Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayan Khadija baida aiki haka zaije yayi ta yawo Koh sisi bazai samuba ya dawo Yana kame kame taliya Koh Maggi Koh indomie nake iba na bawa Khadija takaima masu shago su Saya da araha kafun mu samu na shifenen Miya,..
Duk da Al'ameen baisan Ina Saida garana ba,


karshe dai ajesa nayi nace ya fadamin me ke faruwa, dashine yanzun,duk lokacin da ya zauna baida aiki sai tunani,


Tukum yamin bayanin bashi da jari yaje tashan kayan marmari sun hanasa bashi duk inda yaje su taimaka Masa sunki,


,"Amma menace maka in Abu ya taso ta wajenka bance ka ringa fada mini ba"?


Hakane Sumayya Amma ni sai Inga Kamar ni ya dace in bukatar ki ya Tashi ki tambayi ni ba Zan ringa daura Miki nauyi ba,


"Au aini ma nufina bashi Zan baka Amma Ina ni Ina baka kyautar kudi sai dai bashi "


Duk da haka dai Sumayya....


Ban Bari ya karasa maganar Saba na tare sa "na baka bashin ne ka rufawa kanka asiri Koh na rike kudina ka cigaba da yawo ba aiki ga azumi saura wata biyu"


"Kuma bara na gaya maka in azumi yazo kayan Dadi zakana sai min Kuma kamin kayan sallah harda Khadija kaji dai na fada maka"


Toh shikenan abani yace Yana gyara zama alamun dai baida mafita,


"Ka Bari sai gobe Zan baka"


Washe gari Khadija na tura yaro yace tazo, ba'a jima ba sai gata aikanta nayi *say* *box* ta Kira mini Daya daga cikin yaran masu shagunan sai da wayoyi da laptop's suzo tare tace Masa amarya ce ni Kuma ban fara fita ba,


Don nasan in na Bata laptop innan za'a Mata cinikin wulakanci ne kawai Koh ma wani ya Mata wayo ya gudu da laptop in don nasan say box ba irin mutanen da babu a ciki,


Munyi ciniki da Mai sayan system in ganin yanda Yama laptop in cinikin wulakanci yasa nace na fasa sayar wa,


Buhun flower na dauko a kitchen Daman ban taba bude Saba nace wa Khadija taje gun Haladu tace Masa xai Saya buhun flower Zan Masa sauki,


Bata jima ba ta dawo tace min yace ta kawo flowern ya gani, Bata buhun nayi taje shagon Haladu ta sayar mini shima naira dubu bakwai ya Saya ba yanda na iyya haka na sayar Masa Amma ni Karan kaina nasan ba haka kudin yake ba,


Yayan khadija na baiwa dubu uku yayi jari na rike dubu hudu na D'an Yi sayayyan abin bukata nayi irin su pad omo sabulu na baiwa Khadija dubu D'aya, tunda har yanzun Basu gyara Mana NEPAn kofar muba don sun biya ganin mu bamu biya ba sai suka yanke wayar kofar mu Khadija na baiwa dubu daya ta mikawa bappa sulaiman kudin wutan NEPAn mu aranan sukasa aka hada mana wayar aka gyara, na baiwa Khadija dari biyar itama πŸ˜‰




Haka rayuwa tayi ta tafiya Rana ya wuce sati ya shude yau Dadi gobe Akatsen sa har Muka cika wata Daya da sati biyu da aure, ba abinda ya taba shiga tsakanin mu Koh da kuwa hada gado ne, in munkwana waje D'aya toh ana zafi munyi kwanan waje ba nepa,


