Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa.


Sannu hajiya ya jikin?


Shuru ta masa taki magana, sai khadija dake gefen tane takece masa jikin da sauki.


Bude laidan da yazo dashi yayi, goran kunun ayane mai sanyi harda raba a jiki, gashi fari tass, ya mikawa khadija, gashi ki bata koh zata sha?


Kaidai yaya Ammar baka gajiya wallahi, kullum ka kawo abu baci take ba, amma koh yaushe sai ka saya.


Mom ina cefa tayi kunu, shine nece ta zubamin a gora guda biyar, zan kawowa sumayya tun jiya na aje a firij.


Karba khadija tayi tana kallon sumayya dake kwance tana jinsu, Amma har lokacin bata d'ago ba, Aunty ga kunun aya mai sanyi.


Shuru tayi sai kuma taji tana jin kwad'ayin sha, mikewa tayi a hankali ta karbi goran.


Tsaya ta tsiyaye miki a kofi, Ammar yace ganin tana kokarin bude marfin.


Koh magana sumayya batayi masa ba, tana bude goron a hankali tasa hancin ta mai tsayi a bakin goron tana tsuntsuna kunun, tare da lumshe ido, kunun sosai yake mata wani irin masifeffen kamshi, dake fita a ciki na aya da dabino.


Habba sumayya menene haka?abinci kike tsuntsunawa hakan bai dace ba, babu kyau fa, yace yana mamakin abinda tayi kamar wata tababbiya.


Kafa goran tayi da bismillah, ta fara sha shatake kamar yar kokowa da sauri sauri, tunda ta kafa goran sai da yayi rabi ta cire a bakinta tana hutawa,kafun ta sake kafa bakin ta akai sai gora ya rage babu kunu.


Ammar da khadija tsakake sukayi suna kallon sumayya, ita da tafi sati biyu ana binta taci abinci, taki sai d'aura mata ruwa ake, duk an bubula mata jiki, Amma yau ba lallama ba banbaki, da kanta tasha kunu har goran faro medium.


Sumayya kam ta kammala da gora d'aya, rike take da gora empty a hannu, tayi shuru amma fa har ranta kari take so, saidai tanajin kunyar tambayar wani,ganin Ammar in baibar d'akin ba.


Bude laidan Ammar yayi ya fitar da wani goran kunu, tashi yayi da kansa ya mika mata, hade da karban empty na goran, ba tare da yayi magana ba ya koma ya zauna.


Ba kunya sumayya ta bude goron ta kama sha, wannan karon kam a hankali take sha tana kurba kad'an kad'an har tayi rabin goran, kafun ta aje sauran a hankali ta koma ta kwanta.


Ammar mikewa yayi ya kalli khadija, ke tashi muje waje zanyi magana dake, yana maganar yana fita waje.


Tashi khadija tayi tabi bayansa, samunsa tayi tsaye a baranda yana jiran ta, karasowa tayi ta tsaya a gefen sa fuska ba walwala, kamar yanda taga yayi.


Shin yayan ki nada abokan hammaya ne?


Babu yayana baida wani abokin fad'a, asali ma yanda na tashi ban taba ganin yayana yayi koda cacan baki bane da wani.


Ok toh akwai wanda yake nuna masa kii koh kyama haka?


Gaskiya babu.


Ok shikenan kawai, yace yana barin wajen ya nufi packing space, khadija ma cikin d'akin ta koma .


Sumayya kam da tafiyan Ammar koh minutes 30 batayi ba, ta sake mikewa da sauri ta d'auki sauran kunun ayan ta shanye wanda ta rege a gora, kafun dare sumayya ta gama da gora biyar innan tas sai fitsari da take akai akai.


Goggo data dawo karan kanta tasha mamakin kunun da yau sumayya tasha, amma batace kome ba.


Da misalin karfe 2 sumayya ta farka da sauri ta mike zaune, jin wani irin azabebben yunwan kunun aya daya farkar da ita, sauka tayi a gadon ta nufi wajen empty in gorunan, bubudesu tayi tana kale a marfi tana sha, tsaban yanda take ji kamar bazata iyya bacci ba in bata sha ba.


