahimta dan da turanci yayi, ashe duk son da take mai ashe yayanta ne shi lallai Allah mai iko ne, mai kuma yanda yaso, mum zuciyarta cike take da damuwa dad ma kam ba'a magana dan yafi kowa shiga cikin damuwa domin yar lelenshi wacce yafi so kaf yaranshi itace yau a kwance a gadon asibiti tana cikin yanayin rayuwa ko mutuwa gashi dr yace babu tabbaci, lokaci daya ya kalli mum yace anya ba zamu fitar da ita waje ba? Idan wani abu ya sami jawaheer bazan iya juran gani ba,mum tace nima haka nake tunani muyi magana da dr din. Koda aka fadama dr shawara ya basu akan suyi hakuri har zuwa gobe su gani sannan koda wajan suka kaita babu abunda zai canza, tare da fadin gwara ma suyi hakuri su barta a nan, dad yace bari dai suga zuwa goben tare da tambayan dr zasu iya ganinta? Yace eh su shiga amma karsu dameta da hayaniya, shiga sukayi dakin gaba dayansu, tana kwance akan gadon dakin ansa mata oxygen baka jin karan komai saina oxygen din da karan ac duk da ac a kunne yake jikinta babu abunda yake sai zufa, lokaci daya fuskanta yayi fayau tayi rama kaman wacce tayi ciwon kwana biyu bakinta yayi fari, mum ta kalli dad cikin kuka tana fadin kalli yanda ta koma yanzu2 anya jawaheer ba mutuwa za tayi ba, na shiga uku ni bilkisu....... Kuka yaci karfinta sosai dad ya jata suka fita m samir shima kukan yake tare da share mata zufan dake goshinta jikinta yayi wani irin dumi gashi kuma kaman babu jini yanda yaji jikin nata yayi wani irin tashin hankali ya kuma shiga tare da fadin wani irin ciwo ne haka lokaci daya?kallan fuskanta yayi yaga tayi haske tayi fayau gabanshi yaji ya fadi tare da fadin no zaki rayuwa my sister kuka ya saki sosai......








*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 21-22












Jawaheer kam ko motsi batayi, m samir iya tashin hankali ya shiga gaba daya ya fita cikin hayyacinsa, mum ce ta shigo dakin domin a lokacin anata kiran sallah la'asar, kama hannunshi tayi wanda ya rike na jawaheer dashi, dagowa yayi da sauri wanda yake zargin jawaheer dince amma sai yaga sabanin hakan, mum ce cikin kuka take mai magana cikin harshen turanci tace kaje kayi sallah,baiyi magana ba sai tashi da yayi ya fita dan yin sallah, haka su mum sukai ta zama amma shuru bata farka ba, abun ya damesu sosai gashi har wajan karfe biyar yanzu gaba daya hankalinsu a tashe yake, mahaifiyar mum ce tace nikam bilkisu itama wannan din yarinyar kice? Mum zatai magana taga kaman jawaheer tana motsi da sauri ta nufeta tana kiran sunanta tare da fadin jawaheer ganin idon jawaheer din a bude yasa ta furta alhmdlh da sauri ta fita lokacin su dad na waje da m samir dad na ganinta yace bilkisu lfya kuwa? Tace ta farka zan kira dr ne, dad yace bari in kira shi, m samir da mum suka koma dakin, m samir suna shiga ya nufeta ganinshi yasa ta sakar mishi murmushi amma ta kasa magana, shima ya kasa furta mata komai sai murmushi da yake ta sakar mata shima, dr ne ya shigo dakin wanda yasa m samir niyan barin wajan amma ta rike mai hannun alaman ya tsaya, dr ganin haka yayi murmushi tare da fadin lovers, matsawa dr din yayi ya fara dubata tambayanta ya farayi amma bata bashi amsa da baki sai dai ta daga mishi kai kota girgiza mai kai, hankalinsu ya tashi sosai ganin taki magana dad yace dr mai yasa bata magana? Dr yace nima abunda nake son sani kenan amma karku damu zatayi, dr yace amma alhmdlh jikin da sauki nayi mamaki ta tashi ba tare da wani matsala ba, gskya ku kara godema Allah, dad yace toh dr ni yanzu magana kawai nakeso tayi, dr yace madam kice wani abu plz, ido ta lumshe alaman karma ya dameta, mum ta matso kusa da ita, tana fadin jawaheer plz kiyi magana, bude ido tayi ta kalli mum lokaci daya hawaye ya zubo mata sannan bakinta ya fara rawa tace mum, kowa ya kura mata ido ta kara matse hannun m samir sannan taci gaba da fadin mum m samir danki ne na cikin ki? Mum dan Allah ina son sani ance sunan mum dinshi khausar ba sunanku daya ba mum dan Allah ki fadamin maike faruwa wlh mum ban san mai yasa na tashi ba amma haka Allah ya tsara dan Allah mum ki fadamin miye tsakaninku ko zuciyata zata samu salama daka radadin da takeyi a halin yanzu, mum kuka ta farayi tare da fadin jawaheer zan fada miki komai kaman yanda kike son ji duk da banso fada miki ba, amma inason in kinsan gskya karki juyamin baya karki gujemu duk rintsi duk wuya.......