A y'an kwanakin nan na fara fuskantan matsen rayuwa Wanda ban Saba ba,


Dole sai abinda ya samu zamuci wani sa'in ma in Bai samo kome ba haka zamuci indomie d'anye wani a dafe da ruwa, in ya samu D'an ciniki Kuma muci shinkafa da Mai da yaji,Inda Allah ya sumuma garana Bai kare ba akwai taliya Mai Maggi kefe shinkafa, Amma duk da haka na D'an fada na chanjin yanayi, saboda yanzun ya hanani Saida Kayana don har Yan unguwa sun fara gulman ya kasa rikeni Kayana nake sai dawa,maganan har kunnen da yashiga shiyasa ya nuna mini baya so ,


yau na shirya da niyar zuwa gidan Goggo Amina, da gidan mu tunda safe na kammala aikina yau mun Sami kudin kayan shaye mukasha da safe' bayan ya fita na kammala aikina dake na sanar dashi Zan fita gidan Goggo Amina ( marikiyar Khadija ) Zan bi gidan mu d'uka Bai Musa ba saboda mun Riga munyi maganar dashi, dari da hamsin ya bani kudin Keke,


Khadija zata rakani kasancewar yaune Zan fara fita, unguwa tunda nayi aure bayan asibiti ba inda naje,


Sai goma Khadija tazo lokacin na fitoh wanka, Muka gaisa ta shiga Wanka Dayake tun jiya ta zo ta guge kayanda zatasa d'aya Daga cikin Wanda nake Bata,


Shiryawa nayi cikin lufaya Mai tsada fari Mai Flowers brown NASA riga long sleeve brown NASA takalmi fari na dau jakama fari fuskata ba kome sai powder da man baki, Khadija dake gefe na tsaye baki bude tana kallona,


"Rufe bakin ga guda zai wuce ciki"nace Mata cikin murmushi Mai karawa fuskata kyau,


Hmm Aunty na gaskiya ke Mai kyauce Allah ne kadai yasan dalilin da yasa ya bawa yayana wannan k'yakk'yawar hallintar nan Ina ma Yana kallo yaga yaran da za'a Haifa Masa πŸ˜…


Murmushi kawai nayi bance kome ba don na lura ita ta yara ma take,


" Khadija kiye sauri kisa kaya don Allah na masu na ganni a gidan mufa Naga abie na"


Toh Aunty tace tana saka dogon riganda na taba Bata,tayi shafe shafen ta tana Gama shiryawa, Muka fita"


Yaune rana na farko Dana taba karewa unguwan sintali kallo unguwa ne da ya hada ruwa biyu masu kudi da talaka wa Yan kasuwa da ma'aikata da masu zaman banxa unguwan nada kyau sosai da fasali,..


Gidan Goggo Amina mukaje da kafa ,


Mun samu tarba Mai kyau ba laifi matar nada kirki sai dai na Lura ita mace ce da Bata shiga abinda Bai shafe taba Sam babu ruwanta,mun D'an jima a gidan kafun Muka Mata sallama na aje Mata laidan Turare Wanda na d'auka a kayan aure na,


ta rakomu har waje Muka tare keke napep ,


Hajiya Ina kukayi? Ya tambaye ni


"Specialist" zaka kaimu,
Ku hau muje yace,


Dukan mu Hawa mukai yaja machine insa muka nufe unguwan specialist,


Muna shiga unguwan mu na Masa kwatancen inda zai sauke mu,


"Yana sauke mu na tambayi sa "nawane kudin ka"


Naira dari da hamsin kudin ku kubiyu,


Sai a lokacin na tuna dari da hamsin inne a jikina kacal Wanda yayan Khadija ya bani Allah dai yasa abie na gida nasan zamu samu na dawowa don karyan mu taka da kafa daga specialist zuwa sintali,
biyansa nayi muka nufi kofar gidan mu


Khadija mutuwar tsaye tayi ganin wani irin gida Mai bala'in kyau Wanda Koh a mafarki Bata taba ganin irin Saba Daman ita ba yawo take ba iyya kacinta kasuwa sai unguwowin kusa da sintali irin mafindi unguwa gadi da sauran unguwowin kusa da unguwan su,


Amma Bata taba zuwa unguwa Mai nisan nan ba sai dai tanaji a bakin Asma'u sunje unguwan specialist Koh millionaire's sweet in suna Bata lbrn gidajin unguwan sai taga Kamar tatsuniya suke Bata bata taba zaton haka gine ginen unguwan yake ba Wai duka wannan a cikin Jala yake?


