Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba pls"


Kiye hakuri insha Allah bazan sake ba,


**Shuru na Masa
Jin Bata amsa ba ya sashi yin shuru




Khadija na Isa gida ta samu jama'a na cike a kofar gidan dam alamu dai wani abinne ya furu don harda motar police ga jama'an unguwan makil...............


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense












πŸͺ€my WhatsApp number
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~


πŸƒ *Rukayya Ibrahim* πŸƒ


✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa πŸ‘Œ
Free book 🀧


Page 1️⃣2️⃣
Cikin tashin hankali Khadija ta nufi kofar gidan tana isa taga an fitoh da inno Akan kadon asibiti da ake daukan gawa Koh Mara lfy tana kwance Koh motse batayi aka shigar da ita Ambulance sai su Inna asabe da baba lami suke ta rusan kuka Kamar ana yankasu,


Khadija Kam iyya rudewa ta rude ganin Yan matan gidan duka kuka suke harda wasu mazan ma


Bappa Dayyabu da bappa sulaiman harda kawu tafawa suka shiga motar Yan sanda da gani dai abin Case ne babba


Ta rasa wama zata tambaya ga Goggo Amina sai kuka take ,


Ganin lokaci na tafiya tasan yanzun bazata samu amsar tambayar taba yasa ta wuce kofar yayan ta shanyar kayan dazun da safe takai d'akin jakar ta dauka da Abubuwan da ta lissafa Mata duka,ta rufe kofar tayi kofar gida


Da sauri ta fita daga gidan ganin har yanzun jama'a na tare Tam,


Hospital ta wuce direct tana isa dakin ta baiwa Sumayya jakar,


Budewa nayi na zaro kudi 50k na mikawa yayan khadija "ga kudin ka dau takardan khadija ta rakaka kuje ku biya"


...Toh Al'ameen yace Yana laluben kudin ya karba hade da zaro dubu goma da dari biyar in safiya da Khadija ta basa ya hada da dari biyar in mangoron sa,ki cire dubu goma da dari biyar a cikin kudin sai na hada Dana wajena na ciki ta na biya,


"Ka bar na wajen Kan ai ba'a sallame niba zasu bukace mu Sai wasu abubuwan irin su hand gloves Koh ruwa da allurai duka ai bamu Gama kashe kudi ba ba iyya aikin bane kawai ka rike kudin a gunka,"


Toh khadija Tashi mu tafi


Toh yaya, ta basa amsa


**Fita sukayi nikam zuciyata tsinkewa ya ringayi da fargaba gani nake kamar bazan rayu ba,


Waya ta da khadija ta kawo mini na dauka number abie na Kira Amma Bai dauka ba,


Sake Kira nayi harna fidda tsammani naji ya dauka cikin sanyin jiki na Masa sallama"assalamu alaikum abie"


Waalaikumu salam ke lafiya?


Lafiya Alhamdulillah abie Daman na kiraka ne nace maka za'a mini operation yau don Allah Abie in nayi maka ba daidai ba kayi hakuri abie ka yafe mini bansan Inna shiga operation room xan fita da Rai Koh a mace ah ah shiyasa na kiraka naji muryarka abie ka samin albarka Koh xanga nasara a rayuwa ta Dan Allah"


Keeeeeee!!!! ce Miki akayi in za'a ma mutum tiyata mutuwa yake ne kin wani kirani kina fadamin Zaki mutu ki mutum Mana keee!!!! bara ma na fada Miki daga yau karki sake kirana!!!!


wallahih, tunda na aurar dake ki barni na huta mana,


***Hawaye ne keben fuskata Wai meke faruwa da rayuwa nane haka,,


Yanzun mahaifina in ma ya juyamin baya,


ganin shigowar Al'ameen da Khadija yasani share hawayen,


"Khadija kin biya"?


