Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi tayi akunyace tana boye fuska murya chan kasa yace "kinsan ni menake so kimin?" da sauri tadago kai ta kalleshi tana girgizakai, ahankali yace "banson kikarama any namiji magana in your life, kowani taimako ko help kikeso komin ina nake ki kirani I will come, banson kowa ya rabeki, zan iya kashe duk wanda yazo yace yana sonki, kisa har lahira, u are my wife Aneesa, Ke gonata ce baby wanda ya isa yazo yace zai shiga gonata ko zai hada wata mu'amalat da ita, promise me I will always be the man u will always love till eternity" gyadamai kai tayi ahankali murya chan kasa tace "namaka Alkawari Ya Aliyu na" murmushi yamata yace "inaso nafada ma Dady ina sonki I want to marry you" makemai kafada tayi alamun a'a, kaman zaiyi kuka yace "why now?" ahankali tace "kaga Ammi na da Abban ka basu dade dayin aure ba mubari sundanyi kwana biyu saimu fadamusu, kumani inaso nai jamb har University nafara ko 100 level ne saimuyi aure" girgiza mata kai yayi kaman zai sakin mata kuka yace "zan iya jira kiyi jamb din tunda ending of this month ne but bazan tsaya jiranki har kifara University ba, ni nakosa nai aure, nakosa kizama matata ki haifan mini plenty babies" murmushi tayi akunyace zai sake magana washing machine din ya shiga kara din din din, alamun yagama wankin tass, kashe machine din yayi yaciro mata kayan yasa mata a bucket yace "muje backyard muyi shanya" daukan mata bucket din yayi itakuma ta dauki empty basket din suka fita har sunkai wurin kofan fita tace "laaa Ya Aliyu ka manta bakadau neck tie din Dady dayace ba" murmushi yayi yace "bakin mantan dani duniyan danake ba, am coming" ajiye bucket din yayi yawuce yakoma ciki tanabin bayanshi da kallo ganin haryadan soma chanza mata daga fara excerise dinshi, akasa ya hango necktie din kusa da kofan wani dan daki haka da suke zuba su omo da hypo abubuwan dai wanki , tsugunnawa yayi yace "gat u" yadauka harzai tashi idanunshi suka sauka kan kafafu hudu tacikin dakin omon, da alamu akwai mutane a wajen kenan all maganganun dayayi da Aneesa angama saurara kafafun babban mace dana yarinya dayagani ne yasa bai bude kofan ba yatabe baki yamike tsaye yasami Aneesa abakin kofa sukai backyard a binsu ko ajikinshi.


