Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a fara komai duk abunda kike bukata sai ki fadamin, amma ina so ki sani indai kika shigo babu saki kar nan gaba kice baki son zaman, murmushi tayi tare da fadin bana tunanin baki na zai iya fadin haka,yace good zamu koma gida anjima sai mu karasa magana dama ke nazo in gani, tace ok sannan ta fara kokarin bude kofar amma yaki buduwa, kallonshi tayi alaman ya bude mata, yace haka zaki faramin babu wani abu sai kawai ki fita, rufe ido tayi tana dariya sannan ta matsa kusa dashi ta mishi peck a goshi, dariya yayi sannan ya bude mata motar ta fita, da ido ya bita har ta karasa wajan su khalil da suke ta fira shida zarah, tace toh saika tashi ku tafi dariya yayi tare da cema zarah sai munyi waya, tace ok, sannan ya tafi, jawaheer kallon zarah tayi tace badai har an kulla luv ba? Zarah tace haba luv a minti nawa, dariya suka sa dai2 lokacin wannan lecturer din yazo yace ma jawaheer tazo yana son ganinta, bayan ta matsa kusa dashi yace ga no dinshi yana son ta kirashi, bata yayi tasa sannan ta koma wajan zarah tana fada mata abunda yace mata, zarah tace haba nayi mamakin dabai koreki ba, ashe ya kamo fish, dariya sukayi har 4 yayi suka shiga lecture basu fitoba sai 6 gida ta nufa direct a gajiye ta shiga gida babu kowa a falo dan haka tayi dakinta, tana shiga toilet ta nufa tayi wanka wardrobe dinta a kusa da toilet dinta yake kaya tasa sannan ta fito tana fitowa taga mutum a dakin yana kalle kalle, kallonta yayi rai a bace sannan yace jawaheer jiba dakin ki duka pics dina ne harta carpet dinki, indai kina sona mai yasa kike kula wasu mazan?? Ido ta dan zaro alaman wana kula..... Tace ni yaushe kum...... Ya isa ban son jinki dazu waye naga yana baki number kina sawa?? Shuru tayi kaman ba zatayi magana ba, can tace lecturer dinmu ne fah, yace lecturer number din mai yake baki?? Tace yace in kirashi ne zai mun magana, ido ya lumshe ji yake kanshi na mishi wani irin tafarfasa lokaci daya idanshi ya kade yace mai zaki mishi idan kin kira shi? Tace nima ban sani ba, kallonta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita fuuuuuuuu, dakinshi ya nufa zama yayi akan gadon dakin shidai yasan bawai son jawaheer yake ba, kawai yana tausaya mata sai yasa yake son ya aureta sannan baya son tana nesa dashi, to mai yasa nake kishi idan wani yana mata magana?? Wata zuciyar tace saboda kana sonta da sauri yace nop, kawai dai dan zan aureta ne dole kuma inyi kishi a kanta,karan wayanshi ne yasa ya dauka yaga dad din su khalil ne dauka yayi dad din yace mishi samir gani na dawo ina falo, yace ok dad ga ninan, tashi yayi ya fita ya nufi falon, samun dad yayi da mum akan dinning dad yace samir ya gida gobe ne tafiyan koh? Yace eh dad, dad yace masha Allah, Allah ya taimaka, yace ameen, yace dad dama inaso inyi maka magana nida jawaheer mun fahimci juna, kuma...... Dan shuru yayi dad yace inaji, yace muna son muyi aure in kun amince, dad cikin murmushi yace alhmdlh alhmdlh abu yayi kyau, mum tace toh yanzu ya za'ayi, amma inaga da an jira an duba iyayenta koh? Dad yace a'a in ba'a gansu ba fah, haka zatai ta zama? Kinga dole kuwa tayi aure, mum tace hakane, m samir yace dad plz ban son bikin ya wuce wata daya, mum harara ta sakar mai tare da fadin toh mara kunya, kai ya sosa tare da tashi yabar wajan suka bishi da dariya, dakinshi ya koma ya kwanta haka kawai yake jinshi cikin farin ciki da annashuwa, haka har bacci ya daukeshi,.