***Harna nufe get Amma sai naji Kamar ba Khadija a gefena juyawa nayi me Zan gani Khadija an sake hanci baki ido ana kalle kalle zuwa kawai nayi na jaho hannunta, sai a lokacin ta farga da kauyancin da ta nuna


Cikin Jin kunya tace Aunty wallahih unguwan nan yayi kiga gidan da zamu shigan nan Kamar aljannan duniya,


Kai Khadija kin cika shirme wallahih mu tafi nikam,


**Get Muka nufa Mai girman gaskiya kamar get In gidan prison haka ma ginin gidan dogayene sosai anyi penti fari get in ma farine k'wank'wasa,makeken kofar get in,nayi


Wani farin buzune ya leko ganina yasa ya washe bakinsa cikin hausar sa da baya fita yake cewa laaa Amarya Kaine hajiya Sumayya wallah nayi kewanka shannu da zuwa lale lalema barkama lale ya fada Yana bude mini get muka shiga,


Shiga cikin gidan mu ya sake ruda Khadija ganin filin gidan mu filine babban bana Wasa ba Wanda yakai girman wani karamin unguwa,ga shuke shuke na Flowers ya kewaye gidan Wanda ya kara haska gidan sosai ga parking space babba Mai dauke da mototi na alfarma wanda akalla zasu Kai talatin duk ciki bamai araha,




Nidai Ina rike da hannun Khadija Muka nufi wani babban part Wanda duk fadin gidan part inne kawai ba wasu Amma daga ganin part in kasan ba karamin duniya bace a ciki ganin shima ginine na gidan sama Mai Hawa uku,babban kofar falon NASA hannun na na bude da sallama a bakine duk da banida tabbacin za'a ji,saboda girman falon,


Khadija Kam mutuwar tsaye ta sake tayi ganin cikin falon gidan mu,


Kusa Kai mukayi cikin falon falone Mai girman gaskiya Wanda ke dauke da kujiru set biyar ga babban plasma na alfarma Kai fadar tsaruwar falon gidan mu Bata lokaci ne na barwa readers su keyasta,


Babban falon gidan mu Yana dauke da d'akuna kusan Sha biyar haka upstairs shima dakuna goma Sha biyar ne Hawa na uku ma haka,Amma duk yawan d'akunan gidan munan falon mu dayane shine falon kasa, Wanda Koh a Hawa na uku kake kana hango falon,


d'akunan kasa na samarine sai kakarmu dake zaune dasu a kasan Wai tana saka musu ido injita, dakunan Hawa na biyu na iyaye ne Hawa na uku shine na Yan Mata da d'akunan yaran gidan da sukayi aure maza,suna zaune da iyalansu ,..


duk yanda Zan fasalta muku gidan mu saifa na rage wani abin,


Kaf gidan mu da colour D'aya aka kawatashi da white colour sai surkin baki Kama daga kujiru labule Abubuwan da aka kawata gidan kome farine daga sama har kasa abin sai Wanda ya gani,


Jama'ar gidan mu duk Muka samu a falo da yake yau weekend ne ba aiki ba makaranta kowa na zaune wasu na kallo wasu na Danna waya wasu na Danna laptop yara na wasa wasu abinci suke ci ganin mu yasa dukansu barin abinda suke suka zuba Mana ido Kamar yau suka fara ganina,tunda Khadija ce Basu sani ba,


