Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwa ake Alwala nayi,jakana na dauka a baranda na shiga dakin,


Jin dis dis Kamar panfo yazo daukewa yasa na lalube wayata a jaka na haska dakin idona ya sauka akan kujiran da yayan khadija ke k'wanciya ya jika jakaf da ruwa saitin wajen na yoyo fita waje nayi da sauri na d'auko baf nazo na tare ruwan,kaya na dauka na bacci na saka da hula harda socks don wani irin sanyi nakeji har cikin k'ashina sallaya na shinfida na Tada sallah mangariba da Isha nayi shafa'i da wutire ,


blanket na dauko nahau gadon na lullubu abina na kwanta da wani irin ciwon Kai da zazzabi nakeji gashi kafafuna sai zuge suke mini nama rasa meke mini Dadi


Al'ameen suna tafiya da Khadija Chan dai Khadija ta kasa hakuri tace ,Yaya nikam na tambaye ka Mana?


Allah yasa na sani dija,


Kai Yaya ni banason dijan nan ai sunan tsofine,


Toh hadixa Ina jinki,




Habba yaya ta fada tana hada fuska,


Sorry toh kanwata Ina jinki


Yauwa Yaya nikam Aina ka hadu da Aunty Sumayyan ne harkace kana Sonta?


....Dam dam haka gabansa ke bugawa , Khadija meyasa Kika mini wannan tambayar,?




Ba kome Yaya kawai na tambaye Kane ,


Ah ah Khadija fad'amin gaskiya nasan baki tambayar Abu banza,


Am Yaya Naga baka taba bani lbrn kana da budurwa ba kawai sai naji Wai kayi aure za'a kawo Amarya,


Toh Khadija ke abokina ne da saina fada Miki Ina da budurwa,
auren Kuma yazone a bazata ban dauka iyayen ta zasu bani ita lokaci d'aya ba,


Amma yaya kaga gidansu aunty kuwa Mai azaban kyau ga Yan gayu k'yawawa a gidan Kuma Aunty ma kyakkyawa fa Yaya toh ma Ina kake zuwa daga Tashar kayan marmari sai wajen sana'ar ka Ina kaga aunty har kuka fara soyayya?


Ikon Allah Khadija Wai tambayar nan Kam na lfy kin sani a gaba da tambaya sai kace wani sa'anki ,


Kayi hakuri Yaya dai dai lokacin suna iso kofar gidan Goggo Amina,


Muje Khadija na rakaki cikin gidan nama Goggo bayanin dalilin yin darenki ,


Toh Yaya ,




shiga sukayi cikin gidan tare,


Goggo Amina ce ta amsa sallaman tasu tana fama da icce a runfar girkin ta


Isa sukayi ya gaishe da ta Yamata bayanin dalilin yin Daren Khadija,..


Wallahih Muhammad Nima sai da na tura yaro yajimin lfy Khadija har dare Bata dawo ba ga aikin dare da tace zata dawo ta Kama mini, ya dawo yace min ba kowa a shashen ku,


Kiyi hakuri Goggo, Basu dawo ba sai yanzun Al'ameen yace Yana mike wa,


Ba kome muhammad shine ka tasata a gaba a ruwan nan Maimakon ku bare Sai ya tsakaita,


Goggo Nima haka nace Mata Amma tace Zaki Mata Holo itakam sai gidan Goggo shine na rakota


Gggo ruwan da yawansa bansan karfe nawa zai dauke ba shiyasa nace gwara na dawo

Hakane Kam da gaskiyar ki Khadija


Toh sai da safe, Goggo


Allah bamu alkhari


Ameen suka amsa ita da Khadija shikam fita yayi ya Kama hanyar gida,


Ina kwance Amma ba bacci nake ba tunani kawai na fada nayi zugum gabaki daya gari yamin zafi,


daidai lokacin ya shigo kofar duk ya jike Daman jallabiya ne a jikinsa ,,


hauro wa dakalin Yayi ya zare jallabiyar sa ya aje a cikin boket in wanka dakin ya shigo daga shi Sai gajirin wando, da sallama a bakinsa


