Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana gaidashi cikin sakin fuska yace zarah right? Tace eh hakane ashe ka sanni yayi dan murmushi tare da fadin eh, kallon jawaheer yayi fuska daure tare da fadin kinyi baqo yana ta jiranki, dam taji kirjinta ya buga, amma saita daure tace baqo kuma anya ni? Bai kuma kallonta ba balle ya bata amsa, saima tashi da yayi ya kalli zarah yace sai mun hadu next time shiga motar yayi yabar gidan, ita kam jawaheer jikinta har rawa yake dan takaici kallon zarah tayi tace amma wannan dr din wlh baiyi ba dan wulakanci in zaka zo wajan mutum ai saika fada mai gani a hanya amma ya tashi ya kashe waya tsaki ta saki tare da fadin muje dallah ni in sallameshi, zarah tace kai ki nutsu mana, hararanta tayi ta wuce gaba abunda tana zuwa falon baki taga professor yusuf a zaune mamaki ne ya kamata dan batayi expecting ganinshi ba, itama zarah mamakin ne ya kamata na ganin professor a zaune, kallon juna sukai ita da zarah murmushi yayi tare da fadin kuna mamakin gani na koh? Mai makon amsa sai suka gaidashi su duka har suna hada baki, amsawa yayi sannan suka shiga zarah tace ni bari in tafi, yace no zauna nima ba dadewa zanyi ba yanzu zan tafi, kallon jawaheer yayi da yaga ta tamke fuska yace my dear i just come to see you sannan inji anyi approving dina? Dan shuru tayi kaman tace mishi dallah ban sani ba amma yana mata kwarjini, dan haka tace kayi hakuri za muyi magana ta waya, murmushi yayi yace amma ai inaga duk maganan waya bata taso ba komai za'ayi muyi ta nan kaman zaifi, tace hakane inaso in baka hakuri an amshi kudin sadaki na a halin da ake ciki yanzu kudin ma yana hannu na, kuma kaga babu kyau neman aure akan wani, dan shuru yayi na wani lokaci sannan yace hakane naji dadi da kika fadamin gaskiya Allah yasa ma aurenki albarka ya bada zaman lafiya, nima Allah ya bani hakuri, ta ansa da ameen, sannan ya tashi har mota suka raka shi ya dauko wasu ledoji guda biyu ya bata tayi mishi godiya sannan ya wuce zarah tace wlh yaban tausayi sosai, amma gwara da kika fada mishi gaskiya koba komai kinga kin rage saura dr, tace hakane mu shiga ciki mana, zarah tace ke tafiya zanyi, muga maiya kawo amsan ledan tayi taga su turare ne da kayan chocolate, daukan wani chocolate zarah tayi ya fara ci, tare da shiga mota dai dai lokacin mum ta fito tace har kun dawo nima gidanku zani zarah bari mu jera toh, mum shiga mota tayi driver ya tada itama zarah shiga tayi aka bude musu gate dai dai lokacin shima samir ya dawo gidan, parking yayi jwaheer ta shige ciki da sauri ya fito ya sameta a falo, kallonta yayi tare da fadin waye yazo nemanki? Tace lecturer dinmu yace maiya kawo shi? Tace yazo mu gaisa ne, wani irin kallo ya watsa mata tare da nufanta ya dauki ledojin dake gabanta ya bude ya gani fuska ya tamke tare da kiran masu aikin gidan ya basu, kallonshi tayi kaman zatai magana amma saita fasa ta wuce cikin dakinta binta yayi da ido harta bace mai, koda ta shiga wanka tayi tare dayin alwala tayi sallah sannan ta kwanta abunta, karan wayanta taji alaman saqo ya shigo dubawa tayi taga samir ne ga abunda yace...... *jawaheer inaso ki sani daka yau shine na farko na karshe da wani dan iska zai kara zuwa gidan nan da sunan nemanki, nd kuma na fada miki ban son yawo amma baki jiba nace in zaki fita ki fadamin amma baki jiba daka yau shine na karshe in kika kara only god knws what wil going to happen* bayan ta gama tayi dan murmushin takaici tare da jefar da wayan, bata dade ba bacci ya dauketa.
















