Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinga cirewa cikin kudin aikinshi, haka muketa rayuwa cikin kwanciyan hankali tunda na haifi khalil ban kuma samin ciki ba, abun yana damuna dan ina son samun yarinya mace, su umar har sun fara zuwa makaranta, wata rana munje anguwa nida mijina, motarmu tayi faci, nan ya fara kwance taya yana gyarawa ni kuma ina tsaye kusa dashi saiga wata mata tana ta gudu da alaman wasu ne suka biyota, tana zuwa wajanmu ta mika ma mijina kwali tana fadin dan Allah gashi akwai komai da komai a ciki ka ceci rayuwar yata daka fadawa halaka, tana fadin haka tabar wajan ta wuce da wajan minti biyar lokacin har mun shiga mota muna jimami tare da fargaban maita bamu, saiga wasu mutane da makamai sunzo sun wuce da gudu suna fadin miyi sauri karta bace mana, jin haka yasa muka gane kasheta suke son yi, haka muka karasa gida muka shiga da kwalin budewan da zamuyi muka ganki kina bacci abunki tare da magudan kudade dollars na amurka, mun tsora sosai wata takarda muka gani anyi rubutu kaman haka..... *salam ga duk wanda ya tsinci wannan yarinyar inaso ya riqemin ita amana wlh yar sunna ce bata hanyar zina aka sameta ba banda lokacin yin bayani sosai kar lokaci ya kure min, sunanta jawaheer duk wanda ya dauketa yayi amfani da wannan kudin na bashi halak malak, idan na rayu zan dawo neman yata wata rana in kuma sun kashe ni, shikenan* kallon juna muka fara nida mijina yace bazai dauki kudin ba zai kaiki wajan police dan yana tsoro ni nayi ta nuna mishi yayi hakuri mu taimakeki mu riqeki amanace mahaifiyarki ta bamu, da farko kaman taso ta ajiye kine sai Allah ya hadamu ta bamu, dakyar ya yarda lokacin da mukaje canzo kudin naira million dari ne kudin dai2 wlh munyi mugun firgita da yawan kudin, tun daka lokacin ya fara business da kudin yabar aikin banki rayuwa ya canza mana sosai, wlh jawaheer ina masifar sonki na dauki son duniya na daura miki haka mijina da nake ganin yafi kowa sonki domin yace tunda ya sameki Allah ya bude mishi kofofin arziki baya son ganin fushinki ko kadan munsha yin fada akanki nida shi, idan kikai abu na miki fada to in raina yayi dubu saiya baci sai yasa kika fi sabawa dashi dan yana yawan tafiya dake wlh ina takaicin fada miki bamu bane muka haifeki..... Kuka jawaheer take sosai lokaci daya ta fara fadin yanzu ba'asan inda iyayena suke ba, na shiga uku shikenan bani da wani gata a duniya mai yasa mum dina bata tafi dani ba, anya ma ta auren aka sameni kuwa kaman yanda ta rubut.... Mum ce ta toshe mata baki duk wanda ke wajan saida ya tausaya mata m samir shima hawaye yake amma bai bari sun gani ba dan da turanci mum ta fada mata komai, wani irin tausayin jawaheer yaji yana shiganshi sosai, shi gashi yaga mahaifiyarshi tare da taimakonta lallai shima ya zama hakki a kansa ya neman mata iyayenta, lokaci daya ya kalli mum yace mum babu wani shaida da za'a gane inda iyayenta suke? Mum tayi shuru can tace akwai international password da hotan mamanta a jiki, da sauri yace yana ina?? Mum tace yana gida abuja, yace mum plz mu koma yau can abuja din, mum tace dare yayi sai dai gobe, jawaheer kam bata komai sai kuka, adda itama fa fara rarrashinta tare da fadin yakamata tayi tawakkali insha Allah zaki ga iyayenki, dakyar jawaheer tayi shuru amma babu komai a ranta sai tarin bakin ciki da takaici yanzu basu dad banr iyayenta inta tuna hakan sai taji kaman tai ihu dan baki ciki, muryanta su mum sukaji tana fadin international password din wani kasa ne? Mum tace saudiya sannan ina tunanin itama yar can ne dan balarabiya ce ita, jawaheer bata kuma cewa komai ba, inda mum take tambayan adda ina mahaifinta adda tace hmmm labari mai tsawo amma bari in baki.......
























