Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi a kan tabon bakin kogi.


Kurawa fuskar Al'ameen ido gid'ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al'ameen, ya d'aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi.


Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d'auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala'i, Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake.


Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki.


Assalamu Alaikum


Waalaikum.......sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid'ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka)


Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d'aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa.


Gid'ado d'obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al'ameen dake kafadar gidado.


Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar.


Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad'ar ka, ka shigo mana ruga akan me?


Don Allah inna a wad'a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa, koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d'aki, d'auke da tsohon ciki tana nufosu.


Kwantar dashi gid'ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace.


Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d'aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi.


Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa?


eh, yi sauri ka d'auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai, bappa ya mammatse masa ciki.


Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid'ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai.


Maganin bappa ya d'auka a kwarya, yana shashafa ma Al'ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d'aga ido ya kalli gidado, husumo ayara ha sudu(ka daukesa ka kaisa d'aki)


Wai bappan gidado ban gane a d'auke sa akai sa d'aki ba, yadaga ganin mutum bamusan daga ina ba, mugune koh nagari?kawai mu d'auko mu aje a cikin gidan mu, ni gaskiya ban yarda ba.


Talatu kena bani mamaki wallahi, yanzun ace mutun baya cikin hayyacin sa, ina kikeso mu kaisa?


Koma ina a kaisa, amma dai gaskiya banda cikin gidan nan, taima ma mugune.


Koh mugune, mu Allah zai dubi zuciyar mu, insha allah bazai basa ikon cutar damu ba, bare ma wannan yaro baiyi kama da mugu ba, daga ka gansa kasan akwai jinin fulani a jikin sa.


Lantana matar gidado kam, mikewa tayi ta shiga d'aki ganin fad'an bappa da inna baya karewa in gari ya waye .


Kai gidado d'auke sa ka kaisa d'akin kusa da gindin murhu.


Toh bappa, yace yana ciccibar sa yakai d'aki, shanu kansa dake binsa a baya tunda ya d'auko Al'ameen har gida, suya kama ya d'ad'aure a turke.......


**************************
Ta bangaren sumayya yau satin ta d'aya a Hospital, har da kwana d'aya, Amma jikin dai za'ace Alhamdulilah, da sauki kad'an duk da baiyi kwari ba, sosai likitoti ke kula da ita, hatta Dr tana iyya bakin kokarin ta, ganin sumayya ta samu lafiya, Amma taki kwantar da hankalin ta sam.


Khadija ma yau sati guda, rabon ta da makaranta,suna faman jinyan sumayya, Goggo ke zama a asibiti, ita kuma ke musu girki a gida ta kawo musu, duk da sumayya baci take ba, sai yan aikace aikacen gida duk ita keyi.


Kamar yau ma, khadija ce ta kammala girki a kofar sumayya, zuzzubawa tayi a kula, tasa a kwando ga flask a hannun ta, ta fitoh gidan Adara, tsallaka titi tayi ta nufi shagon yayan ta, shagari ta samu zaune yayi tagumi gabaki d'aya yaron ya shiga damuwa ainu na b'atan Al'ameen, duk da shike kula da shagon yanzun, amma sai yanajin shagon kwata kwata baya masa dadi.


Assalamu alaikum.


Wa'alaikumu salam, khadija zaki wuce hospital in kenan harkin shirya?


Eh na gama girki.


Ok yace yana mikewa, laida ya d'auko ya zuzzuba ayaba da kankana mai yawa, ya rufe shagon, kwandon hanun khadija ya kamar ba, ya bar mata flask in yana rike da laidan kayan marmarin a d'aya hannun, suka kama hanyar FMC da kafa, don shagari duk da muhammad baya nan, amma baya masa Almubazza ranci da kudi, asalima tattalin sa na yanzun yafi nada, hatta kudin asibiti duk Abinda aka bukata shiyake biya, ya hana sumayya kashe koh sisi.