Eh Aunty.... Sunce 7:00 na dare za'a shiga operation room in,


"Toh bara nayi sallah mangariba Koh kafun Azo a dauke ni" na fada zuciya takaraya sosai wallahih,


Shima masallaci ya tafi nida Khadija mukayi Sallah muna idarwa na sakasu suci abincin da ya rage tun safe Basu sake saka kome a cikin su tun karyawan safe na taliya da wake,,


Daker suka iyyaci Amma kadan nikam na kasaci tsabar fargaba,


Karfe bakwai akazo za'a dauke ni,


*** Da kafata na fitoh nurse suka sakani a gaba har nayi nisa Al'ameen ya k'wala mini Kira tsayawa nayi ya iso inda nake lalubar hannuna yayi ya rike cikin damuwa sosai nasan daurewa yake,


Sumayya insha Allah Zaki fitoh cikin nasara kinji ki cire tsoro a ranki kinji Allah ne ya jarabceki Kuma insha Allah shizai baki lfy kinji,


"Kukane ya k'wace mini yau wa'innan bayin Allah sune gatana a yau bani da kowa a kusa Dani sai su dame Zan biya su babu, Allah ne kawai xai biyasu" rungumar sa nayi cikin kuka nake cemai "insha Allah insha Allah"


Lokaci fa na wuce wa ki shige mu tafi Naji muryan Nurse


***Sakensa nayi na rungumi khadija wance tun tuni kuka take,


***Na juya Ina tafiya a hankali Kamar wance k'wai ya fashewa a ciki sudai suna bin mu a baya har Muka Isa kofar operation room aka dakatar dasu tare da nuna musu su koma Kan kujirun d'ayan block in su zauna......




Bayan da Al'ameen baiyi ba Khadija ta koma gida taje ta kwanta Amma Taki tace anan zata kwana sai da ya nuna Mata Jan ido kafun ta yarda zata tafi 500 ya Bata ta hau nepep sauran change ta rike a hannun ta ,,,
. godiya ta Mar sosai ,ta dauki kula ta fita,.....






Zama Al'ameen yayi agun har akayi Kiran isha'i yaje yayi sallah yanata Addu'a Allah ya yasa aiyi aiki a sa'a ya Bata lfy(muma mukace Ameen)


Bayan wasu hours Sumayya aka fitar akan gado tare da kayan tiyata da hulan duka Koh motse batayi aka kaita dakin da ake aje,wa'inda akama tiyata Basu farfado ba shima binsu yayi har dakin ya shiga sun dauke ta sun daura akan gadon dakin,


kujira ya samu a Gefen gadon ya zauna ganin an shanja musu daki ba dakin emergency bane tashi yayi yaje ya tattara kayansu na dakin emergency ya dawo dashi dakin da take yanzun, zama yayi a Kan kujira,


Har dare yayi sosai Bata farka ba, sai karfe 2 na dare ta farka tana fizge fizge bakin ta dauke da salati tana ambatan sunan abie yayi hakuri karya gujita itama,,


Abirkice ya mike Yana kakamata ganin irin girgiza da take ya tsorata da sauri ya k'wala ma nurse inda ke dakin a zazzaune Kira ganin inyace zai tashi Sumayya zata iyya raunana kanta,


Da gudu suka yi kanta suka kakamata surutai tayita Yi Akan Abie da salati sai Shan anjima kadan Sumayya ta koma bacci,


Likita lafiya kam meke faruwa ne da Matata?ya fada hankalin sa a mugun tashe,


Ka kwantar da hankalinka ana samun haka Daman in dai mutun zai farfado sai yayi ta sambatu,..


Toh doctor yace Yana komawa Kan kujiran ya zauna hannunta ya laluba ya rike yanajin wani irin tsoro a ransa,


Har asuba Yana zaune sai da yaji ana Kiran sallah kafun. Ya Mike ya fita yaje yayi ya dawo ya cigaba da zama...




Khadija Taki fadawa yayanta abinda ta gani a gidansu gudun kada hankalin sa ya tashi ta Sansa da saurin birkice wa gashi Yana fama da Sumayya tazo ta Kara Masa da wani Kuma,




Keke napep tahau ta wuce a kofar gidan su Goggo Amina ta sauka ta biyasa kudinsa ta shiga gida da sallama. ......


Goggo Amina ta samu zaune sai rusan kuka take Kamar wance ake yanka namar jikinta,


Da sauri ta karaso gareta cikin tashin hankali tana cewa Goggo Amina lfy menene ya farune wallahih tunda na tafi hankali na yaki k'wanciya?


Wallahih Khadija kedai ki bare kawai mutanen gidan mu sun dawo kashe junansu,


Kamarya Goggo ban gane ba?