Ina kwance cikin duhu don na kashe hasken wayana naji buruntu ana kokarin shigowa dakin don ni Sam banji sallamar ba, hasken wayata na kunna me Zan gani yayan Khadija ba Kaya, murd'adden damtsen hannunsa naci Karo a waje ga fafad'an kirjinsa mai cike da yalwan gashi,baki sitik kwance akan farar fatarsa kafarsa farare tas sai gashi ke kwance a lallausar fatar kafar tasa ai bansan lokacin da na k'wala ihu ba na dirko a saman gadon,na Kama hanyar waje don ni sai ma gani nake kamar ba wando a jikinsa don ajike wandon yake tsabar birkita hanyar kofa na nufa zanfita na bar Masa dakin,


Jin ihunta sai ya birkitasa ya dauka Koh wani abune ya sameta Jin ihun take akai akai hakan yasa ya gigice shima ya fara neman hanyar kofa cikin lalube,da D'an saurin sa Jin itama kofar ta nufo tana ihu har lokacin,


Ji kake gauuuu! sun garu da juna a kofa daga shi har ita ihu suka saka a tare, sai kawai suka kuma zubuwa ji kake timmmmmmm............


*Gobe Monday Ina da jarabawa bazakuga update ba fan's* πŸƒβ€β™€οΈ


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page1️⃣8️⃣&1️⃣9️⃣
Washhhh yace jinsa a k'asan cafet ya zube,Bai farga ba Yana kokarin mikewa, yaji ta Fad'i a kansa daga shi har ita Kara suka saka sai Kuma sukayi shuru tare,


ido na ware jina a jikinsa cikin rawan jiki duk na rikice na fara chuku chukun mikewa naji yasa hannu ya zagaye hips ina,
sosai ya kara matsota kusa dashi,


"Kai me haka" ? Ka sakeni Mana, Mena rike min........sai Kuma tayi shuru ta kasa karasawa,


Cikin sanyin halinsa ga jikinsa na wani irin rawa Jin mace a jikinsa a karon farko a tarihin rayuwar sa kenan, yaji mace a kwance a jikinsa, Mena rike Miki? Ya tambaye ta Yana yawo da fuskarsa a kafadar ta Yana neman fuskarta, so yake ya Hada fuskar ta da tasa,


"Wai ma Ina ruwanka ne don Allah nikam sakeni haii" nace cikin ihu


Jin muryarta hakan ya tabbatar Masa da inda saitin fuskarta yake hada fuskar yayi da tasa har suna Jin numfashin juna,


"Wai menene haka bazaka sak".........bai bare na karasaba naji saukan lips nashi masu uban dume akan nawa lips in wani abu naji ya tsargar Mini daga tsakar kaina har farcen kafana cikin wani irin birkita na yunkura zanbar jikinsa zan mike ji kawai tayi ya fisgoni gabaki d'ayana na zube Akansa ,
cikin wani irin zafin nama da kuzari ya cafke lallausan bakinta cikin nasa da wani irin zafi zafi yake tsotsarta Jin sai k'okarin mikewa take a jikinsa yasa kafa ya harde kafarta da nasa kafar,daga ita harshe rawa jikinsu yake,


Tashin hankali da nake ciki ba'a saka Masa Rana kuka nake so nayi Amma ba Hali hawayene kawai kebin kumatuna,


Jin saukar hawayenta akan face nasa ya saka sa sassauta Mata riko a hankali ya zame bakinsa cikin nata,


Ai da wani irin azabebben sauri na mike tsalle D'aya nayi na fita a d'akin na tsaya a baranda duk sanyi da ake da ruwanda ake zugawa na g'wammaci na kwana a waje Data kwana a d'akin nan inaaaaa,