Sunzo sharan kwanan doruwa, kawai suka ga anyi packing moter a gabansu, khadija kam koh duban motar batayi ba, kokarin kaucewa take ta gefe, ta wuce abinta, dayake shagari bai wani waye Ammar ba, yasa bai ma saurare saba yabi bayan khadija.


Ke yar kauye, mai tafiya bata kallon gaban ta.


Da sauri khadija ta d'ago jin muryar Ammar,ina kwana?tace.


Kin Amsawa yayi ya dubeta, ina zaku kuma da abinci haka.


Asibiti, ta basa Amsa.


Waye ba lafiya?


Aunty sumayya .


Subhanallah, yayan naki nacan ne?nima yau na dawo da asuba, shine nace bara na biyo gunsa.


Shuru khadija tayi bata basa Amsa ba, sai kaucewa da tayi taci gaba da tafiya.


Da sauri ya fitoh a motar, yabi bayan ta, keee ba magana nake miki bane?kina tafiya?


Kala batace ba, tana ta tafiyar ta.


Hannun ta Ammar ya rike, da sauri ta juyo tana kallon sa, sakemin hannu?


Naki na saken, ina miki magana kina manna mini hauka, ina wasa dake?


Kuka khadija ta sake masa da karfi, ai da sauri Ammar ya sake mata hannu, ya juya yana kallon shagari, dake tsaye yana kallon su, fuskar sa A hade, haka kawai yaji ya tsani Ammar, ganin yanda ya wani rikewa khadija hannu.


Kai meke faruwa ne?Ammar ya tambaye sa.


Fuska a hade yace, An sace oga ne shiyasa daka mata maganar, ina yayan ta, take kuka.


Sai a lokacin Ammar ya gane shagari, watoh shine wanda muhammad yace zai d'auko su zauna a shago, abu na biyu daya basa mamaki kuma wai an sace muhammad, sai kace kaza, ban gane an sace saba?


Eh an sace sa, haka kawai wasu a mota sukazo suka d'auke sa, a bakin titi


Tsabar razana har tuntube yayi, yau kwana nawa kenan?


Sati d'aya.


Amma har sati d'aya, police basu d'auki wani kakkauran mataki ba?mutum ya bata kamar wani kaza koh d'uriyan sa babu?


Koh report bamu shigar ba, Shagari ya basa Amsa.


What?? ba'a kai kara ba, akan me?


Sumayya na asibiti, ni kuma tsoro nake ji, shiyasa ba wanda yakai.


Amma ai koh baku kaiba, nasan labari zaije wa yan sanda, tunda kuna kusa da station, yaci su subibiye Lamarin.


Shuru suka, masa.


Ku shiga muje asibitin, yace yana karban flask in da khadija ta dongorar, yasa a mota.


Shagari ma shiga yayi ya zauna a gaba, har lokaci tana tsungune a kasa, hannu kawai Ammar yasa ya fizgota, ya jefa a bayan motar, ya zagaya driver sit ya zauna, yaja motar suka nufi Hospital.


Suna shiga hospital in, dashi da shagari ne suka d'auko kula da flask, harda laidan, khadija kam an kaikaya mata inda yake mata kaikayi, kuka har lokacin yinsa take, duk yanda shagari keta bata baki tayi shuru, amma ina.


Keeee wallahi in na sake jin koh tarinki, a asibitin nan saina saba miki, banason shirme tun d'azun, sai cika min kunne kike nayi shuru, yanzun mun shigo asibitin ma bazaki rufe bakin bane? saikin tara mana jama'a.


Shuru khadija tayi, harga Allah wannan Ammar in kamar mai Aljanu haka yake, zafi zafi sanyi sanyi.


Shagari kam gaba ya kara, dayake yasan d'akin da sumayya take, bai saurare tahowar suba, yayi tafiyar sa, yana maijin haushi a ransa.


Shiya fara shigowa d'akin, da sallama.


