Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin kallon nan daza'a kira da kallon tuna duk abubuwan daya mata, girgiza matakai Dady yayi hawaye na zubowa daga idanunshi zarrr, awani irin hankali yace "am sorry daughter na, am sorry for all the suffering, the trauma and everything am sorry, forgive Abban ki Aneesah, Abban ki yay kuskure, nai shirme kiyafemin, I am so sorry" wani irin fashewa da kuka Aneesah tayi harda shesheka majina shaaa tsabagen kuka tuna da takeyi bana wasaba, hannu ahankali Dady yabude mata alamun tazo yana girgixa mata kai he is feeling bad cutar da ita dayayi kaman yayta ihu, cikeda rauni yace "kiyafema Abbanki, Abba is sorry sosai plsss" Dady yakarasa maganan wasu sababbin hawaye na zararomai dawani irin gudu Aneesah tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka sosai ahankali Aliyu ya leko dakin yana goge hawayen dasuka zubomai da bayan hannu daga Dady har Aneesah sun bashi tausayi, Dady yay kuskure but he's so sorry, Aneesah kuma is hurt an cuceta ba kadanba, ta wahala akan abinda kazafi akamata, jingina yay da bango yana goge kwallan dake zubomai yana kallon zama he is way too happy Aneesah ta yafema Dady shi now his mind is at peace ✌️ ._how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



8️⃣4️⃣


_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Kankameta back Dady yayi yana bubbuga bayanta yana girgiza mata kai cikin wani irin tone na rarrashi yace "am sorry daughter, is okay, ya isa" yana bubbuga bayanta, tadade tana kuka a jikin Dady kafin ahankali yacirota daga jikinshi handkerchief dinshi yazaro daga aljihu ya sharemata fuska tass harda hancin, hannunta itama takai ahankali kan fuskarshi ta gogemai hawayen dasuka zobomai, Murya chan kasa tace "na yafema Abba na, karka kara zubda hawayen ka sabida ni kokuma wani abu dakamin, dudda abinda kamin har kasan zuciyana wlh ban tsaneka ba Abba sabida ina sonka sosai starting from rana na farko dana bude ido naganka da bani da lafiya, you are a good man Abba ko soyayyan dakake ma Ammi na kadai abune agareni da bazan iya rikeka dashi ba, Abba am sorry too kayafemin I was not nice to you kuma na yarda da kaddara zuwana gidan yari kaddara ce dakoda bakai la kaini ba still sainaje sabida Allah yariga ya kaddara saina je gidan yari, kuma shairi kayan kwalba ne ai yanzu da kwalban yafashe bagashi wacce tayi asirinta ya tonu ba, Komi yawuce Abba na karka sake zubar da hawaye akaina na yafema nima kayafemin kaji Abbana" tai maganan wasu sababbin hawaye na zubo mata sharemata su Abba yayi da sauri kafin ahankali ya ijiye handkerchief din yay cupping fuskarta, ahankali ya daura bakinshi kan goshinta ya sumbaci goshinta tareda janye bakinshi ahankali yace "Allah yamiki albarka, bakimin komiba dudda haka na yafemiki duniya wa lahira, yanda kika yafemin dinan ubangiji Allah ya yafemiki duka kura kiran dakikamai, Allah yamiki albarka Aneesah ya kyautata rayuwanki sanan ya azurtaki da wadatan zuci thank you daughter na" murmushi tayi hawaye na bulbulowa ahankali tace "Ameen Abba na" murmushi yamata yace "No more crying" gyadamai kai tayi da sauri tasa hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata, Teddy bear daya shigo dashi yadauka yamika mata, ahankali tasa hannu takarba tana murmushi ba'a taba siyamata Teddy bear ba saiyau, tana yawan sonsu datana yarinya intacema Ammi ta saimata sai Ammi tace babu kyau ranan lahira ana kiranka ka huramusu rai, rungume Teddy tayi tana murmushi, murmushi shima Dady yayi ya zauna da kyau yajawo jakan daya shigo dashi yana cicciro abubuwan daya siyomata wanda almost duka kayan kwalama ne, kafin yadauko wani red box da aka rubuta am sorry aciki yace "kinsan menene acikin nan daughter?" girgixa mai kai tayi tana kallon cute box din, Dady yace "kinsan sushi?" girgiza mai kai tayi da sauri tace "a'a Abba" gefenshi ya nuna mata akasan yace "zauna nan yau zamuci sushi tare, asalin Sushi abincin yan Japanese ne da akeyi da shinkafa, garnish with vegetables dakuma raw sea food dinan dakuma veniger, abinda yasa Sushi keda farin jini sabida shapes dinsu ne, they was this saying da ake cewa idan kaima mutum laifi to always apologise with sushi no matter yanda wanda kema laifin ke fushi dakai just a glance at Sushi zaisa yay murmushi, so are you ready daughter let's verify this saying are u in?" Dady ya daga mata hannu alamun high 5 cikeda so, hannu Aneesah ta bashi cikeda murmushi danta kosa taga ya Sushi yake tace "yes Abba am ready" bude box din Dady yay ahankali wasu hadaddun Sushi ne guda 8 sai gefe guda kuma chopsticks ne da ake amfani dashi aci, sai wasu bottles guda uku daya na ketchup, daya na soy sauce, daya na mayonnaise wanda zakaci dasu, wani irin murmushi Aneesah tayi dan Shushi looks super good to the ears yan micil micil dasu looking so adorable and takeaway, wani irin murmushi Dady yayi yana clapping yace "yayyyy the saying is absolutely right kema kina murmushi" dariya Aneesah tayi tace "Abba nakosa naci" da sauri Dady yace "okay wait, bari na zubamiki soy sauce yafi dadi dashi" yay maganan yana daukan bottle din soy sauce bedewa yayi yazuba kan sushi sanan yadau chopsticks 🥢 yadauko Sushi daya yakai bakinta, bude bakinta tayi ahankali ta karba Dady ya tsaya yana kallonta, ahankali take taunawa dudda yama bakinta wani iri dan this is the first time she is eating the food, but is testy she must admit cinyewa tayi tass tace "Abba another one" dariya Dady yayi looking so happy ganin she likes it yakara dauko na biyu zaikai bakinta.