Da yake asibitin ba'a barin mutane fiye da d'aya da mara lafiya, yasa goggo barin khadija da sumayya a dakin ita ta koma wajen block in ta shimfida taburma ta kwanta, kamar yanda sauran yan uwan majinyata keyi, shiyasa buruntun sumayya, khadija ya tayar mikewa tayi a hankali tana kallon sumayya, Aunty lafiya?


"Khadija kunun ayannan nake so, kuma ya kare"


toh kiyi hakuri Aunty, zuwa da safe sai inje in sai miki, kinga yanzun dare yayi.


Sumayya kam ji take yanzun in bata sha kunun nan ba zata mutu, mikewa tayi ta d'au hijab tanufi kofa.
Aunty ina zaki kuma?
"Neman kunu, ta bata amsa"
A daren nan ina zamu samu wani kunu , don allah ki dawo bara nafita ni naje na saya miki.


Dawowa sumayya tayi ta zauna a bakin gadon, ta d'auki goran kunu tana shinshinawa.


Fita khadija tayi tun sumayya na tsammanin ganin ta har ta fara gajiya, ta jira kusan awa d'aya bata dawo ba, mikewa kawai tayi ta fita a dakin,ba tare da ta damu ba don yanzun damuwar ta kunu ne, ba dare ba,bakin get ta nufa daga ida sai hijab, data d'aura akan zanin ta sai takalmi koh kudin kunu ma bata d'auka ba a hakan ta nufi get.


Security ne suka tare ta da mamaki, ganin zata fita da uwar daren nan, duk yanda taso su barta, ki sukayi itama taki koma wa ciki, tana tsaye a bakin get in harta gaji ta koma gefe ta zauna, ta had'a kai da gwuwa.


Tsayawar mutun taji a kanta, da sauri ta d'ago ta dubesa sai kuma ta mike da sauri cikin mamakin ganinsa a wannan lokacin.................🍀🍀🍀


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~


🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


Page6⃣8⃣&6⃣9⃣
Da mamaki take kallonsa"kaine da daren nan?


Kala Ammar baice ba, mika mata goran dake hannunsa d'auke da kunun aya.


Da sauri sumayya ta karba, ta fara kokarin budewa jikin ta har rawa yake.


Sumayya ki tashi ki tafi daki mana, yanzun fa 3:30 na asuba amma kinzo nan kin wani zauna kamar turmin tsakar gida, kina wani bude gora, sha zakiyi anan?don Allah tashi muje na rakaki ciki.


Shuru sumayya tayi taki tashi kafa goran tayi a baki zata sha, da sauri ya fizge goran, kinsan Allah in bazaki bi abinda nake so ba, in ban koma da kunun nan ba.


Da sauri ta mike tsaye, sai kuma ta juya tana kallon sa "toh ka bani mana"?


Mika mata yayi, yayi gaba tana binsa a baya har suka iso block in da take, goggo ne da khadija tsaye a kofar d'akin sun zuba musu ido, juyawa Ammar yayi zaima sumayya magana, kawai ya ganta tsaye da gora a hannu babu kunu, da mamaki yace kuttt ke sumayya tafiya kike kina sha koh me naga gora ba kome?


Shuru tayi sai kuma ta bata fuska, guda d'aya fa ka kawo mini, ina ma laifin takwas.


Takwas???goggo da Ammar harda khadija suka hada baki wajen tambayar ta.


Sumayya kinsan gora d'ayan nan ma, a ina na samosa bayan likita ya kirani yace khadija taje ta same sa, akan kinason kunu?


Kunya nema ya kama sumayya, a hankali ta wuce d'akin goggo da ido ta bita tana kintsima abu a ranta .


D'akin sumayya ta shiga rike da goran, ajewa tayi ta kwanta abinta a take bacci ya d'auke ta.


Ammar ma tafiyar sa yayi, khadija da goggo ma duk komawa sukayi suka kwanta.


Da asuba bayan sunyi sallah, sosai sumayya ta uzura ma khadija Akan kunun aya, haka khadija tun asuba taje bakin get ta zauna har saida masu tallah suka fara fitowa, bata samu kunu ba sai 8:00 na safe, ta sayawa sumayya gora uku.


