Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama a yan uwansa sun rasa ransu, a rikicin da ya afku.


Bayan kome ya daidaita, shugaba ya saida duk wani kadara nasa na kauye wanda mahaifinsa ya mutu ya bar masa, don shikad'ai babansa ya haifa namiji sauran matane kuma duk sunyi aure, ya dandanka musu nasu gadon.


Jalingo babban birnin jahar Taraba, ya tattara iyalansa suka dawo jalingo, gida madaidaici shugaba ya saya, yasa yaransa a makaranta, dada tana kula dasu kamar y'ay'anta na cikin ta, sam bata nuna musu banbanci da nata duk d'aya ta d'auke su, wannan abin shiya kara dasa soyayyar ta, a zuciyar mijinta.




Bayan wasu shekaru kudi sosai ya fara zama a Aljuhun shugaba, don business yake na manya manyan shaguna zanunuwa a kasuwa yana order daga kano, aje aje yakoma na mototi, Arziki kullum gaba gaba yake ga yaransa na makaranta, duk wanda ya gama secondary, kwasar waje yake turasa karatu.


Lokacin da yaransa suka fara nisa a boko , hakan yasa ya sakar musu wasu kud'ad'e su gwada tasu kasuwar, babuji da Abubakar sune suka fara kammala karatu, suka fad'a business abinka da yan boko, kuma kwararu a bangaren business, kankace kome kudine ya zauna company suka kafa mai zaman kansa, tare da haden gwuwar junan su, sosai arzikin su ya fantsama.


Babuji da Abubakar a rana d'aya sukayi aure , wasu yaran jalingo suka aura wa'inda suka hadu a makaranta, bayan auren su, saida suka haifi yara bibbiyu, kafun gaddafi da Usman sukayi aure.


Abdulsalam ya kammala karatunsa Amma sam yaki aure kaman yan uwansa, duk yanda iyayen sa sukaso yayi sai abin yaki, dada har magani take saka masa a abinci koh Aljanane ta aura mata yaro, Amma ina shuru abu yaki kowa aka nuna masa yace baya so, bata masa ba hardai su gaddafi suma suka hayayyafa sosai , a lokacin yaran babuji biyar, na Abubakar uku, yaran gaddafi biyu, na usman hudu.


Bayan wasu yan shekaru shugaba ya kwanta ciwo, baiyi wani dogon jinya ba Allah ya karbi rayuwansa, gadon da aka raba musu shi suka had'a suka gina katafaren gida a unguwan specialist, gabaki d'ayan su suka tattaro kan iyalansu suka dawo cikin gidan da zama, don a lokacin Babuji da Abubakar suna da company kansu har biyu, yayinda gaddafi yake aikin goverment, usmanu d'an siyasa ne, Auta Abdulsalam shi ma'aikacin Bank ne(Accounter)kasance warsu rikankun yan boko ga naira ga kyau, kowa yasan yanda fulanin gembu keda tsananin kyau.


Rayuwa ake a cikin shugaba family house mai kyau, daban sha'awa, mazan basu bawa matansu daman da zasu kawo musu tashin hankali ba sam, koh kara kika kaiwa mijinki matar wansa ta miki kaxa, had'a meeting ake a kira kowa, ku maida maganar hakan yasa matan sam suka daina fad'awa mazajen su, saidai ayi iyya mata da mata kasa kasa.


Auren Abdulsalam ne yaxo musu da sabon salo, saboda yarinyar da ya kawo akan ita zai aura, yar maiduguri ne Amma tana karatu a TSU, tazo bank inda yake aiki cire kudi, Allah ya had'asu kanuri ce, hakan yasa dada tace ita sam bata yarda da auren nan ba, bazasu aure babarbariya ba, abinda ya xamo cecekuce a gidan kenan, duk yanda Abdulsalam yaso fahimtar da ita son da yake ma yarinyar, abu yaci tura sam taki Amince wa katafau tace bata yarda ba, shikuma Abdilsalam yace muddin ya rabu da Hafsa toh shikam bazaiyi aure ba.


