Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

khadija


Eh Aunty sa'a, khadija tace


Yauwa Daman nazone akan in ba damuwa,Koh Asma'u zata samu lalle inda halima harda mu,don jiya na turo kawayen ta sunce Wai bazakiyi ba shiyasa nazo da kaina,


"Gaskiya hajiya ni Ina da aure bazan iyya zuwa in ma amarya lalle ba,tunda Henna day ne yau"


Habba wallahih ba kome zamu zo har gida ki Mana itama Amaryar zatazo saiki mata,tunda ba'a d'aura aure ba kuma gida baki da hanci


"Shikinan hajiya"


Yauwa nace zata iyya zuwa yanzun don anjima akwai Algaita da yamma,saiki Mata kwalliya ma duka


"Toh hajiya gaskiya bazaku samu lalle yauba don indai lallen Amarya ne Dole za'a jima ga kwalliya duka"


Saiki Mana gobe da safe,tunda Walima ne kwalliya kawai zaki Mana da yamma saiki Mana lalle da safe,


"Ku nawa ne"?


Mu bakwai Zaki ma lalle da Amarya 8 Amma bansan kawayen ta mutun nawa ba


"Ok za'a ma Amarya lalle da kwalliya yau"In yaso ku sai amuku gobe hannu bibiyu sai kwalliyar walima,saboda time"Amma banda kawayen don bazasu samu ba


Ba damuwa Daman booking mukayi har Agama bikin zakina Mana kwalliya in ba damuwa


"Ok shikinan"


Nawane kudin ki?


"Hajiya kwalliyar Amarya kashi biyu ne ana heavy make-up a dinner, bud'an Kai, kamu sai light make-up anayi a Walima, Algaita, Arab night
Kinga kenan light make-up Zan mata yau"


"Kudin kwalliyar yau 5k ne, lalle 10k na Amarya"


"Kwalliyar ku 3k ne Koh wani mutum D'aya"


Ok na gobe fa ?


"Lallen ku na gobe hannu bibiyu ne Kuma ja da baki za'a muku a hannun dubu D'aya da d'ari biyar ne, in da lalle na Kuma 2k Koh wani mutum D'aya"


Ok tace ta hada lissafi ta bani kudin a hannun,gashe kudin kwalliyar Amarya da lallen ta nayau da kwalliyar mu sai na lallen mu na gobe,in mukazo kwalliyar walima sai muyi lissafi harda na dinner,tace tana mamakin wayewar Sumayya,
da akace mata MATAR MAKAHO ne ta d'auka Koh zatazo taga bagidajiya sai taga hatta MAKAHO ma bazaka zata baya gani ba


Ok hajiya" nace Ina karban kudin kirgawa nayi Naga ya cika,hajiya watoh harda kudin lalle Kika bayar kenan"?


Eh zuwa kawai zamuyi goben,Amma Amarya na zuwa da lallen ta,kinsan ana kawo kayan rufi da lallen Amarya ?


"Gaskiya ne shikenan saina ganku anjiman"


Allah yasa tace tana Mike wa ta tafi


Khadija Kam da Al'ameen mutuwar tsaye sukayi,Wai kwalliyar da ake gogiwa shine za'a biya dubu biyar ayi ai gwara ma lalle zaiyi sati..


Aunty yanzun duk wannan kudin na lalle ne kawai da kitso? khadija ta tambaye Sumayya


"Kai Khadija ba abin yayi bane,Kuma kayan kwalliyar ma tsadane dashi"


Ikon Allah,tace


"Kinga khadija tashi maza kije kasuwa ki mini sayayyan lalle sai ki sai Mana semolina yau tuwo zanyi na gaji da shinkafan nan na fada Ina Mika Mata 10k ki sai Mana harda kaji biyu a gyara Miki a kasuwan,ki hada mana da kayan Miya harda su vegetable"


Toh Aunty tace tana karban kudin


Al'ameen Kam baice kome ba ,Yana shanya kayanda yawanke


Khadija na fita Koh minutes uku batayi ba mukaji Karan faduwa timmm sai muryar Khadija data k'wala Kara,irin na azabar nan,dagani harshi da gudu Muka nufi kofar fita a shashen mu, ganin tsabar rudewa Bai gane hanyar kofa ba yasa na Kama Masa hannu na Masa jagora Muka fitoh,


me Zan gani khadija ce a..........







πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page 2️⃣8️⃣&2️⃣9️⃣
Khadija ce a zube a kasa cikin ruwan cab'alin rijiya,salame na ruwan cikin ta,ta hakikance sai jibganta take


Sake hannun yayan khadija nayi Da wani irin gudu nayi Kan salame,don na fahimci Yan gidan nan in har baka koma irinsu ba zasu kasheka,yarinya sa'ar khadija Amma khadija ta sake jiki tana dukanta Koh martani Bata mayarwa sai k'okarin Kare kanta,kafun na Isa ba zatoh ba tsammani sai kawai Naga Iro ya kwashe salame da kafa daga Kan khadija yayi ball da ita sai da ta zube a Gefen rijiya bakin ta ya sare simintin rijiya,kafun kace me tuni ya rufe salame da duka sai a lokacin Yan gidan suka firfito,Abu kamar Wasa fad'a ya zama babba,don fadan yanzun Kam mutane sunkai biyar suke dambe,kama khadija nayi wance tunda Iro yayi ball da salame take gefe tana kuka duk jikinta sai rawa yake, "khadija tashi mu shiga kofata sannu"


Mikewa tayi a hankali,suka nufi kofar shashensu


Al'ameen Kam Yana tsaya Kamar andasa sa don baya gane kome tsabar yanda surutai da koke koke ke tashi a tsakar gidan,sai raba ido yake kawai


Muna zuwa saitin inda yake hannu kawai nasa na Kama NASA Muka shiga cikin kofar tare,
Sake hannunsa nayi,
Ruwa na iba na Kai Mata band'aki na Kama hannunta muka shiga, kanta na wanke Mata kafun na fita na barta tayi wanka
Kaya na makala Mata a jikin kofar band'akin,
Tana fitowa.


D'aki Muka shiga zaunar da ita nayi da sauri na d'auko D'an kwalina na d'aura Mata akanta dake ta zubar da jini"khadija meya hadaku meya faru?


Wallahih Aunty Ina fitowa kofarki kawai nazo wuce gindin rijiya,Daman salame na iban ruwa kawai ta kwashi kafafuna na zube shine tahau kaina tana dukana,kallifa Aunty ta fasamin Kai,ta fad'a tana Kara karfin kukanta


"Kiye Shuru khadija,share hawayen ki yanzun za'a bi Miki hakkinki wallahih in sunsan wata Basu San wata ba" nace Ina duba inda na aje wayata


In Raina dubune yau ya baci na gaji da bala'in Yan gidan nan da Talaucin da muke ciki zamuji Koh da tashin hankali'wayana na d'auka tunawa da nayi,da wani school mate nawa lokacin da na shiga jami'a shi Kuma Yana final year insa,yanzun police ne yana da babban mukami a hukuma, muna mutunci sosai kamar yan uwa danayi aure ne dai bamu sake magana dashi ba.


Me zakiye Sumayya? Al'ameen dake zaune a kujira yayi tagumi ya tambaye ta


"Mataki Zan d'auka"


Wani irin mataki?


Akwai Wanda Zan Kira wallahih Koh tantama banayi daga gidan nan direct sai prison Koh station bazata shiga ba Kuma sai naso za'a bada belin ta".


Wa Zaki Kira?


"Wani friend Ina ne"


Toh wallahih ba'a gidan nan ba


"Ban gane ba'a gidan nan ba kenan kana nufin abarsu suci bulus kenan kaga yanda suka fasawa yarinya Kai kace a barsu"


Ina dai kanwata aka fasawa Kuma nace bana bukatar ki d'auki mataki


"Ok nuna mini kake khadija ba kanwata ba koh"fine shikenan gaka ga Yan gidan naku,Daman nice bare"nace Ina aje wayata na fita waje sosai maganar Al'ameen tamin zafi Wai kanwarsa Kuma yace baya bukatar mataki,watoh ba ruwana kenan a maganar


Al'ameen Kam harga Allah Bai Fad'a,don wani abuba kawai ya fad'ane don ta janye maganar rufe salame,baisan maganar zai Mata zafi harta fassarasa wani iri ba