Tana shigowa ta samu sumayya zaune a bakin d'akin, koh magani takisha duk yanda nurse sukayi da ita taki, koh ruwa tace an daina saka mata kenan Alamu dai yau da rigima ta tashi.


Tun daga nesa sumayya ta hango khadija mikewa tayi da sauri ta nufeta, "habba khadija zuwa sayan kunun ne, saikije ki zauna"?


Yi hakuri Aunty wallahi masu kunun ne basu bude ba saida na jirasu.


Karban kunun sumayya tayi ta nufi d'akin zama tayi, takama sha.


Khadija kam.kwanuka ta tsina da kayan sumayya masu datti, zata koma gida.


"khadija inkin koma gida kibi wajen shagari, ya baki dabino, da kudi kisai min aya rabin kwano, da sugar da kwakwa flavour kimin kunun aya, kisa a firij in zaki taho saiki zomin dashi"


Tab Aradu Aunty ban iyya kunun aya ba.


"Baki iyya bafa kikace khadija"?sumayya tace tana kallon goggo, dake ta binta da kallo tunda gari ya waye.


Kauda kai tayi tama khadija bayanin yanda zata had'a kunun, dayake baida wahala yasa khadija ganewa.


Tana zuwa kamar yanda sumayya tace hakan tayi shagari dubu biyu ya bata, taje tayiwa sumayya sayaya har change ya rage, kunun ta dama mata tasa a firij kafun la'asar yayi sanyi haka ta jidi kunun a gora kusan 6 ta kaima sumayya hospital sauran ta barsu a firij.


Yau sosai jikin sumayya yayi sauki kamar ba ita ba, da yamma da Ammar yazo likita ya basu discharge,Ammar da khadija ne suke tattara kayayyaki suna kaiwa mota.


Sumayya ce tsaye a jikin motar Ammar, sanyi take da riga da siket na atamfa sai hijab mai corona, sosai kayan ya karbeta gashi tayi wani irin fari tayi fresh sosai, idanun nan nata sun kara fitowa sosai saboda kumburin da kasan idon yayi kamar mai ciwon ido, saidai kwayar idon ya kara haske, rike take da goran kunun ta da ya rage kuda d'aya a hannu duk da basha take ba a lokacin.


Tun daga nesa yake kare mata kallo, shikaran kansa ya rasa wani irin ciwo ne haka, duk wanda ya santa, ramar da tayi ne kad'ai shaidan bata da lafiya.


Ganin ta d'ago yasa sa kauda fuska, kamar ba ita yake kallo ba, boot ya bude ya saka akwatin hannun sa, ya tsaya yana jiran khadija ta karaso da tata jakar, tana zuwa ya rufe boot in .


Shiga baya sumayya da goggo sukayi, dole tasa khadija shiga gaba, Amma yaja motar suka cillah.


Gidan mai Ammar ya shiga zaisha mai yayi packing,ana loda masa mai A hankali ya sace kallo sumayya, gani yayi gabaki d'aya ta maida hankalin ta gefen glass inda take, alamu dai wani abin take kallo.


Juyawa yayi yaga wata yar Christian ne zaune a tsallaken titi tana gashin masara, bayan an gama zuba masa mai jan motar yayi daidai wajen mai masara gasheshen, ya mika mata 500, ta saka masa.


Da sauri mai masara ta mike daman ta gaggasasu suna zaune, jimbo ta d'auko tazo ta zuba musu masara guda goma, Hamsin hamsin ne, karba yayi ya aje a mota.


Suna shiga sintali gidan goggo suka bi ya ajeta, masara ya d'auko kuda hudu ya bata Amma taki karba.


Gida ya wuce dasu sumayya, dayake goggo tace khadija tabi sumayya gidan ta tana ibe mata kewa.


Yana packing sumayya kam fita tayi, tayi cikin gida, tana bude kofar su a hankali ta zubawa kofar ido, hawaye na cika mata ido"nayi kewanka yanda ya kamata mijina, nayi kewanka so tarin yawa, don Allah ka dawo, kamin Alkawari bazaka taba barina ba, saidai in nine na gaji da zama da kai, gashi sun rabamu, bansan halinda kake ciki ba, "tana maganar tana hawaye sosai taji kewar mijinta.