Toh dazun bayan la'asar iro ya dawo daga aiki yazo zaici abincin ranan sa ashe suwaiba( yar baba lami) ta dauka taci shine da yazo dauka yaga babu yake tambayan inno ya abincin sa babu a kula shine fati tace masa suwaiba ne taci,


Tashin sa ba wani tunani ya zaro wayan wuta ainahin na bol ya zuba mata ita kuma da taji zafi tana ihu ta zari tabarya zata muka Masa,


Inno Kuma ganin za'a bugawa iron ta tabarya tazo zata k'wace kawai tabarya ya sauka a kanta,shine fa Kika ga ta mike Koh motse batayi,


Ni tsorona ma yanda naga Kan Bai fitar da jini ba kinsan akwai babban hatsari ka bugu irin wannan ace jini Bai fitoh ba,




Shine iro ganin inno a yashe a kasa yaje ya ibo Yan sanda akazo aka tafi da suwaiba, gabaki daya gida ya hargitse su bappa nayinku duk sun bisu station wasu suna asibiti har hanzun ba'a San takamammen halinda inno ke ciki ba mutuwa Koh rayuwa😭😭😭 wayyo ni Aminatu,


ta fada tana sake rushewa da kuka ita dai Khadija Allah ya kiyaye na gaba tace ta Mike taje ta ajiye kulan Sumayya a kitchen sai gobe zataje kofarta da safe,wanka tayi, tayi isha'i ta kwanta don batajin yunwa taci a asibiti,haka tayita juyawa Amma bacci yaki daukan ta tashi tayi ta Kama lafilfilu tana nemawa Aunty Sumayyan ta lfy da nasaran aiki sai 1 ta kwanta


Bangaren Al'ameen bayan sallan asuba har lokacin yana zaune Dayake dakin da suke yanzun babban falo ne Mai dauke da majinyata masu yawa wa'inda aka ma operation shiyasa Basu kadai bane a dakin,


sosai Yan dakin ke mamakin MAKAHON nan shin baida Yan uwane da zasu kula da wannan Mara lfy sai MAKAHO chap lallai Kam kowa gulma na cinsa( Niko nace gulma zai karku bazakuji kome ba)




Tun asuba Khadija ta farka Bata koma. Bacci ba wanke wanken Goggo Amina ta fara ta hada harda kulan aunty ta duka ta wanke tayi shara tana Gamawa ta daura dumame ganin yau Goggo Kamar Mara lfy haka da tashi ,tana Gamawa ta dauki key sai gidan yayan ta,


Yauma sai da tayi shara ta daura ruwan zafi Yana tafasa ta juye a flasks ta dafa indomie da kwai lokacin karfe 7:30 wanka tayi tasa kayan ta data dauko a gidan Goggon ta tadau abincin tayi hanyar FMC




****Da misalin karfe bakwai na safe na bude idona Wanda nakejin Kamar an zuba mini barkono a ciki a hankali na sauke k'wayan idanuna a kansa a zaune yake ya tasani a gaba Kamar wani Mai kallo yayi tagumi kallo daya zaka Masa kasan a cikin zullumi yake sosai.......






πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin Koh kinsan mace sai da kamshi da* πŸ˜‰


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turaren Suna d'ayane Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno (habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam) (khumraBlack & while*)
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth*
πŸ€ *Na d'aki (halud Al'oud)*


*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌ πŸ’ƒπŸΌ


πŸ€ *Suna bada kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


*Contact them vie*
08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page1️⃣3️⃣
**** zuba Masa ido nayi Ina kallonsa sosai na hango damuwa a fuskar sa ga idanunsa manyan nan sun kumbura sunyi ja' sosai alamun baiyi bacci ba Daren jiya hannu na dake cikin nasa na motsa,


Cikin firgita yake furta Alhamdulillah Sumayya kin tashi kin bude idonki Kina kallona kin gane ni???