Sonia tunda ta farka taga m samir baya nan, tace may be yaje ya dawo ne amma taji shuru data bincika sai ake fada mata ma yabar kasar, ranta yayi mugun baci tayi alwashin saita sameshi tako wani hali, sannan duk wacce yake tare da ita ko waye sai taga bayanta domin indai bata sameshi ba toh babu wata mace da zata bari ta sameshi dan tsaki tayi tare da fadin dole inyi mishi black magic in bai dawo hankalinshi ba........ Kuyi manage
























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 49-50


















Washe gari tunda jawaheer tayi sallah asuba ta koma bacci dan kwana biyu bata samun bacci gashi tana da lectures karfe goma, karan wayanta ne ya tasar da ita, tsaki tayi ta dauka ba tare data duba ko waye mai kiran taba, tana dauka taji muryanshi yana fadin plz kimin wannan abun da mukaci a yola rannan white din nan da miya mai yauki, bata san lokacin da dariya ya kubce mata ba dan ta gane tuwan semo yake so miyan kubewa, yace miye abun dariya? Tace babu komai, kashe wayan yayi taci gaba da dariya, tashi tayi ta fita kitchen ta nufa ta daura karamin tukunya tasa ruwan tuwan gefe kuma tasa kayan miya da manja da nama dasu dry fish, bude wata cooler tayi taga akwai farfesun kaza tace yauwa basai nayi ba, cikin minti arba'in ta gama komai ta shirya a try ta ajiye mai akan dinning saida ta shiga dakinta sannan ta kirashi tace ta gama yana dinning tana fadin haka ta kashe dariya yayi dan yasan bata son taji yace ki kawo min daki na sai yasa ta kashe, toilet ta fada tayi wanka dan ta kusa tafiya skul koda ta fito shiryawa tayi cikin wata jallabiya mai ruwan baki da maroon yayi mata bala'in kyau ta yafe gyalen jallabiyan kallo daya zaka mata kace ba yar kasar nan bace domin kyau iya kyau ne ya hade a wajan, feshe jikinta tayi da turare sannan ta fito a dinning ta sameshi yana cin tuwan tunda ta fito ya kura mata ido harta karaso inda yake, yace kinyi kyau sosai amma ki koma kisa abunda zai rufe miki jiki danni kadai ya kamata inga wannan kwalliyan, baki ta dan turo tare da fadin nifa nayi late banza da ita yayi yaci gaba dacin abincin shi, ganin bashi da niyan tanka mata yasa ta juya tana gun guni ni mutum ba aurena yayi ba amma ya dinga matsa min ina da anyi auren aina shiga uku, kayan ta cire tasa dogon wando da wata top mara hannu sannan tasa hijab, fitowa tayi idonshi na kanta harta karaso yace wannan ma yayi kyau ni skul din nan dole ne ki dinga yi ta online mana, ganin so yake ya hanata zuwa yasa tace dan Allah ka barni in tafi ina da test karfe goma dai dai kuma gashi yanzu saura 30mnt, yanda ta marai raice mai take magana sai yaji ta bashi dariya yace ki zauna in gama sai muje tare dan ban yarda da zuwa wannan skul din ba, babu yanda ta iya dole ta zauna bini bini ta kalli agogo, gashi yana cin abincin kaman baya ci, duk abunda takeyi yana kallonta amma sai yake nunawa kaman bai masan tana yiba, ganin bashi da niyan tashi tace lokaci na tafiya fah, bai ko kalleta ba balle ya tanka mata ba, saida ya gama bata mata lokaci sannan ya tashi yace muje tana ta zunbure zunbure suka fita, bude mata gidan gaba yayi ta shiga shi yake tuki har cikin skul din nasu, bayan yayi parking ta bude kofar amma taji a rufe kallonshi tayi alaman ya bude mata, tambaya ya jefo mata wannan fushin fah? Bata ce mishi komai ba kuma bai bude kofar ba, ganin goma saura minti hudu inta biye mishi zata rasa test din yasa tace dan Allah ka bude min inje inyi test din nan, yace sai kin fadamin dalilin da yasa kike fushi, tace nifa ba fushi nake ba kawai na kosa inzo skul inyi test ne banso inyi missing, bude mata kofar yayi tare da fadin ina jiranki in kin gama tace toh ta fita da sauri, tana koh shiga lecturer din ya shigo ya basu test.