Ahankali Mama tabude kofa tafito Hajar datai kini kini da fuska biye da ita tace "nidama Mama naga yanda yake yawan kallon yarinyar, harda jiyama dasuka dawo, ashe sonta yake saisa ya wulakanta Nafisa" shiru Mama tayi tayi mugun nisa atunani, tabata Hajar tayi tace "Mama kinko maji menake cewa kuwa? Tunanin me kikeyi haka?" kallon Hajar Mama tayi for few seconds tace "Hajar lokacin koyama Aliyu lesson yayi and yarinyar nan dakike gani is what am going to use, shekara da shekaru ina harin yaronan Allah bai bani damaba yau da Allah ko yasa mukaji conversation dinsu is a sign cewa kome zanmai yanzu zanyi nasara" murmushi Hajar tayi cikeda jin dadi tace "Mama ki ramamin dukan da mugun yamini, sanan ki rama hana auren Rauda dayayi da Nazif," gyadamata kai Mama tayi tace "uwa ta auri uban d'a, idan kuma nabari d'an ya auri yarinyan uwan aiza awayi gari mun rasa komine, duka kadaran mahaifinku maidama Aliyu da yarinyar nan su ubanku zaiyi to bazata yuba" dan rage murya tayi kafin tace "kawo kunnenki kiji Hajar" da sauri Hajar ta mikama Maman nata kunne cikeda kosawa taji me maman zatace, wani magana maman tafadi mata akunne a mugun tsorace Hajar ta fizge kunnenta ta kalli fuskar Maman tata tace "Mama kisan kai?" rawa jikinta yafara tana girgizakai tace "a'a gaskiya Mama, kema kinsan banson Ya Aliyu, na tsaneshi sosai kome zamumai mumai banda kissan kai Allah yahana wlh, a'a I always support you Mama kema kin sani but wanan no, kashe shifa Mama zamuyi how? Haba kashe rai nidai a'a Mama" wani mugun harara Mama ta watsa mata tace "dan ubanki kina dagamin murya so kike ajimu?" da sauri tace "sorry Maman mu, ai babu kowa a wurin, mama kinga dai karki kara furta maganan" dan dariya Mama tayi tana kara kallon koina ganin babu ko mahaluki daya yasa tace "listen to me jor, angayamiki banda hankaline? Bakiji kalmata ba zamuyi amfani da yarinyar nanne babu ubanda zaima san damu, we are going to use one bird to kill two stones, kinga dai yanzu daga maman ta har babanku babu wanda yasan da soyayyan su ko so is a good thing gwara mu aiwatar da abin kwanan nan tun kafin asan da suna soyayya, kawo kunnenki kiji plan dina" kunnenta Hajar tabata Mama tamata wasu maganganu dagokai tayi tareda gyadama Maman tasu kai duk tai wani iri harga Allah batason abinda Mama ke shirin aiwatar wa but Yaya zatayi hannunta Mama taja sukai daki tace "don't forget abinda nafada miki yanzu aikin ki shine samusu ido and watch all their moves, kibar komi a hannuna I will not involve you in this kinji" tai maganan tana bude kofan dakinsu suka shiga inda Rauda da sauran yaran ke kallon cartoons, daure fuska Mama tayi dan haryau bata amsa gaisuwan Raudan sanan tawuce dakinta Hajar tabita abaya suka shiga suka rufo kofa, tabe baki Rauda kawai tayi tacigaba da kallonta abinta.




Yau asabar yaune second week din Ammi agidan Dady, wani irin rayuwa take ginawa itada Dady dako Aliyu abin burgeshi yake, tuni Dady yamata kyautan wata dalleliyar mota, dan Ammi is every with a plus arayuwan shi, she gives him happiness, kwanciyan hankali da komi, kome yace yanaso shi zai ci idan yanacikin matsala he don't need to say it Ammi na ganin fuskanshi zata gane ta lallasai, in bed kuwa kullum saiyay sumbatu saisa ko kadan baya iya daga mata kafa, gurxanta yake kaman ba gobe.

mai fitarmin da littafi waje, wlh ban yafemiki ba, Allah kuma yana kallonki
Wani irin soyayya Aneesa da Aliyu sukeyi asirrace na fitan hankali, yanda take juya Aliyu yanda takeso ko saika rantse tamai asiri ne kowani abun, idan tacemai tanaso yay kaza she don't need to repeat it zaiyi saisa itama ko kallon maza batayi dan she really really love Aliyu da duka zuciyanta, Sosai Dady ke bala'in mamakin chanjin Aliyu all of a sudden dudda yaso dagowa kaman soyayya suke da Aneesa amma dai ya share yasan komeye zaiyi tsami watarana suji, yanzu yaronshi aiki yake zuwa office ba fashi and he's so good dan yanada ilimi kan business sosai, ga training dayake yi babu kama hannun yaro all in the name of abinda Aneesa kesone so zaiyi.
Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, keda Allah, kibiya anan duniya ko a lahira, littafina na kudi ne.