Toh Allah yayi dare gari ya waye, Ammar daya shigo da akwati a hannunsa da laida yace.


Matsa masa sumayya tayi ta zauna akan dakali tayi tagumi, mika mata laidan masara Ammar yayi


Ba musu sumayya ta karba, a Hankali kamar wance aka sakata dole tace "thank you for everything" tace tana zaro guda d'aya ta b'amb'are tana ci,


Da mamaki Ammar ke kallon ta jin yau ta masa godiya, amma dai baice kome ba ya juya yayi waje.


d'aga ido tayi tana kallon Ammar ganin ya dawo, don a zatonta yawuce kenan, da sauri ta mike tsaye tana murmushi har hakoran makkar ta suka bayyana tare da fararen hakoran ta, ganin manyan elagement in hoton su, da Ammar ya fitar a boro.


"Wow masha Allah, kamar kasan abinda ke raina akan hoton nan kenan, ka kwashe mini waya" tayi maganar tana karban hotunan a hannun sa tana kallo.


Hotuna ne guda biyar, d'aya ita da mijinta, sai kuma d'ayan ita kad'ai, d'ayan shima shi kad'ai, sai d'aya kuma shi da ita da khadija, d'ayan kuma su da kannen Ammar ne, sosai hotunan yayi kyau, abinka da hotuna daukar iphone da background.


Yanzun kam kin daina jin haushina kenan koh?


"Eh na daina jin haushin ka, tunda har kamin wannan"tana magana tana nuna hotunan.


Hannu yasa a Aljuhunsa, ya fitar da wayar ta zai mika mata, Amma wayam yaga bata.


Sumayya kam ganin khadija ta bude kofar d'akin yasa ta saurin shiga, wai zata bubbuga hotunan a jikin gini, sake fitowa tayi tunawa da tayi bata da kusa.


Sumayya ga wayar ki, yace yana mika mata wayar, kimin Alkawarin mundin kika manna wannan hotunan duk lokacin da kika gani Addu'a zaki masa Allah ya kubutar dashi ba kuka ba.


" insha Allah"tace tana karban wayan.


Kallon khadija Ammar yayi, kee muje na samo kusa na baki ki kawo mata.


Murgud'a baki khadija tayi, wallahi ta tsane yace mata kee innan , haka dai ta bishi a baya.


Ba'a jima ba khadija ta dawowa da sumayya da kusa, bubuga hotunan tayi a d'akin ta.


Har dare sumayya masaran nan ta ringa ci inta shake tasha kunu a firij, Abinci ma khadija daidai bakinta ta dafa, sumayya kwance take akan gado hannunta rike da masara tana b'amb'ara tanaci, suna kallo da khadija dake zaune akan kujera.


A haka sumayya tayi bacci da masara a hannu, tsakar dare ma data farka wanke baki kawai tayi ta gwaguye masara ta koma ta kwanta.


Washe gari khadija ta koma makaranta, ganin jikin sumayya da sauki sosai, ta mata wanke wanke da shara, breakfask ma taliya ta dafa laida d'aya taci ta rufe sauran, don sumayya tun asuba ta karya da masara.....


*****************
Washe gari kamar yanda bappa ya fad'a haka muhammad yayi maganin sa, yana gamawa ya fitoh kenan ya samu matar gidado ta fitoh zatayi wanke wanke da tsohon ciki, hanata yayi da kansa ya wanke kwanukar ya jido musu ruwa ya ciccika randuna.


Suna karyawa yabi gidado kiwo, basu dawo ba sai yamma, kayan sa kala biyu da jallabiyar da yazo dashi da wanda gidado ya basa, ya had'a ya wanke, ya shanya, wanka yayi ya fitoh wajen kofar gidan ya zauna yana bin garin da kallo.