Amsa masa sumayya tayi, wance ke zaune daga ita sai dogon rigan kanti, kanta koh d'ankwali babu, tana zaune a bakin gadon, rike da wayarta, hawaye nabin kumatun ta.


Ina wuni Aunty, ya jiki?


Kai kawai ta d'aga masa, ta mika hannu ta d'auki d'an kwalinta, dake gefen gadon ta yafa a kanta.


Zama shagari yayi yana bin d'akin da kallo, ganin baiga goggo ba.


Assalamu alaikum, Ammar ne yayi sallama a bakin kofar d'akin.


Amsa masa shagari yayi, ba tare da ya d'ago yaga bakin kofar ba.


itama sumayya bata d'ago ba, sanin wake sallamar, don ta shaida mai muryar.


Shigowa Ammar yayi, idanun sa ya sauka akan sumaya, dake zaune gabaki d'aya ta chanja, ta rame sosai sai haske data kara a yan kwanakin nan, har yayi yawa,tayi fari kamar ka tabata jini ya fitoh.


A hankali ya tako har inda take, hannu yasa ya amshe wayar, sai a lokacin sumayya ta d'ago ta dube sa, hade da mika masa hannu, Alamun ya bata wayar ta.


Matsawa yayi gefe, ya kurawa screen in wayar ta ido, hoton tane da suka d'auka, ita da muhammad ranan sallah a gidan su.


Sumayya ya kamata kima kanki fad'a, wannan abinda kike kara cutar dakan ki kike, kuka bashi ne magani ba, koh mafita, kin zauna kina kuka, gaki ba lafiya bane dake, ki dubi yanda kika koma fisabililahi.


Gaya mata kam D'an nan, haka nake fama da ita, bansan me take gani a wayar nan ba, ta tura khadija ta d'auko mata, shikenan tamai dashi madubi, tana kallo tana kuka, goggo data fitoh a toilet na d'akin ne take maganar.


Hoton mijin tane a ciki mama, Ammar yace yana latsa wayar sumayya, dake hannun sa.


Au shiyasa take kuka?/lalle sumayya baki jiran kanki, kiga yanda kika zama gabaki d'aya kin koma, kashi da rai sai haske da kike tayi kamar mai ciwon far d'aya.


Kyaleta mama, hotunan duka zan goge.


Kuka sumayya ta sake, jin abinda Ammar yace wai zai goge hoton muhammad a wayar ta"ka bani wayata karka goge na rokeka don Allah"


Ah ah bafa zan baki ba, in gaya miki, tunda zaki tasa wayar a gaba kina kallo kina kuka.


"Allah nayi Alkawari zan daina" tana magana tana kuka


Toh yanzun me kike in ba kukar ba?


Don Allah ka bata wayar ta, sai kuka take tana maka magiya, kana wani ja mata rai, khadija ce tayi maganar cikin jin haushi ganin iyayin da yake ma Auntin ta.


Wani kallo Ammar ya watsa mata, jin maganar da take masa kamar sa'arta.


Bata sake magana ba, aje abincin tayi tana kallon sumayya, in zuba miki Aunty?


"Ah ah banaci"


Wani irin bakici?sumayya yau kwanan mu tara a asibiti, abinci kirki baki ciba ya za'ayi kiyi lafiya.


Shuru sumayya tayi, ta koma ta kwanta bata kara magana ba, don ta fahimci bazasu gane abinda ke damun ta ba.


Ammar kam kallon khadija yayi ya sake kallon, Goggo,meke damunta , sukace mama?


Damuwa ce d'an nan, hawan jinine ya kamata, maimakon ta nutsu ta samu lafiya, Amma ina sai kara kwantar dakan ta take A gado.


Allah ya bata lafiya, in ba damuwa mama, ina so zan fara bincike akan case in batar Al'ameen, in muna bukatar cikekken bayani zan tuntube ku.