Agurguje Aneesa ke hada breakfast dan kar azo ita kadai direban su ke jira sutafi hadda tariga tai wanka ta shirya tsaf, shigowa kitchen din Ammi da dawowan ta daga dakin Dady kenan danyau itace mai girki ganin yanda Aneesa dabama ta lurada ita ke sauri ba yasa tace "ke lafiyan ki wanan saurin fa" kaman zatai kuka tace "Ammi banso nasa muyi lattin hadda ne kinga takwas saura fa" shigowa kitchen din Ammi tayi tareda dan sauke ajiyan zuciya tace "bakuda hadda yau harma gobe I think, mai makarantan ku yarasu da asuban nan aka kira babanku aka sanar dashi kar yara suzo ba makaranta karfe Tara ma za'ai jana'izar shi babanku ma yaja Aliyu sun tafi gidan rasuwan" ahankali Aneesa tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ammi na sanshi fa shiyamin interview da Abba yakaine, yanada kirki wlh, Allah ya jikanshi ya gafarta mai yasa yahuta" ahankali Ammi tace "Ameen" tasa mata hannu suka hada breakfast din sanan suka kai dining, divan wanda zataci Aneesa tayi taci sanan takoma sama duk jinta wani iri take, Al Qur'ani ta dauka tacigaba da haddan ta a abinta har wuraren 12, tana zaune kan dadduma adaki Dady ya kwala mata kira da sauri tafito ta sauka kasa atsaye taga Dady hakan yasa takarasa wajenshi tace "ina kwana Abba na ya hakuri" kanta ya shafa yace "hakuri Alhamdulillah, je kitchen kima yayanki pancake kinji zansa mamanki wani aiki a part dina" ya kalli Ammi datake murmushi kasa kasa yace "kitahomin da breakfast dina part dina Ummu Aliyu bari naje nadan watsa ruwa" gyadamai kai Ammi tayi tace "Tom" Dady yawuce yafita, Aneesa kuma tai kitchen tashi Ammi tayi zuwa dakinta asama wasu yan magunguna taciro tasha sanan ta sauko tadau basket mai kyau thada breakfast din Dady akai sanan tawuce tafita daga flat din.



Fitan Ammi bayan fitan Dady da Mama tagani dan tuntuni take tsaye jikin window dan tasama flat din ido kowani motsi sukayi akan idanunta. Ahankali tabude kofa da saurinta tai backyard tana gyara daurin wani abu a haban zaninta, ta wajen window kitchen dinsu Aneesa ta tsaya tareda rage tsawo kafin ahankali tai knocking kofar, da sauri Aneesa dake tsiyaya coffee a mug ta kalli kofan, kara knocking da akayi yasa tai kofan da sauri tace "waye?" cikeda fara'a maman su Rauda tace "nice, maman su Hajar ce Aneesa" ahankali Aneesa tabude kofan cikeda mamaki amma dai ta boye mamakin ta, shigowa kitchen din Maman su Rauda tayi tana kallon ko ina tace "nazo shanya ne shine naji kamshi duk ya cikamin hanci me kike dafamana haka Aneesa?" dan murmushin yake Aneesa tayi danko kadan bata saba da matan ba hasalima koda taganta ta gaida ta bata amsawa itace yau harda mata murmushi, matsowa kusada ita Maman su Rauda tayi tana kallon non stick pan din dake kan gas da pancake ke ciki tace "wa kike soyama pancake haka?" ahankali tace "na Ya Aliyu ne" murmushi Maman Rauda tayi tace "wow yarinyar kirki, toni baza'a sammin bane dan kamshin shi yakado ni nan" murmushi Aneesa tayi tace "to" plate ta janyo da sauri Maman Rauda tace "guda daya ya isa ma basai kin samin a plate ba".
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣4️⃣

_duk wacce ta fitar min da book waje batare data tuntubeni akan hakan ba Ban yafemiki ba_


