Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni harshe jikin mun yayi sauki,


Fita yayi Alwala ya wuce masallaci,,


Nima sallar nayi na wuce kitchen Jin zazzabina ya sauka sosai ruwa na daura a wuta yana zafi na surka a baf na zuba salt na tsoma kafata a ciki sosai na gasa kafar,naji dama dama


Kayan da Khadija ta wanke Mana na nade nakai whtdrp harda nasan TV na kunnan Ina kallo sosai na maida Hankali na akan TV don bani da aikin da zanyi kome Khadija tamin,


Al'ameen daga masallaci bairon mangoron sa ya wuce ya yaye buhun da yake rufewa,
cikin hukuncin Allah sai yayi cinikin dari,Jin ana Kiran mangariba yasa ya rufe,


Masallacin ya sake shiga ana idar da Sallah shagon jambosko ya wuce,sosai ya basa hakuri ya basa darin da yayi ciniki akan gobe in Allah ya kaimu zai basa sauran,


Ganin cika alkawarin Al'ameen yasa jambosko ya karbi D'arin,




Gida ya dawo lokacin Nima sosai naji saukin jikina Ina zaune a waje Kan darduma don yau d'auke NEPA sukayi daga Kiran mangari ba gashi sai zafi ake Kamar me,


Shigowa yayi Jin motsena akan dardumar shima lalubar dardumar yayi ya zauna a hankali,


"Daga tafiya sallah sai yanzun kuka idar kenan" na tambaye sa


Ah ah naje na bude Mangoro ne,


"Jikin yayi sauki.kenan"?


Alhamdulillah gaskiya nikam naji sauki bakiji muryana Yana fita ba Daman jambosko Kam indai ya hada ma mutun magani irin na kananun ciwo wukan nan haka ana Jin sauki cikin hukuncin ubangiji,


"Gaskiya ne Nima Alhamdulillah zazzabin ya sauka sosai,"


Allah ya kara sauwa kewa,


"Ameeeeeen bara na kawo maka abinci, kasan Khadija dafawa tayi da yawa Yar albarka"


Toh yace


Nikam tashi nayi na ibo Mana abincin kuma dukan mu ba laifi munci da yawa Koh nace naci da yawa don shikam baiji sauki bama ci yake abinsa,




Yau a waje Muka kwana dukan mu washe gari da karfin jiki Muka tashi Alhamdulillah Allah abin godiya,


Da safe da kaina na kimtsa kofa Amma bamuda abinci karyawa Koh sisi Bai kwana dashe ba fita yayi waje Koh Allah zai sa ya samo Mana na cefenen,


Al'ameen kam
duk buga bugansa Bai samu kome ba har karfe Tara Amma shuru ba Wanda ya Saya mangoro bare ya samu na cefene,


duk ya shiga damuwa sosai na rashin kudin da zai sayi kayan Miya sannna baison karban bashi a shagunan Yan unguwan don har sun saka Masa ido, duk da Daman ba basa bashin suke ba bare suce baya biya Amma har ya Kai idan suka gansa Yana tunkarar shagunansu sai sun Kama gulmar sa atunanin su yazo tambayan bashi,


*********
Ganin har 9:30 Bai dawo ba yasa na mike indomie na d'auka guda biyu, na soya Mana da Mai Koh albasa Babu bare tarugu,


Ina sauke indomie na juye Masa rabonsa a kula iban nawa nayi a plate na koma Kan darduma na zauna na Tasa indomie a gaba shukali nasa na iba a hankali Zan Kai baki bansan lokacin da wani irin kuka ya taso mini ba lallai duniya abin tsoro ne,tabbas duk rufin asirin da Allah ya maka tabbas zai jarrabeka don gwada imanin ka,


Ada Koh da sunan Wasa Ban taba tunanin akwai Randa xaizo nasha ruwan masu ruwa bama bare Wai ruwan rijiya, yau abinda nake ci Ada Koh Mai gadin mu yanacin Wanda yafi Wannan,


*********
Hawaye na share nakai indomie baki chusawa kawai bake Amma bawai don inajin dadin Saba don harma na gaji da indomie, taliya,shinkafa, macaron,i sukenan abinci a gidan nan tunda na aure yayan Khadija su nake ci,


