Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne adda tah, adda tace ni karki samin ciwon jiki miko min jakata, tashi tayi ta dauko mata jakar tata, adda ta bude ta ciro wata leda, gora ne guda hudu, taba ma jawaheer gora daya tace gashi maza shanye, tace miye wannan kuma? Adda tace dallah shanye ban son surutu dariya tayi tare da fadin toh mutum zaisha abunda bai sani bane, tsaki adda tayi tace kyaji dashi, bude goran tayi ta kafa kai ta shanye, adda ta kara mata wani, duka gora uku ta shanye, ya rage saura daya adda tace wannan kuma gobe zan baki shi, tace toh yar tsohuwa, nan sukai ta fira tare da bata shawarar yanda zata biyar da mijinta....... Adda tace jawaheer aure ba abun wasa bane, ba abunda za kayi bane yanzu anjima kace bakayi, shi aure anayin shine har abada, dan haka ina mai baki shawara da kiji tsoran Allah ki riqe mijinki da hannu bibbiyu kiyi mishi biyayya yi nayi bari na bari domin aljannarki na karkashin kafarshi yin biyayya ga miji na kara mishi son matarshi, sannan duk inda kike ki zamto mai riqema mijinki mutuncinsa, zaisa mijinki ya yarda dake karki kuskura ki bashi hanyar da zai fara zarginki, domin zargi yana lalata aure, tayi ma jawaheer nasiha mai ratsa jiki inda daka karshe tace mata shi zaman aure hakuri ne gaba dayanshi kin san duk abunda akace bauta sai anyi hakuri, sun dade suna fira kafin ta tafi dakinsu taga zarah nata bacci abunta wayanta taga yana wuta da sauri ta duba taga 11 miscall sa sauri ta bude taga duka na samir ne, kiranshi tayi kashe wa yayi ya kirata da sauri ta dauka tambaya ya jefo mata da fadin ina kika shiga? Tace ina dakin adda, yace tazo ne? Tace eh dazu tazo shine naje muna ta fira, murmushi yayi tare da fadin shine kika manta dani koh dan kinga adda, tace ko daya kana raina koda yaushe kasan ni ce nake sonka kaga kenan bazan manta dakai ba, yaji dadin magananta sannan yace wani irin so kike min? Tace sonda nake maka bazai iya misaltuwa ba, amma ka bari a hankali zaka fahimta, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin gobe ina nan tafe mai zaki tanadar min? Tace mai kake so? Yace ke kawai nake son gani dariya tayi tare da fadin saurin mai kakeyi? Yace nayi missing dinki sosai uhm kawai tace, murmushi yayi tare da fadin bari in barki sai na dawo goben, tace ok Allah ya kawo min kai lafiya ya amsa da fadin ameen, itama kwanciya tayi tana tunanin samir dinta yanzu gobe shikenan mun zama mata da miji.












Rana dai bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji masu iya magana, yau take friday ranan daurin auren jawaheer da samir da misalin karfe daya da rabi aka daura auren akan sadaki naira dubu dari wanda dubbanun mutane suka shaida cikin daurin auren harda shugaban kasar spain da manyan yan kwallon kafa da abokan arzikin samir duk sunzo tare da masoyanshi shugaban kasar nigeria shine wakilin jawaheer, an daura aure mutane sun watse ana ta san barka, tunda aka daura auren aka fadama jawaheer wani irin faduwa taji gabanta nayi ga jikinta yayi mata wani irin nauyi ta rasa gane wani irin yanayi take ciki farin ciki take ko akasin hakan, tana zaune a dakin adda ta kwanta adda ta shigo tana fadin kinzo kin kwanta a nan ga mutane can anata tambayanki har samir dinma ya dawo ashe kina nan, bata motsa ba balle tayi magana, jin muryanshi tayi ya shigo dakin lumshe ido tayi yau itace rana ta farko da take jin kunyan hada ido dashi, kiran sunanta yayi da jawaheer tashi kiga kyautar da nace zan baki ranan daurin auren mu, kamar karta tashi amma ta tashi taga wata mata amma tasa nikaf da wani namiji kallo daya zaka masa kasan balarabe ne, namijin ya fara fadin Allahu akbar wlh wannan yarki ce nadia ga kaman ku nan sak, jawaheer kam ta shiga rudani, matar ta cire nikaf jawaheer bata san lokacin data saki ihu ba tare da nuna matar da hannu dan tabbas itace a wannan hotan na passport lokaci daya kuma tasa kuka tare da fadin dama kina raye shine baki taba nema naba? Matar ta matso kusa da ita tana kuka dai dai lokacin mum da dad suka shigo dad yace tabbas itace ta bamu jawaheer, matar tace jawaheer shekaru ishirin da biyu yanzu ina fama da ciwo wanda ba komai yaja min ba sai tunanin kina wani hali, a ina zan ganki na bata tsawon wannan lokacin da tunanin inda zan ganki iyayena sunce in cireki a raina dan sun san hala kin mutu amma naki yarda da hakan, sai gashi a yau tunani na ya zama gaskiya ta nuna m samir tace lallai jawaheer kinyi dacen miji shine ya sadani dake Allah yayi ma aurenku albarka, jawaheer cikin kuka tace mai yasa kika bayar dani mai yasa kika gujeni tun ina yar karama ta? Matar ta nisa sannan ta sauke ajiyan zuciya tace yanzu zan fada miki.....