Sumayya!!! Sumayya!!! yake kiranta cikin tsarkewar murya shima ya mike Yana lalube ya fitoh wajen,


ganinsa ya sakani zabura Amma tunawa da nayi baya gani yasa na tsaya naki Koh motse kirki Ina jinsa sai kirana yake Yana lulube na a baranda in yazo lalubar Gefen da nake saina matsa a hankali na koma inda ya laluba,jikina nata rawa,


Jin baijita ba don karfin ruwanda ake Bai bare yaji Koh D'an motsen taba don ruwa ake harda tsawa,sauka yayi a baranda yanakan lalube,
ruwa na dukansa Yana zaga kofar Amma Bai jita ba har kofar shashen ya taba Jin kofar a rufe yasa ya gane Bata fita a kofar ba,


Don Allah Sumayya ki kulani Koh zanji hankali na ya kwanta don nasan kina jina kina ganina,


Wani irin tausayin sa naji ya kamani ,cikin sanyin jiki da fargaba nace "ganinan anan,"


Ai da hanzarinsa ya nufi barandan jikinsa ya jike jakaf da ruwa haryana diga ga gashin kansa da gemunsa duk ya jike ya k'wanta g'wanin sha'awa ,


Da hanzari ya iso wajen ta cikin rawan murya ya fara magana, Sumayya pls mu koma d'aki kinji,


"Nidai yau bazan k'wana da kaiba a d'aki D'aya ba "nace Ina kuka Kamar karaman yarinya,


Kiye hakuri kinji Sumayya muje mu k'wanta Allah bazan miki kome ba kinji Koh,


"Wallahih nidai bazan shigaba" Ina fada Ina kuka, ganin Yana matsowa kusa Dani yasa na k'wala Kara Zan ruga cikin ruwa naji anyi sama Dani,


D'aukarta yayi duk yanda take kuke kukenta kin kulata yayi sai ihu take tana ya sauke ta, sosai ya riketa Gam a kirjinsa Yana lalube har suka shiga dakin ya tura kofar da hannunsa d'aya d'ayan na rike da ita ,


A hankali yake lalube harya Iso bakin gado a hankali ya haura saman gadon kwantar da ita yayi a hankali ya lalube blanket inta ya rufa Mata ,ya sauka Akan gadon cikin lalube ya shiga neman Ghana must go in kayansa wani jallabiyan ya dauka a wanke tas ya zura ya zame jikekken gajeren wandon sa,
lalube yayi ya fita waje a aje a cikin kayansa jikakko daya aje a boket,


Nikam tunda ya saukeni a Kan gadon jikina yake ta rawa sosai naji wani irin tsoron Daren nan, zazzabinane ya Tashi sosai nakejin kaina na Sara mini yau tension Yama kaina yawa,


Dawowa yayi Kan kujira zai k'wanta Amma yaji baho a saitin wajen, lalubawa yayi yaji kujiran a jike hakan ya tabbatar Masa lalai yo-yo wajin ya ke filon kujiran da yake k'wanciya dashi ya dauka ya lalube cafet ya aje ya k'wanta a kasan dakin wani irin sanyi ne ke shigar sa don a lokacin baiki ya samu abin rufuwa ba Amma Bai dashi Kuma baida karfin gwuwar tambayar Sumayya tunda ba ita tayi niyar basa ba,




Jin motsen yayan Khadija yaki natsuwa sai jujuyawa yake ga atishawa akai akai alamudai murace ta kamasa,


Wayarda na wancakalar dashi na dauka na haska inda nakejin motsen sa ganinsa nayi a kwance sai jujuyawa yake alamudai sanyi yakeji,


D'an tausayi ya bani sai Kuma na tuna lokacin da bani da lfy dashi da Yar uwarsa su sukayita d'awainiya Dani Amma yau shine na Bare a kwance a kasa ga sanyi,
ni Ina kwance a gado da bargo,


