Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a bakin sa ganin wani irin kitcheen na Alfarma mai dauke da kayan Alatu na zamani, sai samari guda biyu dake kitchen in a tsaye suna aiki,jin motsen su muhammad da sallamar suce yasasu juyowa.


Amsa sallamar sukayi, bayan sun gaisa da yaron yake musu bayanin Al'ameen ne zai karbi, sarkin shayi harya warke, sannan sarkin shayi yace su koya masa had'a shayi, sannan shi zaina kaiwa sarki shayi kullum, duk da yare yaron ke musu bayani.


Muhammad kamfa ya shiga tsaka mai wuya don shi dai ba yare yake jiba, tayaya zai iyya zama da wa'innan mutane wai daman babu hausawa ne a nijar koh dai wannan garine baida hausawan oho?kuma gashi baba ya iyya hausa?


Yaron ne yajuya zai fita a kitchen in da sauri muhamamd ya bisa a baya, da mamaki yaron ya juyo ya kalli muhammad cikin mamaki yake tambayar sa yaya kuma zaina binsa?


Gaskiya nifa ban gane ba kowa a gidan nan sai yare yake mini, nifa baji nake ba.


Dariya yaron yayi karka damu kaji, wasu a cikin su suna ji sai dai in an ganka za'ayi tunanin koh kanajin yarene shiyasa wasu ke maka yare, Amma in suka maka magana kana musu hausa kaji zasu maka suma.


Toh nagode kawai muhammad yace, ya koma kitchen in, sosai suka sakasa aiki goge kofuna d'aura shayi saka wanshan ganye ah ah yi kaza sai kusan azahar, bayan sunyi sallah aka fara rabon shayi a gidan, shima wasu kofuna da buta na Alfarma masu shegen kyau da sheki ruwan Gold suka zuba shayin a butan, aka jera a karamin tire da shukali sai bolw na zuma, shima Golden colour da shukali biyu, mikama Al'ameen sukayi Hade da had'asa da wani a cikin ma'aikatan ya nuna masa flat na sarki.


Duk abinda Al'ameen kiyi tsananin bugun zuciyar sa nayi, har wa yanzun da suke nufar sashen sarki, hannunsa d'auke da tiren kayan shayin, suna isa kofar shiga falon, ma'aikacin ya koma ya bar muhammad tare da nuna masa kofar da hannu alamu dai nan zai shiga, yafi minutes 2 yana tsaye ya kasa shiga zuciyarsa na matukar buga wa da sauri-sauri, ganin wani bawa zai wuce yasa muhamamd saurin sa hannu ya murd'a kofar falon bakinsa d'auke da sallama, Amma bai shiga ciki ba a bakin kofar ya tsaya.


Amsa masa sallamar akayi saiga wata mata ta fitoh, sanye da kayan da bayin gidan ke sanyawa, hade da masa iso zuwa cikin falon, shigowa Al'ameen yayi yana bin bayanta har suka karaso cikin falon, falone babba mai girman gaske da kawatuwa irin falon nan na sarakuna, masu ji da lokacin su, wuce falon sukayi suka nufi wani kofa daban, nan ma falone Amma baikai wanda suka wuce girma ba Da kayatuwa, kara nausawa sukayi cikin wani kofar, saigasu a wajen shakatawa mai d'auke da shuke shuke na flowers mai ban sha'awa da kamshi, jefa kafa kawai muhammad yake don yayi matukar gajiya da tafiyar nan, da yake daman bai gama sauke gudun hijiran da sukayi ba, ga matsanan cin bugun zuciyrsa kiyi da karfi, lokacin da idanunsa suka sauka akan mutanen dake zaune su biyu cikin shiga na Alfarma wanda koh ba'a fad'a ba kasan sarkine tare da matarsa dake sanye da Alkimba mai masifar kyau da d'aukar ido, farace tas kyakkyawa da ita, yayinda sarkin ke sanye da rawanin buzaye a kansa ya rufe fuskar sa luf banda idanunsa babu abinda mutun zai hanga don koh kafar sa da hannunsa boye yake a cikin suturansa, shuru sarauniyar tayi ganin su Al'ameen da Alamu dai magana take da mijinta Da sallama a bakin su Al'ameen suka karaso inda suke, da sauri sarkin ya dafe daidai saitin zuciyarsa yana Ambatun sunan Allah a zuciyar sa, yayin da muhamamd suka tsunguna a kan gwuwuwinsu A hankali ya d'aura tiren akan table inda ke gabansu, hannunsa sai rawa yake wanda baisan dalilin hakan ba, tsiyaye shayin ya fara a kofi yana had'awa da zuma.


