Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaja bargon kafin tace "wani abu ya dauketa sai bayi, wanka yamata mai kyau yatayata tai wankan tsarki sai wani daddauremai fuska take sanan yanadota a towel suka fito falo tsaneta yayi ya shiryata ta hanyar maida mata da kayan ta shikuma ya koma wardrobe yadauko wani white jallabiya ya shimfida dadduma yajasu salla sukayi bayan sun idar ya rungumota jikinshi suna azkar lamo tayi tana azkar dinta dan sosai takeson kamshin da Dady keyi, ahakama wani baccin yay awon gaba da ita akan jikinshi, bakinta dataji ana tsotsa yasa tabude ido, hada ido sukayi da Dady, ture shi tayi cikeda masifa tace "me haka dannazo dakinka nace kamin wani abune?" da sauri Dady cikeda lallashi yace "a'a bakice ba yakuri" kwafa tayi ta mike tsaye tace "nina tafi na shirya kaduna" kallonta ya tsaya yi yama kasa mata magana tabude kofa tafita tana tafiya ahankali afalo ta tsaya tadau gyalenta tafito tanadan murmushi what a nice night she had, flat dinta tabude ta shiga bayi ta shige direct tahau wanka already ta riga ta shirya kayanta a akwati tsaf, fitowa tayi daure da towel a kirji tana rikeda karami tana shashare jikinta, bude kofan da akayi yasa tadago kai Dady ne yashigo dauke da tray da mug din tea ke kai sai sliced bread, dauke kai tayi abinta ta cigaba da shiryawa ahankali yazo kusada ita yace "zokiyi breakfast" batare data kalleshi ba tana makala dan kunne a kunnenta tace "ka ajiye a wurin ina zuwa" ajiyewa Dady yayi ya zauna agefen gado yana kallon yanda take shiryawa cikin wata atampa mai kyau saida tagama tsaf sanan ta taho tea ta karba tahau sha, ahankali Dad yace "bread dinfa" "ni banson bread" bai karacewa komiba sai kallonta yake ko kadan baison taje babu yanda dai zaiyine dole yabarta taje bikin yarta, gamawa tayi ta ijiye cup din ta mike zata wuce da sauri yarike hannunta jawota yayi yace "zonan muyi magana plss" zaunar da ita yayi agefenshi, ahankali kaman mai tsoronta yace "na ijiye direban dazai kaiki harchan, nabaki sati daya da kwana biyu shi zakiyi a wurin kidawo, banda haka" yasa hannu yazare wata envelope a aljihu ya ijiye mata akan cinya yace "dan Allah, dan Allah nace badan niba ki kaima Aneesah wanan" da sauri Ammi tadauka dantai alkawari inhar kudine bazata taba karbaba dan babu abinda Aneesah zatayi da kudinshi, jin paper ne aciki yasa ta kallai ahankali yace "wasika ce namata inamai rokonta gafara tayafemini" ajiye envelope din Ammi tayi a gefe dan itama tanaso takai abu makamancin hakan dan Aneesah tasan he's sorry, kudi masu yawa yaciro ya ijiye mata akan cinya yana kallon fuskanta yace "kirike wanan tareda me incase, ko ciwon kai kikaji ki kirani kifadi mini dan inada doctor a kaduna yazo yaduba ki, don't stress yourself in anyway, kibani address din gidan zanzo ma Aneesah daurin aure in sha Allah" tabe baki tayi tace "bama gayyatan ka mu mahaifanta kadai mun isa" tamike tsaye tareda jawo handbag dinta sai kallonta yake ta tura envelope din da kudin daya bata ciki wanda suma ta karba ne dan duka kudaden dayake bata lokacin dasuke shiri shita hada ta turama Baffa ama Aneesah kayan daki dashi, hada komi tayi tsaf tazura hijabi zata sa hannu taja akwatin ta da sauri Dady yakarba yace "kibarshi lemme help u" Jan mata jakan yayi suka fito har waje ya kulle mata flat dinta sanan suka fito tsakar gida kallo daya Ammi tama Aliyu dake kan exercise machine dinsu yana kallonsu shima ahankali yadauke kai yacigaba da abinda yakeyi zuciyarshi kaman zata fashe Dady jiyayi kaman zai mata kuka, mota ta shiga Dady ahankali ya duko yama forehead dinta kiss murya chan kasa yace "be safe, love you" dauke kai tayi yadanyi murmushi tareda maida kofar motar yarufe driver yajata suka fita daga gidan karasawa Dady yayi wurin Aliyu zaiyi magana Aliyu yadaga mai hannu yana gudu akan treadmill dinshi batare daya kalli Dady ba yace "when is the wedding?" ajiyan zuciya Dady yasauke kafin ahankali yace "on Saturday" cigaba dawani irin gudu Aliyu yayi da sauri da sauri kaman zai tsinke kakafunshi yana fuzar da iska zufa ya zuba daga goshin shi zuwa kirjinshi, kasa jure kallonshi ahaka Dady yayi yajuya da sauri yakoma flat dinshi.