Kamar bazanyi magana ba a hankali nace ",kazo ka kwanta a gadon kasan nan akwai sanyi Kuma naji Kamar mura nason kamaka"


A hankali ya mike ya Soma lalube harya Iso bakin gadon cikin nutsuwa ya haura dai dai ta bakin ya kwanta,


Nikam Ina karshen gado ta wajen jikin gini ganin Bai taba blanket in ba bare ya rufa, yasa na mike na dauko wani a whdrp na aje Masa a kansa na wuce filina na kwanta addu'ar bacci nayi na shafa na juya masa baya ,


Jin ta aje Masa blanket yasa she d'auka ya lulluba shima addu'ar bacci yayi ya lumshe idonsa Sam yaji bacci ya kaurace Masa wani irin yanayi yau ya tsinci kansa a ciki,Mai ban Al'ajabi


Daga shi harni Babu Wanda ya rintsa har 1:00 na dare kafun bacci ya dauke ni shikam bansan lokacin da yayi bacci ba,




*********
Yaukam dagani harshe sai kusan 6 mukayi sallan asuba a dadafe dukan mu biyu da ciwo Muka kwana ga yunwa don tun karyawan safe dagani harshe bamu sake saka kome a bakin mu ba,


muna idarwa gado Muka koma muka sake k'wanciya don baccine ya cika Mana ido na rashin Yi da wure jiya,
Jin Yana matsowa kusa Dani yasani matsawa da sauri ji kawai nayi ya mike zaune ya zura hannunsa ta saitin da nake ya jawoni duka jikinsa a hankali ya koma ya kwanta Dani a jikinsa ,




Yanzun Kam ban neme k'wace jikina ba saboda zazzabinda nake fama dashi ma ya isheni,


A hankali nace Masa"Wai meke damunka ne tun jiya kake ta tabani"?


Nima ban sani ba haka kawai nakejin inason kusanci dake,ya fada da muryarsa da ta dishe don mura kamasa Tay sosai ga fuska jazur kamar ka taba jini ya zuba,


Kala bance Masa ba don ni jikina ne ya dameni,shuru mukaye gabaki d'ayan mu har bacci ya dauke mu a haka,


sallama nake ji kamar muryar Khadija sama sama cikin bacci sai Kuma naji yayan Khadija na zame jikinsa a nawa,


Bude ido nayi Wanda nakejin nauyinsa sosai ga xaxxabi,


Khadija Kam ganin takalmin Aunty da na yayanta a bakin dakali yasa ta juya zata fita Amma dai tana mamakin har 10:10 na safe yayan ta Bai fita ba,


Mikewa Al'ameen yayi ya fita a d'akin Jin alamun Mai sallamar na kokarin fita a shashen Kuma ya shaide muryar Khadija ne,


Waalaikumu salam Khadija ya kina komawa kuma?


La Yaya Daman nace bara nazo na duba Aunty jiya kafarta tun a hanya ya kumbura Amma dai ba kome anjima Zan dawo,


Saboda me?


Naga baku tashi ba Yaya,


Ah ah ai gwarama da kikazo Nima Yanzun nakeson fita na nemi yaro ya kiramin ke,


Lafiya Kam Koh? Naga fuskarka ta kumbura tayi ja ga murya a dishe Daman Saida na tuna haka wallahih ruwan jiyan nan ya kare a kanka,


Ai bani kadai bane Khadija Aunty kima ba lfy ,


Subhanallah meke damunta Hala kafar ke ciwo,?


Ah ah Khadija zazzabine,
Meya faru da kafartan ne da kike ta cewa Yana ciwo,?


Ba kome kasan jiya bamu samu Keke da wure ba Koh?da kafa Muka ringa takawa,




Uhmm lallai fa,yace Yana dafe kansa dake Sara Masa,


Sannu yaya kanne?