Al'ameen Kam Yana zaune a kofar gidan har yanzun Sam ya kasa shiga ciki saboda baisan me zaice Mata ba,


Nikam Ina Gama cin abinci na tatara Kwanukan daidai lokacin aka kawo NEPA d'aki na shiga TV na kunna na kamo KungFu channel ana wani film Mai Dadi sosai na Bata hankali akai,ada Sam ban Damu da TV ba Amma yanzun karfe da yaji na zama Yar kallo
waya da laptop Kam duk na kashe su na aje,tunda Koh kudin data bani dashe Kuma bamai kirana,




Khadija ce take tahowa gidan yayanta tun daga nesa ta hangosa zaune a dakalin kofar gidan,


Assalamu alaikum yayana na kaina


Waalaikumu salam khadin Goggo kene ??


Eh Yaya Ina kwana?


Lafiya Alhamdulillah, khadija ya gida,?


Alhamdulillah,
ya jikinku da Aunty duka,?


Da sauki sosai wallahih khadija,


Allah ya Kara sauki


Ameen


Amma yaya yakake zaune a kofar gida Koh bazaka bude bane karfe 10:43 fa yanzun,Koh jikin baiyi kware bane


Lafiya klau khadija


Shuru kawai ta Masa Amma ita Karan kanta tasan akwai abinda ke damunsa boye Mata yake,


Toh Yaya bara na shiga ciki na kawowa Aunty kulanta ne,
Kuma na fad'a maka zanje Fulani Dance na auren Asma'u Inka Amince




Toh khadija a Ina ne za'a yi program in?


Yaya a Muri Hotel ne


Gaskiya khadija bana son kina zuwa ire iren wajajen bukukuwan shirmen nan ki dai bare Walima sai keje Mana?


Habba Yaya wallahih ba abinda zai faru kuma kasan yanzun ana saka Yan sanda a get bare auren Asma'u ba kowa za'a bare ya shiga ba,


Gaskiya khadija banason zuwa irin wannan program, Amma tunda kin nace Allah ya dawo dake lafiya,


Ah ah na fasa zuwa tunda baka so,ta fada amma fuskarta ba walwala don tanason zuwa Asma'u ce kawa ta farko data taba gayyatar ta biki Sam kawayen ta basason sakata a kawance saboda sunsan ba Anko zata Saya ba Amma Asma'u Bata damu ba a hakan ta gayyace ta ta shigo kawancen auren ta,


Ah ah khadija kije nasan Asma'u yarinyar kirkice duk da iyayen ta sai addu'a halinsu,


yauwa yayana na gode ,cikin farin ciki


Da yaushe za'aje Fulani Dance in?


Da yamma,


bani da kudin da Zan baki na machine khadija Amma in kin tashe tafiya ki biyo ta bakin titi taima nayi ciniki sai na baki,




Ka barshe Yaya jiya bayan na koma gida nama wasu yara kitso sun bani dari da hamsin zai isheni ,


Toh khadija muje ciki,


Shigowa sukayi da sallama karar TV yasa ban jisuba sai da ya shigo d'akin tukun na juyo "Ina ka shigane tun sassafe ga karyawan ka na zaune na Gama"


Sumayya ban samu na kayan Miya ba shiyasa ban dawo da wure ba,


"Allah yasa mu dace"kawai nace


Ameen, ya amsa a sanyaye


Ina kwana Aunty?


"Wai ni ba muryan khadija bane nakeji a waje",


Nice Aunty


"Toh ki shigo mana"


Ah ah Aunty kula na kawo na aje a kitchen Zan wuce,


"Ai baki Isa ba daga zuwanki sai tafiya"


Kai Aunty kin manta nace Miki kawata zatayi aure,
ai yau za'a fara bikin auren,


"Wai su kawayen Amarya kenan toh da safen nan Zaki gidan sunne"?