Washe gari jawaheer nada lecture karfe 8, dan haka da wuri ta shirya duk da ranta a jagule yake, dan tasan m samir yana fushi da ita, gashi yau zai tafi, ji tayi ba zata iya tafiya ba har sai ta ganshi, dakinshi ta nufa taga baya nan, fita tayi ta nufi falo taga mum na gyara kayan abinci akan dinning, tace morning mum, mum tace har kin fito? Tace eh mum gashi har na kusa makara, na tafi sai na dawo, mum tace ok samir yace in fada miki ya tafi, sannan ga sako ya bayar a baki, dam taji kirjinta ya buga wato tafiya yayi shine bai mata sallama ba......




















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🀝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 41-42
















Mum ta dauko wani karamin bag ta bata, amsa tayi ta koma dakinta ta ajiye tare da fashewa da kuka, wato haka za'a fara kenan, kallon jakan tayi ta bude taga kudi masu uban yawa kuma duk dallar, sai wata takarda data gani a ciki, budewa tayi taga anyi rubutu kaman haka...... *ga kudi nan kisai duk abunda kike bukata kin san ban san ya al'adunku suke ba, ki fara siyayyan abunda kike bukata inna dawo sai mu karasa wasu abubuwan, sannan inaso ki sani ni bana daya daka cikin maza marasa kishi dan haka kisan wa zaki aura ina da kishin kaina dan haka dole inyi kishin iyalina, idan kika kara kula wani ban yafe ba sannan idan na sami labari zaki hadu da fishina bye* baki ta sake tana mamaki lokaci daya kuma tayi dan murmushin takaici, tare da tunanin yanda rayuwan aurensu zai kasance ita dashi, bata taba tunanin zata aura mijin da zai bude baki yace baya sonta ba har kuma ta yarda da auran, wani siririn hawaye ne ya silalo mata a fuska jin karan wayanta yasa tayi saurin goge hawayen zarah ta gani, dan haka ta dauka da sauri ban san mai zarah tace mata ba naji tace gani nan zuwa, har takai kofa ta tsaya tare da waigowa komawa tayi ta dauki jakar ta fita, a falo ta kara ganin mum tace yauwa mum gashi kudi ne a ciki yace in fara siyayya kafin ya dawo, murmushi mum tayi tare da fadin ok in kin dawo mayi magana tace ok tare da fita.










Makaranta ta nufa direct bayan tayi parking ta kalli agogon dake manne a hannunta tare da fadin 8:03 Allah yasa bai shiga ba, jakarta ta dauka ta fita ta nufi department dinsu a tare da lecturer din suka shiga, kallonta yayi yace u r lucky 2day, murmushi kawai tayi ta nemi waje ta zauna, inda ya fara koyar dasu harya gama ya musu text, sannan ya kalli jawaheer yace sameni office dina yanzu, yana fadin haka ya fita, kallonshi tayi ta banga mai harara ta baya tare da fadin ko uban me zan mishi oho, zarah tazo kusa da ita tare da fadin sai ki tashi kije, hararan zarah tayi tare da fadin muje ki rakani, zarah tace wa? Ni din? Tab ai in kin ganni a lahira kaini akayi, ke yace kije dan haka babu inda zani, tashi tayi ta fita zarah tayi dariya tare da bin bayanta har kofar office dinshi zarah ta rakata amma taki yarda ta shiga, nocking jawaheer tayi taji shuru karayi tayi sannan akace come in, budewa tayi ta shiga, akan kujera ta sameshi yana duba wasu takardu, ganin ta shigo yasa ya saki murmushi, tare da fadin jawaheer right? Kai ta daga alaman eh, ya nuna mata kujera tare da fadin zauna mana, zama tayi fuskanta tamke, yace jawaheer mai yasa baki kira niba? Tace na manta ne, yace ok so yanzu ni sai ki bani number dinki, ko kuma ki kirani, tace zan kira inna koma gida, yace ok muga wayanki, kaman karta bashi amma babu yanda ta iya ta miqa mai, kiran layinshi yayi sannan ya mika mata wayan tare da fadin baki saving din number dina bama, dan murmushi tayi yace bari in gabatar miki da kaina sunana yusuf, ni dan garin kaduna ne wato dan zaria, ina da mata daya da yara biyu, jawaheer tunda na ganki naji Allah yasa min sonki sannan ni bada wasa nake ba da aure nake sonki, shuru tayi tana kallonshi, tare da takaicin kalaman da yake fada mata, amma ya dan burgeta dan da farko tayi zaton kalan lecturer din nanne masu bata yan mata, amma sai taji sabanin haka, sannan yusuf ba laifi yana da kyau sannan mijin nu nawa ne a ko ina, amma ita bata ganin kowa sai samir dinta kawai.... Katseta yayi da fadin jawaheer ya naji kinyi shuru, magana za tayi ta kasa ganin haka yasa yace kije zan kiraki zan baki lokaci kiyi tunani akai, da sauri ta tashi ta fita, wajan zarah ta nufa, zarah na ganinta ta tashi tare da fadin ya akayi? Tace hmmm muje kiji, suna tafiya tana bama zarah labarin abunda ya faru, zarah tace kai amma ni kam jawaheer mai zai hana ki yarda dan naga....... Tace dakata taya zan yarda bayan nanda wata biyu biki na, ido zarah ta bude tare da fadin ke dawa? Jawaheer tace m samir, shuru zarah tayi tana nanata sunan tare da fadin ni kam ina jin sunan, yauwa na tuna wani dan kwallon kafa ne mai irin sunan, jawaheer tace to ni dan kwallon zan aura, zarah kwashewa tayi da dariya tare da nuna jawaheer da hannu tace wannan wasan naki daban dariya yake, jawaheer tace kece kike da ban dariya amma banda lokacin miki bayani in lokaci yayi zaki gani, zarah dai dariya take tayi alama jawaheer wasa take mata, ganin tana kokarin mai data mahaukaciya ko kuma makaryaciya yasa jawaheer tace ni kinga tafiya ta, tayi gaba abunda zarah saboda dariya ma kasa binta tayi, ita kam jawaheer tayi gaba abunta.