Wallahih Khadija,


Toh kaje ka kwanta Mana bara na gyara kofar,


Khadija Aunty ki tun karyawan jiya bataci kome ba zoki karbi D'arin nan ki sai Madara 50 da bornvite 50 akwai sugar n jiya da safiya da Lipton ki hada Mata tie Koh zata iyya Sha?


Toh Yaya Kaifa,


Khadija hada Mata kawai taima kayan shayen bazai Isa ba?


Zai Isa Yaya,


Toh shikinan ki hada hardani


Toh


D'akin ya shiga yadau kudin ya mikowa Khadija ya dawo ya kwanta, tare da matsowa kusa dani


Nidai Ina jinsu shuru kawai nayi,


10:30 Khadija ta dafa Mana shaye harda k'wai ta soya dayake jiya yasai kayan Miya na dare yazo ya samu bamu dawo ba,


Tana Gama shirya kayan Karin ta nufi dakin,


A bakin kofa ta tsaya tana sallama Bata shigo ba ,


Mikewa yayi ya zauna a bakin gadon ya sauke fararen kafarsa a kasan cafet,amsa Mata yayi hade da Bata izzinin ta shigo, Khadija ki shigo mana,yace Jin Taki shiga,


Da sallama a bakinta ta shigo d'akin aje kayan hannunta tayi akan cafet,zata juya,


Khadija d'auki baf in Kan kujiran nan kikai waje kizo ki jona fanka naji Kamar an kawo NEPA ki juyashi saitin kujiran samun ya bushe,


Toh Yaya tace tana daukan baf in tayi waje dashi zubar da ruwan tayi ,


Ta dauki tsintsiya ta shigo dakin tire in kayan karyawan ta dauka ta daura akan kujiran ta share dakin,
fanka ta kunna ta matso dashi Kusa da kujiran,Kamar yanda yace


Turarukan UMSAD INCENSE da ta Gani a jere akan mirror ta d'auka na d'aki jona kaskun lantarki tayi Aiko take dakin ya dauki kamshi Mai Dadi (kowa yasan yanda Turaren wuta yake da kamshi a d'aki especially a damuna),


Khadija na fita ya matsoni a hankali hannu yasa Yana laluba ta nikam sai matsawa nake duk inda naga hannunsa zai taba saina matsa agun,.


Don Allah Sumayya ki tsaya Mana kaina ciwo yake wallahih Koh motsasa bana sonyi kina ta bani wahala yace Yana dafe Kan,


Toh ni sai ka min magana da hannune bazaka mini da baki ba saikayita tabani,


Sorry tashi kije ki wanke bakinki ga breakfast Khadija ta hada Mana yace Yana kwanciya,


Toh Kaifa bazaka wanke bakin bane kake k'wanciya sai yayi ware? nace Masa Babu alamar Wasa,




Murmushi yayi har fararen hakoransa masu tsananin kyau suka bayyana,ai kinfi kowa sanin bakina nada ware Koh babu tunda kin d'and'ana jiya , ya fada muryarsa a shake


Ohon maka dai nace cikin Jin haushi mikewa nayi a hankali na nufi kofa shima mikewar yayi yabi bayana ,




Kofata nabi da kallo tasss Khadija ta share samunta ma nayi tana wanke wanke ga kayan na data cicire a igiya ta zuba a boket,


Khadija kibar d'aurayan nan don Allah daga kin wanke Kwanukan nan ya Isa haka ke baki gajiya da aikine,


Toh aunty tace mini,


Wanke baki mukayi muka koma daki abincin na jawo Mana ganin hadamu tayi plate d'aya tie ne kawai kowa da cup nashi,


,k'wala Mata Kira nayi"Khadija Khadija"


Na'am Aunty ganinan zuwa,, tace
Tana shigowa dakin


"Jiki d'auko wani cup da plate"toh tace ta fita sai gata ta dawo dasu


Ajjyemin tayi zata fita,


"Tsaya Khadija" nace zuba Mata tie nayi na ibi k'wai data soya Mana NASA Mata a plate itama" d'auka kije kici nasan dafawa kikayi baki ibi naki ba Khadija kullum Ina gayamiki in kin girka Abu ki ringa zuba rabonki kinji Koh kin manta nan ma gidanku ne"?