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Ahankali Aliyu ya share hawayen daya zubomai yajuya ahankali dan baiso su ganshi yay hanyar stairs sauka yayi kasa, nauyin da zuciyan shi kemai ne ya sauka sosai he is super happy Aneesah ta yafema mahaifin shi, bude kofar falon yayi yafita ya wuce part dinshi zuciyar shi wasai, ahankali yabude kofar falonshi ya shiga Hajar daya gani atsaye a tsakar falonshi yasa ya tsaya chak daga wurin kofa ya mugun daure fuska yana kallonta, kafin ma yay magana da sauri ta saukar da duka kafafun ta kasa ta hade hannayenta batare data dago kantaba cikin wani irin cool murya tace "Ya Aliyu dan girman Allah badan niba bakima dan halina dana Mamata ba kadubi son dakake ma Rauda yau naci darajan marigayiya Rauda karka koran ka saurareni dan Allah wlh kainazo nema" Allah data kira dakuma darajan Rauda da takira taci yasa Aliyu bai kadataba, shigowa dakin yayi batare daya ko kalleta ba yawuce kitchen dinshi yogurt ya tittilo a kofi yafito rikeda shi yadawo kan kujera shi yazauna yana kallon TV dake aiki, kurban Yogurt din yayi sanan yadago kai ya kalleta from head to toe, tarame iya rama tai duhu dudda dama Rauda ce kadai mai haske adakin dan Dady tabiyo Hajar namanta tabiyo dan bakace ita daman amma bakin datayi yay yawa ga shegiyan rama tausayi sosai yaji tabashi ya kafe kafafun ta da kallo yanda suke rawa danta gaji da kneeling, da yatsa yamata alamu data tashi ya nunamata kujeran dake facing wanda take kai, tashi tayi ahankali sum sum taje ta zauna tana kallonshi yogurt dinshi yasake kurba sanan ya kalleta yace "ina jinki talk" shiru tayi gabanta nafaduwa kafin ahankali tace "Ya Aliyu zan fara da kaina, dan Allah Ya Aliyu ka yahakuri da dukkannin abubuwan danamaka abaya, sai yanzu da babu Mama babu Rauda nagane no matter yyaya kai wanmu ne duk inda za'aje adawo kai wanmu ne Ya Aliyu no body can deny this, I never knew a day like this was coming" tai shiru dan bakinta na rawa tace "Ya Aliyu dan Allah kacema Dady ya yakuri ya yafemin, baya amsa gaisuwana sanan gabaki daya ya kwashe kannina ya gyara flat din Amarya dama yariga yasa an fitar da kayansu an kai musu gidansu yamaida flat din dakin yara duka yaran suna flat din yakawo musu Nany kusan guda shidda kullum a musu girki amusu wanka a tafi dasu school da yamma haka sutafi islamiyya, ya Aliyu rabona danaga kainaina kona rike musu hannu na manta sainai na hangosu ana shiga mota dasu, Dady yace karya sake yaji labari nama shiga flat din so yake ya hada kan yaranshi bayason na batamishi su da mugun halina wai ni kadai naita zama a flat din Mamana ya barmin flight din, Ya Aliyu Dady ya tsaneni banda abinci baya bani komi yanzu baimason ganina nasan kawai sabida babu yanda zaiyi ne da wlh har korana zai iyayi, ni banda saurayi har yanzu danai aurena nahuta nima da wanan tsanar ta Dady, Ya Aliyu bansan mesa Dady ta tsaneni ba, wlh wlh Ya Aliyu katuba CCTV camera kaga na laundry ranan da Mama tacemin zata kasheka har fada munkusa yi saida nace mata kome zatayi tayi banda kissa, kisa babban abune dudda nasan banasonka den but I felt somehow