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 25-26














Mum tace maiya faru adda?? Adda tace bayan kin tafi na bujire ma mahaifinki akan bazan yarda ba dole a dawo dake gida yace sai dai in biki in kuma na biki a bakin aurena, muna zaune aka kirashi mai gari, bai dawo ba sai can cikin dare yazo yana fadin an miki aure kuka nasa ina fadin haba mlm kai yanzu baka san kaddara ba? Wlh abunda ka aikata ko wanda baije islamiya ba bazai aikata ba, kaine limamin wannan garin mlm mai yasa bazaka dauki kaddara ba? Mai yasa zaka yanke wannan danyan hukuncin wlh mlm ka manta da nauyin dake kanka na amanar da Allah ya baka na yaranka, yanzu da kuka mata aure kasan wata aura?? Miye sana'an mijin?? Dan gidan mutunci ne?? Duk baka saniba, kai dai burinka tabar inda kake saboda kunyar data dauko mata wanda bai wuce ya fada kan kowa ba, mlm ina iliminka?? Da har zaka bari wai magan ganun mutane suyi tasiri akanka harka manta da kaddara bayan Allah yace muyi imani da kaddara khairan wa shairan, Kai ka sani ko wannan jarabawan da Allah ya maka inka jure shine silan shiganka aljanna, amma saika kasa jurewa....... Kuka mlm ya saki yana fadin kaico na kaico na lallai yau na yarda da manzon Allah yace gwara ka auri mace mai addini, yau gashi matata ta tunasar dani abunda na manta saboda kunyar duniya , yau idan Allah ya dauki rayuwa na mai zance mishi, lallai ban kyauta ma bilkisu ba, ban mata adalci ba, yanzu ina zan ganta?? Adda cikin kuka tace nasan ganinta zaiyi mana wuya amma ni burina ka gane ka kuma fahimta amma alhmdlh tunda ka gane, nasan ko mu dade ko mu juma wata rana zata dawo garemu insha Allah kawai mu tayata da addu'a duk inda take Allah ya kareta, abun ya mata yawa ga batan yaronta ga koranta da akayi kai wannan wani irin ibtila'i ne, mlm yace wlh koni inayi mata duk abunda nayi bada son raina ba, lallai nayi dana sani wanda bashi da amfani a yanzu Allah yasa mijin data aura ya riqemin ita da amana, adda tace ameen ,mlm yace zanyi ta bincike har in gano inda take, adda tace Allah yasa a dace, tun daka wannan ranan mlm yake ta tunaninki kullum burinshi ya ganki yaga wani hali kike ciki, abubakar yayi aure yana da yara biyu, maryam da abdullahi sunan yayanki aka samai suna kiranshi da hamman, shi kuma abdullahi ya sami aikin mota yana zuwa gari2 yayi hatsari ya rasu munji mutuwarshi sosai, abubakar yake mana komai na rayuwa duk da shima bawai yana da wani karfi bane, mahaifinku ya saida shanayenshi ya gyara gidan nan tare da fara sana'a a kasuwa yana saida su hatsi wanda shida abubakar suke zaune suke saidawa tunda babban shago ne, duk da mahaifinki ba wani lfya gareshi ba kullum burinshi ya ganki ko ya sami labarinki amma shuru har yanzu, kinji abunda ya faru bayan tafiyanki, amma bilkisu ban taba tunanin zaki rabu damu ba tsawon wannan lokaci, tace adda kiyi hakuri wlh ina son inzo duk da nasan har yanzu baba yana fushi dani, amma inna tuna shida kanshi ya koreni sai inji bana son zuwa amma kullum kuna raina kuma kuna cikin addu'a na koda yaushe, Allah sarki ya abdullahi lokaci yayi Allah yaji qanka ashe bazamu sake haduwa ba, adda ta kalli dady tace Allah ya biyaka yanda ka riqe min yarinya tsakani da Allah kaima Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, dady ya amsa da ameen.












