Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad'a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d'auko Aisha yayi ya Basu d'aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.


Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar
Al'ameen da kamila


An Kai Yusuf kotu,Amma bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.




Bayan Shari'a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci ma gagaransu yake Dole karatun su Al'ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba


Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d'aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d'aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,


Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma'aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu


Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.


Al'ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,


Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki


Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.


Tunda kamila.taga Al'ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al'ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu'amalar Al'ameen da kamila ba ganin Al'ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu


Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa




Yau ranan juma'a Al'ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al'ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta


Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka


Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d'aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan sun gaisa zainab ta d'aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad'i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta


Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d'auki maganar ba Amma na g'wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki


Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari


Gaskiyan abinda ya faru maman Al'ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha


Kamar ya bangane ba zainab?


Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had'a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al'ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta


Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.


Da gudu matar Bala dake tsaye tun d'azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti


Al'ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad'a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa'inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha


Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d'aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga


Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har zaurawa da samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa da kafa suka taka har gidan ubangari.


Zainab Kam gabaki d'aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d'auke, zainab Kam kin fad'a Mata gaskiya tayi


Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d'akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.


Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had'asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k'wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta ba Saida ta farfado da duka


Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day'an kallo, abinka da Friday kowa na gida,


bayan zuwan police kafun aka samu aka k'wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad'ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad'an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D'aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha?


Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad'a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d'auki kowa ba.


Ta bangaren Aisha Kam ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba'a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby.


Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad'an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari'a,


An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa


Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had'a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu'amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa


Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D'aya yake fad'a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama


Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi.


Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne


A hankali ta Kama hannun Al'ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al'ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine.


Al'ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba,


Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi


Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa


Kai muhammad ya gyad'a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa,


Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d'akin yaje Kiran Doctor


Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m...................







πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page 4️⃣2️⃣&4️⃣3️⃣
Aishan ADARA ne kwance Bata motse, cikin sauri Al'ameen ya Isa gareta yana kuka,don zuwa yanzun sun fara sanin ciwon kansu daga shi har Salim in,rungumar mahaifiyar sa yayi Yana kuka,don Allah Mami karki tafi ki barmu mami karki tafi ki barmu wayyo mamin mu yace Yana fashewa da kuka Salim Kam tsabar tashin hankali ciwon sa ne ya tashi,da sauri likitoti suka Kira baban Aisha dake waje a zaune yazo ya fitar da Al'ameen shi Kuma Salim Nurse suka d'aukesa zuwa wani gadon.


Sumayya dake kwance a kirjin Al'ameen kukane ya k'wace Mata hannu tasa ta Kara rungumar sa tana kuka,shikam gabaki d'aya jijiyoyin kansa sun mike sosai, kallo D'aya mutum zai Masa yasan ran maza ya tsogalu.


Kafun ya Kara bude baki, ji kawai sukaye kuka na tashi a bakin kofar d'akin su da sauri Sumayya ta mike hade da kamo hannun Al'ameen suka fitoh wajen tare


Khadija ce duke tana kuka fuskarta harta kumbura Alamu dai ta Dade tanayinsa kasa kasa sune dai basuji ba.


Yaya Daman gidan ADARA ba dangin mahaifin mu bane? Shiyasa suka nuna Mana launin fata,khadija ke tambayar yayan ta


Ah ah khadija ba saboda haka bane suke wulakanta mu dama can haka kaddarar Rayuwar mu take, kishare hawayen ki maza ki tafi gida


Ni wallahih Yaya inason Jin karashin labarin mu don Allah Yaya kaga ba Wanda ya taba ban Tarihin iyayen mu kullum na tambaye ka Koh Goggo sai kuce mu Marayu ne.


Al'ameen nada niyar magana Sumayya ta regasa"gaskiya ne khadija tayi girman da zata San abubuwanda suka shafeta especially irin wa'innan Tarihin"


Shikenan naji ana Kiran azahar bara nayi sallah Kuma kuyi Inna dawo saimu d'aura daga inda na tsaya,yace Yana Mai laluben buta


Da sauri Sumayya ta nufi butar dake zaune a Gefen baranda ta Mika Masa.