Aijin haka yad'agawa dada hankali don tasan sarai halin Abdulsalam, akwai kafiya kamar me, tayaya ma aka samu ya samo hafsar kullum yace yakusa aure shuru baiyi ba, bare yanzu yace bazaiyi ba ai magana ta lalace.


Babu yanda ta iyya da banbakin su babuji ta Amince da auren hafsa, har maiduguri akaje da zancen auren.


su karan kansu iyayen ta sunso gardama amma ganin sannanen family ne, yasasu karbansu da hannu bibbiyu, tare da kafa sharadin yarsu zata cigaba da karatu insun amince, zasu basu ita?


Amincewa kam sunyi saboda kaf gidan shugaba yan boko ne, hatta matan gidan na zuwa aiki, rainon yara ma dada keyi da masu aiki.


BAYAN AURE
Hafsa fa ta fara fuskan tan banbancin launi a gidan su Abdulsalam, kasancewar ta baka kuma kanuri, sabanin yan gidan shugaba farare ne, daga matansu har maza da yara gasu fulani kyawawa, don Abdulsalam baza'ace kyaune ya rud'asa akan hafsa ba, ah ah sonta ne kawai Allah ya diga masa a zuciyar sa yaji baya ganin kyaun kowace mace sai nata, sosai ake nuna mata banbanci kuma ba wanda ya fara asasa hakan sai dada, haka zasu zauna suna hira daga sun ganta zasu koma yi da yare basa janta a jiki, inta matso garesu basa sonta rabesu sam, kansu a hade Amma ita sun ware ta.


Hakan dasuke, yama hafsa zafi, yasata watsar da kowa na gidan, ta kama karatunta daga ta dawo makaranta ta shiga kitchen tayi girkinta, zata haura upstair's, ta shiga d'aki bata fita sai mijinta ya dawo.


Abdulsalam yasha had'a meeting da korafi akan abinda akema matar sa, duk da bata fad'a masa ba, yaga alama yayunsa mazane kad'ai ke sonta.




A haka fa abu yaki chanjawa abubuwa sai cigaba suke a haka, hafsa zaman hakuri take a gidan, babu zagi babu duka, Amma ana nuna mata mugun hali kam, a hakan cikin hukuncin Allah ta samu ciki, wanda kaf gidan babu mai farin ciki sai ita da mijin ta da yan uwan mijinta, amma babu ruwan matan dasu dada da ita, gashe cikin yazo mata da laulayi, bata iyya aikin kome, kuma babu mai taimakon ta, karshe dai Abdulsalam d'aukar hutu yayi a bank ya zauna a gida yana kula da matar sa, amma abu yaki karshe dai kiran iyayen ta yayi aka turo masa kanwar hafsa, tazo ta zauna da ita har cikin ya tsufa bata koma ba.


Wata ranan Alhamis hafsa ta tashi da nakuda tsakar dare, Abdulsalam da kanwar hafsa ne, suka kaita asibiti don baiko sanar da yan gidan tana nakuda ba, hospital aka kaita kafun asuba Ta santalo yarta kyakkaywa fara tas, jinin gembu mai tsananin kama da zuriyar gidansu, koh kama da hafsa batayi kome na babanta ne.






Sosai Abdul yayi farin cikin samun wannan baby, ga wani irin sonta daya ke sosai yaji son babyn sa, washe gari ne yan gidan suka tashi sukejin labarin haihuwar a bakin mazajen su, Dada da matan sunje asibiti bada son ransu ba, saidai ganin yanda Abdulsalam yahad'a wa kowa fuska, gaisuwa ma dada kawai ya gaishar, ya shiga yad'auko kayan baby ya fita, hakan yasan su zuwa duba baby.