Khadija Kam sosai taji Bata kyauta ba a sanadin ta ma'aurata sun samu sabani,mikewa tayi ta fita waje,
wajen da Sumayya ke zaune ta karasa


Aunty bara naje kasuwar


"Khadija Wai kina nufin kudin nan na hannunki"?
Ni na d'auka ma Koh kin yasar dashine tuntuni"


Ah ah Aunty Daman a bakin zanina na soke Kuma Allah ya taimakeni Bai fad' ba


"Ok kibar zuwa cefenen"nace Ina karban kudin hannunta


Ah ah Aunty maganar Yan lallen fa,don Allah Aunty karki fasa lallen nan,Akan abinda ya faru.


"Ah ah khadija rike 1k innan kije chemist a Miki dressed in wajen Naga har yanzun jini Bai tsaya ba"


Toh Aunty na gode tace tana mikewa zata fita


Khadija tsaya muje na rakaki, Sumayya ki kawo cefenen Inna rakata chemist sai na wuce kasuwar, Al'ameen yace


Kala bance Masa ba don haushin sa nakeji sosai,hakurin sa yayi yawa shiyasa ake cutar sa kullum




Aunty Yaya na magana Wai zaije kasuwan,


"Ka barshi kawai gobe Zan aiki Yan lallen suje kasuwa su sai mini abin hadin"


Toh Aunty ki basa kudin cefenen sai ya sayo muku,ya iyya zuwa kasuwa, khadija tace cikin rashin Jin Dadi ganin yanda na Had'awa yayanta fuska




"Ungo"na Mika Masa 6k


Matsowa yayi Yana lalube ya karbi kudin a hannuna


Me da me Zan Saya?


"Ka tamabaye khadija na Mata lissafi "


Ok yace cikin sanyin jiki don wallahih Bai d'auka maganar zatayi zafi haka ba


Suna kokarin fita Asma'u na shigowa da kawayen ta,suka gaisa da Al'ameen kafun suka shigo,khadija kuma suka fita


Shimfid'a musu darduma nayi,suka zazzauna


Tashi nayi naje na chanja kaya,na manna Gam a faranti,na kwaba lalle,Muka fara


Khadija ta dawo lokacin kusan karfe 10
"khadija ki shige d'aki kije ki kwanta Naga an kawo NEPA ki huta kinji"nace Mata Ina kallon kanta da aka mannawa plaster


Toh Aunty tace tana shigewa d'akin, kwanciya tayi a kujira,banci ya d'auke ta


Al'ameen Kam kasuwa ya wuce yaje yayi sayayan kayan abinci,Amma Sam yau Baya cikin walwala tunda suka D'an samu sabani da Sumayya,don shi Sam bayason yayi abinda zai bawa wani haushi harya kullace sa abin damunsa yake


Yan matan sunata Hira,inama Amarya lalle,saiga Al'ameen ya dawo da laidodi a hannunsa na sayayyan kasuwa,mikewa nayi na karbi laidan gudun kar na tozartashi a gaban su,kitchen na shiga da laidodin shima bayana yabi


Yan Mata Kam sai ido suke bin MAKAHO da MATARSA suna mamaki


Muna shiga kitchen in,na aje laidodin


Sumayya Naga Yan sana'ar sunzo Koh Zaki kawo na girka Mana abincin? in yaso


"Kai bazaka fita bane"?


Zan fita Amma sai bayan azahar


"Toh ka iyya girkine? koh da wani idon zaka girka Mana abinci muci"?


Eh na iyya girki,sai ki jera mini Abubuwan da Zan girka Zan iyya


"Bana bukata"nace Ina Shirin fita


Jin Amsar da ta Bashi ya tabbatar har yanzun haushi takeji,hannu yasa a hankali ya rikota Jin zata fita a kitchen in


"Ka sakeni"nace ba Wasa a muryata


Sumayya kiye hakuri in abinda na fada Bai Miki Dadi ba


"Ka sakeni nace maka"


Am sorry


"Ka sakeni"


Baki hakura ba?