Toh Aunty tace tana karban plate da cup in tayi waje,


Bismillah na Masa ya matso yasa hannu kad'an naci,naji ya isheni don bakina ba Dadi sam tie kawai nashanye duka, Koh aje cup banyi ba wani irin amai ya tasar mini da gudu na fita waje na ringa shika Amain sosai,


Mikewa yayi yabi bayana daga shi har Khadija sai sannu sake mini Mika min ruwa tayi na wanke bakina na koma d'aki
duk k'wanciya Muka sake don shima bazai iyya fita wajen sana'a ba,


Misalin karfe d'aya na Rana ana kiraye kirayen sallah azahar ya mike ya fita, wanka yayi a dadafe ya nufi waje zaije chemist in jambusko Koh zai basa bashin magani Koh iyya Sumayya kawai ma in zai samu a Bata ya gode Allah duk da yasan halin inyamurin daker ya ya basa bashi,


Yana fita Nima mikewa nayi Ina Jin jiri jiri na fitoh waje Jin ana kiraye kirayen sallah Khadija na samu ta wanke Mana kayan mu daya jike jiya,tana kitchen wani aikin Kuma take,


"Khadija Wai me yasa bakiji ne nace Miki kibar aikin haka "


"Ke kullum kikazo guna baki abinyi sai aiki"


Toh Aunty in ban Miki ba wazan ma ba lfy bane dake ga kofa kasha kasha Koh abincin da zakuci bazaki iyya girkawa ba toh Aunty in ban muku ba wazai muku


A gaskiya bansan dame Zan sakawa Khadija ba Allah ne kawai xai biyata


Nagode Khadija Allah ya barmu tare ya nuna mini auren ki in ban mutuba,hhhhhh nace Ina dariya


Kai Aunty tace tana rufe fuska Wai kunya,


Yana fita gida massalaci ya shiga ana idar da Sallah yanufi chemist in jambusko,


Yana Isa sanin ba musulmi bane yasa ya ce Masa , excuse,?


Yes wanene?


Nine jambusko,ya basa amsa Dayake inyamurin ya Dad'e a Jala yanajin hausa sosai ,


Wai MAKAHO Kaine anan yau kuma?


Eh wallahih madam ce ba lfy zazzabi ke damunta........


Bai bare ya karasa bama ya ce kaima ai harda Kai bakaga muryarka ba ga fuska yayi ja ido ya kumbura,kana mura,


Eh harda ciwon kaima shiyasa nazo wajen ka ka taimaka kaban bashi inna d'an ji sauki zuwa anjima zanfito in Allah yasa na samu kasuwa saina biyaka, ya fada cikin zullumi don shi kansa Allah ya gani kwata kwata bayason roko Koh bashi Amma ya zaiyi bazai iyya zuba ido Yar mutane ba lfy ya barta haka na shi Karan kansa Saida lfyr zai nema musu abinci




Heeeee chinekeeeee gaskiya MAKAHO nii...........




*Gaisuwa na musamman gareki ummee zariya Naga special comments naki Kuma Nima na yaba Miki sosai naji dadi* πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page2️⃣0️⃣&2️⃣1️⃣
Niii bazan iyya baka bashi ba true,


Habba jambosko ka duba dai pls insha Allah Zan biyaka,


Ok shikinan na nawa kake so?


Ni koh na nawa ma ka bani yanda kaga ya dace ,


Ok Zan baka na d'ari 300 Kai na d'ari 150 madam na150 kaga kudina 300 kenan ,


Nagode sosai,


No problem,


Maganin ya basa nata da nasa ya kamo hanyar gida.....