Ah ah zanje na wanke Kaya nane nama Goggo girkin Rana zuwa yamma Zan wuce,


"Toh khadija ki kula da kanki kinje iyya kacinki wajen program Kuma 5:30 nayi ki kamo hanyar gida kinsan waje irin Wannan in dare ya fara akwai hatsari fa,"


Wallahih Aunty ni kwanaki ma haka naji lbr Wai ana tambe a wajen program har aka tsokawa Amarya wuka a ciki ta mutu,


"Toh ba kin gani ba khadija Allah ya tsare"


Ameen,tace tana kokarin juyawa,


"Yauwa khadija shiga kitchen akwai indomie a kula ki iba "


Wallahih Aunty na koshe


Ganin Taki yarda ta iba yasa na barta ta tafi ni Kuma mikewa nayi na ibo Masa indomie kadan yaci,


don wallahih Sam baijin dadi a waye gari baida Koh sisi da zai Saya abun da zai baiwa Sumayya,


"Nikam Koh jikin ne"? na tambaye sa ganin sa a salube,


Ba kome yace Yana mikewa ni Zan fita me za'a Saya na Rana da dare,


" Duk abinda ka samu ka Saya daidai aljuhunkan"


Ba karamin Dadi yaji ba ganin Sam bata nuna Masa Koh a fuska ya Gaza riketa ba,
insha Allah Yana fatan zamansa da Sumayya ya d'aure,


**********
Har yamma cinikin dari biyu yayi,
saboda cika alkawari yasa Yana tashi daga bairon mangoron chemist ya wuce ya biya jambosko dari saura d'ari,


d'ayan D'arin Kuma ya sai Mana albasa da tarugu sai tunanin halinda Sumayya take kawai yake fama tun fitarsa da safe Bai samu kome ba sai da Allah ya Sosa wata baiwar Allah tazo tasai Mangoron dari biyun na,


Nikam ganin Bai dawo da Rana ba nasan Bai samo kome bane indomie d'anye na ci guda D'aya,


Sai goshin mangari ba Al'ameen ya dawo da cefene gonin tausayi Yana rike da laidar cefenen d'ayan hannun Kuma sandar sane,


karban kayan Miyan nayi na d'aura macaroni dafa duka,don yanzun mun zama masu cin dafa duka bamu da abinci sai she karfinsa baikai muci da Miya ba,


Wanka yayi ya d'aura Alwala ya wuce masallaci sallan mangariba Bai dawo ba Saida aka hada da isha'i


Vayan ya dawo mukaci abinci ya rufe kofar shashen mu muka shiga d'aki akan gado na kunna Tashar Arewa 24 ana kaddaran rayuwa na satin nan sosai nake dariyan Karam sosai ganin reaction nasa lokacin da saurayin preter ya shigo,


Al'ameen Yana zaune a Kan cafet ya kurawa TV ido kamar wani Mai kallo sai kyetkyet su yake,


Hala kinajin dadin kallon film in kenan?ya tambaye ni


"Sosai ma wallahi kasan me" Nima na tambaye sa


Cikin Jin Dadi ganin na fara sakin jiki dashe yace ah ah,


Dariya na sake sosai kamar ba abinda ke damuna"Wai karam Yana cewa sameer Wai kafadun saurayin d zaizo ganin preter, Wai kafad'arsa Kamar marikin Lena haka fa yayi da hannunsa lokacin da zai Fadi marikin lema" Ina kara sakin dariya,


Shikam sakake yayi Yana sauraranta abin sai mamaki yake basa irin dariyar da take innan,


"wallahih ni inason preter innan da Karam suna burgeni sai dai dukansu Basu ma San suna son juna ba Kuma Anya Wannan saurayin da yazo gidan su ba shine saurayin shalin ba kowa"?


Don me kike sonsa da preter in toh?


"Suna burgeni ne",


Suwa kenan?


su biyun"


Harda namijin kenan?


Juyawa nayi cikin mamaki Ina kallonsa Wai me mutumin nan yake nufine Kam
Shuru na Masa


shima Jin tayi Shuru Bai sake magana ba,


Sai 11:7 na kashe TV kayan bacci nasa na kwanta


Jin tana bude whtdrp ya tabbatar Masa zata kwanta kenan yanzun, mikewa yayi ya dau pillow daidai lokacin yaji ta tana addu'an bacci kasa kasa,


Shima haurowa yayi bakin gadon,


Da mamaki nake kallonsa ban Gama Shan mamaki ba Saida Naga ya kwanta Yana lalube na


"Wai Kai malam tsaya me kake nufi ne Koh ruwa ake yanzun da zaka hauro wajen kwanciya na" nafada ina kallonsa da mamaki


Jin tambayar da ta Masa ya sakasa gane saitin da take,


A bazata kawai naji ya damko ni yana cewa


Eh ni yau.................