da Mama tai wishing dead akanka, to Yaya zanyi? Nasan ba Aneesah tasama gubaba amma Inna tona Mama zata iya tsinemin albarka Yaya zanyi?" tafashe da kuka sosai kurban yogurt Aliyu yayi batare daya kalleta ba yace "inda Rauda ce ba tsinuwaba ko tsireta maman ku zatayi Rauda saita fadi gaskiya, Rauda is such a brave good sister, sometimes I use to wish dameke uwarki ta kashe ba Raudana ba" yay shiru zuciyar shi na zafi baiso yana tuna rasuwan Rauda dan injury din dawomai fresh yake he just wish tana alive, shiru yayi yana sauraron yanda Hajar ke kuka, in a very bitter manner yace "an bakin halinki ne yasa haryau baki da mashinshine, as small as u Are Hajar ur mind is so evil, am at the point of Death ga baiwar Allah dat has noting to do with evil dunku kukaja taje prison for selfish reason naku tayaya mace irinki zata sami miji eh? Ko my enemy I will never wish for him ya auri yarinya kamar kiba, Evil mind, evil character, mena taba miki in this world dakika tsaneni eh? Tell me?" fashewa dawani irin kuka Hajar tayi gwanin ban tausayi ta zamuyo daga kujera takara kneeling tareda hada hannayenta alamun Yaya hakuri tana kuka sosai tama kasa magana, dan tabe baki Aliyu yayi yace "yau ina uwar taki mai dauremiki gindi? Where is she now to protect you ta baki duk abinda kikeso? Mai koyamiki duk abinda kikeyi kinayi thinking all your life she will always be by your side protecting you tana ina yanzu?" Aliyu yamata tambayan yana daga murya kafin yay dan murmushi yace "tana prison" dan shiru yayi yana kallon yanda take kuka yace "kin manta lokacin ko ganina kikayi saidai kiyi tsaki, kiyi habaici, in Rauda tazo Gina kuhadu kumata duka, ki zagen kiyi dis kiyi dat, yau meya hanaki yin hakan Hajara? Is it because mahaifiyar ki bata gidan nan? Have you release your mistake? Bari kiji duk yaron dazai zauna ya dinga tapka iskanci, dakowace tsiyace thinking iyayenshi nanan zasu karemia they always have his back that child is mistaking nobody knows tommorow, idan Allah bai rabaka da iyayen ta hanyar daukan ransu ba to wani abu nanan faruwa, annabi yace ama iyaye biyayya quit sure but ba'ama iyaye biyayya awurin sabama Allah" shiru yayi yana kallon yanda take kuka tabashi tausayi but ina bazai taba nunamata hakanba is her time to ripe what she saw danhaka so be it, ajiye kofin yogurt yayi ya rungume hannunshi yace "kinzo kin samen kan inbama Dady hakuri? Listen and listen attentively, hear me loud and clear Hajara bakida matsayin dazanje na rokan miki Dady, problem dinki is u and him so deal with it alone, abu daya zan iya gayamiki shine go and ask Aneesah dakuma mahaifiyarta for forgiveness inba hakaba bakida komiba alhakin wani baya yafuwa sai inshi ya yafemaka, and lastly kitashi dust ur kneels and leave my room jejely before I loose my temper dan am not gonna be as nice as this Aliyu dakike gani sitting down haka" mikewa tsaye tayi ahankali tana kuka sosai tai hanyar fita daga kofa tana kallonshi ya rakata da harara harta fice. Ajiyan zuciya yasauke ya cigaba da shan tea dinshi. _how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