Idanuna ne ya sauka a Kan kakata dake zaune tanacin kefe sai uncle's nawa dake zazaune wasu na cin abinci wasu na Hira wasu na duba takardu,


wani abune ya tsayamin a makoshi Mai kamada Takaici sun aurar Dani Basu damu da rayuwar da nake ashan ba gasuna suna zaunen su Kamar Basu San wata Sumayya da aka bawa MAKAHO ba Basu neme sanin ya rayuwa ta kare ba waima me dalilin auran Dani ne tunda gasu Aunty miemie sun girme ni nesa ba kusa ba Amma saini kadai aka aurar auren ma da MAKAHO ba lafiyaye ba,Koh don anga mahaifiyata Bata gidan ne Kai Koh mahaifiyata Bata gidan ai ubana nanan


Koh da kowa zai nuna Mini kiyayya dada zata sassauta tunda ita ta haifi babana amma Ina abin ba sauki,


"Ina kwana dada,"nace Ina zama a cikin Daya daga cikin kujirun falon,




Toh matan miskinai ne agidan namu yau Koh idonane,?


Ah ah Kaka ba idon ki bane kinsan azumi ya karatoh anzo amsan zakkah ne,


Hhhhhh Kai miemie baki da dama Amarya ce fa tazo ganin gida mutun da gidansu kece yazo karban zakkah,kubra ke fada tana dad'a tunsirewa da dariya


Waiku yaran nan wasu irin Yan iska ne me yasa baku da mutunci shegu kawai ai gwara ita tayi aure Koh?


Keee koh miskini kin samu yazo wajen kine da sunan aure, a cikin ku waye ta samu miskinin na zuwa wajenta,Yaya Abdu ya fada ransa a bace,


Ai itama ba zuwa yayi ba lika Masa akayi,miemie ta basa amsa,..


Rufe mini baki karna ci ubanki Yar iska Abdul yace Yana mikewa,


Ai duk laifin dadane Sam bansan me yasaba, Dada (kakar mu) itace babba Amma ita ke sasafo Mana bala'i yaya kabiru yace Yana maijin takicin ahlin gidansu,


Abubakar kanajin abinda shegen yaron Kan nan kabiru yake shimin mutunci kayi shuru kana kallonsa,,,


Kiye hakuri Dada Kai kabiru zanci kaniyarka fa inka sake shiga abinda ba ruwanka uwarka aka zaga Koh me da zaka saka bakinka a ciki,


Mikewa Kabir da Abdul sukayi sukabar falon,


Ganin yanda aka Mai Dani Kamar kashi ba Wanda yabi ta kaina kowa na Harkan gabansa


Ganin Banga Abie na a cikin falon ba yasa na mike nayi hanyar upstairs na nufi d'akin sa nabar Khadija a falo wance ke rakube Kamar ace kitttt ta ruga,


Bude kofar d'akin nayi nasa kaina na shiga Abie nane zaune a kasan tiles Yana duke da Kai sai momy (yadikko na) zaune a bakin gado daga Gani dai magana suke..................






πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣
Shigowa d'akin nayi cikin hanzari na karasa kusa da abie na banyi wata wata ba na rungume sa na fashe da kuka maicin Rai,,,,


Ji kawai nayi momy ta dakawa abie tsawa,


Kai Abdulsalam mainace maka akan yarinyar nan?,


Ai da sauri Naga Abie ya hankad'ani a jikinsa ya mike tsaye cikin wani irin hada fuska Wanda. Bansan abiena dashi ba Naga ya mike cikin hargage yake magana Sumayya fita a dakin nan banason ganin ki banace Miki bake bani ba Koh bance ki zauna a dakin kiba,


"Abie Kai nazo gani don Allah Abie Koh kowa zai juyamin baya Kai karka Bari a rabamu don Allah Abie," nace Ina fashewa da kuka,


Waye uban naki?? keh daga yau niba ubanki bane bansan wata y'a Sumayya ba kaf zuriyan shugaba babu yarinya Mai suna Sumayya ki fita a gidan nan da zuriyan mu bake bani Koh mutuwa nayi banason ganinki akan gawata,yace idanunsa na taruwa da hawaye daga Gani dai maganar fatar bakine bana zuciya ba,


"Amma abie menene nai maka da har zaka yanke dukkan alakar ka Dani har haka atunani na Koh kashe mutum nayi bazaka yanke alaka Dani ba abie ka rabani da mahaifiyata tun bansan kaina ba yanzun Kuma ka sallamawa duniya ni" wa nake dashi in ba kaiba kaf duniya nan abie why Abie why"😭😭??