Ba karamin dadi sukaji ba ganin yarinya kamar su ta biyo, bama kamar dada a murna, zama tayi a asibitin taki tafiya ita kema yarinya wanka, duk da yar uwar hafsa tazo washe gari Amma dada ta karbi kome na baby, harsuka koma gida dada fa na leke da yarinya, ranan suna yarinya taci sunan dada sumayya ana kiranta da momcy, haihuwar sumayya shine musababin zaman lafiyar hafsa, sosai taga change agun dada haka ma matan gidan, sosai suka koma damawa da ita, itama bata rikesu a rai ba, a sannu sannu har itama ta fara jin fulatanci duk ta maida martani na bata wuya, amma babu abinda zaka fad'a da fulatanci bata sani ba, dayake gidan sosai suka rike yarensu, suna hausa Amma ba sosai ba.


Sumayya(momcy) tana da shekara hudu Abie inta ya shigar da ita makaranta, lokacin hafsa(ummi)ta kammala karatunta na jami'a ta fannin koyarwa, taso kara gaba Amma abie ya hana, aiki yasama mata na koyarwa a makarantar secondary, wannan kenan.




Sumayya na cika shekara biyar kanin Dada Allah ya masa rasuwa a gembu, dukansu sukaje taziya, bayan sadakan bakwai dada ta d'auko yarsa daya haifa guda d'aya, mai suna safina(momy), bayan dawowar safina family shugaba, sai abubuwa suka fara bullowa saboda tunda safina ta shigo gidan shikenan ta fara likewa Abdulsalam(abie)duk wani iyayinta abie baya kulata, asalima sai ya daina zaman falo kwata kwata koh abinci ne saidai suci da ummi a d'aki, abin har yakai ga dada ta lura da hakan, sosai ta nuna masa bacin ranta akan yana nunawa safina mugun hali don tana zaune a gidansu.


Zama ya fara rashin dadi lokacin da safina ta fitoh karara tace ita abie take so, sam abi yaki zancen kuma ya nuna bazaiyu ba, ummi karan kanta a lokacin ba karamin bakin ciki taji ba, don gwara tayi kishi da kowa akan safina, irin yaran nan ne shegun kauye masu shiga idon mutane, gashi batada kunya sam.


Dada fa ta tuntube abie akan zancen ya nuna bazaiyu ba, hakan yasa dada bata tilasta masa ba ta watsar da xancen, abinda ya konawa safina rai kenan, kaf gidan babu mai supporting nata, kowa ya nuna baya goyon baya akan zancen, harda matan babuji basa sonta.


Safina makaranta aka saka ta na islamiyya, don sam taki zuwa boko duk yanda akayi bazata ba islamiyyar ma daker ta fara zuwa, zuwan ta islamiyya shiya had'ata da kawa nafisat, nafisa irin yaranan ne watsansu marasa jin magana, haduwar su da safina, yasa nafisa nunawa safina abubuwa da yawa, ta kara kangarar mata da kai, bata tsoron uban kowa.


Abin yayi matukar d'agawa dada hankali duk yanda taso rabata da safina abin ya gagara, gashi a lokacin nafisa bazawarace harda y'a d'aya take dashi, hakan yasa dada mawa safina barazanan zata maidata kauye, amma safina koh a jikin ta, ta nunawa dada koh ta maidata kauye tasan hanya, duniya da fad'i.


Bayan wata uku da haduwar safina da nafisa, lokacin sumayya nada shekara 6 a duniya, hafsa ta fara ganin change a zaman su, sam yanzun zaman ba dadi tsakanin ta da mijinta, kullum cikin rikici suke wanda itama karan kanta batasan dalili ba, sosai abin ke damunta, wasu lokacin har Abdulsalam na dukanta, Amma bata taba fad'awa iyayen ta ba, koh wani nata saboda tanason mijinta, sai kawarta wance suke karantar wa a makaranta d'aya, don lokacin kanwar ta da aka kawo mata lokacin cikin sumayya tayi aure, batada wani nata kusa.


Yau an waye gari da wani masifa a gidan shugaba, amma dada satan sarkan gwal inta, sosai tayita masifa tana zagin yan aikin gidan wance ke mata gyaran d'aki kamma koranta akayi, koh sati ba'a kara ba aka sake ma hajjo(matar babuji) sata, ba'a kama barawon ba, haka aka ringa sace sace kusan wata har rashin yarda ya shiga tsakanin juna, kowa na zargin d'an uwansa, ba yan aiki kad'ai ba.