Tunda ta fita ya kwantar da set din motar ya kwanta bai kashe motar ba dan ya kunna ac, pictures din jawaheer yake ta kallo a wayanshi yana murmushi lokaci daya ya furta u wil be mine very soon, jin kaman ana kokarin bude motar yasa ya dago dakai ya ganta ita da zarah, bude mata yayi ta shigo zarah ta gaidashi ya amsa tare da fadin gobe zaku tafi koh? Tace eh insha Allah, yace ok ki kulan min da ita fah sosai, dariya zarah tayi tace baka da damuwa indai dan wannan ne, yace ya gode tare da fadin in kun dawo sai inji ya kuke irin naku bikin zarah tace ok zaka ji komai da komai dariya yayi sannan sukai sallama, jan motar yayi suka bar skul din, mai makon suje gida saiya biya dasu wajan wani shan ice cream wanda turawa da manyan masu kudi suke zuwa wajan, mutane na ganinshi suka rugo da gudu suna daukan hoto dashi tare da basu takarda yayi musu signing saboda yawan mutane ko ice cream din ma basu shaba ya samu ya kubce ya shige mota, ita kam jawaheer dariya tai tayi yanda taga ya silale ya shige mota, kallonta yayi yace wannan dariyan fah? Tace babu komai kawai naji ina son yi ne hancinta yaja tare da fadin saina cire miki shi, dan kara ta saki tare da fadin akwai zafi fah, hararanta yayi tare da fadin ai na sani, baki ta turo, tuki yaci gaba dayi yana fadin mutum bashi da daman yin rayuwan da yake so sai mutane sun dameka, mtsww ya saki dan gajeran tsaki, jawaheer tace uhm toh ai mutane rahma ne, yace haka ne amma ai ba irin haka ba, sunyi tafiya mai nisa ta daiga bashi da niyan zuwa gida tace wai ina zamu? Yace zan sai daki ne, dariya ta saki tare da fadin tab lallai ma, cikin wani hotel suka isa, yace fito muje. Bata musa ba ta fito suka shiga wani daki suka shiga inda ya tsaya yana nocking, jim kadan aka bude dad dinshi ne hugging dinshi yayi tare da fadin dad yakake? Dad mai makon amsa sai kiran sunan jawaheer yayi da fadin shigo mana, shiga tayi cikin jin kunya ta sami waje ta zauna cikin kujeran dakin, hotel din ciki da falo ne, gashi ya hadu sosai, gaida dad tayi ya amsa cikin fara'a cikin jin kunya tace dad tun tuni nace ya kawo ni yace wai ka koma, wani irin kallo samir ya mata wanda yasa tayi saurin kasa dakai, dad kuma yace baka kyauta ba samir, shuru yayi ba tare da yace komai ba sunyi fira sosai dad dinshi yana son jawaheer sosai dan ya yaba da tarbiyanta da hankalinta uwa uba rainan bilkisu ce, dad din yace yaushe zaka spain din? Yace ran friday zan tafi inna gama kuma sai in tafi saudiya bazan dawo ba sai an daura auren daka nan sai mu koma spain din dan acan za muyi dinner, dad yace Allah ya taimaka an kawo card din ne? Yace eh an kawo dad yace ok nima idan aka daura auren zan tafi kwa sameni can, samir yace dad tare zamu tafi akwai private jet da za'a diba kowa mai cin mutane 120 dad yace ok ba damuwa, sai wajan karfe daya dad ya tashi shida samir dan zuwa masallaci, bayan sunyi sallah sun dawo suka tarar da ita tana sallah itama, bayan ta idar suka ma dad sallama suka tafi, suna tafiya cikin mota ya dan kalleta tare da fadin yaushe kika ce in kaiki wajan dad? Tace toh ai baka fadamin wajanshi zamu ba kuma ya kamata ka fadamin inyi mishi wani abu, tace yauwa mu ma bar wannan maganan tafiya za kayi shine baka fadamin ba, yace eh haka naga dama, shuru tayi ba tare data kara cemai komai ba, har suka karasa gida, a falo ta tarar da khalil da