Tun daga nesa data sauko a machine ta hangosa kara sauri tayi, bako.. bako...bakon nigeria, tun bata karaso ba take kwala masa kira, sai washe baki take irin dai yanda mutanen kauye kiye in sunga bako(mutanen kauye akwai d'aukaka bako kam)


Yajita sarai Amma ya mata banza, harta karaso inda yake d'auke da robobin nonon ta, bako ina kwana?au ina wuni.


Lafiya yace yana basar wa don Wallahi yarinyar ta fara isarsa.


Kasan me bako? Bata jira amsar saba tacigaba, ai in gaya maka ina zuwa birni nayi kawa yar gayu, harna mata tadin ka, gashi tace tana mika masa abu.


Juyawa yayi kawai ya kalleta, ya sake kauda fuska, jin tace masa gashi, menene wannan?


Uhmm abune na saya maka, ka bude ka gani.


Ba musu ya bude abin, ai baisan sanda dariya ya kwace masa ba, bread ne wani yanka kamar na ashirin, gaskiya karbi kayanki ni baxanci ba babu ruwa na, tunda kudin nonon inna kika saya dashi.


Don Allah kai hakuri kaci, in ba haka ba inna dukata zatayi na kashe mata kudi.


Gaskiya bazanci ba sai dai na aje miki, in zaki fita kizo ki Amsa.


Shikenan in zanje kallon shadi gobe saina karba


Shadi? Gobe bazakije tallah bane?


Eh gobe a........


Bata karasa ba taji dundu a bayanta mai masifar zafi dimmmm, saida ta wantsala gefe, daga muhammad har indo zaro ido sukayi sai kuma suka dubi wanda yayi wa indo dundu..........
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Kuyi manage na page innan wallahi yau typing nayi by mistake ya goge😥😥da yamma.


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~


🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


Page7⃣0⃣&7⃣1⃣
Inna Talatu ce tsaye, sai huci take cikin masifa, Wallahi indo in baki fita harkar yaron nan ba, saina saba miki mena fad'a miki akan sa?


Don Allah inna kiyi hakuri, bazan kara ba, tace tana mikewa tsaye.


Uban me kike mika masa a laida?


Inna aikana yayi fa.


Shige nace, tayi maganar tana hankad'a indo cikin gida.


Al'ameen kam da ido ya bisu, watoh a rayuwa koh baka ma mutum kome ba, in kaje waje sai kaga masoyi da makiyi, zaka ga ka burge wani, wani kuma haushi kake basa.


Tsoho kai kad'ai kake zaune ne?gidado daya fitoh gida yace.


Eh gidado, yace yana matsama gidadon ya zauna.


Gobe fa babu zuwa kiwo.


Meyasa?


Akwai shadi ne.


Ina da yamma ne,?muhammad ya tambaya.


Au harma kana da labari kenan?


Eh indoce take sanar dani wai bazata tallah ba.


Eh gaskiya gobe za'ayi wasa da yamma.


Chap sai kuma ya hanaka kiwo?basai muje mu dawo da wuri ba, itama indo taje tallan tah ta dawo da wuri ba.


Gaskiya ne, Amma mudai anan in za'ayi shadi duka yan kauye basa zuwa koh ina a ranan.


Ok kana nufin kaima kafun kayi aure saida aka farfasa maka baya? kamar yanda nake jin Labari, don mu an daina a garin mu.


Eh nima kafun na aure matata, duka akamin Hamsin, yace yana cire rigansa ya nunawa muhammad bayansa.


Zare ido Al'ameen yayi ganin wasu bulalu kwance a bayansa rututu duk da sun warke amma tabon su na nan, yanzun kana ji kana gani gidado aka maka wannan?


Eh yanzun kai yanda kake kaunar sumayya bazaka iyya tsayawa a bulale ka, don ka mallake ta ba?


Zan iyya harma yafi wannan, indai akan tane.


Toh baka gani ba, nima zan iyya jurewa.


Gaskiya ne Allah yabar kauna, Al'ameen yayi maganar yana kallon gidado.