Ba kome yaro mun gode, Allah ya saka sai dai ban gane kaba?


Abokin muhammad ne.


Au koh dai kaine Ammar, da yake sanar dani ka bude masa shago?ai munga abin Arziki Allah ya biya ka.


Ameeen mama.


Sai a lokacin shagari da khadija, suka san Ammar ne ya bude ma Al'ameen shago.


Fita Ammar yayi bai bawa sumayya wayar taba, ita ma bata sake magana ba.


Ta bangaren Al'ameen kam har dare bai dawo hayyacin sa ba, gidado yayi ta zuwa dubasa yafi a kirga Amma shuru.


sai da gari ya waye, ya farka jujjuyawa yayi sai kuma ya bude idanun sa, da sauri ya koma baya da mamaki, ganin yarinya budurwa zaune a gaban sa kyakky.................🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~


🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


Page6⃣6⃣&6⃣7⃣
Kyakkyawa tana sanye da kayan fulani, ga wani kitso manya manya a kanta, ta kura masa ido, da sauri ya mike zaune keee lafiya?ya tambaye ta cikin Al'ajabi.


Wallun hakkiloma, tace masa tana murmushi.


Da mamaki yake kallon ta, kafun ma yayi magana yaga wani saurayi da bazai wuce shekara 21 ba ya shigo d'akin, baki ne kamar yarinyar sai dai yarinyar ta fisa kyau sosai, duk da shima ba mummuna bane.


laaa ka tashi?yace da sauri yana karaso wa kusa da Al'ameeen.


Al'ameen kam ya cika da mamaki wai inane nan? gashinan a cikin wani daki kamar akurkin kaza, haka yake kallon d'akin, sai dai jin fulatanci a bakin su yasa sa gane fulanine su, duk da gidan Adara fulani ne sai dai sam basa magana da harshen su, da hausa suke magana sai dai koh yaya ne indai mutum ya zauna a jalingo, zaiji fullaci koh bai iyya maida martani ba bare shida yake zaune a unguwan fulani, shima cikin fullaci yake tambayar su nan inane yake.


Murmushi yaga saurayi yayi, sai kuma ya juya ya kalli yarinyar, indo wai har yanzun baki tafi tallah ba?kinsan in inna tazo ta samu baki wuce ba ranki zai baci koh,fita ki d'auki nonon ki kitafi.


Ba musu ta mike duk da ranta baiso ba, ta fita a d'akin, juyawa gidado yayi yana kallon Al'ameen, sunnu ya jikin naka?duk da fulatanci yake magana.


Sosai Al'ameen yake mamakin wannan Al'amarin, wai garin yayane ma yazo inda yake nan, yanaji gidado nata masa magana amma kala baice ba.


Ganin yaki magana yasa gidado tashi yabar dakin,cikin gida ya shiga yaje ya sanar da bappan sa bakon ya farka, amma baya magana don shi ya d'auka koh wata matsala ce, ya hana muhammad magana.


Al'ameen na zaune kamar gunki yana tunani abubuwan da suka faru dashi, a yan kwana kin nan, sai kuma tunanin sumayya ya fado masa, koh yanzun a wani hali take?lumshe idanunsa yayi yana kiyastata amma yagagara hasko kaman nin ta, yaso ace itace mutum na farko da zai fara gani, bayan dawowar idanun sa.


Gidado da bappa da suka dade da shigowa, sai magana suke amma Al'ameen baisan ma sunayi ba, dafasa gidado yayi, da sauri ya zabura sai kuma ya d'aga ido yana kallon dattijon dake kusa dashi, ya zuba masa ido, sunkuyar da kansa yayi Amma baiyi magana ba.


Akwai inda yake maka ciwo ne?


A hankali y dago kai ya kalli mutumin, sai kuma ya basa amsa cikin fulatanci kamar yanda yamasa magana, babu abinda yake mini ciwo.


tashi ka fitoh kayi Alwala ka biya sallan da ake binka, gidado zai kawo maka kaya ka saka da abinci kaci.