Kamar yau aka sacewa Matar abubakar agogonta na demond, yau kam masifa aka sake akan sai anbi d'aki d'aki anyi bincike, sai an fitar da barawon don kaf gidan tunda safe babu bakon daya shigo koh ya fita, kuma kowa na gida ranan don weekend ne.


Bincike aka ringayi har akazo d'akin hafsa, kamar a mafarki aka ga agogo da wasu sarkoki na dada a cikin wardrop na ummi abinda ya kawo cece kuce dacin mutuncin hafsa a gidan.


Daman mai hakuri bai iyya fushi ba don ita da iyya gaskiyar ta, bata d'auki kome ba yama za'ace a iyya tsawon zamansu bata taba sata ba? sai yau sannan ita aitafi karfin sata tunda bayar matsiyata bace ita, sosai ta fara maida martani kowa ya gaya mata bakar magan fad'a masa take ita ma, ana cikin haka abie ya dawo daidai lokacin dada ke zagin hafsa, ita kuma ta gaya mata bakar magana, daman tun asali bata son zaman ta da d'anta, shiyasa ta had'a baki aka lika mata sata.


Abie babu tambayar ba'asi yaja ummi d'aki ya rufe, duk da sumayya yarinya ce, amma a ranan tasan gidan shugaba sunyi ma mahaifiyar ta ba daidai ba, duka abie yama ummi kamar zai kasheta daker aka kwaceta.


Cikin kuka ummi ta kira kawar ta a waya don ta tsorata lokacin, ganin jini nabin kafafunta, bayan zuwan kawarta, asibiti ta kaita ashe karamin cikine da ita wanda likitoti suka tabbatar daya zube, ga rauni kota ina a jikinta, wayar hafsa kawarta ta d'auka ta kira iyayenta, ta fad'a musu duk abinda ke faruwa tun zaman hafsa a gidan, kamar yanda hafsar ta taba fad'a mata.


A ranan mutanen borno suka diro Taraba, cikin tsananin bacin rai, direct hospital suka dosa, duk da isan dare sukayi, ganin halinda hafsa take ciki abin yayi matikar musu ciwo sosai, kotu suka maka abie Amma ina abin ya gaggara saboda iko da kudi da abie suka fisu dashi a jalingo, hakan yasa shari'a taki bima hafsa hakkinta, karshe dai mahaifinta yayi rantsuwa hafsa bazata zauna da Abdul ba, saiya sakar masa da yarinyarsa, ba jinkiri agun abie ya saketa, ya basu takarda a hannu, wannan ciwon yasa mahaifin hafsa yace koh bayan ransa baiyarda hafsa ta kuskura ta sake taka gidan shugaba koh da wasa ne babu ita babu sumayya, ta manta ma ta taba haifar y'a, yajama abie kunne mundin ya taka kafa a gidansa koh sumayya , zai nuna masa ikonsu a maiduguri.


Wannan shine dalili koh ince musababin rabuwar sumayya da hafsa, su karan kansu yan gidan basuso sakin hafsa ba duk da abubuwan da ta sace musu, Amma bakin Alkalami ya bushe.


Bayan tafiyar hafsa sosai sumayya ke kewar mahaifiyarta, kullum haka zatayi ta kuka a kaita wajen ummin ta, duk yanda dada zatayi rarrashe ki take, karshe da abie yagaji bulala yake mata kafun tayi shuru, a haka haka ta fara cire abin a ranta, soyayya sosai ake gwada mata a gidan baga dada ba wanda ita ke kula da ita yanzun, d'akinsu d'aya haka matan gidan na mugun sonta da mazan, wannan karon harda safina amasu nuna mata so, ba kamar daba inta ganta kamar ta cinnnta a wuta, sosai yanzun sumayya ke wa yara lalle na wasa, daman tunda haka ta tashi da abin abien ta na kara mata karfin gwuwa, duk da kananun shekarunta don lokacin tana neman shekara 7.