Sarauniya ita ta kula da halin da mijin ta ke ciki da sauri ta matso garesa Ranka ya dade lafiya meke faruwa zuciyar ce?


Shuru ya mata, itama bata damu ba don tasan halin mijin ta zata masa magana sau dubu ba Samun Amsa zatayi ba, yasha yarfata a gaban bayinta Amma tun yana damunta yanzun koh a jikinta, kara tambayar sa tayi zuciyar sa na ciwo ne?


Girgiza mata kai kawai yayi baiyi magana ba, jingina yayi da jikin kujeran da yake zaune akai ya lumshe ido yana maimaita innalilahi.....


Al'ameen na gama had'a shayin ya mike abinsa ya fita a lambun, sai a lokacin sarkin ya zare hannunsa daga kan kirjinsa yayinda idanunsa sunyi matukar kaduwa zuwa ja, sosai jikinsa ke rawa, ganin hakan yasa sarauniya mikewa da sauri ta fita a lambun ba'a jima ba saiga ta, ta dawo da wata tsohowar mata cikin shiga ta Alfarma kyakkyawa da ita fara, ta karaso garesa hannunta d'auke da magani, da saurin ta balla hade da karban kofin ruwan dake hannun sarauniya ta kafa masa a baki, ba musu ya karba yasha maganin, ka tashi ka koma ciki kaji?tsohowar tace


Girgiza mata kai kawai yayi vaiyi magana ba, Alamu dai yafison zaman nan in, ba musu daga matar tasa, har tsohowar suka basa waje don haka yake indai ta shine yafi kaunar a basa waje ya zauna shi kad'ai sau dubu akan ya zauna da mutane.


Al'ameen kam yana komawa kitchen in abinci aka kawo musu na rana, mai rai da lafiya harda kaji sukaci, zama sukayi a falon da kitchen in ke cikinsa suka kwanta a kan kujerun dake wajen alamu dai daman falon donsu akama,(ma'aikatan shayi) sai la'asar suka sake dafa sabon shaye wannan karon Al'ameen ne ya d'auka shi kad'an sa, ba tare da rakiyar jakadiya ba ya shigo falon, yarane zaune a tsakar falo su uku, biyu suna zaune a kasan cafet dake shimfid'e a tsakiyar falon, suna rubutu a takarda dukansu mata ne d'ayan zata kai shekara goma sha biyar, d'ayan kuma zata kai shekara Goma, Lokacin da yaran suka d'ago suka kallesa baisan lokacin da tiren shayin dake hannun sa ya tsubuce a hannunsa ba, a take kome ya tarwatse a wajen, suma yaran zare ido sukayi ganin barnan da muhammad ya musu a falo, d'aya yarinya ta ukun dake zaune akan kujera tana danna waya bazata wuce shekara 20 ba, ta mike cikin masifa da izza, kai wani irin wawane koh ince dolo kana da hankali kuwa zaka shigo mana falo kazo ka zubar da abu, sannan ka tsaya kana kallon mu, jira kake mu kwashe maka koh me?


Habba Nabila baikamata kima mutum babba kamar wannan irin zagin nan va, baikama taba gaskiya ki gyara halinki, d'aya daga cikin yaran da ke zaune a kasan cafet in tace ma nabilar.


Kinga muhibbat babu ruwan ki dani ki daina mini irin wannan abin da kike mini, niba sa'arki bace Amma na fahimci kina mini shishigi a lamurana be careful, takarasa maganar da barin falon tana hararan sa.


Muhibbat ce ta kallesa kaga malam tattara abinda ka fasan nan ka tafi store a baka wasu kayi sauri ka kawowa Abba shayi?duk da Turanci suke magana.