Jawaheer koda taje gida a wajan bukka taga mum dinta da dad suna fira ga kayan abinci nan a wajan kala kala, nufansu tayi cikin fara'a tare da fadin dad mum sannunku da hutawa, amsawa sukayi su duka da fadin yauwa, zama tayi tare da fadin mum ina khalil ne wai? Tace ya fita shida ozil, tace lah ya dawo ne? Mum tace eh ya dawo dazu, dad yace jawaheer kinci abinci kuwa? Tace a'a yace haba bakinki ya nuna hakan, mum ta fara zuba mata tare da fadin babu yanda banyi da itaba amma taki ci da safe, mutum yaita zama da yunwa in kika jajibo ma kanki ulcer aike kika sani, ita dai jawaheer shuru tayi tare da amsan abincin ta fara ci, taci sosai sannan ta ajiye, bayan ta kammala mum tace jawaheer nasa an canzo kudin da samir ya baki duka kudin million 200 ne, zamu tafi dubai muyi siyayya a can na kayan akwati kafin ya dawo muji yanda yake son a tsara dan kin san mutum celebrity bazai rasa yanda yake son bikinshi ya kasance ba, cikin jin kunya tace toh mum, dad yace amma kudi ai yayi yawa, mum tace baiyi wani yawa ba,yar tawa ai mai tsada ce, dariya dad yayi yace nima haka dan nawa, ita dai jawaheer tashi tayi dan wani irin kunyan mum taji tanayi yanzu, suna ganin ta tashi suka sa dariya.