A wannan lokacin ne safina ta sake yad'a manufarta nason auren abie, kamar wanshan karon ma abie yaki amince wa, amma dada ta murza ido tace bata yarda ba aure dole koh yaso koh yaki, haka abie yana ji yana gani aka D'aura masa aure da safina, batare da son ransa ba, sam sam yarinyar batayi masa ba yaji baya kaunar ta.


Tirkashi dada batasan wannan aure shine ummul'kaba'isin kome ba..............🍀🍀🍀🍀🍀


Anya gobe akwai update kuwa🤔🤔


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃


Page7⃣6⃣&7⃣7⃣
Bayan Auren abie da safina, a lokacin safina tafito da duk wani mugun halinta a gidan, ta buwayi kowa, har dada bata ragarwa ba, shikuma abie daman ba sonta yake ba, shiyasa sam koh ana meeting, safina naci musu mutunci baya saka bakinsa a maganar, tunda su suka kakkaba masa ita, badason rasa ba.


A lokacin safina tasaka sumayya a gaba da duka zagi, sai da dada ta sanar da abie, ranan da yasan abinda safina ke aikata wa yarinyar sa in baya nan, baraxanan sakin ta yayi ya zazzage ta, kai ranan anyi kwanan bacin rai a gidan.


safina ganin auren ta zai iyya mutuwa yasa ta shafawa kanta lafiya, bata koh ga maciji da sumayya, daman ba'a hannunta take ba, a hannun Dada ne.


Lokacin da sumayya takai shekara 12, har lokacin safina(momy)bata haihuba, kuma abie bai wani damuba, tunda yana da sumayya, duk wani soyayya da kulawa sumayya na samu a gidan, baga bappanayen taba, ba dada ba ga abien ta, momy ce kawai bata kaunar ta, har lokacin safina na tare da nafisa, duk da nafisar ta koma gidan tsohon mijinta, lokacin.


Haka kawai sumayya ta waye gari duk yan gidansu basa kaunar ta, daga su babuji har matan su, dada karan kanta bata shiga tsabgarta sai in babu mutane a wajen, ga tsoron momy da suke, da bin umurnin ta kome tace jiki na bari zasuyi inka cire abie, sosai sumayya ta shiga wani irin mawuyacin hali, abie inta ne kawai ke tsaya mata akan kome, baya taba yarda a cutar da ita, kuma duk wanda yama yarsa abu a ranan zaiga bacin ransa, ana hakan ne fa momy rana tsaka ta dake sumayya, wai ta b'ata mata labulen d'aki da lalle, a ranan abie saki d'aya ya mata ya korata.


Amma safina taki tafiya, dada tace sayya maidata d'akin ta, ganin matsaloli da sumayya keta fuskarta a lokacin, ga kananun shekaru, abin harya fara tayar mata da kewar mahaifiyarta, yasa abie saka a FGGC boarding school, ta cigaba da rayuwan ta a hostel, shikad'ai ne gatan ta, sai wata rana Dada tana zuwa mata visiting a boye, kuma tace mata karta fad'awa kowa tazo wajen ta, sumayya koh marmarin komawa gidansu hutu batayi, amma hakan take komawa in anyi hutu tana Allah Allah a dawo hutu.


Sumayya lokacin da ta cika budurwa, ta tashi da wani irin hali, akwai jijida kai da ganin tafi kowa, kasancewar ta mai kyau, ga Arzikin gidan su, ga rashin sabo da mutanen gidan, ga rashin mafadi don har lokacin xaman hostel take.


Sumayya inta dawo hutu duk yanda saurayi zai biyota, saita raina masa arziki gani take kamar tafi karfin sa, in kuma yakasan ce mai kudi sosai, sai taga kamar zata samu wanda ya fisa, in mai kyaune sai taga kamar nan gaba zata samu wanda ya fisa kyau, sumayya nada kawaye, koh saurayin kawarta ta gani ta ringa dariya kenan, tana kushe sa mummuna talaka kaza kazan, wasu Friends inta da dama in auren su ya tashi basa gayyatanta, saboda rainin wayo da take zuwa ta musu a wajen biki.