TUNA BAYA.....


sunana nadia ahmad yar kasar saudiya iyayena mu biyu suka haifa nida yayana muhd, mun taso cikin gata da kulawa kasancewan mahaifina mai kudi ne shi sosai, ummi na tana ji dadi fiye da komai nata tun ina yar karamata ake fadamin inada kyau, tun banyi wayau ba nake da burin zama doctor sau tari in ummi ko abba na tambaya na mai zan zama sai ince doctor haka na taso da son zama dr har na gama secondary skul dina na fara jami'a inda na sami course din da nake so wato dr, zan karanci fannin zuciya hawan jini da suger, a lokacin maza da dama suna rubibina amma bana basu dama, domin karatu nasa a gaba, gashi iyayena duk abunda nace shi sukemin har yayana yayi aure amma ni ban taba tunanin yin aure ba harna kammala karatu na fita da first class gwamnatin saudiya ta bani aiki duk da dad dina yaso ya gina min asibiti na kaina nace a'a kasata zanma aiki, ana cikin haka wani dan uwan abba na yazo yace yana sona naki yarda abba na har yayi fushi tare da fadin ya kamata ace nayi aure, nace mishi zanyi amma ba yanzu ba, ana cikin haka shugaban kasar nigeria a lokacin yazo da mahaifinshi asibitin da nake aiki wanda a lokacin ciwon zuciya yake nice dr din da zan dubashi, cikin ikon Allah na fara dubashi yana samun lafiya, ashe president muktar kabir sona yake lokacin kasancewan mahaifin nashi ya dade a asibtin yasa muka saba dasu, harya samu sauki aka sallameshi bayan sun koma muna waya akai akai harya fito ya fadamin abunda ke ranshi a lokacin nima banyi musu ba na amince mukai ta soyayya har magana taje wajan iyayena inda suka nuna su sam bazan auri dan nigeria ba sai dai in auri dan kasata, haka naki yarda na bijire musu har abinci na daina ci na daina sha na rame sosai, ganin haka yasa sukace sun amince amma duk abunda ya biyo baya babu ruwansu, hakan yamin dadi ba tare da tunanin komai ba nace na amince, haka akayi bikin mu aka tawo dani nigeria muka sauka a villa, inda matarshi take mai suna hauwa, matarshi ta amsheni hannu bibbiyu hakan yamin dadi, saida mukai sati biyu muna amarci kafin ya koma kan kujeransa wanda yaba mataimakinsa na wucen gadi, mutane da dama suna ta bani kyauta dan inyi musj hanya wajan mijina, daka baya ya hana dan baya son kowa ya sanni, haka na daina fita amma ita uwar gidanshi kowa ya santa, haka muke zama dashi bai taba haiyuwa ba, ina zuwa kam na sami ciki, tun daka lokacin na fara ganin sauyi wajan kishiyata yayin da mijinmu ke murna, a lokacin ta fito da kishinta karara harda kanin mijinmu yake biye mata ita tana tsoran in haiyu in mijin mu ya mutu in fita gado tunda ita ance ba zata taba haiyuwa ba, shiko kanin mijinmu yna tsoron in haiyu a hanasu gado, hka suka tsangwameni, wata rana president yayi tafiya suai hatsari a jirgi babu wanda ya rayu, gashi a ranan na haiyu, a gida aiko inata wajan window din daki na naji hauwa da kanin mijinmu suna fdin suje su kashe abunda na haifa, babu shiri naje dakina na dauko kudade nasa da password dina nayi sauri nayi rubutu, na fita daka gidan ashe sun ganni suna ta bina shine na hadu da wa innan bayin Allah na basu ke da nufin koda sun kama ni, ni daya zasu kashe, amma Allah bai basu sa'a ba na tsere, dakyar na samu akamin password da wuri nabar kasar na koma saudiya wajan dangina, koda na fada musu abunda ya faru, abba ya fadama gwamnatin