Muhammad kam mutuwar tsaye yayi yana kallon yarinyar, koh dai mafarki yake ne yarinyar kamar khadijar sa haka yake jin muryar ta, yanda khadija ke magana ba R haka ita ke magana, kaman ninta kome nata yana masa irin na yar uwarsa,duk da khadija na yarinya ya makance amma hakan bazai hanasa gane taba, a gaskiya abinnan ya basa mamaki matuka da kuma tsoro gasu su biyu masu tsananin kama da juna, koh yace masu kama dasu, jin ta sake masa magana cikin yanayin mamaki ya tsunguna ya kwashe fashashun kofunan ya fita a falon da sauri.


*****************
Sumayya fa yanzun ci yafi nada ga bacci babu aikin da take yanzun kome khadija kiyi in taga aikin yama khadija yawa saita, sata ta musu take Away kawai, don khadija na kokari ga zuwa school har yamma take dawowa ga aikin gida ga masu kitso, amma Alhmdulilah baza'ace aikin mai yawa ba tunda sharane kawai sai girkin abinda zasuci don yanzun cin sumayya yafi nada gashi cikin yayi girma sosai ya kara hurata, jiki tayi bana wasa ba kafafunta haka suka cika tim,An hanata cin gishiri ma A hospital yanzun ganin irin huruwar da tayi.


Yau weekend babu school khadija ce zaune a baranda tana ma mutane kitso, yayinda wasu ke zazzaune suna jiran layi yazo kansu, sumayya ce ta fito cikin shiga ta Alfarma zanine less da hijab nata mai hannu medium size, sai jakan sakalawa a kafad'a da waya a hannunta sosai tayi kyau, hannu tasa ta maida kofar falon ta rufe, "khadija lailar ta fitoh ne"?


Ah ah Aunty bata fitoh ba koh na dubo miki itane?


"Ah ah khadija ki bari kawai bara naje flat natan sai mu wuce"


Toh Aunty saikun dawo


Tana sauka a kan barandan tace"Yauwa khadija"


au na manta me zan dafa ne na rana?


"Kibari kawai khadija naga yau akwai layin kitso sosai in muka shiga kasuwa zanbi restaurant nai mana take Away"


Ok toh Aunty adawo lafiya


"Allah yasa khadija"wucewa compound in gidan tayi ta nufi sashen laila, harta haura dakalin d'akin ta saigata ta fitoh cikin shirin fita, ah ah sumayya harkin shiryane?


"Bazan shirya ba laila so fa nake mu dawo kafun Azahar don wannan zafin ranan ba lafiya bane"


Gaskiya kam bare ku masu ciki.


"Kinga laila don Allah ki shige muje bana son yawan tsayuwar nan habba"


Yi hakuri hajiya muje, kawai laila tace suka kama hanya da sumayya.


Kasuwa laila da sumayya sukaje da taimakon laila sukayi sayayyan kayan baby, dana haihuwa kama daga baf gadon yara kayan sawa feda kome daya dangance baby da sumayya wanda zatayi Amfani dashi lokacin haihuwa da bayan haihuwa ita da babyn ta duk sumayya ta saya, kaya niki niki haka suka zuba a Texi, har sun shiga mota sumayya ta hangi mai mangoro, take tunanin mijin ta daya zamo mata jiki ya fado mata, sai kuma taji tanason sha, hakuri ta baiwa mai motar ta sauka, da sauri ta nufi wajen mai mongoron bata saurare maganar da laila kece mata ba,tana kokarin bude jakar hannunta, gabaki d'aya hankalin ta na kan jakan, bata koh ganin gabanta.


Ji kawai tayi an bangajeta da karfi tayi baya tagal tagal zata fadi............πŸ€πŸ€


✨Ruqeenjalal✨
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ


Page8⃣4⃣&8⃣5⃣
Tagal-tagal tayi zata fadi gabaki d'aya ta gama sadakar wa itakam yau saita Allah, rumtsa ido tayi tana Ambatun illahilahi, saiji kawai tayi an tarota cikin zafin nama ta sauka a hannunsa.