Toh kawai Al'ameen yace, yana mikewa tsaye da taimakon gidado ya fitoh a d'akin, kasance war dakin a hanyar kofar gidane , yasa yana fita yaga inna zaune tana gyaran zogale a tsakar gida, ina kwana?


Mtswww kawai inna Talatu tayi, tacigaba da abinda take ba tare da tabi takan gaisuwar saba.


Sanin halinta yasa gidado d'aukowa Al'ameen buta ya mika masa,shima Al'ameen dayake ya saba ganin abinda yafi na inna yasa bai wani damu ba, don duk Abinda zata masa lafilane in an had'a da rashin mutuncin gidan Adara.


gidado dakinsa ya shiga, kaya ya d'auko kala uku na fulani, sai nono da matar sa ta dama,ya had'a da dambu ya kaima Al'ameen a d'aki.


Bayan muhammad ya idar da sallah, wanka yayi bayan gidado ya iba masa ruwa a rijiya, ya chanja kaya, abincin ya bude kasa cin dambu yayi, nono kawai yasha, kad'an duk yabi ya shiga damuwa halinda sumayya da kanwar sa zasu shiga a rashin sa.


Sai bayan muhammad ya gama kimtsawa, kafun ya mike a hankali ya fitoh a d'akin bappa ne da gidado zaune a gindin bishiya, sai inna dake zaune a gefen su rike da fifita, karasowa yayi kusa dasu bappa a hankali, ya zauna a gefen su,duk da bansan tayaya nazo nan ba, amma dai nasan taimako na kukayi, nagode Allah ya saka da Alkhar, yace musu.


Ameeen,bappa da gidado har suna had'a baki suka amsa masa, sai kuma bappa ya kara tambayar sa, yaro garin yaya babba dakai har ruwa ya jaka?koh wani abinne ya faru dakai?


Shiga ruwan nayi zan sha, shine yajani, ya bashi Amsa.


Kai bako ne hala koh?don ruwan mu bayason bako.


Eh ni ban taba zuwa kauyen nan ba, baba


A ina kake?


Jalingo.


Jalingo kuma?inane haka, nidai bantaba jin sunan wannan gari ba, gidado yace da mamaki.


Bappa ma kara tambayar sa yayi inane jalingo kuma?


Muhammad kam sai yanzun ya tuma ashe bafa a kasar NIGERIA yake ba, yanzun toh Amma a ina yake haka, gadai mutane kamar na kasan sa fulanine musujin yare, wani kasane wannan, dan uwa?yayi maganar yana kallon gidado.


Gidado ya juya ya kalli bappa, shima bappan gidadon ya kalla suka had'a ido, sannan suka sake maida kallonsa kan muhammad, Cameroun.


A hankali yace musu ba'a kasar nan nake ba.


Kamar ya ba'a kasar nan kake ba?


Eh baba ba'a nan nake ba, a nigeria nake.


Nigeria, a ta ina kasar take? gidado ya tambaya da mamaki, don shikam baisan wata kasa nigeria ba, murmuahi bappa yayi yana kallon gidado, nigeria ai na sha zuwa, lokacin da muke cikin ganiyar kuruciya, har kasar muke zuwa kiwo tun daga Cameroun, har nigeria.


Wai bappa kasan kasar ne?inji gidado


Sosai ma nasan jahohin kasar, kai yaro a wani jaha kake?ya tambaye muhammad.


Taraba, ya basa Amsa yana kallon inna dake ta zabga masa harara tun daga inda take.


Allah sarki ai naje jaharma dashi, da gombe harda Adamawa, amma tunda kace a taraba kake kenan ta Gimbu ka shigo kasar cameroun?


Nima ban sani ba baba kawoni akayi.


Kamar ya yaro aka kawo ka, ban gane ba?


Shuru muahmmad yayi yama rasa ta ina zai fara.