Dakinta ta shiga tare da ajiye jakarta, ta fada toilet tayi wanka, wani irin nishadi take ji sosai, duk da tana cikin damuwa na sauyin da samir yake nuna mata kafin ya tafi, gashi yau abunda ya mata ya bata mamaki tafiya babu sallama, wayarta dake kan gado taji tana ringing nufan wayar tayi tare da dauka taga zarah ce, dauka tayi taji zarah na fadin wlh jawaheer kin bani dariya dazu, tsaki jawaheer tayi tare da kashe wayan tace banda lokacin wannan tsokanan naki yanzu wlh zarah, kiran zarah dinne ya kuma shigowa dauka tayi tare da fadin miye kuma? Zarah tace miye na kashe wayan kuma? Tace naga kina son mai dani kaman mahaukaciya ne, zarah tace ko daya abun da kika fada ne kawai yake sani dariya, amma wai wasa kike koda gaske? Jawaheer tace akan mai zan miki wasa bari in turo miki saqo ta whtsapp yanzu, kashe wayan tayi ta tura mata pics dinsu da m samir kala kala, aiko tana gani ta doko ma jawaheer kira amma taki dauka daka karshe ma da taga ta dameta saita kashe wayan, tana fadin bari ke in manna miki haukan, batai minti shabiyar da kashe wayan ba taji ana nocking, tashi tayi ta bude kofar wa zata gani inba zarah ba, baki ta sake tare da fadin maiya kawo ki? Hararanta zarah tayi tare da fadin kinfi kowa sani ai, dariya jawaheer tayi tare da janyo hannuta suka shiga ta rufe kofar, zarah tace nazo inji gaskiyan lamari wlh tunda naga pics din nan na kasa zama, a ina kika sanshi? Jawaheer tace ai baki yarda ba kika sani mako editing nayi na pics din, zarah ta harareta tare da fadin ban san wulakanci fah, dan Allah ki fadamin, jawaheer tace toh bari kiji nan da wata biyu za muyi aure, zarah tace kai plz fadamin yanda kuka hadu, labari jawaheer ta fara bata tun daka sanda ta fara ganinshi a tv ta rude, har yanda suka hadu tare da fada mata dan mum ne, bata dai boye mata komai ba dan tasan wata rana kowa zai san gaskiya, zarah tace kai ikon Allah, wlh na tayaki murna kunyi mugun dacewa amma sai dai naji kince baya sonki? Jawaheer tace uhm, zarah tace nifa nasan yana sonki inda baya sonki wlh bazai yarda ya aureki ba, jawaheer shuru tayi can tace kai anya hakane kuwa, tausayina kawai yake, zarah tace tausayi alaman soyayya ne, jawaheer tace da kamar wuya, zarah tace nan gaba zaki gani, Allah ya bayyana miki iyayenki jawaheer ta amsa da ameen, nan suka ci gaba da fira yanda zasu tsara biki, zarah tace nasan a can kasar su za'ayi, jawaheer tace aini ko a ina ne buri na a daura dariya zarah ta saki tare da fadin Allah ya nuna mana zamu dauki hoto da manyan celebrity, dariya jawaheer tayi tare da fadin ke kuma shine damuwarki, tace eh din, tashi jawaheer tayi tare da fadin ina zuwa fita tayi jim kadan sai gata dasu snack da drinks ta kawo ma zarah, zarah tace ni a koshe nake drinks din zansha kawai, fira suka dinga yi har jawaheer ta dan manta da damuwanta duk da abun yana dan damunta na rashin jin m samir, zarah sai wajan 5 ta tashi zata tafi fitowa sukai tama mum sallama sannan suka fita tama mum sallama har wajan motarta jawaheer ta kaita wanda yayi dai2 da shigowan khalil fakawa yayi kusa da motar zarah, fitowa yayi cikin fara'a yana fadin kice da banzo da wuri ba dakin tafi tace wlh kuwa, ozil shima fitowa yayi jawaheer ta saki ihun murna tare da fadin manya an dawo garin, dariya yayi yace kai m samir kina kawo light fah, naji labarin kinyi nasara, dariya tayi tace haka yake, yace zamu sha biki, lallai Allah ya amshi addu'arki, dariya tayi sannan suka gaisa da zarah ta shiga motarta ta wuce su kuma sukai cikin gida.












BAYAN SATI DAYA






yau ake wasan su m samir tunda ya tafi basu waya da jawaheer ba, tayi mugun shiga danuwa sosai, a yanzu haka tana zaune a daki tana jiran lokacin wasan nasu yayi ta kalla, lokaci nayi ta kunna tv dinta, tana kunnawa taga sun jeru a fili ga mutane nata ihu, hangoshi tayi cikin kayan kwallo wanda yake kara fito mishi da kyanshi, wani irin murmushi tayi na ganinshi koba komai kallonshi da tayi yasa taji dadi,wasa aka farayi inda su m samir suka lashe wasan, jawaheer kam tayi murna sosai musamman da samir dinta ne ya lashe zaban, haskoshi akayi yana daga hannu mutane nata ihu, fitowa sukayi inda yan jarida keta cinjirindo tare da son yin magana dashi,tsayawa yayi yan jaridan suka zo, yace abu daya zance nasan yanzu someone is missing me alot, nasan komai nake kina kallo na i just want you to know that i miss you too, jawaheer dake kallon tv taji wani irin dadi tare da sakin dariya lokaci daya fuskanta ya canza ganin sonia tayi hugging dinshi.........


