Abin yaso bani dariya bandon halin ciwo dake damuna Wanda Koh magana bana sonyi Dana dara ganin yanda ya zarge lokaci daya Kamar Wanda akace Masa za'a min dashin zuciya ,


Sumayya kina jina Koh dai idonki Bai budu bane Amma Naga hannunki na motse Kamar kin tashi bara dai na Kira nurse, yana yunkurawa zai Mike hannun nasa na rike cikin nawa hakan yasa shi komawa ya zauna Yana Mai cigaba Damon sannu tunda dai yanzun Kam ya fahimci na farka maganar nedai bazanyi ba, daidai lokacin Khadija ta shigo falon tana zazzare ido tana neman gadon da muke,har dai ta gan mu,


Isowa tayi bakinta a washe gani na ido a bude sai dai na Dan rame sannu Aunty Allah ya Kara sauki,


**nidai sai ido


Khadija jike Kira doctor kice ta farka, toh yaya tace tana fita








Karyawa Al'ameen yayi kafun ya ce zaije gida Khadija ta zauna Dani




Bayan fitar sa keke napep ya hau zuwa gida ,ya sauke sa a kofar gida, da sallama ya shiga gidan Jin gidan yayi yau kamar ya Bata hanya Sam Kamar ba gidan su ba, gabaki daya shuru ba hayani da suratai Kamar da don gidan su tun daga bakin kofa zakana Jin hayaniya na tashi Amma yau sit Keke ji lalube yake da sandar sa ya shiga kofar su,






Wanka yayi ya shanja Kaya ya kwanta don wani irin bacci yakeji Wanda Bai samuyi ba Daren jiya har kansa na ciwo, sai azahar ya farka massalaci yaje yayi sallah sai agun yake Jin abinda ya faru a gidan su sosai hankalinsa ya Tashi don shi mutum ne Mai son nasa duk wulakancin da suke masa in Abu ya samesu sosai yake damuwa daga massalaci police clinic ya wuce kamar yanda akace gun aka kaita,




Yana Isa ya hadu da Rabin Yan gidansu a farfajiyar asibiti gaidasu yayi yaukam ya samu amsa ya tambaye jikin inno ance masa Basu Bari a ganta har yanzun,,,


Zama yayi shima a asibitin duk hankalin sa nakan Sumayya sai la'asar ya koma FMC,




Haka Al'ameen da Khadija suka ringa jinyata a asibiti har muka Kai sati sosai Khadija ta tallafamin itace girki itace kaikawo tsakani gida da asibiti yau satin mu daya aka sallame mu, kudin hannu na ya kare Daman dubu d'arine abokin abie ya damka mini lokacin da naje ma abie sallama a falon sa ranan da za'a kawo ni gidan su Al'ameen,


na kashe kudi a gidan Al'ameen kafun naje asibiti na biya kudin aiki nasai madara da bonvita gongomi manya su sugar shi nayi ta Sha a asibiti da Abubuwan da aka bukata a asibiti shi Karan kansa naira d'ari shida ya rage agunsa,


**Keke napep muka hau dukan mu uku sai sintali har kofar gida ya sauke mu Khadija ta taimaka mini muka shiga cikin gida shi Kuma ya biya Mai keke ya dauko Mana kayan mu ya shigo,




Kofar mu Muka wuce nikam sai mamaki nake ganin gidan shuru babu hayaniya kamar an musu kulle Amma ban tambayi Khadija ba, kofata muka nufa Yana binmu a baya da kaya muna shiga nabi kofar da kallo kamar ina nan gaskiya Khadija yar arzikice har raina yanzun nake kaunar yarinyar sosai daki muka shiga na kwanta a Kan gado,


shima shigowa yayi da kaya ya aje "khadija kunna mini fanka"nace Mata,


Wallahih Aunty babu nepa an yanke muku wuta,




"Anyanke wuta kuma Daman wake biya"


Hada kudi ake duk wata a biya wannan watan inno ba lfy ba Wanda ya saurare Yan NEPA,


Allah ya bata lfy nace ina mikewa waje na fitoh Khadija ta shimfida mini darduma da filo na kwanta abina,


"Khadija kije gida kinji kije ki huta yau basai kin Mana abincin dare ba yayan ki zai sayo Mana yaukam ki huta abinki kinji"


Badon ranta yaso ba ta amsa mini da toh ta juya zata fita,


"Khadija dauki taliya uku a caton in kinje gida ki dafa muku kinje akwai Maggi da Mai duk ki eba,"


Toh Aunty ta shiga kitchen in ta dauka ta tafi,


shikam fita yayi ya rasa Meka Masa Dadi yanzun Sam baida jarinda zai Kama sana'a sai d'ari shidan nan koma dashi ya biya kudin Keke 200 saura d'ari 400 gashi yanzun abinci zai Saya Kamar yanda nace Masa Khadija taje ta huta zama yayi a kofar gidan ya zuba tagumi abin duniya ya damisa,