Subhanallahi baiwar Allah bi a hankali baki ga halinda kike ciki ba, haka kuke saiku d'auko ciki rududu rududu ku shigo kasuwa tsabar neman fitana da salon jawa mutan masifa.


jin abinda mutumin da ya bangaje sumayya yace, yasa yaron da ya tarota ya taimaka mata ta zauna a bakin wani shago, da sauri ya nufi guy in, wanka masa mari yayi, ya cakumo wuyarsa cikin bacin rai yake magana, kai wani irin dabbane wawa kawai baka dubi halinda take ciki ba, ka tashi ka bangaje ta batare da ka dubi halinda zata shiga ba, kazo kana gayawa mutane maganar banza.


Hannu guy in ya d'aga zai rama marin sa, da sauri yaron daya taro sumayya ya kama hannunsa, wasa wasa fa dambe ya kaure a tsakanin su, yayinda sumayya ke gefe gabaki d'aya jikin ta rawa yake, don ita d'auka tayi ma yau innan dai sai abinda Allah yayi.


Da sauri jama'a suka shiga raba fad'ar, don gudun kada abin yakai ga yan sanda kuma ya zama babban magana, daker aka samu yaron ya hakura, guy in ya tafi, da sauri ya dawo wajen da sumayya ke zaune, sannu Aunty badai binda ke damunki koh?


Girgiza kai sumayya tayi a hankali, tana kallon laila data gaji da jiranta tabiyo baya, don ita bata ga abinda ya faru ba.


Kalamu-wahid!!!!!Daga nesa aka kwalama yaron kira da sauri ya juya, yana kallon mai kiran nasa,Na'am babayo ina zuwa pls.


Babayo dake tinkaro inda su sumayya suke, bakine kamar Kalamu-wahid sai dai kalamu ya fisa kyau, duk da shima ba tayan baya bane, kuma babayo nada zanen kanuri a fuskar sa, sabanin kalamu da baida zane sam.


Ke sumayya lafiya sayan mangoron ne, kika zo kika zauna?bata jira Amsar sumayya ba ta kalli kalamu, malam lafiya ka saya mata a kai?


Sumayya ce ta bata amsa, "Lafiya laila taimako na yayi, saura kad'an yau nasha kasa"


Sumayya dakin kashe kanki, shiyasa nake ta miki magana Ki tsaya na sayo miki, amma kememmen kika ki saurarata.


Yi hakuri Aunty laila ba laifinta bane, kalamu yace, yana tattara wa sumayya jakanta daya watse a kasa.


Kalamu lafiya mayya tsayar da kai kuma, ka barni a mota tun d'azun?


Yi hakuri babayo bara mu sauke wa'innan a gida.


"Ah ah ka bari kawai mun tare taxi harna saka kayana a ciki"


Ah ah aunty sumayya muje dai na kaiku, kuyi hakuri wallahi da zuciya d'aya nake son d'aukarku.


Shuru sumayya tayi tana kallon yaron da mamaki, bazai wuce shekara 19 zuwa da 20 ba, daga hadu d'aya har ya shiga jikinta ga Aunty sama Aunty kasa"toh shikenan sai muje ku d'auko kayan mu dake mota"


Ok toh muje ku shiga mota gashi shan, yace yana nuna wani had'aden mota dake tsallaken titi, babu musu sumayya ta mike da sauri ya karbi jakan nata, laila na binsu a baya sukayi wajen motar, baya sumayya da laila suka shiga, yayinda babayo da kalamu-wahid suke gaba, babayo ne mai tukawa kalamu na gefe, da nuniya sumayya suka nuna musu taxi in, tattara mata kayanta sukayi shida babayo suka zuba a boot, wasu kuma a baya don kayan yawane dashi, shiga sukayi hade da tambayar su unguwan da suke.


Da mamaki kalamu yace laaa ai unguwan mu d'aya daku wallahi, jin unguwar da laila tace.


Laila ce ta kallesa Au da gaske, ku a wani gida kuke kenan?


Muna kusa da gidan hayan Malam sale uba?