saudiya ta kwatar min yancina yanzu hauwa da kanin mahaifinki suna bursuna za suyi shekara hamsin da aiki mai tsanani tunda sunyi niyan kisan kai Allah bai basu dama ba, har yanzu ba'a raba gadon mahaifinki ba saboda baki dawo ba kuma hauwa na prison, nasha zuwa nigeria ko zan ganki amma babu wani labari sai shekaran jiya wannan bawan Allah yazo min da maganarki da farko ban yarda ba saida muka ga pics dinki ya kuma fadamin shine zai aureki, naji ddi sosai domin shiba karamin mutum bane sananne ne, kuma naji dabi'unsa masu kyau ne ta nuna mutumin da suka zo tare tace ga yayana , rungumeta jawaheer tayi tana kukan murna tare da kara godema Allah da aka haifeta ta hanyar aure nadia taita ma su dad godiya bayan an kimtsa dad ya dauko kudi yaba nadia yace ga kudin da kika bamu lokacin, kai ta girgiza tare da fadin dawainiyar da kukayi da jwheer banda abunda zan biyaku wannan kudin naku ne halak malak, dad yana ta mata godiya, samir kam sai kallon jawaheer yake yana bukatar su kebe amma taki tashi kuma ta lura da hakan.......
































*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 53-54














Mum din jawaheer ta kalli samir tace wani shirye shirye za kuyi kuma yanzu? Yace dinner ne amma a spain za ayi da yau kuma so mu wuce can ma dan dinner din gobe ne, nadia tace eh toh sai a shirya koh tunda kun tsara hakan, hakan ko akayi aka fara hadama jawaheer abubuwan bukatanta harda kawayenta aka akai airport cikin masu tafiyan harda adda😀 jawaheer ita da m samir suna mota daya driver na jansu, hannunta ya riqe tare da matsewa yace kin kara kyau da girma miye sirrin? Fisge hannunta tayi dariya yayi yace nayi laifi kenan? Kai ta girgiza alaman a'a, tace ban san da wani baki zan maka godiya ba, amma zan dan gwada nagode daka sadani da mum dina yau ya kasance min ranan farin ciki ranan da aka daura min aure kuma ranan daka kara min wani farin cikin nima Allah ya bani ikon faranta ma.... Toshe mata baki yayi da hannunshi sannan ya matsa kusa da ita yace yau nima zaki bani abunda nake so, tureshi tayi ya fara dariya ita kam ta rufe fuska har suka isa airport suka shiga jirgi, jirgi biyu ne aka basu dan mutanan sunyi ma jirgi daya kadan dan naga harda yan jawaheer fans group a tafiyan da yan hausa novels da yan maryam obam novels da sauransu...... Kowa ya shiga jirgi aka daga zuwa kasar spain duk yawan mutanan nan a hotel aka saukesu sannan ance suci komai kyauta duk abunda sukeso ga kudi da aka basu gaskiya sudai shar yan biki, ita kam jawaheer da mum, dinta da dad dasu adda gidansu na kasar suka sauka, jawaheer da mama take kiran mum dinta, jawaheer na makale da mamanta shiko samir gidanshi ya nufa yana shiga yaga sonia abun ya bashi mamaki hugging dinshi tayi tare da fadin congratulations na tayaka murna, abun ya bashi mamaki musamman da bata nuna komai ba akai, dakinshi ya nufa ya fada toilet dan yayi wanka bai dade ba ya fito yasa wasu kananan kaya sunyi mishi kyau sosai, ji yayi yana son jin muryan jawaheer dan haka ya dauki wayanshi ya doka mata kira, amma a kashe dan tsaki yayi tare da fadin bata sa sim dinta na nan ba, tashi yayi ya fito baiga sonia ba dan haka ya fice direct gidansu jawaheer din ya nufa inda ya samesu su duka a falo suna ta fira, shima zama yayi aka fara firan dashi, mama