Nikam wanka nayi nayi Sallah na kwanta duk yanda Khadija tayi nacin naci abincin da ta dafa na Rana, na kasa itama tana gama aikace aikacen ta shigo d'aki,


Aunty'ya jikin dai?


"Da sauki Khadija"


Toh Allah ya k'ara sauki bara na tafi Aunty Koh kina da wani aiki da Zan Miki


"Khadija bani da aikin kome kije ki huta kema",


Toh Aunty tace tana kokarin fita a d'akin


"Khadija ki dauki kula ki zuba abinci a ciki ki tafi dashi gida"


Toh Aunty,


Khadija kitchen ta shiga ta ibi abinci kamar yanda Aunty tace,ta kama hanyar waje zata fita,
a kofar gida suka haduwa da yayan ta zai shigo ,


Yaya baka da lfyn ma yawo kake,?


Khadija chemist naje fa na samo Mana magani Wai yaushe na fara Wasa da kene,


Hhh sorry toh ni Zan wuce yaya Allah ya yaye muku


Ameen Khadija ki gaida Goggo sannu da aiki


Toh Yaya zataji,


Cikin gidan ya wuce a hankali yake tafiya gaskiya mutuwar innon nan ta shiga jikin Yan gidan su yanzun gidan shuru,




Da sallama ya shigo d'akin , Assalamu alaikum,


amsa masa nayi "waalaikumu salam"


Ya jikin dai ?


"Da sauki",


Toh ga magani nan Amma ya kamata ki samu kici abinci kafun Kisha,


"Wallahih banajin dadin bakina Sam"


Haka dai Zaki daure kinji


Toh nace ina mikewa fita nayi waje,


kitchen na shiga nad'au kulan da Khadija tace ta saka Mana abincin na bude,


Dafa dukan shinkafa da wake ne Kuma da D'an yawa ta dafa harda na dare kenan,iba nayi na zuzuba a plate guda biyu nasa shukali d'auka nayi a hankali ina taka kafata dake ciwo har yanzun,


na shiga d'akin aje abincin nayi na bude firij na siyaye ruwan randa danake zubawa a roba NASA a firij don yanzun Koh pure water bani da kudin saya bare drinks,


Ruwan na tseyaye a cup inda na jejjera a saman tire akan firij don irin haka,


Ruwan na iba na dawo na zauna tura masa nasa nayi hade da masa Bismillalahih,


Hannu Al'ameen ya saka ya fara cin abincin sa don shi Yana d'aya daga cikin irin mutanen nan da ciwo baya hanasu ci,


Nikam tsakura nayi na aje shukalin ruwan Randa Mai dumi na ibo nasha maganin dashe don ance ba'a Shan magani da ruwan sanyi na kwanta na barsa zaune yana cin abinci,


Harkin koshi kenan Sumayya?


"Nace maka bakina ba Dadi fa Amai zanyi wallahih Inna sake Kara Koh shukali D'aya ne"


Yana gama cin abincin ya mike ya tatara Kwanukan yakai kitchen dawowa yayi da ruwan Randa yasha maganin mikewa yayi zai sake fita,


"Ina zakaje Kuma"?


Zan D'an fitane ,


Zuwa Ina?


Zanje wajen sana'a ne,..


"A baka da lfyn zaka fita kaje ka zauna a Rana",


In Rana ya Isa wajen bairona Ina komawa jikin shagon Haladu na zauna,


"Zirga zirgan fa magani fa kasha kadai bare itan Rana yadan fade kaji saukin jikin naka sai ka fita"


Ok toh yace ya lalube pillow ya jefa a kasan cafet ya kwanta,


Dukan mu bacci muka koma saboda maganin mura da mukasha,


Kiran la'asar shiya tashe mu Alhamdulillah daga

Please Login or Register in order to submit comment