Jawaheer kam kallonsu take Amma ita daya tasan abunda take saqawa a ranta, shiko m samir idonshi na kanta gaba daya tausayinta yake ji, ya rasa dalili mai yasa yake jinta a ranshi yanzu, amma ta wani gefen yana ganin kaman tausaya mata yake dan shima ya taba shiga irin halinta na rashin mahaifiya lokacin da yasan mum dinshi na raye ba karamin ciwo yaji abu, itace ta zauna kusa dashi tare da kwantar mai da hankali wanda gashi yau sun hadu da mum dinshi duk ta sanadin jawaheer din, gashi kuma sanadin haduwanshi da mum dinshi yasa jawaheer tasan basu bane iyayenta, ido ya lumshe tare da fadin no matter what i will stay by ur side, jawaheer matsawa yayi kusa da ita, kallonshi tayi ta sakar mishi murmushi wanda bata san ya fito ba, shima murmushin ya sakar mata tare da fadin ya jikin naki? Tace naji sauki sai dai bana jin dadin zama a nan, inaso in koma abuja, yace kiyi hakuri gobe zamu tafi, kai ta daga mai alaman toh, adda tace bari inje gida dare yayi kar mlm ya dawo yaga bana nan,nama san yana gidan yanzu inna koma a kawo abinci, dady yace ki bari adda zamu siyo yanzu, nima inaso inga mlm ya kalli mum yace bari muje, jawaheer tace dad, cikin sauri duka suka kalleta, tace kuje da mum itama nasan tana bukatar ganin kakana, kowa dake dakin saida yaji tausayinta, mum tace a'a babu inda zani dawa zaki zauna, tace mum naji sauki kuma m samir zai zauna dani kije kiga kakana, mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da zuwa wajan jawaheer ta rungumota tana fadin dan Allah duk wuya karki barni jawaheer ban taba banbantaki da yaran dana haifa ba, jawaheer ina sonki haiyuwanki ne kawai banyi ba amma wlh baki da banbanci da yarana, jawaheer itama cikin kuka tace insha Allah mum bazan taba gudunki ba, bani da wata uwa saike.... Kuka yaci karfinta dakyar ta seta kanta tace mum kije dare nayi, mum kallon m samir tayi tace ka kula da ita nima anjima zan dawo tare zamu kwana da ita, yace ok, sannan suka fita.












Bayan sun fita m samir ya zauna kusa da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer kibar kukan nan haka, ya isa, murmushi tayi tare da fadin yana da amfani domin shine kawai nakeyi inji dadi, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar dakai gefe, kirjinta yana buga mata da karfi duk sanda suka hada ido jin muryanshi tayi yana fadin bakya jin dadi in kina tare dani?? Da sauri ta waigo suka kara hada ido wani tambayan ya kuma jefo mata yace jawaheer mai kikeji in kina tare dani?.......






