"Ka sakeni"


Toh innaki fa,ba Matata na rike ba


"Matar ka ai da Ina da wannan matsayin da gaske da bazaka nuna mini banda matsayi agun khadija ba"


Amma ba nace kiye hakuri ba,yace Yana jawota jikinsa


"Nima ai bance maka naji haushi ba"


Amma gashe sai fushi kike


Haka dai Kai kake gani,nikam sakeni Rana yayi bamu karasa lalle ba


Bana gani sai dai ji


"Oho maka dai"


Mana dai,ba ni kadai ba


"Toh sakeni Mana",nace Ina banbare jikina a nasa


Sumayya abinda yasa Kika ga naki ki d'auki mataki,da hukuma toh a gidan nan Babu Mai tsoron station Koh prison don ba bako bane agunsu, bare ya saka musu tsoro don kinsa an rufe salame,wata fitinar kika kunna,zaman gidan nan sai ya gagare mu


"Kai kake tsoron fitina bani ba' akan gaskiya na Koh Ina zanje"


In Miki girkin?yace Yana kauda maganar


"Ka bare Zan girka"


Toh shikinan,yace Yana saketa,


Tsayawa nayi ya rigani fita a kitchen in,
Ya Kama hanyar kofar fita a shashen mu


Nima fita nayi,"am please bara na d'aura Abinci, Rana yayi sai nazo mu karasa"


Aunty bara na d'aura miki,wata Yan Mata a cikinsu tace


"Ah ah ki bare kawai"nace Ina tunanin karfa Bata iyya girki ba ta Bata mini kaji a banza


Kai Aunty Koh dai kina tunanin ban iyya girki bane?


Ba haka bane,Daman Ina tunanin karna takura Miki ne,Amma tunda kina sonyi shikenan,ki tuka semo laida babban duka,


Kitchen ta shiga
ni Kuma d'aki na shiga naje na leka khadija har lokacin bacci take


Sai azahar na kammala lallen Amarya,na tashe khadija mukayi sallah abincin da farida kawai Amarya ta girka na zubawa yayan Khadija nasa, na zuba na Daren mu, sauran na zuba ma kawayen, na ibawa Amarya na zuba Mana da khadija,sosai Tuwon yayi Dadi,bamu Gama ciba aka turo yara da kulolin Abinci daga gidansu Amarya shinkafa muka dad'a,
yaran na baiwa na yayan Khadija su Kai masa


Ganin da sauran lokaci yasa nama farida lalle (wance tamin girki)




Sai la'asar Asma'u tayi wanka sosai na zuba Mata light make-up tayi kyau Kamar me,ganin kawayen nata d'aukar ta hoto yasa Nima na fitar da wayata,na d'ad'auki hotonan lallen ta da kwalliyar da na Mata duk da hoto nason gida Mai kyau Amma wanka na gyara hoto ma ba gida kawai ba




************
Bayan tafiyar Amarya da kawayen ta, wanke wanke nayi na share kofar don yayi kaca kace,kowa yasan gidan Mai lalle in ta Tara customers,yanda yake baci


Wanka nayi,donna gaji sosai yau innan,vest nasa na d'aura zani don ba kowa a kofar nawa khadija ma ta tafi gida,don yau ba zuwa program Kai ya fashe


Bayan sallar mangariba ya dawo Kamar kullum wanka yayi mukaci Tuwon da farida ta dafa Mana da rana




Bayan sallan isha'i yau Koh jiran ya dawo masallaci banyi ba na kwanta don gabaki d'aya bacci nakeji ba kad'an ba ga gajiya sosai.


Yana dawowa ya tarar tayi bacci shima gadon ya hau don tabbas yau yasan ta gaji,tabata yayi yaji alamun bacci take,a hankali ya cire mata vest in jikinta daga ita sai wandon bacci,shima kayansa ya cire dagashi sai guntun wando a hankali ya rumgumeta,kome a hankali yake gudun karya ta tashi,sosai yaji wani irin yanayi Mai matukar shauki a tare dashe,amam haka yake dannewa,har bacci ya dauke sa




Misalin karfe 3 na asuba kamar a mafarki naji ana tattaba min kirji da sauri na bude ido,tashi nayi na zauna jina ba riga,sake taba jikina nayi don na tabbatar Aiko da gasken bani da riga,


"Wai meyasa kwana biyun nan ka chanja ne kanamin abinda ranka yake so"?


Mutum da halaliyarsa, ya Bata Amsa Kamar Wanda tama Dole




"Ka tashi mini a wajen kwanciya"


Ina kenan?