ta lura da jawaheer yake son gani dan haka ta kalleta tare da fadin jawaheer tashi ku dan zaga mana, tashi tayi shi kam dadi yaji, tashi yayi shima suka fita, wajan wata bishiya suka je a bayan gidan, zama sukai a kasa ya janyota jikinshi tare da fadin na rasa mai yasa bana son inga ina yin nesa dake, in nayi nesa dake sai in dinga jin wani iri, dariya tayi tare da fadin toh fah, toh mai yasa hakan ke faruwa? Yace shine nake so ki fadamin miye sirrin abun, hannunta ya riqo yana shafawa bata ce komai ba ganin haka yace jawaheer yau zan tafi dake koh? Da sauri ta dago tare da fadin dan Allah ka rufa min asiri, tamke fuska yayi yace kaman ya keba matata bace? Ina da iko inyi duk abunda naga dama dake babu wanda zaice min danme, tace hakane amma ai saika bari a kawo ni kaman yanda al'adanmu yake, yace ni bana son wani al'ada tunda ba addini bane, baki ta dan turo alaman taji haushi bata ankara ba taji bakinshi cikin nata, kissing dinta yake sosai tun bata mayar mishi da martani harta fara, sunyi wajan minti biyu suna tsotsan bakin junansu sannan ya saketa ta lumshe ido, ido ya zuba ma fuskanta yana kare mata kallo, lallai nayi dacen mata kyakyawa mai addini yar gidan mutunci, Allah na gode maka daka bani jawaheer a matsayin mata, gaba daya jikinta yayi weak bude idonta tayi taga ita yake kallo tayi sauri ta kuma rufewa dariya yayi tare da dagota daka jikinshi yace oya tashi muje yunwa nake ji, tace akwai abinci a ciki bari in kawo ma, yace nop muje akwai inda zamu ci, tace ok ina zuwa ciki ta shiga jim kadan sai gata ta fito ta canza kaya ido ya bita dashi komai jawaheer tasa yana amsanta, motarshi suka shiga shike tukawa har wani katon hotel ciki suka shiga, direct restaurant din hotel din suka nufa, masu abincin suka basu list na abincin suka nuna ba'a dade ba aka kawo musu, sunci sunsha sannan suka tashi wani daki taga ya bude gabanta taji ya fadi, amma haka ta daure ta shiga, bayan sun shiga kwanciya yayi akan gadon dakin tare da kallonta yace kunna min ac din, kunna mai tayi sannan ta sami waje ta zauna cikin kujeran dake dakin, kallonta yayi tare da bude mata hannunshi alaman tazo inda yake yi tayi kaman bata ganshi ba, ya lura da hakan yayi dan murmushi tare da tashi ya dauketa cak ta fara zillo amma ko a jikinshi kan gadon ya ajiye ta, tazo zata tashi ya janyota jikinshi tare da fadin muyi bacci, a hankali tace ni bana jin bacci, bai kulata ba sai kara manneta da yayi a jikinsa, bai dade ba bacci ya daukeshi yayi bacci sosai har wajan magrib tashi yayi tare da salati jin ana kiran sallah yasa ya tasheta da sauri tare da fadin tashi kiyi sallah, fita yayi ya nufi masallaci shima, koda ya dawo yaga ta ciro wani zanin gado ta yafa tayi sallah dashi, bayan ta gama yace su tafi, shiryawa tayi suka fita, bayan sun shiga mota yace mata gobe karfe hudu masu gyaraki za suzo, saiki zama ready suna tafiya yana mamin wakar da yasa na nicki minaj, har suka karasa kofar gidansu ya sauketa shima ya karasa nashi, koda ta shiga ta gansu a falo sai taji kunya amma sai basu nuna sun sam tana yiba, sai adda da tace sai yanzu bata ce komai ba ta sami waje ta zauna kusa da mum, tace mum gobe 4 masu makeup za suzo yace in shirya mum tace Allah ya kaimu, tashi tayi ta musu saida safe sannan ta wuce dakinta, tana sallah isha'i ta kwanta bacci.