Lokacin da sumayya tayi candy, taci jamb A lokacin tana da shekara 18, aka shiga university sai abin ya d'ara na da, ganin yanda ake tururin sonta, babu ranan da zata fita ba'a biyo taba, hatta cikin gidan su Abdul(wanda lokacin da sukaje gida, bayan aure aka mata wulakanci, yace zai rage musu hanya ita da khadija)da kaninsa sunsha dambe akanta, Amma haka ta murza ido tace basu mata ba, karshe dai Abdul aure yayi, harda yaransa biyu ya fita harkar sumayya.


Sumayya bata gane kuranta ba, sai lokacin da takai shekara 23 lokacin ta kammala digree inta har tayi service, zuwa lokacin duk samarin ta sunja jiki da ita, kowa yana baya baya koh hira suke ta sako musu zancen aure, sai su kama kaucewa wasu kamma gudu suke, rabin kawayen ta duk sunyi aure, sai d'aid'aikune suka rage.


Bayan dawowar ta gida lokacin yaran gidansu sun d'ara nada, a yawa wasu sunyi aure wasu na aiki, itama rashin miji yasa abie nema mata aiki a bank nasu dayake aiki , dayake statistic ta karanta, tana aikinta tana samun Albashin ta, Amma maganar samari fa babu yanzun, ita karan kanta aure take so Amma babu mazan, ga kyau ga aiki ga kudi, mijine kawai matsalar ta.


Shekara 2 sumayya tana aiki a bank lokacin tana da shekara 25 a duniya, ganin haka yasa dada nema mata maganin farin jini, amma ina tayi tayi abin shuru, karshe dai dada ta nemi kanin abdul ya dawo su daidaita da sumayya, amma ba kunya a idon abie yace shi bazai aure sumayya ba, yarinya yar 15 xai nema ya aura ba rikekkeyaba abinnan yama abie zafi matuka, hakan yasa sa zagin kanin Abdul sosai abin ya zama babban magana.


Wannan dalili yasa babuji rantsuwa sai sumayya ta fitoh da mijin aure nan da wata uku, tunda dai zaman ta a gida fad'a zata had'a a tsakanin su, kamar yanda momy ta kitsa musu, don Abie indai akan sumayya ne baya ganin kowa da gashi, jin abinda akace ma sumayya yace sam bai yarda ba, ga yaransu su kubra da miemie sun girmi sumayya ba'a saka musu ka'ida ba sai yarsa.


Kuka dada tasa akan abie zai nuna musu iko da sumayya, abinda ya sa abie yarda kenan, sumayya har wata uku ya shige bata samu miji ba, su babuji sukace aikin da take shiya hanata aure, hakan yasa sukasa abie dakatar da aikinta.


Sumayya kam ganin an rabata da aikin ta da tafi so, don lagon sumayya kenan, kace zaka kaita garin su mamanta, koh kace makaranta, hakan yasata d'aukar takardun ta, ta tafi asibiti neman aiki babu wanda ya sani.


Dayake result nata nada kyau, yasata samun aiki a pharmacy tana musu lissafin kudin magani.


Kullum take fita aiki, ba tare da aisan ina take zuwa ba, abie bincike yayi ya gano aiki take zuwa, wannan ne dalilin kwace mata ducument da yan uwan mahaifinta sukayi, sannan suka rabata da aikin ta.


Ta dawo zaman gida, daga baya taga bazata iyya ba, tanemi shagon make-up tana zuwa training, daman ta iyya lalle, da sukaga ba sarki sai Allah, yasasu barinta tana zuwa koyon make-up in, basu hanata ba.