*Gaisuwa na musamman gareku*
πŸ€ *Princess*
πŸ€ *Maman Ammar*
πŸ€ *Sakeenat*
πŸ€ *Faeexetion*
πŸ€ *Oum Abdullahi*
πŸ€ *Umme zariya*
*Naga comments naku na yaba sosai*








πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣
Yau da Matata Zan kwana gaskiya


Da mamaki nake kallonsa"waye matarka"?


Ga tanan ya fada Yana kwanciya Da ita a jikinsa


"Wai menene haka ka matseni fa" nace Ina kukarin tashi a jikinsa


Fuska ta ya hada da tasa fuskar har hancin su na gogan na juna,


Karan in TV nan Kam kyakkyawa ne shiyasa yake burgeki?


Ikon Allah yanzun Kam na gane inda mutumin nan ya dosa, maganan Karan innan ya damesa"mummuna ne kamar Kai"na basa amsa,har lokacin Ina kwance a jikinsa don karfe ya saka mini sosai


Murmushi yayi a hankali yake goga Mata gashin gemunsa a Gefen fuskarta


Wani Abu nakeji sosai a tare dani"Kai me haka"?


"Kana goga mini gonan ciyawa a fuskata Koh so kake ya garceni ni"


Kinji Dadi kenan?


Kuma ni ba mummuna bane sai dai kece mummuna


Hhhh shap ai in fada maka "Kai mummuna ne sosai gaka bak'i,gajere, Mai guntun hanci, ga tumbi"


Wannan Karo Kam dariya ya kamayi don sosai yake cikin nishadi, ganin ya samu abokiyar Hira


Farine ni, Kuma hancina dogone Ina da ido bakina irin na khadijata fuskata dogone Mai dauke da gashin gemu Mai yawa haka na kaima, akwai tabon sallah a goshina,ya Bata Amsa yana Kai hannunsa kanta ya zame hularda ta saka a hankali ya Kama gashinta da khadija ta kitsa Mata har gadon baya,
Da Ina Tara gashi sai yafi naki yawa


"Kutt wallahih bazaifi ba duk ma Wanda ya farfada maka haka kamannin ka yake kawai zaginka yayi Amma ba wani yanda na fadan nan dai haka kake"


Dariya kawai yayi sai Kuma yace,
Da ace ban taba ganin kaina a madubi ba dayau kinyi Dani don d'auka zanyi da gaske hakan nake


"Au Daman ka taba kallone kafun ka makance"?


Shikarata 18 na zama MAKAHO Kinga ai zuwa yanzun kamannin Bai sauyaba


"Ya sauya kam gashi harda tumbi kayi"na fada Ina murmushi haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki yau na samu abokin Hira Wanda rabon da nayi harna manta sai in khadija tazo


Cikin hanzari ya birkitota zuwa kasa shi kuma ya koma Saman ta,


Zaro ido nayi cikin Al'ajabi da tsoro bakina har rawa yake"yayan khadija me haka wayyo kirjina nauyi ka d'agani"


Ina da tumbi Koh Babu kinsan ba gani nake ba shiyasa na saka Miki tumbin don kiji akwai Koh Babu


"Wayyo Allah cikina kirjina nauyi ka sauka a kaina wallahih baka da tumbi washhhh numfashina xai d'auke"


Jin yanda duk tabi ta gigice yasa a hankali ya d'aga nauyinsa akanta Amma Bai sauka ba,


"Ashhhhh toh ka sauka a kaina Mana"


Shuru yayi yaki magana yanajin ta sai masifa take, ya sauka a kanta ya Mata banza don yanzun Sam baicika Jin shakkarta ba Kamar da


"Ina Jin fitsari"