Saida sukai nisa sosai sanan Ammi tacema driver ka kaini Park, da sauri direba yace "but Alhaji yace kaduna zan kaiki Madam" cikeda masifa Ammi tace "nadaice ka kaini Park kona kira Alhajin nacemai kaki yimin abinda nace kayi ne" da sauri yace "No sorry Ma" yay kwana wani babban Park din motoci yakaita, parking yayi Ammi tace "kafita kayomin shattan motan dazai kaini Kaduna" kallonta yayi amma baida bakin magana dan aikinshi a gidan Alhaji yafimai komi intasa Alhaji ya koreshi yanzu yaya zaiyi" saukowa yayi nan tulin direbobi suka tareshi ina zuwane malam yace "shattan mota mukeso" suka jashi ciki wani mota mai kyau yasamo mata motar yabiyoshi yabude motan yace "Madam ansami motar ga direban nan dubu ishirin da biyar zaki biya" gyadakai Ammi tayi tace "shikenan sa akwatina a boot" saukowa tayi ta shiga motar direban na gaidata ganinta babban mace harda ciki, sanan yaja motar ajiyan zuciya Ammi ta sauke bukatar ta tabiya tasan Alhaji can use the direba yakawo su daurin auren Aneesah ran biki itakuma batason haka, addu'an tafiya tayi sanan tacigaba da kallon hanya she can't wait to see her Aneesah, burinta kawai taga yarta. Wayartane daya shiga kara ta kalla Dady datagani yasa tai murmushi tasan za'ayi hakan dama, maida wayar tai silent ta ijiye abinta.