Nafada Ina kallonsa gani nayi hawaye nabin fuskar sa,ya daga ido Yana kallon momy,


Toh munafuki kallon me kake mini,Ke Kuma wuce ka sata a gaba tabar Mana cikin gida yanzun,


Nikam mutuwar tsaye nayi nashiga uku yaushe abie ya zama haka zaushe ya koma yaron momy,abie da na sani ne kuwa kafun na bar gidan nan Koh maganar banxa momy Bata Isa tamin a gabansa ba bare yau har tana basa umurni ya koreni,


Ban farga ba naji an janii kiiiiiii!!! Anyi hanyar steps Dani,


Cikin mamaki nake kallon abie yau ni yake ja Kamar wata saniya zai koreni a gidan sa lallai fa,


Jana yake tayi har Muka sauko falo abin gwanin tausayi,nikam kuka nake Kamar Raina zai fita gabaki d'aya naji duniya tamin zafi,
Ganin abie ya nufi kofar fita falo Dani yasa Khadija tasowa ta biyomu a baya Yan falonka da ido suka bimu wasu na dariya ganin yanda uba ke fincikar yarsa


Fincike hannuna nayi na dawo cikin falon na tsaya a gaban babuji (kanin babana) " babuji abani ducument Ina, Ina bukatar su,"




Don ubanki lokacin da uwarki ta haife ki da results ta haifiki ne,,,,,




Don haka baza'a bayar ba koma bara ma kiji daga yau Koh a kasuwa ne karki sake hada sunanki da family shugaba,


"K'warai kayi gaskiya babuji ba'a haifini da results ba Amma da kudin ubana na same su in Kuma hassadace yasa kuka k'wace karfa ku manta arziki nufin Allah ne in Allah ya tsaga da rabonka sai kayi arziki ruwa da iska Koh guguwa bazai Hanaka samuba",


"Ba karatu bane kadai abinda ke sa bawa arziki rabonsa baya wuce kansa"


"Baiwa ta jarina"sannan wannan tsinannen gidan naku wallahih ku rubuta ku aje sai yafi muku prison ganin..................


Tassss naji saukar wani azabebben Mari a kumatu na Wanda yasani sumar wucen gadi,ba kowa bane yamin Marin nan sai sahabi yaron babuji,


Ke karamar Yar iska watoh kema harkin zama Yar bariki irin mutanen gidan da kike Koh zakizo nan ki gwada Mana kin falle toh baki Isa ba ki tsaya kina gayama ubana magana in barki ya fada Yana fincikata juyawa nayi Ina kallon abie Wanda ke tsaye kansa a duke,


Bai tsaya aku Ina Dani ba har Saida ya dangana da get turani yayi waje Yana ma Mai gadi warning daga yau in ya sake barin Mai Kama Dani ya shigo gidan nan a bakin aikin sa,Yana fadan haka ya juya abinsa yayi cikin gida, ya dauko jakana da takalmi ya watso mini a jiki,


Baba buzune ya fitoh yazo inda nake zaune tunda ya jefoni ban matsa ba mamaki tsoro da kuma wani irin tsana naji ya tsargan mini na family mu duka ban cire kowa ba, aciki nayi alkawari daga yau na yanke duk wata alaka da shugaba family house,


Kayi hakuri yaro haka rayuwa take kaji,
kayi zaman auren ka ka rike mijinka Allah zai baka mafita kaji hajiya Sumayya,kayita addu'a kaima Allah ya tsareka gidan nan yanzun sai abinda matar babanka yace,
ya fada cikin tausayi,nidai Ina duke dakai sai kuka nake inda Allah ya Soni ma unguwan mu ba irin sintali bane nan kowa na cikin gidan sa Babu mutane a waje,


Jin ana kamani anason mikar Dani yasa na daga kaina Khadija ce wance bansan yaushi ta fitoh ba ,Ashe tun Marin da aka kwada mini ta ruga tayi waje tazo ta Saya,...