TUNA BAYA.....






Garin yola garine na fulani mu uku iyayena suka haifa a duniya ni daya ce mace a wajansu, yayyina maza ya abubakar sai ya abdullahi saini bilkisu wacce naci sunan kakata ake cemin khausar, mahaifina mlm kabiru shine limamin anguwanmu mutane suna girmamashi mahaifiyata kuma nafisa, muna kiranta da adda, ita daya ce wajan mahaifinmu duk wani gata da dan gata yake samu suna nuna mana duk da alokacin ba'a karatun boko bawai ba'ayi bane a'a anayi sai dai ba'a bashi muhimmanci, mahaifina koda haiyuwa akayi kasancewan shine liman shine yake radama yaro suna, sannan komai mai gari zaiyi saida saninshi, tunda na taso nake tallan nono domin wannan dabi'an fulani ne musamman wanda suke kauye, akwai dan mai gari wanda yake sona bayaji sosai gashi kashe mutum a wajanshi ba komai bane, sannan iyayena tun ina karama suka bashi ni dan haka irin tasu al'adan yake ana haifanki za'ayi kamunki, a bama wani ke ma'ana anyi miki miji tun kina karama, gashi kuma koda bakwa son juna baku isa ku karya alkawari ba, tunda na taso na tsani auwal, gashi yana bala'in sona, ko yazo wajena bana wani bashi fuska, akwai wani ma'aikata da nake kai nono inda na hadu da muhd mahaifin samir lokaci daya muka saba harya fara koyamin turanci daka baya ya fara sona, ya sami mahaifina akan yana sona, inda ya nuna mishi bazai hada zuri'a da farin fata ba wato bature bai fito ya fada mishi anyi min miji ba, babu yanda baiyi ba amma mahaifina yaki, irin son da muke ma junanmu wata rana naje wajanshi dan saboda shi gaba daya aka hanani tallan nono, na sata jiki naje, inda mukaci kukanmu har yakai daya fara ban hakuri yana sharemin hawaye sanadin da shaidan ya rinjayemu kuka ta saki sosai sannan taci gaba mun aikata sabon Allah, tunda na tafi ban kara fitowa ba har saida aka gano inada ciki hankalin iyayena ya tashi sosai nan sukai ta buguna tare da yayyina inda sukace in ban fadi wanda yamin ba sai sun kasheni, jin naki magana sukace wlh zuwa dare in ban fadaba sai an jefeni gashi kowa a gidan lokacin ya shareni babu maijin tausayi na, haka na sata jiki na samu muhd nake fada mishi abunda ya faru, mai makon inga yayi fada sai daga hannu yayi yana godiya tare da fadin rabo rabo lallai koba ta hanyar aure ba inda rabo sai an samu, kuka na fara mishi akan yabar garin dan wlh zasu iya kasheshi da farko yaki yarda sai dakyar ya amince dan saida na mishi alkawarin baza'a zubar da cikin ba sannan yabar kasar gaba daya, haka na koma gida iyayena suka kara rufeni da duka kaman zasu kasheni waina dauko musu abun kunya, in ban fadi wa yayi min ba sai sun kasheni, da naji wuya tare da tunanin muhd yabar kasar ma yasa na fada musu wanda yamin sun shiga tashin hankali sosai, gashi anje inda yake aiki ance yabar kasar, haka iyayena sukace a zubar da cikin naki yarda babu irin abunda ba'ayi ba amma cikin yaki zubewa, har yan gari suka san labarin abun kunyan dana aikata ko waje bana fita dan gori da zaki abun bama ni daya ba harta iyayena ana musu gori wanda hakan yasa aka cire mahaifina daka liman akaba wani, abun yama mahaifina ciwo wanda hakan yasa kaf yan gidanmu suka kara tsanata har gwara adda tana tausayamin in babana baya gida, ana haka har na haiyu cikin rashin gata, har nayi arba'in cikin dakin datti nake kwana da yarona, kwananshi arba'in da daya a duniya na nemeshi na rasa, nan aka dauka mahaifina ya kashe yaron ya boye, aka tsanemu a garin da kyara zagi wanda mahaifina yayi zuciya tare da fadin inbar gidan sannan inna kara zuwa mai gida Allah ya isa bai yafe min ba, babu irin hakurin da adda bata bashi ba amma yace inta kara magana a bakin aurenta, haka tana gani na tafi yayyina sune masu kara zugawa waina dauko musu abun kunya basa iya shiga cikin mutane, haka nabar gidan cikin dare banda kudi banda kowa, duk wannan abunda akamin ban damuba kaman rashin yarona wanda nake gani kaman mahaifin nawa ne ya daukeshi dagaske din, gaba daya na kara tsanan zaman kauyen ma tare da fadin gwara da aka koreni ma, haka naita tafiya cikin dare harna bar anguwanmu ina cikin tafiya ne cikin sauri saboda tashin hankali ko gajiya banyi ba, wata mota ta rugo a guje saura kadan ta bugeni, Allah ya taimaka, mutumin ya fito yana fadin haba baiwar Allah miye hka bakya duba hanya gashi cikin dare ina zaki, nace duniya zan shiga, yace subhanallah, haba baiwar Allah mai yayi zafi haka, kuka na saki tre da bashi labarin abunda ya faru ya tausayamin sosai inda yace in shiga motarshi muje ban musa ba na shiga sai naga ya nufi anguwarmu, direct gidan mai gari mukaje inda yayi2 in fito naki, haka ya shiga jim kadan saiga mai gari da mutane sun fito inda akasa na fito dole, mai gari yace wannan yar iskan zaka aura bawan Allah ko dai kaine ka mata ciki? Yace wlh ko daya, nan aka tura aka kira mahaifina bayan yazo ya ganni yace baya kaunar ganina, mai gari yace ya nutsu nan aka mishi bayani inda yace shiba mahaifina bane ya sallamani zan iya yin duk abunda naga dama tare da fadin har abada baya bukatar ganina,haka mai gari ya daura mana aure da mutumin da ba'asan ko waye ba......






