Wuraren karfe uku ta isa kaduna har kofan gidan Baffa, parking motar yayi tabude ahankali tafito tana murmushi tsabagen murna daidai lokacin Baffa yafito zai tafi masallaci la'asar ganin Ammi yasa yarike baki. "wai wai wai, barka da zuwa, marhaban dasu lale Maman Aneesah" yakaraso wajen yana karban jakan Ammi daga hannun direba daya ciromata daga boot itakuma Ammi tana gyara hijabin jikinta tana murmushi cikeda murna ta mikama direba kudin nashi tace "nagode" tace "Baffa ina yini" cikeda barkwanci Baffa yace "bar gaisuwan nan bari nadawo daga masallaci tukun, ai yar wajen naki nacikin gida sai kinga abubuwan da aketa dafa miki a gidan nan yau ni wlh banmasan sunan wasu abubuwan da ake bani inaci ba" dariya sosai Ammi tayi da maganan Baffa ta kwada sallama. "Assalamu Alaykum mutanen gidan nanan" wani irin ihu Inna da matar Nasani sukayi suka taho da gudu. "oyoyo oyoyo, ga baki ga baki, ga mutanen Abuja sun shigo, ke Aneesah kina ina ga Ammin kinan ta iso" Inna ta kwalama Aneesah kira tana rungume Ammi, dan dariya Ammi tayi tana bubuga bayan Inna tace "sannu, sannu fa da kokari Innan su Khaleel, Maman Walili na ina yarona yake?" tama matar na Sani data karbi handbag dinta tarike tace "Alhamdulillah Maman Aneesah sannu da zuwa" Baffa yace "kunga ni gaisuwan taku ta isheni ungo jakarnan Maman Hamma kaita ciki natafi masallaci" karba Inna tayi Baffa yafita da sauri, Inna tace "kumuje ciki mun tsaya atsakar gida kaman an dasamu" dariya duk sukayi suka daga kafa suka fara tafiya. "Ammi nah!" Aneesah datun dazu tafito daga bayi tana kallon bayan Ammin nata takira Ammin da karfi, chak Ammi ta tsaya jin muryan yarta datayi har cikin ranta kafin ahankali ta juyo, Aneesah tagani daure da zani a kirji duk kumfa awuyanta kana ganinta kasan bamata gama wankan ba tafito, tundagakai har kafa take kallon Ammin kaman mafarki take Ammin tane yau atsaye agabanta hawaye yaciko idanunta sosai, ahankali muryanta narawa sosai tace "Ammi na" wani irin murmushi Ammi tasakan mata kafin ahankali tabude mata hannuwanta alamun tazo dawani irin masifar gudu Aneesah ta taho zatafada jikin Ammin inna ta rikota kar ai aika aika tace "ke bakiganin maman takine wanan tsalle haka dakikayi zaki fada jikinta aisaiki kashemata abin cikinta" dawani irin sauri Aneesa ta kalli cikin Ammin daya fito ta hijabi dan ko kadan bata luradashi dazuba, hawayen daya zubomata ta share tana kallon cikin kafin ahankali takarasa gaban Ammin dake kallonta ahankali hannunta har rawa yake tadaura kan cikin Ammin, wani irin shafa cikin tayi kaman wawuya sanan tadago kai ta kalli Ammi da idanunta dasuka cika da kwalla sosai dayawani irin gangaro tace "Ammi za....zaki haifan min kani ko kanwa Ammi nima inzama inada kanni?" gyadamata kai ahankali Ammi tayi tana kallonta, wani irin fadawa jikinta tayi tafashe da kuka sosai kaman yar yarinya tace "Ammi thank you, inason kannai zaki haifamini nima inada kani ko kanwa thank you Ammi na, am so so so happy yau" tafashe da kuka sosai dan wani irin farin ciki take na ganin mahaifiyarta da kuma na ganin ciki, Ammi bata tabajin kaunar cikin nan ba saiyau dataga Aneesa na wanan kukan murnan akan cikin tanaso ahaifa mata kanni, murmushi tayi tadan share hawayen daya zubo mata tadago Aneesan dake kuka sosai, bakin hijabinta tasa ta share mata hawayen tana kallon fuskanta kafin tadan lakaci hancinta tace "oya kukan ya isa haka daga ganina sai kuka, jeki karasa wankan yimaza saikizo" murmushi Aneesah tayi ta gyadamata kai ahankali tace "kinajin yunwa Ammi namiki girki fa" goshinta Ammi ta sumbata tace "Tom jekiyo wankan kizo kibani, I sauri" ahankali ta duka tama cikin Ammin kiss Inna tace "laaaaa kagamini iskanci tun aciki zaki batamana yara, wuce dalla kiyo wanka" murmushi Aneesah tayi akunyace tawuce bayi da sauri Ammi tabita da kallo tana wani irin murmushi tanajin son yartata aranta kaman ta hadiye ta, hannunta Inna takama tace "muje ciki kihuta bake kadai bace kina bukatan hutu" binta Ammi tayi suka shiga ciki nanfa hira ya barke, agurguje Aneesah tafito daga wankan tawuce dakinta tasa doguwan riga, komai bata tsaya shafawa ba ta tattaro abubuwan datama Ammi tataho dakin Inna dasu nan fa aka bude sabon shafta itadai tana makale da Ammi daga bayama baccinta tayi kanta kan cinyar Ammi, Ammi sai kallonta take ganin yanda fatarta tai kyau tai bulbul, ganin tai bacci yasa takawo ma su Inna zancen gyaran jikinta tace tama wata mata magana da Maman yar aikinta tahadata da ita gobe zatazo daga Abuja yar Chad 🇹🇩 ce, zatama Aneesah gyaran jiki in and out.