kabeer ozil da mum suna fira, tace ozil kai fa yanzu kayi wuyan gani, yayi dariya yace aikin dana samu akwai wuya wlh, tace sannu da gida mum, dai dai lokacin shima ya shigo falon zama yayi kusa da mum ozil ya fara tsokananshi da ango indai za'a ganka toh tare za'a ganku, dariya kawai yayi, kallon yanda yake da ido yasa jawaheer ta gane yana jin yunwa dan haka ta nufi dinning ta zubo mai abinci ta daura a plate ta daura a center table ta janyoshi gabanshi kallonta yayi yace thanks, sannan ya fara ci, mum kam tana jin dadin yanda suke nunawa juna kulawa sosai, khalil yace sis idan kun tafi ki siyomin phone a can naso muje tare amma banda time, jawaheer tace ok ka dauki excuse mana sai mu tafi, yace dad ai ba barina zaiyi ba wlh aikin nan akwai wuya shi bros umar ya huta wlh, dariya kabir yayi yace kalleka ai gwara naka aikin akan nawa, mum tace kun daiji jiki yara sai son jiki miye wahalan aikin zama ne fa a office ga ac sai signing shike nan fah, dariya jawaheer tayi tare da fadin mum wlh ni nama fi su dauriya, samir dai jinsu kawai yake yana cin abincinshi amma bini bini ya kalli jawaheer, ya rasa mai yasa ako da yaushe yake son ya kasance kusa da ita, jawaheer tashi tayi ta shiga kitchen ta hada ma dad abinci kalan na kasar su, dana nigeria kuma, mum ta shigo kitchen din tace baki za muyi yau kenan? Tace a'a mum za'a kaima dad ne, mum ta gane wanda take nufi dan haka tayi dariya ta fita, bayan ta kammala ita da kanta ta fita taje takai mai yana ta sa mata albarka, gida ta dawo ta shige dakinta, tana kwance taji nocking dan haka ta tashi ta bude, kallonta yayi daka sama har kasa ya dan cije baki, sannan ya shigo dakin binshi tayi a baya, zama yayi akan kujeran dakin mai dauke da hotanshi, yace nazo yin godiya ne, tace name? Yace dad yace kin kai mai abinci mai dadi, nagode, bata fuska tayi tare da fadin kaman ya ka gode nima fa dad dina ne, yaji dadin yanda tayi magana dan yana son dad dinshi yana kuma son mai sonshi, tashi yayi yazo kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinshi yace hakane sorry na tuba a daina fushi murmushi tayi tare da kokarin matsawa, janyota ya kuma yi tare da fadin haka za muyi sallama din kin san fah gobe zaki tafi in kin dawo kuma ba gani na za kiyi ba sai ranan biki, baki ta dan turo tare da fadin Allah ya taimaka, yace ameen tare da ja mata hanci ta saki kara mai dan sauti tace akwai zafi fah, yace dagaske? Daure fuska tayi alaman taji haushi yace idan kina fushi kinfi kyau, dariya tayi tace ba wani nan, shima dariyan yayi yace dagaske nake, jawaheer kina da kyau tako ina, murmushi tayi cikin jin dadin yabon da yake mata, duk da tasha jin ana fadin tana da kyau ita da kanta tasan ta hadu, amma idan taji a bakin samir tafi jin dadi, jin hannunshi tayi akanta yana shafawa ido ta lumshe, jin muryanshi tayi yana fadin saida safe tunda ba za'ayi min sallama ba, da sauri ta bude ido tare dayin hugging dinshi tace gashi nayi maka ko akwai wata sallama da tafi wannan? dariya yayi tare da girgiza kai yace bazan ce komai ba yanzu, itama dariyan tayi tare da kokarin jan jikinta daka nashi, tashi yayi ya mata peck a goshi yace sai da safe naji mum tace 10 zaku tashi zanyi kokari in tashi muyi sallama, tace ok fita yayi ta rufe kofarta ta kwanta tana tunanin irin kulawan da zata bashi in sunyi aure, har bacci yayi awon gaba da ita.