Ahankali ta debi guda biyu tasa mata a plate din tabata karba Maman su Rauda tayi tace "wow Allah amfana Aneesa, gako pancake din so fluffy daga gani yaji su baking powder, naji gidan na kamshin kunun gyada kunyi kunan gyada ne?" ganin yanda Aneesa ta tsaya tana kallonta yasa tace "don't mind me fa, abinki dame karamin ciki Alhaji baya barinmu mu sarara wlh yanzu haka mamaki ma nach....." da sauri Aneesa tace "Ak....akwai kunun gyadan, uhmm munyi" danko kadan batason taji karshen maganan banzan da Maman su Rauda ke mata, murmushi Maman su Rauda tayi ganin tai accomplishing abinda takeso tayi tace "to ina kunun yake nadan diba?" ahankali Aneesa datai flipping pancake din dake wuta tace "yana kan dinning a falo" da sauri Maman su Rauda tace "dan dauki kofi ki debomin kinji yar albarka yabiyabimin rai karkima yaron cikina rowa yafito sa tabon rowan ki" murmushi Aneesa tayi tace "to" cup tadauka tawuce tafita daga kitchen din.
_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa_



Da sauri da sauri Maman Rauda ke warware kullin zanin ta taciro wani katin magani dakeda kwayoyi yan mitsi mitsi, ahankali ta ballo guda daya ta jefa a coffee da Aneesa ta zuba a cup wanda tasan na Aliyu ne, balle wani kwayan maganin tayi ta jefa cikin kullin pancake din ta danna ciki da sauri ta tura maganin cikin zaninta daidai Aneesa ta shigo rikeda cup din kunun gyadan da sauri ta tare Aneesa ta karba tana murmushi tace "Allah yamiki albarka, bari naje dashi nagode, wanan kamshi haka" bude kofan backyard din tayi tafita ranta fess agaban babban bin dinsu ta taka marfin yabudu ta jefa pancake da mug din kunun ciki tai gaba abinta tana kakkabe hannu tace "yauce ranan ka ta karshe aduniya Aliyu, lemme go and call Nazif akwai muhimmin abinda nikeso yamin".
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, zaki iya turo katin MTN dari uku idan bakida banki_