8️⃣5️⃣

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_



Ammi tadade jikin kofar dakinta tanajin draman Abba da Aneesah, Aliyu data hango ta hole din kofarta yasa bata fitoba tana kallon yanda yake goge hawaye sosai taji gabaki dayansu sun bata tausayi, Alhamdulillah komi yawuce yanzu sai new life, yanzu zata fara planning gagarumin bikin yayanta guda biyu, ganin Aliyu yatafi yasa itama takoma kan gado tazauna saikuma ta tashi ta shiga bayi ta watso ruwa tana fitowa ta chanza kaya tareda kwanciya ko minti biyu batayiba wani bacci mai nauyin gaske yay awon gaba da ita abunku damai ciki kaman ba itane tagama bacci dazun nan ba, ko cikin bacci taji anyi cuddling nata saidai takara shigewa jikin Dady batare data tashiba dan mugun bacci takeji.
Inkika karanta baki biyaba banyafe mikiba


Wani gagarumin shirye shiryen biki aka shigayi, fess Ammi tahana Aliyu shigowa part dinta Aliyu tsabagen rashin kunya harda kai karan Ammi wurin Dady, Dady ma yagoyama Ammi baya yace shida ran Saturday zasu tafi C.A shida Aneesah me abun damuwa, yahakura yanzu abun mata ake kuma dama haka yake a al'ada ba'a bari ango yaga amarya sai ranan biki ranan bakin ciki kaman ya kashe Aliyu. Tuni Momma da Abdul zunzo sun bama Ammi hakuri, Ihsan tadawo best friend din Aneesah, aka shirya aka manta komi, tunda Ammi ta lura Nani Dady ya kwasoma yaranshi tanunamai fushinta sosai akan hakan nan tasa akabar Nani daya sauran aka sallemesu ta karbe yaran duka tana bamu tarbiya mai kyau tana lura dasu kuma alhamdulillah yaran suna sonta saidai yan matsalan da ba'a rasaba yau da gobe, Dady na bala'in alfahari da ita, ga ciki ga nauyin yaranshi sanan ga hidimar biki duk ita kadai, duk in yatuna abinda yama Aneesah dudda sun riga sun nunamai komi yawuce sai yaji kunya yakamashi, hakama saida Ammi tasa baki sanan Daddy ya yafema Hajar dan taso ta rokesu gafara, a lokacin da Ammi tanunama Dady tanaso tadawo da Hajar flat dinta nuna mata yayi ina, a barta a flat din uwarta tacigaba da zama anan amma bazai taba bari tadawo flat dinta ba sai tazo ta kashe su wata rana inaaa.