Aranan da daddare Hafiz yazo ya gaida Ammi, Ammi ta yaba da hankalin yaron sai anan hankalinta yakara kwantawa, dudda yaso ganin Aneesah hanawa Inna tayi tace "shikuma da Amarya sai in an kawota dakinshi" hakanan yatafi yana kunci danyaso ganinta._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



6️⃣8️⃣



_Bonus kumin addu'a dan Allah, Allah yabiyamin bukatuna na alkhairi_



_Asabar_
"Yau antashi dawani irin mahaukacin ruwa a Nigeria gabaki dayanta, daidaikun garine kawai ba'a wanan ruwan saman fa haka naji a sanarwan redio nagarta kaduna, matsalan bukukuwan Augusta kenan ruwan sama ke hana shagali" cewan Inna data shigo baranda da matayen makotan su dasuka shigo da wurwuri dan afara dafe dafen abincin biki tana zuge leman data dauko, Maman Walili ne tace "wai Inna ina Aneesah ne, ina nemanta nabata jakanchan da abokin Likita yakawo yanzun nan yace nabata wai shine kayan dinner dazata saka da daddare" da sauri Inna tace "kai kekam Maman Walili Allah ya yiki da mantuwa, Aneesah na nan makota fa gidan talatu anan take fatin su na amare, kinsan yaran Talatu su Salamatu kawayenta ne, sunama chan banma jin tayi wankaba tukunna dan yar Chadi natare da ita ana mata surace ne" da sauri Maman Walili tace "au, namanta wlh, ban leman nan kiga naje nakai mata" mika mata leman Inna tayi ta karba tabude tareda ficewa daga gidan tana tafiya da sauri, gidan dake kusada nasu ta shiga tana korafi. "Allah natuba wanan ruwan dai yabata mana biki wlh, ruwa tun asuba har yanzu takwas saura bayida ma shirin daukewa" shiga gidan tayi ta hango wasu yan mata kusan su bakwai cikinsu biyune kawai kawayen Aneesah yaran gidan, sauran zugan kawayen su ne suka gayyato dan Aneesah batada kawaye, hangosu yasa Maman Walili takarasa wurin rumfar dasuke girki tana kallan abinda sukeyi pepper meat tace "ahh lallai ango yabada kudi enough wanan da ake pepper meat" duk dariya sukayi daya daga cikinsu tace "wlh angon yayine maman Walili babu mako hakama abokin shi, kome mukece subamu bamasa tayi bamu suke kai tsaye, indai haka likitoci suke zanso nima na chapko wani" dariya duk suka shigayi, Maman Walili tace "nidai ina amaryan?" dariya duk sukayi sukace "tana dakin Maman mu tareda Ammi da wanan matar" cikin Maman Walili tayi tai sallama babu kowa afalon hakan yasa tai corridor da Ammi taci karo dake fitowa tareda maman su kawayen Aneesah tace "Ammi ina Aneesah sako abokin ango yabani nabata" dakin dasuka fito daga ciki Ammi ta nuna mata tace "ninayi gida zanje nadan kwanta kaina naciwo" "assha sannu, nima ganinan zuwa abin nan kawai zan bata sannu, karfa kiyi ciwo ana bikin yarki wayaga maman Amarya ba lafiya" dariya dukansu sukayi harda Ammin tadan bugi kafadar Maman Walili datai gaba, ahankali tabude kofar dakin tareda sallama yar Chadi kadaice zaune tana juya wani cup da wani ruwa kaman ruwan bunu ke ciki dake tiriri sosai sabida zafi tace "ina Aneesah Yar Chadi?" "tana bayi" baki Maman Walili ta tabe tace "wlh bazan iya jiran ta ba, gashi kibata abokin mijinta yabani nabata, nizan koma girkin daurin aure mukeyi" da sauri tafita.