*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 27-28


















Idonshi nakan nata yana jiran yaji mai zata ce, yayin da ita kuma tambayan yazo mata a bazata, dan haka yasa ta kasa koda motsa baki balle ta bashi amsa, ganin irin yanayin data shiga yasa ya hura mata iska a fuska wanda yasa ta lumshe ido da sauri, ido ya kara kura mata yana dan murmushi tare da fadin jawaheer kina da kyau sosai, da sauri ta bude ido dan ta gani ko shi dinne dagaske yake fada mata haka, ido ya kashe guda daya kaman yasan abunda yake ranta, yace kina mamaki koh? Gaskiya nake fada miki, kina da kyau mai daukan hankali jawaheer tun sanda na ganki naji kina min kama da larabara ina mai kyautata zaton kina da jini da larabawa, duk namijin daya sameki zaiji dadi sosai, sannan duk wanda ya aureki zanja mishi kunne ya riqemin ke da kyau, wani iri taji domin magananshi ta karshe ya nuna mata bawai yana sonta bane, jin tayi shuru yasa yaja hancinta tare da fadin jawaheer kin sani cikin farin ciki sosai ta sanadinki yau gani ga mum dina, kema Allah ya nuna miki iyayenki, kai ta girgiza tare da fadin bana bukatar ganinsu har abada zanyi rayuwa na ni daya ba tare dasu ba, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar da kanta gefe, yace har cikin zuciyarki kike fadan wannan maganan?? Shuru tayi ba tare da tace komai ba, yace ki bani amsa, kuka ta saki tare da fadin mai zance da yafi wannan? A da ina farin ciki sosai tare da iyayena, amma lokaci daya komai ya canza min tunda nasan basu bane iyayena, ina mamakin mai yasa mum dina ta bada ni, ta tafi ta barni...... kuka yaci karfinta sosai janyota yayi jikinta ya rungumeta yana bata hakuri akan tayi shuru, dakyar ya samu tayi shuru, yace jawaheer inaso koda yaushe ki kasance maiyi ma kowa uzuri, karki yanke hukunci akan abunda baki san miye asalin faruwanshi ba, haka kawai mahaifiyarki ba zata bada keba, lallai akwai wani abu a labarinki, wanda hakan ya zama dole mu nemi mum dinki, jan jikinta tayi a nashi tace nemanta bashi da amfani bani da wani buri daya wuce in sami namijin da nake so, shima yana so na, wanda za muyi rayuwa cikin jin dadi sai sai kash, hakan bamai yihuwa bane, ina tunanin barin kasar nan gaba daya inyi nesa da kowa na wani lokaci, ido ya kura mata yana kallonta harta gama, yace har dani za kiyi nesa dani? Shuru tamai ba tare data bashi amsa ba, yace ina jinki jawaheer? Tace ni kawai so nake in huta, yace ba amsan da nake son jiba kenan, satan kallonshi tayi amma sai akayi rashin sa'a shima din ita yake kallo caraf suka hada ido, ya daga mata akai alaman ina jinki, tace nifa bance zanyi nesa dakai ba, murmushi yayi yace gashi kince za kiyi nesa da kowa, tace ni banda kai nake nufi, wannan karan dariya yayi tare da fadin jawaheer bazan taba barinki ba har sai na sadaki da mum dinki wannan shine alkawarin dana daukan miki, wani hawaye ne ya zubo mata tace mai yasa zaka min haka? Yace saboda u r my sister my best friend, ke kawata ce daka yanzu, wani irin murmushi ta saki lokaci daya tare dayin hugging dinshi tana fadin thanks alot.












Bayan su mum sunje gida dad yaba driver kudi yace yasai abinci yakai masu jawaheer, sannan suka shiga cikin gidan, koda suka shiga falon baki suka zauna, basu dade da zama ba saiga mlm ya shigo falon yana fadin kai yau na gaj..... Bai kai da karasa maganan ba idanshi ya sauka akan bilkisu duk da tayi dan jiki kadan da kuma haske, hakan baisa mlm yaki ganeta ba, da hannu ya fara nunata yana fadin bilkisu, kece? Sai kuma ya daga hannu sama yana ma Allah godiya tare da hawaye wanda kana gani kasan na farin ciki ne, yace khausar matso kusa dani, da sauri mum ta karasa wajanshi itama tana kukan rungumeta yayi yana fadin dan Allah ki yafeni khausar nasan nayi miki ba dai dai ba, ki gafarce..... Tace haba baba ka daina neman gafara na kaifa mahaifina ne, komai kayi a kaina kayi dai dai, mlm yace Allah ya miki albarka khausar sai a sannan ya lura da dady, yace jibrin sannu, nan dady ya gaida mlm cikin girmamawa, mlm ya fara mishi godia akan irin riqon da yayi ma yarshi dan daka gani bama sai an tambaya ba kasan tana cikin kwanciyan hankali, adda ce ta shigo dauke da tray ruwa ne akai da zobo da kofuna, ta ajiye a falon, mlm yace yau ina cikin farin ciki sosai adda tayi dariya tace ina abubakar? Mlm yace yanzu zai shigo yaje anso mi..... Kafin ya karasa sukaji sallamanshi amsawa sukayi su duka ya shigo shima dai ba karamin farin ciki yayi ba na ganin kanwar tashi, nan adda tahau bama mlm labarin abubuwan da suka faru mlm yasha mamaki, yayi shuru can yace ita yarinyar tana asibiti ne da yaron naki? Mum tace eh amma yanzu zan koma dan inaso in kwana da ita gobe wai take son ma mu koma abuja, mlm yace kai da wuri haka muje asibtin tare nima inga yaron da kuma ita mai jikin, haka suka fita harda abubakar adda kawai suka bari a gida.