Yau Thursday dayake gobe Friday za'a fara sha'anin biki tun safe Aneesah tafadama Dady cewa zatace tarabama kawayen ta yan Suleja katin aurenta, Dady yace to shikenan yabata driver dazai kaita itada Ihsan, Ammi tace "kidawo dawo dawuri karfe uku yar Malaysia zatazo" murmushi tayi tana kama hannun Ihsan tace "saimun dawo Ammi da Abba" adawo lpy Dady da Ammi dake zaune falo suka mata suka fito tsakar gida, sosai Aneesah take kallon hanyar flat din ya Aliyu dantai mugun kewanshi rabonta dashi tun ranan da akai ruwan saman nan iyakanta dashi test messages da wayarshi iPhone 11 dake hannunta, bangaje mata kafada Ihsan tayi cikin zolaya tace "dalla zomuje part din Ya Aliyu kusoye abunku wlh Ammi ce tahana shi shigowa bangaren ku, dazun nan ma suka gama workout shida Ya Abdul keda mijinki dalla muje" hararan ta Aneesah tayi tace "nidai muyi sauri banmaso ya ganni wlh" da sauri Ihsan tace "wlh kam dan wanan kyau da kikayi Aneesah in Ya Aliyu ya ganki saidai yakira waya yacema Dady kuna California" fashewa da dariya sukayi atare suka shiga mota driver yajasu har tsohuwar anguwan su Suleja saida tabi gidajen kawayen ta duka da wayanda tasan su tasanadin lalle duk ta kaimusu hadadden invitation card dinta sanan hakanan kawai taji tanaso takaima Madam katin biki hakan yasa tacema driver suje express road.


_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_


Agaban bakery dinsu driver yay parking wurin Ihsan ta kalla tace "inane nan Aneesah kinsan wani ne?" dan murmushi Aneesah tayi tana kallon wajen tace "nai aiki anan da, Madam zan kaima katin biki, muje" tai maganan tana bude motar suka fito atare, tundaga mesa Yusuf Security ke kallon Aneesah yakasa yarda cewan itane yaje gidansu Aneesah kaman zai haukace yana neman ta saidai makota suka cemai maman Aneesah tai aure sun koma cikin Abuja yanzu, karasawa har wajen kofa sukayi tashi Yusuf yayi yana kallonta ahankali yace "Aneesah kece ko idanuna ne" yay maganan yana kallonta tundaga kasa har sama, dudda dai Aneesah ce haryau da wanan hijabin daya sani Amman takara wani mahaukacin kyau tadawo wata yar gayu, wani hadadden takalmi ne na tomford akafarta tana rike da jakan Keith and Charles, fuskarta babu makeup amma fatarta har haska fuska yake tsabagen yanda yake kyalli, lips dinta sunyi jajir gashin goshinta sun kwanta lubbbb alamun tasha hutu, na giranta sunyi baki sidik suna shining, cikin wani irin yanayi na mamaki yace "Aneesah kece" dan murmushi Aneesah tayi tana daura hannunta kan kofan ganin baida niyyan budemusu sai kallonta yake tace "nine Yusuf" ta tura kofan itada Ihsan suka shiga, gani tayi babu ko customer daya a shagon sai Fatima dake bayan kanta tana taunan cingum tana danna waya, ganin Aneesah yasa itama ta saki baki ta tashi daga kan kujeran datake zaune tana kallonta, murmushi Aneesah tamata ba tace komiba sukai sama har gaban office din Madam, tunawa tayi da duk lokacin da zatazo wurin yanda gabanta ke faduwa hmm rayuwa kenan.
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_