Agurguje Aneesa ke karasa soya pancake din sai turo baki take dan yanda tabama maman su Rauda biyu saitaga kaman bazai ishi Aliyu ba dan idan akwai abinci guda daya dataga yanaci da mugun yawa shine pancake dinta, karasa soya kullin dayarage tayi tai guda uku dasu sanan ta kashe gas ta wanke roban kulin da pan din Agurguje tadau tray tahada coffee da har yanzu ke tiririn zafi da pancake plate din akai, tsamai sliced raspberries asama sanan tazubamai honey tadauka tai dinning ta ijiye sanan tadau wayanta dake kan dining kiran layinshi tayi kaman zai katse sanan ta dauka, ahankali tace "your pancake is ready kazo kaci kaji" murya chan kasa yace "I can't come Baby am sick" wani irin faduwa gabanta yayi da sauri tace "subhanallah menene Ya Aliyu meke maka ciwo?" murya chan kasa yace "just stomach ache, ki kawomin naci am so hungry" da sauri tace "okay halama yunwa ne yasa stomach kema ciwo, yau kadade bakai breakfast ba, sorry kaji" tafada cikeda tausayin shi tareda katse wayan ta ijiye kan dinning, tashi tayi tai kitchen tadauko plate da kuma karamin plate tadawo tarufe pancake din sanan tarufe mug din, tadau hijabinta dake kan kujera tasaka sanan tadau tray tafita, slippers tasaka tasauka kasa tai hanyar flat dinshi gabanta nafaduwa sosai, sallama tayi ganin babu kowa afalo sai TV dake aiki a tachan ball yasa tai hanyar bedroom dinshi gabanta nafaduwa still, ahankali tai knocking muryanta nadan rawa tace "U...uhm Ya Aliyu nine, nakawo ma kana ciki in shigo?" murya chan kasa kaman wanda ke shirin suma taji ance yes, ahankali tabude kofan, dakin duhu bamata iya ganin ciki sosai kodan sabida tafito daga rana ne oho, maida kofan tayi tarufe tanadan kyafkyafta ido dan bata gani sosai tace "Ya Aliyu bangani sosai" dan shiga dakin tayi kaman 3 steps sanan ta tsugunna ta ijiye tray abincin awurin tamike tsaye tana tattaba bango kokarin neman switch din kunna wutan dakin danso take taganshi ta bala'in damu, hannun mutum dataji kan waist dinta tacikin hijabi yasa da sauri ta saki hannunta tajuyo azabure dan ta tsorata, kafin ma tasan meke faruwa taji an daga hijabinta sama an shige ciki anwani irin rungumeta da karfi ana nitsar da fuska a kirjinta, wani irin faduwa gabanta yayi sabida yanda taji ana mata gashi jikinshi zafi kaman wuta, da sauri tashiga tureshi tace "Ya Aliyu me haka kasakeni? Baka da lafiya jikinka mugun zafi" make mata kafada yayi yana kara tura kanshi akan boobs dinta yasa hannu ya yaye hijab dinta duka ya yar akasa, sosai jikinta yahau rawa tama rude tasa hannu tana ture kanshi daga kirjinta tana gab da sakin kuka tace "dan Allah Ya Aliyu kasakeni naje nakira maka Abba akaika asibiti wlh bakada lafiya kaji" da muryan shi data shake sosai yace "please Anebaby let me play with you cikina, my stomach hurts badly, it will stop idan nayi, you are my wife u are all I got" da sauri ta girgixa mai kai tace "a'a wlh kasaken ni am not your wife" ahankali yake running hand dinshi abayanta harya sauke kan hook din bra dinta tabaya ya shiga kokarin cirewa, cikin wani irin mugun rudewa takira sunanshi "Aliyu! Ya Aliyu stop am not ur wife, kaga karkaja najimaka ciwo, I don't wanna hurt you kasandai bakada karfi ko" kokarin cirewa dataji yanayi kaman baimasan metagama cewaba yasa ta tureshi daga jikinta da karfi baya yayi tangal tangal kaman zai fadi hakan yasa da gudu tajuya zata fita wani irin fizgota yayi yasake shigewa jikinta tareda sakin mata kuka ahankali akan kirjinta yace "please Aneesa lemme touch your breast, please kinga bantaba ganinsu ba, please wlh dazaran nataba zan barki kitafi babu abinda zan miki I swear, please lemme touch your boobs" yanda yahaukace mata ya rirriketa gam ko motsi bata iyawa yana mata maganganun banza da bamataso taji yana mata kuka yasa tasaki salati. "innalillahi, Ya Aliyu, you are not my Yaya Aliyu danake so, bakai bane, kasa ke ni wlh kona wanka maka mari banza kawai!!!" bamatsan lokacin data zageshi ba tsabagen mugun haushin dayabata, ba karamin tabashi zagin datamai yayiba cikin muryan kuka sosai ahankali yace "nine banza Aneesa?" cikeda tsiwa tace "yes, kai banza ne, in fact you are very very stupid, how dare you took off my hijab and try to touch me eh? Common ka sakeni kona mugun tsinka maka mari kazaci niyar iskace dat u can do anyhow dani, banza kawai, dalla chan kasaken stupid boy, banza kawai" ahankali yasaketa dan zagin yamugun shiganshi baitaba zaton zata iya zagin shi hakaba no matter what, kwanciya yayi ahankali kan gadon yajuyamata baya yarike cikinshi dayake ji kaman zai fashe yasa dayan hannu yana goge hawayen dake zubomai, wani irin mugun tsaki taja ta kunna bedside lamp, dakin yay dan haske hijabinta tadauka daya yarmata akasa tasaka tanajin yanda yake fitar da sautin kuka chan kasa dahar zuciyanta takejin yanda yake kukan amma haushin shi ya rinjayi tausayinshi tajuya tafita daga dakin da sauri saikuma tasa gudu tabude kofa tafita daga flat dinshi da gudu tai flat dinsu sai dakinta kan gado tafada tasaki kuka sosai......

Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, pay aduniya or pay alahira🤷🏿‍♀️ duk wacce ta watsamin book waje batare da izinina ba ban yafemiki ba har abada.


Yakai almost 30min yana kuka, ya tsani raini, ya tsani zagi, and abinda Aneesa tamai yau is a total raina, _Banza kawai, you are very very stupid, zan tsinka maka mari, zan mugun tsinka maka mari stupid boy_ duk shi kadai tama uban zagin nan, jin kanshi na neman fita yasa yatashi da kyar ya lallaba yadau paracetamol dake kan side drawer shi ya balla ya jefa abaki sanin babu kyau shan kagani babu komi acikinshi yasa yamika hannu yadauki coffee data kawomai dake kan tray dudda baiyi niyyan cin abincin ba yakafa abaki daga kwancen dayake saida ya shanye duka sanan ya yar da cup din kasa, yaja bargo yana lullubewa dan bala'in zazzabi da ciwon cikin fitina ke nukurkusan shi kaman zai mutu.






_next page, anjima da magrib, in sha Allah_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣5️⃣






Ko minti biyar baiyiba yawani irin yaye bargon da sauri yatashi zaune sabida jidayayi kaman hanjin cikinshi na harhardewa tundaga wuyan shi har zuwa cikinshi zafi yakemai kaman an watsa garwashin wuta akansu, wani irin kara yayi yana juyi "ahhhh" yajuya yana nukurkusu yana nishin azaba, azaban dayakeji yawuce misali, goran bottle water dake kan side drawer dinshi ne yadauka yabude ya kurba ko ya ragemai ciwon kaman yazuba gishiri a ciwo haka yaji hakan yasa yawani irin bankare yana ihu yana lankwashewa......





Shigowa gidan Nazif yayi yay parking motarshi Mama dahar lokacin ke jikin window tana kallon komi dake faruwa na tsakar gidanne gabanta nafaduwa tana addu'a Allah yabata nasara ne tabude kofa da sauri tamai alamu da hannu daya yakarso da sauri, karasowa yayi kafin ma yay magana taja hannunshi suka shiga dakin tamaida kofan falon tarufe, hada ido yayi da Rauda dake zaune da kanninta suna kallon cartoon, daure fuska tayi kaman batasan shiba dan ta mugun tsananshi yanzu, hararanta Mama tayi tace "bance ki cinyemin d'a da idanunki dasukai kama dana ubanki ba mai bakin hali kawai, common tashi kifitan min daga flat, wuce kitafi wurin Yayan ki mayya nasan abinda kikeso kenan" da sauri Rauda ta kalleta dan bata yadda da abinda taji Mama tafada yanzun nanba, anya Mama ce zata turata wurin Ya Aliyu willingly kuwa?, cikin daga murya da masifa Mama tace "kindaiji menace ko, tashi ki barmin daki kiwuce wajen Yayanki magana zanyi da Nazif mai mahimmanci" dawani irin gudu Rauda tai tsalle ta mike tsaye tai hanyar fita Nazif yabita da kallo, cikin rawan jiki Mama tace "kai yanzu ba lokacin kallon Rauda bane wani muhimmin abu nikeso kamin yanzun nan muje kaga" sama tai dashi wani dakin Dady tabude ta shiga yana biyeda ita tasa Hajar gadi afalo dazaran taga Abba kokuma Rauda tafada mata kota mata signal.......