"Kai aimu a gidan hayan muke "sumayya ta basa Amsa.


Babayo ne yace, Ah lallai kam rashin ziyara ne babu, ace unguwan ku d'aya har ginin gidan ku a manne bakusan juna ba.


"Gaskiya kam"kawai sumayya tace tayi shuru ganin sun iso get na gidan su, sauka sukayi kalamu ya sauke musu kayansu, tare da bawa babayo umurni daya shiga gida, shi zai shigar wa da sumayya kaya, duk yanda sumayya ta hanasa kiyayi, haka ya kinkimi kaya shida laila sukayi cikin gidan su sumayya, yayinda ita kuma ke binsu a baya.


Khadija dake zaune a falo tana cin abinci, sannan ga laptop a cinyarta tana kallo,sai munira da kaninta a gefe, suma tasa musu abinci daban a plate, da sauri ta d'ago jin muryan namiji na sallama a bakin falon su, kafun ma ta Amsa har an turo kofar an shiga.


Laa Aunty kun dawo?sai yanzu, da sauri yaran laila suka mike sukayi wajen mamansu suna mata oyoyo.


Sai yanzu khadija sayayyar ce da yawa, yauwa kalamu aje mana kayan a falo.


Aje kayan kalamu yayi, laila ma ta aje nata, juyawa yayi zai fita yana musu sallama.


"Ah ah kalamu dawo ka zauna, ke khadija kawo masa sallaya, falon namu Empty ne ba kome sai katifa"


Kai Aunty dama kin bari wallahi nagode


Da sauri sumayya tace"Ah ah kalamu kadai zauna ta kawo maka abinci kaci don Allah karkace ah ah"


Gaskiya ne kalamu ka zauna mana kaci abinci, nima khadija ibomin abincin nan yunwa nakeji, kinsan na fita gida banci kome ba, laila tace tana nufar kitchen in sumayya, karban abincin kawai tayi a plate ta fita.


Zama kalamu yayi yayinda sumayya ta wuce d'aki abinta, zata watsa ruwa sosai taji dadin girkin da khadija tayi, don ita tama manta tace zata musu take Away.


Kawowa kalamu Abinci khadija tayi da ruwa ta aje masa a gaba, komawa tayi inda ta tashi taci gaba da cin abincin ta, shukali kalamu yasa ya ibi abinci sai kuma ya kalli khadija da mamaki ganin tunda yazo falon koh gaidashi batayi ba, sai wani cin magani take kamar bata ga bako ba, damuwar ka da bawa kenan bai iyya samun yanci ba saiya zage.


Jin abinda yace yasa khadija gane kanuri ne, cikin dariya tace eh tsabar rashin yancin wasu koh gangan tarihi basu dashi a fada.


Kutt ke wallahi karyane kune bayi, kauyawa in banda kauyanci mutun yaga bako yaki gaidashi?


Baki ma ai iri-iri ne, akwai kalan gaisuwa akwai kalan kori.


Da mamaki yake kallon khadija, kutturu amma yarinyar nan ta iyya bakar magana, waike anya ba makarantan harshe kike ba?


Ah ah na kutare nake


Shuru kalamu yayi jin abinda tace masa, yaci gaba dacin abincin sa.


"Waini maganar me nake jine tun d'azun ina bathroom"?


Wallahi Aunty bakon kine da iyayi, harda zai gayawa fulani magana.


"Ke kuma sai kikayi me"?


Saina fad'a masa ba sugari, mudasu waza'a kira bayi.


Jin abinda khadija tace da sauri kalamu yace, kune dai bayin.


Wallahi badai muba.


"ke khadija ya isa haka, banason zagewa da yawa kinsan dai ummina kanuri ce koh?toh ki sassauta musu"


Dariya kalamu ya sake, shikenan Allah ya kamaku duka


Itama sumayyar dariya tayi," babu wani Allah ya kamamu nadai kwace ka kawai yaro"


Kai Aunty yaro kuma a gaban wannan yar rainin wayon?


kai wallahi ya isheka karka sake cemin yar rainin wayo, ni bance maka ba sai kai zaka fad'a mini.