****Nikam bayan fitarsa tunani na hauyi tunda na kwanta rashin lfy babu yan gidansu Koh namu da yazo dubani hatta Yan unguwan makwanta basuje ba sai Goggo Amina kawai itama sau daya taje, lallai rayuwa abin tsorone,


Sai da yaji ana Kiran sallan mangariba kafun ya mike ya tafi masallaci daga nan ya wuce bakin first bank dake D'aya tsallaken titin kofar gidan su ta Gefe ya sai abinci plate daya naira dari uku ba nama haka ya sai plate daya aka Masa take away ya dauka yayi hanyar gida,


Nima sallah nayi naci gaba da k'wanciya a inda nake, naji shigowar sa da sallama amsa Masa nayi, ya karaso Kan darduman ya zauna a gefe na Dayake yanzun ya daina shakkar rabar inda nake tun zaman mu a asibiti,


Ga abinci nan na sai Miki shinkafane fried rice ,


Toh nace na karba budewa nayi na fara ci Ina tambayar sa nasa" Ina take away in ka Kai Kuma" agun naci ya Bata Amsa,


abinci rabi naci,nace yaban. ruwa dauka yayi ya kawo mini nasa" sai da akayi Kiran isha'i yayi Alwala ya wuce masallaci yayi sallah sai karfe 9:00 ya dawo lokacin nikam na gigice ga zafi ka sauro sai fifita nake da caton in taliya,
Dolen sa ya fita yaje yasai maganin sauro na ishirin,kudin hannunsa saura 80 kacal ya rage,


Yauma a darduma daya Muka kwanta shiya rigani tashi da asuba ,,,


Vayan fitarsa nayi Sallah sai 7:00 ya dawo wanke wanke yayi ya jawo ruwa yakai kafa biyar yasa a randa nikam bacci nake a daki


Khadija ma tazo ita tayi shara ta shiga kitchen zata daura mana karyawa sai dai babu kayan miya,fita tayi tazo ta same sa,


Yaya ba kayan miya aban kudi na saya,


Me Zaki dafa?


Shinkafa ne


Sai dai Khadija ki Mana shinkafa da wake da Mai da yaji don bani da kudi sai 80 innan ,gasu nan ma kije ki sai Mai da borkono da Maggi,


Yaya akwai Maggi kam da Mai da manja galam ma babba a kitchen in sai dai na sai borkono na talati kawai yaya,


Toh yace ya Mika mata Yana cewa tayi abinci gabaki daya harda na Rana direct, hamsin ya Bata,


ta karba ta koma kitchen in ta daura shinkafa a gas da wake,taje ta sayo barkono ,




****Sai 8:30 na tashi na safe fita waje nayi Naga Khadija na aiki a kitchen shi Kuma nata Jan ruwa,gai Dani tayi na amsa shima gaishini yayi amsawa nayi na ibi ruwa a buta na Kama brush,


Sai karfe 9:00 ta kammala abinci ta zuzuba Mana karba nayi na fara ci Sam ba cimana bane shinkafa da wake Amma ya zanyi ni Karan kaina nasan Basu dashi Dole na koyawa kaina cimar su ,


Yana Gama cin abinci ya Mana sallama ya fita wajen Yan sarin kayan fruit ya wace inda yake saya yazo ya kasa,da sallama a bakinsa ya karasa gun dukansu suka amsa masa suna tambayar sa lfy, baya zuwa kwana biyu Koh ya chanja sana'a ne,




Lafiya Alhamdulillah Ina zama agun mara lfy ne a asibiti shiyasa bana fita, Yana fada ya karasa wajen customer in sa, Dan Allah malam Hafizu nazone ka taimaka ka bani bashin mangoro na dubu daya inje in kasa in Allah yasa nayi kasuwa sai na kawo maka kudinka ka bani wani, wallahih bani da Koh sisi sai naira talatin,


Chap gaskiya bazan iyya wannan kasuwan cin dadawan kauye ba ,


Habba malam Hafiz mun saba da Kai shikara nawa Ina sayan kaya a gunka don yanzun jarina ya karye bazaka iyya tallafa mini in mike ba,?


Bazan iyya ba,yace cikin masifa ,kala Al'ameen baice masa ba yaje kusa da table in dayan makwancin malam hafizu Amma yaki yarda haka ya zagaya Tashar kayan marmari Anki Vasa duk da sun Saba dashi Amma haka suka ki basa jiki a sanyaye ya kamo hanyar gida,..