Dafasa bappa yayi, kaga yaro ka fad'amin gaskiya, mu bazamu cutar dakai ba sannan haka muke fata agunka.


A hankali muhammad ya gyara zaman sa, ya fara bawa bappa da gidado labarin sa, har Auren sa da sumayya, da batar mahaifin su , har zuwa sanadin zuwarsa kasar nan, ya kara dacewa, sannan baba ina so na koma kasata koh don ganin halinda na tafi nabar mai d'akina a ciki.


A hankali bappa ya d'aga ido yakalli muhammad da kyau, ya sunan ka?


Muhammad Amma anfi sanina da Al'ameen.


Ashe sunan baba nane dakai, Zan fad'a maka gaskiya, akwai asiri a jikin ka har yanzun, sanan bakai aka ma asirin ba, an ma wasu asirin ne a jikin ka, anyi amfani da tauraren ka anyi asiri da kai, dole kana bukatar ka zauna ka nutsu, komawar ka gida yanzun matsala ne duba da abinda mutanen da suka kawo ka sukace, zaka bata musu aiki sanan kwangilar kisan kai aka basu, watoh kaga yanzun an daina Amfani da boka, da zahiri ake son ganin bayanka, ka zauna anan zan maka jinya da izinin Allah duk asirin dake jikin ka zai karye, wa'inda akama asirin ma zasu dawo hayyacin su, sannan zan taimaka maka da maganin kariya babu wani asiri da zai sake cinka bi'izinillah,kaima ka dage da Addu'oin neman tsari a wajen Allah, don yawan ibadan ka shiyasa har yanzun basu gama cin nasara akanka ba.


Shuru muhammad yayi amma sam ransa baiso ba, baiso hakan ba, yaso ace ayau innan ya koma gare ta, yaje yaga halinda take ciki ya kalleta da idanun sa, yaga wani irin farin ciki zatayi yau idan taga yana kallo, amma babu hali, sannan maganar mutumin nan bai kwanta masa ba, don shi ba mutum bane mai bin maganganu irin wannan na magani magani, aa tsari tsarin nan sam basu ransa.


Ka kwantar da hankalin ka babana, ni magani zan baka don nema maka lafiya, sannan mu sama ma wasu lafiya, domin samun lafiyar ka, warakan wasu ne, karkaji kokonto ni bana aiki da Aljanu koh wani shirka, magani nake bayarwa wanda Alllah ya hure mini sani akan ganyen itatuwa da sassaken su, tunda na ganka nasan Akwai sihiri a jikin ka, Amma inga sarkan da mahaifinka ya baka.


Hannu yasa ya kunce sarkan ya mikawa bappa, kurawa sarkan ido yayi nad'an wani lokaci sai kuma ya mike ya dauko ruwa a kwarya ya saka sarkan, ya zuba magani kad'awa yayi sai kawai ruwan maganin ya zama fari tas, wannan sarka d'ayan biyu ne Amma bazance maka kome ba Akansa, bappa yace.


Shuru Al'ameen yayi sai kuma ya gyada kai a hankali alamun ya amince,ya karbi sarkan ya makala, kamar kwana nawa ne zamuyi baba?


Murmushi bappa yayi sai kuma yace,ka kirani da bappa haka yarana ke kirana, sannan maganin ka bana kwana bane, na wata ne.


Kamar wata nawa kenan bappa?


Kamar wata uku, kuma kasan inka gama magani dole sai kunje cikin cameroun asai da shanu mu baka kudin mota.


Shuru muhammad yayi kamar ya fashe da kuka, yanzun har wata uku yana zaune a wannan kauyen, ba tare da sumayya ba ai sai kewan ta ya kashe sa, tun lokacin sa baiyi ba, toh nagode bappa Allah ya saka,mikewa yayi a hankali ya nufi kofar da yake hango fili ta waje , alamu dai kofar gida kenan.


ina zaka?Gidado daya mike yake tambayar sa don ya d'auka tafiya zaiyi


Waje nake son fita, ya basa Amsa.