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🀝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 43-44


















*BABA BUHARI DODAR CONGRATULATION BABA BUHARI NEXTLEVEL NEXTNIGERIA ALLAH YAJA KWANA BABA BUHARI YA TAYAKA RIQO BABA BUHARI YACI ZABE KAI KUBAN KIDAN MASU GUDU SU GUDUπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ*










Wani irin hawaye ne ya zubo mata tare da fadin dama har yanzu suna tare, gani tayi ya waigo domin ta baya tayi hugging dinshi da alama yana son ganin waye ya riqeshi, ganin sonia ce yasa ya saki dariya jawaheer na ganin haka ta kashe tv din tana kuka, wayanta keta faman ruri jin karan kaman ya dameta yasa ta duba dan taga ko waye, ganin sunan zarah yasa ta kura ma wayar ido, har ya tsinke, wani kiran ne ya kuma shigowa dan haka ta dauka, tana dauka zarah tace jawaheer kina kallon abunda ke faruwa? Jawaheer tace eh ina kallo, zarah tace amma wacece ita? Jawaheer cikin kuka tace itace sonia da nake cewa basa tare, ashe har yanzu suna tare nidai na shiga uku, zarah tace ina zuwa anjima kadan zan zo, jawaheer tace sai kinzo tare da kashe wayan, taci gaba da kukanta tare da jin wani abu na sukanta a zuciya, lallai tana son m samir amma bata tunanin zata iya hadashi da ko wace mace domin tana da bala'in kishi, ji tayi kirjinta har nauyi yayi dan tashin hankali, tana cikin wannan halin zarah ta shigo, tsayawa tayi tana kallon ta, matsawa tayi kusa da ita ta dafa mata kafada, firgit tayi dan bata san tama shigo ba, ganin zarah ce yasa ta goge hawayen dake fuskanta, zarah dan murmushi tayi tare da fadin jawaheer miye haka? Hararan zarah tayi tare da fadin ban sani ba, bayan kin gaka komai amma kina wani tambaya na, zarah tace haba jawaheer ke yanzu wannan abun kike ma kuka? Cikin kuka tace to mai zanyi zarah? Wlh ina son samir ina kishin shi ban san inga wata mace kusa dashi, wlh ji nake kaman zuciyata zata buga, zarah tace wlh jawaheer kina bani mamaki duk da nasan so ba karya bane kina ma samir mahaukacin so wanda bakya gane gabanki balle bayanki, namiji yace yana sonka ya ka kaya balle ke kika ce kina sonshi aiko kin san hakuri ya zaman miki dole akan duk abunda zaki gani, balle ma shi wanda kike so celebrity ne kinga baki da bakin magana, cikin kuka tace zarah nasan celebrity ne nasan bazan rabashi da mata ba, amma ki fahimta ita sonia budurwanshi ce, zarah tace eh na sani amma hakuri za kiyi ni in banda so sone aida nace wlh kiyi hakuri dashi tunda shi bawai yana sonki bane, jawaheer tace zarah idan na hakura dashi wa zan aura duk namijin dana aura toh ba zuciyata ya aura ba face gangar jiki na, domin zuciya na da ruhi na yana wajan samir ina gudun tarin zunubi domin wlh koda na auri wani tunanin samir zanyi tayi kinga kuwa haramun ne inyi tunanin namijin daba miji naba, zarah tace ikon Allah gaskiya Allah ya jarabceki, jawaheer tace hakane ina fatan Allah ya bani ikon juriya da hakuri, zarah tayi murmushi tace a hakan dan wannan abun da kika gani hankalinki ya tashi kin kasa sukuni, dariya tayi sannan tace zarah baki san kishi ba ina son samir fah wlh amma kin san wani abu kuwa? Zarah tace sai kin fada, jawaheer tace wlh bazan iya juran ganinshi da wata mace ba musamman sonia indai koh suna tare zan hakura dashi har abada, zarah ta kwashe da dariya tare da fadin kaman dagaske, jawaheer tace wlh kuwa dagaske nake gwara sonshi ya kashe ni akan inyi kishi da wata, zarah tace kawai ki yardan da yusuf musha biki hararanta tayi tare da fadin rufamin asiri ina zan kai mai mata harda yara biyu, indai zan iya auran mai mata inyi hakuri da samir dina mana, dariya zarah tasa tare da fadin kai jawaheer toh ba gwara ki aura mai sonki ba, jawaheer tace na bar miki shi, ni tashi ma mu dan fita ko zan danji dadi, zarah tace ok amma ya kira ki kuwa? Tace a'a bai kira ba na kira kuma yaki shiga, Zarah tace son maso wani....... Tsaki jawaheer tayi tare da fadin ke kika ga wahala, fita sukai cikin motar zarah wajan saida ice cream suka nufa.