Yayi shuru don yasan ba fitsarin zatayi ba muddin ya saketa guduwa zatayi


"Koh bakaji bane, ya matseni fa"


Kiyi anan kawai, ya Bata Amsa


Ganin ya manna mini hauka yasa nayi shuru ganin da gaske fa ba sauka zaiyi a kaina ba bare akan gadon,ganin baida niyar yimin kome yasa hankali na ya kwanta har kusan 1 na dare idanun mu biyu daga karshe dai bacci barawo yayi gaba Dani,


Jin saukar numfashin ta ya tabbata tayi bacci a hankali shima ya ringajin bacci na d'aukarsa zamewa yayi ya kwanta a gefe ya dagota ya d'aurata a kansa ya lumshe idanunsa har yaji babushi,


Kiran farko na Assalatu shiya sauka akan kunne na a hankali na bude idanuna na,masu cike da bacci jina ajikin mutum yasani tunawa Ashe fa jiya tare muka kwanta zame jikina nayi a hankali Zan mike


Jin tana zame jikinta a nashe ya sakasa bude ido sai alokacin yaji Kiran sallah ake


Daga ni harshe waje mukayi na ibi ruwa a buta na aje Masa"ga ruwan Alwala kar a shiga sallah baka Kama Alwala ba ka rasa jam'i"Na fad'a Wai karya tuna wani abu, don yau na iba Masa ruwan Alwala




Butan ya d'auka Alwala yayi ya tafi massalaci sai tunanin abinda zasu karya yake baida Koh sisi Kuma inya bude Mangoro da safe ma ba ciniki yake ba kwana biyu nan, amfiya D'an Saya da rana Koh yamma


Alwala nayi na shiga d'aki,
Ina iddar da sallah na kwanta a Kan sallayan don harga Allah bacci nakeji jiya ban kwanta da wure ba


Gida ya shigo don ya rasa mafita Sam baisan me zayi ba,a Ina zai samo musu na karyawa tsoro yake kar hakurin Ta ya Kare wata Rana ta guje sa, da sallama ya shigo d'akin Jin Bata amsa ba yasa ya fara laluben ta akan gado Amma Bai jita ba ya sauka Yanata tattaba kujira a tunaninsa Koh tana jinsa kin amsawa tayi,
Sumayya!! Sumayya!! ya kirata baki biyu Amma shuru,hankalin sa a tashe ya shiga tattaba kome na d'akin Yana nemanta hardai yajita a kwance akasan cafet,sosai hankalinsa ya kwanta shi Karan kansa ya rasa meke damunsa akan Sumayya Sam baida jarumta akan lamarin ta, Koh don ta kasance mutum na farko dake da kusanci dashi a duniyarsa ta yanzun ne oho,hannu yasa a hankali ya cicibeta Yana lalube harya Isa bakin gado kwantar da ita yayi,ya fita waje,boket ya d'auko ruwa ya ringa ja a rijiya harya cika Randa ya wanke kwanuka harda shara yayi Amma dai sharan Koh na yara albarka saboda kwata kwata batayi kyau ba (sharan Mara ido)




Yana Gamawa d'akin ya shigo da lalube ya isa Kan gadon Hawa yayi,hannu yasa ya fara tataba ta Yana neman fuskarta har hannunsa ya sauka akan kirjinta


Waro ido nayi Ina kallonsa Jin yaki cire hannunsa a kirjina yasa na buge hannun"me haka don Allah"?


Da nayi me?ya sake tambayar ta


"Ai kafini sani waima menene kake ta faman laluba ta Ina bacci"


Nidai bansan kome ba tunda ba gani nake ba nadai San na taba Abu mai laushi Amma bansan kome Nene ba,ya Bata Amsa


Lallai mutumin nan ya Raina mini wayo ai Koh Bai taba kallo ba a rayuwar sa yasan meya taba bare harya Kai 18 Yana kallo,jin rainin wayone ma ban sake magana ba


Kin tashi lfy?