Muna zaune da Khadija a kofa tana mini kitso Ina kwance a Kan darduma a baranda Hira muke akan bikin kawarta Yar wani Mai kudin unguwan saura wata Daya da sati biyu,


Aunty kinsan Allah Asma'u tana sona da kawance Amma mamarta Bata so shiyasa yanzun bana zuwa gidan su itama Bata zuwa namu sai dai mu hadu a hanya mu gaisa da auren ta ya kusa ma kaninta ta aika ya fadamin date na auren ,




Kuma ,, kawayen ta suna wulakantani tun muna makaranta basaso na da Asma'u,sai nake ji Kamar kar naje bikin,


"Don me bazakije bikin ba"?


Saboda banaso.a wulakantani Aunty,


"Ai.in bakije ba baxataji Dadi ba Kuma basai kin kulasu ba zasu wulakantaki ,"


Shikinan Aunty Allah ya kaimu,..


"Ameen Kenan in anyi bikin da wata Daya azumi"?

Wallahih Aunty yanzun bakiga sai aure ake ba akai akai azumi yazo,


"Toh Koh kema za'ayi nakine kafun azumi tunda ba karatu kike ba"? na fada Ina dariya,


Shap aunty aini Koh saurayi bani dashi ban ma tabayi ba,


"Kutt don me Amma dai Inaga ke kike kinsu Koh Amma duk kyau inkin nan kice baki da saurayi"


Aunty Kenan ai samarin ma Yan Mata masu kwalisa suke so ba Irina ba,


"Karki Kara cewa haka ki gode wa Allah wata ma batasamu gata kamarki ba kinji insha Allah wata Rana sai lbr ",


Insha Allah Aunty




tsayuwar mota mukaji a kofar gidan ba'a jima ba sai Muka fara Jin Ihu da salati na dandazon Yan gidan sai koke koke ake dagaji bana lfy ba ne,,,,....


Khadija ce ta Mike da gudu ta fita a kofar tayi cikin gida Koh takalmi babu ni karan kaina na tsorata,


Koh minutes uku batayi ba Sai gata ta dawo da kuka tana haki ta Fadi a kasa kusa dani cikin gunjin kuka ta bude baki tace Aunty I.................






πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* πŸ˜‰




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


πŸ€ *Na tsunguno(habil)*
πŸ€ *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
πŸ€ *Turaren turara jiki after birth* ,
πŸ€ *Na d'aki(halud Al'oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*


πŸ€πŸ€πŸ€ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


Contact them vie
πŸͺ€08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ§‘β€πŸ¦― *MATAR MAKAHO* πŸ‘¨β€πŸ¦―
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya* *Ibrahim* πŸƒ

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπŸ‘Œ
free book 🀧


Page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣
Aunty' inno ta rasu tace tana Kara karfin kukanta,


"Innalilahih wainnailaihir rajuun" Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta" nace


Ameen Aunty tace tana mikewa tadau hijab inta ta nufi cikin gida,


**Banyi niyar zuwaba saboda jikina Amma ganin mutuwa ne Kuma Abu da gida babba hakan zai iyya zama abin magana, yasa na mike na fita zuwa cikin gidan,


Ai ban tashi sanin Yan gidan ba sai da Naga manya da yara Suna kuka harda na tashin hankali kuka suke ba manya ba yara Mai makon a ma mamaci Addu'a sai ihu da kuka nidai Ina zaune a Gefen matan makwanta da suke shishigowa Ina kallon ikon Allah


Al'ameen da wannan sanyin jikin ya iso kofar gida ya tarar da jama'a makil, inno ta rasu mutuwar ta dake sa sosai don alokacin sai da mutuwar mahaifiyar sa ta dawo Masa sabo,ganin yanda iro ke kuka Wanda yasan halin iro ba kome ke tsorata Sa bama Amma yau kuka yake,


tabbas mutuwar iyaye akwai ciwo,(Allah kajikan iyayen mu)


Ankai inno gidan ta na gaskiya yau har anyi sadakar bakwai gida ya koma kamar yanda yake kowa na sha'aninsa sai yaranta da sukayi sanyi kadan na rashin uwa,


A tsawon satin nan na fahimci

Please Login or Register in order to submit comment