Washegari tun da safe gidan ya kacame anata gyare gyare duk da ba taro za'ayi a gidan ba, lokaci kadan gidan yayi kyau ga kamshi na tashi tako ina, jawaheer sai wajan 10 ta fito adda ce ma take ta buga mata kofa sai yasa ma harta fito, bayan ta fito adda tace mutum ya kwanta yaita bacci har yanzu, tace kai adda bazaki bar mutum ya huta ba wlh, adda tace malalaciya ni ban taba ganin amarya mai son jikinki ba anya ma zaki dinga dafa mai abinci kuwa? Jawaheer tace haba girki sai kace zamaninku salati adda ta saki tace amma ko wannan zamanin naku ba abun arziki kuka koya ba, toh a ina zai dinga cin abincin? Tace wajan saidawa adda taita bala'i wai taya zata bae mijinta ya dinga cin abincin saidawa saboda lalaci, su mum kam babu abunda suke sai dariya, dinning ta nufa ta zuba abinci ta fara ci, sallamanshi taji idonshi na kanta ganin irin kallon da yake mata yasa ta sakar mai murmushi, adda data lura dasu tace mutum dai ya kalli gabanshi kar yaje ya fadi, shi kam ba hausa yake jiba, jawaheer kam ta gane dasu take, dan haka ta kawar da kanta daka kallonshi, taci gaba dacin abincinta, gaida su mum yayi da mama suka ansa sannan ya gaida adda da fadin ina kwana adda? Amsawa tayi da lafiya qalau, itama jawaheer gaidashi tayi da fadin morning, amsawa yayi ba tare daya kalleta ba, zama yayi kusa da mama yace ya kwanan kasar? Mama tace alhmdlh ya shirye shirye? Yace an gama komai babu abunda ya rage, tace toh alhmdlh Allah ya taimaka, ya amsa da ameen khlil da dad da muhd da kabir da umar ne suka shigo cikin gidan, gaisawa sukayi sannan suka zauna anata tattaunawa yanda abun zai kasance samir yace ya gama shirya komai karsu damu, jawaheer bayan ta gama cin abinci barin falon tayi ta nufi dakinta, kwanciya tayi dan bata koshi da baccin ba adda ta tashe ta, amma sai dai kuma me gaba daya ta kasa baccin sai tunani, yau itace a matsayin matar m samir, tashi tayi ta fito falon ta kalli samir tace plz ina aka sauke baki zarah na can tace tare da kawayenmu zasu zauna, gashi ina bukatarta a nan, yace zaku hadu ai daka wajansu nazo nan, na bada kayan da za susa ankai musu ma, tace ok tare da komawa ta zauna akan kujera kusa da adda, m samir tashi yayi ya wuce haka sukai ta fira.