Tunda yayi sallah asuba bai koma ba, wajan 8 ya fito ya nufi dakinta yayi nocking ta bude kallonta yayi yaga tayi kyau tasa wata jallabiya pink, yace har kin shirya? Yace eh tare da fadin barka da safiya bai amsa ba sai jakar daya mika mata yace gashi saiki kara nasa an canza miki kudin dubai ne, tace wanda ka bani ya isa fah, fuska ya tamke yace bana son musu inna baki abu ki amsa kawai koda bakya so inna tafi saiki kai bola, amsa tayi tare da fadin kayi hakuri ba haka nake nufi ba, kafada ya daga alaman ke kika sani, yace in kin dawo zaki sami card a gida tace ok, tare da fadin nagode, kallonta yayi ji yake kaman yayi hugging dinta ko ya dan sami saukin abunda yake ji a halin yanzu, ganin inya ci gaba da kallonta komaj zai iya faruwa yasa yace in kun tashi tafiya saiki fadamin tace ok, falo ta nufa lokacin yayi dai dai da shigowan zarah da dan karamin akwatinta rungume juna sukayi sannan suka sami waje suka zauna, suna fira basu dade ba mum ta shigo falon gaidata sukayi tace saiku kai kayanku mota 10 zamu tashi kafin mu kai yayi, suka amsa da tam jawaheer itama ta shiga ta dauko kayanta tasa a mota sannan sukai breakfast, bayan sun gama ta kira samir tace zasu wuce falo ya fito ya gaida mum sukai sallama su mum suka fita jawaheer ce kadai a falon tace mun tafi janyota yayi yasa bakinshi cikin nata ya tsotsa na wajan second biyar sannan ya saketa tare da fadin ki kulan min da kanki, jiki a sanyaye ta fita dan ya kashe mata jiki, shima daki ya koma driver yaja su har airport suna zuwa suka shiga jirgi karfe goma dai dai suka daga zuwa kasar dubai siyayyan kayan akwati.










Kwanan su jawaheer 7 a dubai suka dawo ba kayan akwati suka siya ba kawai harda kayan daki dan mum tace mata ya siya gida koda sunzo nigeria, akwati talatin da shida suka siya, ko wanne makil yake da kaya, atanfa materia english wear etc... Jawaheer tana kewan samir sosai gashi tunda suka tafi sau biyu sukai waya, taga katin bikin saura sati daya tayi mamaki ita ba kawaye gareta ba dan haka zarah ce taita rabo ta dai bama yan class dinsu, mum ta dauko mai gyara ta fara gyara mata yar tata, kun san farar mace babu wuya abu ya amsheta fatar jawaheer tayi laushi tayi silbi gwanin sha'awa har wani sheki takeyi da walkiya, ga kirjinta ya kara cika domin masu gyaran gaske mum ta dauko mata, anata hidiman biki ita jawaheer abunda yake damunta shine rashin wayan da basayi tunda sukayi a dubai yace mata shima yana spain zai raba kati, basu kara waya ba, gashi wayanshi baya shiga..... Yau za'ayi mothers day wanda mum ta shirya a wani haddan hall wanda saika amsa sunanka zaka iya kamashi manyan mata sun taru sosai masu hannu da shuni amarya saboda bala'in kyau dakyar na ganeta yan class dinsu sunyi mata kara sunzo matan dan event din na mata ne, sannan sunce zasu spain din harda mazan, anyi taron mothers day wanda mawaka daban daban suka baje basirar su, anci ansha kowa yaji dadi ga calender da aka raba wanda zarah ce ta hada musu cikin pics dinsu da jawaheer ta tura mata kwanaki sunyi kyau sosai mutane da dama sunyi mamaki da suka ga mijin nata suna ta fadin sun dace ashe dan kwallo ne kai ta sami mai mugun kudi, bayan sun koma gida saiga kiran samir da sauri ta tashi tayi toilet dan akwai kawayensu na class dinsu a dakinta dauka tayi cikin murya kaman zatai kuka tace hello, yace dear maiya sameki? Tace bakai bane kaki kirana ka kuma kashe waya, yace sorry dear jibi ina nan tafe uwar haka jibi kin zama tawa koh? Dariya tayi tare da fadin insha Allah ina ma auren soyayya mukayi kana so na kaman yanda nake sonka aida abun yayi armashi dariya yayi yace wani irin armashi? Tace mai zaka siyomin? Yace mai wayau kiban amsan tambaya na, dariya tayi danya gano ta tana son canza maganan ne, tace nima ban san amsa ba, yace zaki sani inna dawo bada wasa zan miki ba, dariya tayi tare da kashe wayan...... Jawaheer na gayyatar kowa da kowa daurin aurenta fans😀




