M samir bayan yaga sonia ce abun ya bashi mamaki itama ta lura da hakan dan haka taja hannunshi sukai mota, aka ja suka wuce, gidanshi aka kaishi suna shiga ta fara fadin baby mai yasa ka shareni dama baka so na? Ashe zaka iya barina ba tare daka neme niba? Yace to mai zan miki bayan ke kika tafi da kanki and kuma kin bani zabi wanda kin san bazan iya bi ba, toh mai yasa zan nemeki? Baki ta saki tana mamaki yanda taga yana mata magana, amma da yake yar duniya ce saita basar tare da matsawa kusa dashi tana shafa mai kirji tace haba dear kabar tunawa kasan bazan iya rayuwa ba tare dakai ba nasan kaima haka dan muna son junan mu, dan tureta yayi tare da fadin is too late now, tace ban gane bah, yace biki na saura 1month 2week, tace what? Lokaci daya kuma tayi dariya tare da fadin u r not serious, murmushi yayi tare da fadin dagaske nake miki, kuka ta saki tare da fadin kasan ina sonka mai yasa zaka min haka dama ba sona kake ba? Ganin yanda take kuka yasa ya janyota jikinshi ya fara rarrashinta tare da fadin sonia ina sonki amma kece kika gujeni, cikin kuka tace kayi hakuri koda na barka naji jiki na kasa hakuri dakai sai yasa nazo gareka gashi kana fadamin zakai aure nifa ya zakayi dani? Dan shuru yayi ba tare da yace mata komai ba, ta kara fadin plz answer me, yace muje ki huta z Muyi magana, dakyar ya jata yai toilet da ita dan tayi wanka, yana turata ya rufe mata kofar duk da tayi kokarin ta janyoshi wai suyi wankan tare amma yaci sa'a ya fita, koda ya fito falo ya koma ya zauna tare da tunanin ya zaiyi da sonia yasan yana sonta sosai domin ita ce first love dinshi, toh amma mai yasa baya jinta kaman da? Jin hannunta yayi a cikin riganshi tana wasa da kirjinshi, da sauri ya janyota tare da cire hannun nata daka kirjinshi kallo daya yayi mata ya kawar dakai domin daka ita sai towel, ta lura dashi amma saita basar ta kuma sa hannunta cikin riganshi tare da fadin i miss you my baby, plz let me feel you, kallonta yayi tare da fadin plz stop it kin san bana son irin haka, tace oh come on baby, ganin inya zauna tana shafa shi komai zai iya faruwa tashi yayi da sauri tare da fadin zan fita yana fadin haka yayi waje, sakan baki tayi sololo tana mamaki bayan ya fita tace uhm samir duk ka gama wayanka dole ni zaka aura bazan taba bari ka auri wata ba, sannan yau din nan sai munyi sex gwara ma ka daina wani guje guje, yar dariya ta saki tare da fadin na dade ina son jin kalan zumanka dan nasan ko kadan kai ba ragon namiji bane, hakuri na ya kare dan haka yau zan dana kalan baiwanka dariya ta saki sosai.












Koda samir ya fita gidan dad dinshi ya nufa, bayan ya isa muhd ali yayi hugging din yaron nashi cikin fara'a tare da fadin my boy ya bubbuga mai kirji tare da daga hannu alaman yana alfahari dashi, sannan yace wasanku yayi kyau, samir yace nagode dad, tare da zama akan kujeran falon, dad din yace ya maganan tafiyan mu jibi? Yace tana nan

Please Login or Register in order to submit comment