"Gado"


Naki, gaskiya yanzun bazanna kwana ni kadai ba alhalin Ina da mata.


"Don Allah nikam ka tashi, kaga yanzun ma Banga rigata ba ga d'akin duhu"


Saiki kwana haka


"Akan wani dalili Zan kwana ba riga,Kuma karka sake ciremin riga in Ina bacci banaso"


Inna cire fa?


"Au tamabaya ma kake sai me?


Eh tambaya nayi


"ka Dameni sai surutu kake sani tsakar dare"


Wani dare ai na yau ya wuce sai dai na gobe


"Ka tashi nace"


Naki


"sauka zanyi na bar maka d'akin ma in baka sauka ba"


Toh na hanaki ne


Mikewa nayi na sauka akan gadon nayi hanyar kofa Koh riga ban dashi,


Ba riga Zaki fita waje?


"Ai baka fini ido ba"nace Ina kokarin bude d'aki, kawai ji nayi y...........


*Aye manage in page bani da charge*






πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page3️⃣0️⃣&3️⃣1️⃣
Ji kawai nayi ya rumgume ni ta baya,
zare ido nayi jinsa shima ba riga,mannani yayi da jikin kofar shi koma ya rumgume ni sosai ya d'aura kansa a kafad'ata


"Wai menene haka don Allah" ?


Dadi ne,ya Bata Amsa


"Dad'au matau"


Jin Amsar da ta Bashi yasa ya juyo da ita da karbi ya rungume ta


Ware ido nayi jina sukutum a kirjinsa dukan mu ba riga


"Wayyo Allah meye haka"


Mele,shima ya Rama


"Nikam.ka sakeni"


Bakinsu ya hada,a hankali yake kissing in lips nata na sama


Bansan garin Yaya ba Koh yaushe ba na tsinci kaina da Kama lips nashi na kasa Nima na shiga tsotsa


Jin ta Kama Masa lips yasa a hankali ya zame bakinsa cikin nata,ai da sauri yaji ta kamo kansa ta sake maisa bakinsa cikin nata


Sosai suka shiga farantawa junan su Rai ,


ba zatoh Koh tsammani muka zube a kasan cafet,nice a sama shi koma a kasa,


da sauri ya birkitota kasa Yana lalube da D'an kokarinsa zai zame Mata wandon baccin da ke jikinta


Da sauri na Kama hannunsa Jin aika aikan da yake so yayi


Don Allah ki bari musamu nutsuwa


"Nidai wallahih ah ah"


Please kinji


Kokarin mikewa na fara a jikinsa,


Da sauri ya kamota,Ina Zaki


"Anafa Kiran sallah"


Sakinta yayi Jin da gaske Kiran Assalatu ake


Mikewa nayi a hankali daga jikinsa Jin ya sake ni,"d'akin ba haske fa"

Ki kunna glop Mana


"Bana gani"


Ok bara na lalubo glop in


"Toh,Ina rigana"?


Bara na kunna wutan sai ki duba,yace Yana mikewa daga kasan cafet


Mikewa yayi Yana lalube ya Isa wajen makunnen NEPA ya kunna


D'akin ya gauraye da haske,da sauri na rufe kirjina da hannu sai koma nayi tsaki tunawa da nayi bama gani yake ba


Menene kike tsaki kuma?


"Banga rigana ba"


Riga Koh vest?


"Oho"


Wai kikam wace irin matane Mai tsewa


"Green in Mata ka aura"


Toh Green Sumayya,mu fita kar ashiga sallah?


"Kai ka fita Mana Koh na d'aureka ne"


Toh Green sumy


Lalle mutumin nan ya Raina mini wayo,ji kawai nayi ya kamo mini hannu Yana kokarin fita Dani a d'akin cikin lalube


"Ban saka rigaba ka sakeni Mana pls"


Sakin ta yayi Jin Wai Bata da rigan da gaske


Bayan fitar shi rigana na d'auka na fitoh Jin harya kammala Alwala ya wuce masallaci


Bayan idar da sallah dukan mu bacci muka koma


Misalin karfe 7:00 na safe aka doka Mana sallama a kofar d'aki,bude ido nayi a hankali ganin Yana kokarin sauka a gadon yasa na gyara kwanciya


Amsa musu yayi ya zura jallabiyar sa ya fitoh,


Ina kwana yayan Khadija?