Kunga ni surutun nan ya isheni haka, ibo mini abinci naci yunwa nake ji, habba kedai kullum fad'a da mutane ga kalamu yazo zai karbi Ammar.


Kai Aunty Allah suke shiga idona, tana maganar tana shiga kitchen


Zama sumayya tayi akan katifar ta, bayan khadija ta kawo mata abinci, cin abinta take koh a jikinta ta rasa me yasa ta sake jiki da kalamu sai hiransu suke da khadija, tana sa musu baki jifa-jifa in taga khadija na k'wararsa a magana, don daga gani ba sabo yayi da surutu ba, kawai yau saka kansa yayi, har suka gama cin abinci kalamu bai tafi ba sai da azahar yayi ya musu sallama ya wuce.


Yana fita bayan su sumayya sunyi sallah kayan sayayyan tasa khadija d'aukowa suka duduba, sosai khadija tayita yaba kayan don yayi matikar kawatuwa, kuma an kashe kudi kam ba karya.


Washe gari da safe principal insu khadija ya kira sumayya, akan baza'a zo d'aukar khadija ba, saboda drivern school buss insu ba lafiya, dole tasa yau khadija da kanta zata makaranta dayake yanzun tana da kudi, karywa kawai tayi tama sumayya sallama ta fita.


Takai minutes 20 a tsaye bata samu abun hawa ba, tun 7:00 ta fitoh gashi yanzun har 7:20 bata samu mota ba, gabaki d'aya ranta ya gama baci, gashi suna jarabawan second team, gani kawai tayi mota yayi packing a gaban ta, da sauri ta d'ago tana kallon wa'inda ke cikin motar, kalamu dake sanye da fararen uniform na nurses, yana zaune a kusa dame tuki, sai students na makarantan su, dake baya su biyune namiji da mace, dukansu fuskar su d'auke da zanen kanuri,sabanin kalamu da babu, murmushi tayi ta gaida mai tukin.


Amsawa yayi.


ba tare da ta kalli kalamu sau biyu ba, tajuya zata ci gaba da tafiyar ta.


In ance ma mutum bakauye yaji haushi, Amma bazai daina kauyancin ba, kinga mun tsaya a gaban ki, aikin san d'aukar ki zamuyi shine zaki wani juya kamar ana sarrafaki da remote.


Ba karamin haushi khadija taji ba, jin rashin mutunci da kalamu ya mata.


Kiyi hakuri kanwa ta, kizo mu wuce munyi late karki kulasa, mai tukin yace.


Babu wani karta kulani babayo, gaskiya dai na fad'a kalamu yace yana danna wayar sa kamar bashi yayi maganar ba.


Wallahi badon ana exam ba, yau da babu abinda zaisa taje makarantar ma gabaki d'aya, bare hawa motar su, amma ba yanda zatayi haka ta bude back seat ta shiga.


Kalamu suka fara saukewa a school of nurse, kafun aka sauke su khadija, babayo ya wuce aiki.


Wasa wasa shakuwa ya fara shiga tsakanin khadija da kalamu-wahid a boye don a gaban sumayya kam fad'a suke, don yanzun duk lokacin da yaso yake zuwa kofar sumayya, suyi hira ya tafi, duk da sumayya bata kawo kome a ranta ba, ganin cewa in yazo har falo yake shiga, kuma in suka zauna da khadija ma fad'a suke akai-akai.


Kamar yau khadija sun gama jarabawa tun Friday, zaune take a falo ita da sumayya, sai ga Kalamu yayi sallama a kofar falon su mikewa khadija tayi ta mikawa sumayya hijab nata kafun suka basa izinin shigowa, sosai sukasha hira yauma, dayazo tafiya bayan sunyi sallama da sumayya tsayawa yayi a waje get, kamar minutes 5 da fitar sa khadija ta mike zata fita a falon.


"Ina zaki kuma khadija"?


Aunty zan tattaro shanya nane naga garin da hadiri?