"Lafiya Alhamdulillah"


Uhmm Sumayya Zan fita, Koh zan samu na karyawa anjima Zan dawa insha Allah ban kwana da kudi ba


"Sai ka dawo" nace Masa Ina sauka a Kan gadon don wallahih yunwa nakeji ba kadan ba


Allah ya yasa,Yace Yana fita a d'akin harya bude kofar shashen zai fita yaji Sumayya na kiransa tsayawa yayi




"Am Daman nace in ka fita pls ka tura yaro ya kiramin khadija"Ina magana Ina bin kofar da kallo da mamaki


Toh,yace mini zai juya


"Wai waye yayi aikin nan duka haka"?na fada Ina murmushi ganin sharan Kamar wata yarinya Yar 3 ce tayi


Nine na Miki aiki yau dai ki huta


"Aiko naji Dadi na" nace Masa don na gane so yake ya burgeni 😌


Da gaske?ya tambaye ta


"Sosai ma,ka tafi Mana samun mu samu na karyawan ka tsaya surutu yanzun ana neman 8:10 na safe"


Ok.toh sai na dawo


"Yauwa"




Yana fita a kofar gida ya aiki yaro gidan Goggo Amina ya Kira Khadija




Nikam tsintsiya na d'auka na sake share kofar na gyara d'aki sosai kwana biyu nan. Nake jina a sake sosai


Khadija ce ta shigo bakinta dauke da sallama,
Assalamu alaikum


"Waalaikumu salam"khadin Goggo


Kai Aunty ni banso sunan fa nasan a bakin Yaya kikaji duk shike Bata mini suna


"Toh khadin Yaya"


Aunty ai khadin ne banaso


"Toh khadija shikenan"?


Eh Aunty Ina kwana ?


"Lafiya khadija ya goggo"


Lafiya Alhamdulillah,tace tana zama a bakin dakali


"Wai ni khadija ya Fulani Dance in dai su kawayen Amarya jiya an rabashe kenan"?


Shuru tayi sai Kuma Naga hawaye ya cika idanunta..


Da mamaki nake kallonta "Khadija me ya faru kuma daga tambaya sai kuka wani abin na Miki"?


Aunty don Allah nida yayana muna da wani abin kyemane a jikin mu, da mutane ke wulakanta mu Koh saboda mun kasance Marayu ne, Koh Kuma don Yaya baya kallo ne, ta fada tana fashewa da kuka


"Subhanallah khadija meyasa Kika Fadin irin wannan kalaman haka"


Dole na fada Aunty kaf unguwan nan yayana baida aboki Sam ba Wanda keson rabarsa gani ake Kamar Inka jashi a jiki zai zama maka kaya, Amma wallahih Aunty yayana baida zuciyan kwad'ayi kullun so yake yaga ya neme na kansa Amma duk da haka in Kinga yayana na Hira toh ta miskinai ne irinsa Amma bayansu ba Mai son Koh Hira da yaya, shiyasa har kullum nake mamakin auren ki,


Ni Karan kaina mujiyace a cikin kawaye, me laifin mu aunty mu muka d'aurawa Kan mu Talauci ne Koh akwai Wanda yafi karfin maraici ne?


"Gaskiya Babu khadija Amma meya faru ne haka"?
Na tambaye ta idanuna na cika da hawaye tabbas khadija Allah ne ya tsare ta a irin zamanin da muke cikin nan yanda Yan Mata suka baci da son kyelekyele Amma ita ta kauda fuska ta cire buri a ranta ta zauna a matsayin da Allah ya d'aurata,samun irin khadija kalilan ne a yanzun yarinya Mai hakuri


Aunty Kinga wulakancin da kawayen Amarya suka mini jiya a wajen bikin nan? ta fada tana kuka


"Ah ah khadija me suka Miki"


Aunty' Wai daga zuwana naje na tsaya agun da kawaye ke tsaye kawai Ina zuwa suka mimmike suka koma wani wajen Wai kunya suke kar abokan ango suganni a cikin kawaye za'a Raina class nasu,kinsan ma Aunty me yafi Bata mini Rai?


"Ah ah khadija"


Wai Aunty danaga duk sun watse saina koma cikin mutane na tsaya kawai kowa na tsaya kusa dashe sai ya Kama matsawa Wai kar ace tare Dani yazo, don ban saka kayan Fulani ba koma banyi ado ba


Sosai naji wani irin haushi kamar zai kashe ni


Aunty bazan sake zuwa bikin kowa ba daga yau


"Yau me za'a yi"?