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 23-24
















Babu abunda nake sai kuka, bayan an gama daurin auren mai gari ya kalleni yace daka yau kar in kara shigowa wannan garin domin kar in lalata musu yara, haka muka tafi muka bar garin cikin dare, babu komai a raina sai tsanar garin da yan garin tare da mahaifina, haka muka shiga cikin garin yalo inda anan gidan mijina yake duk da bamai karfi bane sosai amma yana da rufin asiri yana da mota golf guda biyu daya ana mishi haya daya kuma shi yakeyi da kansa, yayi karatun boko rashin aikin yine yasa ya fara jan mota, iyayenshi sunyi mamakin auren da yayi amma da yake suna da tawakkali duk da abun ya bata musu rai ace yayi aure bada saninsu ba, haka suka hakura dan mamanshi ta dade da rasuwa wajan matar babanshi ya taso, suna nunamin gata sosai haka shima duk da yasan labari na, ina mamakin mai yasa ya yarda ya aureni, wata rana muna fira yake fadamin wai ya taba ganina ina tallan nono tun daka lokacin yaji yana sona, amma sanin al'adun mu na fulani yasa ya boye komai dan yasan kauyenmu kana jariri ake maka miji, sai kuma gashi yanzu kin zama matata, ina kokarin kyautata ma mijina, domin kaf duniya banda kamanshi dan ina ganin yafi kowa kaunata, shekara daya da aurenmu na haifi dana namiji santalele inda aka sa mishi sunan baban mijina wato umar, lokacin daya cika arba'in matar data riqe mijina ta rasu, munyi kuka sosai, tun bayan rasuwanta baba shima ya fara ciwo sosai, tsakaninsu wata uku shima ya rasu, kai munji mutuwar baba sosai, inda gaba daya zaman garin yalo ya ishemu dan dama ni bana son garin ina dai zama ne kawai, haka muka tattara muka koma kaduna muka sami gida muna haya, shekara biyu tsakani na kuma haifan da namiji muka sa mishi khalil, a lokacin mijina ya sami aiki a banki, lokaci kadan rayuwanmu ta fara canzawa, daka wajan aiki aka dawo dashi abuja inda aka bamu gida karami za'a

Please Login or Register in order to submit comment