Alwala sukayi Sumayya kudi ta baiwa Al'ameen 1k in zai shigo gida yasai musu doya soyayye a bakin titi na 500


Ba musu ya karba ya fita
Bayan an idar da sallah Al'ameen doya yasai musu suka ci su ukun, duka a plate d'aya bayan Sumayya ta matsa musu don har lokacin khadija kuka take Kamar yau Abubuwan da suka shige ya faru.


Khadija inkin San kuka zakiyi toh Zaki bar gidan nan Banga amfanin kina kuka Kuma kice na cigaba da baki labarin ba kije ki samu wani damuwanne Koh me? Al'ameen ya fad'a ransa a bace,don shima dauriyane kawai


"Don Allah yayan khadija kayi Hakuri mutuwar iyaye Koh shikara d'arine zafine da shi"


Kayi hakuri Yaya,khadija tace tana share hawayen ta


Dukansu Basuci wani abin kirki ba Al'ameen Kam doya yanka biyu kawai yace khadija Kam ma tanaci Amai tayi saboda yanda take ajiyar zuciya


Bayan sun wanke hannunsu Al'ameen ya cigaba........
Bayan mutuwar Aisha Alhaji ubangari yaso d'aukar su Al'ameen ya rike, Amma baban Aisha ya murza ido yace ba dashi ba Koh kudi ubangari ya baiwa su Al'ameen sai an mayar Masa da kayansa sosai abubuwa suka ma ubangari yawa don yanzun Koh fita zainab Bata iyyawa,tana fita ana nunata .




Khadija Kam, kanwar Aisha aka bawa wance ta h Bata jima da haihuwa ba ta shayar da khadija, Amma khadija Taki karban nono Sam sai madara,ganin Amina Bata taba haihuwa ba yasa baba karban khadija ya Baiwa Amina Amana.


Al'ameen sunyi matukar kewar iyayensu Wanda Salim yafi saka abin a ransa shiyasa kullum cikin ciwo yake don yanzun dai Al'ameen wani abokin babane ya ajesa a shagonsa Yana sayar Masa da kayan marmari duk Rana Yana biyansa,da wannan yake Tarawa su had'a da baba akai Salim asibiti


Duk da wannan d'awainiyar Salim Bai hanasu karatu ba a hakan Alameda yake zuwa makarantan gwannati Dayake lokacin duniya sanyi kalau ba kamar yanzun ba da ake kashiwa makarantan gwannati kudi.


Relationship insu da kamila ba abinda ya ragu kullum saiya rakata gida kafun ya nufi unguwan su sosai Abu kamar Wasa shakuwarsu ta Kara karfin sosai saidai kamila Bata taba zuwa unguwan dasu Al'ameen suka koma ba shine dai Mai zuwa gunta,


Ubangari Kam zaman jalingo ya gagaresa don lafiyarsa Dana zainab sai a hankali don yanzun saita kwana ta wuni Bata cewa kome makarantar ma yanzun Bata zuwa sosai rayuwa ta musu kunci,ganin Halinda suke ciki, yasa matar ubangari Kiran Yan uwansa ta sanar dasu abinda ke faruwa,


Aiko a yanda suka tarar da ubangari da zainab don har an dakatar dashi agun aiki ganin Halinda yake ciki yasa Yan uwansa Saida gidan da suke ciki suka tatttarasu dashi da yaran NASA suka koma garinsu,Daman aikine ya kawo ubangari jalingo, Wannan kenan.


Khadija taci gaba da samun kulawa Awajen Amina Alhamdulillah yarinya ta fara girma ga wayo sai daifa Sam Bata da jiki Yar firet da ita kyakkyawa sosai don Kamar ta da Yusuf ne sak shiyasa ita da Al'ameen Koh baka sansuba ka gansu kaga jini d'aya Daman Salim ne baki a cikin su don da Aisha yake Kama.


Zaman su a gidan Adara Bai sauya musu hali ba, da yake abin a jininsu yake sanyi Hali da hakuri Amma fa Salim akwai zuciya mundin aka Bata Masa Rai in fa baisamu ya Rama ba saiya kwanta ciwo.


Bayan wasu shekaru mahaifin Aisha dai ya kwanta ciwon kafa Wanda Koh kofar gida baya iyya fita Sai an Taimaka masa,
don haka Abubuwa sun ma Al'ameen yawa ga kudin maganin Salim ga D'an abinda yake D'an kaima Yar kanwarsa khadija ga zaman shago ga zuwa makaranta ga soyayyar kamila wanda yake jinta har ransa.