Koda suka isa asibitin, suka karasa dakin inda suka iske jawaheer na sallah shi kuma m samir na danna wayanshi ba komai yakeyi ba sai game, dan bashi da sim card din nigeria bai samu ya siya bama, ganin sun shigo yasa ya tashi da sauri yana fadin sannu da zuwa mum, cikin harshen turanci amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan tace mai jiki anji sauki kenan, yace eh alhmdlh, sai a sannan ya gaida su mlm da abubakar, mlm murmushi yayi tare da mika mai hannu danshi baya jin turanci, amma abubakar naji, mlm yace ni wannan yaran naku ban iyashi ba, duka suka saka dariya, mum tace ma m samir ga kakanshi shine babanta, ga kuma yayanta ta nuna abubakar, nan m samir ya kara gaidashi tare da fadin uncle ina farin cikin haduwa daku, abubakar yace nima haka uncle dinka yana cikin masoyanka danni dan barcelona ne, kuma kai nake so, dariya m samir yayi tare da fadin thanks my uncle, dai dai lokacin jawaheer ta idar da sallah, itama gaida mlm tayi cikin harshen hausa, amsawa yayi tare da fadin ya jikin naki? Tace da sauki alhmdlh, sannan ta gaida abubakar shima ya amsa cikin sakin fuska, nan mlm ya zauna kusa da jawaheer suna ta fira yana ta janta da surutu tana ta dariya m samir kuma ya matsa kusa da uncle dinshi yana fadin wai mai yasa take dariya mai ake fada mata haka? Dariya abubakar yayi yace wasa yake mata yana fadin shine zai aureta amma itace zata biya sadaki dan taimaka mata zaiyi, shima m samir din dariya ya farayi yi, tare da fadin uncle nima ina son koyan wannan yaran naku, abubakar yace ai babu wuya sai in fara koya maka, gashi naji ance gobe zaku tafi, kallon jawaheer yayi yace sis mu dan zauna a nan na kwana biyu mana, murmushi tayi tace ok duk yanda kace bani da zabi, yaji dadin abunda tace yana son biyayyan jawaheer tana son abunda yake so, mum ce tace au nama manta taci abincin kuwa?? M samir yace eh taci amma bada wani yawa ba, mum tace jawaheer kin taba ganin ana ciwo babu cin abinci?? Tace mum nafa ci kadan na rage, murmushi mum tayi dai dai lokacin dad ya shigo dauke da ledoji a hannunshi, mum ta tashi ta amsa tare da ajiyewa kayam fruit ne dasu kaji gassasu, mum taba jawaheer kaza daya ta mika ma mlm da abubakar mlm yace a'a shi tare da matarshi zaici dariya duka sukayi m samir shima yaci kazan yana ta fadin kazan akwai dadi suna tamai dariya yanda yake ta santi, dad yace jawaheer kinji sauki koh? Tace eh dad sai dai bana jin dadin komai amma ganin mum da kakana yasa naji dadi sosai, kowa ya fahimta abunda take nufi wato shiryawan mum dinta da mahaifinta yasa taji dadi sosai, kowa dake dakin saida yaji tausayinta tare dayi mata fatan itama Allah ya hadata da iyayenta, dad yayi murmushi tare da fadin Allah ya kara miki lafiya bari muje mu kwanta dare yayi, duka kowa ya fita amma banda m samir da mum, m samir yana son yi mata magana amma bazai iyaba dan mum na wajan haka ya fita tare da fadin good night, ji tayi kaman ta bishi, koda ya fita ya tarar dasu a waje, abubakar yace ma m samir a gidanshi zai kwana, security dinshi sukace ma abubakar dan Allah yayi hakuri an basu tsaronshi ne idan wani abu ya faru dashi zasu shiga matsala, duk yanda abubakar yaso m samir ya kwana a gidanshi haka ya hakura akan gobe zasu hadu, koda m samir ya koma hotel din daya sauka wanka yayi ya kwanta amma bacci yaki zuwa, sai juyi yake tayi gaba daya tunanin jawaheer yake tayi wanda ya hanashi sakat, ya rasa dalilin da yasa yake tunaninta har yake kokarin hanashi bacci abunda bai tabayi ba kenan ko sonia da yake so baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a yanzu, dan tsaki yayi tare da fadin tausayinta nake ji sai yasa nake tunaninta.....


