Tsaye take abayi ga ruwan turaren da aka hadamata akace ta shiga amma ko shiga batayiba tana tsaye jikin window tana kallon yanda ruwan sama ke sauka tayi nisa atunani. Tarasa meke damunta she feels restless yau dinan, gabanta sai faduwa yake, tafadan ma Ammi, Ammi tace sabida yau za'a dauramata aure, yauzata dawo matar aurene yasa takejin hakan amma duk intaji hakan tadinga cewa. "Allahu Rabbi La ushrika bika shai'an" koma menene Allah zai jibinci Al amarin, duk in gaban nata yafadi saita furta haka, gatanan ne kawai she's not happy she's not sad either, deep down she feels empty, she feel kaman she want something else but batasan meyeba, she feels she want something more but batasan wat ba exactly, everydrop of water daya sauka kasa saitaji sound din har cochlear dinta, lumshe ido tayi da sauri sabida feshin ruwan saman daya watso mata a fuska dake dauke da kamshin ruwan sama da kuma kamshin kasa, knocking kofar da akayi yasa da sauri tabude ido yar Chad ce tace "kin gama da ruwan turaren Aneesah" da sauri ta shiga ruwan bahon jikinta har rawa yake tace "a...a'a nakusa Anty" to kiyi sauri, agurguje tai wankan tafito sai wani irin mahaukacin kamshi take nan yar Chadi tabata ruwan bunun maganin aka cigaba da harhadata dan makeup artist karfe sha biyu zatazo amata makeup sabida 2ne daurin auren, dinner kuma karfe bakwai din yamma da abokanan Hafiz suka hadamai.







_Abuja_

Wani irin mugun zazzabin daya turnike Aliyu ayau dinan yasa dagashi har Dady babu wanda ya iya zuwa masallaci sallan asuba, agida sukayi Dady na rikeda shi, cikeda rarrashi Dady da kaman zai haukace yace "Aliyu dan Allah karka kasheni, ka warke for my sake Gadanga na, nasayo ma brand new ferrari jiya, bullet proof car as compensation na rashin samin auren Aneesah amma kaki ka warke, kahanani kiran Dr, me kakeso namaka? So kake kamutu Aliyu? Am sorry Aliyu na actions dina ya cutar dakai ba kadanba, am so so sorry Son kayafemin kaji" hawaye ne suka zubo ta gefen idanunshi ahankali yakama hannun Dady yadaura kan kirjinshi dake wani irin abnormal beating ya daura nashi hannun akai yana wani irin sauke ajiyan zuciya kaman wanda yay kwana dari yana kuka ya lumshe ido gabaki daya kaman wanda yay bacci, addu'a Dady yacigaba da tofamai ganin bacci na neman kwashe shi, Wani irin wahalallen bacci ne yay awon gaba dashi....

_ahankali wani mutumi da duka duka bazai wuce sa'an Dady ba yana sanye da fararen kaya ya tsugunna agabanshi, wani farin ruwa ya yayyafamai a fuska hakan yasa ahankali yabude idanunshi dake cike da rashin lpy, murmushi mutumin yasakin mai tareda cupping fuskarshi yana kallon yanda yake kallon fuskarshi da shanyayyun idanunshi_ _yace "don't give up yet Aliyu Hydar, ba'a riga an daura ba, kanada sauran lokaci har yanzu, kanason Fateema har zuciyanka ninasan da hakan, ka shirya hakura da salwantar da duka wanan soyayyar ne ma wani chan?"_ _cikeda wani irin yanayin ciwo ya girgiza mai kai, murmushi mutumin yayi ya bubbuga kafadarshi harsau uku,_ _yace "katashi, kanemo duk inda abin kaunar ka take aduniyan nan u still have time Aliyu, you still have time! You still have timeeee!!! Katashi yanzu! Yanzu!! Yannnnzuuuuuu!!! "_