Haka rayuwa yake tafiya, A hankali A hankali har muhammad ya saba da rugar su gidado, yanzun ya waye a kiwo, wata rana har raba shanu suke da gidado, kowa ya kama hanyar sa, tsakanin sa da yan gidan akwai mutun tawa da ganin darajan juna, duk yanda inna ke nuna masa kyama da masifa, bai taba koh d'aga ido ya kalle taba saboda darajan gidado da bappa.


Jikinsa Alhamdulilah shi karan kansa yaji sanji a jikin sa, ba kamar da ba, haka tsakanin sa da indo akwai mutunci, duk da ba shiga tsafgarta yake ba, amma makale masa data ke, yasa yakan d'an rage mata wani abin.


A sannu sannu gashi yanzun Muhammad na neman wata biyu, a ruga kuma yana cigaba da maganin sa.








**********************
Sumayya ma tana nan da halinta nacin masara, sosai ta maida masara da kunun aya abinci, duk lokacin da Ammar zaizo dubata duk da ba shiga cikin gidan yake ba , a waje yake tsayuwa, saiya kawo mata masara koh kunu, sosai take ganin darajan sa kamar d'an uwan ta na jini, tunanin muhammad kam har gobe bata daina ba, saidai ta rage, Ashe haka b'atan d'a da miji yake? har gwara mutuwa wannan ka gama tabbatar wa kanka ya tafi kenan.


Yau asabar babu makaranta, khadija ce ke wanke kayan ta a kofar sumayya, yayinda sumayya ke zaune a gefe tana latsa system nata, hannun ta rike da masara


Assalamu Alaikum,wani yarone yayi sallama a bakin shashen su sumayya.


Wa'alaikumu salam ta Amsa masa tana mikewa zaune, shigowa yayi da kwano a hannun sa ya mikawa sumayya, wai inji goggo Amina.


Amsa sumayya tayi tace, yacewa goggo ta gode, budewa tayi gwaten shuwaka ne, yaji kyad'a da tsaki sosai, yawunta ya tsinke da sauri tamike ta d'auko shukali, ta faraci, "khadija ga gwate"


Ah ah aunty kici nagode


Kala sumayya batace ba, cigaba tayi dacin abinta, harta cinye tass, sai kuma taji bata son shan kunu aya sam, ruwa tasha sai kuma taji yawo ya cika mata baki.


Haka sumayya ta wuni tana zubar da yawo, gashi ba yawo kad'an ba, karshe dai kunun nan rabawa yara tayi.


Tun daga Ranan sumayya ta maida gwaten shuwaka da macikan zogale, sune abincin ta sai goruba haka ta maidasu abinci, masara duk sun zama tsohon yayi, haka Ammar ma ya maida ganye abin kawowar sa, sam baya gajiya da hidimar sumayya.




Yau wata biyu kenan da batar Al'ameen, haka kawai taji a daren tana son cin tsire mai yajin bakuru, da cabbage, haka tasa khadija a gaba suka fita wajen mai nama tsallake sukaje suka saya, sunzo zasu tsallake titi kawai sukaga wani MAKAHO da d'an jagoran sa, zasu tsallake titi alamu dai dare ne ya musu wajen bara.


Sosai sumayya tabisu da kallo hawaye na cika mata ido"ina suka kaimin mijina"?


Don Allah aunty kiyi hakuri, kinga mun samu kin samu lafiya karki sake jajibo ma kanki ciwo don Allah.


Shuru sumayya tayi suka tsallake titi, suna zuwa gida bayan sunci namar ta kwanta akan gado , khadija na kujera,Har khadija tayi bacci itakam ta kasa, , haka ta raba dare idanun ta biyu tunanin Rayuwar da mijinta ya shigane ya dameta.


Da asuba da mugun ciwon kai ta tashi da zazzabi, khadija taso suje asibiti Amma haka ta ki zuwa, kafun azahar sosai cikin yayi tsamari




Cikin ikon Allah Saiga Ammar yazo, shiya kaisu asibiti, bayan sunga likita ya mata tambayoyi, yace nurse ta bata roba tayi fitsari akai lab.


Tunda sumayya taji haka, sam bata damu ba don ita ta d'auka koh ahone ire iren da aka mata, lokacin da hawan jini ya kwantar da ita.