*******""""


Banyi musu ba na nike tsaye Kayana ta hau karkade mini nidai sai kuka nake Kamar zararriya gashi bamuda Koh sisi da zamu tare abin Hawa ya kaimu gida gashi Koh a gidan ma bani da kudin da Zan biyasa Kuma banda tabbacin yayan Khadija na dashi, yasa na Kama tafiya da kafa Ina kuka,


Dukawa Khadija tayi ta dauki jakana Dana Bari,sai hakuri take bani Amma nai Mata banza a haka muka fara fasa hanya,


Mota na gani Tasha gaban mu tayi packing Abdul ne ya fitoh a ciki ya nufe mu,


don Allah Sumayya kiye hakuri da abinda kikaje Kika tarar a gida wallahih yanzun gidan mu sai addu'a abin sai gaba gaba yake, Kuma na rasa me yasa duk gidan mu ke suka tsana,


*****Kala bance Masa ba don shima wani tsanar sa nakeji a Raina Sam yanzun naji banason ahalina kwata kwata na yanke duk wata alaka dasu daga yau Kamar yanda Suma suka yanke Dani,


***Kaucewa nayi na fara tafiya bance Masa kala ba,


Biyo ni ya sake Yi Yana mini magiya, Sumayya don Allah badon ni ba kizo ki hau na kaiki gidanki Kinga yamma yayi bazaki samu Keke napep ba anjima anan,


Wallahih Abdul Ina Ganin kimarka Inka kuskura ka kaini bango Zan maka abinda bazaka manta Dani ba Kai asuwa zakazo ka tsaya kana bani umurni wallahih daga yau Babu ni Babu Kai Koh a hanya ban sanka ba na tsaneku mugaye kawai azzalumai wallahih ku jira karshin ku,




Habba Sumayya menene laifina in sun Bata Miki ni meyasa Zaki had'a Dani,..


"Ai Wanda suka Bata mini su waye ne a gunka"?na tambaye sa Ina kallon sa ido cikin ido,


Iyayen mune da Yan uwan mu,ya bani Amsa,


"Iyayen kadai da Yan uwanka daga yau bana D'aya daga cikin family shugaba in baka sani ba ka sani yanzun ka fita harka ta "


Sumayya kada bacin Rai yasa ki ringa furta maganganu da Basu dace ba,




"Na furta Abdul Koh kaima dukana zakayi" na fada Ina wuce sa


Shikam mamaki ne yake son kashesa Anya Sumayya da ya sani ce wannan shuru shurun ashe haka take ganin bazata yarda tahau motarba yasa ya zare kudi a Aljuhunsa ya mikawa Khadija gashi Yan Mata kuhau Keke Koh ya fada Yana duban Khadija,..


"Wallahih Khadija Kika karbi kudin nan sai na nuna Miki true colour na"


Khadija Kam ta tsorata da sauri tayi gaba kamar yanda taga nayi,


Muka barsa a tsaye kamar gunki,




Tafiya muke har lokacin hawaye baibar zuba a. Idanuna ba wani irin zafi nakeji a Raina a haka muka ringa fasa unguwa unguwa muna wucewa tafiyarda tunda nake. Bantaba yin irinsa ba yau shi nake kafafuna duk sun kumbura na rashin sabo, Amma yanda zuciya ke cina Bai bare naji wahalar ba, Khadija kam Koh a jikinta,