firgigit Aliyu yafarka daga baccin daya kwashe shi yatashi daga kan kafar Dady yana kallon ko ina yana neman mutumin dayagani yanzun nan yamai magana, mafarki yake ne?. "Gadanga na kai lafiyan ka, me kake nema?" juyowa yayi ya kalli Dady ahankali cikin muryanshi dabata fita sosai yace "Dady a ina Aneesah take?" cikeda tausayin dan nashi Dady yace "a kaduna ne wurin Baffan ta Alhaji Isma'il Maikwato" kujera ahankali Aliyu yadafa zai mike da sauri Dady yace "ina zaka?" cikeda rashin lafiya yace "I want to shower Dad" tashi Dady yayi yataimaka mai yakaishi har cikin bayin sanan yace "mezan dafama mezakaci?" yatsine fuska yayi yace "cook Indomie for me Dad, with omelette sai coffee" da sauri Dady dudda bai wani iyaba yace "to dan Albarka na, Aliyu Hydar namiji, bari nadafo ma da sauri be fast" fita daga bayin Dady yayi cikeda murna ganin harzaici abinci yay kitchen dinshi ganin babusu Indomie a kitchen dinshi yasa yafita, flat din su Rauda yayi yasan su Hajar bazasu rasa Indomie ba, Hajar yakira daduk tai sanyi yanzu suka shiga kitchen din tare tana tayashi yanyanka veggies dan Aliyu nason veggies a abincin da kuma sea food, he's not a fan of red meat amma yanaci but not always.


Agurguje yay wankan da ruwan zafi sosai sanan yafito daure da towel a waist jikinshi amurnurde tsabagen exercise, agurguje yabude wardrobe wani sky blue VIP giznar shi dabaima taba sawaba yadauko ya shirya cikinshi bakaramin kyau yayiba, ya feffesa hadaddun turaren shi yadau wallet dinshi dake dauke da kudade da atm cards dinshi yazura herms cover shoe dinshi yana tafiya ahankali danhar jiri jiri yake gani, idanunshi ne suka sauka kan key din ferrari motar shi da dad yabashi dake cikin kwali, kwalin yadauka da sauri yabude yazaro key motar ya yar da kwalin sanan yafito ahankali yana daddafa bango kaman wanda ya sha giya harya karasa wajen motar data mugun hadu fara fat, bude motar yayi yazauna wajen direba cikin motar looks like heaven tsabagen kyau, yatada motar yaja Gate man dinsu yabude mai dawani irin masifaffen gudu dama motar badai guduba kaman zata tashi sama yakejan motar dan yanzu is 10:50 shadaya saura.



Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa
Ikon Allah ne kawai ya shigo da Aliyu garin kaduna misalin karfe daya, ganin idanunshi na juyawa kaman zai suma yasa yay parking da sauri wajen daidai signboard din Eye center kaduna yafito yana tafiya da kyar ya karasa wani babban shago dayagani, murya chan kasa yace "give me farm fresh yogurt" da sauri mutumin yace "to Alhaji" dauko yogurt din mutumin yayi yana kallon fuskan Aliyun yace "sorry Alhaji hala ba lafiya ne" gyadamai kai Aliyu yayi yana karban yogurt din yabude ya kafa abaki yafara sha saida yay kusan rabi sanan ya ijiye mutumin yace "sannu" wallet Aliyu yazaro yaciro dubu biyar yamikamai yace "hold d change" cikeda jin Dady mutumin yace "nagode Alhaji sosai, Allah kara sauki Allah kuma yabaka lafiya" ahankali yace "Ameen" yana kara kai yogurt din bakinshi saida ya shanye tass sanan ya sauke ajiyan zuciya yadanji dan karfi da dama dana dan baya ganin jirin yanzu, dagokai yayi ahankali ya kalli mai shagon hakanan ranshi yagayamai ya tambayay, ahankali yace "tambaya nike Malam" cikeda farin ciki mai shagon yace "Allah yasa nasani" ahankali Aliyu kasan please kasan gidan "Alhaji Isma'il Mai kwato da ake bikin yar wajenshi yau?" da sauri mai shagon yace "laaaa ba shakka nifa Ince naganka kaci gayu haka kaman ango, ashe kaima daurin auren kazo aiko ninasan gidan mai kwato dan abokin sana'a nane wajenshi muke sayan shanu da ragunan salla" wani irin ajiyan zuciya Aliyu ya sauke kaman ya kulle ido yabude yaganshi agaban Aneesah, da sauri yace "inane banso nayi missing daurin auren" da sauri mutumin yace "kaga kamike express road dinan sambal karkadau wata kwana kaita kallon bangaren haggun ka zakaga wani gidanmai mai suna Danaba, layin jikin danaban zaka shiga dazaran ka shiga zaka gane gidan bikin dan dandan babban mutum zata aura likita ne yaron anguwan makil yake da motoci danma wanan ruwan dayaki daukewa ne yama mutane cikas wlh da tuni ko ina yacika da hayaniya" sosai Aliyu yaji zuciyar shi namai zafi, ahankali yace "dan Allah a ina ake saida hijabi inaso nasai hijabai ne" dariya mai shagon yayi yace "hala gudunmawar ka kenan dan amaryan akwai sa hijabi, bantaba ganin yarinyar da gyale ba, kaga kaita tafiya kawai akan hanya zakaga masu saida hijabi dasu safa da nikabi" , ahankali Aliyu yace "nagode" sanan yajuya ahankali ruwa na sauka akanshi yawuce ya shiga motarshi mai shagon na leko motar yana mamaki wanan kodai dan shugaban kasane yaro ga kyau ga kudi jibidai mota mai numfashin dayake ja.