Lafiya Alhamdulillah


Gun Aunty Sumayya mukazo,Yan matan sukace


Ok,bara na kirata yace Yana komawa d'akin


Hawa gadon yayi,ya yaye blanket inda ta rufu


"Menene"?


Baki kikaye,Kamar Yan lallen ne fa


"Gaskiya bazan tashi ba suje su dawo anjima"


Ah ah Sumayya wulakanci ba kyau ki lallaba dai ki tashi kinji Green sumy


"Wallahih Inka sake fad'amin sunan nan Mai rabani da Kai sai Allah"


Me Zaki mini ai Babu abinda Zaki mini sai abinda Allah yaso


"Hmm" kawai nace na mike,fitowa nayi na shimfid'a musu darduma muka gaisa Yan matane guda biyu Amma ba kawaye bane,
"ban fa Saya lalle jiya ba bansamu D'an aika ba gashi 8:00 ake bude kasuwa Koh zaku karba kuje ku sayo"?


Eh Daman mu biyu mukace bara muzo kafun a Gama Mana kafun sauran su karaso,ba damuwa a bamu kudin bara muje mu sayo in


"Ok bara na kawo muku kudin"dakin na shiga na d'auko musu kudin,suna fita wanka nayi na kimtsa kofata yayan Khadija ya ibo Mana ruwa,


Shinkafa da wake dafa duka na dafa Mana direct harda na Rana


Bayan mun karya fita yayi, ni Kuma muka fara lalle,
Sai kusan 3 na karasawa matan lallen su dukansu su bakwai kowa hannu hannu na Masa ja da baki,sai kwalliyar walima


Gaskiya yauma ba laifi na damka kudi Mai tsoka sosai..


Naso.muyi cefene Amma yau khadija batazo ba ni koma ba fita nake ba bare na aiki yaro


Yayan Khadija Kam Yana fita yaje ya bude mangoron sa duk sun rube haka ya zubar dasu don Koh ya bude ba Saya za'a yi ba haka yayita zama har yamma don yasan tabbas Sumayya zata sama musu na abinci Amma yanajin kunya ace kullum ita ke ciyar dashi


Haka yayita zama sai mangari ba ya mike bayan yaje masallaci ya kamo hanyar gida jiki a sabule


Bayan sallar mangari ba ruwa na Ina na shiga wanka


Yana shiga gidan da sallama ya shigo kofar Jin shuru Bata Amsa ba ya zata Koh tana d'aki ne,ruwa ya Iba ya shiga ban d'akin


Goga soso nake a zaune kawai naji mutum ya shigo bayan gidan


A matukar tsorace na kwana Kara,"wayyooo"


Shikam zuciya D'aya ya shiga bandakin Bai d'auka tana ciki ba shiyasa ihun yazo Masa unexpected,yasa ya gigice, Sam Bai d'auka dalilin shigarsa bane yasata ihun,d'auka yayi Koh wani mummunan abune ya same ta


Subhanallah Sumayya lafiya? yade?
yace Yana matsowa inda yaji ihun nata


"Wallahih Inka zo inda nake saina kwara maka ruwan nan",nace cikin tsawa Ina d'aukar bokatin ruwan wanka na in,damuwa na kawai na ja towel inda na makala a saman kofar band'akin,na d'aura


Sai yanzun ya gane dalilin ihun nata,manna Mata hauka kawai yayi ya Kama cire riga


"Wallahi ka fita a toilet innan na ratse Zan kwara maka ruwan nan",duk tabi ta rikice


Ikon Allah waini idone Dani bare na kalli abinda kike boye wan


Kuturu,kawai nace,Ina daga boket in ruwan ganin Yana matsowa inda nake


Jii kawai yayi shaaaaaaaa Sumayya ta kwarara Masa ruwa,Bai d'auka da gaske take zata kwara Masa ruwan ba,


Nikam ganin Yana ta faman sharte ruwan fuskar sa yasa,na ruga zanyi waje da gudu Koh Kaya bansa ba ,