Haka baban Aisha yayita fama da ciwo har Allah ya d'auke ransa Wanda kafun ya mutu Saida ya jaddada wa yaransa Koh bayan ransa Bai yarda Yusuf da Salim Subar gidan nan Adalilinsu ba d'akinsa da yake ya bar musu halak malak, baya cikin gado, Wannan shine kalmarsa ta karshe Kuma itace sukecin Albarkacinta har yanzun suna cikin gidan ADARA.




Bayan mutuwar baban Aisha rayuwa fa ta zamo ma su Al'ameen wani iri Sam a gidan Adara Babu Mai taimaka musu Koda ta abinda zasuci ne,Dole tasa Salim shima ya fad'a Tashar marmari Yana ma wasu jiran Kaya suna biyansa,saisu had'a da kudin Al'ameen su fidda na asibiti su fidda na abinci su fidda Wanda zasu baiwa Amina ta rage d'awainiyar khadija,hakan yasa Al'ameen aje karatunsa don ko yaje makarantan baya fahimtar kome tsabar damuwa,


Ganin ya aje karatunsa Salim ma yaki zuwa makaranta ba yanda baiyi dashi ba Amma yake ganin Al'ameen ya matsa Masa yasa sa cewa Al'ameen,Yaya moha Koh naje makaranta asaran kudi zakayi tayi Kaine yafi cancanta Kayi karatu Koh don kanwarmu ta samu rayuwa Mai inganci


Jin Amsar da Salim ya basa Saida Hankali Al'ameen ya tashe cikin damuwa yace Masa,salim ban gane ba kana nufin Kai Babu Amfanin karatun nakane, ka sani Koh Kaine Mai rabon Tallafawa Khadijan?


Ah ah Yaya Kaine ya dace Kaye karatu don Allah badon niba Yaya ka koma makaranta nikam bazanje ba karatun ya isheni haka ya karasa maganar da kuka


Rungumar sa Al'ameen yaye shima sai yaji hawaye nabin fuskarsa don yanzun sosai sukayi wayo girma ya fara zuwa musu Kuma labarin abinda ya faru ya riskesu,sosai suka kullace zainab a ransu Kuma har abada bazasu manta da fuskarta ba.


Haka ba yanda Al'ameen ya iyya ya koma makaranta don lokacin ma ya Shiga SSS class yayinda khadija ta Kai shiga primary school da Taimakon Goggo Amina aka sakata


Soyayya Kam tsakanin kamila da Al'ameen tayi girma don har abin yakai ga iyayensu sunsan kome,don kamila Kam Amfara zama Yan Mata kowa yazo da sunan soyayya haka zata koresa itakam fa sai Al'ameen,sosai mahaifyarta ta tsani wannan mu'amalar Al'ameen da kamila ganin ba'a San Asalin ubansa ba haka zuriyan maman sa Yan Ta'adane,gashi baida wani kakkauran sana'a Koh inda zaisaka kamila,Amma haka kamila ta nace sai shi,
duk yanda zata zugata Koh fad'a Mata abinda ya dace kamila bataji Bata gani itafa sai Al'ameen.


Hakan yasa baban kamila Kiran Al'ameen don ya yaba da Tarbiyan sa ga nutsuwa, yace Masa zai basa kamila Amma ya dage yayi karatu in waec nashi yayi kyau,ya d'auki d'awainiyar karasunsa harya kammala shi Kuma ya Masa Alkawarin xai basa kamila.


Jin hakan sosai muhammad ya Kara dagewa da neman na kansa da Kuma karatunsa don sosai yanzun yake son kamila


Shekaru sunja lokaci ya tafi rayuwa nata juyawa yau Dadi gobe Akatsen sa,hakan take a wajen su Al'ameen


Ranar 3/8/2009 ranar da Al'ameen bazai taba mantawa dashi ba,yau ne suka kammala waec nasu gabaki d'aya makaranta kowa ka gani farin ciki ne d'auke a fuskarsa wasu Kam har kukan rabuwa da juna suke, don irin Wannan ranane Inka rabu da wani har abada bazaka Kara ganinsa ba