Kanason zaga gari ne?


Eh ina so, yace cikin ransa yana dariya wai wannan kauye ne gari.


Toh jirani barana kunce shanu mu fita kiwo, saina nununa maka wajaje, yace yana tafiya tirkensu domin kunce shanun.


Da sauri Al'ameen ya biyo sa wai zai tayasa kuncewa, ai yana saka hannu a kafar shanun da sauri yaja baya, ganin yanda shanun ta hafto kamar zata tunkudesa da kahon sa.


Dariya gidado yayi, kai kaja baya fa shanun nan saimu, yana maganar yana kunce su .


Matsawa muhammad yayi gefe yana kallon gidado yagama kunce su yana kad'asu yayi waje bayan ya karbi guzirin sa a wajen matar sa, muhammad na binsa a baya yana mamaki wai d'an yaron nan ne da mata.


A haka suke tafiya gidado sai hira yake masa, duk inda suka wuce saiya ringa masa bayani, ga gonan wane, ga shanun su wane, ga kogin kaza a haka har suka nausa daji, wuni sukayi suna yawo sosai Al'ameen ya gaji bayan gidado ya kunce boronsa daya rataya, abinci ne a ciki sai goran ruwa, bayan sunci ne suka kamo hanyar gida basu suka iso ba sai goshin mangari ba, suna isa suka samu har an kira mangariba da sauri sauri gidado ya d'aure shanun suka tafi masallaci.


Sosai jama'ar garin suke bin muhammad da kallo, ganinsa ras dashi kamar ba gawan jiya ba, gashi kyakkyawar bafulatani, suna idar da sallah, gida suka koma suna shiga muhammad yaga yarinyar d'azun da safe zaune a gefe tana cin tuwo, kai koh d'an kwali babu.


d'aga ido tayi ta kalli Al'ameen da sauri kuma ta mike, cikin fullaci tace, laa bako kaine ka tashi, ya jikin naka yau sai sauri nake nono na ya kare na dawo gida, Amma bai kare da wuri ba.


Shuru Al'ameen yayi baiyi magana ba, yana nazarin yarinyar kenan khadijar sa zatafi yarinyar nan a yanzun, Allah sarki yaci burin ganin su duk da bai taba tunanin ganin sa zai dawo ba, Amma yaso ganin sa na farko yafara dasu, ganin yanda ta bata fuska alamu dai bataji dadin shurun da ya mata ba, gashi gidado na kusa dashi, yasa a hankali yace eh na tashi.


Washe baki tayi sai kuma da sauri tace, nakai maka abincin ka d'aki bappa yace na kai.


Kai ya fahimce yarinyar nan yar damuwace, fadi ba'a tambaye taba, kamar ya sata, rijiyar dake tsakar gidan ya nufa jan ruwa yayi a kwalla ya wuce bandaki, bayan ya d'auko kayan da zaisa, bai wani jimaba ya fitoh Alwalan isha yayi jin ana kiran sallah ya wuce masallaci.


Bayan an idar da sallan gida ya nufa a hankali ya shige dakin da aka ware masa, zama yayi akan gadon kaba da aka saka A dakin, ya buga tagumi abin duniya ya dame sa, tunanin matarsa kawai yake, adaidai wannan lokacin ne suke cin abinci, shin itama abincin take cine koh me take yanzun?


Gidado ne ya shigo dakin da sallama.


Amsa masa muhammad yayi, tare da gyara zaman sa.


Har yanxun bakaci abincin ba tsoho?


Da mamaki muhammad ke kallon sa, tsoho kuma?


Eh man tunda ka haifi bappa aikai tsohone, yace yana aje agushin hannunsa.


Murmushi muhammad yayi sai yanzun ya tuna,

Please Login or Register in order to submit comment