Ahankali tasa hannu tai knocking kofar, daga ciki Madam tace "come in" bude kofan ahankali Aneesah tayi ta shiga Ihsan biyeda ita, chak madam ta tsaya tana kallonta tayi mugun mamakin ganin Aneesah, baki Aneesah tabude zatai magana cikeda masifa Madam tace "karma kifara kicemin kinzo karban salary kine dakika bari baki karba ba talauci ya koroki, wlh bazan barki ba, baneman daban miki ba Aneesah, har Yusuf security nasa yajemin gidan zuwanshi na farko yacemin yaganki rashin lafiya kikayi, zuwanshi na biyu aka fadamia cewa maman ki tai aure kun koma garin Abuja hala rashin kudi yasa kika dawo toki koma bana bukatan ki, kin zaci dan kinbar shagona zai mutu ne ba gashi yanzu kin ganiba still going smooth and alive, meya kawoki office dina?" murmushi Aneesah tamata dan yanzu ko kadan bataji tsoro ko dare din datasabaji ba in Madam namata bala'i, murmushi tasakeyi ta ijiyema Madam hadadden katin bikin ta tace "Madam katin bikina daman na kawo miki" da sauri Madam tabude katin bikin tana karanta content din ciki senate president of Nigeria datagani da tambarin eagles din Nigeria datagani a jikin invitation card din yasa tawani irin mike daga kan kujera takasa dena mamaki tadafe kirjinta tace "Aneesah dandan senate president zaki aura na Nigeria?" shiru tayi Aneesah bata amsata ba, Ihsan da Madam tagama bata haushi ne tace "eh shi zata aura, the only male child of the senate president of Nigeria ma for that matter" wani irin zubewa Madam tayi kan kujera tace "chineka e chidimandara, alobidani, Lord you are the most high alobidani, Indeed you are father to the fatherless" kallon Aneesah tasakeyi tace "chaiiiiii Aneesah you this black gurl na you senate president pikin talk say he wan marry jesus christ of Lord chaiii, why he no see my pikin naaaa chaiii" baki Ihsan ta tabe ta kalli Aneesah tace "dalla chan mutafi mesa kika kawomu nan, wuce mutafi" ahankali Aneesah ta rataya jakarta back tace "okay muje" bude kofa sukayi sukafito Madam sumbatu kawai take tana mamaki dama yaran masu kudin nan naganin bakake suce sunaso, jibi fa Aneesah baka kirin, yar talakawa da sauransu, why he no see her fine pikin now, yellow paw paw da ita Chioma.
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_


_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Daidai sun fara saukowa daga stairs wayar Aneesah ya shiga kara irin ringing din iPhone dinan kafin ma Aneesah taciro wayar daga jaka Fatima tadago kai dan taga daga ina takejin ringing din iPhone, wayar Aneesah taciro ganin Snuggles ajiki yasa tadanyi murmushi, ahankali tai picking call din takara akunne daidai sun karasa saukowa kasa sunyi hanyar fita daga eatry.


Daga ta dayan bangaren cikin fushi sosai Aliyu yace "wa kika tambaya izini kafin kifita eh? Waya baki izinin fita?" yanda Aneesah taji yana maganan azafafe kanaji kasan ranshi yabaci yasa gabanta yafadi sosai to ita taga su Abba sun riga sun bata izinin tafiya me zatawani cemai zata fita banda hakama an hanashi ya ganta, daidai sun karasa wajen kofa da sauri Yusuf Security yabude musu kofa yana kallonta kaman tsohon maye yace "dan Allah Aneesah minti daya, inada magana dake mudan kebe maganan mai mahimmanci ne" cikin wani irin

Please Login or Register in order to submit comment