Har mangariba yayi bamu ma kusa Isa sintali ba


Aunty Koh zamu tare kekene in munje gida Yaya ya biya Kinga fa mangariba yayi ga hadari sosai? Khadija tace


Kala bance Mata ba tafiya kawai na cigaba dayi don nasan Koh na hau munje bazamu samu kudi ba tunda cinikin nasa duka ya hada ya bani Ina zai samu wasu dari da hamsin,


Tafiya mukaci gaba dayi ga yunwa don rabona da abinci tun ruwan shayen safe Amma bacin Rai baisa naji ba har aka Kira Isha adaidai lokacin aka fara yayafi sai ruwa ya sauko Kamar da bakin k'warya ganin mun iso bakin kasuwa yasa ban tsaya wani labewa ruwa ya dauke ba tunda dare ne Babu Wanda zai gane mu gashi NEPA sun dauke a haka ruwa na dukan mu muka shiga sintali hanyar gidana muka nufa tun daga nesa Muka hangesa




Al'ameen ne a tsaye a kofar gida ruwa na dukansa daga ka gansa kaga Wanda hankalin sa yake tashe,


Muna Isa Khadija ce ta fara Masa magana nikam cikin gidan na nufa don bana bukatar Jin kome,


Yaya ya Naga kana tsaye a cikin ruwa haka gashi duk ka jika lafiya Kam?


Ina Naga lfy Khadija baku dawo ba Ina Aunty take Allah dai yasa Yan gidan su basuce bazata dawo ba wallahih naji tsoro Khadija karsuce zasu rabamu?




Hhhh habba Yaya bafa wani abu da zai rabaka da matarka insha Allah sai mutuwa Kama daina mugun tunani irin wannan,


maganan dadewa Kuma abin hawane bamu Bamu ba da wure, shiyasa naso ma mu kwana Amma Aunty tace mu dawo kar hankalin ka ya Tashi(Tamar karya don ya kwantar da hankalin sa)


Shap in kuka kwana ai nashiga uku kenan ,


Amma me yasa baku Kama hanya da wure ba kuka bare sai yamma kuka fitoh,gashi ruwa ya muku duka,


..Kai Yaya abinci fa muka tsaya muka ci,
Yauwa Yaya kasan me yau ran aunty a bace yake don Allah ka bita. A hankali inda Hali ma karka Mata magana yanzun ka Bare sai da safe ka Mata magana in ma kaga change a tare da ita ka Mata uzuri,


Meya faru Khadija?


Ba kome Yaya kawai dai sun D'an samu matsala da yaran gidansu ne sai Randa ya baci,




Bai yarda ba don yasan halin Khadija akwai surutu akwai boye abinda ba'a sata fada ba,shiyasa kawai ya shanja zancen,


Toh khadija muje ciki in ruwan ya tsakai ta sai na raka ki gida


Ah ah Yaya dare yayi fa yanzun ana neman 8:00 na dare nikam Zan koma Goggo zatayi fada,


Muje na rakaki gida sai nama Goggo bayanin dalilin jimawar ki karta Miki fada,


toh yaya,ta fada tana Kama hannunsa suka nufi layin su Goggo Amina,


Nikam Ina shiga cikin gidan da yake ana ruwa ba kowa a tsakar gida shashen mu na nufa,aje jakana da takalmi nayi a baranda na kwabe lufayar jikina da yajika jakaf da ruwa na makala a igiya,
dakin na shiga nadau towel na daura na zame dogon wando da NASA da under wear na makala a igiyar kofa ,


Kitchen na shiga na kunna gas na daura bojuwa (tukunya) na zuba ruwa a ciki,boket na dauko na ibi ruwa a Randa na tsaya a cikin kitchen in ruwan na tafasa na juye a boket in daidai yanda zanyi wanka na dauki boket in nayi bandaki,wanka nayi na fitoh,har lokacin

Please Login or Register in order to submit comment