Wajan 5 masu makeup suka zo, saida tayi alwala kafin ta zauna aka fara mata, ana cikin makeup din aka kira sallah, saida tayi sallah akaci gaba, kwalliya ake mata na kece raini, wedding gown aka sa mata, jin kiran sallah isha'i yasa tace a cire mata abun kanta tayi sallah, haka suka cire tayi sannan suka kara gyara mata, wow fadin irin kyau din da tayi bata lokaci ne, bazai ma iya faduwa ba, bayan an gama aka rufe mata fuska suka fita cikin wata dangareriyan mota suka shiga da ita, a ciki ta sami samir shima yasha suit fari irin kayanta fari, kallonta yayi tare da fadin wow my princess kinyi kyau sosai, murmushi tayi ba tare da tace komai ba, driver yaja mota suka tafi bayan sun karasa dangareren hall din tare suka jera da kawayenta da suka sa black gown mazan ma haka har cikin hadaddan hall din, zama kowa yayi inda karan kida ke tashi masu rawa nayi, amarya da ango akace su fito su zo suyi rawa, hannu ya miqa mata ta miqa mai nata suka fara rawa gwanin sha'awa zarah taki yarda tayi rawa da kowa saboda khalil na wajan, bayan amarya da ango sun zauna nan aka fara basu gift suna amsa, cikin masu bada gift din harda sonia wacce taba zarah ta amsa tayi godiya, murmushi sonia tayi tare da komawa ta zauna, anci ansha gaba daya kayan aka kwashe akai mota dasu, yanda aka tsara daka dinner zai tafi da ita, ita bata ma san hakan aka tsara ba, saida aka gama suka shiga mota, wani dangareren gida suka nufa bayan mota ta faka yace ta fito fita tayi sukai ciki, gidan ya hadu sosai a falo suka tarar da gift din da aka basu, gaba daya anyi raping dinsu, gasu manya wanda sonia ta bata ta dauko shine karamin ciki, zata bude samir ya amsa ya fara budewa zobuna ne guda biyu masu shegen kyau ko wanne an rubuta S&J ma'ana samir da jawaheer kamo hannunta yayi yasa mata daya shima yasa nashi, tunda yasa mata ta zauna a kasa murmushi yayi tare da kokarin dagata amma tayi wani irin wurgi dashi wanda saida ya bugu da bangon dake kusa dashi, cikin tsoro da mamakin irin tureshi din da tayi ya fara kokarin tashi nufanshi tayi ta shake mai wuya tare da fadin yau zan kashe ka, lokaci daya kuma ta saki dariya tare da kara jefar dashi wannan karan akai ya bugu harda jini ya fara zuba, dariya ta saki mai karfi tare da sauti gashin kanta duk ya mimmike tsaye........ Toh fah muje zuwa
















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 55-56
















Riqe kanshi yayi da yake ta zubar da jini, a wannan karan baiyi yunkurin tashi ba, sai kallonta da yake da ido, yana mamakin maiya sameta lokaci daya haka, kodai aljanu gareta? Kai anya inma aljanu ne...... Ganinta yayi a tsugunne a kusa dashi tana dariya mai karfi magananta yaji ya canza kaman ba nata ba, gashin kanshi ta danqo da karfi duk da yana jin zafi baiyi kokarin hanata ba, haka ta dagashi sama ta kuma yin wurgi dashi tare da fadin zan kashe ka, ka shiga gonar daba taka ba duk cikin turanci take maganan, lokaci daya kuma tasa kuka mai ban tausayi, samir kam tunda tayi wurgi dashi ya bugi wani glass bai san inda kanshi yake ba, jin ruwa yayi a kanshi da sauri ya bude ido ganinta yayi tana dariya ga idonta ya rune yayi baki sosai, ga gashin kanta duk ya mimmike a hankali ya sauke idanshi akan komai na falon duk ta faffashe komai na falon komai ya wargaje ga jini itama na zuba a jikinta alaman taji ma kanta ciwo, da sauri ya tashi da nufin ya riqota amma ina wani irin ihu ta saki tare da shako mai wuya lokaci daya kuma tayi 'kasa tana surutai ganin ta sakeshi yasa yayi kokarin fita dan ya kira security dinshi su taimaka a kamata ji yayi ta janyo shi tare da wurgar dashi a kasa, tace kar kayi tunanin yin wani abu duk wanda ya shigo cikin gidan nan saina kashe shi, matsawa tayi daka inda yake ta zauna akan kujeran falon tana kallonshi tana dariya, shi kam gaba daya ya firgita da ita ya rasa ma abun yi, bai kara yinkurin tashi ba ga dariyan da takeyi babu dadin ji, ga tsoro, ganin karan ya isheshi yasa ya yankura ya tashi ganin ya mike yasa ta nufoshi amma wannan karan addu'a ne a bakinsa harta karaso inda yake tana kamashi ta sulale kasa tabata yayi yaga alaman kaman ta sumene da sauri ya dauketa yayi wani daki da ita ya rufe da key, fita yayi daka gidan cikin daren direct gidansu ya nufa, nocking yayi aka bude mai, mum ta tsorata da ganin dan nata jiki duk jini, tace samir lafiya maiya sameka? Bai iya furta komai ba sai shiga falon da yayi ya zauna yana maida numfashi kowa dake gidan ya

Please Login or Register in order to submit comment