Bala'in gudu Aliyu yake yana kalle kalle har idanunshi suka sauka akan shagon da ake saida hijabi tsayawa yayi yafito yana tafiya ahankali yacema mutumin shagon "Malam hijabi nakeso kaman wanda zaima mai tsawona har kasa yanajan kasa" kallonshi mai shagon yayi yace "okay yadi shidda da kusan rabi kenan" zama Aliyu yayi kan kujeran ahankali yace "OK ayanka adinkamin yi sauri, kuna saida nikabi ne?" "eh muna saidawa yallabai" gyadakai Aliyu yayi ya daga agogon hannunshi na rolex yana kallo about 1 :15 yanzu, ganin yanda yayyafin da akeyi ke zuba kanshi yasa mai shagon yace "ka shigo ciki Alhaji kar ruwa ya jikaka" dan shigowa ciki Aliyu yayi yana kallonshi, cikin minti baifi gomaba yagama dinka hijabin sanan yace "a dauko nikabin ne yallabai" gyadamai kai Aliyu yayi yadauko yace "kudinka ya tashi biyu da dari takwas" zaro kudin dabaimasan yawansu ba yayi yamikamai yajuyo yashiga mota da gudu haryakai wajen daidai gidan man danaban kafinma ya shiga unguwan ya hango motoci shiga yayi yayi parking daga baya baya, tareda kashe motar, ajiyan zuciya ya sauke ya kalli hijabi da nikabin da aka dinkamai, ahankali yajawo hijabin ya warware yasaka daga zaunen, sanan yadauko nikabin yana gyara madubin gaban motan ya daurashi tsaf, farin glass din mai karamin lens daya daukone yasaka a idanun sanan yabude motan yafito yana numfashi sama sama dan baisababa jiyayi kaman nikabin ya shakemai wuya, kallon kanshi yayi ta jikin glass din motar yanda hijabin ya saukanmai danko takalmin shi ba'a hangowa yay kato cikin sanan yay kato ciki, kulle motar yayi yafara tafiya ahankali kaman mace yana shiga anguwan sosai ruwa na sauka akanshi yana kallon tulin mazan dake cikin wata runfa an tsaitsaya ana magana za'aja daurin auren zuwa karfe uku sabida ruwan da akeyi ga Baffan ta na zuwa dan sun fita dole ajirasu, wasu yan mata dayagani sunci gayu suna sanye da anko sun fito daga wani gida ya tare tareda lankwasar da muryan shi kaman wata mace yace "yan mata dan Allah wani gida amarya take zanganta ne is urgent" daya daga cikin yan matan ne tanunamai gidan dasuka fito daga ciki tace "nanne tana dakin su salamatu" baima tsaya musu godiya ba yashiga gidan da sauri gabanshi nawani irin faduwa ya kalli yan matan da sukacici gayu ana kwalliya, falon dayagani abude ga takalmomin yan mata yafada, yan mata ya gaggani zaune wasu nacin abinci wasu na rawa dan sun kunna wakan Zee baby a speaker falon yacika da hayaniya, wajen wata dayaga tanata kallonshi yayi tunda ya shigo da sauri

Please Login or Register in order to submit comment