Sumayya ta cigaba da koyon make-up, har ta iyya aka sallame ta, taso abie ya bude mata nata shagon, Amma yaki karshe dai kawaye da yan gidansu, in sun tashi aure koh yan unguwansu take ma, ana hakan ne lokacin Aikin hajji yayi, kamar koda yaushe daman duka gidan ake tafiya hajji koh wani shekara, amma bana sunce baxasu ba, sumayya da abie suje.


Ba musu sumayya suka tafi aikin hajji, wanda zuwa lokacin bazata iyya kirga sau nawa taje ziyaran d'akin kaba ba, bayan sallah abie ya dawo, sumayyya kam daman akwai yar babuji dake aure a saudi, kin dawowa tayi ta zauna agunta har sai da tayi wata 7,lokacin ta cika shekara 26 ta dawo, kamar wasa tana dawowa yan gidan sukace sun mata miji, akwai wanda ya ganta yana so, hankalin sumayya ya tashi a lokacin, amma abie ya kwantar mata da hankali, akan zaiyi bincike akan mijin.


Duk yanda abie yaso yan uwansa su sanar dashi waye ne mijin, sunki Amsa d'aya suke basa, shine sun isa da yarsa, haka ba yanda ya iyya dagashi har sumayya suka zubawa sarautan Allah ido, sumayya duk azanta wani shararen mai kudi za'a aura mata, koh d'aya daga cikin samarin gidan.


Abu kamar da wasa, ya zama gaske don maganar auren sumayya babu inda baije ba, sai shirye shirye ake duk da ba auren soyayya bane, sumayya ta kwantar da hankalin ta koh banza tasan mijin classic za'a bata koh ajeboter.


RANAR D'AURIN AURE
Sai da sumayya ta tuno da mahaifiyar ta, haka kawai ranan tunda ta tashi sai kuka take, shi karan kansa abie a zullumin rabuwa da yarsa yake, yasan ba'a kyauta mata ba sam.


A waje kofar gidan shugaba, ake shirye shiryen d'aurin aure, sumayya dake d'aki da kawayen ta Ansha kwalliya kamar me, za'a aure classic kanta sai wani kara fashewa yake yanzun kam koh kukan ta daina, ji kawai sukayi Ana Alhamdulilahi An d'aura auren sumayya Abdulsalam shugaba, tare da Angon ta Muhammad Al'ameen yusuf, akan sadaki naira dubu 20, da mamaki sumayya tace "dubu ishirin kuma?wani irin mijine haka dubu ishiri ai mu tunda muke aure a gidan nan ba'a taba biyan sadaki haka ba"


Kawarta ce ta kalleta, kai sumayya sadaki fa Albarkansa ake nema, ba yawa ba kika sani koh mijin Alu-sunnah ne, irin samarin nan ne ustaxai, ga gemu ga d'angalalen wando kinsan fa irin su sunfi dadi love.


Gabaki d'aya kawayen dake d'akin dariya suka saka da shewa, don harga Allah sun d'auka mai zafi sumayya zata aura, sanin da suka ma halinta na rainako, ke ina ga fa irin samarin nan ne yan 20 something zuwa 30.


"Allah ya sauka bakin ki ya sare guntun kashi, habba 30 ai nima na fara jin kamshin, 30 ina laifin 35 irin ya bani shekara 9 nan" sumayya ta bata amsa


Duka suka kwashe da dariya, ana ta nishadi, kamar daga sama suka fara jin hayani yana tashi a babban falon gidan, muryar abie ne yake cewa bai yarda da auren nan ba, bazai yafe ba arasa wa za'a aurawa yarsa sai miskini, saboda babuji yaga ba yar gaddafi bane koh Abubakar shiyasa har ya iyya had'ata da yaron nan, yau sai an raba auren bai yarda ba, jin haka yasa sumayya da kawayen ta rugawa da gudu suka shigo falon don jin ba'asi.


MAKAHO ne ya ganta yana so, ba sai a basa ba tunda ba manemi bane da ita, babuji yace.


Kafun abie yayi magana sukaji timmmm sumayya ta yanke jiki ta fad'i jin wai

Please Login or Register in order to submit comment