Bayan wasu hours, nurse ce ta dawo da result a hannun ta, mikawa likita tayi ta juya ta fita.


a hankali likitar ya kalli Ammar ya kalli sumayya, harga Allah ya d'auka ma'aurata ne, Congratulation Aboki na matar ka na d'auke da cikin wata biyu da sati d'aya.


Ammar kallon sumayya yayi, daidai lokacin itama ta kallesa sai kuma suka sake kallon likita har suna had'a baki, "ciki"??


Eh ciki wani abune, ya tambaya da mamaki ganinsu haka.


Ah ah ba kome likita, Ammar yace yana kallon sumayya data d'aura hannu akan cikin ta, tanna hawaye na farin cikine?koh name oho baigane ba.


Am bayan wannan akwai wani abin, ya kamata aboki kana kwantar mata da hankali a matsayin ta na iyalinka, ya kamata ka bata kulawa yanda ya kamata, yanzun juna biyu gareta Amma yanda take saka tunani a ranta, zaku iyya rasa baby ku, ciwon kannan nata tunani ne ya jaza mata, bp nata yahau, kuma bama son haka, a halinda take ciki yanzun nan.


Insha Allah doctor za'a kiyaye, Ammar ya Amsa kawai, yana karban takardar magani da likita ya rubuta musu.


Fita sukayi xuwa pharmacy, magani ya saya mata suka shiga mota, har lokacin hawaye sumayya take abin gwanin tausayi.


Kinga sumayya yanzun fa Dr yaja miki kunne akan damuwar da kike sakawa kanki, waike wace irin mutunce? kukar ne zai dawo dashi kome?


" na daina"kawai tace tana share hawayen ta.


Me zan sai miki?


Girgiza masa kai kawai tayi, Alamu batason kome.


Tsayawa yayi a bakin asibiti yasai mata Alale, ya dawo motar ya mika mata


Ba musu sumayya ta karba, ta rasa me yasa duk Abinda Ammar ya bata sai taji tanason ci.


a haka Rayuwa yake ta tafiya yau farin ciki gobe akatsensa yanzun cikin sumayya nada wata uku cip, bata laulayi haka cikin yazo mata, kamar babyn yasan babu Dad a kusa, saici yanzun kam kome ta samu ci take kamar me, koh zabe batayi.


Babu abinda ta nema ta rasa, Ammar na mata goma sha, shagari shike cefenen gidan ogansa, da duk abinda zata bukata shike bayar da kudi,asai mata, maganar lalle ma yanzun batayi sai make-up kawai shima Amare take ma, duk maiso tazo gida, a hakan take ta tara yan kud'aden ta, yanzun sunyi yawa a Account in khadija.


Yau dai tunda ta tashi da safe takejin wani irin nishad'i wanda batasan dalili ba, tana tashi da safe dayake yanzun sam batason saka riga,don rigunan sun mata kad'an, sosai nonuwan ta suka cicciko, have vest da zani ta maida su kayan sawan ta, ko mai bata shafawa saboda wari yake mata, haka turare ma koh wani iri bata Amfani dasu.


Zaune take a taburma ita kad'ai ta mimike kafa, don khadija ta tafi kasuwa, babu school yanzun suna hutun first time, kosai ne a gaban ta da kunun kyad'a tanaci, sosai sumayya tayi jiki tayi kiba, wuyanta har guru guru yayi, hips natan nan sun kara buduwa haka ma breast nata, daman akwaisu bare yanzun da dalili.


Sallama akayi a tsakar gidan, na muryoyin mutane abin ya bata mamaki jin kamar muryar sani, bata gama shan mamaki ba saida taji suna gaisawa da y'an gidan Adara dake tsakar gida, suna tambayar su kofar sumayya.


Mikewa tayi tsaye koh d'an kwali babu tsaban mamaki daga ita sai zani a kwankwaso da have vest, jin sun nufo kofar ta, kamar a mafarki Amma dai bara ta tsaya taga ikon Allah, bude kofar shashin ta akayi, da sallama




Suman wucen gadi tayi, wallahi ita harta manta da wasu shugaba family, sai sa'i da

Please Login or Register in order to submit comment