Sallama Rauda tai a part din Aliyun jin shiru yasa tabude kofa ta shiga abinta ta maida kofan tarufe tana hararan TV dake aiki a tashan kwallo tace "shi ya Aliyu kullum, kullum ball, ball ball uhm" tai maganan tana daukan remote ta chanza channel zuwa cartoon ta ijiye remote din tai hanyar bedroom dinshi tana kwalmai kira. "Ya Aliyu, Ya Aliyu kana bathroom ne? Ya Aliyu" agaban bakin kofanshi ta tsaya tai knocking jin shiru yasa tabude ahankali dan tasaba shiga dakinshi kai tsaye daman kuma baya hanata, dayake itama daga rana take batagani sosai dudda bedside lamp dinshi akunne yake, ahankali tadaga hannunta zata kunna switch din wutan dakin tace "bacci kakene Ya Aliyu?" kunna wutan tayi dakin yay haske, idanunta ne suka sauka kan Aliyu dake kasa yana wani irin mimmikewa kaman wanda ake zarema rai idanunshi na juyawa, harshen shi yafito daga bakinshi wani irin kumfa nabin gefen bakin nashi, wani irin talo idanu waje Rauda tayi tana kara kallon Ya Aliyu danta tabbatar shine koba shi bane yana sanye da dogon jeans dinshi blue jikinshi ba riga lying on the floor yana fizge fizge jijiyoyin wuyanshi dana fuskanshi sun fito tsabagen yanda yake stretching din azaba, wani irin ihu Rauda tayi da saida gabaki dayan flat din Aliyu ya amsa. "Ya Aliyuuuuuuuu!" da gudu tai kanshi ta tsugunna agabanshi tana tabbatashi bama tasan metake yiba. "Ya Aliyu, Ya Aliyu, Ya Aliyu menene menene wanan sabulu kasha ne?" ganin Aliyu baimasan waye akanshi ba kakkari yake yana har yanzu harshen shi awaje bakinshi nafitar d kumfa yasa tai wani irin jumping tsaye tama rasa mezatayi da gudu tafita tana kwalama Dady kira da duka muryanta. "Dady, Dady, Daddy Ya Aliyu" yanda take kwalama Dady kira zaka zaci ta haukace ne da gudu tai flat din Dady hannu ta daura kan handle ta shiga murzawa amma kofan a kulle hakan yasa tasa duka hannayenta ta shiga bubbugawa tana kwalama Dady kira. "Daddy, Dady, Dady Ya Aliyu, Dady ya Aliyu zai mutu wlh, wayyo Allah Ya Aliyu Dady"

Kaman daga sama Dady yaji ana bubbugawa kofa ana kiranshi da sunan Ya Aliyu dayake suna bedroom ne saisa basujiba, Ammi ce ta tureshi tace "subhanallah, Alhaji Aliyu, tashi muje muga" da sauri Dady yadagata yadau boxer shi yazura tareda daukan jallabiyan shi yasa yay sitting room dinshi da sauri, doguwan riga ta Ammi tazura tareda saka hijabinta tabi bayan Dady da sauri, daidai Dady yabude kofa, da sauri ya tare Rauda dake neman zubewa muryanta harya shake tsabagen yanda take kwalamai kira, da sauri yace "subhanallah bani ruwa Ummu Aliyu" da sauri Ammi takoma ta dauko ruwa tabude mai tabashi karba yayi zaibama Raudan ta karban da hannunshi ta hanyar mikewa daga jikinshi tamai pointing flat din Aliyu tana haki tace "D....Da...dy, Ya....Y....Al....yu mutu, mutu zai mutu" arude Dady yace "w..... Wat? Meya sami Aliyu na?" kasa magana tayi dan her heart is beating way too fast zaunar da ita yayi a wajen yace "jikina yabani ba lafiya zauna da ita anan Ummu Aliyu, bari nadubo Aliyun" da dan gudu gudu sauri sauri Daddy yay flat din Aliyu tareda tura kofan yana kiran Aliyu. "Gadanga na, Gadanga na kana ina? Meya hadaka da Raudan ka

Please Login or Register in order to submit comment