Ai.jin gudunta yasa ya bita shima da gudun


Ina kokarin fita a band'akin kawai naji ya jawoni ciki, Allah yasa Ina kusa ta towel jawosa nayi a hannusa


Wallahih Sumayya baki Isa ba ki kwaramin ruwa Kuma ki.gudu


Ganin fa na shiga hannu,inda Allah yasoni ma na d'aura towel in"don Allah kayi hakuri yayan Khadija kuskure ne"


Kuskure ai baki isaba kinji na rantse


Kuka na fara ganinsa in yaci serious,Babu Wasa a fuskarsa da gaske yake b barina zaiyi naci bulus ba
"To Kayi hakuri"


Naki,ke Inna Miki Abu ai baki hakura


"Wallahih inayi kaji yayan khadija"


Bazanfa hakura ba malama


To me koma Zan maka Koh dukana zakayi ne?


Ah ah wanka Zaki mini


"Wanka"😳?


Eh Kinga Daman ba gani nake ba kullum.bayana baya fita


"Nima ai bana ganin bayana kuma ni ban iyya ma manya wanka ba"


Ah ah kina kallo Mana,Kuma Zaki koya


"Wallahih ni banason irin abinnan, nace maka ka sakeni kanaji fa ana Kiran isha'i Kuma sai magana kake sani a bayan gida kasan ba kyau fa"


Tsakanin nida ke waya fara magana a ban d'akin nan tunda ba idone Dani ba, ba kallo Miki abin zanyi ba me na ihu harda kwara mini ruwaπŸ€₯


"Toh kayi hakuri kaji yayan Khadija wallahih mantawa nayi baka kallo"


Da gaske kina mantawa bana gani?


"Eh sosai ma,ai ba kowa.ke.ganinka yasan baka kallo ba"nace don ya barni


Ok wayo Zaki mini kenan harda wani yabona toh naki wayon in Kinga na barki kin fita toh kin zabi Daya a cikin ukun nan,
Koh ki wanke mini baya
Koh ki wanke mini Kai
Koh ki haske mini gemu


Lallai mutumin nan yaga wajen baccina nice ma Zan wanke Masa baya Kai Koh aski,


Toh Zan maka aski Amma sai gobe kasan yanzun dare ne bazaiyi kyau ba gashi ba NEPA Kai Kuma bakada shaver"


Kinyi Alkawari Zaki aske mini gobe?


"Eh"


Toh wanke mini


"Toh,ka sake mini hannu Mana saika zauna na wanke maka"


Na sakeki ki gudu


"Allah bazan gudu ba"


Ban yarda ba


Yace Yana Jan hannuta,ya zauna akan kujiran hannunsa na rike da nata


"Toh a hakan Zan wanke maka Kai kana rike da hannuna"


Ai Inna sakeki nasan guduwa zakiye


"Allah bazan guduba"


Toh tunda kikace Allah na sakeki,yace Yana sake Mata hannu


"Ina abin wanke Kai in"?


Gashe yace Yasa hannu a k'wandon soson nasa ya d'auko guntun soda,gashi nan


"Kana nufin da soda Zan wanke maka Kai"?


Eh man ba Yana kunfa da cire datti ba


"Uhmm Ina zuwa",nace Ina kokarin nufar kofar band'akin


Kinye alkawari fa Zaki wanke mini,shine kike son gudu


"Abu Zan d'auko na dawo"


Toh yace Yana kokarin cire jikekken rigansa


Ina fita a band'akin na shiga d'aki bude akwatina nayi na d'auko Abubuwan wanke gashi, na Mata masu kyau da shaver,na dawo ban d'akin wayata na kunna na jinginasa da jikin gini matsowa nayi inda yake zaune daga shi Sai wando dogo na jeans


Rangwafawa nayi na fara wanke Masa gashinsa sosai na zuzzuba Masa Abubuwan wanke Kai gashinsa mai yawa irin na Fulani,sosai ya fita nasa Masa Abubuwan laushin gashi cikin Yan minutes gashinsa yayi masifar kyau, shaver da na d'auko na saka Masa a fuska zan aske Masa gemu


Ke sumayya ragewa fa zakiye ba askewa ba


"Na sani ai"nace Ina gyara Masa gashin gemun


Ina Gamawa nace NASA"ka duba Koh yayi"


Ina

Please Login or Register in order to submit comment