"Ah ah kidai tattaro shanyar, Amma garin nan kam ba hadiri bayan yanzun damuna ta wuce"


Jin Abinda sumayya tace yasa khadija sunkuyar da kai, ta fice a falon da sauri ta nufi igiya ta dauko hijab nata, tayi get, tana bude get in aiko kamar yanda ta zata inne Kalamu na tsaye, kai lafiya tun a falo sai ketket-ta mini ido kake?


Wallahi khadija magana nake so nayi dake daman.


Da mamaki da kallesa au yau kuma kunyar Aunty kake ji kome?


Ah ah ba haka bane kinsan next week zamu fara exam? so bazan samu daman shigowa ba shiyasa na kawo miki wannan, yace yana mika mata bakin laidar dake hannunsa.


Ba musu khadija ta karba hade da tambayar sa menene a ciki?


Wayace harda sim, na miki register sai muna gaisawa daidai na samu zama, don zan kwana biyu gaskiya bazan leko ba?


Kaga karbi abinka wallahi babu ruwana?


Kamar yaya ba ruwanki khadija?


Kamar yanda nace maka, so kake Aunty taga rashin kyauta wata gareta? tayi mini dukkan kyautatawa baika mata na nuna mata rashin godiyan Allah ba.


Yanzun khadija karbar wayar ce rashin godiyan Allah?


Kayi hakuri Amma bazan iyya karba ba sai dai in zaka kaiwa Aunty da kanka ka bata?


Babu damuwa muje na batan.


Ah ah wallahi ka fara zuwa dai kaikad'ai kar tace mun had'a baki, tana maganar ta koma cikin compound in tana tattara shanyar ta.


Ba musu Kalamu ya koma kofar sumayya, da mamaki take tambayar sa lafiya kuwa ya dawo?bayani ya mata akan waya ya baiwa khadija taki karba shine ya kawo mata koh khadijan zata yarda ta karba?


Da mamaki sumayya ta karbi wayar ta bude, wayane sumsung Galaxy S9+" Kalamu nima karan kaina nayi tunanin saya wa khadija waya, Amma nafi son saita kammala secondary ta mallaki hankalin kanta"


Aunty yanzun ma khadija tayi hankali fa, shekara 19 take nema wasu a shekarun tan nan ma, suna jami'a don Allah aunty ki barta ta rike wannan in?


"Au haka ta fad'a maka kenan bazan barta ta rike ba, kuka had'a baki kazo waje na koh"?


Ah ah aunty kawai dai na fahimci khadija nada biyayya ne.


"Shikenan Allah ya sanya Albarka, harda shekarunta ta fad'a maka kenan"?


Ameen Aunty Amma nidai kiyastawa nayi bata fad'a mini ba, yace cikin murna ya fita ganin Aunty ta karbi wayar, yana fita a falo yakusa cin karo da khadija dake makale a kofar falo tana sauraron su, cikin murna tace Aunty ta yarda?


Kai kawai ya d'aga mata ya wuce get ya fita, Khadija kam kasa komawa cikin falon tayi, taci gaba da tsayuwa a bakin kofa.


Sumayya dake jiran Khadija ta shigo, shuru shuru bata shigo ba, yasata mikewa fuska a had'e ta nufi kofar falon.......


*************
Jikin muhammad sai rawa yake yaje ya karbo wasu kayan, ya karbo sabon shayi, ya sake shigowa falon wannan karon tsohowar ce da yara biyun, wanda d'ayan bai manta sunan taba muhibbat sai karamar , gaida tsohowar yayi ya wuce falon sarki, Wannan karo sarkin baya falo yana ciki, aje masa shayin yayi a table ya tsaya a gefe, kusan 30 minutes kafun ya fitoh yauma kamar kullum fuska a rufe,, a take gaban Al'ameen ya soma bugawa da karfin gaske, zama sarkin yayi a hankali akan d'aya daga cikin kujerun falon, da sauri Al'ameen ya dukar da kansa a hankali ya matso da table in ya siyaye masa shayi hade da gaidashi, hannu kawai sarki ya d'aga masa ba tare da yayi magana ba.


Yana gama had'a shayin, ya fita a falon, direct kitchen in shayi ya koma, yama abokan aikin sa sallama duk da lokacin

Please Login or Register in order to submit comment