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 29-30














Haka yaita tunani kala2 yayinda yake ta tursasa ma zuciyarshi akan tausayinta yake kawai, wasa2 har wajan karfe biyu amma babu alaman bacci a idonsa sai tunanin jawaheer gaba daya ma kanshi ya kulle yama rasa mai yake ji a kanta, ganin babu baccin a idonsa ga tunanin yaki barinsa yasa ya tashi ya shiga toilet yayi alwala, sallah yazo yayi tare da roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi a rayuwanshi, ya dauki lokaci mai tsawo yana roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi, kafin ya tashi ya koma gado yana kwanciya bacci ya daukeshi.










Ta gefen jawaheer ma haka abun yake bata so m samir ya tafi ba, ita inda so samu nema dashi ya kwana da ita amma sai dai hakan bamai yihuwa bane, babu abunda take sai tunaninshi tare dason qara ganinshi, duk da sau da yawa zuciyarta tana kara nuna mata tayi baya dashi dan ba sonta yake ba, amma ta kasa, a yanda takeji inda tana da halin cireshi a ranta data dade da cireshi, itama haka taita tunani har bacci barawo yayi awon gaba da ita.










Jawaheer tunda ta farka tayi sallah asuba, bata koma bacci ba, har adda tazo da kayan abinci ita da mlm, jawaheer ta gaidasu cikin girmamawa inda suka tambayeta ya jiki ta basu amsa da fadin da sauki, dad dinta ne ya shigo cikin dakin yana fadin mai jiki anji sauki kenan? Murmushi tayi tare da fadin alhmdlh dad, dai dai lokacin dr ya shigo dakin tare da wata nurse, jawaheer na ganin dr ta tashi tare da fadin dr yau zani gida koh? Dariya dr din yayi daya kafeta da ido yace a'a ai kya bari ki dan kara jin sauki koda nanda sati biyu ne, ido ta zare tare da fadin ni kam yau gida zan tafi dan na warke sosai, dr yace shikenan zaki iya tafiya amma ki dinga kiyaye wa ki rage yawan tunani, tace insha Allah, murmushi yayi tare da kallon dad yace alhaji Allah ya kara mata lfya, jiki yayi sauki komai yayi normal, dad yace hakane mun godema Allah komai yayi kyau, dr ya kuma waigawa wajan jawaheer yace zanzo gida inji mai kike tunani haka har ya miki yawa kika fadi lokaci daya, mlm yace likita ni take tunani amm zanyi hakuri in aureta haka, duka suka sa dariya, jawaheer sai tunanin maiya hana m samir zuwa take tayi, haka suka fara shirya kaya har suka fitar da komai aka bama jawaheer magani Suka shiga mota, direct gidan adda suka nufa, koda suka isa jawaheer dakin adda ta shiga ta kwanta dan bata son wata fira a halin yanzu tafi jin dadi ta ganta tayi shuru, tunawa tayi da wayanta dan haka ta fito ta dauki hand bag dinta dake falo, mum tace mata yauwa jawaheer maza kizo kiyi wanka saiki kwanta gaba daya, tace to mum, dan shuru tayi can tace mum kayana basa nan suna hotel din da muka sauka, mum tace bude akwatina ki dauki zani anjima ko gobe kyaje ki kwaso kayan bata kara magana ba ta nufi dakin da kayan mum suke ta dauki zani ta nufi bayi dan tayi wanka, bayan ta fito daka wanka daka ita sai saurin kirji sai kayan data cire a hannu, kasancewan bayin gidan a waje yake, tana saurin ta shige ciki sukaci karo wanda shima a dai2 lokacin ya shigo gidan kuma bayin daka shi sai kofar gidan, tsayawa tayi taga dawa ta buge ganinshi tayi yana mata murmushi itama bata san lokacin data sake murmushin ba, sai taji kaman tayi hugging dinshi, a hankali ya furta mata ya jikin ki? Tace da sauki, yace naje hspt akace min kin dawo gida, ban tashi da wuri ba yau jiya

Please Login or Register in order to submit comment