*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 51-52














Kiranta ya kuma yi dauka tayi yace naga pics kinyi kyau sosai, tace waya turo maka? Yace zarah nasa ta tura min pics din duk event din da akayi dariya tayi tare da fadin nasan banyi wani kyau ba zolaya na kake, yace uhm idan na dawo zan tabbatar miki da kyan da kikayi dariya ta kara saki tare da fadin sai anjima nabar mutane, yace mutanan sun fini ne? Tace a'a yace gud sai ki tsaya dan ban gama jin muryanki ba, tace uhm janta yayi da fira sosai sannan ya barta sukai sallama fita tayi zarah tace har an gama soyewan dan gulma waya shine a bayi, dariya tayi tare da fadin ehdin ina ruwanki ban san gulma, sauran sukai dariya tare da tashi suka mata sallama ita dama zarah yau tazo sai bayan biki zata koma, tare zasu kwana, raka su sukai har wajan gate akan sai sunzo gobe kamu, ciki suka koma jawaheer tace wai miye tsakaninki da khalil ne? Zarah tace mutunci jawaheer tace uhm in tayi wari maji, dariya zarah tayi suna cikin haka mum ta shigo dakin hannunta dauke da wani cup taba jawaheer tace ta shanye amsa tayi ta shanye sannan mum ta amshi cup din ta fita jim kadan sai ga kayan fruit an kawo musu, zarah ta amsa suka fara sha.












Yau za'ayi kamu tun karfe biyu aka farama jawaheer makeup ba'a gama ba sai wajan 5 danma tayi alwala kafin a fara saida tayi sallah kafin aka fita zuwa wajan kamu kwalliyan yau tafi ta jiya, a wajan taga adda dariya tayi domin taji dadin zuwanta haka aka sa lalle duk abunda akeyi zarah na daukan ma samir tare da videos anci ansha an kashe naira kaman ba gobe, harda mutanan da ba'a gayyata ba sunzo yau domin kawai ansan dan kwallon kafar da duniya takeyi dashi shine zai auri yar nigeria abun yaba ma mutane da dama mamaki amma duk wanda yaga amaryan sai yace eh gaskiya sun dace domin itama ba'a baya ba wajan kyau koda zarah ta tura ma samir hotuna ganin yanda tayi wani irin bala'in kyau abun ya bashi mamaki uwa uba yaga ta kara girma da cika, ji yake kaman yayi tsuntsu ya dawo gida amma ba hali sai gobe, ranan gani yayi lokaci baya mishi sauri burinshi kawai ya dawo yaga jawaheer dinshi, bayan an gama komai aka koma gida jawaheer dakin da adda ta sauka ta tare tace adda shine sai yau zaki zo? Adda tace ni rabu dani ja'ira sai inji shuru tunda kika tafi sai kawai naji ance wai zakuyi aure shin yaushe kuka fara soyayya ne haka har abun yayi karfi? Dariya tayi tare da fadin to ni ta ina zan fara bada amsa? Adda tace tako ina, labari taba adda yanda abubuwa suka kasance har da amincewan da yayi zai aureta, adda ta nisa tare da fadin hmmm samir kenan ni nasan yana sonki idanshi kawai za'a kalla a ga sonki a ciki, dariya jawaheer tayi tace uhm adda nidai banga komai ba, wai ni kam adda ina dr ne? Adda tace kwanki yazo gida na, nake fada mishi maganan aurenki ai, jawaheer tace eyya kwanaki ya kirani yace min zaizo bai zoba na kirashi lokacin wayanshi a kashe, adda tace kai mutumin nan yana sonki shima sosai Amma zabin Allah koda yaushe muke nema, jawaheer tace haka

Please Login or Register in order to submit comment