Haka take a wajen Al'ameen ranar farin cikinsa ne ya kammala karatunsa na secondary sai Kuma jiran result,farin cikinsa harda hawaye ganin yau ya Gama jarabawa Amma bayada Wanda zai zauna ya nuna Masa farin ciki Kamar yanda sauran daliban iyayensu ke Basu kyaututuka da walima na murnar Ranar


A hankali yake tafiya jikinsa sanye da uniform na makaranta Yana tafiya Yana tunane tunane rayuwa don a lokacin sun girma shi yanada shekara 18 Salim 15 Khadija 6


Ji kawai yayi wata mota Tasha gabansa kafun ya Ankara ma har sun Wasa Masa wani abu Bai Kara tuna Koh sanin inda yake ba sai bayan sati D'aya


D'aya bude ido ya jisa a asibiti Amma baya ganin kome sai duhu,Wanda yake zaune dashi shine Wanda ya tsintosa a bayan gari wajen kauyensu ya fitoh gona kenan yaga wasu sunzo sun yarda Al'ameen a cikin ciyaye,shine ya daukosa ya kawosa hospital da vajin jikin uniform NASA aka gane makarantarsu har labari yaje gidan Adara Amma Amina ne kawai da Salim suka zo asibitin Kuma suke kokarin jinyansa da taimakon mutumin da ya tsintosa,


Al'ameen sosai ya Shiga damuwa Daya waye gari baya gani gashi Doctor's sunyi iyya binciken su Amma basuga ciwo ba shi Karan kansa Al'ameen bayajin kome a cikin idon nasa


Haka tun Yana kuka harya sadakar ya karbe kaddararsa,bayan makantarsa abin mamaki Koh da kamila ta samu labari batazo Koh duba Al'ameen ba sai abokansa na makaranta dana unguwan sune sukazozzo don ganewa idanunsu shin da gaske ne labarin da sukaji Al'ameen ya makance


shine da kansa Yakama Salim ya Masa jagora zuwa gidansu kamila Amma Koh ganinta basu samuyi ba duk abokansa yanzun basa son Koh zama waje d'aya tare dashi kowa gudunsa yake


Bayan waec ya fitoh Salim ne ya karbo Masa result,ya samu 9credit sosai Al'ameen ya rungume result nasa a kirji Yana hawaye,yaci buri akan result nan yayi karatu har bacci bayayi,Ashe ba rabon zaiga abinda ya samu ma da idanunsa sai an duba an fad'a Masa.




Rayuwa fa Tama su Al'ameen zafi don abinda zasuci ma ya zamo musu aiki sai salim ya fita ya nema kafun su samu gashi yanzun an sallame Al'ameen a shagon da yake zama don ganin baida ido duk yanda yaso su taimake sa zai iyya ciniki koda ba idone abin ya gagara




Bayan wata D'aya da makantar Al'ameen yaje gidansu kamila yafi kafa goma Amma kullum sai ace Masa Batanan,Wasa Wasa jikin Salim ya Tashi don ba'a je ganin likita ba har wata ya wuce,ganin ciwo yaci karfin Salim ga bamai taimakonsu, yasa Al'ameen neman taimakon yaran unguwa suka kaisa asibiti


Likita yace Masa wannan karon aiki za'a ma Salim gashe kudi masu yawane,sosai hankalinsa ya Tashi ga rashin ido gashi basuda abinda zasu Kama su sayar sai sarkanda mahaifinsa ya bar Masa Wanda shi kad'aine abinda yake gani a matsayen Abu Mai girma da muhimmaci a Rayuwansa Wanda zai buga kirji yace Awajen iyayensa ya gada,Amma baikai Dan uwansa ba muhimmaci ba.


Haka ya d'auki sarkan yakai kasuwa don a Saya Amma masu sarka sukace bazasu Saya ba gudun karsu sayi abin sata bare sarka Mai shaki Kamar Wannan Basu taba ganin sarka Mai zubinsa ba


Duk inda Al'ameen yasan zai samu a taimaka Masa yaje Amma babu Wanda yayi yunkurin taimakon sa har gidansu kamila yaje Amma Koh sauraron sa mahaifinta baiyi ba


Karshe dai Koran

Please Login or Register in order to submit comment