Kamu,ta bani Amsa


"Zaki je bikin nan khadija har a Gama dake za'a Gama insha Allah"


Aunty ni bazan sake zuwa ba a wulakanta ni,don Yaya yace Koh mutun baida kudi in dai ya rike mutuncin sa bazai wulakanta ba


"Ki kwantar da hankalinki insha Allah bazasu sake wulakanta kiba" na fada Ina Mai Jin tausayin baiwar Allah nan


D'aki na shiga na barta tana kuka akwatina na bude Kaya na d'auka Atamfa da les masu azaban kyau a dinke sai Turare na d'auka guda D'aya na fitoh a d'akin dasu a hannuna


"Khadija rike kayan nan Naga kamar akwai tailoli a tsallaken titi ki Kai musu wa'innan kayan su rage Miki yayi daidan ki yanzun in Kika fita,
wannan Turare Kuma kasuwa nakeso ki Kai shagunan masu Turare Koh zasu Saya kudin sa 20k ne Amma Koh 10k Kika samu Koh kasa dashe ki karba kawai"


Aunty ba Yaya yace ki daina Saida kayanki ba?


"Khadija Zan zauna da yunwa ne Ina da abinda Zan tsayar naci a cikina sai na zauna"


Gaskiya ne Aunty Amma fa Yan kasuwa bazasu Saya ba don yanzun Suma tsoron sayan kayan hannu suke karsu Saya na sata,sai dai akwai wata Mata dillaliya ta bayan kasuwa sai na Kai Mata don ance itakam Koh kayan satane Saya take don Yar rikici ce sosai


"Yauwa khadija Allah yasa ta Saya wannan kayan in kin fita ki fara kaisu shagunan dinki"


Aunty wazaki bawa kayan Kuma ai Naga daidan kine naji kince a maidashe daidai na?


"Ina ruwan Ki,nidai tashi kije mini aika na,
sannan in ta Saya Turaren ki shiga kasuwa ki sai Gam bak'i Mai kyau ki hada da Turaren lalle,sajan,tsamiyan kanti, ki sai bakin lalle guda biyu shima"


Aunty lalle zakije ne?


"Kai Khadija banson tambaya ki sai mini kayan Miya duka,in kin dawo ki biya tailan kudinsa ki karbi kayan Saiki saimin doya soyayye a bakin titi na karya"


Toh Aunty tace ta karbi kayan tasa a laida ta fita


D'aki na shiga Ina ta tunanin halin rayuwa da khadija ke ciki


Sai karfe 10 khadija ta dawo kayan na bubbude na Bata ta gwada Aiko yayi Mata daidai jikinta sosai kayan ya karbe ta,doyan na bude Mana mukaci tare


Kam in na manna a tire na kwaba Jan lalle, "khadija zoki zauna na Miki lalle"nace Mata Ina zama akan dakali


Aunty Daman ni Zaki ma lallen ne har Kika Saida Turaren ki Mai tsada a naira 5k?


"Khadija bazan d'auki wulakanci ba Sam insha Allah yau saikin fi Amaryar kyau bama kawayen ba"


Daman kin iyya lalle ne Aunty?ta fada tana zama


"Sosai ma khadija ai lokacin da nake primary school innaje makaranta sai nayita zana flower lalle a takanda na Inna dawo gida sai ummie na tace zata buge ni sai abie ya k'waceni yace bazata bugeni ba ai batasan Koh baiwar da Allah ya mini ba kenan,
sai ya sai mini takkadar lalle daban duk lokacin da zanyi Zane saina dawo makaranta sai ya bani takardar na zana, lokacin da na Gama primary sai ya sai k'wallon dayes ya baiwa Mai aikin mu ta dafa mini da lalle,sai nayi mole na zuba a ciki,abie ke saimin hydrogen Ina ma yaran gidan mu lalle harda yaran makwanta,
harna girma Ina lalle duk yaran gidan mu da aka aurar Mata Ninake musu lallen aure da make-up haka kawaye na da Yan unguwan mu sosai nake Alfahari da lalle khadija"nace Ina

Please Login or Register in order to submit comment